Hausa NovelsMusabbabi Book 2

Musabbabi Book 2 Page 4

Sponsored Links

MUSABBABI BOOK 2
Na

HABIBA ABUBAKAR IMAM
( mrs Aliyu Mayere )

Page 4

Cikin alfarmar Allah, Afrah ta sami gurbin shiga makaranta, inda zata karanta acounting, murtala ya yi ƙoƙari sosai, domin hatta Mallam Mahmud da Inna Halima sai da suka yi masa godiya. Musaddiƙ ya ba kowa mamaki yadda bai nemi taimakon kowa ba da albashinsa ya samu ya gama yi ma Afrah duk hidimar makarantar.
Ana gobe zata fara zuwa makaranta kuwa musaddiƙ ya shigo mata da baƙar leda ɗauke da ɗinkakkun hijabai da sabbin niƙaf harda safa. Afrah jinta take kamar babu wanda ya fita sa,ar miji duk duniya, domin dai ta fahimci musaddiƙ bashi da buri sai na ya sanyata farinciki, tayi masa godiya mara adadi, haka zalika ya ƙara shiga ranta fiye da tunanin me tunani, soyayyarsa ta ƙara kamata bata da wani buri itama da ya wuce ta gan shi cikin farinciki da kwanciyar hankali gami da nutsuwa.
Komai yana tafiya yadda mafarkin Afrah ke nuna mata, abubuwan da bata taɓa zaton zata same su nan ta kusa ba. A ranar da zata fara zuwa makaranta ta shiga ɓangaren Haj kilishi domin ta dubata da jiki sannan kuma ta gaya mata batun fara zuwanta makaranta kamar yadda musaddiƙ ya yi mata umarni wanda ba don haka ba ba ta yi niyyar shiga ba balle ta gaya mata komai, tunda dai don ta ciwon da take yi ne abin yq kusa zama jiki.
Yau duka Hassana da Hussaina ne a gidan suna jinyarta tare, Afrah ba tayi mamakin ganin Hussaina ba, tunda musaddiƙ ya kirata a waya ya yi mata tatas akan taƙi zuwa ta gaida mahaifiyarta sai taga dama sannan zata leƙo sau ɗaya, tana ganin dalilin da yasa ta zo ta zauna kenan yau.
Daker Haj kilishi ke ciɓa ƙafarta tana bin bango ta fito daga banɗaki, cikin gajiya ta faɗa kan gado ta ɗan kishingiɗa gami da ɗage ƙafafuwan nata da suke yi mata azaba tamkar zasu bar jikinta.
Afrah ta yi mata sannu, sannan ta sanar da ita maganar fara zuwa makarantarta.

Tamkar an watsa mata garwashin wuta, ta dubeta da birkitattun idanunta da babu komai a cikinsu sai tsananin ƙiyayya da tsana, sun kaɗa sunyi jawur, murya a cushe tace “To zaman aure za kiyi ko yawon zuwa makaranta?”, Afrah ta dubeta lokaci ɗaya ta miƙe ta gyara zaman niƙaf ɗinta a fuska, sannan tace “Duka zanyi, in sha Allah da taimakon ubangijina”, tana gama faɗin haka ta juya gun su Hassana tace “Allah ya bata lafiya, Hassana ni na tafi makaranta”. Duka su biyun su ka haɗa baki su kace “Allah yasa a fara a sa’a”, cikin jindaɗin addu’ar Afrah tace “Amin nagode”. Dagananan a gaggauce ta fice.
Haj kilishi ta dafe ƙirjinta da hannu ɗaya sannan ta maida idonta ta rufe, wani abu ke yi mata yawo a duka sassan jikinta mai matuƙar zafi da ƙuna.
Karo da dama kenan da ta yi tunanin menene ya hana Haj Rakiya zuwa yau da wuri tana matuƙar son yin magana da ita, ta buƙe idanunta ta janyo wayarta a karo da dama ta ƙara kiran wayarta amma wayarta na kashe, ta maida wayar a hankali ta aje ta na saukar da numfashi.
Afrah zata cigaba da karatu idanunta zasu ƙara buɗewa, zata kara fahimtar komai, a hankali wata magana da boka mai Rakwacam ya taɓa gaya mata ya faɗo mata a rai, “ idan ki kayi wasa wannan yarinyar itace zata zama sanadiyyar tonuwar dukkan asiranki”. Gabanta ya ƙara faɗuwa, tabbas alamu sun fara nuna haka, amma bata isa ba zata yi yaƙi da Afrah ko da zata rasa makaman yaƙin, ba zata taɓa yarda Afrah ta kaita ƙasa ba.

Afrah bata samu wata matsala ba a makarantar saboda ta saba mu’amala da mutane,ta cigaba da kare kanta da mutunta kanta, musamman irin shigar da take yi,dole duk wani me mutunci ya mutuntata mara mutunci kuma dole ya yi shakkar takata. Sai dai ta fahimci ba zata iya haɗa karatunta da koyarwar islamiyya ba, saboda wani lokacin yana haɗuwa da dai dai zuwa makarantar ta, don haka dole yasa ta aje koyarwar ba wai don tana da zaɓi ba.
Aje koyarwar kuwa sam baiyi ma ya sayyadi Habib daɗi ba,
Amma babu yadda ya iya tunda cigaba Afrah ta samu, kuma yasan babu abinda yake so irin cigabanta, yasan burinta akan karatu, don haka sosai ya tayata murna tare da yi mata fatan alheri, ya kuma sanar da ita ƙofarsa a buɗe take a duk lokacin da take buƙatar tallafinsa, ya kuma ƙara tabbatar mata da cewa kullum musaddiƙ na cikin addu’arsa da yara sauran ɗalibanta, in sha Allah yadda rayuwa ta fara yi musu kyau haka zata cigaba har zuwa lokacin da Allah zai kawo ƙarshen komai, sai da har cikin zuciyarsa yasan sunyi asarar malama mai ɗimbin sani da kaifin tunani sama da shekarunta, zahiri Afrah babu abinda zata ce da ya sayyadi domin shi ɗin mutumin ƙwarai ne, samun irinsa sai an tona, daga masoyi ya zamar mata yaya mai kula da lamuranta.

Sosai Afrah ta dage da yin karatu domin tasan dama sau ɗaya take zuwa a rayuwa, duk kuma wanda ya sami dama bai kamata ya yi wasa da ita ba. Tana kuma son ta zama abin alfaharin musaddiƙ, ta gefe ɗaya kuma bata taɓa ɗaga ƙafa wajen cigaba da yi ma mijinta addu’a ba kamar yadda ba ta ɗauke zargin Haj kilishi a cikin zuciyarta ba, sai dai ta bakin Inna Halima ne tunda bata da wata shaida dole ta rufe bakinta ta cigaba da yin abinda ta ga ya kamata wato cigaba da yi masa addu’a tare da karanta masa ayatul sihir kullum yama sha kamar yadda ta saba, addu’a takobin mumini ce don haka tana da yaƙinin zata sami dacewa komai daren daɗewa.

Wannan makon Alh yusuf sanda ya dawo, sai dai duk yadda Haj Hudah ta matsama zuciyarta ta jidaɗin dawowarsa ta kasa, yadda take ɗokin ya dawo wannan karon komai ya canja, asalima gata ga shi amma wani al’amari me dasa tashin hankali a gareta shi ne yadda suffar musaddiƙ ke bayyana a cikin idanunta, hatta sha’awa irin ta aure babu a tare da ita nasa, duk iya daɗewar da ya yi bata jin wani shauƙi na son kasancewa tare da shi, shin wannan wace irin masifa ce ta yanko ta faɗo mata.
Karfe ɗaya da rabi na dare ne, Basu daɗe da gama aiwatar da sunna ba, sai dai duk cikinsu babu wanda ya samu wani gamsuwa, adalilin kowa ya yi ne cikin rashin jinfaɗin zuciya, a hankali Haj Hudah ta jiyo da kanta tana kallon Alh yusuf sanda wanda idonsa ke rufe, a ganinta baida wata matsala da alama har ya koma bacci, a hankali ta zare kanta daga cikin bargon ta zuro ƙafafunta ƙasa ta miƙe, ta lalubo doguwar rigar baccinta ta sa, a hankali ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita zuwa falo, ta nemi ɗaya daga cikin kujerun ta zauna gami da sakin wata ƙatuwar ajiyar zuciya ta runtse idanunta gaba ɗaya, hawayen da take ƙoƙarin hana su sauka sune suka fara fita daga kwarmin idanunta.
A hankali Alh yusuf sanda ya buɗe idanunsa yana jinjina kai, lokaci ɗaya shi ma ya tashi ya gyara kayan dake jikinsa, sannan ya taka a hankali zuwa bakin ƙofa, ta saman ƙofar inda aka bar ɗan rami wanda kana iya ganin mai shigowa ɗakin, anan ya tsaya ya ɗora idonsa akai, hakan ya bashi damar hango Haj Hudah tana sharar hawaye, lokaci ɗaya kuma ta buɗe wayarta ta fito da ɗaya daga cikin hotunan da aka ɗauke su tare da musaddiƙ da sauran jami’an tsaronta a lokacin wani taro da suka je aka ɗauka.
Duk da Alh yusuf sanda baisan abinda take kallo ba a cikin wayar, tunaninsa tuni ya tafi inda ya karkata.
Haj Hudah ta ƙurama faffaɗan ƙirjin musaddiƙ ido, nan mafarkinta yake son ta kwanta, ta dubi dantsensa me alamun ƙarfi da nagarta irinta ɗa namiji, nan ma ji tayi tsigar jikinta na tashi, ta dawo da kallonta kan lallausan sajen fuskarsa da ya kwanta luf baƙi sidiƙ, ta lumshe ido tana jin wani irin sonsa yana fisgarta kamar yadda mayen ƙarfe ke fisgar ƙarfe.
Ta kai hannu ta shafi bakinsa ɗan matsakaici, duk da dariyar da ya yi a waya baisa bakinsa ya faɗaɗa ba.
Idanunsa masu cike da gaskiya, da son ganin kowa cikin farinciki, ta ƙara zubama ido, musaddiƙ baida makusa, shin ya zata yi ta yaƙi zuciyarta daga son musaddiƙ da tasan masifa ce a gareta, lalle wannan yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa addinin musulunci ya hana keɓencewa tsakanin mace da namiji da ba muharraman juna ba sabida fitintunun da hakan ke haifarwa.
Hakika da tasan inda labarin zai kaita da bata ko yarda ta haɗu da musaddiƙ ba balle harta faɗa cikin wannan masifar, tunda ta gane tana sonsa take ƙoƙarin yin yaƙi da zuciyarta domin ta cire sonsa a ranta amma abin ya faskara, ta yi yunƙurin daina ganinsa don har hutun kwana bakwai ta bashi amma a daddafe ta iya kwana biyu bata ganshi ba, da kanta ta kira shi tace ya dawo bakin aikinsa, to ta ya ya ta ina zata iya fita daga wannan ƙangin.
Kawai ji ta yi ta ƙara rushewa da kuka tasa hannu ta toshe bakinta gudun kada sautin kukan nata ya taso Alh yusuf sanda.
Sai dai abinda bata sani ba shine babu abinda bai gani ba, cikin wannan murmushin nasa ya juyo ya jingina jikin ƙofar ya haɗe girar sama da ta ƙasa, kai kace abin da ya gani ya dame shi, amma kawai daga bisani sai ya bushe da dariya sosai ya taka da ƙarfinsa ya koma kan gado ya kwanta ya janyo bargo, babu damuwa ko kaɗan a tare da shi, sai ma wani nishaɗi da ya ji yana yi, yana kuma fatan a cigaba da tafiya a hakan. Ya yi tunanin yadda yaga mugun canji daga Haj Hudah tun kafin ya dawo, yanzu kuma bayan ya dawo ya ƙara fahimtar canjin da tayi ya wuce ma yadda ya yi tunani, sai dai ko ajikinsa.Baccinsa ne mai daɗi ya yi awon gaba da shi tabbatar da gaske baida damuwa akan ko ma wace matsala matarsa ta ke ciki.

Cigaba da karatun Afrah fa ya ƙara dagulama Haj kilishi lissafi, malaman bogi uku Haj Rakiya ta ƙara samowa inda suke gudanar da kasuwancinsu cikin kwanciyar hankali, domin dai Haj kilishi kuɗi kawai take fitarwa domin biyan buƙatarta, wata rana idan ta ji ɗan sauƙi suna tafiya tare, ko kaɗan bata taɓa sawa a ranta wai Haj Rakiya zata iya cutarta ba ko cin amanarta ba, hakan yasa hankali kwance take wadata ta da komai, hatta ciwon da take yi yanzu neman taimako take yi akansa, Haj Rakiya kuwa harka ta buɗe.
A wannan tsakanin Afrah ta fara jin ciwo me tsanani a cikinta, tana matuƙar daurewa domin bata son musaddiƙ ya sani balle ya tada hankalinsa, sau tari wani lokacin a makaranta sai taje wajen shan magani ta karɓi maganin ciwon ciki ta kan kuma kwanta anan wani lokacin harta rasa lectures, ciwon na damunta, nan da nan ta fara ramewa, wanda ko musaddiƙ ya tambayeta meke damunta ne takan nuna masa karatune kawai ya sata gaba.
A yau kuwa tun safe Haj Rakiya ta nufi rugar mai Rakwacam bisa umarnin Haj kilishi domin ta karɓo maganin da ya debi kwanaki yana haɗawa na ciwon Haj kilishi, sai na ɓangaren musaddiƙ da Afrah amma wannan karon shi ma shirmensa kawai ya haɗa tunda ya fahimtar da ita asalin gaskiyar, Afrah da musaddiƙ na cikin kariya da katangewar ubangiji babu wani abu da zai iya cutar da su, amma ta dage dole asamo wata mafitar shi yasa tunda ba ya son rasa kwastama yasa ya fara yi mata aliya acikin aikin,
Rana fatsar fatsar ta isa rugar, amma wani abun tashin hankali, a wajen bukkar mai Rakwacam ta tadda mai Rakwacam ɗin an kwantar da shi a cikin wannan zazzafar ranar, akan tabarmar karauni, gefensa wasu tsoffi ne guda biyu marasa ko kyan gani, ɗaya gefensa matarsa ce domin Haj Rakiya ta santa sosai wani lokacin ma hannunta suke karɓar magani idan yq bar mata ajiya baya nan, duk ta kwantsame ta buga tagumi hannu biyu, idanun Haj Rakiya yana ɗore akan mai Rakwacam tana ƙoƙarin gano abinda ke faruwa.
Idonta ya sauka akan cikinsa da ya yi ƙato tamkar mai shirin haihuwa ko yau ko gobe ya, idanunsa duk da suna rufe su ma sun kumbura matuƙa sun ɗago sosai kamar zasu fito waje, ta fahimci hatta numfashi wahala yake yi masa, ta matsa a hankali wajen matarsa tana kallonta cike da kaɗuwa tace “sannu dai”, ta ɗago ta yi mata kallon tsaf sannan ta amsa a hankali, “ sannu ka dai”, ta ƙara kallon mai Rakwacam tace “ me ya sami boka ne, na ganshi a haka”.
Ta aje wata nannauyar ajiyar zuciya cike da ɗimbin tashin hankali da fargaba tace “Azal ce ta faɗo masa, tun jiya da daddare yana kan yin wani aiki kawai aka yi wata irin tsawa ta kuma faɗa masa, tun cikin daren a haka yake bai ko yin motsi ga ciki ya kumbura ga idanu duk sun fito daker muka iya rufe masa su, amma kinga harshensa har yanzu a waje yake duk ya zaro mun rasa yadda za’ayi ya koma”, ta juyo ta nuna tsofaffin dake tsugune gabansa tace “ Tun daren muke kiran abokan aikinsa bokaye yan’uwansa amma babu wanda ya iya tsinana masa komai, waɗannan su ma gawurtattun bokaye ne amma tun asuba suke gabansa har yanzu sun kasa yin komai, na karaya domin na yi imani wannan daga Allah ne”.
Taga taga Haj Rakiya ta yi kamar zata faɗi saboda kaɗuwa da razana, ta kasa cewa uffan sai ido da ta ƙara ɗorawa mai Rakwacam tunani ya cika zuciyarta lalle wanda suka kauce hanya suna zuba kuskure a rayuwarsu, yau ga mai Rakwacam ko kansa bazai iya taimaka ba balle ya taimaki wani. A gaggauce ta bar gidan ba tare da ta ƙara tofa wata magana ba. Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, sakayya ce Allah ya fara yi ko yaushe ta su sakayyar zata zo oho?, tunanin hakan yasa Haj Rakiya ƙara tsorata da kaɗuwa, ta firgita tsoron Allah ya kamata jikinta har rawa ya ke yi. Haƙiƙa a yau ɗin nan ba don tana da wata manufa ba da daga nan kai tsaye bakin kuka zata dire ta tone asirin da aka yi ma musaddiƙ, ta kuma nemi gafarar Allah tun kafin ya yi mata kamun huhun goro.
Amma ina tana da abinda da take son cimma, gidan da ta fara ciniki take son ta gama samun kuɗin a jikin Haj Kilishi da zaran kuwa wannan burin nata ya cika zata fasa baragurbin ƙwan komai warinsa.
Cike da tashin hankali ta isa gidan Haj kilishi mai taxi yana tsaida motar, wani a daidaita sahu yana tsayawa a gaban gidan, a hankali cikin galabaita Afrah ta fito daga ciki, daƙer ta iya bashi kuɗinsa ya karɓa yana cewa “Allah ya sauwake”. Da sauri Haj Rakiya ta fito daga cikin motar dama ta riga ta biya shi kuɗinsa don haka da sauri ta yi wajen Afrah da take neman faɗuwa ta tarota ta rungumota zuwa jikinta, “ Afrah lafiya me ke damunki”, ta kasa magana sai cikinta da take dafe da shi. Tuni Haj Rakiya ta fahimci ba ta da lafiya ne, don haka ita tq riƙeta da jakar ta ta makaranta zuwa cikin gidan, ganin halin da Afrah take ciki yasa damuwa ta cika masa zuciya ya bisu har cikin bsngaren Afrah yana son sanin abinda ya faru, musamman da ya ganta da Haj Rakiya, sam mutanen nan bai yarda da su ba, kamar Haj Rakiya ta fahimci abinda ke cikin zuciyarsa yasa ta yi masa bayanin komai, Afrah tana kwance tamkar matacciya saboda galabaita, Haj Rakiya ta bi shawarar maigadi inda ta ɗauki wayar Afrah ta kira musaddiƙ bugu ɗaya a cikin na biyu kamar yana jira ya ɗauki wayar.
Jin muryar Haj Rakiya cikin damuwa ya gigita musaddiƙ ya shiga tambayarta ina Afrah, a gaggauce ta gaya masa halinda take ciki, bai gama jinta ba ya kashe wayar ya miƙe a gaggauce yana fitar da numfashi, Haj Hudah ta bi shi da kallo yadda ya gigice yasa tace “ meke faruwa ne”, murya na rawa yace “ Matata ce ba lafiya, zan tafi gida na kaita asibiti”, kafin ta yi magana tuni ya buɗe ƙofar motar ya fice bai saurari komai ba ya buɗe get ya fita, cikin mugun yanayin da Haj Hudah bata taɓa ganinsa a ciki ba.
Ta saki baki tana kallon ƙofar get ɗin, wani irin takaici ya kamata, karo da dama kenan da ta ji haushin Afrah, wannan karon ma har da wani abu mai kama da tsana. Ƙarya kawai ta yi ma musaddiƙ na cewa akwai inda zasu amma gaskiyar magana yau so kawai ta zauna tare da shi a keɓaɓɓen wajen da zata su daɗe zaune tare tana jin sautin muryarsa, amma Afrah ta rushe mata jin wannan farincikin na yau, ji tayi hawaye ya cika zuciyarta, direban ya juyo yace “ haj mu tafi ne”, ta girgiza kai a sanyaye gami da buɗe ƙofar motar ta fito, ba tare da tayi magana ba ta shige cikin gida, zuciyarta cike da duhu.

Da Taxi musaddiƙ ya ƙarasa gida, yana shiga gidan kuma bai saurari komai ba matarsa ya ɗakko cak zuwa mota, Haj Rakiya da Baba maigadi na binsa a baya, har suka bar ƙofar gidan kai tsaye asibiti ya wuce ba tare da ya jira komai ba, yana girgizata yana jin tamkar ya maida ciwon kansa, amma wani abu mafi tashin hankali Afrah ko motsi bata iyawa gashi dai tana numfashi amma babu wani ƙarfi a tare da ita, tunda musaddiƙ yazo duniya bai taɓa shiga tashin hankali ba irin na yau.
Suna zuwa asibitin gado aka ba Afrah, Allah yasa akwai kuɗi a jikinsa, da su ya yi ta biyan kuɗalen asibitin. Likitoci suna kanta domin gano abinda ke damunta, anata gwaje gwaje.

Tun shigar Haj Rakiya falon Haj kilishi take labarta mata halin da taga Afrah, sai dai bata gaya mata ta taimaketa ba asalima cewa tayi tana dawowa ta ga musaddiƙ ya tafi da ita asibiti, ba kunya ba tsoron Allah kuma ta karkace ta zubo ƙaryar cewa “ Dama Tsiduhu ya gaya min ina dawowa zan sami Afrah rai a hannun Allah”, cikin fara’a Haj Kilishi ta dubeta tace “Tsiduhu kuma? Amma kuma ai wajen mai Rakwacam na tura ki mai ya haɗaki da Tsiduhu kuma?”.
Sannu a hankali ta gaya mata halin da ta sami mai Rakwacam, dalilin da yasa kuma kenan ta wuce wajen Tsiduhu da maganar ko ciwo ne ya ɗora mata , tunda dai damuwa ake so su shiga.
Haj kilishi ta fashe da dariya harda ƙyaƙyatawa, ta miƙama Haj Rakiya hannu suka tafa, tace “Aikin ki na kyau aminiyata, kinyi dai dai nagode ƙwarai da gaske”,
Haj Rakiya tace “ sai dai kuɗin aikin da yawa don dama nace masa ba zamu ba da ko sisi ba sai aiki ya ci tukuna, kuma gashi aiki ya yi Haj”,
Ta dubeta cikin dariya tace “ Nawa yace za’a bashi, ta muskuta tace “ Dubu dari uku “, ta ce “ Ai yama yi sauƙi zan baki ki kai masa”, Haj Rakiya ta numfasa tace a ranta, a haka zan gama haɗa kuɗin gidana ba tare da kin gane komai ba. Haj kilishi tace “ shi mai Rakwacam ɗin ya ake ciki da shi”, Haj Rakiya ta taɓe baki, bata son ta gaya mata gaskiyar komai domin bata son ta karaya kamar yadda itama ta karaya, tafi son ko zata tuba ta bari sai ta gama yasheta ta gama kwasar rabonta, don haka tace “ Ke nifa sai daga baya na fahimci kamar kunyar yadda ya kasa yi miki aiki ne yasa ya ƙirƙiri wannan ciwon tunda yasan yau ce ranar da yace mu dawo”, Haj kilishi tace “ kuma fa hakane, tunda ko shi da kansa ai ya yi ma kansa aiki ya samu waraka, ni dai yau ai ina cikin farinciki rabom da ayi min irin wannan aikin harna manta lalle Tsiduhu ya haɗu”.
Haj Rakiya ta yi dariya tace “ sosai kuwa ai Tsiduhu ba daga baya ba”, ta janyo wayarta ta kira musaddiƙ, yanayin muryarsa kawai da ta ji, mai cike da ɗimbin tashin hankali da firgici, shine ya ƙara jefa mata tsananin farinciki da jindaɗi. Muryarsa na rawa sosai tamkar ma kuka yake yi yace “ Haj Afrah ba lafiya, gata nan cikin mawuyacin hali”, ta dubi Haj Rakiya tana murmushi tace “ Kayi haƙuri ka natsu zata sami lafiya, yanzu me likita yace yana damunta,” ya girgiza kai “ Har yanzu basu ce komai ba suna ta dai gwaje gwaje”, ta yi dariya sosai, sannan kuma ta shiga kwantar masa da hankali, ta kuma tambaye shi asibitin ya gaya mata, tana jin muryar Mallam Mahmud da muryar inna Halima, haka zalika tana matuƙar jindaɗin yadda take tsintar damuwa da tashin hankali a cikin muryoyinsu.
Bayan ta aje wayar ne, ta ƙara rushewa da dariya, ta tashi daƙer ta bi bango ta shiga ɗaki, Haj Rakiya ta bita da kallon takaici, a ranta tace “ zanyi maganinki”. Dubu ɗari uku da ashirin ta ɗakko ta bata, sam bata rabo da kuɗi a gida domin tasan cikin ko wane lokaci zata iya buƙatar manyan kuɗaɗe, ta karɓa ta kuma yi godiya sannan ta tafi tabar Haj kilishi cike da farincikin da ta rabu da jin irinsa.
Daga musaddiƙ har Mallam mahmud da Inna Halima sun kasa zaune sun kasa tsaye, cikin tashin hankali su ke, burinsu ɗaya su san abinda ke damun Afrah.
Amma har sai yamma sannan wasu daga cikin sakamakon gwaje gwajen Afrah suka fito.
Inda da kansa likitan ya buƙaci ganinsu a ofishinsa, gaba ɗaya musaddiƙ a rikice yake addu’arsa ɗaya ce Allah yasa ba wani mugun ciwo Afrah take da shi ba. Sai dai addu’arsa ba ta ci ba. Domin takardar da likita ya miƙo masa ta ƙarasa jefa shi cikin mawuyacin hali ya ƙurawa takardar ido, a yayin da likita ya fara bayani…………….

Yar gidan Imam✍️

Leave a Reply

Back to top button