Mutum Ko Zaki Hausa Novel
*MUTUM KO ZAKI*
*NA*
*A’ISHATULHUMAIRA*
*~Mikiya writer’s Association~*
*Page 1&2*
Gajeran labari ne.
Bismillahir Rahmanir Rahim.
______ Ni’imantacciyar iskar dake kaɗa korayen itatuwan da suke kewaye da manya manyan tsaunikan wajen sune suka bada wani kalar launi da tsari me matuƙar kyawun gaske, tsaunika ne manya manya guda biyu masu fuskantar juna kowane da irin tsarin da ubangiji yayi shi, yanayin su ya matuƙar ƙayatarwa kamar ginin manyan masarautu na ƙarnin baya. Ruwa ne me gudana babba tar-tar me kyan gaske da ďaukar hankali a tsakanin waďannan tsaunika wanda shine iyaka dake tsakanin su. Kyawun ruwan da furannin dake kewaye dashi kaďai abin shagala ne wajen kallo, daga tsakiyar ruwan wani babban dutse ne a ciki wanda ya kasance hanya ta wucewa zuwa ko wane tsauni hakan ya kara kawata wajen sosai.
Ɓangaren dama shine ke ɗauke da korayen ciyayi da flowers red da yellow masu kyau da tsari wanda suka kewaye dukkan tsaunin da ɓangaren nasu baki ɗaya. Cikin tsaunin kuwa wanda girman shi da faďin shi ya wuce tunanin me tunani yake ɗauke da part-part ma banbanta da unguwan ni wanda mutanen dake rayuwa wajen ne suka sassaƙa shi suka yi muhallin zama a ciki.
Kasancewar basu da wani yawa domin ba zasu wuce mutane ɗari biyu ba hakan ya taimaka masu wajen kayata wajen ainun . Irin bishiyu da furanni dake wajejen ya ƙara ƙawata tsaunin wanda in ka shiga ba zaka taɓa cewa a cikin tsauni ka ke ba saboda tsananin kyansa, ɓangaren shakatawa da wajen swimming pool ɗin su kuwa yayi bala’in haɗuwa ga wasu kalan furanni da suke kewaye da ruwan baka taɓa cewa a cikin tsaunin yake.
Yayin da ɓangaren haggu kuma yake ɗauke da ciyawo da red din flowers gaba ɗaya masu kyau da ɗaukar hankali, cikin tsaunin babban fili wanda yake kamar babban falo ko masarauta ɗauke da wasu irin ciyawu masu laushi sai gefe manyan kofofi ne da ƙanana masu wani irin ado me daukar ido har zuwa can saman tsaunin. Tsarin cikin yayi matuƙar kyau da tsari bazaka taɓa tunanin manyan Dabbobi ne ke rayuwa a
Ciki ba.
Ta kowane ɓangare suna zaman lafiya da juna sai dai wani babban al’amari daya gifta tsakanin su na neman kawo masu ƙalubale babba wanda hakan ne ke assasa lamarin, sai dai kuma alƙawarin dake tsakanin su na neman dakatar da komai dake shirin faruwa.
Asalin labarin……..
Garin kathub babban ƙauye ne wanda usulin larabawa matafiya da dabbobin su suke zaune a cikinsa, cikin daji ne sosai hakan yasa rayuwarsu su kaɗai suke yinta babu me zuwa inda suke sai masu fita karatu duk Wanda ya taso in bai son fita karatu anan zai rayuwarsa har aure. Suna noma amma basa siyar wa babu abinda basa nomawa tunda ga kan kayan marmari har zuwa hatsi komai suna dashi na more rayuwa ɓangaren cima, abubuwan zamani basu damu dasu ba domin kuwa ko ƴaƴan su suka fita karatu anan suke dawowa domin amfanar da sauran yan uwansu ilmin su, da haka ne har da yawansu suka zama wasu a cikin ƙauyen suka buɗe makarantu da asibiti da masallaci basa zuwa ko ina, babu irin karatun da basu dashi domin kuwa zakayi mamaki idan kaje ƙauyen . Sun samu cigaba sosai inda har suka fi wasu state din kasashen dake makwabta ka dasu.
Akwai yan ƙasar Egypt sune suka haɗu dana Saudi Arabia suna ta tafiya har suka yada zango a ƙurmin dajin da su kansu basu san wace ƙasa bace domin ko turawa masu zuwa yawon buɗe ido basa shiga wannan daji .
Rayuwa suke tamkar yan uwan juna sun haɗe sun zama tsintsiya ma ɗaurinki daya, kansu haɗe yake haka ma kan yaransu haɗe yake babu banbanci, kwatsam wata rana aka yo masu turen sojoji suka buɗe masu wuta ta ko ina ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba sai dai abin yazo masu da sauƙi kasancewar sun ma garin kafi sosai ta yadda babu me iya shiga ciki sai ɗan garin. Ganin da gaske ba kyale su za’a yi ba yasa yah Kathub haɗa zama da manyan garin. Kathub ya kasance shi yafi kowa shekaru a cikin manyan garin kuma yafi kowa manyan yaya shiyasa suke girmama shi da maganar sa shine shugaba a wannan ƙauye mafarin da suka saka ma garin *KATHUB* . Bayan kowa ya hallara ne ya fara masu bayanin abinda ke shirin faruwa dasu duk da sun sani, mafita suka fara nema ma kansu sai dai sun fara tunanin tunda aka san dasu a wajen baza’a barsu su zauna lafiya ba dan haka suka yanke shawarar ƙara ma garin kafi sosai ta yadda har su gama shirin su na tashi baza a cin masu ba . Haka Kuwa akayi nan da nan aka sanar da kowa suka fara shiri tafiya manyan gari kuma suka cigaba da sa kafi gaba daya kewayen garin.
Watan su ďaya suka kammala duk wani shiri nasu suka fara shirin tafiya, can cikin dajin suka kara nutsawa mai makon su fito, sunyi shiri sosai na shiga babban dajin dan haka komai nasu na tare dasu saboda ba ƙaramin hatsari dajin keda shi ba, akwai manyan namun daji bila adadin da aljannu shiyasa shirin su ya kasance na musamman. Sunyi tafiya ta kwana biyu kafin suka fara hango wasu manyan tsaunika guda biyu masu girman gaske, tunda suka fara kusanto wannan tsaunika suka fuskanci tashin hankali na gaba domin kuwa wasu manya manyan halittun dabbobi ne suke tunkaro su gadan gadan
Gaba ɗaya sun kasa cigaba da tunkarar wajen sun tsaya kawai suna jiran ikon Allah……
Toh meke faruwa ne haka nace meke faruwa?
Nace kin taɓa jin irin wannan salon kuwa?
Meke shirin faruwa tsakanin waɗannan Manyan Dabbobi da kuma waɗannan mutane ?.
Shin wai wane ma irin mutane ne ma haka?
Waɗanne kalar Manyan Dabbobi ke rayuwa kusa da mutane?.
A wace duniya ce wannan abu ke faruwa?.
Shin wane alƙawari ne tsakanin su
?.
Chakwakiyar dake ciki hasashe ko dogon tunani bazai taɓa hango wa ba har sai an karanta.
Kudai ku biyo alƙalamina don jin labarin da yadda zai kasance .
A’ISHATULHUMAIRA ❤✍*MUTUM KO ZAKI*
*NA*
*A’ISHATULHUMAIRA*
*~Mikiya writer’s Association~*
*Page 3&4*
Bismillahir Rahmanir Rahim.
_____Cikin wani irin hargagi na tashin hankali Dabbobin ke ƙara tunkaro su, sai dai ko gezau basu yi ba a wajen sun tsaya tamkar an dasa su in banda addua babu abinda ke fita daga bakin su.
Suna isowa gun kayayyakin su waɗannan manyan dabbobi suka nufa kasancewar zagaye suke da dukka shanun su da raƙuma da ƙananun dabbobin su shiyasa waɗannan manyan ma farautan dabbobi basu isa garesu ba, wata irin girgiza tare da wani kuka babban zakin cikinsu yayi wanda da gani shine shugaban su , nan take duk sauran dabbobin suka dakata daga niyyar fara kai ma mutanen farmaki. Zagaye mutanen zaki ya fara kamin ya ƙura ma yah Kathub ido saboda ganin shine gaba ya fahimci shine shugaba ga mutanen.
Kamar yah Kathub ya fahimta yayi shahada ya isa gaban zaki ya duƙa Yana kallon shi da sauran Manyan Dabbobi dake bayan Zaki sannan ya fara magana.
“” Dan Allah ayi mana afuwa mun shiga in da ba muhallin mu ba a gafarce mu, hanya ce ta biyo damu nan bada san ran mu ba, tada mu akayi daga wajen da muke rayuwa mafarin isowar mu nan kenan”.
Tsit wajen yayi babu wanda yayi motsi mutanen wajen banda addua babu abinda yake bakin su, yayinda waɗannan manyan dabbobi a harzuƙe suke jira kawai suke a basu umarni su ida kai farmaki ga mutanen.
Sai da Babban Zakin ya gama kalle kowa sannan ya juya zai koma sai dai karar takun dabbobin ya dakatar dashi domin sun tunkari mutanen ne da wani irin gudu, sai dai basu kaiga cimmasu ba Babban zakin ya juyo da mugun hargowa hakan yasa duk suka tsaya suna ja da baya. Dawowa yayi ya iso gaban mutanen kafin ya kalli sauran yan uwanshi dabbobi yayi masu alamar da su suka fahimta nan da nan kowa ya koma bayan shi sannan wata babbar zakanya ta iso kusa da Babban Zakin takai fuskanta dai-dai tashi fuskan kamar masu raɗa a hankali kuma ta koma baya sai ga Giwa ta fito itama ta kwanta gaban zakin sannan ta miƙe ta nufi babban tsaunin nasu. Bata dade ba ta dawo dauke da wata tsohuwar mujallah nan naɗe da bakinta ta iso gaban Zakin ta aje wannan mujallah.
A hankali Zakin ya buɗe baki ya ɗauke wannan mujallah ya fara tafiya da ita har ya iso gaban Kathub sannan ya aje mai ita ya juya ya koma daidai inda yake tsaye ya tsaya.
Duƙawa Kathub yayi ya ɗauki wannan mujalla yayi bismillah ya buɗe ta, rubutu ne a jiki shafin farko da larabci sai kuma shafi na biyu akayi da turanci. Gyaran murya yayi sannan ya dubi yan uwanshi sai kuma ya kalli mujalla ya fara karantawa kamar haka:-
* *
* , , . ‘ . . , , *. * . , * . * *.
* *.
* *
* *.
* *.
* *
* *
* *
* *
* *
* *.
Kathub na gama karanta masu wannan mujallah ya juya ya kalli yan uwan shi don jin mai zasu ce saboda ya fahimci dokar su ce suka basu idan sun yadda a dajin zasu zauna .
Ba tare da dogon tunani ba ko nazari manyan suka ce ma Kathub sun amince don a gajiya suke mafaka kawai suke nema.
Juyawa yayi gasu yah Babbah yace masu.
“Mun yarda mun amince da dukkan wata doka tasu indai zakuyi mana lamunin zama a wannan daji”.
Ya miƙa mujallah ga wani gorilla babba yama tsufa. Amsa yayi ya kalli yah Babbah ya sunkuyar da kansa alamar girmamawa.
Jinjina Kai yah Babbah yayi alamar gamsuwa ya juya sauran suka bishi, shi kuma gwaggon birin yayi ma su Kathub alamar su taho suma.
Gaba ɗaya mutanen sun shagala da kallon wannan manyan tsaunika guda biyu basu taba ganin abu me kyau kamar su ba ga wannan ruwa dake tsakiyar su me bala’in haɗuwa da daukar hankali, nan da nan suka cika da farin ciki ganin sun samu inda yafi inda suka baro kyau.
Bangaren dama aka basu su zauna yayin da dabbobin ke bangaren hagu, har ciki gwaggon birin ya kaisu sannan ya fito yayi tafiyar sa. Su kuma suka ajiye kayansu suka zazzauna suna hutawa masu jin yunwa kuma suka fara ciye ciye.
Sai da suka yi kwana biyu sannan suka fara sassaƙa wajen nasu suna tsara shi yadda suke so sai da sukayi wajen sati ukku kafin su gama kowa ya kama gidan shi da unguwan shi Amma duk da haka basu ko rabin cin wannan tsaunin ba.
Gidan yah Kathub babban gida ne me dauke da manyan dakuna da babban filin tsakar gida, matan yah Kathub biyu ……
Share Fisabilillah
@A’ISHATULHUMAIRA✍❤*MUTUM KO ZAKI*
*NA*
*A’ISHATULHUMAIRA*
*~Mikiya writer’s Association~*
*Page 5&6*
Bismillahir Rahmanir Rahim.
_________ Gidan yah Kathub babban gida ne me ɗauke da manyan ɗakuna da babban filin tsakar gida, matan yah Kathub biyu uwar gidansa khairiyya tana da yara ukku duka maza na farkon Muhammad na biyu kuma Usman sai Aliyu shine auta daga shi bata ƙara haihuwa ba. Muhammad yana da mata ɗaya Khadija shekarar su biyar da aure har yanzu Allah bai basu haihuwa ba sai usman Yana da mata ɗaya zainab da ɗa ɗaya umar. Aliyu ne bai yi aure ba saboda bai dade da dawowa daga karatu ba wannan abin ya ritsa dasu.
Kulthum itace matar yah Kathub ta biyu tana da yara biyu mace da namiji zainul abeedeen da Amina.
Rayuwar su gwanin burgewa basu da wannan mahaukacin kishin nan irin mu , kansu a haɗe yake babu cuta ba cutar wa a tsakanin su kowace zaune take da yar uwarta tsakani da Allah. Ɓangaren yaransu kuwa baka iya banbance su sai ka ɗauka duk uwa ɗaya ce ta haife su, hakan yasa duk sadda zaka gansu to a tare zaka gansu yadda kasan abokai haka suke, basu iya ɓoye damuwar su ga junan su damuwar daya damuwar su ce duka. Hakan ba ƙaramin daɗi yake ma yah Kathub ba ganin yadda iyalansa kansu haɗe ko yaushe suna tare cikin farinciki.
Kasancewar Usman shine ya fara haihuwa hakan yasa dukkan su suke matuƙar ji da wannan yaro komai suka samu toh akwai na Umar a ciki.
Bikin Amina suke ta shirye shirye dama sun taho da dukkan abinda zasu buƙata na bikin wanda dama sun dade da tanadar shi bikin kawai suke jira. Haka shima wanda zai aureta ya ɗibar masu waje ya gyara masu daidai su ya kawata ginin nasu da furanni masu kyau sosai gidan ya haska.
Zainul Abeedeen kuma ba yanzu ba sai zuwa gaba zai nashi auren yace sai angama da kowa shine ƙarshe.
Aliyu dai akwai yarinyar da yake so tun tana ƙarama yake fada ga matar sa harta Ammin su (wato khairiyya ita suke kira da haka kulthum kuma suna ce mata Ummu) ta sani kuma tana goyan bayan sa domin ita kanta tana son yarinyar sosai, yarinyar ɗiyar kanwar yah Kathub ce maryam ita ta haifi fatima wadda suke kira da Zahra . Aliyu yana matuƙar son Zahra bai iya ɓoye yadda yake sonta hakan ne yasa kowa yasan shi ke jiranta kuma shi aka bama auren ta, Zahra kyakkyawa ce sosai a duk yaran dake kauyen babu wadda takai ta kyau komai Allah ya bata, haka shima Aliyu yana da wani sihirtaccen kyau na usulin larabawa. Sai ta gama karatu za’a yi bikin su lokacin tana shekara sha biyar domin yanzu duka shekarar ta goma cif. Shi kuma aliyu yana da ashirin da biyar . Baban Zahra wato sheikh Ibrahim shima ƙani yake wajen yah Kathub ta wajen kakannin su auren zumunci ne akayi masu shida maryam har Allah ya basu Zahra.
Yau suka kammala ginin asibitin su, cikin ikon Allah yau matar Muhammad wato khadeejarh ta tashi da zazzabi da amai sosai ta galabaita suka ɗauke ta zuwa inda suka gina a matsayin asibitin su nan da nan Muhammad ya fara duba matar shi kasancewar shine babban likitan kauyen nasu, yana mata awo kuwa sai ga ciki wannan shine tsanmaci abinda bakayi tsammani ba, murna da farinciki wajen wannan ahali ba’a magana kowa ka gani cikin farin ciki yake da annuri. Muhammad kam ba’a magana yama rasa ina zai sa kansa saboda murna hada hawayen shi ita kanta khadijerh tayi murna sosai ta kuma godewa Allah bisa wannan kyauta da ya mata sai dai kawaicin ta yasa ba Wanda ya gane irin farin cikin da take ciki. Ammi da ummu kam kamar su maida ta ciki don murna sai nan nan ake da ita.
Tana samun kulawa ta kowane fanni sai dai cikin yazo mata da mugun son shiga cikin dabbobi, tun dai tana daurewa harta samu Muhammad da maganar akan tana son ta fita taga dabbobin wajen. Haka ya amince mata aikuwa tayi ta murna da yamma suka shirya suka fita wajen tsaunin, suna fitowa ta lumshe idanuwa saboda dadin iskan dake kaďawa a wajen, baje hanci tayi tana shakan iskan wajen cikin shauki da farin ciki. A hankali ta buďe idanuwan ta da suke rufe ta sauke su akan tsaunin su yah Babbah.
Ba karamin kyau ta kara ganin wajen yayi mata ba, ga wannan ruwa mai tsananin kyan gaske. Haka nan taji sha’awar shiga ruwan ta tsallaka dayan bangaren.
Muhammad kam ya shagala wajen kallonta a duniya ba abinda yake kauna kamar farin cikin ta dana abinda ke jikinta ya shagala sosai wajen tunanin yadda zasu tsara rayuwar su bai ankara ba sai gani yayi ta kusa shigewa bangaren su yah Babbah kafin ya kirata ta ida shigewa nan hankalinsa ya tashi matuka ya biyo bayanta da sauri.
Tana shiga ta iske dukkan wani kalan namun daji a wajen gasu nan iri iri yah Babbah nakan munbari inda yake zama kenan kamar dai kujarar sarki alamar taro suke yi. kamar ana janta haka ta cigaba da takawa har inda suke gaba ďaya suka juyo gareta sai lokacin gabanta ya faďi ta rasa ina zata dosa ….
Share Fisabilillah *MUTUM KO ZAKI*
*NA*
*A’ISHATULHUMAIRA*
*~Mikiya writer’s Association~*
*Page 7&8*
Bismillahir Rahmanir Rahim.
_________Tana shiga ta iske dukkan wani kalan namun daji a wajen gasu nan iri iri yah Babbah nakan munbari inda yake zama kenan kamar dai kujarar sarki alamar taro suke yi. kamar ana janta haka ta cigaba da takawa har inda suke gaba ɗaya suka juyo gareta sai lokacin gabanta ya faɗi ta rasa ina zata dosa . Wani irin tashin hankali ne ya ziyarce ta ta fasa wata uwar kara tana duke wa a wajen ganin duk kan namun dajin dake wajen zagaye suke da ita, ganin babu wanda yayi yunkurin cutar da ita ta dago kanta tana binsu da ido tare da sauke ajiyar zuciya me ƙarfi. Tashi tayi tsaye tana raba ido sai ga Muhammad ya shigo a kiɗime inda take ya nufa ba tare da ko jin tsoro ba Yana zuwa yace mata.
“Wace irin kasada ce wannan kike yi da rayuwar ki da ta abinda ke jikinki”?.
Kasa magana tayi sai dai ta bishi da idanuwa ta kasa furta koda kalma ɗaya, juyawa tayi da nufin ƙara komawa cikin namun dajin ai kuwa Muhammad ya rikota cikin magiya yace. “Habibti ki daina wasa da rayuwata dan Allah, kiyi hakuri gobe sai ki dawo amma yanzu magriba tayi muje gida haka nan”.
Ba tare da ya tsaya jin me zata ce masa ba ya kama hannunta suka fara tafiya. Haka nan dai khadijerh ta haƙura amma suna tafiya tana wai gawa tana daga masu hannu fuskar ta dauke da murmushi har suka fita. Suna isa gida ya zaunar da ita Yana mata nasiha akan irin wautar da take neman farayi da rayuwar su ita da abinda ke cikinta saita kama yi mashi kukan shagwaɓa ba hali kuwa dole ya kyale ta ya koma lallashi Yana jin dama bai mata faɗan ba duk sai yaji haushin kansa.
Har aka kira sallah Yana aikin lallashi dakyar ya samu ta haƙura sannan ya samu natsuwar fita zuwa masallaci, ana idar wa kuwa gida ya dawo abinda bai saba ba sai gashi yau bai zauna ba har akayi isha’i ba ya dawo saboda Habibti tana ta rigima. Kwance ya sameta ta gama sallah yana zuwa ya ɗaga ta ya maida ta jikinsa ta kwantar da ita Yana fasha bayan ta alamar lallashi, ita kam tayi lamo abin nema ya samu sai zuba shagwaɓa take kamar karamar yarinya anan ya jasu sallar isha’i taki barinsa ya tafi masallaci saboda shagwaɓa shi kuma ya biye mata.
Da kyar dai ya lallaba ta taci abinci sannan yayi mata wanka ya kwantar da ita yana mata tausa a haka har tayi bacci sannan yaji hankalin shi ya kwanta shima yaci abincin yayi wanka sannan ya kwanta yayi masu addu’a tare da rumgume Habibtin shi sai bacci.
Bangaren su yah Babbah kuwa cigaba da hidimar su sukayi kowa yasan babu cutarwa a tsakanin su da mutanen haka yasa basuyi yunkurin cutar da khadijerh ba, yah Babbah ya kara ja masu kunne sosai akan hakan da yaren su na dabbobi har suka kammala sannan masu fita farauta suka fara fita kowa ya kama harkar gabansa.
Daga nan bangaren suna jin kiran sallar da yake fitowa daga bangaren su yah Kathub hakan yasa wajen nasu tsit babu wani mugu da bai natsu ba wajen har sai da aka gama kowa ya kama gaban sa.
Matar yah Babbah babbar Zakanya ce ita ke naƙuda zata haihu manya manyan namun dajin na kewaye da ita har ta sauka lafiya ta samu zaki me kyan gaske . Nan da nan namun dajin suka rikiɗe da murna da koke koke na farin ciki.
Washe gari ma da rigima Habibti ta tashi da ita a dole sai ta tafi ɓangaren namun dajin nan da kyar ya lallaɓa ta akan ta bari sai rana ta fito sai ya rakata suje a gano su ta dawo. Duk yadda yaso su koma ta samu wadataccen barci ƙiyawa tayi dole ya haƙura ya kyale ta wajen ƙarfe 9:00am ta gaji da jira ta miƙe ta fita haka ya haƙura ba dan yaso ba ya bita suka tafi duk da baya son abinda zai sa ta wahala amma ya kasa fahimtar cikin ne yazo mata da haka ko kuwa ita ke son shiga cikin namun dajin.
A hankali cike da natsuwa suke tafiya har suka iso bakin ƙofar ɓangaren, Addua tayi tare d shigewa tana mai jin farin ciki daba tasan kona miye ba, zagaya cikin tsaunin take duk Inda taga kofa sai ta leƙa wata kuma bata leƙawa sai dai ta wuce.
Da yawan namun dajin suna nan suna ta sabgogin su sai binta suke da ido duk inda ta gifta, ita kuwa ganin ba suyi mata komai ba ko dar bataji ba na tsoron shiga cikin su har ta wuce ɗakin da matar yah Babbah take ta dawo ta leƙa ganin ta kwance gefenta dan karamin zakin data haifa yasa khadijerh saurin shigewa ta duƙa kusa da ita haɗe hannuwan ta tayi alamar gaisuwa sannan ta ɗora hannunta kan karamin zakin da aka haifa ta ɗauko shi ta rungume cikin farin ciki ta fara magana kamar tanayi da mutum.
“Mama Babbah ina son ɗan ki kibar min shi na dinga wasa dashi zanji daɗi sosai idan kika amince”. Ta faɗa cike da shauƙi ba tare da Mamah Babbah tace komai ba ta miƙe ta nufi ƙofa itama miƙewa tayi ta biyo bayanta suka fito cikin kogon ɗakin da matar yah Babbah take. Cike da murna tayi ta binta a baya suna zagaya cikin tsaunin tana ma Mama Babbah da ɗan zakin da ta haifa labarai nan ta raɗa ma ɗan zaki suna
*SARAKI*. Kiran sallahr azahar da taji ne yasa ta aje Saraki ta nufi inda Muhammad yake zaune suna ta wasa da ƙananun birai.
Yana ganin ta ya miƙe yayi masu bye suka fita daga ɓangaren suna tafiya suna fira gwanin burgewa har suka isa gidan su, wanka sukayi sannan sukayi sallah sannan suka tafi gidan yah Babbah domin suci abinci suna zuwa kuwa aka kawo abinci kala wanda aka girka musamman domin khadijerh sai da suka ci suka koshi sannan taɗan kwanta ta huta.
Zuwa can kamar an tsinkule ta ta miƙe tare da cema su Ammi ta tafi waje shan iska bata jira me zasu ce ta fice da sauri ta nufi ɓangaren su yah Babbah tana isa ta iske su Saraki in da ta bar su nan ta zauna suna ta wasa har guje guje sai da sukayi dasu duk da a hankali take bi saboda tasan abinda ke jikinta.
Muhammad na komawa gidan yah Babbah ya iske bata nan, su sunyi tunanin suna tare ko gida ta wuce wajensa shi kuma yana asibiti duba mara lafiya da aka kai duk tunanin shi da hankalin shi yana nan ya ɗauka tana nan ashe ta fita.
Haka kawai jikinshi ya bashi tana ɓangaren su yah Babbah juyawa yayi ya fita yana zuwa can kuwa ya iske ta hankalin ta kwance tana ta farin ciki a cikin dabbobi, shi kansa ganin ta cikin shauki sai ya tsinci kansa da jin wani irin farin cikin sosai.
Da kyar ya lallaɓa ta suka tafi gida acan sukayi sallah la’asar suka nufi cikin lambun dake dan gidan su suna ta labari suna dariya farin ciki kam bai misultuwa wajen su.
Sai da aka kira magriba sannan suka fito lambun sukayi alwala ya wuce masallaci ita kuma ta shiga ɗaki tayi sallar ta.
Yau dai bai dawo ba sai da yayi sallar isha’i sannan ya shigo, aikuwa kamar jira take ya shigo ta kama kuka akan yayi zaman sa bayan an gama sallah bai taho gida ba.
Sosai hankalin shi ya tashi duk ya rikice yama rasa ta ina zai fara lallashin ta tabar kukan da take. Da kyar ya iya control ɗin kansa ya fara mata magana cikin raunin murya kamar zai fashe da kuka.
“Kiyi haƙuri Habibti nah yah Kathub ne ya tsaida ni wallahi kuma sai da na koma asibiti domin duba marar lafiya da aka kai ɗazu amma kiyi haƙuri bazan ƙara ba kinji masoyiya ina sonki keda baby nah”.
Ajiyar zuciya ta sauke jin uzurin shi me ƙarfi ne dan haka tace.
“Na yafe maka Habibi Amma kada ka ƙara kaji indai ba dalili me ƙarfi ne yasa ba Ina sonka”.
Murmushi yayi mata cikin jin daɗi ya rungume ta yana mata godiya tare da kalamai masu ratsa*MUTUM KO ZAKI*
*NA*
*A’ISHATULHUMAIRA*
*~Mikiya writer’s Association~*
*Page 9&10*
Bismillahir Rahmanir Rahim.
________Washe gari koda suka tashi da rigima sosai Habibti ta tashi akan lallai sai ta koma ɓangaren su yah Babbah babu yadda Habibi baiba akan ta hakura sai da anjima amma furr taki yadda, dole ya kyaleta saboda ya gama fahimtar cikin ne yazo mata da haka babu yadda zai yi sai dai haƙuri.
Gaba ɗaya hankalin ta da tunaninta na wajen *SARAKI* so take kawai ta ganshi suyi wasa tare, ko gyaran gidan bata tsaya ba saboda ta ƙa gara ta isa can wajen namun dajin nan, tana fitowa taci karo da Haidar Ummu ta aiko shi kawo mata abinci tana ganin shi ta washe baki sanin abinda take so ne Ummu tayi mata dan haka ta koma cikin gida Haidar na biye da ita suna gaisawa.
Shimfiɗa tayi mai ya zauna sannan tace mashi” Gadanga Angon Zarah ina ka boye aka bar ganin ka kwana biyu?”
Dariya yayi sosai dama yasan zata ce haka saboda nan ne wajen zuwan sa su sha fira kwana biyu kuma lambu da suke zuwa ne ya hana sa shigowa, suna mutunci sosai fiye da tunani ko shawara yake nema wajenta yake zuwa su kashe su rufe akwai kyakkyawar fahimta tsaninsu.
Muhammad ne ya fito yace,” wato na fahimce ki Habibti da yake Haidar ne dan gidan ki shine kika dawo kika fasa tafiya amma ba irin lallashin da ban maki ba kika ƙiji koh” Ya ƙare maganar cikin shagwaɓa.
Dariya sukayi gaba ɗayan su khadijerh tace mashi” Haba Habibi kaifa ka cika saka ido baka ga abinci Ummu ta aiko min dashi ba na dawo inci”. Itama ta ƙare tata maganar cikin shagwaɓa
Haidar ne ya kwashe da dariya ganin yadda suke ta zuba shagwaɓa a gabanshi duk da sun saba bawai kunyar shi suke ba wajen nuna ma juna ƙauna.
“Wai ku tsaya ina zata ne naji sai magana kuke akai ne ko can Babban gida zata ne”. Haidar ya ƙare maganar yana kallon su cikin sigar tambaya.
Habibi ne yayi saurin rigata magana” bangaren namun dajin can take zumudin ta tafi ta barni shine ta ganka ta dawo”.
Kwalalo ido Haidar yayi cike da mamaki yake kallon khadijerh ita ko tsoron su cinye ta bata yi duk gani yake kamar wasa suke mai ya za’a yi ta shiga cikin namun daji tace zatayi wasa.
“Amma dai wasa kuke ko?”.
Haidar ya ƙara tambayar su don ya tabbatar da gaske ne ko wasa.
Khadijerh tace” wai baka yadda ba toh tashi muje yau kai zaka rakani ma”.
Ta faɗa tare da mikewa takai kwanon da ta gama cin abincin daki sannan ta fito ta kalle su tace “muje”.
Mikewa sukayi gaba ɗaya suka mara mata baya har suka fita sashen Yah Kathub zasu tsallaka sashen Yah Babbah.
Ganin su yasa Haidar aro jarumta ya cigaba da binsu amma gaba ɗaya a tsorace yake sosai. Har suka iso bakin kofar bai magana ba sai su ke tayin firar su, ɗauke da addu’a suka saka kafafun su cikin wajen, Haidar dai daurewa kawai yake yana kuma mamakin su khadijerh da har suka iya shiga kai tsaye tafiya kawai suke abinsu.
Yana nan tsaye sai ga wasu birai guda biyu da gudu sun nufo shi, aikuwa ganin kanshi suka yo ya kwasa a guje maimakon yayi waje ko inda su Muhammad suke sai yayi inda wannan bire suka fito da gudu, baisan nan wajen su bane kogon su ne me matuƙar girman gaske ya shiga.
Yana shiga ya ganshi a babban waje me haske da bishiyu a ciki gwanin kyau sai dai ruɗewar da yake ciki ta hana shi ganin kyan wajen.
Tsayawa yayi yana maida numfashi aikuwa sai ga biran nan kala kala suna fitowa kamar ana turo su zagaye dashi. Wani irin ihu ya yayi cikin matuƙar tsoron su ya shiga basu hakuri sai dai su a wajensu kamar nishaɗi abin ya basu ana suka fara dariya irin tasu ta birai. Guda biyun da suka biyo shine suka maƙalƙale shi aikuwa nan take ya zube masu sumamme.
Ganin shi kwance male-male sai abin ya basu nishaɗi ai kuwa suka hau zagaye shi wasu Kuma na kan jikinshi, zuwa can wani biri ya ɗauko wani abu kamar buje na ganye ya kawo ya ɗaura akan jikin Haidar aikuwa suka fara dariya nan take suka taru suka saka mai a ƙugunshi.
Dariya suke suna zagaya shi zuwa wani lokaci kuma wani biri ya ɗauko wani baƙin abu suka shafe mai fuska dashi wani kuma ya ɗauko abin ƙafa kamar sarƙa suka saka Mai suna ta tsalle tsalle suna dariyar su ta birai. Ruwa suka ɗebo suka sheƙa masa a jiki aikuwa ya sauke numfashi a hankali yana buɗe ido ya ganshi zagaye dasu ya ƙara fasa wata ƙarar nan take ya ƙara sumewa.
Ruwa suka ƙara zuba mai ya farfaɗo ya miƙe a zabure yana kallonsu, su kuwa abin dariya yake basu sunata yi. Ganin abinda suka saka mai ya kalle su a tsorace yana magana.
“Innalillahi shaiɗan ku shaiɗan ne meyasa kuka saka min wannan”. yana nuna ƙugun shi.
Wani biri ne ya ruga ya ƙara ɗauko irin abin ya saka yana rawa aikuwa nan da nan suka fara dariya abin nishaɗi yake basu shine suka sanya mashi.
Haƙuri yayi ta basu ganin dariya ma yake basu ya fara tunanin hanyar guduwa a daburce aikuwa ya hango ƙofar da suka shigo kafin su ankara ya zuba da gudun tsiya yana gudu yana ihu kamar mahaukaci.
Yana fitowa kogon su ya ƙara zurawa da uban gudu ganin kuraye kwance suna hutawa, ganinshi yana gudu suma suka biyo shi da gudu ai kuwa ya kara himma yanayi sunayi maimakon ya fita sai suka cigaba da zagaya wajen har Allah ya bashi sa’a ya nufi inda su Muhammad suke suna ta wasa dasu Saraki.
Ai da gudu ya isa garesu sai dai yana isowa wata zakanya ta taso a fusace ta ɗauka zai cutar dasu khadijerh ne, aikuwa ganin haka ya ƙara ruɗewa ya juya da gudun bala’i yayi waje bai tsaya ko ina ba sai Sashen Yah Kathub.
Da gudu ya shiga yana ihu aikuwa nan da nan mutane suka ruɗe kowa gudu yana neman ma ɓoya duk inda ya gifta sai a ruga da gudu kamar aljani, bai tsaya ko ina ba sai gida yana shiga ya faɗa tsakiyar su Ummu aikuwa basu gane shi ba da gudun tsiya suka ruga ɗaki suka banko kofa ji kake bamm. Ai kamar jira yake shima a 360 ya an taya cikin nashi ɗakin ya banko ƙofar.
Yah Kathub ne dake zaune bai gudu ba duk da ya tsorata amma yana kallon Haidar ya gane shine shiyasa bai gudu ba, Fita yayi yaga har lokacin mutane gudu kawai ake ana komawa cikin gida ya tsaida wani yana tambayar sa meke faruwa yace mashi” Nidai naga ana ta gudu shine Nima nake ta gudu na koma gida naji ance Aljanu da birai ne ke wasa inji wasu.
Me yah Kathub zai yi inba dariya ba ganin da gaske Haidar ya tsorata mutane aikuwa gida ya koma yana ta dariya abinshi sai da yayi me isar sa sannan ya tashi ya ƙara sa ƙofar ɗakin Haidar yana magana.
” Aliyu maza buɗe ƙofar nan ka gaya min abinda ke faruwa duk ka tsorata mutanen gari”.
Jin muryan Yah Kathub yasa hankalin Haidar kwanciya ya taso a hankali sai da ya leƙo yaga yah Kathub ne kaɗai sannan ya buɗe ƙofar ya fito.
Ganin irin kaya da kwalliyar jikin Haidar yasa yah Kathub kara tuntsirewa da dariya har da zama, sai da yayi dariya har ya gaji sannan ya dakata yana kallon Haidar dake ta raba idanu yace mashi.
“Meke faruwa ne naga wannan kwalliya a jikinka da wannan abin na ƙugunka ina ka samo shi”.
Kuka ya fashe dashi yana gaya ma yah Kathub abinda ya faru sannan ya koma cikin ɗakin shi yana kallon kanshi a madubi, wani kukan baƙin ciki ya ƙara saki yana tunanin ta hanyar da zai ci uban namun dajin nan don gaba ɗaya ya tsane su tsana mafi muni, kayan ya cire sannan ya fito ya shiga banɗaki yayi wanka ya goge bakin da suka saka mai.
Juyawa yah Kathub yayi yana dariya ya kwankwasa ɗakunan su Ammi suka fito ya basu labari suma dariyar suka shiga yi kafin Ummu tace ma yah Kathub.
” ya kamata ka fita kayi sanarwa a masallaci don hankalin mutane ya kwanta”.Jinjina Kai yayi na gamsuwa sannan yasa kai ya fice yana yar dariya ƙasa ƙasa. Nan su Ammi suka zauna suna firar abin suna dariya.
Ɓangaren su Habibi kuwa bayan tahowar Haidar dariya suka sha sosai sannan suka cigaba da wasan da suke suna fira fira sai da suka ji ƙaran loudspeaker ana sanarwa sannan suka yi haramar tafiya su kwashi dariya sun ransu.
Suna shigowa suka ga mutane ba yawa sai ɗaiɗai ku nan suka ƙara sauri domin isa gida suka ga ya Haidar yake, tafiya suke suna dariya ganin yadda gaba ɗaya mutane suka tsoro ta abin ya basu dariya sosai.
Suna shiga gida Haidar na fitowa wanka ya wanke baƙ
in nan tass, kallon su yayi ya banka masu harara ai kuwa daga su har su Ammi suka kwashe da dariya suna kallonshi, kwafa yayi sannan ya shige daki ya watso kayan da biran nan suka saka mai ya banko ƙofar.
Abin ba ƙaramin dariya ya basu ba nan suka zauna ana ta maida magana ana dariya sai ga usman shima ya shigo rike da umar a hannun shi. Yana zama kuwa aka bashi labari ai sai dariya ta ƙaru anan, zuwa can Haidar ya leƙo yace masu.
“”Ku gama dariyar wallahi nine Ajalin namun dajin can ko ni ko su mu zuba dan halak ka fasa daga yau gaba ce tsakanina dasu har kuma gaba da abada””.
Tsit sukayi suna sauraren shi yana kai ƙarshe suka kara saka dariya harda yah Kathub daya shigo yaji furucin Haidar……..
More comments
More read more*MUTUM KO ZAKI*
*NA*
*A’ISHATULHUMAIRA*
*~Mikiya writer’s Association~*
*Page 11/12*
Bismillahir Rahmanir Rahim.
_______Sosai Gidan yah Kathub suke cigaba da kula da khadijerh tare da taimakon mijinta har cikin ta ya girma watan shi biyar ya shiga na shidda ya fito sosai, ɓangare ɗaya kuma wata irin shaƙuwa ce ta ban mamaki ta ƙara shiga tsakanin ta da namun dajin nan musamman Saraki da sukayi wata irin shaƙuwa sosai kusan anan wajen ta yake zama in bataje ɓangaren su ba sai ya biyo ta nan ya zaua suna firar su da wasannin su.
Babu yadda mutane basuyi ba akan yadda take shige ma dabbobin nan ta bari amma sam bata ko sauraren su balle taji, tana fahimtar su sosai haka itama suna fahimtar ta duk da ba magana suke ba amma babu kalan halittan dabban da bata iya maganar su ba ko ince fahimtar su ba. Haka suma suna jin mai take faɗa in tayi magana mai da mata ne kawai basa iya wa domin Allah bai basu wannan ikon ba na magana, sosai suke girmama ta ko magana tayi sukan sunkuyar da kansu ƙasa alaman girmama wa in kuma magana tabin umarni ce sukan aikata kamar yadda ta buƙata.
Abin ya wuce dukkan tunanin me tunani, suna nuna mata soyayya ta ɓangaren kula da duk wani motsin ta in ta shigo ɓangaren su haka kuma suke zuwa musamman wajen cikin ta su kanga kansu akai alamar gaisuwa ga abinda yake cikin ta. Tun abin na ba Muhammad tsoro har ya koma bashi mamaki ganin yadda suke mu’amala sai dai bai hanata ba saboda shima ya kaunar duk abin da Habibtin shi ke so shiyasa ya daina mamaki domin ya fahimci wannan haɗin daga Allah ne.
Yau tunda ta tashi take ta sauri taje ɓangaren yah Babbah saboda bataji motsin Saraki ba, yakan zo da wuri wajen ta koda bata ganshi ba yana zuwa yayi ta yan tsalle tsallen shi a cikin gidan kafin su tashi bacci, wani lokacin in taji haka to sauri yake da inda zaije kuma bai so ya tafi basu gaisa ba sai ta fito su gaisa ya tafi amma yau shiru take jinshi babu alamun shi shiyasa take ta sauri taje taga lafiya dai ko duk hankalin ta yayi wajen su.
Tana zuwa ta iske Saraki kwance, dukkan sauran namun daji na wajen yana ta fidda kumfa a bakin shi alamun ya kusa mutuwa, kallo ɗaya tayi mai jikinta ya bata guba ce ya ci ko yasha ko aka dura mai ita haka ta ruga da gudu ta isa gareshi tana girgiza shi tana kuka, ganin kukan bazai mata ba ta tashi da gudu tayi ɓangaren su tunawa da tayi akwai taimakon da zata iya ma Saraki.
Cikin ikon Allah tana isa taje wajen yah Kathub tayi mai bayani ya bata maganin da suke ba dabbobin su in sunci guba, aikuwa ba tare da tunanin komai ba ya bata saboda suna da tarin dabbobi yayi zaton wata dabban ce bata lafiya ko taci yo guba cikin nasu tazo ta amshi magani.
Tana amsa ta fita da sauri ta nufi ɓangaren yah Babbah da ɗan gudun ta ta isa garesu duk sunyi jigum jigum sunata kai kawo, tana zuwa ta ɓude kwalban ta ɗura ma Saraki a bakin shi wanda har jikinshi ya fara saki alamun dai gab yake da mutuwa, sai da ta tabbatar ya shiga cikin shi sannan ta aje ta zuba mai ido tana hawayen tausayin shi.
Cikin hukuncin ubangiji sai Saraki ya fara amai a kwancen da yake tun yanayi a hankali har ya fara yunƙurin tashi nan da nan ya amayar da komai dake cikin shi ya koma gefe ya faɗi, hamdala Habibti tayi sannan ta koma inda yake ta rumgume shi tana dariya .
Ganin ta tana dariya yasa sauran namun dajin suka fahimci ya samu lafiya, aikuwa suka mimmiƙe suna murna maman Saraki kuwa da yah Babbah rumgume Habibti sukayi cikin murna ganin ta ceto rayuwar ɗan su.
Sai da ta tabbatar Saraki ya samu lafiya sannan hankalin ta ya kwanta ta zauna suna ta wasa, sai da ta gaji sannan ta miƙe tana masu sallama zata koma ɓangaren su, har ta tafi yah Babbah ya biyo ta tana waigawa taga yana biyo ta sai ta tsaya tana mai murmushi, yana zuwa ya ɗaga ƙafarshi guda ɗaya ya ɗaura akan cikin ta tare da lumshe ido ya daɗe a haka sannan ya sauke ya jinjina mata kai alamar girmamawa.
Murmushi tayi sannan ta juya ta taci gaba da tafiya duk da tayi mamakin abinda yah Babbah yayi mata saboda a lokacin daya ɗaura ƙafar shi kan cikin sai da cikin ya dinga wutsil wutsil wanda bata taɓa jin irin shi ba.
Harta isa gida tana ta tunane tunane koda habibi ya dawo ta bashi labarin komai murmushi kawai yayi saboda yaji daɗin yadda ta ceci ran Sarakie sannan haka kawai yaji daɗin abinda yah Babbah yayi ɗin.
Bai ce mata komai ba suka cigaba firar su cikin so da ƙauna wanda yawancin firar tasu duk akan namun dajin suke yinta.
Ɓangaren Haidar kuwa cikin farin ciki yake ganin yadda zai ɗauki fansa cikin sauƙi ba tare da sanin shi aikata hakan ba, tunda yaga bai ga Saraki ba yasan ya mutu saboda gubar daya ɗura masa yasan bazai kai labari ba.
Yayin da yake ƙara tsanin tsanarsa ga namun daji, ko kallon ɓangaren yah Babbah bai ƙaunar yi balle yaga wata halitta data shafi dabba. Shi kaɗai yasan me yake shiryawa akan ƙudirin daya ɗauka akan su.
Sai kash! Abinda bai sani ba Wanda ya riga ka kwana to dole ne zai rigaka tashi.*MUTUM KO ZAKI*
*NA*
*A’ISHATULHUMAIRA*
*~Mikiya writer’s Association~*
*Page 13/14*
*Bismillahir Rahmanir Rahim*.
__________ Tsaye yake gaban babban ruwan daya kasance ruwa mafi kyau da tsari, wanda ya kasance ruwan sha ne ga namun dajin dake ɓangaren yah Babbah, dukkan natsuwa da hankalin shi na kan abinda yake ƙoƙarin zubawa a cikin ruwan. Ba tare da tunanin komai ba yake ƙoƙarin zuba wannan abu daya gama kwancewa a cikin kyalle, ya duƙa zai zuba kenan akayi sama dashi aka buga da ƙasa, a matuƙar razane ya miƙe don bai taɓa kawo ma ransa irin hakan zai faru dashi ba.
saboda cikin dare ne babu wani mahaluki da yake ido biyu sai dai halittun da lokacin neman abincin su ne, sai kuma aljanu, ba tare da haidar ya gama dawowa cikin hayyacin shi ba aka ƙara sama dashi aka tiƙa da ƙasa wata irin ƙarar azaba ya kwalla tare da ɗaga kai yana kai duban shi ga abinda ke shirin halaka shi.
Yah Babbah ya gani a gaban shi a asalin zakin shi yana wani huci me ban tsoro da razanar wa, hantar cikin Haidar sai da tayi mugun kaɗawa saboda kiɗima abinda bai sani ba taya akayi Yah Babbah yazo wajen har yasan abinda yake ƙoƙarin Aikatawa.
Abinda bai sani ba dukkan wata dabba suna jin abu idan zai samu wani ma balle su sai dai in ƙadarar ubangiji ta faɗa kansu amma da wuya dai abu ya dirar ma dabba haka kawai balle su yah Babbah da suke da nasu kadarin ba haka kawai suke ba a dabbobin da tsafi jikinsu sosai Wanda iyaye da kakan ni da manyan Aljanun da suka basu yana jikin su, ba abinda basu gani kuma ba suji indai zai tunkaro wannan dajin nasu.
Tun fara shirin shi na zuba wannan guba a ruwan da suke sha yah Babbah yana ganin shi yana kuma sane dashi yaga ko zai aje makaman yaƙin nashi sai dai bai da niyar hakan shiyasa ya fito mashi a ainihin Zakin ya iso gareshi ranshi a ɓace ganin irin abinda yake ƙoƙarin saka masu dashi.
Wani irin kuka yah Babbah yayi kafin wani lokaci duk wani kalan namun daji ya taho da mugun gudu saboda da sunji kalan wannan kukan sun san babu lafiya ana ɗaukan shekaru kafin irin haka ya faru.
Za gaye suke dasu gaba ɗaya suna jiran umarni daga yah Babbah akan abinda suka fahimci yana faruwa, wata irin hankaɗa yah Babbah yayi ma Haidar sai gashi gaban babbar giwar su ganin shi gabanta ya ƙara jin wani tashin hankali marar misultuwa amma saboda kaifin zuciya da yadda yake jin tsanar su hakan baisa yaji zai iya haƙura da ƙudirin shi ba.
Kafin ya ankara giwar ta naɗe shi ta juya suka nufi ɓangaren su dashi. Sai da suka isa babban filin da yake bangaren su inda suke wasan su na dabbobi sannan suka yadda shi anan suka yi mai zobe.
ko ɗar Haidar baiji ba sai ma jin da yake kamar ya bisu ya kashe su ɗaya bayan ɗaya.
Igiya babba wasu birai suka ɗauko suka aje sai suka koma suka ɗauko wasu kayan da wani kalolin fenti suka ajiye suka koma gefe suka tsaya.
Wani babban gwaggon biri ya taho sai wasu a bayan shi suka tsaya gaban Haidar da yake ta binsu da kallo cikin tashin hankali amma a fuskar shi sam baka gane yanayin da yake ciki, biyu ne suka rike shi kam, sai ɗaya ya fara ɗaure shi da igiya sannan ya ɗauko kayan ya saka mashi hada bindin shi kamar biri sak, sai fenti da suka shafe ma fuskar shi, wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne yazo ma Haidar wuya ganin yadda suka maida shi biri.
cikin wata fusata ya fara kai masu duka ta ko ina, ko gezau basuyi ba suna ta kallon shi sai da yayi ya gaji sannan ya dakata su kuma suka fara Jan igiyoyin da suka ƙulle shi dasu, in wannan yaja Haidar yayi wajen shi kafin ya ƙarasa sai wani yaja shi kiiiiii wajen shi haka suka dinga wasa da Haidar kamar yadda ake wasa da biri iya galabaita Haidar ya galabaita ko numfashin kirki baya yi.
Har gari ya waye suna wahalar da Haidar ya suma kusan sau ukku amma basu kyale shi ba, daya suma sai su saka shi cikin ruwa daya dawo hayyacin shi sai su cigaba da azabtar dashi.
Ɓangaren Habibti kuwa yau batajin zuwa ɓangaren su yah Babbah, dan haka tana gama gyaran gida tayi kwanciyar ta tana bacci sai da akayi sallar azahar sannan ta tafi gidan yah Kathub ta taya su aiki sannan suka ci abinci tabi mijinta asibiti, suna asibiti sai da aka mata awo sannan ta dawo gida saboda cikin nata yayi nauyi gab take da haihuwa.
Tana kwance sai ga Saraki ya shigo yana zuwa ya kwanta jikinta taga dai jikinshi duk yayi sanyi sai ta tambaye shi lafiya baiyi mata yadda ya saba ba sai dai ya miƙe ya nufi hanya ganin haka sai ta mike ta ɗauko mayafi tabi bayan shi.
Suna zuwa taga babu kowa kuma ɓangaren nasu tsit dan haka ta kalli Saraki tana son magana sai taga ya juya ya cigaba da tafiya zuwa inda suke , turus tayi tana bin wajen da kallo ganin gaba ɗayan su a waje ɗaya. Murmushi tayi a ranta tana ayyana abubuwa da yawa game da yadda suke rayuwa kamar mutane duk a tunanin ta wasa suke yi ko kwallo shiyasa duk suka zo nan wajen.
Zagaya wa tayi inda ke da fili yadda zata ga komai da kyau ta tsaya sai dai ganin kamar da mutum suke wasan yasa taji gabanta ya fadi sosai ta kara kura ido sosai.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raju’un Haidar” shine abinda ya fito bakinta tsaf ta gane shi, ta ruga da gudu gaban shi ta fashe da kuka, tana ɗago shi ganin kamar ba rai jikinshi. Yah Babbah ne taka zuwa gabanta yayi mata alama da ta matsa gefe amma ta girgiza Kai alaman A’a.
“Meye hakan da kuke yah Babbah meya yi kuke son kashe shi iyeeh”.
Birin nan ne ya ɗauko guban ya kawo gabanta ya ajiye ya fara mata bayanin abinda Haidar yayi kokarin aikatawa a akansu, cikin tashin hankali ta kalli Haidar tana ja da baya a matuƙar razane don batayi tunanin Haidar zai iya hakan ba sai dai nan take furucin shi na rannan ya shiga dawo mata daki daki.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raju’un Haidar meyasa zaka aikata haka garesu bayan irin Halaccin da suka nuna garemu”.
Kuka take sosai tana magana, tashin hankalin da take ciki ya wuce misali nan da nan cikin ta ya fara juyawa mararta ta murďa amma bakin ta bai daina basu hakuri ba akan abinda Haidar ya aikata masu.
Cikin dauriya ta nufi inda Haidar yake kwance ta fara ƙoƙarin miƙar dashi yah Babbah yayi ma giwar nan alama nan da nan kuwa ta ƙarasa garesu ta naɗe Haidar d bakinta ta nufi ɓangaren su dashi, bin bayansu tayi tana tafiya a hankali cike da dauriya sai dai tana zuwa daidai ɗakin su Saraki ciwon yaci ƙarfin ta, ta durƙushe a wajen ganin haka su yah Babbah suka nufe ta da sauri manyan biran ne suka kamata suka nufi dakin su Saraki da ita.
Can cikin bangaren su yah Kathub giwar nan takai haidar ta aje shi, gaba ďaya kamarnin shi ya sauya bai iya daga yatsan shi. Yah Kathub aka kira yazo wajen, yana zuwa ya gane Haidar ne dan haka yasa aka dauke shi aka tafi dashi asibitin su.
Taimakon gaggawa aka shiga bashi har aka samu numfashin shi ya daidaita sannan hankalin su ya ďan kwanta, sai dai yana buďe idon shi da kyar yace masu.
“Ina Aunty nah ku duba ta” iya abinda ya fita a bakin shi kenan allurar baccin da aka mashi ta fara aiki, aikuwa nan da nan suka ďin guma zuwa bangaren yah Babbah.
Suna shiga suka ce karo da Saraki da gudu zai tafi bangaren nasu, yana zuwa yayi wajen Muhammad da gudu ya ďane jikinsa sai kuma ya sauka ya bi hanyar dakin su. Muhammad na ganin haka yabi bayan Saraki sauran ma suka mara mai baya .
Suna shiga suka ďakin suka ganta kwance tana juye juye mama Babbah na kusa da ita sai wata babbar gorilla mace , Hankalin Ammi da Ummu ba karamin tashi yayi ba ganin khadijerh cikin wannan halin, nakuda take sosai bata gane ma wake kanta.
A tare Ammi da Ummu suka isa gareta haka ma Muhammad suna niyyar ďagata kenan tayi nishi me karfi sai ga kan ďa ya fito, ganin haka sai suka maida ta suka kwantar da ita mazan duk suka fita sai Ummu da Ammi kawai da mama Babbah suka tsaya sai wannan gorilla.
Nishi ta kara yi da karfi sai ga babyn ya ida faďowa akan mayafin Ummu yana canyara kuka.
Alhamdulillah! Alhamdulillah! Shine abinda suke ta furtawa, Ummu ta ďauko ta saka shi jikin mahaifiyar shi yaji ďumin ta, sai da ta dawo hayyacin ta sosai sannan suka ďauki babyn sunata murna bakin su yaki rufuwa.
Waje suka fito dashi aka mika ma yah Kathub ya dauka cike da farin ciki ganin jikanshi na biyu a duniya, addu’a yayi mai sosai sannan ya mika ma Muhammad da yake jin shi kamar a sararin samaniya saboda farin ciki.
Yana amsar shi su khadijerh na fitowa daga cikin dakin sai ya mika ma gorilla dake kusa dashi babyn ya nufi khadijerh ya rungume ta yana mata addua da kalamai masu dadi ya rasa ina zaisa kanshi saboda murna.
Sai da duk namun dajin nan suka gama ganin babyn sannan Muhammad ya amsa ya ďaga shi sama.
“Alhamdulillah! Allah ya raya mana Muhammad Quraish”.
Wata irin murna ta kwace a wajen baka jin komai sai Alhamdulillah dabbobin kuma sai ihu suke na murna……..*MUTUM KO ZAKI*
*NA*
*A’ISHATULHUMAIRA*
*~Mikiya writer’s Association~*
Gajeran labari ne.
Bismillahir Rahmanir Rahim.
*page* 15&16
______Ranar sunan kuraish anyi shagali sosai duka bangare biyu, dabbobi sunyi nasu haka ma mutane sunyi nasu sosai abin ya kayatar, wasa na musamman su yah Babbah suka shirya ma sunan a bangaren yah Kathub aka shirya shi cikin babban filin dake bangaren nasu. Manyan bire suka shirya wajen da adon furanni masu kyan gaske kalan ja da ďorawa, mutanen dake rayuwa bangaren yah Kathub abin ya matuƙar basu mamaki ganin yadda manyan namun daji ke shigowa suna ta hidima abin sai ya tsorata su kowa ya lafe sai hange daga nesa.
Wajen ƙarfe huɗu suka fara shagali, birai sun saka kayan wasan su, haka ma sauran jinsin namun dajin kowane da kalan adon da sukayi, sosai abin ya kayatar, in wannan suka shiga fili sukayi irin nasu wasan sai wannan su shiga a haka har aka zo kan su yah Babbah.
Mutane duk sun fito kowa na wajen zagaye suke da namun dajin suna kallon ikon Allah.
Zaki a dawa sarki ko ina sai ya nuna shi din babba ne shigar su yah Babbah cikin filin kawai zaka san manya ne wajen, wani irin wasa suka fara tamkar sun shiga daji farauta hakan yasa mutane suka dan fara tsorata, wata irin girgiza wani zaki yayi tare da rugawa da gudu ya nufi inda me jego take da lullubi sai jariri a hannunta bai wata wata ba ya hangame baki ya fisgo jaririn daga hannunta ya juya d gudu zuwa cikin filin, yana zuwa ya dire jaririn gaban yah Babbah nan da nan suka fara wani irin wasa dashi kowa sai da ya dauke shi da bakin shi, ganin irin wasan da suke da jariri yasa mutane suka dinga guduwa kowa na neman wajen b’uya.
Mai jego kam da zuri’ar su babu wanda ya matsa kowa na kallon ikon Allah,
sai da suka gama sannan Mama Babbah ta dauko shi ta maido shi gun mamarsa su kuma suka cigaba da shagalin su.
Su yah Kathub wajen jaririn suka nufa ganin babu wani alama na ciwo ko gajiya a tare dashi sai abin ya basu mamaki sosai, murar da yaron yake dan yi wadda ta sarke numfashin shi sai suka ga babu alamunta yana ta baccin shi hankali kwance. Har sai da magriba tayi sannan aka tashi kowa ya koma muhallin sa.
Cikin so da kauna tare da kulawa ta musamman habibi da Habibtin shi suka cigaba da kula da Ƙuraish, sai dai wasu abubuwa game da Ƙuraish yana basu mamaki domin duk yadda yake bacci da lokacin zuwan Saraki yayi yake tashi ko kuma in yaji zuwan nasa toh ya gama bacci har sai kuma idan Sarakie ya tafi sannan ya koma.
A lokacin da suka fahimci hakan sai abin ya ɗaure masu kai sosai saboda kasancewar ƙuraish jariri taya yake sanin zuwan Saraki har ya farka daga bacci. Tun suna mamakin abin har suka daina, suka mayar da hankalin su wajen kula da yaron su.
Ɓangaren Haidar kuwa jikin shi sai a hankali don ba ƙaramin jigata yayi ba har sannan bai gama dawowa hayyacin shi ba, duk ya rame saboda wahala amma a hakan zuciyar shi bata haƙura ba akan ɗaukar fansa ba sai ma abinda yayi gaba.
Yayi alwashin yana warkewa zai cigaba da shirin sa na kauda duk wani dabba dake cikin dajin nan. Baƙin cikin shi ďaya yadda aka bashi labari su yah Babbah sunyi shagali a bikin sunan Kuraish kuma a ɓangaren su yaso ace lafiyarsa lau daya koya masu hankali sai dai kash babu yadda zai yi a halin da yake ciki.
Ko kaɗan su yah Kathub basu yi tunanin Haidar zai iya aikata abinda yayi ba, sun masa faɗa sosai akan abinda ya aikata ga su yah Babbah. A fili ya basu haƙuri ya kuma ce masu hakan bazata kuma faruwa ba, sai dai iya bakinsa ne kawai ke furucin amma a cikin zuciyarsa ba hakan bane.
Su yah Babbah kuwa murnar zuwan ƙuraish ta mantar dasu abinda ya faru, hidimar su suka cigaba da yi. Sai dai yah Babbah yana kallon duk wani abu dake faruwa ya kuma ɗauki alwashin koya ma haidar hankali. Daki na musamman suka ware ma Ƙuraish wanda zai rinka wasa duk wani kayan wasa da suka san zai amfani sai da suka sanya a cikin ɗakin saboda murna .
Saraki koda yaushe yana hanya wajen Ƙuraish, Dabbobi ne amma yadda suke abubuwa game da haihuwar Ƙuraish sai abin ya baka mamaki sun nuna murna sosai sun kuma yi kara da halacci…..
_______
Idan har ya kasance kun kasa saka Alkhairi da Alkhairi to mayar da sharri bazai taba zama jindadi ga ruhin da aka yi ma halacci ba, canza kudirin ku yana nufin zaman lafiya a gareku, aka sin haka barazana ne ga rayuwan da basu ji ba basu gani ba.
Mafi girman kuskuren da ďayan ku zai aikata, shine mafi girman zunubi a wajen wasu, in ma dakatar da hakan in ma kasancewar abinda ba’a yi zata zo.
Akwai jinsi mafi karfi daya kasance namu kuma a cikin ku, gaurayar tsakuwa cikin aya ba yana nufin duka zasu taunu a cikin baki bane.
Firgigit ya farka daga wannan mafarki daya matuƙar tayar mai da hankali ainun. Me hakan ke nufi? Kenan akwai abinda yake shirin faruwa? A razane ya mike tare da fitowa waje kamar ana janyo shi..
Comments
Share Fisabilillah *MUTUM KO ZAKI*
*NA*
*A’ISHATULHUMAIRA*
*~Mikiya writer’s Association~*
Gajeran labari ne.
Bismillahir Rahmanir Rahim.
*page* 17&18
_______
A kwana a tashi ba wuya, anata rayuwa lokaci yana ta tafiya. Yau kwana arba’in da haihuwar Kuraish, abubuwa da dama sun faru ciki harda abubuwan da yake naban al’ajabi, yayi wayau sosai ya kuma san kowa .
Yau gidan yah Kathub suke tafi tun safe, tarba me kyau ummu tayi masu sai nan da nan ake dasu, kowa ya dauki kuraish sai dai wani abu daya ba kowa mamaki yadda Haidar ya dauke shi ya saka kuka, duk yadda yaso ya dauke shi amma sam kuraish yaki bada hadin kai.
Amma duk wanda ya dauke shi zai yi shiru abinshi ya lafe, amma banda Haidar gashi Allah ya daura mashi wata masifaffiyar kaunar kuraish, wani irin so mai ratsa bargo da zuciya yake ma kuraish gashi yaki ma yadda ya zauna hannun shi ko zai samu yaji dadi a ransa.
Ammi ce tace” Lallai kam abin yaron nan yana bani mamaki ku duba yadda yake yadda da kowa amma sam yaki yadda Haidar ya dauke shi kamar wanda yayi wayon sanin mutane”.
Dariya sukayi gaba ďayan su, kowa yana gida anan suke shan yini hakan yasa kowa sai da ya dara akan maganar da Ammi tayi.
Usman ne ya kada baki yace ” Ammi kibar mamaki yaran yanzu da wayon su ake haifar su dan haka kima daina wani mamaki”.
“A’a nifa gani nake dan baida lafiya bai je ya dauke shi ba lokacin da aka haife shiyasa yake kin yadda dashi” ummu ta faďa tana dariya.
Suma dariyar suka sake yi maganar Haidar ta katse masu ita.
“Ai wallahi duk laifin yan iskan dabbobin can ne su suka ja min gashi duk nafi kowa son shi amma bai yadda dani”.
“Lallai ma wallahi duk nafi ku san Kuraish dan baku san yadda nake jin yaron nan bane” usman ya faďa da iya gaskiyar sa, yana jin kuraish fiye da yadda yake jin ďansa umar.
“Duk kumayi shiru wallahi nafi kowa son Muhammad dan ni danayi aure gidana zai dawo gaba ďaya har sai na aurar dashi Dan kusani ma” zainul abeedeen ya faďa tare da kara rungume kuraish dake hannun shi kamar za’a kwace masa ita.
Gaba ďaya wajen dariya aka saka harda yah Kathub dake gefe yana jin maganar yaran nasa.
Muhammad ne cikin jin dadi ya kalli yan uwan nasa gaba daya yadda duk suka dauki son duniya suka daura akan ďanshi sai abin yasa shi farinciki yana fatan kada Allah ya kawo abinda zai raba kan su.
“To yanzu tunda kun dauke kuraish tun yanzu ke Ummu kiyi hakuri ki bamu Umar Farouk ya dawo wajen mu da zama” Muhammad ya fada yana kallon khadijerh da farin cikinta ya kasa boyuwa.
“Eh hakane gaskiya Ummu dan Allah kibar mana Farouk dama shine ďan mu ai”. Ta faďa tana murmushi
Ummu wurga masu harara tana cewa.
“Babu mai rabani da mai gida na ku sake haifar wasu mana kuma ai matar usman wani cikin ne da ita sai ku bari inta haihu ku amsa”.
Gaba ďayan su sai murna ta karu kowa bakinsa yaki rufuwa, matar usman kuwa tashi tayi ta shige dakin ummu, bata yi zaton za’a yi saurin gane tana da ciki ba tun yanzu, ko usman din baisan tana dashi ba so tayi kawai ya ganshi in ya fito , sai gashi Ummu ta tona mata asiri.
“Nima dai nan da shekara biyar zanyi auren nan my Zahra zata zo ta haifa maku yara banda ni amma dan ni wallahi kuraish ne dana sai Farouk dan kusani ma”.
Dariya ce ta kubce ma yah Kathub jin irin furucin da Haidar ke yi.
“Aliyu Gadanga Angon Zarah kai dai na daban ne ‘yayanka sune naka, naka kuma sune nasu, dama haka abin yake ai ga wanda suka san alakar jini”.
Yah Kathub na rufe baki, Amina tace
“Ni wallahi na kama jaririn da matar yah usman zata haifa dan ma kar wani yace ya riga ehe”.
Dariya suka sa gaba ďayan su, kowa ka gani cikin farin ciki yake, wunin ranar anan sukayi shi, sallah kawai ke tayar dasu.
Gefe guda kuma sosai yah Kathub ya damu akan mafarkin da yayi, sai dai ya rasa da wane ma’auni zai auna maganar ciki. Ganin ba wata mafita ya tattara zancen ya watsar.
Bayan wani Lokaci kuraish ya iya zama har yana mikewa in ya dafa wani abu, abubuwan ban al’ajabi game da kuraish kuwa sai karuwa suke domin a wannan lokacin da bai wuce wata biyar ba har magana ya fara kokarin yi, idan Sarakie yazo kam hayewa bayan shi yake su tafi yawo idan basu idan yah Kathub to suna bangaren su yah Babbah.
Sosai wata irin shaƙuwa ta shiga tsakanin su bacci kawai ke raba su amma koda yaushe suna tare, tun abin naba mutane mamaki da tsoro har ya daina basu.
Su yah Babbah kuwa sun saba da kuraish sosai, duk sanda yaje babu wanda bai kwanciya kuraish ya hau bayan shi suyi yawo dashi. Kuma ko kaďan bai jin tsoron namun dajin sai ma shakuwa data shiga tsakanin su, ko ina ya sani a bangaren su haka kuma duk inda ya shiga zai iya fiddo kanshi……
Comments
Share Fisabilillah *MUTUM KO ZAKI*
*NA*
*A’ISHATULHUMAIRA*
*~Mikiya writer’s Association~*
*Gajeran labari ne.*
*Bismillahir Rahmanir Rahim.*
*page* *19&20*
________Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, idan kaga Ƙuraish sai ka ɗauka yakai shekara biyar, yayi tsawo da kiba sosai duka shekarar shi huɗu ya shiga dai ta biyar din ne, amma babu inda bai takawa da kafar sa, ga surutu kala kala sai dai ba kowa yake mawa ba. Yasan kowa, kowa kuma yasan shi, baida abokin faďa sannan kuma bai da aboki, dukkan wani lokaci nashi yana wajen su yah Babbah, hakan yasa bai shaku da mutane ba kamar yadda ya shaku da su yah Babbah, babban abokin shi Saraki ne, duk inda zasu je tare suke zuwa.
Zaune yake shi da Zahra, suna ta fira akan yadda bikin su zai kasance, duka yau saura kwana hudu bikin nasu. Shirye shirye ake sosai akan auran nasu, ta kowane bangare shagali ake tasha kamar yau ne bikin, a bakin kofar shiga bangaren su suke firar, basu ďauki lokaci ba sai ga tawagar su yah Babbah sun zo zasu shiga domin ayi shagali dasu.
Haidar na ganin sun kusa shiga ya miƙe da sauri ya isa bakin ƙofar ya tsaya, yadda ya tsane su, baya jin zai iya bari halitta daya daga namun dajin yazo hidimar bikin shi.
“Kada ma ku fara wannan kuskuren, niba irin sauran bane da zanji tsoron ku, dan kun bamu gurin zama ba yana nufin zaku dinga yi mana yadda kuka ga dama bane”.
Babu wanda ya motsa a wajen duk da sunji abin da ya fada amma ba zasu iya mayar wa ba,
Zahra dake gefe tana kallon su tace “Habaa masoyi ka basu hanya mana shagali fa zasu je ayi dasu, ni banga aibun su ba, bansan meyasa ka tsane su ba. Dan Allah ka basu hanya su wuce, tunda basu cutar damu ba don me kai kake son ganin ka shiga rayuwar su?”.
Wani banzan kallo yake jefa mata zuciyar shi na zafi, wadda yake so a rayuwar shi ita ke nuna soyayya ga abinda yafi tsana a duniya.
“Babu inda zasu shiga Zahra, ni bana buƙatar su a shagalin auren mu, dan haka su koma inda suka fito, bana kaunar ganin su a rayuwata wallahi”.
“Hmmm! Masoyi kenan yau ni ake kira Zahra saboda Ina gaya maka gaskiya, to kasani wallahi wannan abin da kake zai iya jawo matsalar da sai kafi kowa nadama, dan haka tun wuri ka gyara kuskuren da kake ƙoƙarin tafkawa”.
“Allah ne shaida ta nine ajalin su, sai na batar dasu, tunda suka wulakanta ni wallahi bazan bar su ba, yanzu na fara shirin yaƙar su, mu zuba nida su”.
Wata irin girgiza yah Babbah yayi, kafin kiftawar ido ai ga Haidar cikin ruwan da babu wanda ya taɓa shigar shi in ba su namun dajin ba.
Wasu irin halittu Haidar ya rika gani cikin ruwan wanda bai taba ganin su ba, su yah Babbah kuwa ciki suka ida sa shigewa suka barshi ciki, wata irin azaba wannan halittun suka fara ba Haidar, Zahra kuwa su yah Babbah tabi da gudu tana kuka tasan in har batayi wani abu ba to tabbas Haidar zai halaka ne a cikin ruwan dan haka tabi bayan su.
“Yah Babbah kayi min rai ka ceci rayuwar Haidar, shine mijin da zan aura idan na rasa shi bansan wane hali zan shiga ba, tabbas yayi kuskure amma insha Allah ba zai sake ba ayi mai afuwa a madadi na”.
ƙara fashe wa da kuka tayi yadda yah Babbah zai ji tausayin ta yasa a ceci rayuwar Haidar.
Cikin ikon Allah roƙon yah Babbah da tayi ya bada umarnin a fiddo Haidar daga cikin ruwan. Duk yadda yah Babbah yaso ya haƙura da zuwa shagalin kasa wa yayi, saboda darajar mutum huďu da suka je suka gayyato shi , Yah Kathub da Muhammad sai Saraki da Khadijerh suka kai mai gayyata shiyasa bai iya musu ba suka taho wajen shagalin bikin.
Komawa inda Haidar yake tayi, tana zuwa wata Halitta ta wurgo shi waje, da sauri ta isa gareshi. Sai dai wani abin mamaki babu wata alama ta ciwo ko jigata a jikin haidar, yasha ruwa sosai a lokacin da yake cikin ruwan, ya jigata kamar bazai rayu ba idan ya fito sai gashi sun ga akasin hakan, kansu ya ɗaure sosai da ganin wannan ikon Allah.
Ƙuraish da Saraki ne suka tarbe su, inda aka ware ma yah Babbah da zuri’ar sa daban, dan haka suna zuwa aka kai su inda aka tana da musamman domin su.
Kamar zuwan nasu ake jira shagali ya fara, mutanen dake wajen kowa kagani cikin farin ciki yake, sai kiɗe kiɗe ake irin nasu na mutane, ana ciye-ciye ana taka rawa. Sai da sukayi mai isar su sannan su yah Babbah suka fara nasu wasan me ƙayatar wa. Baka jin komai a wajen sai tafi da ihu ana ta murna.
Wannan shagalin da ake musamman ake yinshi saboda da mutane da su yah Babbah, babu amarya ba ango sai isu isu kawai ke shagalin, ansha shagali sosai har magriba sannan aka tashi kowa ya koma muhallin sa. A haka shagalin biki yayi ta tafiyar har ranar daurin aure. Inda duka mutane da namun daji suka shaida ɗaurin auren Haidar da Zahra.
Yah Babbah yana matukar kaunar Kuraish hakan yasa komai Haidar keyi yake kyale shi, saboda albarkacin Kuraish din da mahaifiyarsa. Shiyasa ya fara tunanin ta hanyar da zai bullo ma Haidar, saboda bai son dalilin mutum ďaya yayi abinda bai dace ba. Koba komai akwai wanda suke kallon su da daraja a matsayin su na dabbobi.
Kiran gaggawa ya haďa na musamman ga dukkan wani mai faďa a ji a cikin su domin bai yanke hukunci shi kaďai dole akwai bukatar su san abinda yake faruwa . Koda suka gama abinsu yah Babbah ya kara mai da hankali akan duk wani motsi da Haidar din zai yi, yana kallon shi yana kuma fahimtar sa. Yana jiran lokacin da zai banbance tazarar dake tsakanin sama da kasa.
A haka rayuwa ta cigaba da tafiya Haidar da amaryar sa Zahra ana ta shan amarci, a lokacin Haidar bai nuna ma kowa akwai abinda yake shiri ba, har ita Zahra bata san me yake shirin yi ba saboda bai gaya mata ba, bai kuma tunanin zai gaya ma kowa. Tunda akayi auren su da tsiya aka bashi Ƙuraish ya dawo wajen su da zama sun ɗauki so mai tsanani sun ɗaura ma Ƙuraish, duk abinda yake so shi akeyi.
Burin shi da fatan shi Zahra ta samu ciki, domin dukkan wani shiri da wani ƙudiri nashi akan Ɗan da zai haifa ne ko ƴar da zai haifa, domin gudan jinin shi zai ɗaukar mai fansa akan su yah Babbah. Sai dai gashi har suna neman kulle wata shida Zahra bata da ciki kuma alamun shi, hakan yasa ya fara ƙoƙarin aiwatar da abinda yake so da Ƙuraish.
Abinda bai sani ba ga Kuraish yana da mugun yawon da sai ya siyar da shi kansa Haidar din kar yake kallon kowa, wayon shi ya girmi shekarun sa. Bai san
yadda ya ɗauki su yah Babbah ba daban ne a rayuwar shi, dan haka koda ya gaya masa ƙudirin shi nasan yaje ya zuba masu wannnan guba me ƙarfin gaske a ruwan shan su, kamar yadda yayi kokarin aikatawa bai samu nasara ba.
Aikuwa nan take Ƙuraish ya birkice masa, gaba ďaya kamannin sa suka sauya ya rikiɗe ya koma wata halitta shi ba zaki ba shi ba mutum ba, ga wani irin gurnani da yake yi. Wata irin hajijiya ya riƙa yi da Haidar a cikin dakin, kafin wani lokaci gaba ďaya kamannin Haidar sun sauya yayi laushi, numfashin shi da kyaar yake fita.
Jin gurnani a ďakin dasu Haidar suke shida Ƙuraish yasa Zahra da take aikin shara aje tsintsiya ta ruga da gudu zuwa cikin ɗakin, abinda ta gani ne ya sata yanke jiki ta faďi sumammiya…..
Share
Comments*MUTUM KO ZAKI*
*NA*
*A’ISHATULHUMAIRA*
*~Mikiya writer’s Association~*
*Gajeran labari ne.*
*Bismillahir Rahmanir Rahim.*
Page 21&22.
_____An ɗauki lokaci kafin Ƙuraish ya koma asalin halittar sa ta mutum, koda ya dawo hayyacin shi yaga halin da Zahra da Aliyu suke ciki sai da ya tsoro ta, da sauri ya ruga da gudu zuwa gidan yah Kathub ya kirasu. Koda suka iso sun tsorata su ma da suka ga halin da su Aliyu suke ciki, da sauri aka basu taimakon gaggawa suka dawo hayyacin su.
Gaba ɗaya lamarin ya ɗaure ma Zahra kai, ita dai zaki ta gani da idon ta yana wuju wuju da Haidar, kuma bata ga Ƙuraish ba a ɗakin bayan tasan su biyu ta bari, abinda ya kuma kiɗima mata lissafi ganin Ƙuraish ba abinda ya same shi, bayan rashin ganin nasa yasa ta ɗauka cewar zakin ya cinye shi. Abinda yasa ta yanke jiki ta faɗi sumammiya kenan,
“Zahra meke faruwa ne a gidan naku” tambayar da yah Kathub ya jeho mata ne ya dawo da ita hayyacin ta, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗaga kanta tana kare ma mutanen dake wajen kallo.
“Bansan abinda ya faru ba, kawai Ina aiki naji ihu da ƙarar gurnani haka shine nazo na gani, ina zuwa na iske wani babban Zaki yana mashi haka daga nan bansan abinda ya faru ba sai yanzu dana ke ganin ku”.
Ajiyar zuciya yah Kathub ya sauke yana kallon Haidar da yake ta runtse ido saboda azabar da yake ji a cikin jikin shi. “Tabbas idan hakane Haidar yayi yunƙurin aikata wani abu ga namun dajin nan shiyasa hakan ya faru dashi, kenan mafarkin da nayi yakan iya zama gaskiya kenan idan har ban yi wani abu akai ba” yah Kathub yake maganar shi kaɗai bayan ya fito daga cikin ɗakin da suke. Gaba ɗaya mafarkin da yayi ya shiga dawo mashi daki daki.
(Idan har ya kasance kun kasa saka Alkhairi da Alkhairi to mayar da sharri bazai taɓa zama jindadi ga ruhin da aka yi ma halacci ba, canza ƙudirin ku yana nufin zaman lafiya a gareku, aka sin haka barazana ne ga rayukan da basu ji ba basu gani ba.
Mafi girman kuskuren da ɗayan ku zai aikata, shine mafi girman zunubi a wajen wasu, in ma dakatar da hakan in ma kasancewar abinda ba’a yi zata zo.
Akwai jinsi mafi ƙarfi daya kasance namu kuma a cikin ku, gaurayar tsakuwa cikin aya ba yana nufin duka zasu taunu a cikin baki bane).
“Yakamata nayi wani abu akai, ina buƙatar wanda zai taimaka min akan lamarin nan, sai dai kuma abin kunyar daga gida na ɓarakar take neman fitowa kuma kowa yasan Haidar ne ke neman taƙalo fitinar nan akan kafiyar shi ta banza”.
“Koda wasa kada ka taɓa bari ya janyo maku fitinar da bazaku iya da ita ba. Ka lallashe shi ko ka tsawatar mashi wannan duk ya rage gareka, amma tabbas ina mai gaya maka zai janyo maku abinda zakuyi nadama babba in kuna da sauran kwana a gaba kenan”.
Ƙuraish ke wannan magana cikin natsuwa kamar ba daga bakin shi furucin ke fitowa ba.
Gaba ɗaya sai kan yah Kathub ya ƙara ɗaurewa akan lamarin domin ya fara zargin abubuwa da yawan gaske game da ƙuraish.
Kafin yayi wata magana yaji maganar khadijerh a bayan shi wato mahaifiyar ƙuraish.
“Tabbas dukkan abinda ya faďa gaskiya ne, Baba dakatar da abin tun kafin yin nisan shi, shine ceton rayukan mutanen da suka mika dukkan yardar su gareka. Domin abinda yake ƙoƙarin yi masu sam ba halacci bane, Kuma basu cancanci hakan daga garemu ba”.
Tana gama faďin haka tayi tafiyarta gida saboda sam jikinta na bata akwai abinda Haidar yayi ƙoƙarin yi gasu yah Babbah, su kuma suka mashi haka, shiyasa ma tana yi masu sannu ta fito domin komawa gida anan taji maganar da ƙuraish ke gaya ma yah Kathub. Duk da tayi mamakin yadda ƙuraish ɗin yayi maganar kamar babba.
Ajiyar zuciya yah Kathub ya sauke domin dukkan abinda suka faďa gaskiya ne, Kuma dole ya ɗauki tsatsauran hukunci akan Haidar. Koda ya juya bai ga Ƙuraish ba domin shima yayi tafiyar sa wajen su yah Babbah, Jikin sa a sanyaye ya juya zuwa gida.
Cikin ɗakin da Haidar yake kuwa, sunyi jigum jigum kowa da abinda yake tunani akan jikin Haidar din, Ummu ce tayi gyaran murya tana faɗin.
“Gaskiya Haidar kayi ma kanka faɗa, ka kiyayi Dabbobin nan domin banga abinda suka tsare maka ba da har kake neman kashe kanka a banza”.
“Hmmm! Kema dai kin faďa ace kai bazaka zauna da kowa lafiya ba, ina ruwan shi dasu da yabi ya takura ma rayuwar su? Kawai kayi ta janyo ma kanka fitina kana zaune lafiya”. Ammi ta faɗa cikin faɗa domin abin na haidar ya fara isar ta.
“A’a ku bishi a hankali mana, kunga fa halin da yake ciki kuma..”
“Anki a bishi a hankalin duk ba shine ya janyo ma kanshi ba, ko kuwa wani yaje ya janyo mashi uhm” Ammi ta katse Muhammad cikin faɗa ba tare da ta bari ya ƙarasa maganar shi ba, dole yayi shiru tunda yaga ran Ammi ya ɓaci.
“Kiyi haƙuri Ammi, zamu zauna dashi akai insha Allah daya samu lafiya, Kuma hakan bazata kuma faruwa ba da yardar ubangiji”.
Usman ya faɗa cikin sanyin murya ganin yadda ran mahaifiyar tasu ya ɓaci.
Haƙuri suka cigaba da bata har suka samu ta sauka, sannan suka cigaba da magana akan lamarin, Zahra dai na gefe abin duniya ya ishe ta.
Ƙuraish kuwa shi da mahaifiyar shi ɓangaren su yah Babbah suka nufa, har tayi gida sai kuma tayi tunanin taje can kwana biyu bata je ba.
Zuwan su ɓangaren yah Babbah ya sata farinciki sosai ganin yadda ɗan ta keta shawagi cikin manyan namun daji , ga wani girma na musamman da suke bashi yadda yake basu umarni abin har mamaki ya bata ya koma kamar yah Babbah.
Sai da ya gama sarautar tashi sannan ya shiga cikin ɗakin yah Babbah, a tare suka fito cikin ɗakin, yah Babbah na gaba ƙuraish na biye dashi a baya, koda suka fito inda take tsaye suka nufa, domin shigar da yayi ďakin yah Babbah gaya masa yayi zuwan mahaifiyar tasa.
Cikin girmamawa yah Babbah ya ďan duƙar da kansa alamar gaisuwa, haka shima ƙuraish ɗin yayi bisa umarnin yah Babbah daya kalle shi.
Murmushi tayi tana kallon su cikin so da ƙauna tare da kulawa ta musamman ta durƙusa tana gaida yah Babbah kamar yadda ta saba tun asali. Kai ya jinjina mata alamar amsawa sannan ya koma inda yake zama ya zauna, fira suka cigaba dayi ita da ƙuraish da kuma sauran namun dajin dake wajen, sun dade sosai suna fira sannan ta tashi ta koma ɓangaren su ta bar ƙuraish nan don shi ba lokacin yake komawa gida ba.
Yah Babbah ne ya tashi ya koma ďakin shi domin kwantawa ya huta, yana tafiya Ƙuraish ya tashi ya koma mazaunin yah Babbah ya zaune, gaba ɗayan su suka duƙar da kai ƙasa alamar girmamawa da miƙa kai gareshi….*MUTUM KO ZAKI*
*NA*
*A’ISHATULHUMAIRA*
*~Mikiya writer’s Association~*
*Gajeran labari ne.*
*Bismillahir Rahmanir Rahim.*
Page 23&24.
_____________Bayan wani Lokaci, abubuwa da dama sun faru ciki har da samun cikin Zahra, Haidar yayi murna da farin ciki sosai akan samuwar cikin kowa yasan da cikin, mutane sunyi murna sosai na samun shi, sai dai babu wanda yakai kuraish murna da farin ciki. Sosai yake nuna kaunar cikin, koda yaushe yana makale da Zahra saboda cikin nan koda yaushe addua yake akan Allah yasa ta haifa masa mace.
Cikin Zahra wata bakwai akayi bikin zainul abeedeen, ansha shagali sosai sai dai wannan karon su yah Babbah basuyi shagali ba kamar yadda sukayi a bikin Haidar da sunan Kuraish, son zo dai amma ba’a yi biki dasu ba. Hakan kuwa yasa yah Kathub a damuwa sosai domin yasan abinda Haidar yayi masu ne yasa suka ki zuwa wajen bikin kamar yadda suka saba duk da gayyatar da yayi masu.
Ana cikin shagalin bikin ne Kuma matar usman ta haihu, ta samu namiji again umar ya samu ďan uwa, sosai murna ta kara kacamewa a wannan ahali nasu kowa kagani bakinsa buďe saboda farin ciki. Sai dai duk wannan abu dake faruwa babu kuraish a wajen, domin tunda aka fara bikin ya tafi bangaren su yah Babbah da kayansa a cikin su ya koma kwana, babu yadda ba’a yi dashi ba akan ya dawo amma yaki dawowa cikin su a cewar shi baisan hayaniya.
Yah Kathub ya shiga damuwa sosai domin ji yake kamar wani abu yana dab da faruwa ta dalilin shi, sai dai ya kasa gane ko menene. Koda yaushe cikin damuwa yake game da wannan mafarki da yayi dan haka ya yanke shawarar kiran Ammi su tattauna akan maganar ya fara samun mafita a gida kafin ya fita da maganar ga manyan garin yan uwan sa. Kasancewar ummu na gidan jego bata nan shiyasa bai kira da ita ba sai Ammi kawai ya aika wani yaro ya shiga ya kirata ta iske shi anan lambun dake cikin gidan su.
Da sallama ta shigo cikin lambun tana kallon mijin nata wanda a lokaci daya ta gane yana cikin damuwa sosai dan haka guri ta samu ta zauna tana kallon shi tare da fara magana.
“Amincin Allah ya tabbata a gareka zauj, ina rokon Allah daya yaye maka damuwar dana gani a idonka, ya maye gurbin ta da Alkhairi, ina rokon Allah daya shiga cikin lamarin ka ya kawo maka haske me dauke da waraka tare da farin ciki. Meke damun mijina haka daya kebance kansa yana tunani?”
Ajiyar zuciya ya sauke tare da jin wata natsuwa na ratsa dukkan jikinsa, wata irin kauna me zafi ta motsa masa wadda yake jin kamar ya maida matar tasa ciki saboda kauna. Yana alfahari da khairiyya saboda hankalin ta da kuma natsuwar ta tasan duk wata hanya da zata bi ta faranta masa tun kuruciyar su har kuma yanzu da suka manyan ta. Auren soyayya sukayi wanda silar rashin amincewar wasu daga cikin yan uwan su yasa suka baro dangin su suka taho nan domin gudanar da rayuwar su, kasancewar sun taho da rakuman su ne yasa sukayi cikin daji anan sukayi ta had’uwa da mutane har sukayi yawa sosai suka kafa garin da suka zauna a farko kafin zuwan su wajen su yah Babbah.
“A koda yaushe ina alfahari dake khairiyya ke din ta dabance a cikin rayuwata Allah ya albarkaci rayuwar ki data zuri’ar ki”.
Murmushin jin dadi tayi tare da amsawa da “Ameen ya Allah zauj” Tana kallon sa.
Gyaran murya yayi ya fara magana.
“Dalilin daya sa na kiraki shine game da matsalar da Haidar yake neman janyo mana, nasan kin fahimci wani abu ko ince kusan kinsan komai dake faruwa. Ya kike ganin zamu bullo ma lamarin ne? Haidar bai jin magana yana neman janyo mana abinda yafi karfin mu domin ba iyawa zamu yi dasu ba kinsani”.
“Hmmmm! Ka sosa min inda ke mani kaikai zauj, Haidar baya ji nayi mai magana ya nuna ya bari amma nasan kafiyar shi ba lallai ne ya hakura ba, Kuma su bamu me zasu iya aikatawa garemu ba muddin muka bari Haidar yayi yunkurin cutar dasu”.
“To ni kaina abinda zasu iya aikatawa garemu ne yake damuna muddin muka bari Haidar yayi masu wani bu domin kuwa kamar butulci ne hakan ga wannnan mafarkin da nayi ya tsaya min rai sai dai na kasa mai kyakkyawarfahimta”.
“Zauj wane irin mafarki ne wannan kuma?”
“(Idan har ya kasance kun kasa saka Alkhairi da Alkhairi to mayar da sharri bazai taɓa zama jindadi ga ruhin da aka yi ma halacci ba, canza ƙudirin ku yana nufin zaman lafiya a gareku, aka sin haka barazana ne ga rayukan da basu ji ba basu gani ba.
Mafi girman kuskuren da ɗayan ku zai aikata, shine mafi girman zunubi a wajen wasu, in ma dakatar da hakan in ma kasancewar abinda ba’a yi zata zo.
Akwai jinsi mafi ƙarfi daya kasance namu kuma a cikin ku, gaurayar tsakuwa cikin aya ba yana nufin duka zasu taunu a cikin baki bane). Ki fahimtar dani khairiyya na shiga ruďani akan wannan mafarki, yana min nuni da wani abu amma na kasa fahimtar menene wannan abin”.
“Idan na fahimta yana nufin muddin Haidar ko wani yayi yunkurin cutar dasu to tabbas rayukan mu da basu ji ba basu gani ba zasu salwanta, kenan kashe mu zasuyi.in har wani abu ya samu dayan su
In ma mu dakatar da faruwar hakan ko kuma mu fuskanci hukunci daga garesu. Jinsin dake nasu a cikin mu kenan kuraish ne sun mashi abinda ya zama nasu, to meye dalilin su na mayar dashi cikin su duk da namu ne?”.
“Tabbas sai da kikayi bayanin nan na fahimci abinda mafarkin nan ke nufi, yanzu kenan alkawarin dake tsakanin mu shine cigaban numfashin mu da zaman lafiyar mu, idan muka karya alkawarin yana nufin komai yazo karshe kenan”.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raju’un! Dole ne mu dakatar da Haidar muddin muna son tsira da rayuwar mutanen mu, saboda nasan bai hakura ba yadai nuna komai ya wuce amma nasan Haidar dole da wani abu a cikin ranshi, zauj kayi wani abu akai tun kafin ya sake wani yunkurin”.
“Khairiyya insha Allah Haidar bazai aikata komai ba kuma zanje naga yah Babbah na bashi hakuri akan abinda ya faru, karki saka damuwa aranki tunda har komai ya warware to komai yazo karshe ai, shiyasa dama na kiraki muyu maganar bansan nayi ta da wani saboda abinda kaje ya dawo. Dan haka ki koma gida bari naje masallaci na dawo”. Jiki a sanyaye suka mike ta nufi gida shi kuma ya nufi masallaci.
Bayan wata biyu Zahra ta haifi ďiyarta me kyau fara sal me kyawun gaske babu inda ta baro Zahra, da nanah khadeejarh Haidar yayi mata huďuba. Ranar suna aka sha shagalin Nanah khadeejarh suna ce mata Nanah. Sosai kuraish yayi farin ciki da samun Nanah koda yaushe yana manne da ita wata irin kauna yake mata, baya son yaji ko kukan nan na jarirai tana yi yanzu zai tada hankalin kowa. Dashi akayi wankan jegon Nanah har sukayi arba’in. Shike rainon ta shan nono kawai ke kaita wajen mamarta.
A haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya da daďi babu har Allah yasa Nanah ta shekara a kuma lokacin har tafiya tanayi, babu inda Bata zuwa, sai dai duk yadda kuraish yaso ya kaita wajen su yah Babbah kin yadda tayi ko kaďan bata yarda yayi hanyar da ita kamar tasan meye a wajen sai tayi ta kuka tana ihu dole ya haƙura da zuwa da ita can din….
Comments
And
Share Fisabilillah *MUTUM KO ZAKI*
*NA*
*A’ISHATULHUMAIRA*
*~Mikiya writer’s Association~*
*Gajeran labari ne.*
*Bismillahir Rahmanir Rahim.*
Page 25&26.
_____________ Tunda Nanah ta fara wayau ta tsani su yah Babbah, wata irin tsana me girma da ban mamaki take yi masu yah Babbah, duk wani abu daya shafe su to abokin gabar ta ne, hakan da ƙuraish ya fahimta ne ya fara kawo masu sabani tsakanin shi da ita.
Wata irin zazzafar shaƙuwa da ƙauna ke tsakanin su, tunda aka haife ta baya ƙaunar duk wani abu da zai ɓata mata rai, duk wata kula da soyayya wajen Nanah yake ƙarewa. Sai dai duk da wannan ƙauna da ƙuraish yake ma Nanah, bata kai wadda yake ma su yah Babbah ba, wuri na musamman ke garesu a rayuwar ƙuraish.
Sai dai kuma Nanah Sam bata ƙaunar su ko kaɗan, duk da shekarun ta biyar ne amma kafiyar ta da shegen wayon ta ya wuce shekarun ta. Babu abinda ta baro wajen mahaifinta, komai shi ta biyo hakan yasa tsanar su yah Babbah tabi jikinta, tun bata kai haka ba mahaifinta ke nuna mata kyamatar su yah Babbah hakan kuwa yayi Tasiri sosai a zuciyar ta, domin kuwa da hakan ta tashi tun ba tayi wayau ba.
A haka rayuwa ta cigaba da tafiya da ďadi da babu, sai da wannan ƙiyayya data gifta tsakanin ƙuraish da Nanah wanda ada ba haka suke ba wata irin soyayya suke ma junan su kamar ba gobe, amma a yanzu kowa tsanar ďan uwanshi yake saboda banbancin ra’ayin su. Har zuwa lokacin da suka girma wannan lamari bai daidaita ba tsakanin su domin kowane yaƙi aje makaman yaƙin shi, babu wanda yake jin zai sauka akan layin da yake kai.
Ɓangaren Haidar kuwa sosai yake ƙara rura wutar ƙiyayyar su yah Babbah a zuciyar Nanah, duk yadda yaga tana alamun sauka akan layin daya ɗaura ta sai hankalin shi ya tashi, domin yasan ba ƙaramin so take ma ƙuraish ba kuma a koda yaushe tana iya canzawa a dalilin wannan son da takeyi mashi.
Tunda ya fahimci shi Ƙuraish akan su yah Babbah zai iya yin komai zai kuma iya rabuwa da kowa, wannan dalilin yasa ya dage wajen haddasa fitina tsakanin su wadda take neman zama gagarumar ƙiyayya. Kullum maganar shi ďaya
“Taya za’a yi ace namun daji sune ke mulkar mu bayan mune yakamata ace suna ƙasan mu sai yadda mukayi dasu”.
Tun su yah Kathub basu jin komai akan maganar ta Haidar har suma suka fara wannan tunanin, sai dai duk yadda suka so su amince da abinda Haidar ďin ke faďa sai wani babban al’amari ya gifta tsakani, hakan yasa suka fara shiri ta yadda zasu yaƙi su yah Babbah ba tare da sanin kowa ba don su mamaye dukkan tsaunikan.
Sosai suka haɗa duk wani makami da zasuyi amfani dashi domin gamawa da su yah Babbah.
Ƙuraish kuwa a bakin Nanah ya samu labarin abinda yake shirin faruwa, dan haka ya nufi gidan yah Kathub ran shi a ɓace tana biye dashi a baya tana dariya. Kasancewar duk ahalin gidan suna nan hakan yasa koda Kuraish ya shigo a tsakar gidan ya isko su suna fira.
“Ban taɓa sanin cewa kuɗin butulu bane sai yanzu, abinda kuke ƙoƙarin aikatawa shine mafi girman kuskuren da zaku aikata, meyasa zaku saka Alkhairi da sharri? Meyasa bazaku kasance masu rama alkhairi da alkhairi ba? Meyasa bazaku rama halaccin da aka maku ba da alkhairi? Meyasa bazaku cika Alƙawarin da kuka ɗauka ba? Idan har Dabba zata riƙe alƙawarin dake tsakanin ku ta kasa cutar daku meyasa ku mutane ba zaku riƙe ba? Wallahi ina jiye maku abinda zaku jawo ma kanku, zaku yi nadama a lokacin da bata da amfani”.
Yana gama maganar shi ya juya a fusace ya bar gidan, shekara ashirin da biyar gareshi amma sai ka ɗauka yakai shekara talatin. Dukkan wata mazan taka ta bayyana a wajen ƙuraish.
Gaba ɗaya wajen jikinsu yayi sanyi domin su kansu sun san abinda suke ƙoƙarin yi ba mai kyau bane, bai kuma dace su aikata hakan ba ga wanda suka masu wannan karamcin. Ita kanta Nanah a lokacin sai da taji babu kyautawa akan abinda suke shirin yima su yah Babbah.
Duk da shekarun ta sha biyar Amma ta fahimci abinda ƙuraish ya faɗa domin bata san komai ba akan zaman su nan ďin ita dai kawai ta taso kuma mahaifinta ya ɗaura ta akan ƙiyayyar su yah Babbah hakan yasa Bata san komai ba akai.
Abinda basu sani ba tuni yah Babbah ya shirya ma zuwan hakan su kawai yake jira su motsa, domin duk abinda yake faruwa ɓangaren su yana gani yana kuma ji sai dai ya ɗauki alwashin koda zai rasa ransa sai ya koya ma mutane hankali.
SHARE FISABILILLAH.*MUTUM KO ZAKI*
*NA*
*A’ISHATULHUMAIRA*
*~Mikiya writer’s Association~*
*Gajeran labari ne.*
*Bismillahir Rahmanir Rahim.*
Page 27&28.
_________Gaba ɗaya mutanen dake ɓangaren yah Kathub sun shirya ma wannan yaƙi da suke ƙoƙarin yi, dukkan wani namiji me jini a jika yana cikin tafiyar, ƙuraish ne kawai babu domin shi ɓangaren su yah Babbah ya koma da zama acan yake rayuwar sa. Sosai yah Kathub da jama’ar sa sukayi kunnen uwar shegu da maganar da ƙuraish ya faɗa masu, duk da sun so su ɗauki maganar nashi amma Haidar ya shiga ya fita har suka shashantar da maganar, kowa kuma ya bada goyan bayan wannan faɗa da zasu yi mahaifiyar ƙuraish ce kawai bata aminta ba amma duk wani wanda ya kwana a wannan ɓangaren ya goyi bayan wannan lamari, sai dai da yawan mutane suna cikin fargaba na samun nasara ko akasin hakan.
Duk yadda khadijerh taso fahimtar da mijinta akan kuskuren da suke ƙoƙarin yi kin sauraren ta yayi, domin ya goyi bayan yan uwanshi akan haka. Dole ta haƙura ta zuba ma sarautar Allah ido, amma ta kasa yadda da cewa zasuyi nasara bayan sune sukayi butulci.
Jiki a sanyaye ta tafi ɓangaren su yah Babbah domin ta samu su tattauna da ƙuraish akan lamarin, sai dai tana shiga ta ga irin shirin da suke akan harin da ake son kawo masu ya tsorata ta sosai, duk wani shiri dasu yah Kathub suke ashe ba shiri suke ba ga wanda suka shirya ma abin nan suna yi, da mutuwar jiki ta karasa wajen dasu yah Babbah suke zaune shida kuraish da Saraki sai mama suna cin nama. Da sallama ta isa garesu, ƙuraish ya amsa mata tare da gaishe ta.
“Barka da yini yah Babbah, mama barka da yini”.
Kai suka jinjina mata alamar amsawa, Saraki ma gaisuwa ya taso ya kawo wajenta irin wadda ya saba tun yana karami.
Magana ta fara yi cike da mutuwar jiki, hawaye na sauka a idanunta, tashin hankalin da take ciki yana da girman gaske.
“Muhammad kana sane da abinda su yah Kathub suke ƙoƙarin yi ga waɗannan bayin Allah da suka masu halacci, suka sanya su a inuwa lokacin da suke neman mafaka, suka aje komai nasu suka yarda dasu da zuciya daya amma yanzu kaga irin butulcin da zasu yi masu”.
Wani irin ɓacin rai ne ya ziyar ci kuraish, ta sosa masa inda ke mai ciwo, ko kaďan bai fatan suyi nasara akan su yah Babbah yafi son su yah Babbah suyi nasara akan su yah Kathub ko dan suyi hankali.
“Ki barsu suyi duk abinda zasu yi tunda su din butulu ne, basu san halacci ba”.
“A’a Muhammad musan yadda zamuyi dai kar wannan faďan ya faru, domin wallahi abin bazai yi kyau ba, gara tun da wuri mu dakile shi ina jin tsoron abinda zai faru wallahi”.
“Kiyi haƙuri kawai amman tabbas sai abinda baki so ya faru, Kuma ni bazan goyi bayan su ba, ina nan tare da su Saraki bazan taba juya masu baya ba, sannan ko faďan ne dani za’a yi shi sai inda karfina ya kare”. Yana gama faďar haka ya mike suka nufi can cikin bangaren nasu yah Babbah shi da Saraki.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raju’un! ya Allah ka kawo mana ďaukin wannan fitina da take neman ballewa”. Jiki a sanyaye ta mike hawaye na zuba a idanunta ta nufi bangaren su, da niyyar isa wajen yah Kathub akan su janye abinda suke neman jawo masu.
Koda ta isa ta samu yah Kathub da maganar, bai na’am da ita ba sai ma ranshi da yaso baci akan neman dakile su da take yi. Haka ta tashi ta tafi gida zazzabi ringis jikinta.
*BAYAN KWANA BIYU*
Cikin sanďa suke ta shiga ɓangaren yah Babbah da makaman yakin su, babu tunani ko dogon nazari kawai suka shiga , kusan duk wani namiji dake can indai bai tsufa ba to Yana nan yawansu yakai mutum ďari tsoffi ne kawai babu sai yara sai kuma likitocin su da aka baro ciki har da Muhammad, yah Kathub ne gaba sai sauran manyan gari a bayan shi, Haidar na ďauke da tawagar samarin su duka. Sai da suka gama shigowa gaba daya sannan suka fara neman inda namun dajin suke, sai dai duk inda suka duba basu gansu ba.
Abinda basu sani ba yah Babbah yana kallon duk abinda suke harta neman nasu da suke yana saman tsauni yana kallon su, sauran namun dajin kuwa suna babban filin su na faďa da kayan yakin su suna jiran isowar su. A shirye suke da kayan faďa masu tada hankali a yau duk wata dabba a asalin dabba take kamar suci babu suke ji, Kuraish ne gaba sai Saraki a gefen shi ya fito a asalin zakin shi. Jiran isowar su kawai suke domin yah Babbah ya cire duk wani tsafi dake jikin namun dajin na hana su taba mutane dan haka suke jin wani karfi a jikinsu.
Isowar su babban filin da namun dajin suke sai da yasa masu faďuwar gaba amma duk da haka suka kasa juya wa su koma ko su canza kudirin su. Babu abinda yafi ďaga ma yah Kathub hankali irin yadda yaga Kuraish a cikin su kuma cikin shirin yaki, tunani ya shiga yi akan mafarkin da yayi, domin yaga abinda mafarkin yake nufi a zahiri.
Wata irin murya suka ji ta fara magana wadda basu san daga ina take fitowa ba.
“Idan baku fahimta ba to ina so ku saurara, Idan har ya kasance kun kasa saka Alkhairi da Alkhairi to mayar da sharri bazai taɓa zama jindadi ga ruhin da aka yi ma halacci ba, canza ƙudirin ku yana nufin zaman lafiya a gareku, aka sin haka barazana ne ga rayukan da basu ji ba basu gani ba.
Mafi girman kuskuren da ɗayan ku zai aikata, shine mafi girman zunubi a wajen wasu, in ma dakatar da hakan in ma kasancewar abinda ba’a yi zata zo.
Akwai jinsi mafi ƙarfi daya kasance namu kuma a cikin ku, gaurayar tsakuwa cikin aya ba yana nufin duka zasu taunu a cikin baki bane. Sai dai lokaci ya kure maku domin wanda kuke ganin shine ďan ku toh ba naku bane namu ne, kun kasa nuna Halacci garemu, kun nuna mana ku butulu ne, zakuyi nadama a lokacin da bata da amfani, zaku girbi abinda kuka shuka, zaku jama wanda basu ji ba basu gani ba”.
Gaba ďaya hankalin su ne ya tashi domin basuyi tunanin karfin su yana da alaka da Aljannu ba, ba kuma suyi tunani akan makomar abinda zai biyo bayan abin ba.
“Babu ta yadda zai muna mutane ace Zaki ne zai mulke mu, bayan munfi ku komai da komai”. Da sauri yah Kathub ya ďaga ma Haidar hannu alaman yayi shiru, sannan ya gyara tsayuwa ya fara magana.
“Muna son sanin Kuraish tsagin ku yake ko namu dan haka kai Muhammad fada mun da bakin ka, *MUTUM KO ZAKI* wane zaka zaba”
Da sauri na kusa da yah Kathub ya amshe zancen da cewar.
“Ba wannan ya kamata ka fara sani ba shin *MUTUM*ne ko *ZAKI*”.
“A aikace zaku gani” suka ji muryar da tayi magana ďazu amma basu san daga ina take fitowa ba.
Kafin su gama tunanin da suke, Kuraish ya fara wata irin girgiza tare da wani irin kuka me ban tsoro, jikinshi yana rikiďewa shiba Mutum ba shi ba Zaki ba. Basu gama gani wannan tashin hankali ba sauran namun dajin sukayo kansu da wani gudu tare da gurnani na tashin hankali. Dole suka fara ciro makamai suma suna nufar su ba tare da tunani ba.
Sosai faďa na tashin hankali ya barke tsakanin su sai dai ganin yadda ake ta yagal gala mutane sauran suka fara neman hanyar guduwa duk da suma sun kashe wasu daga cikin namun dajin amma ance sarkin yawa yafi sarkin karfi domin su yah Babbah sunfi yawa. An kashe mutane sunkai hamsin da wani abu sauran da suka ga haka sukayi ta guduwa domin ceton ransu, koda Haidar yaga mutane na guduwa kin tafiya yayi sai ma kara dagewa da yake wajen kashe namun dajin.
Yayi barna sosai sai dai yana tunkarar Saraki da niyyar kashe shi yaji karar yah Kathub ya faďi kasa matacce.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raju’un shine abinda ya furta tare da rugawa da gudu wajen mahaifin nashi. Ganin haka kuraish ya dakatar da faďan tare da basu umarnin yin baya, shi kuma ya nufi inda Haidar yake rungume da yah Kathub yana kuka.
“Yanzu me hakan ya jawo? Kaine silar mutuwar mahaifin ka, akan wani banzan kudirin ka, ka rasa wanda ya kawo ka duniya. Meye ribar daka samu? Wace nasara kasamu akan kashe waďannan bayin Allah da akayi? Tirr da hali irin naka baba, da wane ido zaka kalli su Ammi bayan kayi silar mutuwar mijinsu?”
Yana gama faďar haka ya juya ya tafi yana share hawaye. Duk abinda suke yah Babbah na kallon su shima dai da alamun baiji dadin abin ba, don dai babu yarda zaiyi ne idan ya bari kashe su za’a yi gaba ďaya.
Sai da yasha kuka me yawa sannan ya ďauki gawar yah Kathub ya nufi bangaren su da ita, koda ya shiga gaba ďaya yan bangaren suna daga bakin kofar kowa kagani kuka yake na fitar hankali, babu me lallashin wani, sai dai ganin Haidar da gawar yah Kathub ya sake haukata dukkan su domin da yawan su sai da suka yanke jiki suka fadi, ba karamin rashi sukayi ba. Ammi da Ummu kuwa da sun farfaďo suke sake komawa suma domin tashin hankalin ya masu yawa ga mutuwar zainul abeedeen gata mijin su usman kuma na can rai hannun Allah.
Sun ga tashin hankali iya tashin hankali sai da komai ya lafa ne sannan wasu sukaje suka kwaso gawar sauran aka masu sallah aka kaisu gidan su na gaskiya…..
Share Fisabilillah*MUTUM KO ZAKI*
*NA*
*A’ISHATULHUMAIRA*
*~Mikiya writer’s Association~*
*Gajeran labari ne.*
*Bismillahir Rahmanir Rahim.*
Page 29&30.
Finally.
_____Bayan kwana bakwai da rasuwar yah Kathub, abubuwa da dama sun faru ciki harda faďan da mutane sukayi da Haidar, a cewar su shine ya janyo masu wannan tashin hankalin da suke ciki. Da kyar dai dattijan garin suka samu abin ya lafa kowa ya ďauki hakuri da dangana.
Gidan maragayi yah Kathub kuwa abin yazo masu a baza ta, sai dai sun rungumi jarabawar da tazo masu da hannu bibbiyu. Tunda aka gama zaman makokin yah Kathub koda yaushe zuri’ar gidan suna nan, sai dai kowa ka gani babu wannan farin cikin da sukeyi idan suka haďu. Duk wanda ka gani babu walwala a tattare da fuskar sa, duk sunyi jigum jigum dasu.
Muhammad ne ya tashi ya fara masu nasiha akan rashin da sukayi, tunda ya fara magana wasun su suka fara hawaye, sosai ya masu faďa tare da basu shawarar yin hijira domin tsira da rayuwar su tunda Haidar ya takalo masu masifa.
Kamar yana jira ya mike ya fara magana yana kuka.
“Babu inda zaku je, kamar yadda nayi alkawarin kawar dasu wallahi sai nayi koda zan rasa numfashi na, anan zaku cigaba da rayuwar ku har karshe nine ajalin yah Babbah tunda har suka kashe min mahaifina sai na ra…” bai ida karasawa ba Ammi ta mike ta wanke shi da lafiyayyun maruka haggu da dama, cikin bacin rai ta fara magana cikin kuka.
“Meyasa bazaka barmu da jimamin rashin da ka janyo mukayi ba? meyasa kai baka jin maganar mutane ne? Ta silar kafiyar ka muka rasa mutanen da basu ji ba basu gani ba, muddin kaje ka janyo mana wani tashin hankalin wallahi sai na nuna maka haifarka nayi bakai ka kawo kanka duniya ba”.
“Bake kaďai ba, koni sai na bata masa rai a wannan karon wallahi in har ya kuma zuwa janyo wata fitinar” Ummu ta faďa ita ma cikin bacin rai.
Basu gama maida numfashi ba Muhammad yace.
“Idan ma ya janyo insha Allah sai dai ya kare kanshi, tunda ba’a isa a faďa mashi yaji ba, ace mutum sai kafiyar masifa babu yadda za’a yi a tankwara shi sai dai in yaso. To wallahi wannan karon bazamu lamunta sai dai kayi kai ďaya, babu yadda khadijerh bayi dani ba akan na fahimce ta na kiya haka marigayi shima yaki sauraranta ashe ta silar haka ne kwanan shi zai kare”.
“Ai yanzu kawai Muhammad ka samu manyan gari kuyi magana a fara shirin tashi don wannan bala’in ba karewa zai ba indai muna nan, tunda bamu sani ba ko sun hakura suma”. Ummu ta fada cikin sanyin jiki.
“Anjima zan same su idan mun dawo da usman gida tunda jikin nashi d sauki sosai Alhamdulillah”.
“Yawwa haka yakamata don na tsorata sosai da wannan tashin hankalin wallahi gara mubar gurin ko mun huta”.
Mikewa Haidar yayi tare da cewa
“Kuyi hakuri ku yafe min insha Allah kamar yadda ta sila ta kukayi kuka haka kuma zakuyi dariya ta sila ta, ko ďauka cewa duk wanda ya mutu to kwanan shi ne ya kare”. Yana gama faďin haka nmya fita cikin sanyin jiki, har yakai kofar fita ya juyo ya kara kallon shi, haka suma gaba ďaya idon su nakan shi har ya juya ya ida fita daga gidan. Kamar haďin baki kowannen su yake jin tamkar kallon karshe yayi ma Haidar.
Nanah ce ta mike ta fita gidan tana kuka ji take kamar zata rasa wani abu me mahimmanci a rayuwar ta.
“Allah yasa iya kar abin kenan don wallahi lamarin nan ya tsorata ni ban taba tunanin zasuyi nasara akan mu ba”. Matar Usman ta faďa cikin wani yanayi
“To ku banda abinku taya zakuyi wannan butulcin sannan kuce zaku yi nasara akan su?”.
Kuraish ya faďa kansa a kasa yana wasa da wani icce.
Mahaifiyar shi ce tayi saurin yin magana,
“Kuraish kar na sake jin bakin ka a wajen nan muddin ba so kake ranka ya baci ba”.
Tana gama magana ya mike ya nufi hanyar fita daga gidan, can wajen wani dutse ya hango Nanah zaune ta kifa kanta da alama kuka take yi.a hankali ya taka zuwa inda take tana kukan da bata san ko na miye ba. Dafata yayi amma kukan da take yi batasan ya dafa ta ba har sai da ya ďan girgiza ta sannan ta ďago a hankali tana kallon shi, yana juyowa idanun shi ya faďa cikin nata, wani irin kallo suke ma junan su me wuyar fassarawa gaba ďaya sun manta duniyar da suke ciki, zuciya ta samu abinda take tsananin so da muradi, bat hawayen dake zuba idanun Nanah suka kafe, wani irin shauki da bege zuciyar su ta lula.
Sun ďauki lokaci sosai suna aikin aika sako ga zukatan su, soyayyar da aka kwantar tsawon shekaru ita ce yau ta dawo sabuwa dal a zukatan su. Zuwan Saraki da wani irin gudu shiya katse masu wannan kauna, kuraish na ganin yanayin shi yasan babu lafiya da gudu suka ruga bangaren su yah Babbah har da Nanah da zuciyar ta ke wani irin tsalle.
Suna isa ďakin yah Babbah suka nufa, sai dai abinda suka gani ya matukar razana su, wata irin kara Nanah ta kwalla ganin mahaifinta kwance babu numfashi ga yah Babbah shima kwance yana gargada kafin su kai mashi wani taimakon gaggawa ya ida mutuwa saboda ba k’aramar yanka Haidar yayi masa ba.
Abinda ya faru shine.
Bayan fitar Haidar daga gida nan bangaren yah Babbah ya nufa wuka kawai ya biya ya dauka tare da soke ta a wandon sa ya tafi. Yana zuwa ďakin yah Babbah ya nufa da isar kawai yaga yah Babbah na bacci kawai ya zaro wukar nan ya caccaka mashi ita a ciki. Yah Babbah a cikin baccin shi aka nuna mai zuwan Haidar da abinda zai aikata, sai dai kafin ya tashi yayi wani abu akai tuni Haidar ya iso gareshi har ya samu dama akansa.
Ganin ya samu nasara akansa shi kuma ya zabura ya cafki wuyan Haidar din bai sake shi ba sai da yaga ya daina numfashi. Saraki ne ya shigo yagansu a haka shine ya tafi kiran kuraish.
Da gudu Nanah ta ruga zuwa bangaren su ta sanar dasu abinda ke faruwa. Tuni mutane hankalin su ya kara tashi, faďin irin tashin hankalin da suka shiga abin ba dama, gaba ďaya mutane sun rikice. Kowa ya kasa zuwa domin dauko gawar Haidar sai Muhammad ne ya daure ya tafi.
yana zuwa ya iske kuraish da wata hula yah mama ta saka mashi ta kuma bashi wata sanda ya rike gaba ďaya namun dajin sun rusuna masa alamar girmamawa ga shugaban su.
Kuraish mutum ne ba Zaki ba dan haka suka zabe shi daya zama me mulkar su, saboda yana da duk wani abu da dabba ke dashi muddin wani mummuna abu zai faru to zai iya rikiďewa ya koma kowane kalan namun daji da yaga dama, hakan yasa yah mama matar yah Babbah ta hana Saraki mulkin taba Kuraish. Domin sun san zai iya kare su a wajen mutanen da suke son cutar dasu.
Kudin tarihin su ma an bashi ya kasan ce dai shine magajin yah Babbah. Gawar yah Babbah suka dauka suma aje ta inda suke ake gawa idan wani dabba ya mutu.
Ganin wannan abun yasa hankalin Muhammad kwantawa da taimakon kuraish suka kawo gawar Haidar aka yi mashi sallah aka kaishi gidan sa na gaskiya.
Bayan kwanaki da rasuwar Haidar komai ya lafa, hankalin kowa kuma ya kwanta domin kuwa kuraish na kula da dukkan su daga bangaren mutane har zuwa bangaren Namun daji. Zaman lafiya ya wanzu a tsakanin su, babu wani fargaba ko tsoro, duk sun maida komai ba komai ba, babu shamaki ga dukka bangarorin su ko ina suna shiga. Da taimakon Saraki kuraish ke gudanar da mulkin sa cikin kasaita da tausayi da kuma kyautawa.
Tun bayan da kuraish ya zama sarki babu wani sauran tashin hankali daya kara tasowa, tsaunikan su ya zama babban gari me dauke da ban al’ajabi. Domin kuwa mutane da dama sun dawo wajen da zama ya zama tamkar wata kasa ko ince babban gari wanda k’asa she ke burin zuwa. Komai na more rayuwa akwai babu abinda babu ga namun daji kala kala, sai dai basu cutar da kowa, hakan yasa wajen ya zama tamkar madubi ga duk wanda yaci ya koshi.kasar *YAH BABBAH* ta amsa ko ina a duniya.
Kuraish zama sarki biyu na mutane da na namun daji.
*Bayan wasu shekaru*
Abubuwa da dama sun faru ciki har da bikin kuraish da Nanah, soyayya suke ta bugawa a jarida. Sun Gina rayuwar cikin farin ciki da kwanciyar hankali har Allah ya azurta su da samun yan biyu mace da namiji. Namijin sunan yah Kathub ne aka saka masa macen kuma sunan ummu yasa mata. A haka rayuwa ta cigaba da tafiya, suna zaman lafiya da soyayya tare da girmama junan su, sannan suna kula da tarbiyar yaransu yadda yakamata…………..
ALHAMDULILLAH!ALHAMDULILLAH!
Anan na kawo karshen littafin *MUTUM KO ZAKI* inda nayi kuskure ubangiji ya yafe mana. Ubangiji ya bamu ikon amfana da abinda yake daidai.
Ina godiya ga masoyana masu bibiyar wannan littafin. Son so domin Allah ❤ ubangiji ya sada mu da Alkhairi. Sai mun haďe a sabon novel ďina bada jimawa ba insha Allah.
I love you all my fans.