Hausa NovelsSawun Kaddara Book 1

Sawun Kaddara Book 1

Sponsored Links

SAWUN ƘADDARA
Na
❤Husnah Muhammad❤

Bismillahirrah-manir-raheem.

Page 1&2

_________Wani irin gunjin kuka take Mai tattare da tsallar tsoro da tunanin Inda xata dosa,ga wata irin cida da garin ke haďawa alamar hadarine sosai agarin,cikin gajiya ta durƙushe agefen bishiyar data tsinci Kanta gabanta.
Wata irin iska tataso Mai haɗe da ruwa me ƙarfin gaske.
Sautin kukanta taƙara tana ƙara Jan hijabinta tana ƙudundunewa ciki ahaka ruwa me ƙarfin gaske yasauka shaaaaa!Banda ƙarar ruwan ba abinda ke sauka. Ta matse jikinta sosai cikin bishiyar nan Amma duk da hakan ruwan ba ƙaramin dukanta yakeba.
Tin tana saran tsagaitawar ruwannan har tadena tafawwalawa sarki me sama lamarinta,can kamar wajan tsakiyar dare ruwan yaɗan tsagaita,alokacin ba abinda ke cikinta illah tsallar tsoron a inda take,

Ba mutam gabas haka yamma, sai iska Dake kaɗawa Me sanyin gaske, dan har haƙoranta suna dukan juna,a hankali takai kanta kan gwuiwa ta matse acinyanta tana Karanto duk adduar da tazo bakinta.
Ahaka Wani wahallallen bacci Mai haɗe da zazzabi ya ɗauketa,
Gabb da asuba ta dinga Jin Nishi tamkar akunnuwanta,da farko ta ɗauka ko mafarki takeyi irin waɗanda tasaba. Amma data Buɗe idanta ahankali sai taji sautin na ƙaruwa, nan take zuciyarta ta buga da ƙarfi saboda tsoro, jikinta yadau kyarrma, ai batasan lokacin da tamike tsaye da ƙafafunta ba tanajin ƙarfin da batasan tana dashi ba. kamar daga sama taji tayi tuntuɓe Timm ta faɗa kan Abu,
Gabaɗaya zuciyarta takusa tsayawa saboda tsoro amma dayake tin asali me kula da addini ce da natsuwa sai taji bakinta ya ɗauki salati. Takai hannu talaluba taji kaman laima akan Wani ƙaƙƙarfa kuma faffaɗan Abu,cikin kuka tace “”dan allah ni mutum ce ba yar uwarku ba kuyi hakuri bada gangan nazo gareku ba natuba””.

Cikin nishin wahala da kokari irin na Wanda ke cikin Jin jiki yace “”ki…ki..kitaimak..”” ya kasa ƙarasawa saboda nishin daya ke, dasauri ta matsa baya tana cewa “wanene? meyasa Meka?””.Wani tari yayi na wahala sannan a hankali cikin fusgo numfashi yace “ki taimakeni kada sudawo su taraddani za..za..za””. kawai sai taji ɗiff,
Ƙirjinta taji yawani Yanke yafaɗi da sauri ta matsa gareshi tana ɗaga ganyayen da suka lullubeshi,alokacin hasken asuba yafara dasauri ta Isa gareshi tana kokarin dagashi Lema taji abayanshi duba hannunta da zatai taga jini sosai kafin tayi Wani motsi taji sawun tafiya daban daban ake wayen wajan,nan take ta ruɗe tarasa me zatayi kamar tatsallake shi Amma kawai taji kamar ana umartar ta data tsaya akwai Wani al’amari ahakan,dakyar tajashi xuwa cikin lungun bishiyar Wanda janshin datayi yajanyo ruwan saman da akayi ya diddigo daga ganyayyakin bishiyar.
Ruwan daya diddiga bisa fuskarshi yasa yasaki ajiyar zuciya ahankali,cikin Hali na tsananin wuya da zafin ciwon daya keji ajikinshi yaɗago hannunshi dakyar yakamo nata yabude Ido yazuba ma kyakkyawar fuskarta,yatsareta da wani irin kallo na ƙurillah,
Tafashe dakuka sosai tana cewa “ciwo kakeji ko? sannu raunine ajikinka sosai jini nata zuba” gabaɗaya ta ruɗe sbd ganin jinin Dake fita ajikinshi Tama manta danata ciwon,
Daidai nan taji an hankaɗo Wani dutse kusa dasu kiris yarage bai danne suba, da sauri ta toshe bakinta ta rungume mutumin tana adduo’i aranta.Da sauri-sauri suka Rika wucewa suna Wani irin yare da batajin mesuke cewa,Amma dai tagane neman shi wannan bawan Allah suke,bayan Wani dan lokaci ta rage jin tafiyar Amma daga nesa tanajin suna ƙara ƙaimin magan ganunsu da tafiyarsu.
Jin an riko mata hannu ya sata wai gowa ta fuskanceshi,farine tass mekyan gani a fuska, fuskarshi zagaye take da saje hannunshi daya riketa dashi taushi libis sedai alamun galabaita karara ta halin daya tsinci kanshi aciki,ahankali cikin murya me rauni,
Yace da ita “Baiwar Allah” bataji meyace ba dan haka ta matso da kunnenta kusa dashi sosai tana fuskantarshi tana kuka a hankali,
Ya cije lebe ya cigaba da fadi a hankali “Bansan meya fiddoki awannan lokaci ba Kuma bansan daga Ina kika fito ba Amma tabbas akwai manufar ubangiji akan cetona dakikai”.
Ya riƙo hannunta ta tsuramai Ido ƙurii yayi tari sannan ya cigaba da cewa,””komi yana da Sila tabbas ƙarshena yazo amma fa bashi ke nufin ƙarshen komi ba,yanzu ma aka fara,ZAKIMUN ALKAWARI INBAKI AMANAH TA””.
Shiru tayi tana kallanshi kawai domin Sam Bata fahinci inda ya dosa ba,Wani irin tari ya turniƙeshi,Wani irin guda gudan jini ya dinga fita Abakinshi da hanci,dasauri ta yunkura danufin ciccibarshi ko sunsamu taimakon Wani akaishi asibiti,
“kada kifiddani nan” ya dakatar da ita,
“nan shine ajalina kinji ƴata,kawai ki faɗa mani amsar tambayata”,kuka takara sawa tana fadin “bansan kaba Nima tawa kaddarar ta fiddoni kada kakara man Wani nauyin dabansan ina zan kai shiba,kabari munemi taimakon xaka tashi insha Allah””.
wani malolon tarin ya mulmulowa dakyar ya tofar,kawai yazaro Wani Abu dakyar daga Wandan kasanshi yakamo hannunta yadora yaci gaba dakyar”komai rintsi dawuya ki isar dashi gareshi kada kibari ya Isa ga azzaluman can,ba guminsu bane maha’intane,munafukai macuta,Kuma kisanardashi kada yakara yadda dakowa INA NUFIN KOWAYE,muddin bashi ya haifeshiba,
Kiroƙamin gafara gareshi nayi iya ƙoƙarina nakasa Amma yayafemin ba abinda yake tunani bane””.
kaf-kaf jikinshi yaɗau rawa Yana Wani kakkafewa yadan keta da ƙarfi kaman zai ɓalla hannunta,ganin yanda yake yasa takarɓa kawai tana fadin “shiwa zanba waye a Ina zan ganshi”. a hankali yace cikin sarkewar numfashi “BADAGI….s,”
Kawai diff diff taji taku ana nufo su da ƙarfi ana faɗin ” ku dakata yana wajen nan”.
Dasauri ya tunkuɗata gefe “kigudu! sun biyo sawu,ki riƙemin alƙawari kada kici amanata,wannan kaddarar kice ki bita duk inda ta kaiki zaki moreta ki tabbatar kin adanata,ki gudu nace bazasu barniba””.
Da sauri ta mike ta mantama dawasu kaya nata harta daga kafa kuma ta juyo tace wazance,”SHARIFF” yafaɗi daɗan ƙarfin daya ragemai Wanda shiyayi sanadin Janyo hankalinsu gareshi ita Kuma tasa kafa ta ruga tana cusa Dan abinda yabata agajeran Wandan jikinta,
Daidai nan suka iso gareshi daya yasa kafa ya hanɓareshi Yana Wani irin yare kaman bama guje alamar yabasu wahala, bahaushen cikinsu dattijone me matsakaicin shekaru yatsuguna gabanshi yasa hannu yasha ƙaremishi wuya Yana fadin “Ai saida nayi Maka warning ka ƙiji gayanan kana gani zaka mutu, bani taswirar kokuwa saina idasa da kaina,Kun hanamin sakat kuda ubanku komi kune agaba wallahi saina ƙarar daku na handame komi naku””.
waɗannan samudawan mutanen basu jin Hausa,ɗaya daga cikin sune ya fisgoshi da ƙarfi yaɓarkemai suturar dasuka gama yageta dama suka,dagashi sai ɗan short nicker suka barshi duk da Shima ba daga baya ba afagen girman…

Komi najikinshi seda suka duba suka tabbatar babu komai sai Tarun raunikan Dake jikinshi……

Comments
Share.
SAWUN ƘADDARA
Na
❤Husnah Muhammad❤

Page 3&4

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Nuni sukayi da cewar bafa komai a jikinshi, da ƙarfi ya daka Mai wata irin tsawa Yana faɗin “Ina ka kai shi ka faɗamin waka ba shi?” sai a lokacin ya tuna yaji Yana faɗin SHARIFF kenan hakan na nufin Wani ya taimakeshi,
Da sauri yace “ku bincika min ko ina akwai Wani a tare dashi Wanda Yaba abun nan” .Da sauri ɗaya ya takeshi sauran ukun suka nautsa dawo alokacin asuba tayi duk iyakar dubansu basu ga komai ba sai kullin ‘yar Jakarta da suka dawomai da ita domin anan kusa kaɗan suka ganta.
Cikin fusata yace “ku idasa minshi kujefar dashi inda ba za’a ƙara Jin koda warin gawar shiba” . kana ya duƙa yace mai, “Nasan ƙila kana jina kaga yanda ka ƙare ko to haka zanbi uban naka da sauranku duk in ƙarar daku! shashasha mara tunani,” cikin fidda Rai da galabaita yace dakyar “Har abadah bazaka ci nasarah ba,ahaka zaka taɓe Kuma Kai zaka wulakanta”.
cikin zafin zuciya da rashin Imani ya murɗe Mai wuya,Yana kakari Yana komai ya ƙarasa da Kalmar shahada Abakinshi,
Allahu akbar-yasaudar da rayuwarshi saboda saving ta wasu Allah kabamu kyakkyawar Zuciya irintashi,
Jakarta suka zazzage Babu wata tsiya aciki sai ‘yan kayanta daba Wani yawane dasu ba sai Wani dankulli acikin wata Leda,yaɓarkeshi cikin kunan Rai,Wani Dan Abu irin nada da akafi Saka awarwaro na gold ko axurfa yagani,yabudeshi dakyar Wani Abu yadallemai Ido,
Wani irin faɗuwar gaba yaji ta sakkomai yaƙure abin da Ido Yana tuna Ina yasan abin amma yakasa saboda ɓacin ran da yake ciki da takaici na mutuwar wannan banzan bai sami abinda yake so ba,Amma bakomai kozai mutu bazai saduda da neman wannan abuba,Kuma koba komai haryanzu asirinshi arufe yake tinda Wanda yaganoshin ya mutu.

Anan yabasu umarnin sud’akko gawar su biyoshi Dan samun inda zasu jefar daita,tayanda Babu yanda za’ai ta Isa yankinsu bare Wani yanuna yasanta har akarrama shi mamacin ai mashi jana’iza.

Wannan shine mafarin duk Wani hargitsi daya Kara kunno Kai arayuwarta.

**** **
Asalin yar garin katsina ce,babanta malam samaila tukur Dan asalin jihar Yola ne bafulatanin usuli,Tako Ina daka ganshi kaga jinin fulani, yanayin rayuwa ne yakawo shi katsina zama,matanshi biyu,Allah yaima daya rasuwa gurin haihuwa,matukin motar kamfanine yakan kaimusu kaya duk inda suke cinikayya, yanada rufin asiri balaifi tinda ba abinda yagagari gidanshi,mama hansai itace matarshi tafarko,yaranta 2 duka maza,Yaya sagir shine babba se Yaya Usman mai bi mashi,daganan haihuwar tadan ɗaga mata ƙafa,
Sai bayan ya auri umma maryama matarshi ta biyu ta dan Daɗe Bata samu haihuwa ba dan sai da ta cika shekara 5 da aure ta haifi ƴarta mace,me tsananin kyau da haiba,Dan duk Wanda yaxo barka sai ya tofa albarkacin bakinsa akan jinjiran,
Ranar suna yarinya taci sunanta (Asma’ul-husna)wato sunan kakarta suna kiranta husna,tinda aka haifi husna malam samaila ya ɗauki Son duniya ya ɗora mata, kodan an rabu da samun karamin yaro ne a gidan,komi yasamo mamarshi,autarshi,hakama yayyenta maza komi suka wawuro ita musamman Yaya sagir ɗinta,
Mama hansai wato mama,wata irin murdaddiyar macece baka Gane gabanta,Dan ta iya makirci,ko kaɗan aranta bata kaunar maryama,saboda ganin Baiwar kyau da allah yaimata,domin batada maraba da larabawa,doguwar macece me matsakaicin Jiki,idanuwanta Dara Dara ga dogon hanci da gira da yalwataccen gashin gira,komi nata masha allah,gatada kyan Jiki Wanda shike Nuna Maka daga gidan Hutu tafito,bugu dakari sai dai kawai ta wayi gari malam yadawo mata da ita wai amatsayin matarshi injita,Aiko ta tada bori sosai tace Bata yadda ba Sam ina shi Ina samun auren balarabiya,sai dai in karuwarshi ce,rigima sosai ta tada,wadda dakyar yakasheta da iyaye da malaman unguwar,daga baya ta dawo takafa hujja dacewa wane aure ne amarya ke kawo kanta inda ta mutunci ce ai iyayenta zasu kawota.
Kullum cikin goranta mata take itadai sai dai ta shige ɗaka tai kuka,tana tuna irin gatan data baro saboda soyayyah. Da taga Bata kulata sai ta koma ta ƙasa,itace wancan bokan,wancan malamin harta samu nasarar Hana mata haihuwa,a cewarta ai itama tata tatsaya dan haka ba me cigaba da ita agidan.
Ahaka har suka shekara ukku a tare,watarana malam bainan yanacan Neman na abinci domin tuni ya ajiye tukin motar kamfanin dayake saboda Wani dalili Wani dalili,yasamu direban wata motar anan katsina,
kamar kullum a takure ta fito tana sanɗa zata shiga bayi ta samu tai wanka da alwala takoma ɗaki saboda ko ran aikinta data gama take komawa ɗaki saboda jarabar hansai.
Harta kusa kaiwa bayi taji kamar ana binta juyawor da zatai kawai taga hansai ce take Shirin watsomata ruwan zafi daga tukunya,da sauri cikin tsoro tadaka tsalle tana kurma ihun ataimaketa,ita kuwa hansai “Fadi take gara inkone Miki shegiyar fuskar dakike takama daita,se inga ƙarshen haƙuri” dasauri tayi tsalle gefe ruwan yayi Wani waje sedan kadan daya fallatsan mata tarike kafar tana kuka sosai tana Bata haƙuri.
Daidai nan malam sama’ila yashigo Dan tin daga waje yake Jiyo hayaniyarta sama sama,dasauri yadaka mata tsawa “ke hansa’u ke!”
cakk tatsaya jikinta nabari dan duk abinta da asirinta tana shakkar malam,yakaraso a fusace Yana fadin “wlh duk abinda yasa meta bazan barkiba,” yamatso da suri ya riƙe ƙafar,kuka take sosai tana yarfewa,kawai kamata yayi suka fita daga gidan yasata adaidaita suka wuce chemist,Akai mata treatment akabata magunguna suka dawo gida.
Tinda suka dawo yakaita ɗaki yanata lallashinta yasamu taci abinci Tasha magani bacci yakwasheta,sai alokacin yafito yanufi ɗakin hansai yatarar batanan har yanzu domin Basu dawo sun tarar da ita ba agidan.
Yazo fitowa kenan sukai kacibus taja baya cikin zare Ido na rashin gaskiya,idanuwanshi suka sauka akan Jakarta data Fadi ya duƙa ya ɗauka Yana zazzageta,tarkacen magunguna ne da layoyi,nantake ranshi yakara Baci,budar bakinshi se cewa yayi.
” iyakar tsubbunki da munafurcinki bazaki iya rabani da maryama ba domin bakisan mafarin haɗuwata da itaba allah kaɗaine masanin gaibu,Dan haka ki wuce na sakeki saki ɗaya idan kinyi hankali da yiwuwar in duba lamarinki shasha kawai,” yadoka tsaki yai gaba,aikuwa ta kurma uban kuka tana tashiga ukku ta lalace ina zatasa kanta malam yasaketa,”yau Nika Saka akan wata banza wadda ko kai bakasan asalinta ba, ila wallahi baka isaba,”
tsiyadai har makwabta suka shigo tana kuka tana faɗa musu ƙarya da ƙaray rayi,kowada abinda yake cewa akan lamarin,hakanan tatai gidansu domin babansu tuni yarasu mamansu Kuma taɗan tsufa sana’ar kulle-kulle takeyi agida,Amma da tayi abincin saidawa to yanzu tsufa yazo.
Tunda ta leka taga bakar wahalar gidan tafara tunanin Taya zata koma gidan mijinta,tabi wancan abokin da kannen mahaifinta,tana rokansu su bashi hakuri,
bazata ƙaraba da hakan aka samu ya maidota da sharuɗɗan daya gindaya mata tace ta dauka

Tofah! ita kuma maryama Jin zata dawo tace wlh tagama zaman duk da bata da kowa a garin,iya lallashi yamata fir taki yadda Dan dole yakama mata haya takoma ita kuma ta dawo gidanta tinda tanada Yara.
Mafarin Kara tsanar maryama kenan da hansa’u tayi,har gobe ta kanyi kuka idan ta tuna igiyar Aurenta daya ta mutu saboda waccan aljanar injita.
To daganan ne abubuwa suka dan ma maryama sauƙi,gidanta ita kadai sai dai kawai tasamu diyar makwafta randa ba girkintaba take tayata kwana,musamman data kasance mace Mai jama’a da iya Hulda da mutane,ita kowa natane kuma Sam batada rowa,dan danan Ta tara jama’a nata nakanta,sai lokacin tasan cewa Ashe da zaman kunci take da takura shiyasa bata san kowa ba a tsawan wannan lokacin.

Comments
Share Fisabilillah ✍️

SAWUN ƘADDARA
Na
❤Husnah Muhammad❤

Page 5&6

Da sunan Allah Mai rahma mai jinkai!!

Sadaukarwa: Na saudakar da wannan littafi zuwa ga Aminiyar Arziki’i Kuma abin kwaikwayona, Oum Neehal ❤️❤️ Ina yinki sosai tawajena,Allah yabar tare..

_______Kwanci tashi maryama takusa shekara biyar da aure,zamanta lafiya sai ďan yau da kullum da ba za’a rasa ba,domin dai hansai tayi iyayinta Amma tagagara takauda iKon Allah,sedai takasa yau inta Sami nasara gobe tafadi,maryama Kam dama macece me riko da addini kowanne dan canji tagani daga gurin mijinta to zata mike tsaye da addua ne da tashin dare har allah yaimata mgnin abun daman itadai batasan boka ba,to inama tasani itadaba yar gariba Kuma bame kwatsaniyaba.
Zuwa wannan lokacin ko bari Bata tabayiba tin tana damuwa malam Yana lallashinta tareda Nuna mata komai lokacine,to yanxuma tafawwala ma Allah lamarinta,duk da kaguwarta dasamun haihuwar domin Wani babban kuduri Dake ranta dakuma nauyin da dole seda haihuwar zata saukeshi.
Kwatsam ranar wata laraba ta tashi dawani irin ciwan kai da zazzabi har Bata iya mikewa,domin seda lantana metayata kwana taje takira mata innarta kana taxo takamata,ta taimaka mata tai tsarki da alwala tasamu tai sallah azaune,takoma ta nannade kan gado,ana haka malam yashigo gidan domin yaga lfyrta daganan yawuce wajan nemanshi,kwatsam yatadda wannan Abu,nandanan yarude yace asibi makwafciyatta tashiryata suwuce asibiti,bari yasamo adaidaita,
Suna Isa ya amshi kati sukabi layin Jira har akazo kansu,likita yaimata ‘yan tambayoyi tarika bashi amsa,daga karshe ya turasu awonjini,bayan results din yafito malam yakamota suka dawo gurin likita, likita yai Yan dube-dubenshi yadago yakalli malam yace”congrt,madam tana dauke dajuna biyu natsawan sati shidda 6″.
Fadin murna da dokin da malam yayi Basu faďowa,likita yasanya ‘yan dokokin daya kamata subi ya sallamesu,suka fito Yana rike daita suka samu adaidaita suka wuce gida bayan yasaimata kayan makulashe namasu ciki,
Tindaga ranan suka cigaba da rainon cikinsu,komi takeso Yana mata tamkar ba’a taba yimai haihuwa ba haka yakeji da cikin,harta Dan samu saukin laulayin cikin yafara girma,danma Allah ya hadata da makwafta nagari suke taimakonta dawani abin inbata iyawa,cikin haryakai wata bakwai hansai batasan dashiba domin dai ba haduwa sukeba kowacce tana gidanta malam Kuma koda wasa be taba furta matashi ba,se watarana da suka hadu da makwaftan maryama awani suna suke gaisawa hansai take musu irin abinnan ya wajan Mero tana lfy ko,asibi da batasan komai ba Dan maryama bamasu irin surutun nan bane dakomi akaimusu sesun fada,A’a kawai sirrinta daga ita se mijinta,
Asibi tabude Baki tace,”bari hansai dama inaso namiki fada yanzu abokiyar zamanki duk irin jikin da tasha tin daga laulayi har ila yau ciki yakusa fitowa ace kosau daya Baki Tako Kin gaishe taba,haba hansai komune aikyazo ko akafane bare duka nawa zaki biya,iyee fisabilillah”,hansai tazaro Ido waje tace “kina nufin maryama ciki gareta,”asibi ta tabe Baki tace “kina nufin bakisan da cikin ba kome”,wata dariyar yake hansai tayi tace “wlh Sam bansani ba malam dai yacemin Bata lfy kashegari nace zan dubota yacemin aitaji sauki Tama fita suna,daganan be kara cemin komaiba nikuma nadauka Dan zazzabi ne kawai,insha allah zanzo nai mata sannu Allah ya raba lfy,”
Uhmm!inji asibi tace”to allah yakyauta ki gaida yaran mu munwuce magariba ta taho”,”to kugaida gida”anan suka rabu,
Ai kafin kace me hansai ta Isa gida ta hada kan yaranta dasuka Dan fara tasawa tasa musu kuka,tana fadin karya da gsky yanzu abinda mahaifinku keyi ya kyauta ace banda arzikin a fadamin waccan Munafukar tanada ciki Amma bandashi,bakomai duk abnd yayi dan kanshi.
(kuskuren wasu iyayen daga miji yabata Miki Rai sai ki zauna kita batashi gaban yaranshi,kinmanta cewa seda taimakonki zasu ganshi da daraja,har su girmamashi kome yai miki wannan tsakaninkune,Amma ‘yar uwa karki sake kome yaimiki ki batashi gaban yaranshi,dominsu Dake duka aljannarku tana karkashinshi,musammanke,sukuma ai se sun bishi zasu ga daidai har rywrsu tai albarka,Kuma kome zai musu kinuna Dan ya isane kada kisake baraka tashiga har yaranku surainaku,plss ‘yan uwa akiyaye).
Sagir na dagowa “yace lahh kenan zanyi kanwa ko Kani inna,Kai Amma naji dadi Allah yasa inna maryamu(haka suke kiranta lokacin tana gidan)tahaifi mekyau irinta,danaji Dadi yeee,”
wata irin mazgah takaimishi tana zaginshi tana banbami,har seda yafara karewa,tana fadin”shikenan Kuma anlasheku wlh Bata isaba Kuma tarabani daku shegiyar,”
banga ta zama ba,tafigi hijabi tayi gaba,
Bata Dira ko ina ba sai zauren malaminta,taimai bayani tana kuka,yatambayeta yanzu me takeso tace akadar dashi,malam Sam begaya mata gaskiya ba yayi ‘yan surkullenshi yabata magani yace tabata taci,tai gdy tayi gaba,koda tadawo gida ranta fess malam yashigo ta tarbeshi da fara’arta,bayan yaci abinci yanatsu take cemai,”wato malam shi sharri bibiya yake ga duk Wanda yataba yinshi koda akuskure ne,”malam yace meyasa kikace haka,”
Kawai sai ta Saka kuka “yanzu malam sbd kuskuren daya wuce Wanda nayi nadama ba adadi Amma ace kanwata maryama tasamu juna biyu har ya girma Amman baka iya fadamin,hartaci ciwo sosai haba malam,wlh nadauka tuntuni kawatsar dakomai nida ita duk mun zama Daya atunanina”,malam yanisa kana yace”to kiyi hkr anyi kuskure Amma baxaa sakeba Kuma kema kinsan Hakan yanada nasaba da abubuwan dasuka faru,to Amma tinda kin natsu shikenan Allah yakara daidai taku,maryama Kam dama Kinsanta batada matsala Sam,” tadago takalleshi Jin furucinshi,yamike Yana fadin “bari infita sallah lkc na karatowa ai saiki shirya ki ganotan tinda haryanzu tana fama kinsan dai yanayin ai sai hakuri kawai”,
“Adawo lfy malam goben se inje in gano ta” da haka yafice yanufi masallaci.

Washe gari ta shirya abinci mai rai da lafiya ta nufi gidan maryama,koda ta ganta Bata Nuna komai ba ta amsheta hannu biyu suka gaisa takawo mata ruwa da abinci tana tambayarta inasu Usman,itama ta amsa cikin fara’arta, kular abincin ta turo gabanta tana cewa” ga alale nayo maki bansani ba ko zaki iyaci nasan meciki da kwadayin kayan yaji”.
Da fara’arta ta Janyo tana godiya tana fadin “Aiko kaman kinsan Ina marmarinta to surfen waken wahala yake man yanzu shiyasa Nake hakura idan makota sunyi sukan kawoman in ďanci”.
Tai yake tana bari amiko Miki kwano to kizuba tunda kin zauna,dasaurinta tace “Kai Yaya bari intashi Amma dakanki”, “bakomi kinjiki menene”
tawuce kicin ta dauko mata plet da spoon ta zuba mata ta mika mata,itama ta jawo Wanda takawo mata Dan sosai tai missing abincinta Dan maryama ba dai iya girkiba ga tsafta komi nata anatse,Danko gidanta Baki cewa name cikine wata bakwai komi agyare,sabanin wasu matan da ansamu ciki sekiga mace komi tasaki koda tanajin zata iya sai ta langwabe gida duk ya lalace sbd ciki.
(to idan baki kulaba anan sai kisa mijinki ya fara kyamarki saboda San Jiki da lalaci, Eh akwai ciki me laulayi sosai Wanda komi sai an miki shi to irin hk kinga dole in kina da kanwa tarika taimaka miki ko kanwarshi kafin kisamu dan karfi ajikinki,plss akula,ita tsafta cikon addinice Kuma ke kanki sai kinfi Jin dadin komi naki kinganshi dakyau).

Kowanne yaci abincin sosai sannan maryama ta kauda komi ta gyara suka Dan taba fira kana tace zata tafi,Maryama tashiga ciki tahado mata ‘yan turarukan wuta Dana Jiki tabata,sukai sallama ta tafi tana jin Dadi domin ita gani take komi yawuce.

Allah kabamu iKon rubuta Abu me amfani Wanda zai datar da duk Wani musulmin kwarai ya Allah🤲

❤Husnah Muhammad❤

Allah ya gafarta ma iyayen mu.

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
SAWUN K’ADDARA.
💕💕💕💕💕💕💕

Na Husnah Muhammad.

Fage 7&8.

Dasunan Allah Mai rahama mejink’ai.

Sadaukarwa:nasadaukar dawannan littafi gareki aminiyar arziki,oum neehal,ked’in Abar kwatancece,inayinki irin sosai d’innan❤️❤️❤️👏👏👏,Allah yabar tare..

____________Murna fall hansai takoma gida tana jiran taji kazamin labari,Amma har aka kwana 2shiru takeji,towa yaisa yaja da allah duk K’wan da allah yanufa seya shaki iskar duniya Aiko ana ruwan maye seya shak’a,

Hardai takasa hkr tacema malam randa yadawo dakinta,”wai malam maryama kalau take”yadubeta yace “eh kokinji Wani abune”tai sauri takare kanta tahanyar cewa “A’a randa najene naga har kuburi tayi har natambayeta Kuma batajin ciwom komi tacemin a’a sedai nauyi dacikin yakemata har kamar baxata iya tafiyaba”,malam yace “uhm lfy Lau nimadai kwana 2 nan tana yawan min wasu maganganu marasa Kai wanda bana sansu Dan jinike tana karyan gwuiwa,ammadai daxaki amince Dana Bata Usman yadinga tayata kwana sbd yanayin haihuwa ko zataxo cikin dare idan yadawo mkrnta seya Rika tafiya can har allah yaraba lfy,aikinga antaimaketa randa nikecan seya kwana gida ko.

Kamar antsikareta tace “usman Kuma,yace”eh mana ba akwai dakiba agefenta seya dinga kwana ciki”, kome tatuna oho,takada Baki tace”gsky sedai sagir Amma Usman yayi kankanta idan yafice wasanshi Ina zata ganshi,” dasuri malam yace “hakanma yayi”dandama sanin Hali yasa yace Usman,tamike tana shigewa daki ranta besoba tna danasanin fara Janyo mgnr.

To daga ranan sagir yake wucewa gidanta tayta kwana,maryama Kam bakaramin Dadi tajiba dahakan tadauki sagir tamkar danta data haifa komi tasmo madadin tace abnd xata haifa setace sagir har malam namata tsiya setace “eh bakomi wata fara gani inba Shiba ai ita duk Wani d’a bayan sagir dinta yake”
Wannan yasa sukai Wani irin sabo harta kaiga yakwaso duka kayanshi yadawo nan yawo kawai kemaidashi gida,hansai taxaga tatsina Amma bedamuba domin dai yasn agaban babansu Bata iyawa Dan tin abinda yafaru farko take shakkar mgn akn maryama,Dan kota kasan datake bin haka taima malam bayanin yanda sukai,Abu beyiba se cemata yai ai cikin yariga yayi k’warine dayawa tayi hkr idan tahaihu se asan yanda za’ai da jinjirin,dahaka tad’an kwantar da hankalinta.

Kwanci tashi bawuya gurin allah har cikinta yashiga wata natara,duk wasu kaya daxa’a bukata malam yatanadesu,duk ranar awo Kuma dakanshi yake kaita yadakkota,duk abinda Bata iyawa sagir dinta kemata,sunyi wata irin shakuwa taban mamaki tamkar tincan tare suka taso aguri Daya,Wani lokaci takan xauna taita bashi labarai na rayuwa tareda yimai Nasiha da dorashi atafarki nakwarai tare da gargadinshi akan sabama allah da manxo da iyayenshi,takan cemai komin lalacewar mahaifi mahaifine musamman idan yakawo mata karar innarshi takan kwatseshi tamai fada sannan tabi da nasiha,
Awata ranar lahadine tayi Wani mafarki gata ga ‘yan uwanta suna mata mgn suna kukan rashinta tana kallansu tanaso taimusu mgn Amma tsananin Nisan dake tsakaninsu yahana sujita tayi iya yinta Amma sungagara koda ganinta sedai tana iya hango alhinin rashinta a idanuwansu,
Firgigit tatashi tana me salati,zuwacan tafashe dawani irin kuka dayasa malam yafarka firgigit yana tambayarta lafy,ko haihuwarce gaba daya yarude,Bata kulashiba seda tayi kukanta me isarta kana takallai tace “malam inaso nakoma gida natabbatar haryanxu hankalinsu atashe yake arashina Dan allah kakaini gida naroki gafararsu kada inrasa Raina awajen haihuwar nan domin tabbas inajin akwai abinda xefaru”.

Wani irin faduwa gabanshi yayi domin tinda sukai aure Bata taba yimai mgnr gidaba tinda suka Aje magana akancewa sesun haihu sesu koma da d’ansu saboda haihuwar tamkar itace masalaha agaresu,rungumota yayi Yana D’an bubbuga bayanta kafin cikin muryar lallashi da matsananciyar soyayyarta yace”haba merona wace irin magana kike haka kinmanta alkawuranmu dakuma abnd zamuje mu fuskanta,kik’ara hkr komai yakusa zuwa karshe dakin haihu kinayin arba’in zamuje tare ba abinda zefaru insha Allahu lafiya Lau zaki haihu,kidena irin wad’annan maganganun, Ina kikeso insaka kaina idan narasaki,kisani cewa soyayyarki Wani bangare na rayuwatane rashinki agareni tamkar rashin ruhine agareni kinga kuwa idan baruhi aiba gangar Jiki,Ina tsananin kaunarki,kidena raxanani da irin wadannan kalaman.

Dubanta takai gareshi tana mejin tsananin sanshi azuciyrta,tana maicewa”kayi hkr inajin tsananin fad’uwar gabane gawani mafarki Daya tasoni gaba duk akan ‘yangida shiyasa hankalina yakoma gida akwanakinnan,malam kad’aukarmin alk’awari ko banrayuba zaka kula da abinda nahaifa Kuma zaka danganashi da dangina sannan karokaminsu yafiya kace suyafemin, K’ADDARAce tasani aikata Hakan garesu.

Dasauri yatoshe mata bakinta yaname rungumeta Yana fadin”kidena karyamin zcy ba abnd zesameki lafiya Lau xaki sauka Kuma inmaidake ga ‘yan uwanki lfy,kada kik’ara fad’in wannan kalaman banaso”,
Ajiyar zcy tasauke tana rungume jikinshi,dahaka ya lallab’ata suka kwanta kowa zcyrshi badad’i,

Sagir Dake tsugune kofar daki yafito fitsari yaji alaman kukan inna meronshi yalab’e Yana saurarensu yagama jinkomai,ahankali ya lallaba yakoma daki da tunani fall aranshi,duk da Yana k’arami sosai bekai yafahimci komaiba Amma abin yazauna aranshi sosai har Yana tambayar to Ina innarshi zata hartake Bada amanar abinda zata haifa,shifa koma mene sedai tatai dashi duk inda zata Dan ba inda zata barshi.

Tindaga ranan maryama takoma wata irin sakwaf da ita,rashin maganarta seya k’aru,ko sagir yatambayeta seta cemai bakomi,batada aiki se zama kan darduma da tasbihi da nafilfili,idankuma malam gidanta yake sukanyi tare domin Shima kwana 2 nan hankalinshi atashe yake,kullum cikin addua yake allah yasaukar da maryama shi lfy

Dayammacin wani lokaci sagir yadawo islamiyya yataradda ita zaune kan sallaya kamar kullum tana addua da hawayennan dai afuskarta,cikin sanyin Jiki ya ajiye jakarshi yajuyo yadafata ahankali,Bata juyoba domin tagane shine danshikadai ze dafata a irin wannan yanayin,seda takammala adduarta kana tajuyo gareshi tana dubanshi cikin karyewar zcy da k’auna wadda ubangiji kad’ai ke had”ata domin dai k’aunarta da sagir daga Allah ce, kana cikin sanyinta tace “sagiru Dan Mero ko?”yad’anyi murmushi kad’an kana yad’aga Kai Dan wani lkc takan kirashi hk,”inaso kafad’amin wacece ni agareka?”.

yad’ago ya kalleta sbd tambayar tabashi mamaki yace”uwata mana,Abar alfaharina wadda komi nazama to sanadinta ne dakuma tarbiyarta agareni,kisani cewa inna Mero ke tarihice dabaze tab’a goguwa arayuwa taba,inasanki tamkar Soyayya irin ta d’a uwa har abadah ke mamatace”, tin kafin yak’arasa maganar hawayen farinciki suka wanke mata fuska,tasaki murmushi tadubeshi da yak’ini axuciyrta tace”tabbas Kai d’a nagarine Kuma ni uwace dazanso ace Nina tsuguna na haifeka,koyanxu Ina alfahari da kasancewarka Yaya ga abinda zan haifa”,

Tarik’o hannunshi ta umarceshi Daya Saka idanshi anata domin tabbatar Mai da muhimmancin abinda zatayi,”sagir Ina Mai damk’a amanar abinda nahaifa ahannunka,Ina Mai fata Kazama uwa Uba,Yaya Kuma K’ani agareshi ko gareta,sagir aurena da mahaifinka tamkar wata k’addarace Dake tafe da abubuwa dadama masu rikita lissafi,tabbas akwai hikimar ubangiji ahakan,sagir kayimun alk’awari komai rintsi zaka kulaman da tarbiyyarshi,bance Ina nufin ko k’warzane kada yatab’ashiba A’a aiduniya bagurin jindadi bane kadai, kowa yazota seya Sha wahala Kuma inda rabo yaji dad’inta,kawai kakaremin mutuncinta ko shi,kada suyi kukan maraici kuma komai rintsi abashi ilimi ko abata,sannan daga k’arshe”,

Tazaro d’an wani Abu awani kwarkwaro kaman nazobe tamik’amai tace”idan sunkai minzalin hankali kasadasu dawannan domin shid’in Wani manuniyace Dake Nuna dukkan Wanda ya mallakeshi to jinine daga maryama wadda tafito cikin Ahalinmu kenan duk inda tashiga indai Yana hannunta to bazata b’uya adangiba domin manuniyace Dake Nuna jinina ne wannan halittar,
“Kazama Mai tausar mahaifinka sannan katunamai idan abnd nahaifa yayi k’wari yasadashi da dangina,Kuma wannan maganar sirrice Kuma ajiyata amanace harse Wanda zaka Bawa yagirma sannan,Kuma Kazama merik’o da addini da rik’on amana da yima iyaye biyayyah,kajiko”,

Yad’aga matakai Yana me saurin cewa,”to inna ke inane garinku Kuma inazaki kibarni”,tayi maiyak’e tana cewa “asalina ni yar camaroo ce,Amma iyayena duka Yan Nigeria ne,kasuwanci yakai babanmu har aka haifemu acan daga baya Kuma muka tattaro duka muka komo gida cikin Yan uwa da komai namu kaga kenan tamkardai ni ‘yarnance ABUJAH”,
K’arancin shekaru yasa beyi wayan tambayarta komaiba gameda suna ko Yan uwanta ko unguwanni,kawai shi tinda tafadamai gari gani yake kotatai ze nemeta dakanshi,tinda basanin girman Abuja yaiba.

Muje zuwa
Yanxu akafara
Taku akodayaushe
Husnah Muhammad.

Plsss.
Share & comments..

SAWUN ƘADDARA
Na
❤Husnah Muhammad ❤

Sadaukarwa ga : OUM NIHAL❤🌹

Page 9&10

Da sunan Allah Mai Rahma Mai jinƙai.

______Kiran sallahr magriba ya tadasu daga nasihohin da takemai,sukai sallah tare hakanan sukaci abinci,suka cigaba da fira kaman wadanda suka Dade Basu haduba,bayan ishai malam yashigo gidan tareda ‘yar tsarabarshi,tayi mai sannu da zuwa ya amsa,ta mike dakyar zuwa kicin Dan haďomai abinci har Yana fadan meyasa ta tashi da ta bari ya ďakko kawai,har yaxauna cin abinci sai ya tuna sakon hansai ga sagir ya kwalla masa kira Yana cewa”Dan gidan baba kana Ina fito da shirinka mamarka tace kaje tanasan ganinka gobe zakai sakko gidan gwaggwonka karbo mata Sako injita”,daga ciki sagir ya xumbura Baki danshi Sam bayason yabar innarshi musamman yau dasuke Shan fira,yafito yaima baban sannu da zuwa Yana cewa”baba to goben naje tinda safen mana nidai in kwana nan mana”,
“A’a kazo kajedai ya zata baka umarni ka coge maza ka fito kawuce mahaifiyarka na jiranka,”Yana zumbura Baki ya shiga ya shirya ita dai maryama uffan ba tace ba domin tinda tayi sallah takejin mararta na kartawa Hakan yasa tayi lamo tana tasbihi,harya shirya yafito kana yakalli innarshi yace “innata nizan tafi kimin addua goben Dana dawo zantaho gida kinji”,tayi murmushi kadan tace”tace Allahu ya tsaremin kai yaran kirki ya baka sa’a aduk inda kashiga ka zama Daya tamkar da dubu kaji yayan Asmaul-husna,” da murnarshi yace “lahhh inna dama sunan abinda ke cikin kenan”tayi murmushi tace”idan macece ba zataci sunan kakarta idan namiji ne Kuma duk Wanda kuka zaba kai da xaujii”.
“A’a inna insha Allahu macece ma husna kawai”,”to allah yabada me albarka kada dai kamanta duk magangaunmu,”
“Tofah wane sirrin Ake boye mana ne”inji malam,
Tacije Baki Jin ya mutsawar da cikinta yayi kana ahankali tace “tsakanin ďa uwa ne ba’aji”,ai lallai kam”,yabata amsa.
Sagir ya juya yawuce Yana waigenta,ta daga Mai hannu shima Yana dagomata,har yafita yakara lekowa yadade Yana kallanta kana yawuce jikinshi na daukar Wani irin sanyi,malam yabmike Yana fadin “bari in zaga inzo mukwanta danji Nike jikina badadi kamar xanyi masassara”.
Haka suka Dade ba suyi bacci ba sunata nanatawa juna irin yanda suke san juna da alkawri ma juna irin masu tsayawa arai,wajan sha biyu nadare suka kwanta bayan malam yayi musu adduo’in bacci.

Wajan biyu nadare tafarka dawani azababben ciwo mara misali,tuntana iya daurewa tana addu’a harta gaza jurewa tafara mutsike-mutsike Wanda yatada malam sama’ila daga barci,firgigit yatashi zaune Yana tambayarta lfy,dasuri yakunna fitila Yana haskata yaga tahada gumi sosai tanata yada Kai,dasuri yadira yanemi jallabiya yasa Yana fadin “haihuwace subhanallah,bari intado asibi ta taimakeni mukaiki asibiti sannu maryama sannu,sannu kinji”,
Ya rungumota yasamu yajinginata da bango yafita,cikin daren nan ya bugama makwafta da yake Allah ya hadasu da nagari haka suka Bude suna mai tayashi jimami,nan makocin nashi yace ko ayimata addu’a agani ko za’adace kafin asuba tinda yanzu kafin asamu abin Hawa taji Jiki,haka akaimata addu’a suka dawo tareda asibi,abinda suka gani shiya daga musu hankali Dan isketa sukai cikin jini male-male,gashi ko motsin kirki Bata iyayi Dan haihuwa jini yayo gaba matsalace babba,to ananfa sukaga rudin malam,dan sosai ya tada hankalinshi ya sabeta da uban cikin nan bai ji nauyinta ba sukai Wani karamin asibiti Mafi kusa dasu,suna xuwa aka Bata taimakon gaggawa akace suwuce babban asibiti domin yaran cikinta akife yake dole sedai manyan likitoci,
General hospital suka wuce kai tsaye baba Kuma yakoma gida duk Wani Dan tattali dayayi yakwasoshi xuwa asibiti,suka samata ruwan nakuda likitoci suka Taru kanta suna kokarin tsaida jinin,har Tara nasafe Abu yafaskara sedai sunyi nasarar tsaida jinin ammafa haihuwa shiru,sunanan kowa yakasa tsaye yakasa zaune musamman malam da ba yake jin tamkar ya maido ciwan jikinshi,ba abinda yake sedai sallah da addua,abufa har la’asar shiru maryama Kam alokacin tagama galabaita,ganin yanda take shan wahala Kuma komi zai iya faruwa alokacin kawai likitoci suka umarci ahado komai na aiki su shiga da ita tiyata Kuma asa hannu,nan fa hankalin malam yakara tashi yatai yahado komai cikin sanyin Jiki,nurses suka mata wanka suka shiryata aka turota zuwa tiyata room,asibi da mijinta sai malam da sagir da yazo dazu kadan,angungurota kenan Suka hadu suka zagayeta takalli malam cikin yanayi najin jiki hawaye Tabb a idanta Shima haka,”tace kayafemin duka abinda nama inamai fatan kasancewa matarka ko a darussalam”,daganan Nishi ya tuketa,yarungumota Yana kuka da fadin”zaku fito lfy insha Allahu ba abinda ki kaimin na yafemiki Koda zakiyi nan gaba,Ina kaunarki maryamu”, da murmushi kadan Jin abinda yace akawuce daita,
2hours suka dauka a theater room din,sukuma kowanne na jingine da addua Abakinshi,tindaga fitowar likitan cikin sauri suka Gane akwai matsala domin sunyi aiki lfy sunciro ‘ya mace Amma dinkin yaki tsayawa dasunyi seya warware,kaff hankalinsu suma yatashi Ananne Wani cikin likitocin yaruga yakira babbansu a consultant din dan komai Yana iya faruwa,malam yatarai Yana lafiya “meyafaru”,bemai mgnba yatureshi yawuce,Koda wancan yakaraso dakyar cikin dabara irinta wadanda sukaci suka gyare yasamu yai dinkin dabe Wani xaunaba,aka turota zuwa Wani daki na jinya me ita kadai,likitoci suka kafa dokoki da sharudda sosai km kada kowa ya motsata,sannan suka Mika musu jaririyar suka wuce daita gida domin yo mata wanka,
Tofah,kullu nafisn xa’ikatul maut,adaren ranar allah yakarbi abinshi bayan Wani jinin yaballe Wanda kafin likita yazo da aka kira harta fara jijjiga anan dinkin ya Idasa warwarewa allah ya amshi kayanshi,😭😭.

Mutuwar data girgiza malam samaila har ya suma sau ba adadi,inya farko ya cigaba da sambatu da kiran yashiga ukku,maryama kitashi ba haka mu kayi ba zan maidake gabansu cikin kwanciyar hankali,kinmanta alkawuranmu ya zaki min haka ya Allah kasa mafarki Nike Kuma kasa kada infarka idan har haka xan iske,kai daga karshe Shima allura aka cigaba da yimai zuwa safiya aka samo kanshi.
Kana akaimata wanka akakaita makwancinta na gaskiya,malam ya yaimata gatan Daya kamata kowacce gawa tasamu,(Allah kasa mucika da Imani)Ameen.
Sagir kuwa kaman amafarki yarika ganin abin seda suka dawo makabarta yaga da gaskene innarshi akarufe kaman yanda suke raka’ wata gawar yau ta innarshi aka kai,idanunshi suka Wani soye ya rungume jinjirar Yana jin tsananin tausayinta na rasa uwa da tayi awannan duniyar,shikenan ita bazata san innaba,Kai duniya abin tsoro,ta bashi asibi tayi tana share hawayen itama tana cewa”kawota sagir aimata wanka”
wata irin zabura yayi ya kankameta Yana cewa”wace ke agareta da zaki Mata wanka,nine nan komai nata dan haka nizan mata komai na rayuwa nine mamarta,nine babanta,nine yayanta nine kanunta nine abokinta nine everything in her life,kowa ya taba min ita zanmai abinda Nima bansan komi yeba,jinin innata jini nace”……,SE alokacin Wani kuka ya kufcemai Wanda yasa kowa nagurin ya koka,tabbas mutuwa na yankan kauna domin malam da sagir sun shiga tashin hankali sosai,duk da Karancin shekaru na sagir Dan lokacin be wuce 11 ko 12 Amma hka mutuwar Nan ta girgizashi.
Malam Kam tin yanajin Yana iya daurewa har abin ya kaishi ga kwanciya asibiti,domin jinin shi yai mugun Hawa harta kaiga idan yamike Yana tangal tangal kaman zai fadi,bayan yadanji dama dama aka sallamoshi alokacin anyi addu’ar bakwai,yakaima masu gidan makullansu dan bazai iya zaman gidan ba,su asibi suka nemi yabarmasu husna su shayar daita Amma Sam yaki yadda yace zai koma da ita gidanshi ga sagir dashi zasu kula da ita ga kuma hansai da yake tunanin ta raunana zata karba,
Shida sagir suka kwashe ‘yankomatsanta Daba yawane dasuba suka Maida dakinta nagidan,bayan sungama malam yakira hansai Dake daka tana fama da zazzabi akwana kinnan,tafito tana yamutsa ita adole an tasota Bata lafiya,dama tinda Akai rasuwar taje ranar sai ran ukku Takoma tana Bada uzurin wai ciwan malam ne yasa Bata zuwa tana asibiti gurinshi bayan Kuma shiyasan ba haka bane,to bata ita yakeba .
“Hansa’u kinga yanda ubangiji yake al’amarinshi nadauko yarinyar mutane Ashe bazata Koma mahaifartaba,Maryama diyar manyan mutanece,Amma kauna tasa ta biyoni inda Bata taba zuwa ba Ashe ajalinta ke kiranta,Ina Mai cike da nadamar rabota da iyayenta Bada saninsu ba,bansan Taya zan samesu ba idanma nasamesu Taya zan fuskancesu In fadamasu sanadin cikina tasu ‘yar ta salwanta wayyoh!rabbi kada kakaini ganin wannan abin kunyar inafatan Nima nabita kafin lokacin”.
“Malam wai kakirani zuba sambatu lfy”,hansai tafadi taname Jin haushin lafazinshi,yadubeta da husna ahannunshi yamika mata Yana fadin “ga marainiya Nan nakawo maki Dan allah kitayani rainanta”,Wani irin tsalle tayi gefe tana fadin “mikace malm Tabb,wallahi bazan iyaba Nima Ina fama da nawa laulayin,kodan kaga ban fada makaba saboda kana cikin yanayin rashin masoyiya,to nimadai allah ya amsa har na wata biyu”.
kallo kawai yabita dashi Dan yarasa mizai fadamata,tashi yayi kawai dan yasan karamai bacin Rai kawai zatai,gidan kanwarshi dasuke abokan wasa yanufa yabata ita tabata nono shikuma yanufi kasuwa Dan hadomata Madara da kayayyaki tinda ba mgnr suna andai rada mata sunan da mamarta tabata ,Kuma malam yaimata hakikanta har2 Daya tanada dama,su asibi suka soya Akai sadka dashi dankowa Rai badadi,
Binta kanwa take agurin mlm Amma Bata ciki dayaba,itama aiki yakawo mijinta Nan suka dawo tare,to Nan rikonta da shayarwarta Yakoma hannunta sai madarori da malam yake hadowa ana hada mata dasu dakuma magunguna Wanda likitoci ke rubutawa,kullum malam da sagir sunacan wajan asma’u in zaifuta sai ya biya in yadawo haka,sagir Kam ai inkaga bai gidan to Yana makaranta,shike dama Madara yabata,yaimata wanka yaimata kwalliya yazauna yanamata wasa shi adole sai tayi dariya wai tamanta maraicinta,kada tasan ita marainiyace,gwaggwo aikinta kawai Bata nono,wannan shine mafarin samun Asmau (husnah)
Ahaka rayuwa ta tura hansai taci gaba da renon cikinta,gwaggwo binta tanaba husna nono sagir nakulawa daita,domin baba yanzu ya zama wata kala tin daga rasuwannan,sekaga yazauna yai shiru yaxurfafa atunani harse Wani nakusa ya xungurai kana yake dawowa duniyar mutane,Kai tabbas so bakarya bane dmin tinda yarasa macen dayakejin tazame Mai Wani sashe na ryw Shima daganan yazama gayanan kawai,ahaka har ciwo yafara sarfa tarshi ahankali,lokacin da hansai tahaihu husnah watanta bakwai7,hansai takaro danta namiji,akasa masa Musa,bayan ta haihu da wata 2 akaima mijin gwaggwo transfer ta aiki zuwa kano,ananfa hankalin malam ya tashi domin bai san yazai da husnah ba,yanasanta har cikin ranshi Dan Koda suka nemi sutai daita kasa hakuri yayi yace ya gode da abinda sukai mai hakama sunyi kokari subarta wajanshi,anannefa suka shawota da hansai sbd kawota yayi yace tahada da Musa tadinga Basu nono,Kiri Kiri nanma taki seda malam yace tota barmai gidanshi,kana taga tarihi zai maimaita kanshi akuma sakinta akan ‘ya bayan na uwa da akaimata,to sananne takarbeta Amma da mugun kullaci aranta Dan ba Wanda tatsana yanzu aduniya kamar husnah,Kuma tayi iyayinta danganin taraba zuciyar malam da santa Amma Ina har yanzu ba’adace ba,komi yakwaso ita ita gata da mazan Amma abanza,ga sagir Daya gama mutuwa akan renon husnah,tantsina tazaga Amma abanza bai fasa mata abinda yakeyi,kullum cikin siyo mata kayan gwanjo yake da cokulate da kayan da yasan yaro naso,aikuwa sunyi wata irin shakuwa harta kaiga indai zai fita gida to da kuka zasu rabu.
Ahaka rainanta yadawo gidansu,idan malam Nanan ta bata nono Shima a wulakance idan kuwa ya fita to da duka da hantara tana fadin me kama da mayu wannan shegen kyan naki bana mutane bane shegiya mayya,da haka ta ida shekara Daya daga nan Kuma tace wlh sai dai ayayeta dan zaxata iya hadasu duka ba,sagir yace to shiya dauka tinda dama ba wani nono take bata ba,dan wani lokaci indai yafita gidan to itada abinci sai inbyashigo koshi ko babansu Dan daga kofar gida zakaji kukanta,
Daga nan fa ta yayeta taci gaba da goyon danta,ko alokacin idankaga husnah baka cewa shekararta Daya Dan tayi girmanta Kuma komi tasamu ci take,Dan yanyanta sagir komi yasamu itace sai dai ya tsakurama innarshi,ta zaga ta tsina abanza,sai dai inya fita ta daki husnahr taci kukanta tayi shiru ta rakube har yayanta yadawo ko babanta ko usaman Wani zubin Yana kulata.
Tofah!watan Musa 13 hansai tasamu Wani cikin tafara laulayi,nanfa komi yakara lalacewa na gidan ga malam ciwo ya tasoshi gaba yau Inda lfy gobe Babu,musan kanshi Bata wani kula dashi bare ita marainiya,seka ganta kaca-kaca taji yunwa taci kuka kafin yaynta yadawo ko babanta sannan suyi Mata wanka idan sun taho mata da abinda zataci taci,sukwanta itada yayanta susha baccinsu,
Cikin hansai nawata takwas malam yayi Wani ciwo Daya kwantar dashi asibiti,likitoci suka tabbatar dacewa idanbe rage tunaniba watarana jininshi zai iyi hawan daba asan akaiga gurin,sosai sukasha yimai fada danse alokacin su sagir sukasan cewa zuciyarsa ta samu matsala saboda yawan Aje damuwa acikinta, Ashe duk wata Yana karban magani, yaki fada musu ne saboda gudun tashin hankalinsu ga kuma tunanin yanda rayuwar husnah zata kasance,
saboda shi dai tuni yakejin cewa bazaiyi wata rayuwa mai tsawo ba ga kuma tunanin dangin maryama da yake saboda tsoron mai zai fadamusu,dakuma kunyar abinda yaimusu,Amma Yana fata Wani sanadi yakai jikarsu garesu Koda bayan bayanan,domin wannan tunanin akullum shike daga mashi hankali,gani yake kaman hakkinsu bazai barshi ba ga hakkin marainiya husnah,
Bayan kwana2 aka dawo dashi gida ya cigaba dashan magani,rayuwa taci gaba da juyawa,har hansai tahaihu takara samun namiji akasa masa Suraj baban hansai kenan tana kiranshi khalifa,tofa daga lokacin duk Wani rainonshi yadawo kan husna,tin tana ‘yarkaramarta tasan Dora yaro afo,wankamei Kashi da daukarshi.
Duk da yafi karfinta Amma haka zata jibga matashi idan Kuma takadashi taimata duka ta hanata cin komai,har yayanta ya dawo kana ya lallasheta yaimata wanka yabata abinda yasiyo mata,atakaice dai idan kaga dariyar husnah to da yayantane Koda babanta ko Usman Wani lokacin,Sam ita batasan shiga cikin Yara tayi wasa ba to yaushe ma tsongama tabarta komi tayi yanzu hansai zata daddana mata zagi takai mata duka,shiyasa batada walwala Sam……

Comments
Share Fisabilillah

❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️
SAWUN K’ADDARA
💕💕💕💕💕💕💕

Na husnah Muhammad.

Page 11&12.

Bismillahir Rahmanir Rahim.

_________ Yauma kamar Kullum babanta ya tafi kai kaya Wani garin,yayanta Kuma ya tafi makaranta Dan lokaci Yana J’s ne,mama hansai tabata rikon khalifa,tun tana daga zaune dashi harta gaji Kuma tana tsoron ta motsa yai kuka taimata duka Kuma ita kanta alokacin bewuce aimata wanka agoyataba.

Tananan dashi bacci yasaceta tabingire yaro yayo gefe daban Amma baikaiga faduwaba tinda kafafunta arabe suke,cann tanata baccin ta daga zaune tajingina da bango abin tausai Allah yakawo cinnaka yagalla mata cizo,tafasa Wani kukan firgici yaro ya wuntsila yafadi,Aiko hansai daga d’aka tafito dagudu Tayo inuwar,ai waigowar dazatai taga tanufota ga zafin cizan cinnaka kawai taiwaje da gudu tana me kukan tsoron abinda zai faru,aikuwa daidai mai mashin yabiyo layin yai sama daita tafadi Timm akasa.

kan kace me guri ya taru da jama’a aka dauketa gefe,ana duddubata,daidai nan hansai tabiyota harkan layin Dan ta damk’a ta iske memashin yarigata aiseta fasa kukan munafurci tana fadin”subhanallahi sai da nace kada tafito tazo taci abinci aimata wanka Amma dayake bataji tafito wayyoh nashiga ukku”.

Nan fa wasu suka yarda ‘yan cikin unguwar Kam dama sunsan bawani San husnah take ba Dan hk bawanda yakulata suka wuce daita asibiti,nanfa aka amsheta dakyar bayan ankirawo ‘yansanda akafara mata treatment,sannan Wani yaro abokin Yaya sagir yaruga makarantarsu yafada masa,nan Danan yanemi excuse yataho dasaurinshi,Koda yaxo allah yatakaita tsagewar Kashi kawai tayi saboda fadowar datayi se Kurjewa kadan,Nan aka mata gyara tanata kuka yayanta narungume daita kana aka rubuta mata mgni suka taho gida,memashin yabiya komai.

Koda sagir ya iso da ita bai cema mamarshi uffan ba yawuce Da ita d’akinsu Wanda shine na maryama ada,yaimata wanka yabata abinci da magani yasamu taibacci,kusa daita yazauna Yana kukan tausayinta da tunanin makomar rayuwarta tin tana karama gashi tafara samun riski arayuwarta,sosai yaji yatsani kanshi ma,gani yake duk sakacinshine dabe zama daita yakula daita,to Kuma inyai Wani tunanin seyaga aidole yafita yanemi ilimi kodan ya inganta ryuwarta da gobenta,yanada babban buri akan rywr husnah,yaso ace zcyr mahaifiyarshi tazama me tausayi tarik’a husnah tsakani da allah,tatayasu rike amanar da aka Basu kodan halaccin da uwarta taimai nakula datarbiyyarshi,to Amma yaya zeyi ai ita k’addara tariga fata.

Dadare malam samaila yadawo,tin awaje yaji labari aikuwa kaman zekifa yashigo gidan,kaitsaye wajanta yanufa ya iske sagir nabata abincin dare,hannun Nan yayi suntum ,kawai tsayawa yayi bakin k’ofar yanajin Wani irin karyewar zcy,da hawaye Tabb a idanunshi yak’araso Yana fad’in “yar babanta sannu,sannu kinji,
kawai seya fashe dakuka Wanda yasa sagir Shima Yakama,bawanda ya lallashi Wani seda kowa yayi shiru dankansa,kana yadafata yace “garinya kikaji rauni meya fiddake bayan nahanaki fita”
cikin gwarancinta tace “Ayifane yafati mama taxo bu’u nayuga,bazan ayaba”
Itawai cewa tai “khalifane yafad’i mama zata bigeta shine taruga Amma bazata k’araba,hawaye suka zubo ma malam,Dan yasan komai da hansai kemata kawai beda yanda zeyine tinda beda Inda zekaita dole nanne mafakarta kumashi dole yafita yanemi abinda za’aci,kawai seya dafa kanta yace
“kiyi hkr,kiyi hkr,kinji ‘yarbaba komi lokacine,Kuma komi yanada karshe,tabbas ke watace anan gaba domin Allah baze barki hakaba,kedai komai rintsi kikama mutuncinki sannan kada kici amanar kowa kizauna dakowa da xcy D’aya k……,
Dasauri sagir yarik’eshi Yadafashi Yana fadin”baba husnah metasani Dakake mata irin wannan kalaman,yarinyacefa dubi yanda take kallanka alaman batasan mekake fad’iba,”
“Nasani sagir Amma kaimin alkawari zaka zama me maimaita mata wad’annan kalaman akullum Kuma akoda yaushe,zaka rik’emin ita AMANAH Kazama komai agareta,kabata ilimi domin shine burin mahaifiyarta agareta,sagiru banjin zanjuri kallan marainiyar Nan ahaka,kazame mata jigo allah yatayaka rik’o kajiko Kuma katabbatar kanemi dangin mahaifiyarta ka rok’a minsu gafara nida mahaifiyarta”.

Haba baba kadena irin wadannan magangann zaka karyamin zcy insha allahu zamu reneta tare harta girma tagana da danginta danaka baki Daya”, baba yai murmushi kawai Dan shikadai yasan yanda zcyrshi ke bugamai alokacin ahankali yamike yakalli husna datayi bacci yafita Yana Mai cema sagir idan tayi nisa abaccin yasameshi adakinshi.

Koda yasamu yakwantar daita seda yai sallah kana yawuce dakin babanshin,sundade sosai kana yafito dawani danmakulli ahannunshi yawuce dakinsu ya Aje kana yai wanka yakwanta,acan dakin malam kuwa hansai ce ta bangazo tashigo bako sallama tana fadin “wai malam mekake nufi inajin dawowarka Amma baka shigoba,sbd ‘yar gwal taji ciwo to badai Nina jimataba garin shegen yawonta tafita mashin yakadeta,
dakyar nasamu taimako aka kaita asibiti memashin ma yaki Bada ko sisi se kudina nabayar dama nace idan kadawo nakarba gurinka”,

dago Kai kawai malam yayi yadubeta yacee “uhmm hansa’u kibi duniya asannu wlh kisan annabi yafaku,Inai Mai jiye maki hakki ya bibiyeki,Wanda karaina yau gobe shine sarkinka kinga kuwa dole kaduk’amai,Kuma husna yarinyace batasn komiba Amma kije kiyi gaki ga duniyar Nan,Kuma insha allahu watarana sekinbi k’afafunta kina Neman agajinta”,,
Hahh,takece dadariya tana fadin “wancan kucakar ‘yartaka zannemi taimako,to ayaushema wai,ai wallahi yanda tazo awulak’ance haka zata koma awulak’ance,’yarda ba’asan Ina kakwaso uwartaba,waya sanima ko aikin ashsha d’inku kuke Aikatawa kawani kawota kace matarkace,hmm mu munsan komai,’yardaba ta halakba”
Wani irin tari yasark’e malam,sosai yakeyin tarin Yana dafe kirji da Bude Ido Kaman ranshi zefita,aifanan Kuma tayi shiru da maganganunta tana fad’in”nashiga ukku malm kada yarinyar Nan tayi ajalinka tin tana ‘yar k’aramarta munbani mun lalace”,

dagudu tayi d’akin su husnah tatado sagir,yafito dasauri yanufi wajan babanshin,ya tallafoshi yaga idanunshi sun kakkafe bakinshi ya karkace kanshi yakoma gefe,inna lillahi yace,mama kamashi mukaishi asibiti dasauri,kinga yanda yakeyifa,
Dakyar yasamo adaidaita suka kamashi suka sashi ciki,alokacin besan inda kanshi yakeba,cikin sauri likitoci suka rufa kanshi,sedai Kash alokacin har yasamu shanyewar b’arin Jiki,iya k’ok’arin likitoci Amma Abu yaci tura,sedai suka rubuta wasu allurai da magunguna suka bama sagir sukace yai sauri yakawo ayimai yasamu bacci yadena jijjiga Dan hawan jinin haryayi worse,juya takardar kawai yadingayi bayan yafito bakin get,Dan kudin hannunshi saura dari bakwai da saba’in 770,Kuma ko makaho yashafa takardar yasan abinda aka rubuta Akai yafi karfin haka.

Gaba daya K’arancin shekaru yasa yarasa tunanin dazeyi kawai Yakama kuka,yakoma gefe yazauna,can Sega wata mota tazo wucewa harta gota Kuma Tayo baya Wani alhaji yazuge glass yabude Yana kallan sagir daketa kuka yace “Dan samari lfy ko”dago Kai yayi Ido jawurr Yana kallanshi kana yace “bakomi idona keciwo” murmushi dattijon yayi kana yace “tasonan kagani”kamar kada yataso Kuma seya tuna halin da baba keciki Hakan yasa yataso yazo bakin motar yatsaya,alhajin ya leko dakanshi kadan yace”wane irin taimako kakeso daga gani shikake bukata,katsaida allah aranka domin daniyya mekyau xan taimakeka”,
Se alokacin yaji hankalinshi yad’an kwanta,takardar yamiko Mai kana yafadamai abnd Ake bukata,cikin sauri alhajin yace shigo mujeto inkuma zaka Jira to”shahada yayi kawai yabi alhajin,tafiya suke Yana tukinshi atsanake sagir yabishi dawani irinkallo yanataso yatuna Ina yasan irin fuskar Nan Amma tashin hankalin dayake ciki yahanashi tunawa Sam!Wani babban pharmacy sukaje alhajin yafita yahado komai da komai yadawo yamiko ma sagir babbar ledar,yazagaya yashiga yatada suka koma asibitin,
Adai dai kwanar asibitin aka kira alhajin yad’aga wayar sukayi mgn,kana yajuyo yadubi sagir yace “D’ana Yi hkr Dan allah Wani Kiran gaggawa yasameni dama Wani patients nashigo gaidawa Amma insha allah zandawo indubaku duka,d’auki kayan kakaimasu afara taimakon mara lfyn Allah yabashi lfy”,sagir dasauri yace “to bamatsala nagode sosai kawu allah yabiya Maka bukatunka”
“Ameen Ameen”alhajin ya amsa yanamai Ciro kudi masu yawa yamikamai kana yajuya yatafi,sagir dasaurinshi yanufi asibitin dankai kayan,yanata Yaba kirkin alhajin tareda tuna inna Meronshi,Dan itama haka take da taimako koda iyakar abinda gareta kenan,allah yajikanki kawai yafada yawuce ciki.

Adai dai kwanar dakin yafara Jiyo kukan mamanshi Wanda yasa kirjinshi yabuga dakarfi,dasauri yaiso gurin Yana me yin kowacce addu’a taxo bakinshi,taradda ita yayi mutane sun rirriketa tana kuka tana fisgewa tareda fade-fade Wanda Hakan yasa yafahimci allah yayi ikonsa akan babanshi,xaman dirshan kawai yayi agaban dakin yanameji tamkar shikadai allah yake jarabta,anan likitoci suka fito da gawar agadon marasa lfy,D’aya daga ciki yadagoshi yanamai jijjigashi Yana cewa”se hakuri kawai k’anena Allah yaimashi rahma,kazo kasa hannu acike komai abaku gawar kuje ku sallasheshi,damuwar tariga takamashi dayawa hattai Mai attack lokaci Daya Kuma yasamu shanyewar Jiki,to se hkr kawai Abu yazo da ajali”.

Kaman mutum mtumi haka sagir yabishi suka cike komai aka Basu gawar motar asibiti tadaukesu harzuwa gida.

Subhanallahi! Kulli nafsin za’ikatul maut,dukkan me Imani alokacin seya tausayama wannan ahali,musamman sagir dako digon hawaye yagagara zubdawa se suyar zuci kawai da tunanin makomar wannan rywa tasu taduniya,anan take yarik’ajin Wani girma nahawanshi,yarik’ajin komai ze faru awannan duniyar tasu yanzu shine bangonsu,musamman marainiyar Allah,se’a lokacin yatuna daita da raunin Dake tareda ita,alokacin gudansu cike yake Tabb da al’umma ba masaka tsinke,anshigar da gawar d’aki wasu daga cikin abokan babansun suna shiryata dayimata wanka,ahaka yakutsa cikin jama’arnan yashige dakinsu inda yahangota rakube da bango tayi wata irin lamo tamkar wata babba wadda tasan meke faruwa ayau d’innan,ahankali yaisa gareta,yadubeta fuskarnan tayi jazir sbda Kuka abinka dama dafarar fata,duk da bawai can za’akirata da faraba,tadafe hannunta meciwon tana kuka ahankali alamar tayishi harta gaji.

Tsugunawa yay yarungumota yafashe dakukan tausayinsu,tad’ago tadubai tace”Yaya,tadena kuya,yima yunwa niceji naje baba benan amma yadena datanan”(kadena kuka Yaya,Nima yunwa nikeji naje baba benan amma nadena gakanan)rungumeta yakarayi yace”tabbas ganinan komi kikeso kifad’amin Dan baba yatai unguwa zaki Dad’e Baki ganshiba,tashi muje innemi Wanda zan ba ke,yakamo hannunta suka fito yasamu wata mak’ociyarsu yabata ita yace Dan allah takula Mai daita kafin sudawo Kai baba,takuwa ansheta tafice daita zuwa gidanta Dan tabata abinci tabata maganinta na ciwan hannu,

Akakai malam makwancinshi tareda Dumbin jama’a,wato baka Gane mutuncin mutum se bayan bashi,domin kaff unguwarnan sunji mutuwarshi,salihin mutum bawan allah ba’a taba rabashi fada dawaniba,kowa nashine tinda sukazo garin,to sedai muce allah yajik’anshi mukuma ya kyautata tamu,

Aka kwana bakwai ana zaman makoki kana akawatse,aranar ne Kuma kowa Yakama gabanshi,dama baba kadaine namji sauran matane kuma dukansu Uba suka had’a,kowacce ta kakkab’e tayi gaba sanin bawani Abu Garaiva Inba gidan dasuke cikiba,shikuma ga yaranshi Nan maza harguda hudu Dan ba mesa husnah alissafi acewarsu basusan sanda ya auro uwartaba.

Sagir ya aika adakko Mai husnah inda yabada ta,matar tabata ‘yankayanta tataho wajan yayanta,shigowar gidan kenan hansai ta fasa Wani irin ihu tana fadin awanne gidan wlh badai nanba kincinye malam zaki dawo kanmu to ta Allah batakiba wuce kikoma inda kikafito,kuka tafashe dashi tinda batai hankalin fahimtar maganganunba,dasauri sagir yawatsa ruwan yafito dandama Yana bayi wanka ya aika adakkota,
Fitowa yayi Yana fadin hava mama wace irin mgnace wannan kikeyi kiji tausayin yarinyarnan mana,”kutumar ubanka nace dankaga Ina kyaleka akanta ko to wlh dama arxikin malam yasa yanzu Kuma seta bar gidannan tinda batada gado acikinshi Dan uwatta asiri taima malam yataho daita amatsayin matarshi Amma mu munsan komi”,nanfa tafara hayagaga harta Tara mutanen layi ta xabga masu karya San ranta hartana cewa “likitoci sunce bawani hawanjini Naman ‘yancikinshi akeci dakadan kadan har akacinye rabinsu tokuma yaxaai yarayu ba Yan ciki rabi,daga gani kamun mayya takusa dashi,Kuma malam kafin yarasu yabata wasiyya kancewa takiyayi yarinyar Nan Dan ita keshirin kasheshi”maganganu dai marasa Dadi seda sagir yazo tsakiyarsu Yana kuka Yana fadin “billahil azim takori husnah Shima tarasashi har abadah Kuma duk Wanda ya yarda da abinda tafadi har ya tsangwameta to shari’ace zata rabasu”,

Yawuce ya hado kayanshi yafito Yana kokarin Jan hannunta,ganin dagaskefa tafiya zai yi yasa tafara Kiran mutane tana cewa”kutafi kada wannan Abu yasha feku mungode ta wargatsamin nawa gidan kowa yai hankali da ita kutai kawai nagode”,
Sai da aka watse tacema sagir taji ta yadda ta zauna Amma wlh ko kofar d’akinta kartaganta Kuma abinci bazata bataba,sannan kwananta kodaya karta taba,ehee.

Dawannan sharadin yace yaji shiyadauka,tofa dahaka taci gaba da zaman gida sedai sagir yakawo mata abinci in ya dawo makarantan yatai yanemo,dadare yadawo mata da Dan biredi dashayi Tasha inta rage dasafe Tasha,shikam ya dukufa Neman Sana’a da karatu Dan acewarshi Dan ita kadai da kannenta yake Nema,shine wankanta shine sabulunta da wankinta,shine tsefe mata Kai gata da gashi,Wani lkcn sai dai ya tai daita wajan mkrntarsu aimata kitso Dan a unguwarsu ba me yadda tashigar Mai gida wai kada ta cinyesu tinda ta iya cinye ubanta,da haka ya Idasa secondary school junior section,da fafitikarshi yasamu yahada kayan senior section yatai ss1,yafara tarin kudin saima husnah kayan firamire yasata,

Watarana sunje debate ya dauko ma makarantarsu na1, akace ya shirya zasuje Abuja wajan Wani competition da wasu manyan masu kudi suka hada amarantar da suka ta bayi tinda da dewa to shine zasuyi old boys suka hada gasa duk yaro me kokarin Daya lashe zasu dauki nauyin karatunshi,har ya gama karatu,a karshen satin zasu tafi,bayan yadawo gida yafadama mamarshi tace allah yakaimu ai sai kaje din,Allahumma yasa da rabo.

 

Taku a koda yaushe.

Husnah Muhammad.

 

Pls share & comments.

❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️
SAWUN K’ADDARA.
💟💟💟💟💟💟.

Na Husnah Muhammad.

Page 13&14

Sadaukarwa:Gareki oum neehal,Allah yabar tare.

 

____________D’aki ya wuce yana mai k’walla ma husnah kira Dan ko yaushe ita tana d’aki tayi bacci ita kadai tayi wasa ita kadai,se in yayanta yadawo yakoya mata karatu,da murnarta ta amsa yashigo yasameta Yana cewa kinci abinci.

d’agamai kaitayi saboda yanxu hansai takan Bata Wani xubin domin komi nagidan kusan itace tintana hakanta,wankin Kashin Yara Debo ruwa amono, D’an wanke wanke da ijin wutar Kara,tin Bata sababa harta Saba inta gama tashigewarta d’aki,Kuma tanada wata dabi’a koyaya kabata abinci zataci tayi hkr dashi,Kuma idan zataga nama kahanata Bata damuba Koda kabatama tana iyak’inci sbd yayanta nayawn fad’a mata tadinga hkr dakadan wata rana meyawa zezo,ita Kuma duk abnd yayanta yafada mata to tarike shi kenan akanta.

“Yaya sannu dadawowa”.

“yawwa ‘yar yayanta yafadi’ Yana zaunawa tareda cire riga yasagale yazauna Yana cin abinci,yaci fin rabi yarage yamika mata yace “anshi nak’oshi cinye sauran yayanki”,

tayi murmushinta mesanyi tace “nakoshi Yaya kaci kaje makayanta”,
“Amsa mana ninace nakoshi ai”,tasa hannu takarba tacinye Tasha ruwa dandama bawani koshi tayiba,kawai dai tasaba rayuwarta tin ayanzu dakomi tasamu tahkr,to wama zataima k’orafin base tanadashiba,mama hansai inbanda zagi da duka da hantara zuwa aibantata ba abnd kehad’asu,Kuma ita batasan Wani abokin wasaba Dan kokadan Bata Saba zama cikin mutaneba tin tana jinjirarta.

Yaya sagir ya dubi yanda tayi shiru tana tunani yajanyota jikinshi Yana fadin”‘yar yayanta zanyi tafiya ran karshen sati,zanje innemo mana yanda rayuwarmu zayai kyau ko”?,
fuska tatab’e alaman kuka tana girgixa Kai,alamar bataso Kuma batayaddaba,cikin lallashi yadago habarta Yana fadin “no don’t cry,badadewa zanyiba k’ilama aranar zamu dawo zanje Abuja ne Wani competition na mkrnt kinga inda raban insamo kudin dazan cika inkaiki mkrnta shikenan ko?se xuwa mkrnt ko,inyee ‘yar yayanta” .

Wangale Baki tayi Jin ya ambaci mkrnt Dan tanason mkrnta sosai,gata da k’ok’arin rik’e karatu Dan kome sagir yakoya mata tofa tarike,Shima har mamakin hakn yake

“to Yaya Allah yasa kaciyo mana,Allah yadawo dakai lfy”,
“Ameen ‘yar yaynta,ban insha to”tabashi hannu suka tafa ta kyalkyale da dry,Shima yanayi Dan shi kullum burinshi yaganta tana wannan farincikn,
Bayan yamike yai wanka yasa kayan aikin gareji dayake zuwa tinda yau ba islamiyya,yai mata peck akumatu itama taimai agoshi yafita yanai mata by bye.

“To munafuka irin mayu kina Ina fito wlh kurwar D’ana dai tafi karfinki,kigama salonki kibarshi shegiya me kama da aljana fito kigoyamin khalifa kiwuce kimin ijin wuta”,

Dasauri tafito dantasan da ita Ake,jikinta narawa tadauki khalifa tagoya duk da yafi karfinta Kuma datsiya taiya goyon bada arzikiba,tawuce rumfar sanwa tana iji tana zakud’a yaro Yana mata kuka itama idonta namata kwallar hayak’i.

Aranar alhamis Yaya sagir suka cilla Abuja tareda malaman dazasu wakilcesu a motar makaranta,sunsha tafiya bakadanba kafin sushiga garin Abuja,nanfa Yaya sagir yabude Ido Yana kallan gari sosai,yayaba dagarin kwarai, ga komai cikin tsari ba cunkosom komi kodan unguwannin masu abun sukaje,bayan sun Isa masaukin da aka Basu kowa yayi wanka yayi sallah aka kawo masu abinci merai da lfy.

kowa yanacin nashi Amma shi kad’an yake tsakura dmn ba abnd yake tunani se husnah shin ita kome taci yanzu? Toya zeyi beda Inda zebarta Wanda yawuce Nan,Amma Yana d’aukar wannan wahalar tata talokacine,dmin duk iya fafutukar dayakeyi yanayine domin ya inganta ryuwarsu musamman ita mace Mai rauni,Yana fata Daya gama karatu yasamu aiki kokuma yayi karfi asana’a idan Allah yaso,yafara biya mata kudi tayi karatu sosai itada Usman kana yagina masu gida sukoma nasu daban nasu mama daban sbd bemasan yahad’asu guri D’aya bare mama tadinga tsangwamarta.

“Sagir Kai sagir lfy?”, Wani abokinshi yadafashi Yana mgn,firgigit yadawo daga tunanin dayakeyi,lukman yace;”meke damunka waikai kullum kake cikin tunani haba bakada Wani aiki se tunani bari hawan jini Yakamaka tin kana under age Dinka”
dariya kawai yayi ganin yadage yanata fada,bece komaiba yacigaba da tsakurar abincinshi kawai.
Washegari dawuri suka shirya Dan halartar gurin Taron dmin 8 za’afara gabatarwa,bayan sun Isa Akai introducing na wadanda suka shirya Taron dakomai kana akafara,
Wajan karfe shadaya aka karasa cikin iKon ubangiji sagir yalaso nabiyu acikin dubun daliban gurin,aikuwa zokuga murna wajan malamansu,nanfa aka karramasu tareda alkawarin wannan kungiya ta manyan mutane zata zab’i d’alibai mafiya k’ok’ari amakarantun dasukaci tadauki nauyin karatunsu,aikuwa kowa murna tarufesu ba malamanba ba d’alibanba.

Bayan andan lafa aka umarci da Adan tsagaita za’aba wadanda sukaci kyauta daga wannan kungiya,anan aka umarci Wani babban alhaji da akeji dashi Daya fito domin karramasu dakansa,alhaji yataso cikin dattako da kasaita irinta wadanda sukaci suka tada Kai,Wanda yalaso nahudu4 akafara ba,kana na3 sannan akaxo kan sagir nabiyu,yafito yadunfari gurin da addua akasan xcyrshi,dagowar daxeyi dinnan idanunsu suka gauraye cikin najuna,Ido yak’walo yanaso yatuna Ina yasan fuskar Nan kuwa,acan gurin alhajima haka take,yaiso ya gabatar Mai da karramawarshi hadeda addua kamardai saura harya juya alhajin yace “idan antashi Kabi wancan yakawoka bakin motata kaji dansaurayi,”

“To” kawai ya amsa daita yajuya yakoma mazauninshi,danseda yazauna kana yatuna inda yasan fuskar Ashe alhajin Daya taimakeshine ranar da babanshi yarasu,kauda tunanin kawai yayi har aka kammala Taron akarufe da addu’a kowa yafito a hall din.

Daga bayanshi yaji ana Fadin”jimana samari bakaine ‘yallabai yace kajirashiba”, juyowa yayi danse lkcn yatuna,”ok nine muje kawai Dama Ina nemankane”

Atare suka taho da direban alhaji har bakin motarshi suka tsaya jiran alhaji dansuna Wani dakin metting akan daukar nauyin yaran dasukai alkawari,anan malamansu suka samesu suna fadin yazo zasu wuce ansanar dasu sauran bayani zasuji daga baya”,
direban yakallesu yace alhaji yace yajirashi kuje za’amaidoshi kawai”, abin mamaki gani sagir yai sunce to kawai bawani tuntubar waye alhajin kodanshi D’an talakane ko cinyeshi Akai bamebin ba’asi.
kawai Dakar dazcyrshi yayi dandama sagir dawuya kagane meke aranshi tin ahakanshi shiyasa kawai yayi fuska suka wuce Yanai masu sallama.
Harkusan biyu2 kana suka fito daga meeting,alokacin sagir harya kulu iya kuluwa,alhajin yaiso Yana fadin “kuyi hkr natsaidaku kunata Jira”,dasauri direban ya russuna Yana “bakomi alhaji sannu da fitowa”,wucewa yayi kawai yashiga motar Yana fadin muje ko,
Dakyar sagir yashiga motar Yana kunburi Dan wlh yajihaushi duk da rashin hasalarshi dawuri,bayan sun Mika datfya alhaji yajuyo Yana fadin “dansaurayi yasunanka ne”yadago dakanshi yadubeshi yace

“sagir samaila tukur” alhaji yai murmushi yace “inafatan kaganeniko dankada kabini cikin rashin sani harkaimin mummunan xato” yai Dan murmushi “yace naganeka Kaine Wanda yataimakeni a asibiti watarana”,” eh kwarai Kaine kayi hkr awashe gari nakoma asibitin dubo Wanda naje dama danshi, toda nanemeka shine akefadamin ai kafin kadawo aranar allah yaima mahaifinka rasuwa,naso nanemeka to abubuwa dayawa sunsha kaina Kuma dama Wani Abu yakaini daganan Kuma allah yamantar Dani lamarin Amma kwarai naso nabibiyeka, Amma yau gashi allah yahadamu ubangijibya gafartama mahaifinka yasa yahuta”.

” Ameen Ameen kawai sagir ya amsa”

Bayan sun Isa Wani gida flat house mekyau suka iske abinci dakoami,alhaji yace yaje yai wanka yacanxa kaya sesuyi mgn,adaddafe yawuce Dan hankalinshi gaba daya yakoma gida wajan husnah,cikin sauri yakintsa cikin kayan dayaga ankawo mashi ya ninke nashin yamaida ajakar Daya Ciro wadancan,daga gani kayane masu tsada Kuma yai fess acikinsu,bayan sunci abinci yasa aka kirawo sagir,anan yabukaci sanin wayeshi?

sagir yabashi D’an tak’aitaccen tarihinshi kana yad’ora dacewa inba damuwa yau yakeso yawuce sbd yabaro mamarshi da k’anwarshi Kuma kusan dashi suka dogara,

Alhaji yadubeshi yace”to sagir naji bayananka Kuma yanzu k’ungiyarmu tad’auki nauyin karatunka tindaga SS har jami’a insha Allah, yanxu inaso kafad’amin Kai akaran kanka mekakeso inama Dan haka kawai nikeji inaso intai makeka”.

Sagir yad’ago yak’urama Alhaji Ido kana yace”
“Burinah nikeso kacikamin na sanyamin k’anwa amakranta domin tasamu rayuwa mekyau tinda ni kund’auki nawa”,
Alhaji yayi murmushi yace ” sagir kannenka nawa? Sagir ya amsa da ” su hudune akwai Usman da husnah danike Fadi yanxu se Musa sannan khalifa karaminmu.
Amma husnah marainiyace Ina tausayinta mamarta tarasu tin tana jaririya”,
Shiru Allaji yayi kana yace “to ta Isa sawa makaranta yanxu”,
“Eh harta wucema danma Ina koyamata agida Kuma tana dauka”,Alhaji yace “to za’asanyama ita makaranta idan kannenta sun Isa suma za’a sasu zannemi Wani agarinku inbashi wannan aikin,Kai Kuma kafara dga makarantar damuka tsaida akungiya idan kagama secondary school semuga abinda allah zeyi, kadage sosai kayi karatu kaji ko”,

Cukin kuka sagir yad’aga Kai Yana fad’in “nagode kawu nagode sosai allah yabaka abnd kakeso yasa kafi haka”,Alhaji yarungumoshi Yana cewa” bakomi wlh har cikin Raina nikejin ka kaman Dana,baseka godeminba nauyine agaremu masu shi mu tausayama nakasa damu,kashiga ciki zuwa dasafe se diriver yakaika ko”.

Badan yasoba haka yakara kwana,Alhaji Kuma yaimashi sallama yatafi yacemai idan yasamu dawowa gobe to,idan Kuma bedawoba to zedaiga Sak’o,Kuma yabashi wata ‘ yarkaramar waya yace kome yakeso yadinga tab’ashi, wanshekare tinsafe yashirya komi nashi yazauna ashirinshi,bayan yakarya driver Nan yasameshi yace sutafi alhaji baze samu zuwaba,Amma ga sak’onan,yabashi kudi masu yawan gaske daganan yai aike zuwa Wani mutum acan katsinan akan sanya husnah makaranta da Musa.

Bayan sun iso gida lfy,driver yai sallar la’asar kana yasamu almajirai yace sukwashe kayan boot sushigar masu dashi gida,sagir sedai yayi tsaye kawai Dan kayan abincine dakomai hada wandama Basu iya amfani dashiba alhaji yahado masu dashi,rasa mezeyi kawai yayi sedai yaitsaye Yana kwalla da tunanin yanda Allah ke ikonshi,cikin kankanin lkc ubangiji yaragemai manyan matsalolinshi,
Gdy sosai yayi,yakuma ce akarama alhaji gdy,daganan driver yasa tafiya gudun kada yaidare,hansai nazaune husnah nacan rumfa tana iji,taga anata shigowa dakaya,dasauri tamike tana fadin ” Kai lfy waya aikoku ko batan Kai kukayine”, tana mgnr Sega sagir yashigo tajuyo gareshi tana “autare kuke Koko daga Ina wad’annan kayan kadadai inji SATA kakoma”.

Murmushi yayi yasallami yaran kana ya tsuguna yace “A’a mama dagacan nadawo dasu bari inrage kaya zanmiki bayani,Ina husnah?”.
mtss taja tsaki “Ina tambayarka kana tambayar wata shegiya can to tana inda yadace daita”, hayaniyar mama hansai tafito daita rumfar Jin ta ambaci shegiya, danta dauka ko kiranta take,aikawai setaga yayanta dagudunta ta iso gareshi ta rungumeshi kawai tasa kuka Dan bakarya kwana2 Nan tagane kuranta dabainan duk da be Isa yahana komaiba Amma ganinshima kanshi rahamane.

Wata banzar tsuka hansai taja tawuce kawai danji take kamar tajanyeta daga jikinshi taimata duka kota Dena shigema danta,dakyar ya lallasheta suka wuce daki yacanza kaya yazo yai wanka yaci abincin data kawomai,bayan yanatsu yaima mamanshi bayanin komai kana yadora dacewa “insha allah husnah da Musa sunkusa fara zuwa makaranta,Kuma wannan kayan abincin duk shi yahad’oni dasu,sannan gakudi kinga se infara Sana’a koyatake kema kiyi aikinga zamu samu sauki ko”.

Seda yagama bayaninshi tace ” Tabb waccar yarinyar za’akai mkrnta tadinga lashe yaran jama’a wlh baze yuwuba adaikai musan ga khalifa Nan inya K’ara wayau ahad’asu,itakuma indiba cikin kayan abincinnan infara abincin saidawa tana zuwa talla Amma waceni taje tad’auko min mgn,Muma nagidan sbd Ina tsayene datuni tagama damu musamman Kai daka nacemata waikai metausai hmm”,

Tinda tafara jawabinta Ido kawai yasamata seda tagama sannan yamik’e yace mata yatai masallaci kawai Dan gani yake tankawarshi bazata haifar da d’a Mai idoba,

Bayan kwana2 Akai sallama hargida Wani yaxo sukai mgn dasagir akan shine maikai su husnah makaranta,sundade suna mgn kana mutumin yatai.

Wanshekare segasu da d’ansanda sagir yatafi makaranta,sukai sallama da hansai,tasa hijab taleko suka gaisa Dan tuni cikinta yaduri ruwa bayani sukaimata akan makarantar yaran, da dokokin makarantar da lokacin xuwa Dana tasowa,sannan Suka Dora dacewa idan har sukai fashi tosu dokar makarantar azo akama iyayen akullesu na tsawan satii da aikin wahala indai ba uxurin rashin lfyba Kuma duk akakama iyayen dahanasu xuwa to kotu zata Yankee masu hukunci,
Tofah anan akasamu hansai tasa hannu akan barinta zuwa makarantar,saboda dagaske tadauka dokarce tindaga sama tinda ita ba ilimin bokon bare na Arabi,Kuma wannan duk Shirin d’antane Yaya sagir domin yayi tunani idan harba tawannan hanyarba bazata bar husnah tai karatu ba.

Acan b’angaren makarantar su sagir tuni komi yakammala ancanza masu sagir wata makarantar wadda anan zasu cigaba,makarantace mekyau me tsada wadda xasu samu ilimi mekyau da nagarta Dan samar da ilimi mekyau ga Al’umma anan gaba,Nan Danan suka fara zuwa karatu ya kankama tinda abin namasu gidan ranane.

Muje xuwa
Kuji yadda zata kaya
Kada kumanta Muna cikin labarin husnah ne..

Yanxu zamu fara
Kudai kubiyoni danjin labari mecike da al’ajabi.
Husnah Muhammad.

 

 

Plss share&
Comments.

🩸🩸🩸🩸🩸🩸
SAWUN K’ADDARA.
❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️.

Na Husnah Muhammad.

Page 15.

Sadaukarwa: gareki Aminiyar k’warai Allah yabar tare,oum neehal👏👏💕💕.

Dasunan Allah me rahma me Jin k’ai.

_________Abangaren husnah ma haka akai tafara zuwa makaranta daga primary 2 saboda gwadata da Akai tanada karatu sosai balaifi,sedaifa har makarantar tafiye mata gidan domin data dawo to cikin hantara da zagi take,gashi tin alokacin duk Wani aikin gidan yadawo kanta,dkyar zata samu takammala tawuce islamiyya,tana dawowa karfe shidda tadorama hansai kaskon tuyar awara ak’ofar gida,sagir yayi yayi tak’i bari,Wani lokacin seta wuni da yunwa,sedai taita rakub’e rakub’e tana lank’wasa ciki Amma dayake Sam batada k’orafi ko hayaniya sedai taishiru harse in sagir ya fahimta yasamo mata d’an wani abin tatab’a.

Haka tin asuba take fara aikin gida,musamman yanzu data D’an fara girma suka Dena kwana da sagir dan tuni yakoma dakin zaure se ita kadai ad’akinta da ‘ yar lamusassar katifatta,haka zata kammala komi kana tasiyo Koko Wani lkcn ko shan shi batayi sedai su khalifa,tashirya tawuce inta dawo har talla takeyi ta kulle kulle kana tatai islamiyya inta dawo tadora wara.

Akowanne lkc sedai Yaya sagir dinta ya zaunar daita yabata hkr danuna mata cewa watarana se labari tadinga hkr da ryw,takancemai “Toni Yaya mena rasa ai mama uwatace duk abnd zatasani danta isane,Kuma ni banjin whl tinda nasaba”.

Ahaka takammala primary school alokacin yayanta harya shiga jami’a da taimakon wannan alhajin Daya taimaki rayuwarsu,Dan wani lkc takanji suna waya har yace agaisheta kawai dai Basu taba gaisawaba,
Ahaka yayanta yahada mata komai zuwa boarding school,Wanda iya jarabar hansai sagir yak’i fasawa Dan acewarta aikin gidan datake matane yake bakin ciki ko tuyar awarar datake mata dadama baso yakeba,shidai hkr kawai yabata ya cemata daga mkrntr data gama aka turata,to dahaka husnah ta tattara tai boarding school js1.

Rayuwar makarantarta Bata Wani canzata sosaiba,sbd tincan ita Bata Saba shiga jama’aba,Bata taba kodayin K’awa arayuwarta ba tinda mutanen unguwarsu bawani kulawa da huld’arta sakeba tun tana k’aramarta,akoyaushe itadin silently ce,mara sakin fuska sosai,Bata damu da rywar kowaba haka Kuma bataba kowa fuskar shiga rywrta ba, domin akoyaushe takan tuna maganar yayantace dayake gargadinta akan shigema mutane da shiga hurumin daba nataba,sannan ya gargadeta akan kada tasake tacanza dabi’a shiyasa ita rywr kowa Bata gabanta,.

Agefe Daya Kuma takasance d’aliba me hazaka dashiga ran mutane,cikin shekara D’aya tayi ‘kuwwa a mates dinsu,tazama d’alibar datafi kowacce krtu da hazaka,nandanan malamai suka Santa,haka daliban kowa sotake takulata su k’ulla k’awance,itadai dayike bata Saba da k’awancenba Bata Wani irin shige musu,duk wadda tazo gurinta tatace hk Kuma bazata bari kishiga jikinta sosaiba sbd tanada tsantsenin Huld’a da mutane,atakaice dai Bata Wani tsawwalawa rywrta.

Duk visiting Wani zezo mata ko yayanta kokuma Wani Dan aike inshi baida lkc sbd yanayin karatu,idan anyi Hutu Kuma shi zezo yad’auketa to Ananne kawai zakaga fara’arta sosai da sosai,Dan Wani zubin inkanaso kaga murmushinta Toka kirata da ‘yar yayanta,yanzu zata D’an Bud’e Maka hkrnta tana murmushi,hk idan tadawo gida zata D’ora daga inda tatsaya a aikin gida,ahaka tazama wata irin murd’add’iyar yarinya,miskilar gaske Dan zata iya kwana2 Bata tankaba kawai duk abnd hansai tasata zata mik’e tayi idan Kuma tasan aikinta to base ansataba,Dan duk Wani kalar abinci na talaka Mai k’aramin karfi ta iyashi,Kai Wani lokacima idan ta anshi wayar yayanta shi take Cema yakamo mata wajan koyon abinci tana karantawa.

Ahaka takammala junior section,tafara senior section, alokacin Wani irin tashen ‘yammatanci yafara zuwa mata,domin gaba daya tacanza,sanda zatakai ss2 kuwa duk wata Alama ta budurci ta bayyana agareta,doguwace Amma tsawo na daidai misalin macen daza’a kira doguwa acikin mata,tanada Wani irin Jiki Mai d’aukar hankalin kowanne Dan Adam kaman dai anzanata,ba fara bace irin candinnan A’a wata irin colour ce datake wahalar samu,irin chocolate d’in nan mai hasken dabata alayin bak’ak’e,tanada hanci shi ba irin dogon nanba harda xeyi yawa sedai kawai dole zaka kirata da me hanci,ga gashin gira zagar-zagar da yayima idanta wana irin kyau kaman ‘yar hula aka kifa,tanada manyan idanu Wanda in akarufesu bakacewa sunkai haka girma seta dallo makasu sannan kaga girmansu da haskensu,bakinta Dan karamine kaman cokali baze shigaba me d’an jaja jaja,girarta ahade take kaman Wanda Ake ma shaving duk wata hk zanenta yake.

Ba siririya bace haka Kuma bame kiba bace,kawai tanada mazaunai masu kamar anzanasu,hk kirjinta yake kaman anhura Balo Dan madaidaici ankifa akirjinta,komi nata kaman ita tayi abunta,sedai kawai nace me karatu ka kiyastota aranka.

Adai dai wannan Hutun Data dawone Wanda dagashi se sunyi exam zasu K’ara dawowa gida gabadaya,shine yai daidai da kammala degree nabiyu Dayaya sagir yayi,inda yafito da babban maki a roll dinsu,inda kungiyar Data had’a tabiya mai karatun sukai shagali sosai tareda yayeshi dasukai afagen karatu dakuma alkawarin sama Mai aiki metsoka,inda bayan ‘yankwanaki alhajin yakirashi yanamai sanar dashi cewa yasama Mai visa tareda wata makaranta a London inda zeyo master na shekara2 daganan idan yakammala seya fara aiki gaba daya.

Yaji dad’in Hakan sosai duk dayaso yadakata hk da karatun yasamu aiki Dan yasamu damar cigaba da daukar nauyin karatun su husnah da musa da Usman tayanda suma zasuyi karatun mezurfi,Amma bayajin ze’iya yima alhaji musu domin shid’in tamkar mahaifine agareshi,Dan hk kawai yace bamatsala tinda husnah saura 1yr takama secondary sch,tashiga jami’a lkcn daze dawo seta dawo hannunshi akan komai na hidimarta tinda yanzu alhaji ke d’aukar nauyinsu.

Kyakkyawan matashine yasauko daga adaidaita sahu cikin suit bakake,farine sosai kana ganinshi kaga Wanda yaci krtu da ilimin addini,yanda tsawo daidai misali haka jikinshi amurde yake,irin maxmzan nandai classic, da samunsu kewuya,yajuyo ckin takunshi na natsuwa yanufi cikin gidan,balaifi gidan yad’anji gyara bakamar daba Daya fara Shan wuya,shigowa yayi Yana fadin “Assalamu alaikum,wai ance husnah tazo inji saurayin dasukai zexo yau”. ,yafad’i haka cikin shak’e murya shi adole kada agane muryarshi,
daga kicin husna tace cikin dry,”kace tana zuwa my noory ya iso kenan”,k’walalo idanu yayi yabude murya yace “whatt”?,

Habawa ai seta fito tana kyalkyale dariya,tace”yess bakai tono naba Yaya”,murmushi yayi kawai yace”Dana gota kafar duk Wanda yazo gurin kanwata Bada izininaba”,
Tab’e Baki tayi tana fadin “ni bawani dazezo Koda saninka duk inda kake inanan idan yayarda Kuma zedawo gidanka to K’ila in iya tunani akanshi”, kallan bakida wayau yaimata domin haryanzu kanta akwali yake,Dan Sam batada wayo nasauran ‘yammata ita ko a makaranta malaman dasuke damunta Bata Wani kulasu karshema dasuka dameta yayanta tafada mawa yakai kashedi daganan suka Dan lafa mata,haka haryanzu batada k’awa ko aminiya,hargara zahrau ‘yar gidan PC dinsu ce takan Dan biyemata Wani lkc suyi fira amkrnt,shine ita zaharau take fad’in ita kawartace ako’ina Amma itadai Bata Wani biye mata,sbd ita tanada hayaniya da surutu itako batasan hayaniya Dan inta dameta da surutu Wani lkcn har baccin karya takeyi.

Yaya sagir ya karasa yazauna Yana me fadin Ina mamar take?”.

“Taje gidan haihuwa tace Kuma zatakai dare”, ” ok bari inwatsa ruwa kindai kusa gamawa ko Dan yunwa nikeji nayi missing abincin ‘yar kanwata sosai”, tayi dry tana cewa” shiyasa nadafa abinda kakeso kuwa my Yaya”, tashi yayi yashiga Yana mata dry,harya shirya yafito sunata wasa da dry tazubo abinci sukaci tare harda Yaya Usman Daya dawo mkrnta yanzu tinda yanakan hada degree ne,suna gamawa Usman yai wanka yafice majalisa.
Ananne sagir yadakko Wani Dan akwati Daya Dade Yana ajiyarshi yazo yazauna bayan yakulle gida Yana fadin “lily zonan zamuyi wata mgn me mahimmanci”, to”tace bayan takauda kayan tazo kusadashi tazauna,
Ya dubeta cikin natsuwa yafara fada mata yanda sukai da kawu alhaji akan tfyrshi London hado masters,

Aikuwa kuka tasa tana ita Bata yaddaba yaza’ai yatai harshekara 2 ita dawa zata zauna,yai dry Yana fadin ” bakiso inje”tadaga Kai tana share hawaye, tayata sharewa yayi yafara lallashinta dafadin ” Haba lilyn yayanta Dana gamafa zandawo infara aiki kema insama maki makaranta mekyau kici gaba da karatunki kizama babbar likta koba burinki kenanba,” tadaga Kai tana share hawaye, yacigaba dacewa”to kinga kawu alhaji yaimana abnda bamuda abnda zamu sakamashi dashi face addua knga be kamata yace ga hanyar Daya kamata inbi ba incemashi a’a Koda bata karuwa tabace bare Kuma niyake amfanarwa,husnah bakiga gidanshi bane bakiga tarin dukiyar Daya tara bane bakisan iya matsayin dayake dashiba,ga ‘yaya harda wadanda suka Fini sosai amaza Amma duk ni’imar Nan behana yajani yamaidani kaman D’an cikinshiba yabani kulawa kamar shiya haifan,Wani lkcn har Hutu yake matsamin inyi agidanshi ga iyalanshi mutanen arziki,husnah kinga aibe kamata intsallake mgnr Shiba ko?.

d’aga Kai tayi tanajin k’aunar wannan kawu alhajin Dayake k’aunar Yaya sagir dinta haka,” tace Yaya Nima inasanshi to watarana zaka kaini inmai gdya da irin San dayake Maka da hidimar dayai mana,Kuma nayarda Allah yasa tfyr tazame Maka alkhairi damu Baki Daya”,
Ya rungumeta yanajin dadin hankalinta da hangen nesa kawai matsalarta rashin wayau ne,Shima Dan Bata shiga Yara bane tayi kuruciyarta ita kadai shiyasa batakai wayan sauran ‘yammata ba,wannan yasa yakara dacemata “kinsan gargadina agareki kada kisake komai rintsi kizubda mutuncinki da darajarki ta ‘yamace,Kuma duk wahalar dazaki shiga gwara ki afka mata daki Bada mutuncinki,husnah Nasha wahala sosai akan tarbiyyarki har dako nayi Dan kawai kirayu da kimarki, kimin alkawari zaki rik’e min mutuncinki har indawo lfy kigama krt inkaiki dakin miji lfy.
Dan allah komai tsanani kizab’eshi akan kibada mutuncinki,Kuma komi kike bukata kisanar Dani awayar audu meshago kafin kigama mkrnt insiya Miki taki wayar”,tai murmushi kawai tace

“Yaya nayi alkawari, da insabama alkawarinka gara nafuskanci whl dayunwa da azaba mara yankewa,kai d’in tamkar uwa da Uba ne agareni yimaka biyayya wajibine insha allah zanyi duk abnd kace”, yai murmushi yafiddo Wani Dan makulli yabude akwatun Yana fadin “kinga wannan akwatin dukya girmemu harni shine gurin ajiyar babanmu,Nima yabanine domin Wani sirri nashi daya taba bani ajiya”,ta kwalalo Ido tanacewa “Yaya harkai yagirma fa kace”, “yess kina mamaki ko yarinya naiya ajiyane ko mama batasan dashiba,dagani seke Dakika ganshi yau dinnan”, ta girgiza Kai alamun mkk kawai,
Ya fiddo Wani Dan akwaku na Zobe kana yarufe akwatun yajuyo yakamo hannunta Yana fadin “yau zan sauke amana tafarko akaina kinga wannan zoben?yabude yafiddo mata, ” zobene da mamarki tabani tin Ina firamary tace intabbatar nasadaki dashi bayan kingirma kin mallaki hankalin kanki,husnah ki Adana wannan zoben domin innarmu ta tabbatarmin akwai Wani abu megirma atare dashi,(yaboye mata cewa zoben manuniyace Dazata Nuna ita din jinin maryamace aduk inda taga danginta,saboda kada watarana tayi gigin nemansu dakanta kafin lokacin Daya tanadarma hkn yayi).

Sewani pic d’in mamarta guda D’aya Daya Bata alokacin tanada cikinta sunje Wani suna ana daukar hoto aka dauka daita bayan anwanko mejegon ta Aiko mata dashi tana tsokanarta wai ta Aje na tarihi lkcn tanada cikin fari,tayi dry kawaii tamikama sagir tace ya Aje,shikuma ya adanah.

fira sukaci gaba dayi Yana Bata labarun kyawawan halaye irinna mamarta, Ananne take tambayarshi Inane asalin garinsu mamarta tanaso taje Hutu gurinsu bayan tagama mkrnt,shiru yayi zuwa Wani lkc,kana yace mata “Nima bansan ainahin inda sukeba husnah Amma dai akwai wasu hanyoyi da babanah yasanarmin alokacin rasuwarsa Amma sekin gama mkrnta zannemesu domin suganki cikin kwanciyar hnkl da walwala”,

Daga Kai tayi tace to Yaya ya Akai duk Saban Dakake Fadi tsakaninku bakasan gidansu mamaba kenan Bata taba zàuwaba tinda tazo Nan grn”.

Rufe mata Baki yayi Yana fadin tashi muyi sallah nagaji da tambayoyinnan domin Nima Ina karami lokacin Kuma bansan tayanda komi yafaru dangane da auransuba,sbd sedai muka ganta da baba Kuma harsuka koma ga Allah bamu tab’ajin tsakaninsuba sukadai sukasan yanda rywrsu tafara,sekuma Allah masani,kawaii dai Allah yakaimu lkc shi ze sanarda mu abnda bamu saniba,tashi kiyi sallah magriba Nima natafi masallaci.
Yamike yai waje domin shiga masallaci,se alokacin tajuyo da hoton ta tsareshi da Ido tanajin kauna tareda kewa matsananciya ta mahaifiyarta,tana kama daita kadan tawajan idanu da gira xuwa tsayinta,se gashi data dakkota,da sanyinta da miskilancinta duk na mamartane,Amma daga haka sauran duk mahaifinta tadakko,tadade tana kallan hoton tana hawaye,kana daga baya taciro xoben tabishi da Ido,Wani irin k’yalli yakeyi daga ganinshi zobene nada ajiyayye Amma Kuma beda maraba da sabo yanda yake walwali,batasn Kona meyeba kawai dai tasan zobene me asali datsada,tafiddo tasaka Adan yatsanta natsakiya,yakuwa Yi ciff kaman Dan hannun akayishi,seya K’ara haska hannun ga k’unshi da hannun be rabo dashi dama…

Daga Husnah Muhammad.

Muje zuwa…..

Plss share&
Comments..

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
SAWUN K’ADDARA.
🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈

Na Husnah Muhammad.

Sadaukarwa:gareki oum neehal, aminiyar arziki,Allah yabar tare👏👏💕💕💕.

Page16&17.

________Hutun sati 2 Yaya sagir yayi agida kana yaje Abuja wajan visa da passpor na tfyrshi,cikin 1week komai yakammala se tfy ranar Monday insha allah,zetashi ta Abuja ne,aranar juma’a yadawo gida,yadauki husnah tarakashi duk gidan ‘yan uwa da abokan ariziki yayo sallama,yabiya da ita yayo mata shopping,daganan suka wuce yawo.

Se sallar magriba suka dawo gida,nanfa ta iske hansai tacika tai fam tadinga zaginta ta uwa ta Uba tana fadin komai rintsi setasan yanda tarabata da danta kafin Shima talasheshi bare tana ganin yazama abinso gakowa da alfahari,itadai kunne ne nata kaman yanda tasaba batace mata uffanba taje tai sallah tafito D’ora sanwar dare.

Akwana2 Nan kaf suna tareda yayanta suci abinci tare sufita yawo,suzauna suyi fira,akodayaushe Yana Kara yimata naseha tareda gargadi akan tarike addininta.

Aranar lahadi dayamma yashirya komai xebi flight xuwa Abuja gobe sudaga,yarungume husnah tana kuka sosai danji take Wani kadaici nashigarta,tasaba ryw da Yaya komi ke damunta shikemata magani yau gashi gashi seta shekara2 Bata ganshiba,Kiya rayuwarta xata kasance Kuma oho!itadai gata ga Allah,sukai sallama da mama tayi shigewarta daki tana tsaki Dan ita kadai tasan metake shiryawa,komi na bukata ya Aje masu,Kuma sunada mekawo masu Sako tuni tinyana mkrnt acikin Dan alawus din dayake samu,har bakin mota tarakashi yahau tana mashi bye bye tana hawaye Shima hk.

Tahawo adaidaita sahu xuwa gida,tana sallamarshi xata shiga gida taji anwani jamata hijab tabaya,juyowa tayi dasauri danganin waye wannan,Musa (‘kwajage)kenan Wani dancikin layinsu ne irin Yan shaye shayennan,wiwi da taba duk ta xukeshi ga bakinnan Baki kirin dashi,tuntuni yake kawo mata hari akan wai Yana Santa,data fito yadinga binta kenan Yana mata mgn,to tindaga randa yayanta yaimashi kashedi yarabu daita,yau Kam ko yaga tfyr yayantane yasa,

Wata mahaukaciyar dry irintasu ta ‘yan iyawuya yayi Yana cewa “baby ya akayine harkin dawo raka’ wancan Dan yarfin ne,ai wlh kawai nakyaleshi ne sbd inasanki,kinajii kawai yanxu mushana tinda ya arce,komai kikeso xanbaki kinji tawa,kinada kyan da kowanne nmj xetashi hankalinshi akanki,hhhhhh inna sameki aina more”,

Galala tatsaya tana dubanshi,danse ayanxu tasan tayi kuskuren barin Yaya sagir yabar kasarnan,Wani irin tsaki taja kawai tafigi hijabinta tawuce,Shima biyota yayi har xauren gidan Yana Neman kamo Mata hijab,aidagudu taida shiga gidan,hansai naxaune tana cin abinci tashigo dagudunta,
“Ke ke!Mahaukaciyar banxa meyene kika fadoman gida haka sekace na ubanki”, cikin rawar Jiki
tace “wancan Dan iskanne yabiyoni Wanda Yaya yahana kulani”,kallan bakida hankali tayi mata kana tace “kina nufin me?kina nufin nixan dinga nemomaki abnda xakici Koko nice xan dafa Miki kaina kici,to tinwuri inma xaki kama irin wadannan kikama Dan wlh sune masu Baki abinci Amma badai ni hansai uwar sagiruba”,
tsaye kawai tayi tana nanata kalaman axcyrta,sosai dama shirun hansai akanta yabata mmk akwana2 Nan Dama abnd take shiryawa kenan tabdi,kafafu taja kawai tawuce daki tana Mai xubewa tareda sanya Wani kukan maraici,domin tabbas yau tasan ita marainiyace,batada gatan gaba ko baya arayuwarta,yanxu yaxatayi kafin Nanda sati Takoma mkrnta,dantasan hansai baxata Fadi abnd baxata aikataba,taci kukanta ita kadai bame lallashinta tayi shiru dankanta,
Dagasken kuwa hansai ko digon abincin dare Bata bataba,sedai Tasha ruwa takwanta,hk gari yawaye tadama kokon hansai tahanata,alokacin Kuma yunwa takeji sosai Danko gani sosai batayi,Ido tafaka tai wuff taxiri hijab tayi waje sewajan audu meshago tace Dan Allah yakira mata yayanta,

Audu yace “to bari insallami jama’a”,bayan yagama yahuyo ya cemata kiyi hkr yanxu sagir Yana wata k’asane kinjiko dole shixe kirani kana inga layinshi nacan,Amma idan Wani Abu kike bukata yace abaki komiye duk lkcn damukai waya nafada mashi,ahankali tace “to kaban biredi da lemu inkarya”, cikin tausayawa yadakko mata danshi yasan Wani abin Game daita tintana karama Tinda a unguwar yake,ta amsa tajuya,

Axauren gidan tasamu tayi maxa taci kana ta sadada tashige daki dukda Bata Wani koshiba Amma dai taji Dama Dama.
Nan Wani baccin whl yakwasheta,Tinda tin asuba take aiki har lkcn Amma abincin daxataci yagagareta,ckin baccin hansai tawatsa mata ruwa tana fadin “ubanki xedoramin abncn ranan Dakikaxo Nan kika kwanta me suffar munafukai”, firgigit tatashi tana kuka tayi waje,dakyar takammala abncn ranan nan,hk Kuma batada rabo acikinshi,ga yunwa tana kwakularta,nanma sedai tafaki Ido tafito da ‘yan kudin da yayanta yabarmata tasai taliya tadanci kana Takoma,tana komawa Musa (‘kwajage) ya Aiko kitanta Nanfa hansai ta korota tarufe gd tana fadin daga tasamu ma ya kalleta yace yanaso ai wlh irinsu ko kare bekulasu,haka tafito tana kuka,ya karaci surutunshi tayi banxa dashi tana kukanta harya gaji yatafi,
Tofah satinnan ahaka ta karasashi ckn matsi da takura ga horon yunwa,lahadi naxuwa ckn murna tayi shirinta tasamu tabar gidan yarinnan.

Hankalinta kwance amakarnta kowa Santa yake Kuma batada matsalar abinci Tinda komi Dan Aiken alhaji duk wata Yana hadamata,Dan haka ka’in da na’in suke karatu sbd karatowar exam Kuma ba Hutu amakarnta xasuyishi,matsalarta Daya Tinda yayanta yatafi so daya yakira wayar PC dinsu sukayi waya yabata hkr akan rashin kiranta dabeyiba Shima yanata uxurin hada kan komai amakarantar ne Kuma Wani xubin Kiran kin shigowa yakeyi alokacin Daya Sami dama,kamar tafada mashi abnd yafaru byn tfyrshi sekuma Taga uwafa uwace Kuma ace kullum tana Jamai xagi daga mahaifiyarshi ai batai halacciba Dan hk kawai setayi shiru,Koda yatambayeta bakomai,setace mashi eh ba matsalar komai.

To daganan harsuka fara exam Basu Kara wayaba,Suka kammala lfy Lau kowa nata murna Amma ita kunci take na komawarta gida,aranar daxasu tafi gida Yaya sagir yasamu dakyar lambar tashigo sbd mkrntar su husnah tincan tanada matsalar network sbd adaji take, Suka gaisa yaimata murnar gama mkrnta,kana yace idan Takoma gida waya Nanan xa’a kawomata,soai taji Dadi tai gdy Suka Sha fira sosai akarshe yabi da nasihar Daya Saba mata har Yana mata alkawarin Daya dawo xefara Neman dangin innarsu,tanata murna Suka rabu takaima PC wayarta.

Acan gida kuwa bayan husnah tataho mkrnta,hansai tanata tunanin hanyar daxata bi danganin sagir bedawo yataradda ita gidannanba,ta Saka wancan ta kwance wancan haka tahana kanta sakat,ahaka wata kawarta datake can bayan layinsu tasameta,suka xauna bayan taimata shimfida tabata ruwa tace
“ke hansai bar ruwannan dga binbashi Nike Kuma kinga wahalar banxa nayo ko sisi bansamoba gayau gidan ba abin sarrafawa shine nabiyo Nan indan huta” hansai tadan tabe Baki tace “uhm bari kulu ke taki matsalar karamace ni bakiga yanda nafita hayyacinaba sbd tunani”, kulu tadubeta tace yo hansai dama aihaka kike kaman andaurama muciya xani yanxuma dakikayi Kumari nibanga wata ramaba,nagadai fuskarki da alamar damuwa gashi na iske kinkasa tsaye kinkasa xaune,toma wai meye kedamunki ke? Allah yadaga yaranki duk sungirma dayama yanxu haka Yana kasar waje ai wlh innice ke yanxu sedai in wanke biyar intsoma Goma”,
Hansai tai murmushin takaici tace ” intabarni ko,inaxata barni komai yasamo ita jinin mayun,tin uwarta nadarai tagama dashi,yanxu gata itama tagallabeni narasa yanda xanyi daita”, dasauri kulu tace “wai wace haka kiketa fada banganeba kawata,ganardani”, hansai ta amsa dacewa “harkin manta da dangin alakakai Wanda bamusan Ina aka samosuba,husnah diyar maryama kishiyata”, Ido kulu tafiddo tana fadin
“kina nufin wai wannan ‘ yar mekama da aljanu tananan haryau bakisan yanda kikai daitaba,cabdi dole kike xama amatsala aini wlh Dan kishiya idanma har yaxo dnyr to badai yarayu tadadiba wlh waneshi”,
Hansai tace “danma bakisan yanda takeso tarabani da me Kashin arxikinba sagir,yanxu hk abinda Nike gudu kenan yadawo yafara aiki duk komi ya tattarashi akanta tinda sungama dashi,shine da Nike tunanin ko wancan shashashan yaron Musa kwajage dayace yanasanta idan tadawo kawai naimashi sadakarta,to Kuma tsoro Nike sagir yadawo yatadda nahadata da sakarai irin wannan wlh baxamu kwasheta tadadiba,danshi bemata lissafinma aure yanxu Wani wai tayi kankanta setayi karatu, aiyanxu andena aurar dayara ashekaru 17 kijifa hmm”,

Kulu tai Wani murmushi tace “auree tab,ai wlh inkikai mata aure to kinmanta mekyau,aikawai kisamu yaran ku daidaita hmm kawo kunnenki kiji’, Nan tamatso sukai radensu sukai dry sukai shewa,hansai tace “Kuma kinga shikenan dakafarta xata kama gabanta, inkuma taxabi hkn to inya dawo nanma jauce,heeee kawata kin iya mugunta shiyasa Nike yinki”, bayan sungama kulle kullensu tatai,itakuma tafita Neman Musa (kwajage),bayan tadawo ta iske musa nata da Usman sundawo sunacin abinci,khalifa Kam yatai balaguronshi Danshikam Dama tinda yatashi yaki mkrnta sedai fadace fadace da rashin ta Ido ita yasa gaba,allah yashirya.

Awashe garin dasukayi paper takarshe Yakama ranar asabarne,kowa nata Shirin gida,duk inda kahanga student ne keta xirga xirga,masu musayar number nayi,wasu Kuma nahada kaya,wasu na hotuna,kamar dai yanda kowanne dalibai suke kasancewa aranar karshe amakaranta,Hakan takasance da Husnah,tagama shirya komai nata Sukayi bankwana dakowa harda kawarta xaharau danse alokacin taji kewarta dantasan agida batada mebata labari hartayi dry,Dama yayantane Kuma bayanan,Danma xata koma gida yanxu tana saran xasu dinga waya dashi sosai insha Allah.

Tahada komi nata da takardunta,saura results Shima seya fito,anan Zaharau tarakota sunata sallama da mutane tahau adaidaita xuwa Tasha,

Cikin iKon Ubangiji tasauka lfy,tasamu napep xuwa gida,aikuwa tana sauka khalifa yarugo Yana “se babbar aunty allah dai yabiya”, tayi murmushinta mesanyi tana fading “yawwa khalifa,yanaga gidan arufe?Tabe Baki yayi Yana cewa “him kema dai kinsan mama da bakin yawan tsiya tana can gantalinta,Amma dai gadan makullin Dake hannuna kibude”, takarba tana fadin “halidai Nanan ko,to Allah yashirya manakai”, yajuya Yana dariya kawai,tagirgixa Kai tayi gaba.
Bayan tayi wanka tashirya,taleka kicin Taga bakomai naci,Dan haka taduba kayan cefane Taga akwai sauran najiya,Dan haka tahura wuta tadora jalop rice,harta gama hansai Bata dawo gidanba,dan haka tasanya taci kana tasanya hijabinta tafita wajan Audu meshago danya kira mata yayanta sugaisa,ta iske mutane agurin, Dan hk seda tadanjira yasallami mutane tukun.

Suka gaisa da Audu cikin mutunci tagaya mashi bukatarta,yai murmushi ya dakko wata Leda da kwalin waya yamika mata Yana fadin “ai yayankima ya hutar dake Neman wayar kiranshi yatura kudi ansai maki sabuwar waya gata seki kirashi dakanki akwai layi dakomai da lambarshi”,
Tayi faffadan murmushi tamika hannu takarba tana godiya sosai,sannan tajuya tanajin wata irin kaunar yayannata,tabbas Yaya sagir Dan halak ne,shidin dayane tamkar dadubu tana fatan duk wata kanwa tamori Yaya kamar nata,dahaka ta Isa kofar gidan,tinda Taga gidan abude gabanta yafadi,tashiga dasallamarta,hansai natsaye tarike kugu,takaraso taduka tagaisheta,tana cigaba dafadin “nadawo nataradda kinfita bayan nayi wanka shine nadora girki,abincin Nan akicin najuye akula babba……,
Tinkafin ta Ida maganar takatseta datsawa “yimin shiru munafuka,aikin dawo xaki addabi rayuwata,kike Wani sinne Kai kamar Akuyar data hangi dusa akwano,mtss, Amma ai nasan maganinki,kitashi kiban guri Kuma kishiga kifiddo kayan datti Dana Tara Miki kiwanke min Dama nadade ban wankeba”,mikewa Tayi daniyyar wucewa, Kawai ledar wayar tafado,hansai tabi ledar da Ido tana tafa hannu tana salati “meyene kika kunso kika shigo xaki wuce dashi,ni hansa’u nabani abun kunya xaki dakko min,to wlh tinwuri gara inxo innemi Wanda xerufa Miki asiri inbamawa kafin kijamin xagi”, dasauri tamika mata ledar bayan tadauko tana maifashewa dakuka tana cewa “kiyi hkr mama wlh Dama Ina niyyar fada Miki,wayace Yaya ya aikomin da ita shine nakarbo wajan Audu meshago,kingani wlh ba inda naje kiyi hkr.

Hansai tabude Ido tana fadin waya? Tabdi!Kice banyi kure ahasashe baba,wato daga dawowarki har xaki fara shiga tsakanina dashi uhmm!ita wannan wayar ta hannuna Bata isaba ko? To wlh kishirya tinkan kidawo munyi mgn da Babar wancan yaran wayake,ihin Musa dama kina dawowa xamusa biki Tinda yayarda xerufa maki asiri gara ayi Kawai kowa yahuta,anjima ma karshenta xaki ganshi Nan indai yaji dawowarki.

Wani irin Kuka tasa tana Bata hkr,tana “Dan allah kada kibanshi wlh bana sanshi ‘dan iskane kitaimaka min”, hansai tafigi ledar wayar tana cewa “iskancin ubanme yayi,ita uwarki data makalema malam bayan tagama karuwancinta Yaya yayi daita?bagashi har ta haifoki kikai ajalinshiba,Da’alla wuce kimin aikin Dana saki kafin magriba Tayi yaxo,wucewa Tayi tana gurxar Kuka,takwaso wankin taxo tafarashi tana Kuka,ga wankin dayawa danhar mangariba tanayinshi, hansai kuwa lekawa Tayi tasamu yaro ta aika majalisar su Musa(‘Kwajage)tace afadamai Husnah tadawo,lokacin aikin dasuka shirya xefara,sosai yayi kuwwa cikin abokai Yana cewa “baba ku saurara wlh nakusa angwancewa”, Suka tafa suna fadin “yaushe akaimaka baiko bamu saniba babah”, yai dryr shakiyanci Yana cewa “Asoro mana,asoro xan angwance,da nayi niyyar ruftawa tose azawanyarta tace Kawai inbula inwuce Dan itama tanan akayi ‘eee,itakanta,toshinefa xan ramama kura aniyarta”, Suka tafa suna shewa sunai maikirari da ango!Ango.

Continue to the nextpage….

Na Husnah Muhammad.

Share &
Comments.

 

SAWUN K’ADDARA.

💕💕💕💕💕😜💕💕.

Na Husnah Muhammad.

Sadaukarwa:gareki oum neehal,❤️❤️❤️.

Bismillah-hir-rahmanir Raheem.

Page 18.

_______Bayan sallar ishai Akai sallama ana Kiran Husnah,tagama sallar magriba data isha kenan hansai tashigo tana hargagi tana fadin “Bakiji anakira bane kitashi kiwuce mijinki nakira,dakuka tafito xauren tana tafiya dakyar ga yunwa na kwakularta,tana xuwa ta toge abakin k’ofar d’akin Yaya Usman dayake arufe domin Yana mkrnta,kuka kawai take,shikuma yataso Yana fadin

“haba kina aikata yawafa baby,kimatso mana mugaisa kiketa Wani togewa kaman ba mijinkiba”.
Toshe hanci tayi sbd Wani irin warin wiwi da taba Daya buge hancinta,hijabinta tasa tana toshewa,Wanda Hakan yasa yamatso Yana cewa

“kisaki jikinki baby komi yafaru ni auranki zanyi nanda lokaci kad’an,kawai kisaki jiki mushana,komi kikeso xanmiki danma yanxu cinikin abar(wiwi)yakwanta Aida kinshana”.

Yana magana Yana tangadi kaida gani abuge yake,dasauri tamatsa tana buga tsaki tana cewa “Allah yaimin tsari da aurenka,wlh gwara inmutu banyi aureba da in auri dansha irinka”,wta dariya yafara Yana cewa “yo daga taimako,waxe auri mara Asali irinki,Nima dandai inasankine sosai inaso mushana kawai shiyasa,kinada kyau dakira mejan hankali shine kawai” yafada abuge,

Kuka take sosai ya rarumota takauce ta tunkudeshi tana Mai rugawa gida,daki tashige taxube akasa tana kuka sosai gashi ta amshe wayar bare tagayama Yaya sagir,taci kukanta tagode Allah,tatashi tayi Alwala tana kaima Ubangijin talikai kukanta,tindaga ranan hansai tahanata abinci,sedai tadafa tahanata,sedai inta fakaici Ido Wani xubin tadanci atukunyar,ga matsin yunwa gana wancan Dan shaye shayen,Danko batajeba hansai seta bita daduka gashi baraxana yake mata Kullum seya runbabeta,Kuma intaje shagon Audu meshago yakira mata yayanta,seyace yakira besame Shiba takirashi awayarta mana,dole ta hkr tafawwalawa Allah al’amarinta,kawai tayima Kanta alkawari komi tsananin daxatai mata baxata bada mutuncinta ba Kuma baxata auri d’an giyaba.

ahaka taci sati ukku da dawowarta,Tana kwance bayan tagama aiki cikinta namata ciwo,Dan duk wata takanyi fama da ciwon ciki lokacin mp dinta,danma amakaranta anabata magunguna to tataho dasauran gida,sutasha tasamu takwanta ko cikin xe lafamata,tana kwance tana tunanin tsawan lokacin da Yaya sagir be nemetaba basuyi wayaba,ta tabbatar akwai dalilin Hakan,Amma komadai mene tana Maifata yakasance Yana cikin koshin lfy.

Tayi xurfi atunani taji anrufto mata daki,ba sallama bare daukar ixini,Kuma tasan mama hansai tafita tindaxu,dasauri tamike ganin ‘kwajage adakinta Yana layi alamun cikin maye yake, dakewa tayi tana fadin “meya kawoka cikin gidanmu har cikin dakinah,kawuce kafita agidannan,mashayi kawai”,

Wani kallo yabita dashi domin rigace mara nauyi ajikinta tabi talafe komi najikinta Yana kallanshi sosai,lashe Baki yayi Yana tangadi ya dunfarota Yana fadin, “bayyy nabi..bik…ki ta la..lama Amma kinki kisaurareni,to….to…yau sena…Maida miyau na…wlh,koki aureni ko karki aureni nidai sena lashi xumarki”,cikin firgici datsoro takalli kofah tana tunanin hanyar bi danta tsira da mutuncinta,dagudu tayi baya ganin Yana rarumota,tafashe dakuka sosai tana Bude murya sosai tana fadin “Ataimakeni,Wani yataimakeni Dan Allah,wayyo ataimakaman”, kuka take tana Neman dauki, Dan yakulle dakin Yana binta tana xillewa,cikin haka yasamu nasarar fixgo rigarta yayageta yabarta daga ita se vest din jikinta,ta kankame jikinta tana dunkulewa guri Daya, tana Wani irin Kuka tana Kiran Yayanta yaxo yataimaketa.

cikin rashin Imani da mugunta ya tadiyeta Yana fadin “yau xanyi mgnin taurin Kai irinnaki,Kuma kisani dasanin wannan shegiyar babartaki,tinda kinki kibarmata gida da ‘yaya toyau xanmiki abnd in yayannaki yadawo xetsaneki domin dakaina xanfada masa kekika kawo kanki gareni,Kuma bani kadai kike sauraraba.
Wani irin tsoro yadirar mata,kenan wannan Shirin Dan ahadata da yayantane,agurbata yadda Dake tsakaninsu,kullum gargadinshi gareta tarike mutuncinta,
Yafisgota Yana hadata da jikinshi da bango,cikin kuka meban tausayi tabude murya tace “Xanbarmata gidanta xantafi karabu Dani”,yakyalkyale da dry Yana fadin “idan nagama can kinfada mata”,ya hadata da bango harkanta yakume takankame guri Daya tana karanta duk wata addu’a dataxo bakinta,
Bude gidan hansai tayi itada kulu kawarta suka shigo,Jin ihunta adakin yasa kulu tace “yisauri kada yabata mana aiki kinsan ‘dan shaye shaye yanda yake bakai”, hansai tajuyo tana fadin, “wlh jinike kamar inbari ya kaddamar ma shegiyar mayya”,kallan bakida sense kulu taimata tana cewa “kina tunanin idan ya lalatata xata iya xuwa Wani gurine acikin halin,ballantana yanda yake abugennan,Kuma inbanda ke yau da gobe labarin baseya fitaba na fyade Akai mata agidanki,mexaki fadama sagir idan yatambayeki kina Ina Hakan tafaru,tin wuri kibude dakincan plan dinmu yatai yanda muka tsara”,
Aijin haka yasa hansai saurin tunkarar dakin tana turawa dakarfi,amatse da bango ta iskeshi daita tana kokuwa dashi Yana tube kaya, “Kai Kai!Musa bari inji tabakinta xata barmin rayuwa Koko seka farkemin shegiya”, aikafin takarasa Husnah Jiki nakyarma tace “xantafi wlh xantafi,kimin Rai kada yaketan haddi”, Musa dayake abuge cikin xafin Rai na shigowa dasukai adai dai lokacin ya fisgota Yana fadin “baba kufice kawai inkaddamar mata Dan…Dan..kawai layi yadibai xuwa kasa,suna ganin haka suka fisgota waje daga ita se vest da undi suka kulle dakin,anan tsakar gida tajefadda ita tana fadin “idan harkin bi umarnina xanbarki kifita gidannan batare da lahanin komaiba,saboda ba burinah kimutuba kokiyi lahani agabana tayanda wahalar xata kare Kainaba,kinsan burinah akanki”,dasauri tagirgixa Kai, hansai tabude jaka taxaro wata cover tafiddo wuka dal se kyalli take tadorata daf da wuyanta tana xaro Ido,Ai alokacin husnah batasan sanda tasaki fitsari ajikinta ba,tsabar tsoro,hansai taxaro Ido cikin rashin Imani tace
“kinga idan kika tsallake sharuddana wlh sena yankaki,bayan nahadaki da samarin layinnan sunmin kaca-kaca Dake,kibude kunnenki dakyau ki saurari bayaninah yanda xexauna a kwakwalwarki dakyau,
Ayau inaso kibarmin gida,kibarmin iyali,kifita arayuwar duk Wani ahali nawa,Ina nufin hada ‘yayan Dana haifa,ko ahanya kika hadu dasu kika nuna kintaba ganinsu wlh kika dawo gidannan sena kasheki Kuma kinsan zaniya,haka Kuma sagir Koda wasa kika Kara tunashi bare kiyi tunanin kiranshi wlh yadawo Dake gidannan sena tsinemai Kuma na salwantar da rayuwarki,
Kibace batt daga garinnan, kekusa Danan ma banaso najiki kitai can kikama rayuwarki,kinemi dangin uwarki mayu kixauna acikinsu,to idan kikai haka kin kib’uta daga sharrina,kinajinah! Wlh kika K’ara yowa wannan yankin”,tadanna wukar awuyanta tacigaba dafadin “da ita zanyankaki”,

Iyaka tsorata tagama yinta,domin tayi sharkaf da xufa,ba abinda take se d’aga Kai kaman kad’angaruwa,hansai ta hankadata gefe tana fadin “zanmiki adalcin dare ya Ida tinda yanxu sallar magriba akafara,kiwuce kihada ‘yankomacanki munafuka kawai,Salon kifita Yanzu ace Nina koroki”.

Dasauri ta rarrafa dakin bayan sunbude mashayin da bacci yake ashe anan Suka janyoshi har dakin soro suna fadin “kafin wawan yatashi tabar masu gidan”,

Wani irin Kuka take tana daukar ‘yan kayanta tana sawa awata jaka,duk Wani Abu me amfani seda tad’auka,tana Mai tuna kalaman yayanta agareta, tabbas gara tatafi,tazabi Hakan data karya alkawarin dataimai,Kuma baxata bari tasilarta atsinema yayantaba,bayan duk gwagwarmayar dayasha akanta.

Tabbas shid’in abin tunawa arayuwarta ne Kuma baxata denamai addu’a ba aduk inda take,akarshe tayima kanta ALKAWARI baxata Kara waiwayar wannan ahalinba,zata gogesu arayuwarta,itama zata shiga takunga aduk inda akeneman kud’i dan tayi ilimi tazama abin dogaro dakanta,akarshe tanemi duk inda danginta suke domin Jin Dalilin banzatar mata da uwa dasukayi.

Cikin irin wadannan tunanikan tadauki duk Wani Abu nata,zobenta na hannunta,haka hoton mamarta da Yaya yabata tasakeshi akugunta,alokacin har ishai tagota,hansai tashigo tana sababi da fixgarta,haka tayimata korar kare.

Tafito gidan dawata irin bushewar zcy,alokacin yaya Usman Yana makaranta Musa ma haka, shi se wannan shekarar zegama secondary school,
Dalilin haka yasa bawanda yasan Asalin meya fitar da ita,Aikuwa cikin bak’ar xuciya tafita gidan,tanajin aranta basauran Dalilin daxe Kara maidota cikinshi.
Ta Miki hanya tana Jan wata ajiyar xcy Dan alokacin ko tsoron bataji,burinta kawai tabar area gabadaya tanufi duk inda ‘kaddara xakuma tajefata, tanajin komiye yatunkarota alokacin to xata karbeshi da hannu biyu Dan tallafama tata rayuwar.

Tafiya kawai take batamasan inda take jefa kafartaba,dahaka harta fita unguwarsu tamiki titi kawai tana tafiyar daba tasan inda tanufaba,seda tai tfyr kusan 2hr kana tadaukema sawun mutane,alokacinne Kuma garin yadau Wani duhu ga cida anayi alamun haduwar hadari,
tsayawa tayi cakk Jin alamun motsi,wasu gungun matasa ne suka keto hanyar ga wukake ahannunsu alamar dai wata wani gurin suka fito kokuma xasu,harta juya baya daniyyar boyewa suka hango kamar mutum,aikuwa Daya yakware Baki Yana fadin “ubanwaye Nan yake tunkaromu”, aijin haka tarike Jakarta dakyau tana yin baya, “Daya daga cikinsu ne yace “kukamo kowaye Dan ubanshi”,
Aitanajin haka tayanki daji dagudu tana mejin tsoro nashigarta,suka rufa mata baya,gudu take sosai harbatasan inda take jefa kafartaba,hartadan samu tayi musu nisa Amma Bata tsagaitaba tana danke da Jakarta Kaman ita akace xa’a kwace mata,seda tayi nisa sosai kana taji tasare alamun Bata iya cigaba da gudun,Dan haka tatsaya Kawai taci gaba dajan kafa tana waige,duk da batajin alamunsu Amma atsorace take ainun.

Abangaren su kuwa ganin sunyi nisa Basu cinmataba,Kuma iya duba sun duba ko Ina Amma Basu ga kowaye ba, Hakan yasa sukai tunanin juyawa musamman dasukaji garin nata hada cida Yana murtukewa,Dan hk sukayi baya suna Fadin “kowaye dasauran Shan iskarshi aduniya”,
Adaidai lokacin kuma iska tataso gari yahade da gurinniya,alamar ruwa naiya sauka akowanne lkc,
Abangarenta kuwa Jin tagaji da tfyr yasa tadurkushe adaidai wata ringijejiyar bishiya tanamai dunkule jikinta guri D’aya tana risgar kuka maiban tausayi, tadaga hannuwanta ixuwa sama tanamai Kai kukanta ga Ubangijin talikai.

“Ya Allah ga baiwarka Nan agareka,kafini sanin faruwar wannan jarabawa agareni domin daga gareka ne,ya Ubangiji Gani gareka,kanunan hanyar mafita ga wannan jarabawar,kasa duk inda nadosa yafiye min alkhairi akan inda nabaro,kabani farinciki ko yayane awannan duniyar mecike da abin tsoro da wahalhalu iri-iri,Ina tuba agareka ya Ubangijina”, takarasa dawani sautin kuka Jin ruwan sama yasauka dakarfin gaske.

 

Wannan shine mafarin k’addarar data fiddota daga gida,gashi tahadu dawata k’addarar,ko’ina rayuwa zata cillata,Kuma Ina zata Nemo mutumin da batasan Inda yakeba,afadin duniyarnan.

Seku biyoni danjin yanda zata kasance,
Taku har Kullum,maikaunar sakaku nishad’i tareda fad’akar daku
Husnah Muhammad.

Plss share &
Comments….

Allah kajikan iyayenmu da rahma.

❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️
SAWUN K’ADDARA
💕💕💕💕💕💕💕💕💕

Na Husnah Muhammad

Page 19&20.

CIGABAN LABARI.

__________Koda husnah ta juya harta fara gudu sosai,se kuma Wani tunani yaxo mata,Dan tabbas tasan xasu bibiyeta idan harsuka ritsashi Basu samu abnda suke nemaba daga gareshi,Kuma tasan idan har suka biyota tofa batada karfin tsere masu,Dan dagajin takunsu ba ‘kananun axxalumai bane,Kuma tabbas idan suka kamata itama xasu kashetane su d’auki abnda suke bibiya,
To dawannan tunanin tahangi,Wani babban dutse dawani Rami yashata ta tsakiyarshi,nesa kadan dagurin data baro,Batayi Wani dogon tunaniba takarasa gurin dutsen,seta iske ashema barami bane Wani irin kologo ne kaman angina acikin dutsen,Dan hk kawai tayi Bismillah tashige tana cusa kanta ciki duk duhun Dake cikin yayi shahada kawai talab’e aciki tanamai toshe bakinta da rage numfashi,

Can kamar minti talatin taji alamun sawun mutane alamun anbiyota,aikuwa takara lafewa ciki tana dauke numfashi,harkusa dadutse sukaxo sukayi lalibensu Allah bebasu iKon shiga cikiba,haka suka juya suka koma,bayan Wani Dan lokaci haka,tafito tana tunanin suntafi,Dan lokacin hasken asuba yakunno Kai,ahankali take tafiya,dab daxata fita dutsen tahangi wasu gungun mutum hudu masu bakaken kaya sedaya dashadda ajikinshi,duk da yayi k’ura jikinshi da alamun shaddar maitsada ce,D’aya acikinsu ya ratayo wannan mutumin Daya Bata amanah awuya k’afufunshi se reto suke tabayanshi,alamun sun kasheshi.

tsak! tatsaya jikinta nawani irin rawa tatoshe bakinta tadauke numfashi kana taduke,daidai lokacin meshaddar yatsaya yajuyo Yana Fadin “kokuma kubinne minshi anan,muyi sauri muk’arasa wajan motarmu ko mun samu mufita titi,shashasha yarasa rywrshi abanza,mtss”,
Ta ‘yark’ofar cikin dutsen take iya Hangen fuskar meshaddar,sosai tak’aremai kallo tana makyarkyata da rawar tsoro,akan idonta suka binne wannan gawar,kana suka juya.

Suna juyawa harsun fara tafiya,irin karnukannan Dake fita yawan dare suka fara juyowa domin dawowa gida wato xasu nufi cikin gari daga dawa,
D’aya daga cikin karnukan Ashe Yana kwance ckin kologon dutsen data l’abe aikuwa yanayin gurnani tajuya taganshi batasan lokacin data fito dagudu tana fasa karaba,karaf se’a kunnansu suka juyo domin Jin murya kaman ta mace,

Ko waige batayiba ta zunduma da Wani irin masifaffen gudu har tana hard’ewa,aikuwa Jin takun gudu suma wad’annan majiya karfi suka juyo danasu Dan ganin waye,batayi Wani nisa sosaiba taci karo dawata gada da ruwa ke wucewa aduk lokacin damina,dama ga ruwan da aka lafta Adaren jiya Dan haka ruwane kegudu kaman ‘dam’ din Daya balle,
Aikuwa cikin rashin sani da tsautsayi taruftama gadar.
Fanjamm!Haka kakejin k’arar fad’awarta ruwan.
Gaba D’aya Suma sedai sukai rivers abakin gadar,sukai tsaye suna me kallan yanda ruwan kegudu kamar ana hankad’oshi,meshaddar cikinsu ne yaja tsaki Yana fad’in “idanma Wanda yataimakeshi ne Shima yataradda nashi ajalin,Dan wannan ruwan badai mutum yaficeshiba,sedai afidda gawarshi,kumuje kawai,Koba komai yanda narasa to kowama yarasa”,
Dawannan suka juya suka kama gabansu,

Al’amarin husnah kuwa,wannan gada data tsinci kanta aciki,wata irin doguwar gadace data shata tsakanin manyan daxuxxuka,asalin gadar wasu turawane suka yita awasu shekaru can dasuka gabata, dalilin xuwansu Wani bincike afannin daxuka,domin masana tarihin wannan guri sun tabbatar dacewa,tsawan gadar seda yakai mikakkiyar tafiyar kilo metre(80)domin gadar seda taketa dajin Nasarawa har tashiga na Jibiya,anan ne Ainihin wata babbar ganuwa da tsauni suka Yanke gadar,
Tofah seda husnah tawuni acikin gadar,ruwa najanta kana takawo wannan ganuwar dagadar tatsaya,cikin iKon Ubangiji Wani babban dutse ya tareta ta mak’ale ajikinshi ad’an gefen ruwan,ahaka duhun magriba yafara tana agefen ruwan kaman matacciya,ba alamar numfashi atare daita,

Acan Wani d’an yanki na dajin,Dake kusa daruwan,akwai Wata tsohuwar fadama wadda Tayi shekaru dadama har yakaiga tacinye kanta tadena tsiro sbd Wani rashin ruwa dayankin yatab’a samu,seya kasance wasu makiyaya da maharba kiwo yatab’a kaisu gurin harsuka gano wannan fadama,to adatsin anyi fama dayunwa inji magabata,shiyasa mutane suka fara sassak’o wad’annan itace domin shiga dasu birane inda Ake wahalar abin wuta suna saidawa,dansu Sami rufin asiri,to dahaka gurin yaxama kamar kasuwar Icce,mutum Yana iya xuwa yakada bishiya yasara yayanka,yakasama manyan motocin dasuke xuwa sari,sushiga gari susaida.

Ayau ma wata akori kura tayanko hanyar dajin Dan d’aukar Icce domin fita dashi cikin gari,Wani d’an dattijo shine matukin motar,se yaran motar masu taimaka Mai su2,tin hantsi suka taho Amma yanayin hanya mara kyau gakuma MOTA Dama tsohuwa,Hakan yasa suka dinga tsaye tsaye Basu samu isowaba har duhun magariba ya ritsasu,
Koda suka iso sungaji tib’is Dan haka kowa yasamu gurin Hutu,gashi suntadda masu tsaran gurin sund’an matsa sallah,dattijan cikinsu yace ma D’aya daga cikin yaranshi “kuduba Kuga muna da sauran ruwa ajarka muyi sallah Muma”, D’aya acikinsu yanufi motar yaduba,Koda yaduba yaga Babu seya dauki jarkar Yana fad’in
“oga Babu bari ind’ebo atafkincan”, sunriga sun Saba xuwa dama,Kuma Wani xubin sukan d’anje Debo ruwa randa na motarsu yak’are,
Yauma kamar Kullum yanufi hanyar gurin Yana me fiddo ‘yar k’aramar wayarshi Dan haskawa sbd duhu yafara,har yakai gurin yad’ebi ruwan yasha,yad’an matsa gefe kadan danyin fitsari yayi alwala,Yana duk’awa kenan yaji yataka Wani Abu kaman Icce,wayarshi ya lalibo yakunna fitila ya haska,

Wani irin tsalle yadaka ganin kamar suffar mutum akwance gagashi yalullub’e fuskarta alamar mace,Aiwani ihu Daya kwarara seda duk nakusa dashi suka jiyoshi,yajuya dagudu da xariyar Wando tana Lilo,tinkafin yaisa garesu suka iso wajanshi sbd Jiyo ihunshi dasukai,dattijon ciki yarik’eshi ganin yanda jikinshi kerawa,Yana fad’in “Kai isah,meye yafaru? Natsu kafad’amin Meka Gani kake wannan ihun”,
Cikin rawar Jiki isah yace “baba Aljana nagani wlh yanxu Abakin ruwa”, baba yad’anyi dariya ganin yanda isah ke firfito da Ido Yana mgn, “kodai tsorata kayi Amma wace Aljana xakagani Kuma tabarka lfy,

“Wlh dagaske nake inkuna tantama kuje kuduba Kugani Kuma,Tananan kwance wajan dutsen bakin ruwan”.
Baba yakalli d’ayan yaranshi da metsaron fadamar yace
“kumuje muduba Allah yasa ba gamo isah yayiba”, nanfa suka rankaya suka nufi gab’ar ruwa kowa tsoro fal afuskarshi,Koda suka Isa wajan isah Yana can daga bayansu yanuna saitin dasuka ganta,aikuwa da sand’a suka lsa wajan kowa na addu’a abakinshi,
“Ilai kuwa”,sani yafad’i Yana me yin baya dagudu,”wallahi aljannace haryanxu tananan wayyo munyi gamo”, haka sani yaruga baya Yana fad’a,shikuwa baba Dayake bayaro bane tsaye yayi Yana dubanta,tareda hasashen abinda yake tunanin xe iya faruwa,Dan tabbas wannan ba aljana bace,Dan haka yayi Bismillah yataka xuwa gareta,yaduka gefe kad’an Yana me dangwalar hannunta kad’an,nanfa yaji Wani irin sanyi ahannun kamar yatab’a k’ank’ara,nandanan yafahimci abinda kefaruwa,cikin sauri yad’aga murya Yana fad’in “Kai kuxo wlh mutumce ba aljanaba,kuxo muyi cetan Allah da annabi”,sunajin haka suka firfito daga inda suka lab’e sunamai fad’in “baba kaduba dakyau kuwa?”.

Tsaki baba yaja yana cewa “kudai mutanen banxa ne wlh,kumatso kukamata mufiddata wlh mutumce ga alama Nan daga tab’a hannunta,haba me Ake da tsoro irin naku”, Jin baba yadage da fad’a yasa suka marmatso kusa,nanfa baba yamirginota ainihin kyakkyawar fuskarta tabayyana,sedai jikinta yad’auki Wani irin sanyi dataushi,tayanda baxaka Gane akwai numfashi atare daitaba,
Cikin sauri baba yafiddota daga cikin tab’on,yajanyota gefe Yana matsar da gashin sosai,kana yacema isah “d’auketa muk’arasa fadamai”,
Cikin sauri-sauri suka iso fadama da ita,baba liti,ya tsuguna yafara fidda ruwan Dake cikinta tahanyar danna cikin,kana ya umarci su isah dasu had’amai wuta sosai,seda baba liti yakai kusan 30min Yana fidda ruwan cikinta sannan yajanyo buxun da aka shimfid’eta Akai xuwa wajan wutar data keci sosai kaman xa’adafa Naman Kai na wata shanuwa, cikin hikima irinta tsaffi baba yad’an yayyaga wasu buhuna da ganyaye yaxagayeta dasu domin dumin wutar yashigeta sosai,sannan suka barta aciki suka fita Dan samun mafita domin dare yafara Yi sosai.

Nanfa baba yatambayi metsaron gurin ba inda xasu Sami ruga nankusa wadda xa’a tatsi nonon shanuwa med’umi,ma’ana tatsar yanxu,
Jatau metsaran fadama yayi shiru xuwa Wani lokaci kana yace “eh to,akwai wata ruga acan kan hanyarku takomawa,Amma kafinnan inaxaku Kai iccen?
“Eh to Wani d’angari ne kusada HIRJI,to anan xamu saukema me Iccen abinshi,Amma inane rugar Dakake fad’i?”.

Jatau yacema baba “to gsky sedai kucanxa hanya Dan rugar Bata hanyar Dakukaxo takeba tawani d’an labine Daya Yanke dagacan kudu da firoja tawannan fadama,Amma fa hanyar bakyau Dan har gara wadda kuka biyo wajan xuwa,Amma itama dakunje rugar akwai hanya nanan tayamma,xata idasa kaiku har HIRJI,
Baba yajinjina Kai yace “ba matsala ai taimako ne bari muga farfad’owarta inda rabo,semuje tacand’in,dahaka kowa yamik’e yayi sallah bayan sund’an lek’ata.

Husnah Kam har tsakiyar dare Bata farkaba,sedai alokacin sanyi jikinta yaragu har jikinta yadau d’umi kad’an Kuma fatarta tad’anyi karfi kad’an alamar tana dawowa cikin yanayin Daya kamata,tun suna saran farkawarta domin sutafi daganan sunemar mata mgnin sanyin Dake jikinta,kafin sushiga gari,har suka fara gyangyad’i wasuma suka b’ingire barci.

Secan gabannin Asuba tayi Wani irin tari da Atishawa Wanda yai sanadiyyar farkawarsu,cikin sauri baba yafito daga ‘yar bukkar gurin dasuke kwance yanufi d’an tantin dayayi mata,yasauke buhunan yalek’a yaganta akwance tana Atishawa da tari,Wata irin majina nafita tahancinta,ganin haka yasa baba yadubi sauran daduka fito yace”dole Muna buk’atar Abu med’umi Wanda xe gasa cikinta tinda sanyin fatar yafita,domin sanyin cikinta Yana iya haifar da matsala acikinta kokuma yasaukar mata da neumonia(Lamoniya)”,

Dasauri jatau yace “inada butar shayi bari ad’an dafa mata dawani magani Wanda yashafi irin wannan matsalar,insha Allahu indai tashashi garau xata mik’e,sedai kuk’ara mata da abinda baxa’a rasaba”,
Baba liti yace “to hanxarta Dan Allah bari indubata,Kukuma kufara yimana Lodi,munayin asuba muwuce tinda tamaro,aikunga xama beganmuba”, Aikuwa kafin kaceme tuni sunfara Loda itace amotarsu,shikuma jatau yahad’a d’an murhu yad’ora butar shayi.

Baba kuwa Koda yashiga,yunk’urata xaune yayi Yana bubbuga bayanta har tarin yalafa tukunna,Takoma lagwab takwanta tana k’okarin bud’e idonta,”sannu kinji yarinya”,

Baba yace mata,Batako kalli inda yakeba illa rawar sanyi data kama,ganin haka yasa baba yad’an tab’a gefen rigarta danjin ko suturar jikinta tabushe,tinda macece basuda hurumin cire mata kaya,shiyasa Koda suka hura wutar suka ajiyeta da kayanta,Jin kayan sunbushe yasa baba mik’ewa Yana tambayar jatau haryau shayin behad’uba,
Jatau ya iso da d’an kofin k’arfe ahannunshi Yana fad’in “gashi dama Ina Shirin mik’owane”, baba ya amsa yajuyo gareta,Yana fad’in “sannu kinji tashi Kisha wannan zazzab’in zelafa dayardar Allah”.

cikin rawar sanyin tamik’e dak’yar baba yakamata tazauna,yakafa mata abaki tafara Sha,tinda takafa Kai Bata d’agoba seda takusa shanyewa Shima baba liti ne yajanye Yana cewa “Sha ahankali kada kicika Kuma kiharar,aikafinma yarufe Baki Wani yunk’urin amai yataso mata,Nanfa tafara amai sosai tana kakari,kaff shayinnan seda tamaidoshi harda ‘dan sauran ruwan Dake cikinta,dan rabanta da abinci tin shekaran jiya kafin tafito gida data gama narana tad’ansamu ta eba taci kafin hansai tadawo,seda aman yad’an lafa kana yabata ruwa tad’auraye bakin,Takoma tai lagaf daita,Amma setaji tadena rawar sanyin zazzab’in har tad’anyi zufa ma,
Seda tad’an huta kana baba yabata d’ansauran yace tashanye,ta amsa ahankali hannunta narawa Tasha,
Baba yjuyo wajansu isah yace “tana buk’atar taci Wani Abu dan tasami k’arfi ajikinta,Dan haka idan kungama lodin kumuje muyi Sallah, muyi Haramar tfy.

Dahaka suka juya kowa yayi alwala yayi sallah,sukasha shayin da jatau yahad’a masu suka fara shiri,seda suka kammala komi na motarsu kana baba liti yazo gurinta,Tananan yanda take akwance,ta k’adandane da Wani malullub’i data Gani akusa daita,baba yazo yatada ita Yana fad’in ‘yata taso mutafi,idan muka shiga gari se anema maki kaya kicanxa ko,
Ai tanajin baba yace kaya tatuna da abinda yafaru,fess komai yadawo mata,cikin d’ank’arfin data samu takai hannunta tana lalibo gajeran wandan jikinta,danjin Amanar data amso,wadda itace silar k’ara shigarta wannan halin,
Cikin iKon Allah taji d’antudun akwakunta da d’aurin Dake k’ugunta yananan,taduba yatsanta nanma xobenta Nanan Daram,Tabbas iKon Ubangiji yawuce tunanin me tunani,Dan haka tayima Allah gdy tayunk’ura tanajin k’arfi kad’an ajikinta danjin wannan akwaku datayi.

Seda baba yakamata ta iya tfy,jatau me fadama yabata Wani d’an malullub’i tayafama kanta,yak’ara Bata wannan shayin mehad’in magani Tasha,sannan sukaimai gdy suka hau motar Icce,su isah suka hau baya kan itace,ita Kuma baba yakamata tahau gaba,sannan yashiga yatada,sukaima juna sallama sunamai cemai “sekuma sunjuyo d’aukar Wani Iccen idan anbasu kwangikar hkan,jatau yace musu “to Allah yabaku ladan taimako,Kuma idan taji Dama kusadata da danginta,kuimasu bayanin abnd yasameta,Allah yatsare,kunga hanyar daxaku binan”, yak’are mgnr Yana nuna masu Wata ‘yar xiririyar hanya,
Baba yajuya kan mota sukayi wajan suna gdy,
Tose muce baba Allah yatsare,

Watoh seda subaba suka biyo wannan hanyar suka tabbatar dacewa waccan hanyar akwalta suke,dansam batada alamar kyau,seda sukakai kusan la’asar suka samu sannan suka fara hango bukkokin fulanin rugar da aka kwatanta masu,alokacin duk sun galabaita,ga ragargaxar mota gata yunwa,danma sunsamu irin manyan bishiyoyin Nan ahanya,na mangoro, ayaba,dasauranku,Dan haka sukad’an tsinka suka Sha,Husnah Kam kasa Sha tayi sedai ruwa,wannan yasa taida galabaita,xaxxab’i yarufeta ruf,
Koda suka k’arasa sukai fakin,sakkowa sukayi,baba yakamo husna alokacin ko tsayuwar kirki Bata iyawa,haka suka isko wata majalisa suka k’arasa baba yayi masu sallama,suka amsa suna Mai tsaresu da Ido, baba yajinginata da bishiya axaune, kana suka gaisa,yaimusu bayanin abinda ketafe dasu,yak’ara dacewa,”Dan Allah kutaimakemu tana buk’atar taimako sosai”.

Kuci gaba da bina,
danjin yanda zata kasance,

Yanxuma aka fara.

Husnah Muhammad.

Share & comments.

SAWUN K’ADDARA.
Na
Husnah Muhammad.

Sadaukarwa ga:Oum Nihal Alkhairin Allah ya isar maki🌹❤

Page 21&22

Bismillahir Rahmanir Rahim.

_________Ɗaya daga cikin fulanin Dake majalisar ne ya mik’e Yana fad’in “ku biyoni muje gidana,insha Allah zamu taimake ta”,ya fad’a cikin hausar sa irin ta fulani mazauna dawa,baba yakamata suka wuce,suka d’an tsaya gefe shikuma yawuce zuwa tsakar gidan da bukkoki sukaima k’awanya,
“Jammade!Jammade”,Ard’o ya ƙwalama uwargidansa kira,tafito cikin sauri tana fad’in “na’am,Ina madafa ne Ina damun fura,domin fito muku da ita majalisa”, Ard’o ya jinjina Kai Yana cewa”yawwa to shikenan ma,Dama bak’i mukayi,suna tafe da wata yarinya da suka tsinto acan kogin fadama,dan haka ga sunan zasu shigo,aimusu tarba,abasu damu su samu su sha,nibari infita dawa inhad’o mata magani,domin da Alama Tasha ruwa sosai”.
Jammade ta rusuna ta amsa da “to adawo lfy,uba ga wannan ruga”,
Ard’o yajuya domin shigo dasu,ya isa ga baba liti Yana fad’in “Bismillah ku shigo,kamata, mai d’akina na nan zata amsheta,Kukuma bari in turo muku jarmai ya kaiku kuyi sallah,inna dawo saimu zanta”.
Da haka Ard’o ya wuce ya nufi bayan bukkokinsu Dan had’o mata magani.

Koda suka shiga,cikin mutunci Matan gidan suka karb’eta bayan sun gaisa,jammade ta tallabeta suka shiga ciki,alokacin jarmai yashigo da k’ok’o ahannunsa wanda Ard’o yasa yayo sabuwar ta tsar nonon wata shanuwa da ba’a ta tsaba da safe,ya mik’o ma jammade,kana yacema su baba,”baffah muje kuyi sallah”.
Suka juya atare suka fita,dan nufar masallaci,

Acan d’aki kuwa sai da jammade ta zaunar da ita kana tayi mata shimfid’a ta maidata akai,ta d’auko wannan nonon mai d’umi ta juyo gareta takafa mata abaki tana fad’in “maza Sha kinji ‘yata,maganine ga duk wata lalura Dake jikin d’an Adam,musamman ke dakika shak’i ruwa,duk Wani sanyin Daya shigeki yanzu zai fita insha Allah”, ahankali Husnah ta bud’e bakin ta fara zuk’a Dan raban cikinta da abinci yau kusan kwana2 kenan,sai da ta zuk’i me yawan gaske,jammade naduk’e takafa mata abaki Kuma Bata hanataba,
Aikuwa Bata saki ba sai da taji Wani amai nata so mata,nan da nan tafara shek’ashi tabaka data hanci,wata irin guda-gudar majina tarik’a fiddawa hanci dabaki,har ta amayar daduk Wani guba Dake cikinta tas,kana ta koma lagaf jikin matar Ard’o,ita kuwa jammade farin ciki tayi dawannan aman,dantasan cutace tafidda musammna sanyin data shak’a dakuma yunwar data dad’e daita,seta tagama kana takamta takaita bayi tatsugunar,taxo tahad’a ruwa mexafin gaske,takai bayin,tad’auko soso sabo na buhu da sabulu kana tashigo bayin,tazo xata fara cire mata kaya,nanfa husnah tak’i tarik’e rigarta tana girgixa Kai alamun bataso,jammade tarik’eta sosai tana fad’in yahakuri kinji ‘yata,wanka zan miki kiji dad’in jikinki,
Girgiza Kai tayi Ahankali tabud’e Baki karo na farko tayi magn tace “zanyi da ka ina”,
Jammade tarike Baki tana cewa “keko yaushe kike da k’arfin yin wanka,kibari nacud’aki to seki k’arasa sauran kinji”,. Shiru tayi kawai amma tarik’e wajan wandanta daidau k’ullin Nan na Amanar data d’auko.
Jammade taja rigar ta cire mata,ta barta dad’an gajeran wandanta,tacud’a mata jikinta sosai ta gasa mata shi da ruwan zafi,ta wanke hada kanta daduk k’asar lakace aciki,sannan tafita tace ta Idasa to tana bakin k’ofa,dak’yar husnah ta zame Wandan tad’auraye jikinta tayi tsarki sosai,sannan ta yadda fant d’in ta maida gajeran wandanta,taname mamakin Ina jinin datake yayi,dantasan randa tabaro gida shi takeyi.
Tana maidawa jammade tashigo,dawani ruwan ad’an k’aramin botiki,da wani k’ullin magani ta mik’a mata tana cewa tazuba maganin ciki Tai wanka,sannan ta juya,
Aikuwa tana juyawa ta Yi wankan tsarkinta daruwan kana ta rage kad’an tasa maganin tagama ta mik’e tana dafa bango,sosai taji k’arfin jikinta,Bata dad’e atsayeba jammade tashigo da zani gyauto tabud’eshi tad’aura mata Suka fita,sadda Suka shiga d’aki,ta iske anshinfid’a mata sallaya da Wani gyauton irinna fulani dantayi sallah,haka tamik’o mata kaya na budurwa irin doguqar rigar fulani,tataimaka mata tasa,sannan tazaunar daita bakin gadon k’arfe tamik’o mata fura damamma tanata k’anshin nono,ta amsa tana Mai cewa “nagode Allah yasaka da Alkairi”,
“Bakomai Kisha kisamu d’ank’arfi kirama sallolin dake kanki”,
Ahankali ta dinga Sha,hartasha sosai,seda taji tak’oshi sannan tamik’a mata Tasha ruwan Dake kusa daita,ta tada sallah.
Sai da ta rama duka sallolin dake kanta azaune,sannan tayi istigari,tareda yima rayuwarta addu’ar makoma tagari,sannan ak’arshe tayima Yayanta abin tunawarta Addu’a tana ayyanawa aranta,yanzu koyasan Bata gida,Koko bai san abinda ke faruwa ba,Allah masani,itadai tayi Alk’awari aduk inda take,Kuma akowanne yanayi,zata cigaba dayi mai Addu’a tare da fata nagari,tanasan Yayanta sosai dominshi bangone agareta,cikin haka ta fashe dawani irin kuka mai tsuma zuciya,tana me fiddo d’ankullin Dake gefen wandanta,tafiddo hoton innarta data k’ulle tinkan tafito gida,ta bud’eshi Taga duk yayi jirwayin ruwa,ammadai and’an ganin fuskar kad’an,danse Wanda yariga yasanta zai sheda itace,ta kallu zoben hannunta dayaketa k’yalli tafashe da kuka ta rungume hoton tana Mai sambatu tana
cewa “inama nice yau’ a hoton nan,Wani ke kallo dantunawa Dani,inna Dana huta da wahalhalun wannan duniyar da bawani Armashi acikinta,meyasa kikatai kika barni ni k’ad’ai awannan duniyar,inna haryau banji dad’iba irin Wanda kowacce ‘ya yakamata tasamu,bansan Koda rarrashi irin na uwaba,balle akaiga d’uminta,yayana kawai nasani Shima Kuma ayau nayi nesa da……”

Jin antab’ata daga baya yasa tayi saurin d’agowa ta juyo,jammade ce ta rungumota tabaya tana fad’in “Gawata uwar muddin kina maraba Dani,zan zameki uwa agareki Mai share hawayenki,Mai tattashinki tareda d’aukar ragamarki,shin kin amsheni?”,
Kuka sosai takeyi itama ta rungumeta tana cewa”ko mahaukaciya nasamu atiti tayimun alfarmar zama uwa tabbas zanbita kwararo-kwararo Dan amsa sunan d’iyatta,bare Kuma uwa irinki,wadda ta runguman acikin yanayi narai ko mutuwa,tawankeni daga dattin daud’a da laka,tabbas ked’in uwace agareni Koda bamu rayu tareba,nakarb’eki babata”.
Tak’arasa tana kukan Dake Nuna xallar maraicinta afili,
“Jammade! Kiran Ard’o ya datsesu daga koke-koken da suke,ta mik’e tanamai kwantar daita kana tafito tana amsawa,
“Kifito da ita suyi sallama zasu wucene,munyi dasu zasu barta nan harta samu sauk’i garas,sai musan yanda zamu lalubi mahaifarta idan sun dawo,sunce Acan k’auyen gyad’i suke yamma da hirji,
“To malam ina zuwa da ita yanzu”, ta amsa tana juyawa d’aki,Koda suka fito,baba liti ya dubeta yaga tawartsake sai k’arashe,nan take fara’a ta bayyana afuskarshi yawashe Baki Yana fad’in “A’a ‘yata Anji sauk’i ko,lallai Ard’on wannan ruga kayi babban jahadi,Muna gdy sosai”.

Ta matso ta duk’a ta gaishe da baban tayi mai godiya ya amsa da fara’arshi sannan yace” to mun riga munzanta da limami Kuma shugaba na wannan ruga Mai albarka,zamu barki anan kik’arasa murmurewa agurinsu,tindasu Allah yaimusu sanin magunguna kala-kala,kinga ko yanzu daga d’azu zuwa yanzu harkin samu k’arfi ajikinki,Amma kinsan Sha’ani na ruwa,akwai lakk’una atare da masu zama acikinshi,to gudun matsala daga garesu dole abaki na kariya da wanka,
Dan haka nanda kwana2 zandawo mu shawarta,insha Allahu nida kaina zan maida ke har garinku ga iyayenki,Allah yakyauta gaba”,
Ai jin yace da kanshi zai maidata gida,Nan Danan taji gabanta ya fad’i,ta Ayyana aranta cewa tabbas Nan ba gurin zamanta bane indai har suka dage sai sun Maidata Asalinta,Dan haka cikin sanyin jiki Tayi musu godiya harda d’an hawayenta,su isah ma suka juya suna bye bye,har isah na Ayyana wa aranshi k’ila yaga mata,irin wannan ziza haka,da haka suka juya gudun dare ya ida yimusu arugar,
Sai da suka ga tashin baba liti kana umma Jammade ta rik’eta suka koma ciki,ta zubo mata tuwan Masara lafiyayye da miyar kubewa d’anya,ga man shanu agefe,aikuwa har sauri take tasa hannu,domin raban ta da samun wannan gatan tin kafin yayanta yatai makaranta,sosai taci tuwan Nan,sannan cikin yanayinta na natsuwa tad’ago Kai taga umma Jammade ta zuba mata Ido Ashe tinfara cin abincinta,Dan haka taji wata irin kunya tarufeta,Ahankali tabud’e Baki tace “kiyi hak’uri umma”,
“Hak’uri name ‘yata?nanfa d’akin innarki ne,kisaki jiki komi kiyishi tamkar agida kike kinjiko”,
Tad’aga Kai hawaye nacika idanta,umma Jammade tamik’ar da ita tace “muje kiwanko hannu muyi sallar ishai ki kwanta ki huta,Kuma ga magani Nan malam yace ajik’a kidinga Sha,d’ayan Kuma kici gaba dawanka”, “to”, ta amsa ta name godiya tafita,
Sai da suka gama komai kana umma Jammade,ta kamata tad’orata agado,ta zauna gefenta tana Mai d’an bubbuga bayanta,
Zuwa can kamar bazata ce komaiba,sai kuma tad’an dubeta tana cewa “Asama’ul Husnah,meya fiddoki har kika fad’a ruwa,Kuma Ina mahaifinki,tinda naji d’azu kina kukan rashin mahaifiya,Kuma wanne gari kika taso?”,
Uffan batace ba,sai ma kuka data fara ahankali,Jin kukanta yasa umma Jammade tace ckin sauri “A’a d’iyata,yi shiru abinki,idan wannan maganar ce bakiso nabar yimiki ita har Abadah,ki kwanta ki bacci ki huta,yi shiru kinji”.

Zata iya cewa tinda take duniya Bata tab’a ganin mace me karamci irin na umma Jammade ba,haka Bata tab’a samun lallashi daga wajan uwa,Koda uwar wanice ba, sai awannan daren,tabbas ita uwace,ga duk d’an da yayi sa’ar kasancewa akusa da inuwarta,
Dan haka cikin yanayi na k’unar zuci ta furta.
“Nima bansan asalin Daya kawoni duniyaba,Amma dai nasan babata da babana sun rasu,dalilin fitowata Kuma shine, SAWUN K’ADDARATA na biyo,Wanda Allah k’ad’ai yasan ina zan ta radda ita,
Wannan shine abinda nasani daga wannan cukurkud’add’iyar rayuwar tawa,kawai Ina fata Koda k’addara ta sake rabamu,to kizama me addu’a ga wannan ‘yartaki”,
Janyota kawai umma Tayi tarungume tana me hawaye tace “tabbas addu’ata zata sameki ako ina kike ‘yata,ked’in wata Abar hangece agurin tsara,tabbas inajin hakan,zakiyi rayuwar farinciki,komin dad’ewa,kedai kada kik’osa kizama Mai juriya da hak’uri tare da godiyar ubangiji tabbas zaki rabauta”.
Da haka taja mata bargo ta rufamata,tana lallaminta hartayi bacci,
Da safe koda ta tashi harta had’amata ruwan wanka Dana magani, sai dai tashiga Tayo kawai,kafin tafito tayi Sallah har an tatso mata madarar shanu med’umi,Dan haka tana idarwa umma tamik’o mata takafa Kai ta shanye,kana tayi shafa ta canza rigar data Gani akan gado,itama dai d’inkin fulanin ce,aikuwa tayi Wani irin kyau kamar wadda xata gasar kyau,baka tab’a cewa dama ba asalin ‘yar rugar bace, sai dai ita harta d’arasu zubin kyau da tsari na halitta,kamar wata jinsin larabawa zuwa Pakistan,
Umma tashigo ta duk’a ta gaisheta tana k’ara yimata godiya,sannan suka fito tare ta gaishe da kowa na gidan har baba Ard’o injita,bayan tayi gaisuwa suka juyo tareda wata ‘yar budurwa wadda da kad’an Husnah zata girmemata,me suna Janare,Janare d’iyar abokiyar zaman umma Jammade ce me suna hairi,
Hairi itace k’arama Kuma ita Allah yaba Yara awajan Ard’o jamard’e,domin umma Jammade ko b’ari Bata tab’a yiba har zuwa yanzu da girma yafara kamasu,ita kuwa hairi zuwa yanxu yaranta hud’u duk mata,hairi itace ta2,su aurar da d’aya,sai k’ananu biyu suna nan,
Rigar Ard’o jamard’e wata rugace da tin asali shiya kafata,Daga can Wani yanki na yola yayo nan kiwo tareda matarsa Jammade,har Allah yayi kafuwarshi anan,to daganan ne fulani dadama idan suka yanko daji kiwo sai su yada zango anan,wasu Kuma daganan shikenan suyi amansu dana su garken sai dai su dinga zuwa yawo gida.
Anan Allah yayi had’uwarshi da baban hairi har Allah yak’ulla Aure atsakaninsu,suna zaune lafiya da Jammade domin Allah yayita da hkr,da kauda Kai,uwa Uba kawaici,
Koda hairi tasamu ciki Bata Nuna komai ba,suka Raina tare har Allah ya sauketa lafiya,suka cigaba da Reno tare,haka taita samun ciki suna Reno tare har ta haifi Yara hud’unnan,to daganan haihuwar ta tsaya,sosai yadage da bunk’asa rugar,ta hanyar bud’e makarantar islama agarin,da Gina rojiyoyi da guminshi,zuwa abinda yashafi masallaci,duk da guminshi yake komai har Allah yasa rugar takafu,daganan suka had’a k’arfe da k’arfi suka inganta rugar.
Basu tab’a samun matsala ba sai wata shekara da ‘yan boko Haram suka tarwatsasu dasu da dukiyoyinsu da matansu,suka kashi na kashewa,suka tafi Dana kamawa ,to a lokacin hankalin Ard’o ya tashi Dan sanda abin yafaru bai nan,saida ya dawo ya taradda wad’anda suka b’uya ciki harda nashi iyalan su duka,to Ananne yashiga birni yakai koke Kuma ya tabbatar anbi musu hakk’insu,sannan ankarb’o na hannunsu ,to tinda rikicin ya lafa sai ya samu (Kahi) yaima rigartashi,muddin Wani bak’o bai shigo rugar ba to ba’a Isa a farmake su ba,sai dai idan dawani bak’o acikinta Wanda Hakan ke nuni da bak’on shine kamar mabud’in wannan Kahi,da zarar ya fita Kuma shikenan zai koma yadda yake.
Koda Husnah ta gama gaida kowa sai suka shiga d’aki da Janare,suka karya atare sannan Tasha magani,zuwa hantsi umma Jammade tace Janare tarakata Taga gari danta d’ebe mata kewar damuwar data Gani a tare da ita…

 

Taku har kullum.

Husnah Muhammad.

Comments
Share Fisabilillah

🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈
SAWUN k’ADDARA.
❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️.

Na Husnah Muhammad.

Page 23&24.

Sadaukarwa:gareki oum neehal, aminiyar Arziki’i Alkairin Allah ya isar maki❤️❤️❤️.

 

________Koda su husnah suka fita ba sune suka dawoba se can tsakiyar rana,duk inda sukaje tananan tana ware idanu,domin tinda take Bata tab’a samun,sake irinna wannan lokacinba,Kai zata iya cewa ita Bata tab’a sanin ana fidda lokaci kawai Dan ayi yawoba se awannan rana,Kuma sanda suka dawo suka iske angama abinci sedai sukaci,ba kyara ba hantara bare kallan banza,tabbas zata iya cewa Bata tab’a ganin mutane masu karamci irin na wannan ahali ba.

Hakan yasa itama komai anatse take yinshi,haka haryanzu Bata sauya ba tana nan amiskilarta,sedai tasamu sake da walwala,
Haka kod’an shiru umma Jammade Taga Tayi yanxu zata hau tambayarta menene?kowani yab’ata mata Rai,ko yunwa kikeji,ire-iren wad’annan tambayoyin dai,to wannan yasa itama tazama me kamewa,komai zatayi bazatayi Wanda za’a ce batayi daidaiba,haka idan Taga ana aiki zata mik’e takama,nandanan taiya dafa cimarsu daduk Wani Abu da suke sarrafawa na abinci,Dama Kuma can duk Wani aiki na ‘yamace tasaba dashi.

Cikin wata D’aya Tayi Wani irin sabo dasu,duk daba meyawan magana bace Amman tasamu kwanciyar hankali,haka Kuma akullum Ard’o seya tambayeta ko tanada matsala,haka zatai murmushi tace “A’a Babu komai boffah”,

Akullum Kuma Tananan mak’ale da wannan Alk’awari data d’auko atare daita,haka Kuma zobenta da hoton innarta,sunanan mak’ale ak’ugunta tare daita,daidai da second Bata tab’a bari sungusa akusa da’itaba.

Awashe garin data cika wata D’aya Arugar,da daddare bayan sunci abinci sukaje baffah yak’ara masu karatu,sbd al’adar gidan ce haka akullum dasafe,se sunbiya karatu kowa yabama baffah haddarshi,kana dayamma suje islamiyya,zuwa dare Kuma baffah yaimusu k’ari,to Koda taji sauk’i itama seta d’ora karatunta daga inda tatsaya,
Tin A boarding tayi sauka dama,Kuma tanada haddar talatin dawani Abu akanta,itad’in mesan karatuce sosai,kawai Bata samu damar Hakan bane,

Dan haka tinda tasamu sauk’i anan tacigaba da karatun addininta.

Bayan sungama biyawa kowa yashige d’aki domin Neman gurin kwanciya,
Tana kwance tayi Nisa atunanin Daya zame mata jiki umma jammade ta kira sunanta,
Jin shiru Bata amsaba yasa tak’ara kiranta cikin d’aga murya,”Asma’ul-husnah!.

Se alokacin tayi firgigit tajuyo dagakan babban gadan datake kwance Akai,ta amsa tana me tashi zaune Dan sauraron umman,
Umma taxauna kusa daita tarik’o hannunta tana Mai cewa “‘ ‘yata nasani cewa akwai abnda yake damunki Amma baxan matsamikiba akan Jin komenene,kawai kifad’amin shin kinaso kikoma gida,domin ad’an zaman danayi Dake ko sau d’aya banji kin ambaci Wani Wanda kikai kewaba,duk da nasan ke marainiyace,Amma dole kinada buk’atar Wani Wanda yake kula da rayuwarki.

Tsuramata Ido kawai tayi tanajin sabuwar kewarshi tana dabaibayeta,Wani irin tsinkewa zcyrta tayi nantake taji hawaye suna bin kumatunta,Ahankali tad’ago ta fuskanci umma jammade tana Mai cewa

“nikuwa nikeda abinda zantuna Wanda yafi zinari daraja,Wanda yafi uwa da Uba agareni domin shine madadinsu,Amma k’addara tasa nayi nesa dashi,nesan da bansan tsawan adadin nisanba,
Shid’in abin alfaharin kowacce ‘yace tasameshi amatsayin garkuwa,INA KEWARshi,Kuma Ina Mai yimashi fatan alkhairi akowanne yanayi tareda addu’a,bantab’a mantashiba daidai da Rabin second,…”
Katseta umma j.Tayi tana Mai cewa, “towaye shi agareki Wanda yafi uwa agareki ‘yata?”.

“Yayana abin alfaharina,shikad’ai nayi kewa tin fitowata gida,Kuma yanxu yamin Nisan da balallai insake ganinshiba,sedai Ako Ina zancigaba da yimai fatan Alkairi,tare da addu’ar samun nasarah aryw”,
Umma ta Jinjina Kai taname juya al’amarin aranta kana tadubi Husnah tace “wacce irin alak’ace haka?Shin dama shikad’aine yarage maki?”,
Girgixa Kai tayi tana cewa “A’a inada wasu ‘yan uwan,Amma shi nadabanne aduk Wani shafi na rywata”,…….
Tindaga sanda tataso taganta ahannunshi tafara Bata labarin irin halaccin dayayi Mata har izuwa ranar tafiyarshi k’araso karatu,
Daganan tayi shiru tana me Jan aziyar zcy tareda share hawaye, daga labarin Yaya sagir Bata k’ara cewa uffanba,komai nata Bata fad’aba sbd itad’in tin can yarinyace mezurfin cikin gaske,musamman abnd yashafi ahalinta,tana ganin kamar tatona asirin kantane Dana Yaya sagir,tinda komai uwarshi zata yimata to Tana nan a mahaifiyarshi.

Itama umma Bata matsamata, taja abin rufa tarufeta dashi tana Mai ayyanawa azcyrta tinda tafara fad’in abinda take kewa,watarana zata fad’i abinda yafiddota,
Amma itadai bazata takura mata ba,Kuma zata rik’eta muddin Rai indai har malam ya amince,domin haka kawai takejin wata irin k’aunar yarinyar har cikin jikinta.

Can dare yatsala gari yayi tsitt! Bakajin komai se kukan tsuntsaye kad’ai ketashi.

‘Wani irin kira aka kwad’a mata dak’arfi Wanda yasa tayi saurin juyowa daga duk’urson datayi domin hutawa,wata irin mik’akk’iyar tafiyace agabanta wadda ita kanta Bata iya hango k’arshen adadin Nisan dake gabanta,
Wata irin murya me amo da kaushi taci gaba dayi mata magana cikin nuni da umarni

“kada ki kuskura ki shagalta daga nauyin Alk’awarin dake kanki,gajiya batakibace Ayanzu,maza-maza kimik’e ki isar da nauyin Dake rataye awuyanki,
Domin Hakan na tattare da burinki,Kuma k’addararki tamkar sawuce agareki,tananan tana binki Har ixuwa inda zata sadaki da mahad’inta,kada ki kuskura kisare ked’in Abar kwatance ce,Ina Mai umartarki daki cigaba da kutsawa har inda Ubangiji yatsaidake,UMARNI ne Hakan agareki”.

Batt! Mutumin yab’ace,Amon muryar Shima haka,gashi tasan fuskar Amma Sam takasa gane a Ina tasanta.

‘Firgigi! Haka tafarka daga dogon baccin Datakeyi,gaba d’aya tajik’e tai sharkaf,jikinta ko Ina rawa yakeyi,dak’yar tasamu bakinta yabud’u takaranto addu’ar Daya Kamata me mafarki yakaranta,
Jin motsinta yasa umma jammade tafarka,ganinta tayi azaune akan gado tahad’a uban gumi kashirb’an,Cikin sauri tasauko dagakan k’aramin gadanta,tak’arasa babban gadon tadafata tana cewa “uwata meya faru?meya tadake tsakar dare haka?”.

Kuka tasa tana cewa “mafarki nayi meban tsoro umma,Kuma inaji kaman gaske abin yafaru,,”,

“Wane irin mafarki kikayi Niko harya tsorataki haka,fad’amin inji mekika Gani?”,

Samun kanta tayi da b’oye ainahin abinda mafarkin yak’unsa,Dan haka cikin share hawaye tace “Nima bansan ainahin ya mafarkin yakeba,bazan iya tunawaba Amma dai natsorata sosai” shafa Kanta umma Tayi tana me sakko daita daga kan gadan,buta tad’auko tamik’a mata,Babu musu takarb’a Tayo alwala tazo tayi shimfid’a tafara jero nafilfili,tareda yin Addu’o’i na kariya daga sharrin mutum ko Aljan,
Ak’arshe tayima nata iyayen addu’a da yayanta,alokacin asubah tayi Dan haka taci gaba da lazimi har aka tada sallah tatashi itama tayi,bayan tagama tabiya karatunta Takoma gado,nandanan bacci yad’auketa.

 

Koda tatashi asafiyar Tayi wanka takarya,seta shiga tagaida matan gidan kana tawuce wajan Ard’o Dan tagaishe dashi,tayi sallama Daga k’ofar d’akin tad’an tsaya
Cikin mutunci ya amsa Mata Yana fad’in “shigo ‘yar wajan ummanta,yau bakizo k’ariba,zonan inji dalili”.

Tayi murmushinta mesanyi tak’arasa shiga rumfar tazuk’una tana gaisheshi,ya amsa Cikin fara’arshi Yana cewa “yanzu seki fad’amin Dalilin k’in fitowa karatu yau”,
Sadda kanta tayi tana cewa “boffah bansamu bacci ba jiya shiyasa na makara tashi yau,Amma na haddace dama yanzu ma zan iya karanta Maka”,
Murmushin Shi yafad’ad’a yace “nasani d’iyar albarka Baki wasa da karatu,duk abnda akafad’i Toya zauna akanki kenan,wato da ace anan kika tashi tin farko Dana tabbata yanzu iwar haka kin k’arasa haddace Alk’ur’ani maigirma”.

Dariya Kawai tad’anyi tana wasa da gefen malullub’inta,baffah yadubeta dakyau yacigaba dafad’in
“Kinga iKon Allah ko wagga ‘ya,haryau Allah besa baba liti yadawoba ballantana muyi mgnr komawarki gida,domin duk inda suke to na tabbatar hankalinsu ba’a kwance yakeba sbd b’atanki”.

D’agowa tayi Kawai taname tsura mashi idanu,domin ba abinda tatsana irin a ambaci komawarta gida,Dan muddin Suka matsa akan sesun kaita gida to ita kanta batasan meze faruba,ayanzu ita kanta batasan ya rayuwarta zata kasanceba musamman wannan abun Dake tare daita Wanda ita kanta batasan dalilin Daya hanata gayama kowa abinda yafaru ba.
Ajiya kuma tayi wannan mafarki Daya tsaya mata arai,tabbas akwai Wani muhimmin al’amari atareda wannan sak’o Dake tare daita,Dan haka kawai zata cigaba da Addu’a har Allah yabud’a mata hanyar isar dashi Ako Inane afad’in duniyar Nan.

Dan haka kawai samun kanta tayi dacewa “ni marainiyace wata k’addarace takawo ni gareku,idan har Kun amince zan bak’unceku nawani lokaci kafin Ubangiji yasamar ma rayuwata mafita”.
Sosai maganarta tatsayama Ard’o axuciya,duk da tambayoyin Dake Cikeda zuciyarsa Amma haka yadanne yak’yaleta,domin jammade ta fad’amashi yanda sukayi,Dan haka Shima yakeji ashirye yake da rik’eta tsakani da Allah idan har batason komawa inda tafito,dahaka yad’ora mata da nasihohi tareda k’ara sanar daita ribar hak’uri.
Hakanan tayi shiru tana saurara,Dan Alokacin ba abinda idanta kegani face Yaya sagir d’inta yanamata Nasiha.

Ahaka rayuwarta tacigaba awannan ruga,harta samu kusan wata2 acikinta.

Awani yammacine bayan sunyi wanka suna zaune d’akin inna hairi,umman janare kenan,
rigar atamfa ce doguwa ajikinta wadda umma Jammade tabayar akayi mata d’inkin doguwar riga irinta zamani Acan gefen rugar aka d’inko mata ita sabd tagaji dasa kayan fulani kullum tinda dama ita basabawa tayiba,balaifi rigar daidai itace,atamfar mesauk’in kud’i,itako Janare kayanata ne nafulani kamar Kullum ajikinta,
Fira sukeyi har Janare tana Bata labarin wata bishiyar malmo wato (zaitun)dakecan d’angefe dagari kad’an,fad’mata zak’in malmon kawai takeyi da santinshi,Dan haka Cikin zak’uwa tace “Dan Allah jana muje mukatso musha yau bayan mungama karatun dare”.

Ido Janare tawaro tana cewa “Tabb kinsan boffa yahana zuwa wajan nan dayamma,dama dai safiya ce semuje muyi sauri mudawo,Amma Yanzu marece ne,kibari segobe narakaki”,
Cikin zak’uwa tace “Kai Jana yanzu fa zamu dawo badad’ewa zamuyiba,mujema mutambayi umma bazata hanamuba”.

“Aiko umma bazata barmuba,mujedai muce mata zamuje gidan baffah jarmai to semu wuce dagacan”,
haka kuwa sukayi,Suka samu umma nashirin yin talge,Suka tambayeta,umma tad’anyi shiru zuwacan tace “kunga dai marece ne kada kukai magariba kuyi maza kudawo kada malam yadawo bakunan”
Aikuwa Cikin d’oki Suka wuce Suka d’auko hijabai,harsun fito Husnah talaluba k’ugunta taji d’an akwakunta nanan tareda hotonta k’ulle amararta,taduba zobenta kamar wadda akace duba,suka fito tana cema umma

“ummata muntafi kikula dakanki inanan dawowa gareki bazamu dad’eba”,
Wani kallo umma taimata tana cewa “har Ina zaki kike fad’in zaki dawo,waima wannan fitar ba’a iya barinta seda safe iyee”,
Aijin umma nashirin soke tfyr dasauri suka had’a Baki suna fad’in “umma Dan Allah yanxu zamu dawo”, dubansu Kawai takeyi harsuka b’acema idanunta Husnah namata bye bye,tagirgiza Kai Kawai tana cigaba da aikinta.

Gidan boffa jarmai suka fara zuwa sbd kada Azo wataran agano bacan suka jeba awayonsu.
Bayan sun fito suka wuce Suka nufi can mahad’ar hanya ta ainihin rugar,suna tafiya suna fira da dariya,dahaka harsuka iso wajan bishiyar,nanfa Janare tayi d’araf tahaye bishiyar tana cewa “zan karkad’o kekuma kidinga tsince mana,idan muntara seki fad’i Mani insakko mutai”,
“To”, tace tanamai Tara hijabinta asaitin data hangota,haka taita kad’owa ita Kuma tana tsincewa,dahaka harta katso dayawa kana tasakko tana fad’in “yisauri kitsince ganinan sakkowa mutai Kinga duhu yasoma”,. Takuwa tsince tsaf tana sakkowa suka durfafi hanya dankomawa gida,alokacin magriba tabada baya.

Wani irin motsi mek’arfi sukaji ya tunkarosu,cakk suka tsaya suna Mai waige-waige Dan ganin menene,shiru sukai suna kasa kunnuwa Dan sauraren inda sawaye ketashi,
Jin motsin natunkarosu sosai yasa Janare tayi Maza tajanyi Husnah suka lab’e abayan wata bishiya, wasu irin fatake suka gani irin masu yawan dajin nan da daddare suna kama mutane dansu cutar dasu kokuma sutai dasu sufad’i mak’udan kud’i kafin subada su,kana ganinsu Sam ba Imani ataredasu.

D’aya Daga cikinsu ne yace “to ina suke in dagaske kake,ai awannan lokacin bame sakin ‘danshi yabiyo wannan hanyar tinda suka fahimci Muna kewayowa tanan”,
D’ayan da akema maganar ne yace “wlh tabbas naga ‘yammata 2,akan bishiyar can ta gabas datsamiya,domin seda natabbatar kana natafi kiranka”,
“to mubincika kaf kewayannan indai sunanan bazasu Shaba”,

Aijin haka Janare taja hannunta tana rad’amata akunne “kirik’eni mugudu kada kisake kisakeni,duk inda nabi kibi tinda bakisan hanyaba,fataken darene mugayene sosai muruga”,
Aikuwa kaman an zaburesu suka arce dagudu tsiya,aikuwa Suma sunajin sawunsu suka rufa masu baya,gudu suke sosai tarik’e hihabin Janare Kam Kam,harsuka zo marabar hanyar data kasu ukku,D’aya itace ainihin tashiga rugar,wato tacan k’arashe kenan,adaidai nankuma………

Daga Mai k’aunar tasaku nishad’i
Husnah Muhammad.

Share
Comment,fisabilillah.

🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈
SAWUN K’ADDARA.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸.

Na Husnah Muhammad.

 

Page 25&26.

 

Sadaukarwa:Gareki oum neehal,Allah yabar tare ta amanah❤️❤️❤️.

 

________ Adai dai wannan marabar Suka fad’i yaraf su duka,kowa yayi b’angarenshi daban malmon dasuka Samo ya watse,suna waigowa Suka hango sun kusa cimmusu,aikuwa azabure duk Suka tashi cikin firgici kowacce takama tata hanyar dan neman tsira Daga wad’annan mugayen.

Suma suna ganin haka Suka rabu kowa yabi D’aya tahanyar databi,gudu sosai Husnah keyi arud’e Dan ita dama batasan hanyaba gashi sun rabu da Janare Dan haka Kawai tafara kurd’awa duk inda k’afarta tasa gaba,da haka tahangi wata motar Icce fake awani gefe,Mai ita yafaka danyin fitsari,Yagama kenan yashiga ze tada Allah yakawo ta dagudu tahaye bayan akori kurar Nan,Mai ita yaja yayi gaba batare dayasan daita acikiba.

Ita kuwa Janare dakyar tasamu tacimma rugarsu tana hango bukkokin farkon gari,anan tazube tana haki Dan Bata iya cigaba dagudun,shikuwa Wanda yabiyota Koda yazo Bakin rugar nantake rugar tashafe a idanunshi,yazama be iya ganin komai se wawakeken Rafi Wanda be iya ganin k’arshenshi,sosai Abin yad’aure mashi Kai,domin Yana ganin sanda taduk’urshe dagacan nesa,(Idan Baku mantaba,dama rugar Ard’o akwai Kahi,atare daita,Wanda indai babak’o bane acikinta to mugu be iya shigarta),
Dan haka dole yayi baya yakoma inda yafito,Koda yadawo nan yataradda d’an uwanshi Shima ba nasara domin yafad’a mashi seda yakusa cimmata Amma tahaye wata mota tayi gaba daita.

Acan cikin ruga kuwa,hankalin umma Jammade atashe malam yashigo ya isketa,tambayarta yahau yi,meya kawota Bakin bukkar waje ko malullub’i Babu,cikin sanyin jiki tafad’a mashi yanda sukai dasu Janare gashi har Yanzu shiru Basu dawoba.

Aikuwa Nan malam yafara fad’a kamar ya Ari Baki,Yana fad’in “Inbanda sakaci yaushe za’abar Yara mata sufita gab da magariba,nan take yayi aike atai ataho dasu Daga gidan jarmai.
Koda akaje nanfa akace tin zuwansu badad’ewa suka tai,to nanfa hankali yafara tashi,wasa-wasa duk aka bincike gidajen rugar nan basunan,Nan Danan aka kasa samarin garin sukayo gefen gari Dan nemansu.

Har kusan Tara nadare bawanda yadawo Daga Ard’on har sauran mutanen,nanfa hankalin jammade dasu hairi yak’ara tashi,kowa yanata addu’a tareda zullumi,
Can kamar k’arfe Tara da rabi Sega Ard’o dawani saurayi d’aukeda Janare ak’afad’a,
nanfa hankali yayo kansu kowa Yana tambayar meyafaru da Janaren,itakuwa umma j..duvan malam Kawai tayi tafashe dakuka tana cewa “shikenan tawa d’iyar ta salwanta, wayyoh ni jumande Ina kike ‘yata,

Hak’uri akaita Bata,Wani saurayi aciki yace “munduba koina bamu gantaba,itama Janaren akan gab’ar gari muka ganta tayi gudu harta galabaita shine tasuma”.

Sosai hankalin kowa yatashi,saboda iya duba ba’aga Husnah ba,Kuma Koda Janare tamaro aka tambayeta Ina sukaje, Bata b’oye komiba tafad’i abinda sukaje samu da yanda aka biyosu har zuwa Inda suka rabu,tana kuka tagama fad’i
Aikuwa malam yadinga yima Janare fad’a Yana fad’in “idan ita bak’uwace batasan komi na nanba,aike ba bak’uwa bace kinsan komi,seki biyemata,aiseki bari dasafe arakaku kokuma atsinko maku Amma kika jata inda Bata saniba”,
Dak’yar akasamu malam yabar fad’annan aka baza samari da makamai domin nemanta,har Inda sukaje Samo abin seda aka dangana Amma Bata ba labarinta,ga dare yayi, Dan dole suka juya gida suka fad’i,nan aka Aje magana kan gobe dasafe xa’a k’ara fita dubanta har Nan cikin jeji dakuma sauran hanyoyin abada cigiyarta.

Kuka sosai umma Jammade Tasha,Dan har cikin zuciyarta takejin k’aunar Husnah kamar ‘yar data Haifa,tabbas tasan tinda aka kwana2 ba’a gantaba to sedai Wani Iko na Allah,itadai fatanta aduk Inda tasamu kanta Ubangiji yasa ba masu cutarwa bane,Kuma zata cigaba dayimata addu’a har illah Masha Allah.
Wannan shine k’arshen zaman Husnah awannan ruga ta mutanen kirki masu karamci.

To Ina k’addara Kuma tak’ara jefa Asma’ul husnah.
Koda tashige bayan akori kurar Nan,haka memota yaita zabga gudu daita batasan Inda yadosaba,ta k’udundune jikinta sosai taname tunanin Ina zata Kuma Yanzu,domin Kodaga Nan yasauketa batasan hanyar daxata maida ita rugar nanba,Kuma ita batasan Asalin sunan rugarba balle idan tasauka Tayi tambaya amaidota,Dan haka tamik’a lamarinta ga ubangiji taname zubda hawaye.

Tafiya sosai sukayi,tin tana saran taji motar ta tsaya alamun anzo har tadena ta k’udun dune jikinta kawai,secan tsakiyar dare sosai taji motar tad’an fara slow alamun takusa tsayawa,Dan haka tad’ago kanta taname kallan yanda gari yahad’e yayi dind’in alamun dare yatsala,cikin wasu gungun motoci yayi parking,alamun garejin motocine gurin.

Driver yasakko Yana mik’a Yana fad’in “Kai Audi rufemana daita da tamfal muwuce cikin gari muci abinci mud’an samu makwanci,da Asuba munci gaba da tafiyar Nan,danna gaji sosai”.
Wanda aka kira da Audi yasakko Yana fad’in “Angama ogana”, da alama yaran motar ne,Aikuwa Husnah naji aka lullub’eta ruf da tamfal kana taji alamun wucewarsu.

Aikuwa Tayi lamo aciki tana kuka ahankali mara sauti,dahaka bacci me nauyi yayi gaba daita,can bayan anyi sallar Asuba masu motar sukazo Dan fidda motarsu suk’ara gaba,yaran motar yayaye tamfal d’in yaname cema oganshi “oga Amma idan mukakai iccen nan zamu k’arasa gidak…..

Ai bek’ara Saba yayi tozali da mutum kwance tsakan-kanin itace,aikuwa ya kwarma ihu Yana sakin tamfal yayo baya, daga can ogan yarugo Yana fad’in “maciji ne halan kakema wannan gudun”,
Cikin rawar Jiki yace “wlh oga gara inga maciji mutum nefa aciki kamar ma mace”, tsaki yaja Yana fad’in “da alama kashawu ne,Amma Ina xamu samu mutum amotarmu”.

Ya iso wajan Yana yima Audi dariyar shi matsoraci ne,aikuwa Shima idonshi yasauka akan husnah tana kanannad’e tana baccinta,
Cikin dakiya da nuna rashin tsoro ya finciko k’afarta yajawo,aikuwa tafarka firgigit tana rungume k’irjinta,Ido 2 sukayi da direban motar kafin yacemata,
“Daga Ina kike? Wayace kibud’emin mota kishiga Dan ubanki”?, Kuka tafashe dashi tana girgiza Kai,aikafin ma tayi wata magana ya fincikota daga motar Yana “Dan ubanki wazakima karuwanci irin naku na wannan tanbad’add’an garin,uban waye besan HIRJI ba da matan banza,to ko ubanwa yaturoki ninafi k’arfinki wlh,shegiya mekama da Aljanu”.

Kwata-kwata betsaya tunanin sauraron taba,saboda yayi tunanin irin matan banzan nanne Dake hillatar Maza tasigar rauninsu,musamman Daya kasance garin na hirji yayi shuhurah awannan fannin na saida miyagun k’wayoyi da harkar bariki zuwa matan banza.
Akaf yankin wannan waje wannan d’angari yayi shuhurah sosai,saboda garine da direbobi kan yada zango daduk wata karuwa data amsa sunanta awannan yankin.

Hakan yasa bewani tsaya sauraranta ba ya jawota dak’arfin tsiya tadiro motar ya watsar gefe Yana me ba yaran motar umarni Daya wuce yahau mota sutai,su sunsaba da ganin yaran bariki irin wad’annan.

Kuka take sosai tana duk’urshe awajan Daya wurgota,tabbas dama haka tsarin rayuwa yake,indai kana zagawa acikin wannan duniyar to zaka gamu da abubuwa mabanbanta,domin Wani ze kalleka da mutunci,Wani Kuma ze wulak’antaka ne,wanima hakanan ze cuceka batare dayasan daga inda kafito ba,to haka rayuwar tagada.

Danhaka husnah tasamu guri takeb’e har gari yayi haske tana agurin tana kuka,tana tunanin dama batace zata Shan malmo ba dayanzu tanacan gurin mutane masu halacci da Kara,Kai ita atunaninta duk duniya ba mutanen dasuka Kai fulanin can karamci da mutunci,tabbas tasan bazata k’ara rayuwar farinciki irin wadda Tayi agurinsuba.

Kenan ita haka tata k’addarar tazo,bazata samu farinciki med’orewaba,domin duk Wani dad’i dawuri yake yankewa arayuwarta,gashi Yanzu batasan ta inda zata gano hanyar rugar ba bare Tayi tunanin kutsawa komin Nisa tace zata,to wadda takasa gane marabar shiga cikin rugar,inaga wannan shatale-tale d’in tafiyar davatasan ta Ina akafaraba,Dan haka kawai ta ayyana aranta cewa tabarsu kenan Suma har abadah,sedai zata cigaba dayi musu fatan Alkairi aduk inda tasamu kanta.

“Zama begankiba Husnah,kitashi kishiga duk Inda Ake Neman halal dan siyama rayuwa mutunci,ko kad’an kada kisare,kekad’aice bakida matallafi awannan rayuwar taki,Maza kidena Kuka banaki bane,Kuka nad’an gatane,me uwa da Uba akusa Wanda idan yakoka za’a tambayeshi meyake damunshi,Maza tashi kinemi nakanki”.

Wata murya tajiyo namata amo daga cikin kwanyar kanta da k’ark’ashin zuciyarta,bugu da k’ari cikinta Dayayi Wani irin Kuka Yana k’ullewa alamar agaji yake buk’ata,se alokacin tasamu damar tuna cewa tin jiya kafin sufito da Janare rabanta da abinci.

“Ke! Mekike anan gurin”,muryar wani mutumi tadawo daita hayyacinta daga dogon nazarin data afka,
“wuce kikama gabanki,zakizomin wajan Sana’a kizuk’una dan neman tuggu irin naku na Saban shiga a bariki”,
Mutumin Nan ya Ida balbaleta yaname nuna mata hanyar barin gurin,dasauri tamik’e daga ita se wannan doguwar Riga data fito daita,se dankwalin data warware tayafa ma kanta Dan suturta jikinta.

Wani irin mamaki yarufeta najin wannan sabuwar ta’ada ta mutan wannan gari,kenan su agurinsu ba mutumin kirki duka na banza ne?,duk da batasan ainihin fassarar Kalmar (barikiba) Amma tasan ba Abu bace mekyau domin tin tana gida mama hansai Tasha kiranta dahakan,Kuma tasan duk abinda ta dangantashi daita to bame kyau bane.

Dan haka tad’aga k’afarta tana tfy tana kallan yanda kowa yake harkar gabanshi,baruwan Wani dawani,ko kallanta Babu meyi bare tasaran tambayarta daga Ina take.

Mutane nata fitowa daga ko’ina na kasuwar,masu shaguna nata bud’ewa,masu Sana’a sunata shigowa daita,wasu Kuma sunata buga Wani Abu atebir,(caca) Dan itakam batasan mene hakanba.

Ganin zata iyakai Azhar batayi sallar Asuba ba tana yawo akasuwar Nan yasa data hangi Wani mono ta Isa gurin,bawani layi sosai,Dan hk tabuga tayi Alwala,tasamu Wani d’anguri gefe kad’an tayi Sallah taname istigfari da rok’on Ubangiji mafita.

Koda tagama mik’ewa tayi tagyara zaman rigarta dakyau taname tab’o ajiyarta Dake k’ugunta,Jin tananan yasa ta lulluba d’ankwalinta,tashiga cikin kasuwar dan neman aikin Yi Dan tasamu abinci, yawo sosai taci Amma ba inda tadace Dan duk inda tace “Dan Allah abata aiki idan akwai,zatayi komi wuyarshi”, me shagon ko rumfar cemata yake “inada masu aiki k’ara gaba k’ila kidace”,
Data gajine ta tazagaya d’an Wani lungu domin tahuta Dan wata irin yunwa takeji har Jiri keneman d’ibarta,hango wata babbar rumfa tayi mutane sun zagayeta mata da Maza Amma bata iya tantance mesukeyi acikiba,Dan haka dak’yar tak’arasa gurin tazauna gefe kad’an tana jingina da wata bishiya.

Wata mata tahanga atsakiyar rumfar zaune akan wata kujera taci uban d’aurin Nan da akecemai ture kaga tsiya,fuskar nan har Wani jaja jaja takeyi saboda bleaching,bakin Nan yad’auki janbaki tanata taunar cingam jikake k’as k’ak’as k’as,
kewaye daita kujerune da tebura burjik Tako wanne sashi na rumfar,ga mutane zaune akan wasu kujerun sunata cin abinci,daga can gefe acikin rumfar wata rumfar ce k’arama ta langa langa akayi da alama sanwa akeyi agurin,

Acan karshen rumfar ma Wani d’akine Wanda da alama anan Ake Kai abinci idan ansauke ana had’owa masu buk’ata,
D’aya daga Wanda kezaune ad’an gefen matar kad’an akan wata kujera shine yamik’e Yana fad’in,

“Haba Aunty jamsy Amma tind’azu ince akawon sakwara da miyar ganye shine har Yanzu ba’a kawoba,inada uzirin gabana fa haba kicanza Yara wlh dansun cika yawa”.

Wani uban Ashar ta mulmulo ta aza tana Kiran “Rabi!Rabi! Kina Ina shashashar yarinya kawai,ubanme kika tsaya Yi acikin,wlh kika kuskura kika tsamar min nama ko d’ayane sena lahira yafiki Jin dad’i”.
Daga can cikin d’akin rumfar aka amsa cikin murya me rawa-rawa alamar tsoro akace “Aunty ganinan nataradda miya yab’arene shine Nike kwashewa”,

Wani irin mik’ewa Aunty Jamsy tayi tana k’arasawa cikin d’akin tana masifa Kamar ta Ari Baki,cikin wulak’anci tafisgota har tsakiyar rumfar cikin dandazon mazan nan tana cewa “Ai wlh sekin biya kud’in miyarnan idan bakeba ubanwaye ad’akin,su tani gasucan akicin,to wlh koki biyata kokuma kidinga min aikin kud’ina har mu fanshe Dan ko sisi nagama Baki”,
Kuka yarinyar take tana Bata hkr Amma Sam tace ita bazata yaddaba,mutane nata Bata hkr Amma Sam tak’i hkr,Wani daga cikin customer ne yace tafad’i nawane kud’in shize biya Amma tasaki yarinyar,

SE alokacin akasamu tasaki yarinyar,haka Kuma bakunya ta tsandara kud’in dasukafi na miyar tafad’i mutumin yabata,kana tajuya tana fad’in “wlh Rabi ban haushine daita shiyasa Nike mata haka,kiwuce kihad’a kwanonin da akaci abinci kiwanke ga mutane Nan nata Jira”,

Rabi tatsuguna har k’asa tanama mutumin gdy,yayi Wani murmushi Yana tauna Baki kana yace “bakomi yammata anjima zan dawo muyi fira,jeki kiwanke Mata kada tafito tak’ara Wani fad’an”,

Duk abinnan Dake faruwa akan idanun Husnah komi yafaru,tai tsam daranta tana ayyanawa aranta wane irin mugun san kud’i aunty Jamsy take dashi haka,duk mutanen Dake gurin abincifa suka siya,Amma ace kan sauran miya take wannan bala’in tafd’i,
Ganin yarinyar tahad’o kwanoni Tayo gurinta gefen bishiyar kenan,ga saura sauran abinci awasu farantan,aikuwa cikn sauri Husnah tamatso dab da Rabi tana fad’in……..

TAKU AKODAYAUSHE..

Husnah Muhammad.

Comment
Share, fisabilillah.

 

💟💟💟💟💟💟💟💟
SAWUN K’ADDARA.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

 

Na Husnah Muhammad.

Page 27&28.

Sadaukarwa:gareki aminiyar k’warai,Allah yabar tare ta amanah.❤️❤️❤️.

Bismilla-hir-rahmanir Raheem.

 

_________ Cikin sauri tamatsa kusada Rabi Dake niyyar fara had’a kumfa,tarik’o hannunta tace “baiwar Allah sannu da aiki”, Rabi ta tsaya da abinda take tana Mai tsura ma wannan mekyan idanu, domin inbaka tab’a shiga cikin mutane sosaiba to tabbas bazakai tunanin husnah ‘yarnan bace,
Cikin d’an rawar Jiki Husnah tace “Dan Allah wannan abincin waye zaki Bawa?” Rabi tazame hannunta tana fad’in “wafa zanbawa, kwashewa Nike intarashi guguda intai dashi gida k’annena suci”,

“Dan Allah kibani inci,tinjiya rabona da abinci yunwa nikeji”, Sororo Rabi tayi tana cewa “banganeba Ina kikazo to, meyasa bakije kinci abinciba? Ko kema kinyi fad’a da uward’akin kine”, girgiza Kai tayi tana me janyo Wani faranti dataga sauran doya da miya Akai tasa hannu tafaraci hannu baka hannu k’warya.

Seda tacinye sauran doyan kana tajawo sauran wata shinkafa,tana gamawa tahad’a dawani sauran tuwan shinkafa,aikuwa Rabi tsuru tayi tana kallanta,kamar wata tab’abb’a yanda take had’a kashin abinci acikinta,k’walama Rabi kira akayi aunty Jamsy tana cewa “wai tsugunon mekikeyi dabazaki kawo kwanukanba”,cikn sauri tahad’e mata sauran awani plet tashiga wankewa tana “gani nan aunty”,

Koda Rabi tamik’e dankai kwanukan cikin rumfar husnah gdy tayimata kana tace “Dan Allah yayata inba damuwa Nima zan dinga wanke wanken kina bani ragowar irinna yau”,
Cikin sauri Rabi tajuya tana fad’in “kibari sena tashi daga aiki munyi magana Indai zaki Jira”, “zanjira wlh ngd sosai Allah yabiya ki”.

Dahaka Rabi Takoma suka cigaba da sayarda abincinsu a rumfar aunty Jamsy,se can bayan la’asar husnah tasamu tayi Sallah amonon datayi d’azu,bayan tadawo ne ta iske Rabi tanayin Wani wanke wanken,

Tasamu gefenta ta zuguna tanayi mata d’auraya idan tawanko,sunyi nisa awanke wanken Rabi tace mata “ke ‘yar inace?kada dai kema kinfito daga gidanku domin kiyi zaman ‘yanci”, “zaman ‘yanci Kuma to mene Hakan kenufin”, husnah tafad’a tanamai sanjin k’arin bayan,

“Hmm!kina nufin kice bazaman kanki kika fito yiba?”.
Husnah tayi shiru tana tunanin meye zaman Kai kenufi,domin ita Bata Saba shiga jama’a ba shiyasa komi batada wayan yinshi,duk wata kalar hausa ko wayau to Indai acikin tsararrakinta ne sunfita nesa bakusaba,Dan haka kawai tayi shiru Dan Bata Gane inda tadosaba.
Fahimtar Hakan da Rabi Tayi yasa tace cikin rage murya “Ina nufin kema kinzo garin nanne dan kiyi karuwanci? Koko kema aiki zakiyi kamarmu?”

Wani irin dafe k’irji husnah tayi tace “mekikace? Karuwanci,Allah yaimin tsari dashi,ni Sam k’addarace tafiddoni gida Kuma komi wahalar dazan shiga bazan tab’a sab’a Alk’awarin danayima yayana ba,niban masan yanda akeyiba,Kuma bana fatan insani”,

Rabi ta girgiza Kai tace “Tabb lallai bakisan wannan garinba,Amma yanda kikeda kyannan aiban tunanin bazaki samu uwar d’akiba,duk dadai Wani zubin sukan tsani mekyau musamman idan sukaga Alhazawa sunyo Mata cahh!
Kawai shawarar dazan Baki itace,kinga Aunty Jamsy mayyar kud’ice tak’arshe, Amma iskanci bedametaba,indai bakida ra’ayi bazata tilasta mikiba, itadai burinta duk me mata Aiki to yazama mek’wazo da tattashin customer tayanda gobe zasu dawo,Dan haka zan tambayar Miki ita inda aikin dazata Baki kafin wata karuwar takai Miki hari,Dan tadinga samun kud’i Dake.

“Nagode sosai Allah yabiya ki,Allah Kuma yasa ta amince,Niko Yaya zata ban,burinah kawai intara kud’in makaranta,insamu inkoma karatu incika ma yayana burinshi”,
Husnah tagama fad’i hawayen tuna yayanata suna zuba.

Rabi tadubeta tana cewa “to ‘yar gidan yayanta da alama dai anaji dawannan yayan”, dahaka Suka kammala tatayata Suka shiga dasu rumfa Suka gyara,kana tafiddo kayan miya na abincin dare suna gyarawa.

Suna cikin gyaranne Aunty Jamsy tashigo rumfar hannunta rik’eda manyan ledoji na cefanan dare da safe,har ta ajiye ledar Bata lura su2 suka taso yimata sannuba,seda Rabi tace “sannu aunty Dama munkusa had’a markad’en”,
“Kunkusa kedawa? bacewa nayi Tani tagyara rumfa ba,shine kuka jibge agyaran kayanmiya kawai,salan abinci yakai dare,mutane suyita Jira”, tafad’a tana Mai yaye gyalen jikinta tana mik’ama Rabi.

Sadda Kai Rabi tayi k’asa kana tace “Aunty kiyi hkr,dama inaso inkin dawo infad’a Miki”,
Waigowa tayi danjin metake fad’i,se Alokacin talura da bak’uwar fuskar gurin tawani yatsina fuska tana fad’in “wacece wannan Kuma har tasamin hannu asana’a batare da saninaba”.

Cikin Inda Inda Rabi tace “baki dawo bane Aunty shiyasa bangaya mikiba”,
“Uhmm inajinki”, tace taname gyara tsayuwa.

“Dama wannan ce,sunanta Husnah,to tazo itama Neman Aikine shine tace Dan Allah kitaimaketa kowanne aiki kika Bata zatayi,danta dinga Samun na abinci da kashewa”,

Wani irin yamutsa fuska takeyi tana duban Husnah,domin tinda take Sana’a awannan gari Bata tab’a ganin yarinya mekyau d’anya sharaf tana yawon Neman aikiba,sedai Abita ana Neman zama daita sbd mutum bak’aramin samu zeyi daitaba,Dan haka tadubeta tace “Ammadai bak’uwace ke?Kuma da alama Baki had’u da iyayen wannan gariba”,
D’aga Kai tayi Daga durk’ushen datayi taname k’ara sadda Kanta kasa,Aunty jamsy tatab’a Baki tacigaba “Agaskiya Rabi kinsan banida aikin da zanbata ayanzu,kowanne aiki akwai meyinshi arumfar Nan,alfarma D’aya zan iya mata itace: Tadinga tayaki wanke wanke da gyaran kicin idan Angama abinci zanbata taci,kafin tasamu aikinyi,Kobe mataba?”.

Cikin sauri tad’aga Kai tana cewa “yayimin Aunty nagode Allah yak’ara arziki”.
Godiya take mata kamar takwanta k’asa,Nan Aunty tace bakomi sutashi sukama aiki kada aikin yaimusu dare.

Wannan shine dalilin fara aiki agarin HIRJI da Husnah tayi,Koda Suka gama aiki dadare aunti tabata abinci wanda ze isheta harsafe,kana Suka gyara komi Suka shirya tebura,duk abinda Rabi tayi itama tana kallo tayi,dahaka hardare yayi mutane Suka fara cika rumfar Dan siyan abinci.

Koda Suka kammala komi aunty tasallami Rabi tare Suka fito rumfar, Rabi tadubeta tace “Toni zanwuce domin gida Nike kwana,ke Ina kika nufa”,
Shiru tayi danbatasan mezata ceba domin dai ita kanta batasan Ina zata kwanaba.

Fuskantar yanayinta da Rabi Tayi yasa tace kozaki bini gidanmu,inrok’i gwaggota kikwana acan kafin kisamu Aiki,ammafa sekinyi hkr Dan gwaggo masifaffiyace,bamuda uwa tarasu,Muna zaune awajan gwaggonmu wato k’anwar babanmu”,
Ajiyar zuciya husnah tasaki tana cewa “muje to nagode sosai,insha Allah zankiyaye daita”, tana me ayyanawa aranta tinda na’iya zama da mama hansai aiban tunanin akwai wadda tafita bala’i.

Dahaka Suka nufi wata hanya datayi can gefe dagari Suka wuce gidansu Rabi,sund’anyi tafiya balaifi sannan Suka iso Wani ragargazajjen gida,wasu irin katangu gareshi ‘yan gudul-gudul nak’asa,har kana iya hango d’akin Cikin gidan,ga k’ofar ko marfi Babu sedai buhu da aka k’ulla aka kare tsakar gidan,dahaka husnah tagama kallan gidan Suka shiga ciki.

Dasallama Rabi tad’aga labulan k’ofar d’akin gwaggo tana fad’in “sannu da gida gwaggo kokinyi bacci ne”,
“Sauken labule da’alla kada sauro yayoman kabbara ad’aki,mezan miki inkin dawo koko bakisan hanyar d’akin nakubane eyee,kinsanfa bansan iskanci fa”, ai husana najin saukar wannan bala’i tamak’ale abayan Rabi jikinta narawa sosai,itakuwa Rabi dayake tasaba kod’ar batajiba se Janyo husnah datayi Suka shiga d’akin kana tasaki labulen.

‘yar cocilan gwaggo takunna tahaska tana fad’in Ina kika Samo wannan kuma me kama da sadaka yallar Kuma,Maza garin kwashe kwashe kigamu da aljanu sakara Kawai”,

Rabi tayi dariya tace “Kai gwaggo mutum cefa kamarni,daga ruga tab’ace tokuma batasan hanyaba shine muka had’u tace Dan Allah kafin Azo nemanta zata zauna d’akina Muna fita aiki tare har Taga Wanda tasani ranar kasuwa,seta bishi yamaidata can ahalinsu na fulani,kinga Nan kusa bawata ruga bare ace zata iya komawa”,
Gwaggo tagama saurarenta tace “kina nufin har sunan rugarma Bata saniba kome,kintab’a ganin inda mutum yamanta sunan garinsu Rabi?”.

Dasauri husnah tatareta tace “Ai bamota yau,Dama zan zauna ne kafin ranar kasuwar idan motocin Icce Suka shigo semu wuce tare”.
Gwaggo tatab’e Baki tana cewa “nifa be dameniba,danni ko maita kike namana yafi k’arfinki,haka ko abincin 5 bazan bakiba daga aljihuna sema doka dazansa inkika Samo to dole kiraba Dani”, dasuri tace “na amince gwagggo nagode”.

To dahaka suka samu gwaggo ta amince da zaman Husnah agidanta,suka fito suka nufi d’aki Rabi tatada k’annenta 2 dasuke kwance tabasu abincin data taho dashi,ita Kuma husnah taraba nata biyu takaima gwaggo rabi taci sauran,bayan sungama Rabi tayi masu shimfid’a agefen yagalgalallar katifar da k’annenta ke kwana Akai.

Tin asuba suka tashi sukai Sallah,suka d’eboma gwaggo ruwa suka cikamata tukunyarta,sannan Rabi tagyara d’akin cikin sauri tana fad’in “yimaza kiyi wanka husnah kada mu makara wajan aiki”,
“To”, kawai husnah ta amsa tashiga bayin da ko marfi besamuba shimadai da tsumman aka kare naciki,tasamu talallab’a tayo wankanta tamaida gajeran wandanta me aljihu da abubuwan Dake ciki tad’aure tamau tafito tashirya,Rabi tabata wasu Riga da siket nata duk sunsha wuya takarb’a tana gdy tasanya.

Kayan sunmata yawa,setayi Wani burum aciki Amma sunyi mata kyau,Koda Rabi tafito itama shiryawa tayi sannan tad’akko musu hijabai k’anana suka sanya suka fito Rabi Tanama k’annenta kashedin kada suje koina,dayamma tayi suwuce makarantar allo dasukeyi acan gaba da k’auyensu.

Wajan bakwai suka iso rumfar,anbud’eta Har Tani tayo shara Dan haka suka gaisa Suma suka kama aka cigaba da gyaran rumfar,anan Tani dasauran ma’aikatan rumfar suke tambayar dama wai husnah ‘yar uwarsu Rabince,itadai Rabi amsa musu tayi kawai da “eh’.

Ka’in da na’in husnah tad’auki aikin rumfar aunty Jamsy,komi tasata Yanzu zata aiwatar cikin sauri,damacan ita aiki ba bak’onta bane,komi wahalarshi sedai inbata sababa,Amma data iya tawuce Jin wahalarshi,
Kuma cikin iKon Allah tayi wani irin farinjini arumfar,mutane har zab’arta suke dankawo abinci,dandanan rumfar tak’ara samun jama’a,domin Wani kyanta kawai zed’ibai Kullum yazo cin abinci gurin,Wani Kuma dawata manufar azuciyarshi yake zuwa Dan sharar fage da cusa Kai.

Itakam ko sau d’aya Bata tab’a kula kowaba,hankalinta nakan abinda aka sata,idan tagama Kuma tataya Rabi Wani aikin dansu gama sutai dawuri,inta gadama seta wuni Bata tankama kowaba tana hidimar gabanta,Danko Rabi Bata cika Jin maganarta ba musamman arumfa,halinta nanan na miakilanci Wanda halittar tane Hakan.

Ganin yanda rumfar tasamu sauyi sosai ta dalilin husnah Aunty jamsy tajawota ajiki sosai,harta sakata cikin masu girkin abincin rumfar,Kuma tace mata duk wata tanda dubu bakwai Banda abincin dazataci, Aikuwa Husnah har kuka seda tayi na murna,dandanan tak’ara dagewa da aikin,yazama duk Wani kalar abincin da ake dafawa arumfar to ta iyashi,cikin lokaci k’ank’ani labarin wata kyakkyawar matashiya arumfar Jamsy yabud’e garin,kowa fad’in albarkacin bakinshi yakeyi akanta,aikuwa Nan Danan manyan karuwa garin sukayo mata cahh Dan dulmiyata aharkar Dan susami kud’i daita.

Nanfa aunty Jamsy tayi ruwa da tsaki tanuna bawata karuwar data Isa,dataga alamar suna binta gida kuwa Dan susami kanta se kawai tayanke shawarar maidota gidanta kusa daita,aranar datace tahad’o kayanta zata koma gidanta ne husnah seda tayi hawaye,tanuna bazata iya barin Rabi ba Amma Rabi Sam tace wlh seta koma,ai komawarta can kamar kare rayuwarta ne dag sharrin maza da matan dasuke kawo mata hari,dan kaff garin ansan wacece Jamsy,batada mutunci ko kad’an shiyasa kowa ke tsoron tunkarar husnah kaitsaye.

Komawarta gidan aunty Jamsy yadad’a sauyata tareda fiddo kyanta,domin zazzagen kaya aunty Jamsy tafiddo mata takai aka ragomata tabata,kayan sunkusa kala Goma, Kuma Basu Wani jijiki sosai ba,danhaka taware kala ukku tabama Rabi sauran tafara sanyawa tana fita rumfa dasu,danma aunty Tayi- tayi takoyi yafa mayafi Amma takasa,itadai tafi ganema hijabinta.

Dahaka taci wajan wata 2 arumfar tana aikinta cikin kwanciyar hankali,Kuma akullum setayi addu’a Allah yabayyanar mata da wanda akabata wannan amanah tashi,haka Koda wasa Bata tab’a gigin Nunama Wani itaba,tadai canza Wandan tasamu Wani cikin Wanda aunty tabata Shima me aljihu tamaida abinta,idan wannan yayi daud’a tacire tawanke tamaida wannan,

To dahaka rayuwa taci gaba da juyawa agurin husnah.

Tofah!bari mulek’a wajan mama hansai Muji wace wainar take toyawa tin bayan takora husnah daga gidan ubanta.

Taku har Kullum .

Husnah Muhammad….

Share
Comment, fisabilillah.

💟💟💟💟💟💟💟💟
SAWUN K’ADDARA.

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸 .

 

Na Husnah Muhammad..

Page 29&3

Sadaukarwa:gareki oum neehal,💕💕💕💕.

_______Acan garin katsina kuwa,bayan fitar Husnah daga gidan, mama hansai tajuyo tabama kulu hannu suka tafa suna shewa cikin farincikin rabuwa da Alak’ak’ai,hansai tadubi kulu tace “wlh harnaji ansakarmin mak’ogwaro,Amma idan Ina ganin yarinyar Nan kada kiji yanda bak’inciki ke hanani sukuni azuciyata”.

“Dole kike kasa bacci hansai Dan wannan yarinyar idan da kinbatta to wlh duk Wani jin dad’i bazaki sameshiba daga ‘yayanki,yanda uwarta tahanaki Jin dad’in na ubansu haka itama zata hanaki na yaranki,nifa tintana k’arama danazo naga yanda sagir keji da ita har wanka waishi kemata,tin daganan nafara tausaya maki wlh”.

Hansai tatab’e Baki tace “hmm kibari kawai nikad’ai nasan abinda nashak’a,Kuma Yanzu ma kinsan inda gizo ke sak’ar? Idan yayanta yakira itace farkon abinda yake tambayo,bansan mezan fad’a mishiba,Kuma wlh bansan yasan gskyr zancen,domin Yana iya tsallako karatun yace zetaho,Kuma kinga yakusa k’arasawa bemakai shekara ba inaga”.

Kulu tafashe da dry tace “shegiya kawata Kice bakison karatun yatsaya,to bari kiji yanda za’ai,idan yakira waya kuka gaisa Daya tambayi inda take seki d’an sauya murya kifara kukan munafurci, kinsan dai menake nufi,
Idan yatambayi ba’asin kukan seki fara cemai,…….takai kunnenta kusa suka gama kitsawa kana tace zata tafi kome kenan idan sunyi wayar tasameta taji yadda sukai,dahaka sukai sallama ran kowa fess acikinsu.

Bayan kamar kwana4 da tafiyarta Audu yadoka sallama agidan yaname cewa bayan sungaisa “dama megida ne yace Dan Allah akawo maku wayar yanata Neman taki data husnah besamuba,nikuma kwana2 naje anguwa badamar kawo maku shine yace idan nadawo akawo maku,Yanzu muka gama mgn dashi”,

Yamik’ama hansai wayar adaidai Nan akakira,yad’aga mata yajuya yayi waje,hansai takara waya tana “hallo kanajina d’annan”,.
Dagacan sagir yayi dry yace “inajinki mama inawuni yagida yayara,dafatan kowa lfy”,
Ta amsa Mai da “duk munanan k’alau ya karatun naka yake ciki”
“Mama lfy Lau karatu munyi nisa shiyasa komi yad’au zafi, kwana2 munje Wani discussion ne acan Wani daji,to Kuma gurin ba network bahalin yin waya dole seda muka fito kana Yanzu nakira, Ina lil sis take kota nemeni mama”.

Hansai tatab’e Baki tana fad’in “Kai kasan abinda kake fad’i niban Gane wannan mgnr ana had’amin da yaren yahudu”,
Yai murmushi yace “oh mama Ina nufin Ina husna ta tashiga yaushe raban da injita tin ranar Dana Bada waya abata,washe gari muka shiga dajin danace Miki,wlh sosai nayi kewarta”.

Aijin haka hansai seta fara rawar murya alamun kuka tana shesheka,sagir yarud’e Yana fad’in “lafiya mama meya faru?kowani abun husnah taimiki ba daidaiba injamata kunne iyinn?”.
Cikin makirci da kissa hansai tafara fad’i cikin kuka “hmm kabari Kawai d’annan tin bayan tafiyarka yarinyar nan gaba D’aya tasauya,abinda Taga dama Kawai takeyi,bame sata bame hanata,yanzuma Wani saurayi tasamo bansan d’an Ina bane Kullum gurinshi take wuni,nayi fad’an harna gaji Amma Sam tak’i bari,
Dana matsa mata da fad’anma se cemin tayi “itafa shi takeso Kuma ko in aura matashi kotatai inda za’a musu aure suyi rayuwarsu,Yanzu haka saboda Taga nazira mata Ido dankar tace zata bishi,tofa shine tatsiri Kullum fita yawo taredashi,
Idan nayi mata mgn ta hayayyak’omin Wani zubin hada zagi,nayita k’ok’arin insameka Amma Ina Abu yaci tura,dole Nashanye damuwar nikad’ai kawai”.

Gaba D’aya sagir tsaye yake kawai da waya ahannunshi Yana sauraren dogon bayanin da mama kemai,Amma komotsi yakasa,husnah!da saurayi har tana ik’irarin binshi in ba’a batashiba,tabd’i ai wlh beshirya yima husnah aureba,toma yaushe ta Isa auran,duka nawa take dahar zatai aure,tabd’i aiji yake kamar yai tsuntsuwa yadawo Nigeria,Dan haka kawai yacema mama “atabbatar da Husnah tadawo annemeshi,yanaso yayi magana daita data dawo”, dahaka kawai yakashe Kiran yaname dafe Kai,
cikin haka wayar shi tayi k’ara yaduba yaga Alhaji kawu ne,Wanda yakawoshi Nan karatu,Koda yad’aga suka gaisa seyaji muryar Alhajin cikin yanayi kamar natashin hankali Dan hk cikin rauni yace “kawu lafiya daiko yasu mima kowa lfy ko”,
Dagacan Alhajin yace “sagir Ina cikin matsala sosai,Wani muhimmin abune nawa cikin manyan kadarorina yake barazanar salwanta,Amma har yau nakasa Gane dalilin Wanda yad’aukai,Dan Yanzu haka annemeshi anrasa,sagir dama d’an daka Haifa ze cuceka akan dukiya,tabbas daya tafka kuskure Dan komi daran dad’ewa wannan (HATIMIN) seya tonashi aduk inda yake,Dan haka kacema d’an uwanka nace Maza yayo Shirin gida tinda suna Hutu Asibitinsu,idan komi yalafa yakoma yahad’o sauran takardunshi yadawo gida”.

Nanfa akeyinta, domin dai sagir kanshi yakulle Sam be fahimci inda maganganun alhaji suka dosa ba,gashi Shima yana fama datashi sabuwar damuwar da husnah takunno daita,Dan haka kawai yamik’e Dan cika umarnin kawun Yana Kiran layin wanda akace yakira.

To tindaga lokacin Daya Sami lokaci zekira Dan Jin ko husnah nakusa,Amma Daya kira se acemai yanzu tabar gidan,kokuma tinsafe rabanta dagidan,Kai har cewa yayi Idan tadawo akulleta har yakira suyi magana amma hansai tace tafad’a mata Amma tatureta tak’i saurararta,haka yadinga bin Audu meshago Shima yacemai wlh yarabu da ganinta tin bayan yadawo unguwar dayaje.

Wannan shiya k’ara tada hankalin sagir yaji komi yafita Mai arai harta karatun,gashi yakusa fara jarabawar k’arshe bare yataho,Kuma Abokinshi Wanda yakesa ran yasanya bincikarmai ita anan Nigeria Shima Yanzu hankalinshi bakwance yakeba da wata gagarumar matsala data samesu,Dan dole ya hkr yafuskanci jarabawarshi da zummar yana gamawa zeyo gida Dan cin uban Husnah daganan yad’auketa daga garin yatai daita inda zefara aiki yasata makaranta,
Dawannan hansai tarufe bakin sagir akan husnah da zummar inya dawo tariga tashirya abinda zata fad’amai akanta.

Su Usman kuwa Koda suka nemeta dashi da Musa haka tazauna tashirya musu k’arya da gaskiya Kuma tahad’a Baki dasu akan kada susake sufad’ima sagir komi saboda kada yabaro karatunshi yataho,Subari idan yadawo yasan gaskiyar komi kawai,dahaka suma suka share lamarin husnah bawanda yanameta tinda ita tasa kanta injisu.

RUGAR ARD’O JAMARD’E.

Acan rugar Ard’o jamard’e kuwa,iyaka Neman duniya anyishi Amma ba husnah ba labarinta,har k’auyuka akadinga bi Amma Ina ba’a daceba,Kuma bawanda yayi tunanin Wani dalili ze iya kaita har gari menisa kaman hirji,Dan haka sukayi tunanin kota fad’a Wani ramine kokuma mutanen dasuka biyosu aranar suncin mata,Dan haka suka sadak’as sukayi fura da dak’uwa me yawa sukayi mata sadaqa dasu,akan Allah yabayyanar daita,idan Kuma tamutu ne to Ubangiji yakai ladat gareta,

Itakuwa umma Jammade takance itadai tanaji ajikinta komi daran dad’ewa husnah zata dawo gareta Bata mutuba.

Bayan wasu ‘yan kwanaki baba liti yaje domin gano husnah dakuma Basu hkr akan rashin dawowarshi akan lokaci,yace musu “wlh akan hanyarsu ta komawa gida bayan sun ajema me Iccen kayanshi,to anan suka gamu da b’arayi sukai musu ta’asa bayan dukan kawo wuk’a dasukai masu suka barsu anan,to bayan sunsamu d’auki aka kaisu gida suketa magani se wannan Datsin yasamu k’arfin jikinshi.

To bayan sungaisa yagama jawabi kenan Suma suka d’ora danasu akan abinda yafaru da Husnah,sosai Abin yatab’a baba liti,bayan sungama jajantawa juna sukayi sallama tareda fatan sake saduwa daita indai tana Raye,dawannan kowa Yakama gabanshi,Akabar husnah da tulin addu’a,to Ubangiji yasa addu’ar tabiya.

GARIN HIRJI..

Acikin zaman da Husnah tayi da aunty Jamsy zata iya cewa tad’an samu kwanciyar hankali,sedai tana aikatuwa kaman jaka Amman Sam ita Hakan bedametaba,sema k’ara k’ok’arin yima Aunty Jamsy duk abinda tasata.

Sabi’u Wani tsohon saurayin Aunty Jamsy ne dasuka dad’e atare dashi,tin zuwanta garin dafara saida abinci suke tare dashi,driver babbar motane,yakan Kai kaya manyan jahohi Nako Ina a Nigeria,to tinda husnah taxo besamu dawowaba garin seyau,sedai suna yin waya Akai-kai da aunty Jamsy.

Yau tinda safe Aunty taketa Shirin zuwan sabi’u bayan sunyi waya yacemata Yakusa shigowa Jibiya,aikuwa duk Wanda ke aiki arumfar seda yasan yau aunty tana farinciki,
Uban gayu ta cancad’a tashirya mashi abinci merai da lafiya,komi natarba seda tashiryashi tsaf, kana tacema Husnah tazauna tatsare mata agida zata lek’a rumfa Taga me Ake ciki kafin yaiso.

Fitar Aunty Jamsy kenan badad’ewa sabi’u ya iso gidan,dasallam yashigo Yana fad’in “my heart,Gani nadawo da d’okin sake gan……..,
Kawai idanshi yasauka akan husnah Dake kwance akan doguwar kujera,kanta ba d’ankwali,tsefaffen gashinta yazubo gefen kujerar,idanta alumshe tad’ora hannunta bisa cikinta,
Gaba D’aya mutuwar tsaye yayi awajan ganin wannan balarabiyar yarinyar agabanshi,Wani irin slow yayi yanemi gefen k’ofar yaduk’a yaname taraddadi azuciyarshi,da tunanin wacece wannan Jamsy ta ajiye agidanta batare data tab’a bashi labariba.

Sallamar Aunty Jamsy tatayar da ita zaune daga inda take kwance,tana juyowa karaf idanunsu yasark’e dana sabi’u ga aunty Jamsy tsaye abayanshi da alama besan
daita bama agurin.

 

Daga
Husnah Muhammad.

Autar babanta..

Kuci gaba da bina danjin cakwakiyar Dake anan gaba….

Share & comment.
Fisabilillah.

💟💟💟💟💟💟💟💟💟
SAWUN K’ADDARA
❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️.

 

Na Husnah Muhammad.

Page 31&32

Sadaukarwa:Gareki aminiyar kwarai Allah yajada zamaninki,💕💕oum neehal👏👏👏.

 

_________ Wani irin fad’uwa kirjinta yayi ganin irin kallan da aunty Jamsy take yimata,cikin sauri tajuya tad’auko hijabinta tayafa ajikinta,shikuwa sabi’u dayake gogaggen d’an barikine,kana kallanshi idanshi abud’e yake,duk Wani kalan iskanci da yaudara yariga yasan makamarshi,Dan haka cikin hillata yajuyo yazubama Aunty Jamsy Ido,yaname kanne Ido Yana fad’in “haba masoyiyata yazaki razanamin zuciya da gangar Jiki,wlh harkinsa nayi zuk’unawar dole,Ina tunanin kece kika rame kika k’anjame haka,se uban fari kaman wata kazar mayu”.

Yadafe k’irji Yana cigaba dacewa “nagode Allah Dana iskeki cikin koshin lafiya da walwala”,
Ai gabad’aya Jamsy tamanta dawani zargi dazata fara d’osanama ranta,tawashe hak’ora taname cewa “barkadai Abincin ruhina,sannu da isowa,mushiga ciki kahuta mana”,
Suka shigo d’akin husnah nagefe kanta nak’asa tana wasa da hijabinta,aunty Jamsy tadubeta tace “kiwuce rumfa aiki nacan nabaro kitai kikama masu ashirya tebura kafin mutane suyi yawa.

Cikin sauri tad’aga k’afa tawuce sabi’u namata Wani irin kallo tagefen Ido Yana lashe Baki,aikuwa tana fita tasaki ajiyar xcy tad’aga k’afa zuwa rumfa.

Aunty Jamsy Kuma suka cigaba da soyewa bayan yaci Abinci yak’oshi yajanyota jikinshi yaname kashe mata idanu da zira hannunshi arigarta.
Bayan komi yalafa Aunty Jamsy take cemai “sweat heart wai yaushe zamu tsaida ranar Auranmu,yakamata ace zuwa Yanzu munyi Aure bawai mudinga Jan lokaciba,har yaushe zaka cikamin Alk’awarin dakakemin ne na aure,kasan dai Kai kad’ai ne nmjn danike bama lokacina inbar sana’ata saboda Ina sanka,to gsky yakamata asan abinyi”,

Zare jikinshi yayi daga nata Yana basar da maganar tareda cewa “kada kidamu lokaci yakusa very soon zamuyi Aure”,
Dubanshi kawai tayi ganin Yana mgn irin ko ajikinshi,Kamar yanda yasaba,bayanda taiya itama kawai tayi shiru Dan tana k’ara mgn zehauta da bala’i haryayi mata zcy,itakuma ba abnd take tsoro irin yayi mata fushi,wannan yasa tayi shiru Dan dole kawai.

Wanshekare rumfar Sabi’u yazo yazauna dasunan Yana tayata fira,Amma duk inda husnah tagifta ita yakebi da Ido,Wanda adacan sam yatsani yazo rumfa yazauna,

Dahaka akasamu kwanaki yanayin haka har Aunty Jamsy tafara fuskantar Wani Abu agame dashi,aikuwa Nan Danan tacanzama Husnah,komi cikin tsawa takemata shi,saboda tanada bala’in kishi akan sabi’u.

Shiko sabiu agaban aunty Jamsy benuna ma husnah komi illah kawai yad’auketa amatsayin k’anwar wadda yakeso,Amma data Bada baya ze tareta Yana mata maganganun banza tareda Alk’awura idan tayadda dashi,Kuma yana yawan cemata shi xed’auketa daga Jamsy idan ma ita take tsoro.

Cikin lokaci k’ankwajan’ani ya firgita Husnah,yazamanto batada kwanciyar hankali arumfa da gida,duk inda take zuwa yake,Sam beda shamaki da gidanta,haka rumfarta,Kuma Wani lokacin Aunty ita kad’ai take bari agidan tatafi hidimarta.

Acikin Hakane watarana Aunty tafita dayamma,husnah kad’ai ce agidan, tanata kakkab’e kayan Aunty tana gyarawa,duk ak’ok’arinta na taburgeta sbd yawan fad’an datake mata akwanakinnan Wanda itadai batasan tushen Shiba.

Dasand’a yashigo gidan Yana lek’e-lek’e,ganin alamar Jamsy batanan yasa yakulle gidan da jamelock yak’araso da cikin d’akin.
Sam bataji shigowarshiba sedai taji anrik’o hannunta nadama kawai,juyowarta karaf idanuwansu suka had’u,dak’arfi tafisge hannun tana bugamai tsaki,tanunashi dayatsa tana fad’in “kafita agidannan kada Aunty tazo tasameka,wlh zantonaka koka fita harkata,tamm”.

Cikin Wani irin d’an iskan kallo dayake mata k’asa k’asa yace “kitona mana baby,aini akanki ba abinda bazan iya d’aukaba,dazaki sauke wannan girman kan naki dakinji dad’i Dani,komi kikeso aduniyar Nan zanbaki shi,inzaga Dake wurare daban daban kiga koina idanki yabud’e sosai kana mushana bayan na Aureki”.

Tab’e Baki tayi tana me fad’in Allah yatsareni da Auranka,inci Amanar mutumiyar data maidani mutum,Toni bahaka nakeba nasan darajar mesona Dan Allah Amma ba irinka ba,mtsss”, tak’aremai datsaki.
Yamik’e Yana dunfarota da murmushinnan nashi na ‘yan duniya,aikuwa tajuya domin wawuro komi tasamu,shikuma anan yasamu damar rungumo bayanta kamar irin ta sigar Soyayya,adai dai Nan Kuma aunty Jamsy tabud’e gidan da key d’in hannunta tana fad’in “rufen gidan Kuma mezaki kamar nasaki”……

Cakk tasaki ledojin hannunta taname zubar dasu k’asa ganin mummunan abinda kefaruwa agidanta Kuma ad’akinta,cikin fushi da fusata tace “husnah mexan Gani haka? Nashiga ukku ni jamila”,. Dasauri husnah dabatsan yak’araso garetaba sedai taji hannunshi ajikinta tawaigo,alokacin har aunty Jamsy ta wawuro tab’arya Tayo d’akin.

Sabi’u naganin haka yamatsa dasuri Yana rik’eta Yana cewa “haba Jamsy kefa matsalata Dake kenan zafin zuciya,kibari naimiki bayani mana,kinsan dai bazan tab’a cin amanarkiba tuni yarinyar Nan tadameni tana Neman lalata Dani,Amma Sam nak’i biyemata sbd kekad’aice agabana,Kuma nayi shirune inajan kunnenta akan Hakan gudun kada kisani dannasan bazaki mata dakyau ba,to kawai yau Nazo take Neman yaudarata kinsan dai halinku namata.

Ai Ina Sam bama tajin meyake k’arasa cewa,idanta yarufe da zafin kishi kawai,tafincike tana zaginta tana cewa

“Shegiya tsintacciyar mage dama Bata mage,wato nahana nawaje karuwanci Dake ko,shine bari kisakamin dayi da masoyina ko,to yau senaga bayanki.

Abu fa kamar wasa bala’i yab’arke har mak’ota suka taru ana rik’e Jamsy tanata sirfama Husnah zagi,tana setaga bayanta,dakyar aka amshe makamin ahannunta,ana tausarta.

Husnah Kam Banda kuka ba abinda takeyi tana fad’in “wlh Aunty bahaka bane Dan Allah kiyi hkr kisaurareni,ban Miki laifiba kiyi hkr”.

Adai-dai Nan wata mata Tayi sallama agidan tana fad’in “lafiya Jamsy tindaga nesa Nike Jiyo hayaniya agidan kamar Wani yak’i yab’arke,kefa matsalata Dake tijara,darashin hkr,Baki iya bin komi asannu,da’alla kuwatse kowa Yakama kanshi”,
Aunty Jamsy ta buga tsaki tana fad’in “ai wlh ba masifaffiya ba ko wuta za’adinga kirana dashi,gwara inci uwar ‘yar iskar yarinyarnan,insauke mata kafad’a shegiyar muga ta karuwanci,Sumi Sumi da ita kamar ta Allah,Nima ai Allah k’araman maganina kenan,Dana d’aukoki bansan daga inda kika fitoba,mayya kawai.

Dak’yar wannan bak’uwar mesuna uwani tajata d’aki tazaunar sannan talek’o inda husnah take rakub’e har lokacin tana kuka tace mata “kitai rumfa Muna zuwa”.
Aijin haka dasauri husnah tafice agidan tana tafiya tana kuka,itakuma uwani Takoma cikin d’akin tadafa kafad’ar k’awarta tana cewa “kekuma nadawo gareki,meya had’aki da waccan kyakkyawar yarinyar har kika Tarama kanki jama’a akanta?”.

Aunty Jamsy Bata b’oyema uwani komaiba,tass takwashe tin daga had’uwarsu tafarko tabata labari har izuwa yau,kana tad’ora dacewa “Amma dayake munafukace yarinyar Nan kinga cin amanar data min,karkiso kiga yanda karuwan garinnan kekawo mata hari dansu nemi kud’i daita,Amma nayi ruwa nayi tsaki nahana kowa isowa gareta,Amma shine zatamin sakayya dahakan”.

Uwani tafashe da dariya sosai harda k’yak’yatawa,harta k’ule Jamsy,taja tsaki tace “da’alla malama dariyar mekike,ke matsalata Dake mugunta,Amin laifi kihana inyi hukunci Kuma kizo kina dry,bansan wulak’anci fa”

Se alokacin uwani ta tsagaita da dryr tana cewa “to aikece da abin dariyar kike,Banda abinki ko aure kike da sabiu kinkawo wannan zankad’ed’iyar budurwar agidanki,bare namijin bariki daze iya cin uwa dadaddare,yaci ‘yarta dasafe,aikema kinsan kinyi ganganci,kawai ai irin wad’annan yaran kinemi kud’i dasu shine Mafi sauk’i Kawai”.

Kallan ban fahimcekiba Jamsy tayima uwani tace “kina nufin nasata tayi karuwanci bayan nibanyi,uhmm nifa kinsan business d’ina,ban takura yaro akan abinda be ra’ayi,tin farko Kuma nalura bataso,ke bama tasan komiba wannan yarinyar ko wayan kirki batadashi ingaya Miki”.

Uwani tayi dariya tace “kinsan batada wayau Amma kike zargin zata iya Kai kanta ga saurayi,kumama gogagge irin sabi’u Haba jamsy idan ganinta anan d’in dayake ne yakeso yafarrak’a tsakaninki dashi to kid’auketa daganan,kikaita can nesa dashi inda sedai Kawai tarik’a Baki kud’i kimata hassafi da abinda kika gadama”,

“Bangane me kike nufiba uwani,yimin bayani dan Allah ko hankalina ya kwanta,ina zankai husnah Indinga Samun kud’i kaman asama,Kuma idan tagirma tayi wayau mekike tunanin zebiyo baya”,

Uwani tayi tafi ta dara kana tacee “zokiji kawata”…………..

Tofah koya zata kasance da Husnah Kuma,
Ina Aunty jamsy zata kaita,Kuma meke tattare dahakan.

Muje zuwa,daga.
Husnah Muhammad.

Shared & comments.

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
SAWUN K’ADDARA.

💕💕💕💕💕💕💕💕.

 

Na Husnah Muhammad.

Page 33&34.

Sadaukarwa:gareki oum neehal,Allah yabar tare yaraya mana neehal ❤️❤️❤️.

 

_________ Uwani tamatso kusa sosai tana cema jamsy “ke Bakida fahimtane,kokin manta business d’ina nayanzu,to bari intuna Miki,irin wad’annan k’auyawan yaran Babu abinda yadace dasu Wanda yawuce aiki,Ina nufin aikatau,kinganni Nan Yanzu baruwana da wata sana’ar hannu kota zuba jari,ko tsayawa yin karuwanci.

Sana’ata d’aya Yanzu itace:Kai Yara aiki gidan manyan hamshak’ai asallameni,sannan Kuma inkoma wajan iyayen yaran suma susallameni,sa’annan duk bayan Wani lokaci inkai ziyara ayimin hassafi,dahaka nasan duk wasu matan hamshak’ai nagarin Abuja da kewayenta,idan har Wata hajiya na Neman me aiki to akwai lambobina awajensu,kirana kawai zasuyi,nikuma na bazama k’auyuka Ina Neman masu d’andama har Allah yasa adace,domin Yanzu suma Basu d’aukar jahilai dole semasu ilimi suke d’auka.

Yanzu haka maganar danike Miki,matar Wani Attajirice takirani akan tana Neman memata girki wadda keyi mata tayi Aure,to shinefa nataso takanas zuwa gareki Dan inji yaza’ai dannasan kek’arshece afagen girki,Dama zuwa nayi cikin yaranki na rumfa inkin yarda kiban d’aya tinda nasan Suma k’wararrune afagen koyawarki,
Kingadai dukanmu zamu samu,Kuma sema nazo na iske wannan abun daya faru Kinga shikenan fad’uwa tazo dai dai dazama koya kikace?”.

Uwani ta Ida maganarta taname tsurama Jamsy Ido ganin tayi zugwui tana saurarenta kaman tasamu karatu.

Aunty Jamsy tasaki ajiyar zuciya mek’arfi kana tanisa tace “naji dogon bayananki Kuma nafahimta Amma abin tunanin shine: Taya zantura yarinya guri menisa bayan bansan daga Ina tafitoba,domin ni haryau ko labarinta bansaniba,Kuma duk randa taso komawa mahaifarta yaza’ayi kenan?kokuma tagirma tayi wayan sanin kanta”,

Dafata uwani tayi tace “kekuwa kafin lokacin Baki Yagi abinda kika yagaba,idan fa tatafi komi tahannunki zedinga biyowa,duk wata da anyi mata albashi sedai kawai kiji alert a banki naki,Kuma base kid’an yimata dabaraba kice zaki dinga Tara mata kud’in agurinki ba,kinga idan aka kawo seki d’an warar mata Wani Abu kekuma kicigaba da hidimarki dasauran,kokuwa yakikace?”.

Jamsy tace “to Yanzu ya za’ai tayadda da tafiyar batare data fahimci me ake cikiba”, uwani tace “kemadai kamar Wata yarinya,kawai kisa akirata kinuna mata yanzu kin fahimci ba laifinta bane,Dan haka kika nemar mata mafita wadda Zata zamar mata Katanga daga sharrin sabi’u,kice mata zaki taimaketa kimata hanyar aiki awani gidan masu kud’i,duk wata kina Tara mata kud’in, harta Tara mak’udan kud’i daganan tadawo itama tafara nata business d’ina,
Natabbatar idan kikai mata haka xata amince bare kince batada Wani wayan kirki,Kinga kinjefi tsuntsu biyu da dutse d’aya,ga samu dazaki dingayi kina habb’aka jarinki,gashi Kuma cikin sauk’i kin rabata da sabiu dayake Neman tarwatsa Miki zuciya”.

Tabbas uwani tazo da shawara Dan haka cikin gaggawa ta amince da batunta,harta d’ora dacewa “Yanzu yaushe kike ganin zaku tafi to?”

Uwani tamik’e tana fad’in “aiba Jira za’atsaya yiba,kinsan dai halin masu kud’i Nan basan Aikine dasuba,kinji wayar datake ta kirana,har nariga nayi mata Alk’awarin gobe zankawo mata tayi hkr,shiyasa na bazamo gurinki yau d’innan,Dan hk kisata tashirya yau gobe tin asuba zanzo muwuce”.

“Ba matsala k’awata nagode sosai,se goben,Kuma kitabbatar kincika Alk’awari,zan tura Miki acc.number d’ina da komai,duk wata inji alert,”
Uwani tabuga shewa tace “shegiya k’awata kefa indai harkar kud’ice Toba sanya,toki tabbatar dai Kinja mata kunne akan tsafta,Gandar aiki,da gyara sanwa”.
“Duka Bakida matsala dasu,domin Koni Yanzu banace tafini ba,sedai ince kankan-kan,Dan haka jeki kawai se goben.

 

Dahaka suka rabu akan se washe gari zata dawo tin asubah,domin tafiyar.

Acan rumfa kuwa,haka husnah ta Isa tana sharb’ar kuka sosai,cikin sauri Rabi tatareta tana tambayarta lfy,kodai ciwan cikin datakeyi duk watane,dantasan yanda yake wahal daita,husnah ta girgiza Kai,Suka nemi guri Suka zauna,seda Tasha kukanta Wanda dak’yar Rabi tasamu tayi shiru,Shima ganin Rabin takusa yine yasa tad’an lafa,kana ta labarta mata abinda yafaru agidan aunty Jamsy,
Rabi cikin bakin cikin jin Hakan tace “hmm wannan d’an iskan,shiyasa tin farko nace kisanar da aunty abinda yake maki,kikace aitsoro kikeji kada tace sharri kike masa,yanzu gayanan munafukin yahad’aki daita,Nan kwanaki haka yad’irkama wata ‘ya ciki,da akazo aka titsiyeshi gaban aunty ya faffallama yarinyar Mari yace k’arya take,nanko aunty taita sababi Anma masoyinta sharri dan arabasu,Sam tak’i yadda tace sabiu baze iya cin amanar taba,ahaka maganar tawatse yacuci yarinyar abanza,Sam ba mutumin kirki bane shege .

Suna cikin maganar Sega aunty tab’ullo ta rumfar tak’araso inda suke zaune,tadubi Husnah data sadda Kai k’asa tana hawaye tace “kisameni gida yanzun nan” daga haka tajuya tahau mashin tawuce,husnan cikin sanyin jiki tamik’e tadubi Rabi zata wuce,
Rabi tarik’ota tace “kik’ara hkr komai lokacine,Kuma kisa ranki kome tace maki Ina tare Dake,ko korarki tayi to Nima zanbar aikin munemi Wani tare,kiyi shiru insha Allah watarana zaki dara”, aijin wad’annan maganganun sedai kawai husnah tarungumeta tana kuka,sosai taji k’aunar Rabin aranta tazauna mata,Dan haka tayi gdy sosai tace bari taje seta dawo,suka rabu suna bye bye kamar wad’anda bazasu sake had’uwaba .

Dasallam tashiga ahankali cikin gidan,k’irjinta na duka kamar zeb’ullo yafito,dagacan aunty tace “k’araso mana ganinan ciki”, Jin muryar da sanyi acikinta yasa tad’anji Dama-dama aranta,tak’arasa shiga ciki zata tsuguna,dasauri anty tatarota tazauna gefen gadon inda take zaune,tad’ago fuskarta idanta cikeda k’walla suka had’a idanu,aunty tashare hawayen tace “husnah Yishiru kinatsu magana zamuyi Dake me muhimmanci”,

Tashare hawayen tak’ara sadda Kanta k’asa tana saurare tace “inajinki aunty kiyi hkr,wlh banyi Miki laifiba”, aunty ta Jinjina Kai taname ayyana rashin wayau irinna husnah,cikin d’an sakin fuska kad’an tace “kiyi hkr,seyanzu bayan nayi tunanin naga bazaki iya abinda Nike zarginki dashiba,Kuma nayi Wani tunani akanki Dan tseratar Dake daga Sharrin mutanen garinnan, musamman sabi’u dayanzu yasa Miki K’ahon zuk’a,nasan halinshi Indai yasama ranshi Abu tofa seyaga bayan abin hankalinshi yake kwanciya,nikuma Ina sankine kamar k’anwata tajini,Dan haka nayanke Wata shawara wadda Zata amfaneki inkin yarda.

Da zuciya D’aya husnah tad’aga Kai tace “to aunty nagode dakika fahimceni,Kuma komiye nayarda,dan nasan bazaki cutar daniba”,

Aunty Jamsy tace “Ato kemadai nasan kinada buri,Kuma kinaso kitara kud’i domin kikoma gida wajan inna dasu”,
Wasu hawaye tamatso tana cewa “banida kowa awannan duniyar se kaina,iyayena sunrasu Kuma ni d’ayace awajensu”, tafad’i Hakan cikin k’unar Rai natuna irin wulak’ancin da Akai Mata da korar kare,tacigaba dafad’in “burinah insamu Intara kud’i inkoma makaranta inyi karatu me zurfi,intsaya da k’afafuna,intai maki duk Wani maraya gudun yayi rayuwa irin tawa”.

Ido kawai aunty tazuba mata ganin yanda take magana cikin bushewar zcy,Kaida Gani kasan daga k’asan zuciyarta take fidda Amon maganar,Dan haka cikin yaudara jamsy tace “yawwa ainasan dole kinada muradin Wani Abu aranki,shiyasa nayi maki wannan taimakon kinaji ko,wata k’awata datazo d’azu aikinganta ko,to ita kesamar ma yara aiki amanyan gidaje na ABUJAH,tuntuni mukai magana daita akan Tani me aikina tace akwai Wani gida da ake Neman ‘yar aiki zata kaita,toshine tazo akan maganar tafiyar gobe gobe,shine nikuma na tausaya Miki nace kawai bari ke kitafi,tinda ‘yan iskan garinnan sunyo maki cahh,Kuma kema Zakifi samu acan,Koko Yakika Gani? Duk wata zaki kwashi kud’inki,Kuma bawani aiki bane me wahala,girkine kawai zaki dingama hajiyar,Kuma kici Kisha ki wanki duk kyauta kana duk wata tabaki kud’inki,har nace maganin wata matsalar ma zanbada acc.nmb d’ita adinga zuba Miki kud’in aciki,idan kika samu ko shekarane sekizo yawo mufidda kud’in muga mekika Tara,

Idan sunkai na makarantar shikenan se wata Takoma amadadinki,kekici gaba da karatunki koya kikace”,

Cikin yadda da aminci husnah ta amince tana ganin aunty jamsy ta taimaketane akan burin rayuwarta,Dan hka tadinga godiya,aunty tace taje tayi sallah tashirya kayanta,gobe tin asubah zasu wuce,dahaka tawuce bayi aunty namata kallan Bakida wayau yarinya.

Tass tahad’a kayanta,kana tacema aunty zatayoma mutanen rumfa sallama,aunty tace seta dawo Amma kada tasake tafad’ma Wani yanda sukai,acewarta wai kada Tani taji tace anmata ha’inci,Dan hk tayi shiru da bakinta,tasamu kowa taimai sallama akan zataje unguwa tadawo bazata jimaba,

Rabi ce kawai ta titsiyeta akan Bata yaddaba sbd tasan meya faru agidan aunty ayau itada sabi’u,bayanda ta iya dole tafad’ima Rabi gsky,Rabi tanisa kana tace ‘To Allah yatabbtar da Alkairi”, Amma ita aranta abun Sam bewani kwanta mataba,to Amma yata iya tinda harsun gama magana,Kuma ita wacece d’inta dazata hanata abinda takeso,Dan hk kawai tayi mata fatan Alkairi,suka cigaba da firarsu,secan dare kana tarakata suka rabu da Alk’awarin duk sadda sukayi waya da aunty jamsy to zata ce tabata sugaisa.

Ahaka takwanta barci da tunane-tunane dayawa aranta,har se gabannin Asubah barci yafigeta,can angama sallah kenan aunty tatayar daita tana fad’in “wai wane irin baccine wannan haka kikeyi,tind’azu nike tayar Dake gashi har uwani ta iso tana buga gida,Amma ko tashi bakiyi ba,bare kiyi sallah”.

Firgigit tamik’e tana mutsitstsika Ido,cikin sauri tatashi Tayo alwala tazo tai sallah,aunty jamsy da uwani sunata azalzalarta,cikin saurin tasamu tagama komai dakomai,Dama tahad’a duka ‘yan kayanta,wad’anda jamsy kebata kwance,tad’auki ‘yar Jakarta tatab’o k’ullinta taji yananan d’aure ak’ugunta,tajuyo taima aunty jamsy sallama suka rabu akan sesunyi waya idan sun Isa,aunty tad’anyi mata Nasiha akan zaman aiki awani gida kana tarakosu Tasha, alokacin har motar Abuja takusa cika suka samu suka shige suka biya kud’in,

Seda motarsu tad’aga kana aunty Jamsy tajuya zuwa gida,
To husnah semuce Allah yatsare hanyar Abuja.

ABUJAH CITY.

Se wajan la’asar suka shiga Cikin garin Abuja,sosai husnah tabud’e Ido tana kallan kyawu da tsari irinna garin Abuja,Bata tab’a tunanin akwai guri mekyan haka awannan duniyarba,sosai tasaki Baki da hanci tana kallan garin,ba abinda yafi burgeta irin yanayin shukokin dasuka kewaye ko Ina na gefen titin garin,ahaka sukaci tafiya menisan gaske kana suka iso wajan da motar zata tsaya,kowa yasauko daga motar,Aunty uwani tajata gefe tana fad’in “kindai Sha zaman mota”, tayi d’an murmushinta kawai tana mik’a,daganan suka shiga taxi,ananne taji aunty uwani nayin waya tana fad’in “Eh hajiya munkusa k’arasowa ai insha Allah,” tad’anyi shiru tana saurare kana tace “insha Allah zama tayi sedai kinganta,to semun isod’in”,

Dahaka ta ajiye wayar taname Maidata jaka.
Wata tafiyar suka shalla har husnah na tunanin ko Wani garin zasu Kuma zuwa Amma dai tayi shiru dayake bame yawan magana bace tin asali,tana Cikin tunanin Taga sunfara shiga wasu manyan gate awata unguwa tadaban, fad’in tsari irinna unguwarma tsayawa b’ata lokacine,anan me adaidaita yace “hajiya askoro adaidai Ina za’a saukeku?” Uwani tace “eh Ina ankare kak’ara gaba zannuna maka inmunzo.

Me adaidaita yacigaba da shiga gate-gate Yana kutsawa har yashiga Wani tamfatsetsen gate kana yatsaya domin dokar unguwar anan taba duk Wani me taxi iKon dakatawa,aunty uwani Bata tsaya tambayar shi Dalilin tsayawarba sbd tasan dokar,Dan haka tace susauka tabiya kud’in kana suka cigaba da kutsawa ak’asa.

Sund’anyi tafiya kad’an suka shiga wata kwana dasuka iske wani gida me wawakeken gate kalar ash,girman gate d’in yakai mutum ya iya tunanin wata unguwa guda zasu shiga,gate d’in sek’yalli yake alamar samun kulawa akodayaushe,anan suka tsaya aunty uwani tayi waya akan sun iso,sunanan tsaye akabud’e karamar k’ofar gate d’in Wani d’an dattijo yalek’o Yana fad’in “hajiya kune bak’in dazanma iso?” “Eh mune baba” uwani ta amsa.

Yabud’e k’ofar Yana “kushigo cikito hajiya tace aimuku iso”, seda uwani tajawo husnah kana tadawo daga duniyar kallan datatai,suka kutsa Kai cikin makeken gidan Dake d’auke da flat ukku, kowanne beda bambamci da d’ayan,acan gefen dama nagidan Wani k’atan gurin shak’atawa ne,ga filin bolly aciki da swimming pool acan k’arshe,daga hagun Kuma motorpack ne da motoci aciki,ak’alla sunkai biyar,Kai tsayawa gaya tsari irinna gidan b’ata lokacine,domin iya had’uwa yahad’u,aunty uwani tajata suka nufi cikin gidan flat natsakiya suka tsaya uwani tadanna doorbell husnah nagefe tana kallan iKon Allah,Dan ita atunaninta buga k’ofar za’ai,

 

Tana Cikin haka kuwa akazo akabud’e akace sushigo ciki,dasallama aunty uwani tafad’a falon,Wanda husnah taji numfashinta naneman tsayawa sbd had’uwar falan,Wasu irin Italian cushion ne zagaye da tsakiyar falan,acan gefe Wani makeken dining table ne,ga Kuma curtains masu muguwar tsada kalar sky blue,to komi na falan seya kasance sky blue ne,jikin bangon falan Wata tafkekiyar plasma da hometheatre ne dasuka cika bangon,Kai iya had’uwa falo yagama had’uwa,domin dai agurin husna wannan falon dabata tab’a ganiba toko a aljanna akabatashi tasamu rahama.

 

Gefe ta zuguna ita Kuma uwani tana kan kujera mezaman mutum 1,can Kamar minti5 Wata Mata tabullo daga Wani d’an corridor tasa Jan leshi jikinta,wuyanta yasha uwar sark’a me tsadar tsiya,tataho cikin yanga da k’walisa irinta macen data amsa sunanta mace ta iso falon tana fad’in “A’a sannunku dahanya Kun iso kenan”, cikin sauri uwani tarussuna tana cewa “barka dagida hajiya mun k’araso,ya gajiya,ya hidima da mutane Kuma”,
“Lfy Lau sannunku,bari akawo maku ruwa,Rabi!Rabi! Kikawo ma bak’i ruwa”,matar tabada umarni dagacan wadda aka kira ta amsa da “to hajiya”.

 

Husnah Muhammad.

Taku AKODAYAUSHE….

Share fisabilillah.

🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈
SAWUN K’ADDARA.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸.

 

Na Husnah Muhammad.

Page 35&36.

Sadaukarwa:gareki oum neehal❤️❤️❤️❤️.

 

__________ daga Wata k’ofar tadaban Wata ‘yar budurwa tabiyo da tire ahannunta,tazo gabansu ta Aje,hajiya tace “kusamu kusha ruwa akawo maku abinci,idan kuka huta semuyi magana ko”, hajiyar tafadi tana mik’ewa Takoma ciki,suka Sha ruwa kana aka kawo masu abinci sukaci merai da lfy sukayi sallolin Dake kansu awani d’aki da akakaisu,bayan sungama tasa aka kirawosu suka sameta falon dasuka bari d’azu.

 

Suka zauna k’asan kafufunta kana tafara magana tana cewa “to uwani dafatan kunci kunsha Kun wartsake gjyr MOTA” uwani ta rusuna tace “Munci munk’oshi wlh hjy,Muna godiya,Kuma wannan itace yarinyar Danazo Miki daita,gatanan kiganta idan tayi maki,nariga nasan halinta tanada natsuwa da hankali,uwa Uba hkr da kauda Kai,Kuma afagen girki tadabance nariga nasheda Hakan”.

Uwani takai Aya tana zungurin husnah data gaisheta,husnah tatashi taduk’ursa tagaishe da matar Kanta ak’asa,matar ta amsa itama da fara’a kana tace “to gaki agidana,amatsayin ‘yar aikin datafi kowanne d’an Aiki had’ari,domin kusan cinmu dashanmu ahannunki zekoma,dafatan Zaki rik’e amanar da aka Baki,Kuma Abu na2 bansan k’azanta,bansan zama da datti ajiki uwa uba ace kibarmin kicin da k’azanta,Kuma akowacce safiya akwai abnda kowa keso shiyake karyawa dashi,akwai time table daza’a Baki Tananan inafatan kin iya karatu ko?”,

Husnah tad’aga Kai tana cewa “eh na’iya abinda baza’a rasaba hjy”.
“Yawwa to ya sunanki? Kuma daga wanne gari kika d’aukota sbd halin rayuwa,Kuma duk Wata ita za’adinga bama albashinta koko iyayenta?”

Uwani tace “eh to batada iyaye sunrasu duka,sedai aubtyn ta wadda nad’aukota awajenta dagacan HIRJI,Wani garine dakecan marabar jibiya da dajin nasarawa,anan suke sana’ar saida abinci,to dagacan nad’auko ta sbd nayaba da hankalinta sosai,Kuma ta iya girki sosai,kud’i Kuma akwai lambar acc.data waya ta yayarta aciki za’a rik’a zuba kud’in,inaga aikunyi magana tin can ko husnah”, ta Ida tana kallan husnah, husnah tad’aga Kai tana kallan uwani Kawai,toda haka suka Ida maganganunsu akan sewata idan yayi za’atura kud’in acc.d’in jamsy, hajiyar tace subata acc.nmb d’in,daganan Sukayi sallama hajiya tasallami uwani da tukuici metsoka,bayan tafad’a masu albashin Husnah dubu 20k duk wata,tatashi tabasu guri Dan suyi sallama domin uwani tace bazata kwana anan ba akwai inda zata wuce anan Abujah takwana.

Seda hajiya tawuce ciki kana uwani tad’akko waya takira aunty Jamsy suka gaisa,tayi Mata bayanin komi dayanda suaki da hajiya,kana tabama Husnah Dan sugaisa, ta amshi wayar takara akunne tana fad’in ” Aunty ina yini,ya gjy,ya muka baroku” dagacan Jamsy ta amsa da fara’arta “tana fad’in lfy Lau my Husnah,ya bak’unta? Yau za’ayi kwanan city ko”, Husnah tayi murmushi kawai tace “Alhamdulillah”.

Dagacan aunty tacigaba dafad’in “to kinatsu kidinga aiki mekyau,Yi nayi bari na bari,nariga nasan bakida matsala Tako wanne fanni,toki k’ara dagewa,duk abinda akasaki shi zakiyi,abinda kikaji yashige Miki duhu to Kicema hajiyar kinasan mgn Dani zata kiramiki ni semuyi magana inganar Dake,Kinga idan kika dage cikin shekara1 Zaki Tara kud’in makarantarki kidawo kifara karatunki,duk Wata za’a tura Mini kud’in nikuma zantara Miki kinji”,

D’aga Kai Kawai takeyi kaman tana gabanta har zuwa sanda tadasa Aya,daganan suka d’anyi fira takashe wayar tamik’ama aunty uwani tana godiya,domin ita aganinta sun taimaketa sosai itada aunty Jamsy,Dan hk take mugun ganin girmansu tareda bin umarnin duk abinda suka sata,to dahaka sukayi sallama da aunty uwani tayoma hjy sallama tawuce bayan tabata lambar wayar aunty Jamsy data acc.

Koda aunty uwani tafita tsuru Tayi afalon dabatasan kanshiba,ita kad’ai tarakub’e ajikin kujerar kusa daita,Tananan har akayi sallar isha’i tatashi Tayi Takoma tazauna,zuwacan wajan k’arfe Tara taji alamun bud’e k’ofa za’ashigo,firgigit tatashi Daga baccin dakesan figarta,wata matashiyar budurwa ce tashigo falan dawani k’aramin yaro data rik’oma hannu,ak’alla yaran zekai shekaru7 zuwa 8,Sam Bata lura da wata halitta afalanba tawuce zuwa hanyar dining,harsun wuce yaran yakalli gefen da husnah keduk’e Kanta ak’asa yace

“laah aunty wace wannan?”

Budurwar tajuyo tace a’ina Kuma…karaf idanta yasauka akan mutum duk’e afalan Kanta ak’asa,aikuwa tadage ta kwarara uban ihun dayasa duk Wani mahaluki Dake cikin flat d’in yafito dagudu bashiri,hajiya kubra,da Wasu yammata 2 suka kwaso aguje zuwa falan suna fad’in “meerah lafiya? Meyafaru,meya sameki?

Gaba D’aya sunrud’e da tambayarta,ita kuwa ba abinda takeyi se ihu tana fad’in aljani ne wlh aljanine naganshi,Dama nafad’a maku akwai aljanu agidannan”,

Se alokacin hjy talura da inda take nunawa,wato saitin da Husnah keduk’e tadod’e kunnuwanta sbd ihun meerah yayi Mata yawa akunne.
Wani uban tsaki hajiya kubra taja tana cewa “ke da’alla yimin shiru Kinja duk mun fito bashiri,mutumce ba aljanaba,sabuwar megirkice aka kawo”, ta Ida tana k’arasowa wajan husnah,alokacin Kuma Meera tanatsu taname dawowa hayyacinta,hajiya kubra tamatso tana fad’in “dama har yanzu kinanan zaune,meyasa tin d’azu Rabi Bata Nuna maki d’akinkuba kinje kinkwantaba,gobe Zaki fara Aiki dasafe,” tajuyo wajan ‘yayanta dasukai cirko-cirko suna kallanta tace musu “oya come for me, ga sabuwar cook ankawo maku,Daga gobe zaku fara gwadata,d’azu Kunfita lokacin dasuka iso,Amma kuyi hkr da ita ahankali zata goge,Kuma balaifi tanada natsuwa”.

Wani irin tab’a Baki sukahau yi suna bin husnah dawani k’ask’antaccen kallo kana babbar cikinsu mesuna zee zee tace “mommy that girl,itace zatana abincin dazamuci,woh toyaushema shekarunta sukakai tafara shiga kitchen bare hartasan dafa Wani Abu,haba dai mom kema kinsan dasake”, ta Ida tana Wani yamitsa fuska danuna husnah dad’an yatsa.

Meerah Kam kasa magana Tayi sbd takaicin Daya isheta,k’aramar cikinsuce wadda dakad’an zata girmi husnah tace “mtss! Kudai wlh ‘yan wulak’ancine Amma aikunbari agwadata ko batun yanzu kuyanke hukunciba,to wlh ba inda zata dole taxauna ko Bata iyaba tashiga makaranta takoyo sannan tazo Tayi mana, Inba hakaba Kuma daddy nadirowa zanmuku had’i dashi ehemm”,

Kallanta Kawai Sukayi suka juya wajan dining domin sunsan tinda tasa baki basuda yanda za’ai saboda bak’ar rashin kunyar leemat harta Isa,Kuma gashi daddy Yana matuk’ar santa duk Wanda yab’ata Mata akaf gidannan tokuwa Shima ranshi seya b’aci,sbd sunan mahaifiyarshi dataci,Dan hk suka juya Kawai Sukayi dining da Anwar wato autansu awannan flat d’in,suna wucewa leemat tazo tajata tana tambayar mommy wane b’angare za’akaita nacikin masu aikin gidan,mommy ta guntse dariyar datake San tayima su zee zee tace A’a d’akin Rabi Zaki kaita,Kinga idan Tayi nisa Wani lokachin za’a buk’aceta,Kuma Bata kusa shiyasa nace ahad’ata da Rabi ad’akinta.

Leemat tad’ago ta tana fad’in muje inrakaki d’akinku k’yale wad’ancan stupid d’in, cikin sanyinta tamik’e taname k’wak’umar jakar kayanta,cikin falon Taga sunyi Wata hanya daban Suka b’illa Wani d’an corridor Sega k’ofa data b’illa can bayan flat d’in wajan lambu,anan Taga Wata k’ofa Suka shiga wadda take kallo k’ofar bayan flat d’in,Suna shiga Taga Ashe d’akine Wanda inba Wanda yasaniba bame Gane dashi ab’angaren.

Tsayawa leemat tayi tana nocking,daga ciki Rabi ta amsa da waye sbd tasan dawuya Wani yazo d’akin sedai akirata tahanyar wayar Dake mak’ale ad’akin ta tarho,cikin k’osawa leemat tace “bangane wayeba,waye kike tunanin zuwanshi awannan time d’in,malama kizo kibud’e mana k’ofa”.

Aijin muryar masu gidan Cikin sauri Rabi tataso tabud’e tana fad’in “Aunty kiyi hkr bansan kebace”,

Tsaki taja tana turo Husnah dafad’in “shine tind’azu ance kikawota d’akinku Amma kika shanyata afalo ko?,to gatanan sabuwar cook ce akakawo amadadin sabira, mummy tace tare zaku zauna Dan haka kisanar daita duk wata doka tagidannan da yanayin tsarin abincin gidan nakullum”, dahaka tajuya tayi wucewarta tabar Husnah anan gurin.

Da ido suka bita harta b’acema ganinsu kana Rabi tajawo hannunta tana fadin “uhmm kishigo se hak’uri lamarin yaran gidannan,bansan Nan za’a ajekiba datun d’azu naje nataho Dake”, “bakomai nagode dahakn ma”.
Husnah tafad’a kana tashigo cikin d’akin,babban d’akine mefad’i d’auke da katifu madaidaita guda2,kowacce da malullub’inta dafilo,gefen kowacce akwai wata ‘yar dirowa tasaka kaya da Abubuwan amfani,se toilet dagacan k’arshe na d’akin,

Tsaye kawai tayi tana kallan d’akin har seda Rabi tace “kimatsa ciki mana,ga katifarki can gefen dama,ga Inda Zaki aje kayanki can,sannan ga bayi can inkika tashi buk’ata,kije kiyi wanka kifito kici Abinci kana muyi magana akan sauran Abubuwan Daya dace.
K’arasawa Husnah tayi ta aje kayan gefen katifar kana tashiga bayi tatub’e tayi wanka tamaido kayanta tafito,tatarar da Rabi zaune da Abinci gabanta harta amso Mata,Rabi tace “yawwa zoto kici Abincin gashi nazubo maki,”
“To ta amsa dashi tana kallan Abincin dake plate d’in,lafiyayyar shinkafa ce fried rice taji uban namomi akanta,Wani miyau tahad’iya taname Maida hankalinta akan abincin,Cikin sauri-sauri tasamu tak’arasa shiri tazo tad’auki plate d’in Takoma gefen katifarta tazauna tanacin abincin,seda taji tayi d’iff kana ta ajiye sauran,domin tin asali ita bame cin abinci bace sosai,iya yunwar datakeji dataci daidai cikinta zata aje domin tin tana k’aramarta rayuwa takoyar daita komi tasamu tayi hkr dashi,Koda tagama tayi Shirin bacci sannan Rabi tafara karanta mata dokokin gidan kamar haka:

Dafarko dai kina gidan Alhaji sagiru metasa,Wani babban k’usane acikin Abujan Nan,matanshi biyu,hajiya Mero da hajiya kubrah wato wadda tad’aukoki Aiki kenan,hajiya tanada matuk’ar kirki muddin kika rik’e mata amanah,babban abunda bataso shine :Rashin gaskiya da k’azanta,Kuma tanada mugun San ‘yayanta musamman leemat wadda takawoki d’akinnan,yaranta hud’u 3mata namiji1 Kuma shine auta.

Akowacce safiya akwai abnda kowannensu yake karyawa dashi,Kuma abinda yaci yau ba lallai bane yacishi gobe,Kuma kowanne baison yatashi karyawa Baki had’a mashi nashiba,akwai timetable ajikin kicin d’in zaki ga zab’in kowanne acikinsu na kullum,sannan hajiya tanada mugun kishi na fitina,dankomu ‘yan aikinta bataso Taga munrab’i d’ayan b’angaren can na kishiyarta bare har muyi tunanin shiga,Sam bame shiga huld’ar Wani cikin suduka,kowa rayuwarshi da ‘yayanshi yake.

Idan Alhaji zedawo to zata kiraki dakanta tafad’i maki abinda za’ayi mashi natarba,musamman idan kin iya abincin gargajiya,danshi Alhaji yafison irin wannan cimar,sannan Abu nak’arshe kiyi hankali da ‘yayanta,Dan Abu kad’an zasu iya tsinkaki cikin mutane kokuma su zazzageki batare da kinmasu abinda yakai nazagiba,Dan bazan mantaba sabira wadda take musu girki ada kafin tayi aure watarana daga tayi d’an kuskure wajan abinci yad’anyi gishiri kad’an wlh haka zee zee tadinga kifa mata Mari Kuma abin haushinma agaban mamansu Amma tafuske dacewa ai rashin kula yasa tayi Hakan,to anyi haka badad’ewa tabar gidan Takoma garinsu akayi bikinta,Toni alokacin bandad’eba Kuma iyakata shara da mopping da wanke-wanke se had’a kayan wanki da gyaran d’akunansu,Ina gamawa Nike dawowa d’aki inbasu guri inba hjy tasani Wani aikinba,Dan haka kikiyaye kixauna dasu lfy.

Wata ajiyar zuciya husnah tasauke bayan tagama sauraren dogon bayani daga bakin Rabi ma’aikaciyar gidan data iske,cikin yanayin sanyinta tace “insha Allah zankiyaye Kuma zanbada k’ok’ari sosai wajan aikina,nagode sosai kid’aukeni Kamar k’anwarki Nima inajinki tamkar ‘yar uwata Rabin Dana baro acan HIRJI,idan kikaga nayi Wani kuskure Dan Allah kisanar Dani kafin sulura domin ba abinda natsana Kamar wulak’anci.

“Insha Allah zanrik’eki kamar yanda kika d’aukeni”, dahaka suka rabu kowa Yakama katifarshi bacci yakwashesu.

Tin asuba Rabi tatashi tatada husnah sukayi sallah,Suna gamawa Rabi tace “Toni zanwuce infara gyaran compound kafin sufito ingyara ciki,kimuje innuna maki kitchen dakomai sbd k’arfe bakwai da Rabi Anwar yake tafiya makaranta,Toshi Alokacin zekarya Kuma Zaki dafamai abinda zetafi dashi makaranta”,
Dahaka suka kullo d’akin suka fice zuwa Ainihin cikin gidan,Koda suka iso bakowa a compound d’in gidan saboda har lokacin gari beyi haskeba sosai,Rabi tabud’e musu k’ofar baya suka shiga,kamar dai tsakar gidan haka falon yake shiru har sedama sukayi switch on na globe d’in falon,kana Rabi tawuce daita kicin tanuna mata yanda Ake amfani da komi na kitchen d’in,musamman kayan wuta Wanda batasan amfaninsuba,ak’arshe ta gargad’eta akan kada tasake tajona Wani Abu tabar gurin saboda had’arinsu,dahaka tace mata “ga komai can a frij Idan zakiyi amfani dasu,Nina wuce domin fara aikina kada inmakara”,

“To”, kawai husnah ta amsa jikinta na kyarma tana tunanin kome zata farayi,bawai tana tsoron aikin bane A’a,kawai tana gudun tayi laifi ne su wulak’antata kamar yadda tatsana.

Cikin haka tad’aga Kai takalli jadawalin abubuwan dako wanne keyin breakfast dashi,nafarko Anwar ne,every day data kasance ta makaranta Yana tashi k’arfe bakwai ne daidai,daga bacci,zexama ruwan wankanshi ready,brush d’inshi ma haka da towal d’in daze tsane jikinshi,wannan duka aikin Rabi ne,bayan Tayi mashi wanka Zata fito dashi taimai shafa tabashi praymat yayi sallah,kafin Yagama tafiddo mashi kayan makaranta dakomi sedai tashiryashi Kawai,Suna gama shiri zasu fito mainpalour,to anan Zata sakeshi yawuce zuwa d’akin mamarshi Dan yagaisheta,to kafin yafito ne akesan husnah ta tabbatar tea d’inshi najiranshi a dining da soyayyen bred dak’wai,da farfesun ‘yanciki agefe,yaxama karyawa kawaii zeyi sannan tamik’a mishi kular abincinshi da zab’in abinda yazab’a naranar Wanda zetafi dashi makaranta,Yana karyawa yafita driver yajashi zuwa school,to daganan sunfita batunshi,se Rabi tawuce tagyaro d’akinshi ita Kuma husnah takoma kitchen Dan k’addamar da sauran breakfast na wad’anda Basu tashiba,

Akowacce safiya zee zee da meerah Suna tashi k’arfe takwas ne suyi wanka sushirya makaranta domin dukansu Suna shekararsu tak’arshe a university ne,bayan sunfito dashirinsu zasu gaido mummy sannan suwuce dinning,zasu Sha tea sud’an had’a da bired insunso kenan,se farfesun dazasu ci zuwa Tara Subar gidan zuwa makaranta,domin su idanba weekend ba Basu Wani tsayawa cin abincin kirki,acewarsu idan mutum yacika cin tsiya to ze aje teb’ane harta sakashi Muni,a weekend Kam Daya kasance tare dakowa zasuyi break todole suke d’ansakin jiki suci saboda fad’an mummy injisu,

SE fitinanniyar gidan wato leemat,ayanzu tana 200level a school of nursing dakecan cikin Abuja,yanzu tana hutune Dan haka Bata tashi se wajan 10,Zata fito dashirinta sukarya tare da mummy,ita batada Wani zab’i akullum abinda takeso shi Zata fad’ama cook yagirka mata sannan Tayi breakfast,idan Kuma Taga abinda sauran sukaci yayi daidai dara’ayinta tozata karya dashi kawai batareda k’orafiba,tanada kirki bakamar sauran ‘yan uwantaba dasuke ‘yan wulak’anci da dizga talaka aduk Inda suka ganshi,itadai kawai barta da rashin kunya tak’in k’ari Kuma Hakan yasamo asaline daga yanda daddynsu ya shagwab’ata tin tana k’arama saboda sunan mahaifiyatshi gareta,bugu da k’ari Kuma bayan anhaifeta mummy tadad’e Bata k’ara wata haihuwarba harta fidda Rai sekuma kwatsam Allah yakawo cikin Anwar d’an auta.

Akowanne sati Alhajin gidan yake dawowa weekend,Kuma akowanne b’angare zeyi kwana1 cal tare dasu Dan ganawa dakuma Jin matsalarsu,aduk randa zesauka sashen hajiya kubrah to abincin dayafi so Ake girkamashi wato tuwo da Miyan yauk’i,dasafe Kuma Kunu da k’osai Koda fanke kodai Wani Abu na gargajiya haka se gasashshen Naman sa dayakeci duk safiya,to bayan kowacce me aiki tagama aikinta,zasu kwashi nasu abin Karin suwuce nasu d’akin sukarya kafin suhuta kafin k’arfe d’aya narana ad’ora complete abincin Rana.

Ayauma Koda husnah tabak’unci gidan Hakan takasance,da d’ai-d’ai sukaita Karin kumallon, Alokacin dasu zee zee suka fito domin karyawa,ba abinda k’irjin husnah keyi face bugawa,domin atsorace take datunanin yazasu d’auki girkinta,Koda suka zauna tamatso kusa taduk’a har k’asa tana gaishesu,cikn yatsina meerah tad’ago Kai dak’yar tawaigo sashin datake duk’urshe tadubeta,

Tsakk tatsaya da maganar Dake mak’ale abakinta dalilin tozali da husnah datayi,Sam jiya dare yasa Bata Wani wayi fuskarba sosai saboda Darene Kuma Suna Cikin b’acinran d’aukar masu k’waila da akayi amtsayin wai ‘yar aikinsu,aikuwa cikin shork tacema zee zee “sis what kind of surprise,kalli wannan small girl d’in dama itace tajiya?”, Ta idasa maganar cikin Nuna tsananin mamakin kyau da haiba irinna husnah.

Jin irin karad’in da meerah keyi yasa zee zee d’agowa Dan duban yarinyar datake fad’in wai itace tajiya .

Aikuwa…………

Muje zuwa danjin irin cakwakiyar dazata kasance asauran shafukan Dake cikin rayuwar wannan marainiya.

Ku kasance Dani,Kuma kuci gabada bina danjin yadda Zata kaya acikin wanna k’ayataccen labari👌👌.

Taku AKODAYAUSHE.

HUSNAH MUHAMMAD.

Share
&
Comment.

❤️❤️❤️❤️❤️❤️
SAWUN K’ADDARA.
🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈

Na Husnah Muhammad.

Fage 37&38.

Dahaka tabar driver anan Tayi gaba dazunmar Zata sanar da hajiya idan ta Isa gida,aikuwa tamik’i hanya Tayi ciki danufin gidan hajiya zata,seda Tayi nisa sannan Taga wata kwana tabi ita atunaninta itace kwanar gidan,sbd kusan duka anguwar tsarinta iri d’ayane,tin daga kan titunanta zuwa layikanta da poll poll d’insu duka iri d’ayane,to tariga yawuce layin nagabansu tashiga,Dan hk Tasha kwana abinta dazummar takusa zuwa,

Aikuwa takai har k’arshen layin bataga kalar gate d’in gidanba,yajuyo d’ayan hannun tak’ireshi Shima haka aifa se anan hankalinta yatashi talura kamar ba layin bane domin wancan layin bekai yawan gidaje kamar wannanba,Dan hk Tayo kwana tanajin Wani irin tsoro nashigarta musamman yanda unguwar tad’auke tai tsitt motsin komai sena tsuntsaye,kunsan dai unguwar masu hannu dashuni yanda take ba hayaniyar komi bare wasu tumaki ko Kaji.

Tin kafin tashiga layin ya hangota shikuma zeshiga kwanar gidansu,tacikim glass d’in motar yabi dogayen k’afufuwanta dakallo yanda take d’agasu ta aje anatse yaja hankalinshi yaki muradin kallan fuskar mamallakin wannan sawayen,Dan hk yafasa shiga layin Nasu yarage gudun motar kad’an kad’an Yana binta dagacan nesa,Sam Bata lura dabinta akeba harta shiga kwanar tagama bilayinta tafito datashin hankali afuskarta tana Neman layin dagidan yake.

Yana cikin mota Yana kallanta tanata waige-waige alamun Wani Abu take nema,anashi tunanin kowani Abu tayadda tadawo dabaya tana nema,Dan hk yafito daga motar yanufota tabaya tana gabanshi,
Tana cikin sauri Takoma wajan baba idan betafiba tace mashi yarakota taji ance “excuse me” daga bayanta,aiwani irin juyowa datayi cikin tsoro tatsaya cakk tana addu’a abakinta,murmushi yayi yace “am sorry nabaki tsoro ko,mutum ne ba aljaniba kiketa faman tofeni da addua”.

Ledar hannunta tak’ara damk’ewa tanaja da Baya batare data juyaba,binta yayi kad’an Yana fadin “mekike nemane tind’azu naga kinata waige waige,plss tell me kozan iya taimakonki,”
Girgiza Kai Kawai tayi batayi maganaba taja tatsaya ganin yanata biyota,juyin duniyar nan yayi Amma tak’i magana ak’arshema kuka tasaka masa,Nanfa yarud’e Yana fad’in “soory idan nine kiyi shiru bekamata mekyau kamarki tana zubda hawayeba,plss nabari jeki gidato Inanan Ina tsaronki harki shiga kada Wani yasacemin ke”,

Aijin ya ambaci asaceta seta k’ara volume d’in kukanta,rasa yazeyi yayi da ita se zuwacan wata dabara tafad’omai yajuya Yana fad’in “ok Yi hkr natafi idan nine bakison Gani”,
Ganin dagaskefa yajuya gashi se ita kad’ai afad’in layin yasa tace cikin muryar kuka “gidan Nike nema namanta hanyar ne”.

Wani irin juyowa yayi cikin mamaki yace “kina nufin gidan naku kika manta?” Ya tambayeta dashakku afuskarshi,
D’aga Kai Tayi tana fad’in “ba gidanmu bane aikena Akai kasuwa daga gidan”, matsowa yayi yace “yasunan megidan to ?

Nanma shiru Tayi domin Bata saniba,sexuwa can tace agidan dai akwai leemat da Meera sekuma Rabi cikin masu aikin gidan”,.
Dariya yaji tazo mashi domin seyanzu yafahimci bak’uwace a unguwar Kuma ga gidan datazo,Dan hk yace mata “ok idan kinaso inkaiki gidan kitasaya muyi mgn to,nikuma Muna gama mgn zankaiki har k’ofar gidan’,
D’aga Kai Tayi tanatsu tana saurarenshi yagyara tsayuwa yafara fad’in “tin da nahangeki dagacan naji kin bala’in burgeni daga yanayin tafiyarki kawaii tinkafin inkalli fuskarki mecike dahaiba,inaso kifad’amin gskyr gurin wa kikazo anan unguwar Danna fahimci kedai bak’uwace”,
Narai narai da Ido Tayi hawayen ciki suka zubo kana tace “Dan Allah nidai karakani gidan wlh hjy jirana take naji idan nakai sak’on zamuyi mgn”,
‘Alk’awari” yamik’a mata hannu danufin waisu k’ulla,tanok’e hannunta tana fad’in”Aini nace nayi”.

Yad’aga kafad’a yanuna mata mota yace muje to ba matsala Amma kitabbatar kincika alkawari.

Dahaka tawuce tashiga motar atsorace tana nannad’e jikinta guri guda acikin sit,bece mata komaiba yayi baya da motar yayi reverse yajuya suka koma ainihin layinsu,Suna zuwa kusada gidan tace “laahh saukeni Nan kawaii nama Gane”,

“Inane gidan to?” Yatambayeta.
Dahannu tanuna mashi get d’in tana murmushi tace ‘nagode sosai Amma”, dariya yayi kawaii Yana ganin yarintarta afili yace “to yanzu alk’awarinmu fa yaza’ai”,
Cikin zak’uwa tace “idan nakai sak’on naxo muyi mgn,ita adole setayi mashi wayau tagudu,Wata irin dariyar ‘yan duniya yayi yace “sunana Salim sagir metasa,kefa ko sunanki bazan saniba?, Daidai Nan baba megadi yawangale gate d’in gidan husnah tahangi motar dasukaje kasuwa tashiga gidan,kenan har angyara driver yadawo ita bama takai sak’onba,

Cikin rud’ewa tace “Dan Allah kataimakeni kabud’emin kaga gawanda muke tarecan harya Koma ni inanan,

Dagacan megadi yahango motar Salim Dan hk yak’i kulle gate Yana Jira yawuto tukunna,fahimtar Hakan da Salim yayi yasa yatada motar yawuce cikin gidan kawai,Yana shiga yayi parking yafito yabarta da Baki hangame tana tunanin sudama haka sukeyi a Abuja shiga gidan mutane Bada saninsuba,aikafin tagama tunanin taga megadi ya iso Yana gaishe da Wanda yakawotan,Aikuwa d’iff wuta taji tad’aukemata,Musamman dataji Suna fad’in “Alhaji k’arami ne yau agidan namu,sannu da isowa ai Alhajinma nanan tace”.

Kenan shid’in d’an gidanne,Toya akayi Bata tab’a ganinshiba ko sau d’aya,kod’an Bata fitowane,tana Cikin hk taji hayaniya awajan Dan hk Tayi sauri tabud’e tafito,leemat ce dawasu wad’anda Bata saniba sun mak’alk’ale wannan saurayin sunata ihu,fitowarta yasa duka suka waigo suka dubeta,leemat ce tace “Kai Yaya me wannan takeyi acikin motarka?”

“Waigowa yayi yadubeta yace “kinsantane?”.

Wani irin fari Tayi tace “tab ‘yar aikin mummy mu ceto,tin d’azu naji Mummy nafad’an ta aiketa kasuwa itada driver Zatayo cefanen girkin daddy Amma taje Tayi zamanta Bata dawoba”.

Ido husnah tazaro Tayi Gaba taji Yana cewa “b’acewa Tayi da motarsu ta lakace shine natemaketa,sis leemat anjimma zamuyi wata hark’alla nidake kinjiko”,
Tad’aga Kai tawuce tana cewa “ok se anjuman to”, Tayi tafiyarta tabar sauran ‘yammatan Suna Wani yatsina da bubbud’a hanci su adole ga ‘yayan kishiyoyi.

Husnah nashiga tatarar da hjy afalo zaune tacika tai fam jiranta kawai take ,aikuwa tana shiga tafara fad’a ta Inda take shiga batanan take fitaba,husnah dai hkr taita Bata tasamu dak’yar tafad’amata abnd yafaru kana Tayi shiru tace tawuce kitchen tad’ora tuwon Masara domin Alhaji nakan hanya,dasuri tawuce tafara aiki gadan gadan.

Kafin la’asar d’in kuwa komi nagidan yakammala Suma ‘yan aikinta sun d’ebi nasu abincin sunwuce nasu d’akin sunbar falon da hajiya da yaranta.

Dab da magriba Alhaji ya iso gidan’ cikin tamfatsetsiyar motar shi k’irar Hennessy,driver yagayara parking yafito yabud’ema Alhaji k’ofa,alokacin duka iyalanshi sunfito harabar domin tarbarshi,Koda yafito da fara’a afuskarshi yatari yaran nashi na kowanne b’angare,cikin zakwad’i duk suka tarbeshi Banda hajiyoyin dasuka kamile agefe suna kallan yaran nasu,cikinsu bawadda takalli ‘yar uwarta Amma kowacce taci uban ado kamar zata gasar kyau,itama uwargidansa balaifi danata kyan sedai daga ita har yaranta wulak’ancinsu yatake na yaran hjy kubra,dansu duk Wani talaka Basu daukeshi mutumba,basuma had’a harka dashi domin hatta da ‘yan aikinta duk masu karatune sosai Sam Bata harka da mutanen dasuka shafi Babu ko rashin wayewa,

Wannan dalilin yasa Basu Shan inuwa d’aya da kishiyarta hjy kubra,domin ita idan kacire San ‘yayanta da bak’in kishin tsiya to tanada kirki Kuma Bata cika wulak’anci sosaiba se idan katab’ota sannan zata taka Maka birki.

To dahakan suka rankaya cikin gidan,inda anan sauran yaran kishiyar suka wuce part d’insu tareda mamansu bayan tayi mashi sannu dazuwa,sekuma yayi wanka yahuta ad’akin dayake zuwa anjima za’ahad’u Gaba d’aya awajen dinner ad’ayan part d’in Wanda shine na Alhajin.

Har ciki suka rankayo leemat najikin babanta hjy nata yimata fad’an ga Anwar Nan shine k’aramin duka gidan Amman Sam bekaita sanjikiba,shidai Alhajin murmushi kawai yaketa zubawa Yana fad’in “eh Ina ruwanki da autana ne,Anwar ai autankine,Dan hk kik’yemin yarinya tahuta”.

Dahaka suka k’arasa ciki yasaki leemat tanayi mashi bye bye akan seya fito dinner zasu had’u.

Alhaji nashiga yataradda hjy gefen gado zaune tana tsumayin isowarshi domin tuni ruwan wankanshi yakammala,cikin murmushi ya Isa gareta Yana fad’in “gimbiyar Alhaji metasa ya akayine?”
D’an fari tayi da Ido tana fad’in “kaifa baka girma wlh,plss garuwa can a toilet najiranka go and shower plss,idan kafito……tak’arasa tana dry.

Mak’e kafad’a yayi kamar Wani yaro Yana fad’in”aikinsan bazan iyaba nikad’ai,plss gimbiyata kinsan dai u miss me more than ko,ya Idasa Yana k’wak’umota,zillewa tafara tana dariya harya samu ya cimmata suka fad’a toilet Suna dariya,dahaka nawuto falo nace kugama lafiya.

Acan falo kuwa Alhaji nawucewa ciki leemat tayi hanyar d’akinsu danufin wucewa,Amma caraf taji ankira sunanta dad’an k’arfi,dasauri tawaigo Jin muryar kamarta yaya Salim,aikuwa shine,ta k’walalo idanu waje Dan harta manta rabon data ganshi apart d’insu.

Salim shine babba akaf gidan,shine d’a nafarko agurin Alhaji sagiru,se k’annensa mata guda3,kamardai yaran hajiya kubra duka yaran Alhaji su8 ne,kowacce tanada 4 mata 3namiji 1,to daganan kowacce tatsaya,yazama Anwar shine autan gidan,

Da murmushi Salim ya yafitota domin duk ciki yad’an fisu sauk’in wulak’anci sedai rik’akk’en Dan barikine lamba1,domin kwata kwata ba’anan yatashiba,yasaba da rayuwar turai da tsarinsu dakomai shiyake bi,domin afarkon dawowarshi Nigeria yasha zuwa da budurwa gidan wai dasunan Zata tayashi kwana da d’ebe kewa,tofa seda gaske da Alhaji yaimai zagir-zagir sannan yasaki wannan d’abi’ar,cikin k’ank’anin lokaci yanemi aiki acan nijer yatattara yawuce yakoma can dazama yaci Gaba da b’alla god’iyar iskancinsa,yaro matashi Gakud’i ga ba kwab’awa aikuwa yanda yagadama yakeyi,sedai duk k’arshen wata gida yakeyin weekend.

Koda Suka zauna da leemat cikin hikima dawayo yanuna mata yazo yagaishe da mummy ne, leemat tace “tana ciki itada daddy ko akirata”,
Girgiza Kai yayi yace “no k’yaleta kawai mungaisa anjima wajan dinner,yakk ya karatu,?”

Leemat ta washe Baki suka dinga fira,sezuwa can yake tambayarta cewa “wai sis wannan yarinyar tad’azu gunwa tazo harta b’ace,Aida kin rakata Tinda bak’uwace itad’in,yanzu daban gantaba Allah kad’ai yasan hannun dazata fad’a”,

Shiru tayi tana kallanshi dantama rasa mezata cemashi,seda yace mata “lafiya kika Wani tsareni da Ido?”.

Se Alokacin tace “haba Yaya nicema zan raka ‘yar aiki kasuwa tabd’i sannu”,

Ido yabud’e Yana fad’in “wai kina nufin ‘yar aikice wannan?”, “Bashakka katambayi mummy makaji,kodan kaganta mekyau daita,to wlh k’walelenka”, shiru kawai yayi domin abin yazo masa abazata,domin harga Allah San gaske yake mata,Amma yanzu yasan Koda wasa mom d’inshi bazata amince ya auri ‘yar aikiba,Kai Koba ‘yar aikiba Dama Yana tunanin Taya zemata bayanin daga b’angaren mummyn su leemat tafito,Dan hk kawai yasama ranshi kota yayane seya mallaki surar Jikin yarinyar Nan Dan dagani sweet 16 ce,’yarshila ga kyau tabd’i,sekawai yamik’e yawuce yanama leemat sallama,itakuwa tabishi da Ido tana dry kana tace “zan temakeka badan halinkaba,zanshawo Maka Kanta.

Bayan Alhaji yagama kimtsawa yafita masallaci sukayi ishai kana yashigo yai Shirin shi suka d’unguma zuwa dining wato can asalin part d’inshi,domin al’adar gidance indai Yana gari akullum da daddare to apart d’inshi zasu had’u ayi dinner daganan yaji matsalar kowa da abinda kowa ke buk’ata,idan akagama tattaunawa zuwa k’arfe 10 kowa yawuce makwancinshi,wadda yake b’angarenta Kuma tatsaya takwana anan.

Toyau ma kamar Kullum Hakan takasance seda yayi nak’ da ruwan husnah har Yana tambayar hajiya dacewa “wai wanna tuwon waye hk,kamar inji yatuk’ashi saboda luliyuwa”, hjy takama dry tace “kaidai ci tuwanka zamuyi mgnr dga baya,nasan dai kasan sabira Tayi aure Amma bakanan lokcin da nad’au sabuwar ‘yar aikita”

Dahaka yacigaba dashan yankakkun fruit d’in data had’a mashi,bayan sun kammala suka tattauna abinda suka Saba kana kowa yawatse akabarshi dashi da gimbiyarsa domin ganawa dasuka kwana2 basuyiba .

Tin daga ranan yakasance Salim yadami husnah tahanyar leemai,domin dai itace ‘yar kiranshi wato mekiramai ita har lambun gidansu,Dan saboda tasaurare Shima har Wani dakin fuska tafara samu daga wajan leemat,Dan Wani lokaci hakanan ma setazo taitayimata fira Dan tasaki jiki da ita,to itadai husnah Bata Saba da k’awanceba hasalima Bata iyaba Dan hk sedai taita binta da to idan tana firarta dahaka harta gaji Takoma Inda tafito.

Sosai yatakura husnah Dan Sam halayenshi basuyi mataba,musamman Daya kasance Inya kirata Wani lokacin yadinga mata maganar banza kenan,kokuma yadinga attempting d’in had’a jiki da ita,sedai taita zillewa,gashi yak’i tafiya wai yasamu hutun shekarane shiyasa yadad’e.

Suna Cikin haka watarana period zezo mata tatashi da matsanancin ciwon mara harta kasa fitowa Tahad’a breakfast,har seda Rabi taje tadawo domin tatasheta setaga halin datake ciki tanata murk’ususu akan katifa,
Nanfa hankalinta yatashi tajuya domin Kiran hjy,aikuwa tana Isa falon d’ai-d’ai nan yashigo Domin Kiran leemat takira mashi ita domin jiya Sam k’inyadda Tayi suhad’u gashi zuwa yanzu jiyake dagaske komi zefaru shidai Yana Santa ahaka,Kuma ashirye yake idan tashirya yad’auketa sutai can gurin aikinshi suyi rayuwarsu acan shida ita,kota hanyar Aure ko akasin hk shidai duka d’ayane agurin shi.

Ganin Rabi arud’e yasa yace mata “lafiya Ina leemat?”
Nuni Tayi da hannu tana fad’in “yallab’ai husnah ba lafiya gatacan kwance tana murk’ususu”,

Aijin haka dasauri yajuyo Yana fad’in”Ina take ne husnah,muje inganta meya sameta?”

Suka d’unguma da Rabi zuwa d’akinsu Dan dubo halin datake ciki.

Tofah!Acan b’angaren su Salim Kuma,cikin sauri kaulat d’aya daga cikin k’annenshi mata taruga zuwa d’akin mom tana cewa “Mom!mom!yatafi yauma zokigani ko breakfast d’in beyiba,ai wlh mummy sungama asirce Miki d’a,ko rannan alambun gidannan nahangeshi dashi da ‘yar aikinta,Wama yasani ko can cikin danginsu ne aka k’ullo munafunci Dan Azo asiye maki d’and’a shikenan namijin dakike da aikinga insuka aureshi shikenan gida yazama nasu ko,hmm”.

Tak’arasa tana jijjiga jiki agaban uwartasu,aikuwa tamik’e cikin fusata dajin haushi tana fad’in”muje inga zahiri har k’uryar munafukar yanda zansamu dalilin cimata mutunci akan hidimar d’ana,Dan wlh ba ita nahaifama sakaranba,muje kirakani Shima Indai gsky ne wlh Sena sab’a mashi”,

Suka wuce part d’in hjy kubra suna banbotai,ilai kuwa adai-dai lokacin yatallabo husnah shida Rabi dazummar fitowa da ita Domin kaita asibit,Wanda Sam hjy kubra batasan meke faruwaba……………………….

Kuci gaba da kasancewa Dani maik’aunar ku akodayaushe.

Husnah Muhammad.

 

💕💕💕💕💕💕💕
SAWU K’ADDARA.
❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️.

Na Husnah Muhammad.

Sadaukarwa:nasadaukar da wannan littafi ga aminiyar arziki,abar Alfaharina,oum neehal❤️❤️💕Allah yabar tare yakuma raya mana zuri’a🤲🤲.
Inayinki sosai tawajena💟💟💟.

Fage 39&40.

Sam hajiya kubra batasan me akeba sejin tashin salati datayi dagacan k’uryarta,Jin Hakan yasa tafito cikin sauri Dan ganin hayaniyar Meye afalon,aitin kafin tak’araso takejin tashin bama-bamai daga harshen hjy lubsy,cikin tsananin mamakin abinda yashigo daita sashenta tak’araso gurin.

Turus tatsaya ganin Husnah nannad’e agefen Rabi ga salim agefe tsaye yadafe Kai,ita kuwa gogar tanata surfa bala’i hartana fad’in “Babu shegiyar data Isa tarabani da d’ana,wato anga Kazama mutum ko bari alallab’o Asan hanyar mak’alema,to wlh tinwuri kifarka domin d’ana ba sa’an wannan munafuka mayyar tsiron dangin naku bace,kekuma!
Tajuyo saitin da husnah ke duk’e tana Jin Jiki tace “wlh tallahi rantsuwar d’an musulmi Idan nak’ara Koda ganin kin kalli inuwar d’ana wlh Sena lahantaki,can kinemi matsiyata irinku Amma badai d’an asali kamar wannan ba,shegiya mekama da mayu”.

Adai-dai Nan hjy kubra taji bazata iya cigaba da shanye wannan wulak’ancin ba,domin ita Sam bama tasan meke faruwa ba har wannan tinkiyar Tatako Mata b’angare ba,Dan hka cikin zafin Rai da kishi itama tataso tana fadin “d’afa kikace,A’ina d’an yake aini banga d’aba anan,domin Daya cika d’an dakike fad’i to da bazaki Tako k’afarki kizo Inda ba huruminki agun,da ace kincika uwa toda d’an kawai zakima kira d’aya tak!Kibashi k’wakk’waran kashedi akan abinda kikazo kina hauka Akai,to daganan ne seki banbance shin d’a gareki kokuma d’an Akuyan sake kika Haifa”.

Gaba d’aya bala’i yatashi agurin kowacce nafad’in abinda yazo bakinta,Salim kuwa rasa yanda zeyi yayi kawai seya d’aga waya yakira daddy domin baya gari,yafad’i mashi abnd kefaruwa yak’ara dacewa “daddy gatanan batajin dad’i sosai Amma kwata-kwata bala’insu yak’i bari ataimaketa Kuma nayi masu mgn sunki su saurareni”.

Ta cikin wayar Alhaji yace yasamusu handsfree kana yafara zazzaga fad’a Kuma yace kowacce tawuce nata b’angaren kafin yadawo yaji me Ake ciki,shikuma Salim yad’auketa yakaita asibitin,dahaka aka samu sukad’an lafa,nanfa hjy lubsy tace ma Salim “muddin Nina haifeka toban yarje Maka kakai yarinyar Nan Wani gurinba,ubanda ya jajibota yad’auketa yakaita,wuce kamuje nace shashasha kawai Wanda besan mutuncina ba”,

Cikin rud’ewa Salim yakalli mahaifiyarshi yanamata magiya Amma Sam tace yawuce tace,suna Cikin haka yaga hjy kubra dakanta tazo takama husnah itada Rabi sunwuce alokacin Babu abnd husnah keyi se kuka da takaicin wannan rayuwa tata,shikenan ita duk Inda tasauka se bala’i yatashi to kodai dagaskene itad’in mayyace kokuma Aljana,dawannan kukan suka k’arasa Wani asibiti anan cikin unguwar,

Acan kuwa leemat takora su hjy da bak’ar rashin kunyarta hartana cemusu “Ass Ass kaji kuwuce kuma Aure da Yaya Salim da ‘yar aiki kamar and’aura sedai kumutu ‘yan Bakin ciki kawaii”, bawanda yatankata sanin halin rashin kunya irin tata,Kuma daddy yadawo yabi bayanta duk Wanda tace yamata daddy ba ragamai zeyiba Dan hk suka wuce ba Wanda yatankata.

Bayan anyi ma husnah awo dakomai likita yayi mata allura yabada mgn,Dama ciwan matar tane nakowanne month data sabayi,sedai wata2 Nan Yana zuwa mata da wahalar datafi tabaya shiyasa Ake ganemata,Dama amakaranta Ake Bata magani,to data dawo Kuma yayanta ke amso mata,yanzu Kuma duka batada wannan gatan se yanda rayuwa tayi da ita,

Bayan sun dawo gida hjy tace taje tayi wanka tacanza kaya bari taje tasa ayo masu order abinci daga gidan’ abinci Tinda itace meyi Kuma ba lfy.
Tashiga dak’yar tayi wanka tashirya Alokacin marar tad’an lafa mata,tana zama hjy tashigo tazo tazauna kusa daita tana Fad’in “sannu yajikin?”.
“Dasauk’i sosai “, ta amsa tana me duk’ar dakanta k’asa,hajiya takira sunanta taname Fadin “d’agonan zamuyi mgn Dake husnah”,
Tad’ago kanta Amma duk dahakan idanta ak’asa yake tanatsu tana saurarenta,hjy tacigaba dafadin “inaso kigaya Mani gaskiyar abinda ke tsakaninki da Salim yaran mijinah,Kuma yaushe Kuka fara soyayyah bansaniba?”.

Zamowa tayi k’asa taduk’a gefen hjyr idanta cikeda k’walla tace “wallahi hjy bantab’a daurararshiba,hasalima tin ranar………………..,
Tafad’a mata tin asalin had’uwar su dashi aranar data b’ata daga ksw,Sannan tace “Kuma wlh koyasa aunty leemat takirani bance mashi komai har yagama maganganunshi yace intaho,Dan Allah hjy kitaimakamin kada kikoreni wlh Banda laifin komai kiyi hkr”, tak’arasa tana Kuka sosai gwanin ban tausayi,

Hjy tasaki ajiyar zcy tace “ke kina sanshi aranki”, dasauri tagirgiza Kai tana Fad’in “Wlh A’a Nisam halinshi beminba”,
Nanfa hjy kubra tace “tom niyanzu bazan Yanke hukunciba tinda Abu yazo da hatsaniya,Kuma har megidan yariga yaji komai,Dan hk dole semun saurari dawowarshi munji hukuncin Daya Yanke tukunna kafin ince Wani Abu,kedai kirik’e gaskiyarki kawai aduk lokacin da Alhaji yadawo”, tamik’e tana Fad’in”kikwanta kihuta gobe zamu k’arasa maganar,dahaka tafita ad’akin tawuce ciki.

Cikin kwana2 Husnah tasamu sauk’i sedai zullumin mezeje yadawo akan zamanta gidan,Kuma harga Allah tafarajin dad’in aikin musamman Daya kasance ba aikin wahala bane,Aikine Wanda tasaba dashi Dan hk bemata wahala,Amma yanzu batabbacin cigaba dayinshi agareta,yanzu Ina zata nufa idan hkn tafaru,domin Tinda tazo sau d’aya sukayi waya da aunty Jamsy Shima itace tarok’i hjy akan takira mata ita,to daga ranarma ko Ankira wayar akashe akecewa,Kuma du k’arshen wata hjy zata cemata anturo mata kud’inta,alissafinta sau3 kenan ana turamata kud’inta wajan aunty Jamsy domin tadinga Tara mata kud’in makaranta.

 

Acikin zaman sauraren dawowar Alhaji Wani satin tana kitchen tana aiki hajiya tashigo dawaya akunnenta tanayi tanad’an rusunawa kad’an alamun girmamawa gawanda take wayar dashi kamar suna ganin juna tana fad’in “eh wlh hjy sun iso tin satin daya wuce,nama nemi layinki bansamuba,dahar inacewa k’ila Sena Tako dakaina kawo Miki sak’on”, tad’anyi shiru tana saurare zuwa can Kuma tace “Ah’ah’ah eh dole abuk’aceshi musamman tinda Dan hkan aka kawoshi,to ba matsala zanturo Wata amintacciyar ‘yar aikina da driver goben dasafe seta kawo, to nagode hjy Allah yabar zumunci”.

Takashe wayar tana murmushi alamun taji dad’in yin wayar, tad’ago tadubi husnah tace “ba’agama aikinba”, tace “eh hajiya nadai kusa doyar yarage kawai indaka in mulmula sakwarar”,

Tace “to kinaji ko,gobe idan Allah yakaimu dasafe zan aikeki can gidan’ wata k’awata Kuma uwar d’akina kikaimata Sak’o keda driver,Kuma bansan wasa kokuma kije kishirma Wani wajan,har gidan za’a kaiki kishiga kimik’a kifito kutaho gida”.

Tai sunkui dakai tace “Insha Allah hajiya bazaki Sami matsalaba”.

Hjy tajuya Tayi ciki ita Kuma tacigaba da aikinta.

Bari mulek’a Yaya sagir muga wacce wainar yake toyawa👀👀.

K’ASAR LONDON US.

Cikin watanninan dasuka shud’e Babu abinda yazama medad’i agurin Yaya sagir face nasarar dayake samu tafuskar karatunshi dakuma d’aukaka acikin turawan k’asar,sosai ya shahara acikin mates d’insu kasancewarshi d’alibi mek’wazo da hazak’a ta karatu,sedaifa duk wannan nasarar farin cikinshi ragaggene nasamun labaran Abinda husnah ke aikatawa Acan gida,

Babu Abinda yake bala’in d’aure mishikai irin yanda tak’i bari ko sau D’aya suyi magana,kwata-kwata ayanda labarin kezuwar mishi Babu Wanda yaisa Yanzu yafad’a ma husnah taji,ak’arshema cemishi Akai setayi sati Batazo gida ba,
Seranda tagadama talek’o tace wai tazo d’aukar Wani abune,har turo hukuma yayi gidan yace duk sanda suka sameta sukame mashi ita sutai daita cells Acan dole tayadda tayi magana dashi ko sau d’ayane,Amma duk sanda sukazo maganar d’ayace batazo gidanba yau kokuma jiya jiyannan tabar gidan,dahaka Suma ‘yan sandan ta shashantar dasu har suka gaji suka Dena zuwa nemanta,yazama koya kirasu sedai suyimai k’aryar sunje Bata gidan,can Kuma gidan inya kira waya yatambaya hansai tace mishi yanzuma sukabar k’ofar gidan wato su ‘yansandan,dahaka sukaita Jamai kud’i abanza harya gaji yadena kiransu.

Ga exam na matsowa dole yamaida hankalunshi Yakama karatu gadan-gadan Dan yasamu yatsallake wannan sirad’in nak’arshe,Wanda dagashi se maganar Aiki da babban kwali insha Allah,sedaifa yaci burin duk randa yadawo k’asarnan se husnah tasan batada hankali,Dan seya koya Mata darasi akan wula’antamai rayuwarta datayi bayan duk fad’i tashin dayake tayi akanta,Kuma duk Wanda yasamu yanada hannu akan zugata kokuma saurayin daya hure Mata kunne wlh seya d’aureshi har igiya tai rara wannan Alk’awari ne yad’aukarma kanshi…

Tose muce Allah yadawo mana dakai lafiya Yaya sagir.

 

(BUDAGG’I ESTATE),Abujah cityy.

Wani irin katafaren estate ne Dake can Cikin asalin birnin Abujah,Asalin estate d’in wani mashahurin hamshakin mekud’i ne yafara ginashi mesuna Alhaji Abdullahi BUDAGG’I, Asalin d’an nijeria ne, anhaifeshi Awani k’auye dakenan cikin Abuja,asalin iyayenshi daga yankin larabawa Suka fito,yau da kullum dakuma fatauci yakawosu k’asar nijeria dazama har Allah yayi masu arzik’i shida iyayenshi,sannu tashi harya fara girma amma mahaifiyarshi ko b’ari Bata k’ara yiba,cikin iKon Allah arzik’in babanshi yaci gaba da hab’aka har yayi suna sosai ak’auyen Daya sauka,alokacin daya kammala makarantar secondary se babanshi yafara janshi aharkar kasuwancinshi agefe guda Kuma Yana cigaba da karatunshi,gab daze kammala degree d’inshi na2 mahaifanshi sukayi wata tafiya menisa ajirgin k’asa anan Ubangiji ya k’addaro masu hatsari duka jirgin bawanda yafita.

Wannan mutuwar tagirgiza Abdullahi k’warai har yakwanta matsanancin ciwo,dak’yar dataimakon abokan arzik’i suka shawo kanshi yad’ora daga inda mahaifinshi yatsaya,Dan dole ya ajiye karatu daga deggre na2 yafad’a harkar kasuwanci sosai Dan habb’aka dukiyar da aka Tara dominshi metarin yawa .

Cikin iKon Allah kafin Wani lokaci dukiyar ta habb’aka sosai har yazama Yana Neman abokin tayashi harkokin business d’in,da iKon Allah dataimakon Wani Aminin babanshi Daya zama tamkar uba agareshi bayan rasa nashi iyayen dayayi,yasamu yadinga cimma manyan kadarori da kamfanika,alokacinne Kuma yak’yalla Ido ya hango babbar d’iyarshi Aminin baban nashi me suna Asama’u cikin k’ank’anin lokaci suka daidaita kansu akad’aura masu Aure.

Zamansu suke cikin aminci da mutunta juna uwa Uba soyayyar dasukema junansu harta wuce misali,d’aya Bai iya jurar b’acin ran d’aya,ahaka har suka haifi d’ansu nafarko mesuna Umar,suka cigaba da renanshi cikin aminci da kulawa,alokacin ita Asamu tana makarantane tana karatun nursing,idan zatatai takan aje Umar gidansu wajan kakanninshi seta dawo se’a maidashi kokuma tabiyo tad’aukeshi.

Rayuwa taci gaba dajuyawa haka har aka yaye Umar,alokacinne Wani babban kasuwanicin gwal da dutse me daraja Yafad’o ma Abdullahi tahanyar Wani abokin siye da siyarwa nashi dayake k’asar cameroo,yazo mashi da shawara akan koze had’a da harkar domin tanaci sosai awannan zamani dasuke shiga, Abdullahi yace to zeyi shawara da baffanshi Kuma sirikinshi tukunna.

Koda yasameshi da maganar seya bashi goyon baya sosai harya Nuna mashi cewa “shi zamani rigane,tinda da zamani abin yashigo Toka gwada Saka rigarshi kaima,Hakan wata hanyace ta fad’ad’a kasuwancinka kaima dakuma shigo dashi zamani”.
Da wannan shawarar Abdullahi yafara tab’a harkar gwala-gwalai tahanyar abokinshi dakecan k’asar Cameroon,ahaka suka dinga juyawa har watarana Wani babban deal yafad’o Wanda dole sedai manyan masu kud’i suhad’a hannu da hannu su afkamai.

Wata rijiyace tazallar man fetur da gwal ak’ark’ashinta aka gano acan cikin k’asar Cameroon,to alissafin abinda za’a iya cimma wannan rijiyar man kafin ma atab’o gwal d’in nak’asanta,kud’in yazarcema tunanin me hankali,Dan hk dole manyan k’asar suka zauna shawara akan anemi taimakon Wasu manyan masu kud’in daga wata k’asar se’a had’a hannu da hannu asamu acimma wannan ma’adanai.

To acikin manyan k’asar akwai abokin kasuwancin Abdullahi Dan haka yasameshi dawannan deal,Musamman gwal d’in Dake k’asa,to Koda yaji wannan harka Kuma yatabbatar dasamun alkhairi sosai aciki seya samu sirikinshi sukai shawara,Amma dole da buk’atar seyana kusa domin zuba mak’udan kud’i haka dole adokan cema sedakai akusa sbd halin mutanenmu nayanzu.

Toda haka yashirya tafiya shikad’ai k’asar Cameroon,Koda yasauka cikin kwanaki k’alilan Suka fara tsara yadda komai zekasance,Daga k’arshe Suka aje mgn akan zebada kaso2 cikin 3 nakud’in su ‘yan k’asar zasu tatse man Dake saman rijiyar shikuma gwal d’in k’asa nashine,afarko yaji tsoron harkar sbd kusan Rabin dukiyarshi zekwashe yazubama su,Daga baya Kuma yatsaida Allah d’aya yasa hannu akan takardar wannan deal.

Cikin lokaci k’alilan aiki yakankama,Wanda adokan k’asar dole duk Wanda zemallaki wannan abinda kecikin hak’on Toya zama mazaunin wannan k’asa,Dan hka hankalin Abdullahi yatashi yadawo yazanta da baffansa,nantake ya amince yace su shirya shida iyalanshi sukoma nawani lokacine,idan harya mallaki rijiyar akwai yanda za’ai tinda Alokacin tariga tazama tashi,Daga haka Suka fara Shirin barin k’asar shida Asama’u shi da Umar d’anshi,

Kwanci tashi bawuya gurin Allah sun koma ba dad’ewa Allah yabama Asama’u Wani cikin me kaulayin tsiya,danma lokacin takammala karatunta tana gida .

Cikin iKon Allah lokacin da wannan aiki yayi Nisa Asam’u tak’ara santalo yaronta namiji,akasa mishi Suna Yusuf,alokacin Tayi kuka kamar ba gobe sbd rashin dangi akusa,sedai aka turo mata k’anwarta daga can Nigeria ta tayata zama har Tayi arba’in.

Bayan nanne aikin Mai yakusa kammala afara nashi nakanshi wato aikin hak’o gwal d’inshi domin fara sarrafashi.

 

Acikin wata na biyar bayan haihuwarta aka kammala wancan aikin rijiya tazama tashi halak malak sauran shi kawai fara hak’ar wannan dukiya,nanfa aka shirya gagarumin biki Dan celebration na wannan abin frnck Daya samu duk Wani Wanda ya dangan ceshi,acikin wannan murnar Wani dattijo d’an k’asar Cameroon yatashi Yana wasashi da kurantashi da kalamai irin na al’adarsu ta can,acikin wannan kalamaine yakirashi da wata kalma ta (BUDAGGI) Wato tana nufin (d’aya da Ake haihuwa acikin Wani k’arni ko zamani), Wanda yake dad’ewa sunanshi na bibiyar zuri’arshi kokuma Wani k’arni dazezo Nan gaba sbd wata baiwa da Allah yayi mashi.

To anan wannan kalma tasamo asali ta budagg’i daga k’asar Cameroon,seya zama yayi shuhura da sunan,duk Wani Wanda Wanda ze kirashi to ze had’ane da wannan kalma ta jinjina da Nuna shid’in me baiwa ne.

Ana cikin fara aikin hak’on wannan dukiya tashi yazama duk kusan fad’in k’asashe na kewayen sun San da zamanshi da kuma irin tarin dukiyar Daya mallaka,alokacin babban d’anshi Umar farouk bewuce shekara 7 ba aduniya.

Acikin haka aka samu wata hatsabibiya acan gefe tana kallan irin rayuwar dayake gudanarwa tajin dad’i da walwala da iyalinshi…….

Muje zuwa.
Husnah Muhammad.

Plss share & comments.

Leave a Reply

Back to top button