Hausa NovelsSakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 42

Sponsored Links

SAKAYAH

 

42

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

 

*Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn, masu cewa wai sun goda suga number’n nayine, ko kuma a’a bari dai in na shirya zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuɗin bai cikaba tukun sai sun cika, ko kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh in ba iyayiba ai duk nisan state da kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen wajema. Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba ku daina min mgnar ku bari sai kun shirya,kada kizo ki ɓata min lokaci a banza, wlh ni na tsani harkar karanta, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuɗin kaya ga account no ga numberta ai sai ki biya kawai kafin kimin mgn. Tunda dai ga alamominshi da duk illar da yakeyi na faɗi in kina dashi faƙat in babu kada ki wani zo kice min bayani dan ko kinzo iya bayanin da zan miki kenan*

Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha’awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni’ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al’ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban  lissafa. Sune manyan alamomin infection.

Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.

Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni’ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya, zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.

KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni’imomin ki, da sha’awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA’AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau,  duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha’awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor’s suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.

INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai Maganin na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi’izinillahi ta’ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma’ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya’ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER’N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA’AURATA.

 

 

Da ƙarfi yayi baya ya zame luuuuu  yana faɗin.

“JJJ”.yana rufe bakinsa ya sume.

Ɗaya daga cikin perciens dake zaune a reception ne yayi saurin miƙewa tare da kallon Moddibo dake kwance babu numfashi atare dashi yace.

“Dr Jameel ya suma fa”.

Ya faɗa tare da ƙara sawa kan Moddibo cike da damuwa yace.

“Bawan Allah!,Bawan Allah!!”.

Ina ko motsa wa Moddibo baiyi ba.

Juyawa Dr Jameel Yayi tare da kallon security cikin fushi yace.

“Kun sanshi?”.

Atsorace security ya kalli Moddibo dake kwance kana ya kalli Dr Jameel Murya na rawa yace.

“Wallahi Sir munyi iya bakin ƙoƙarin amma mun kasa motarka na shiga shima ya shiga da ganin yanda yake tuƙi yasa nayi ƙoƙarin hanasa badan na kauceba bige ni zaiyi”.

Ɗaya matar dake tsaye cikin tashin hankali tace.

“Dr dan Allah katemaka min ƴata na cikin hatsari katemaki Rayuwar ta”.

Jin haka yasa ya juya tare da take step zuwa inda Office dinsa yake mutumin dake tsaye kan Moddibo yayi saurin Kallonsa cike da damuwa yace.

“Dr Jameel suma yayi fa a duba al’amarin sa shima yana bukatar temakon gaggawa”.

Tsayawa Dr Jameel Yayi ya rasa shin me zaiyi cikin raunin matar dake biye dashi tace.

“Dr ƴata dan Allah”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe kana ya kalli sauran Norses ɗin yace.

“Ku kula dashi”.

cikin sassarfa ya nufi Office ɗin sa yana shiga ya cire Jacket ɗin sa ya maƙala ajikin kujera ya fita kai tsaye Theater room ya nufa yana shiga ya samu angama shiryata kawai shi ake jira Atake ya fara aiki cike da tsananin ƙwarewa da iyawa na cikakkun likitoci ya fara mata C’S.

 

Acan ɗakin da Moddibo ke kwance kuwa baki ɗaya Norses ɗin sunyi iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin numfashinsa ya dawo amma abin ya faskara da alama ya tafi suma da wani ɗan ciwone dake tare dashi.

Dr Jameel kuwa sai bayan awa ɗaya ya fito daga Theater room Agajiye ya fito domin mata biyu yayiwa Cs ɗin, Norses na biye dashi abaya tsaye ya hango Mahaifiyar Yarinyar atsaye abakin wajen kallonta yayi tare da sakar mata da murmushi kana yace.

“Alhamdulillah ancire yaro yana lafiya kuma Insha Allah itama tana lafiya”.

Cikin sauri matar ta sauƙe ajiyar zuciya kana da murmushi afuskarta tace.

“Alhamdulillah”.

Dai-dai lokacin Norses suka turo gadon matar na kwance akai wani Corridor suka nufa yanayin tsarin asibitin komai na musamman ne,  ɗaya daga cikin Norse da sukayi Operation ne ta fito rungume da jariri kana ta miƙawa matar dake tsaye da murmushi afuskarta tace.

“Alhamdulillah ga Baby boy nan lafiyarsa ƙalau”.

Murmushi matar tayi kana tace.

“Alhamdulillah Allah Nagode maka”.

Dr Jameel kuwa kai tsaye Office din sa ya nufa cikin sauri Norse dake kan Moddibo ta ɗago ta kalli Dr Jameel da alamun damuwa afuskarta tace.

“Dr har ka fito?”.

Kai ya gyaɗa mata alamar Eh.

Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

“Sir Wallahi har yanzu fa mutumin bai farfaɗo ba Dr kazo ka dubasa nayi ƙoƙari Inje in Samu Dr Mubarak ya dubasa to kuma already ya tafi”.

Numfashi ya fesar kana yaja siririn tsaki Ido ya zuba mata kana yace.

“Ina Dr Eshaa?”.

Cikin sanyin murya tace.

“Itama bata nan tun Azahar ta fita tace suna da biki”.

Dafe kai yayi kana yace.

“Kenan ba Dr acikin asibitin?”.

Cikin sauri ta girgiza kai tare da cewa.

“A’a akwai perciens ne sunyi yawa akansa shiryasa nace basai na masa magana ba bari inzo wajenka”.

Tsaki yaja kana yace.

“Toh”,Yana ƙoƙarin sauƙa ɗaya daga cikin Norses da sukayi C’S ta kallesa cikin wani narkakkiyar murya tace.

“Sir”.

Cak ya tsaya tare da juyawa ya kalleta wani irin juya masa Idanu tayi tare da kashe masa ido kana ta hura masa kiss.

Dogon numfashi yaja tare da ƙanƙance Idanunsa kana ya narkar da muryarsa yace.

“Ohhh My Baby kasheni kike sonyi ko?”.

Bai jira cewar taba ya juya ya nufi ƙasa yabi bayan Norses data kirasa kana ita kuma wacce ya kira da Baby ta biyo bayansa.

Yana shiga ɗakin da Moddibo ke kwance ya tsaya ya zuba masa ido yana karewa fuskar bawan Allah da karo na farko kenan arayuwar sa ya fara Kallonsa, sai dai tabbas komai nashi baida banbanci dana Ibrahim, toh shin waye shi din.

Ɗaya daga cikin Norses dake ɗakin ne tace.

“Sir ataima ka mishi ya daɗe da suma fa yanzu kusan awa ɗaya da rabi kenan fa yana sume”.

Nunfashi ya fesar tare da sunkuyowa kansa cike da tsantsar ƙwarewa da iyawa da kuma bijinta na ainihin ƙwarerren Likita wanda yasan aikinsa In and Out ahankali ya kamo tafin hannunsa ya fara murzawa kana ya kamo tafin ƙafarsa yana murzawa yana danna jijiyoyin tafin ƙafarsa yana murzawa da sauri ya kai kimanin minti goma yana murzawa kafin ya koma murza jijiyoyin bayan wuyansa ahankali ya sunkuya kansa ya ɗaura bakinsa akan hancinsa ya fesa masa numfashin tare da zuƙo nashi ahankali.

 

Hannu ya miƙawa Norse dake gefensa cikin wani salo ta ɗaura tafin hannunta akan nasa ta riƙe tana murzawa.

Ahankali ya juya ya kalleta kana cikin wani shu’umin murya yace.

“Ruwa zaki bani ba hannun ki ba”.

Yanayin da yayi magana kaɗai zai tabbatar maka da cewa shi ɗin shu’umin Namiji ne na ƙarshen zamani mai cike da shu’uman da sanin barikanci.

Kai ta gyaɗa kana ta fita kai tsaye Office ɗinsa ta nufa ta ɗauko masa goran ruwa ta dawo ta miƙa masa karɓa yayi kana yasa atafin hannunsa ya watsawa Moddibo ruwan da ƙarfi dogon numfashi Moddibo yaja kana cikin wata raunan’niyar murya yace.

“Ummi naga J ɗin mu Ummi J ɗinmu bai mutu ba Ummi ga Jameelun ki bai mutu ba”. Yayi mgnar da larabci kasancewar dashi ya sume a bakinsa.

Baki ɗaya ido Norses ɗin suka zuba masa musamman wacce Dr Jameel ya kira da Baby wani irin kallo take bin ilahirin jikinsa dashi musamman Lips ɗinsa da yake tattarewa yayi pinch dashi.

 

Dr Jameel kuwa ahankali ya ɗago Ido ya kalleta cikin wani narkakkiyar murya yace.

“Ya dai Baby wani irin kallo ne wannan kada fa ki cinye sa yana kwance agadon asibiti”.

Sai alokacin ta lura da kallon ƙurullan da take bin Moddibo dashi numfashi ta fesar kana ta narkar da murya tace.

“Masha Allah kaga madaran kyau babu algus ga haiba da kamala”.

Harara ya watsa mata cikin muryarsa dake ɗauke da kishi yace.

“Ya fini ne?”.

Kallonsa tayi kana ta kalli Moddibo tace.

“Hmmm in dai kyaune da ƙasaita ya fika sai dai kuma ai kaine nawa kuma jaruntarka na sani”.

Ɗaya Norse data kirasa ta watsa masa Harara kana ta taɓe baki.

 

Moddibo kuwa ba tare daya dawo hayyacinsa ba ya cigaba da cewa.

“Ummi ga Jameelun ki ki daina kuka Abba ga J ɗina na gane J ɗina”.

Maganar Moddibo da Dr Jameel yaji shi yasa ya janyo hankalin sa ahankali ya sunkuya da kansa daidai kunne Moddibo yace.

“Ikon Allah”.

Moddibo kuwa Jin sautin Muryan ma sak ta J ɗinsa akunnensa yasa  sannu Ahankali ya fara buɗe idanunsa domin ba zai taɓa mantawa da muryarsa ba akan Dr Jameel da har zuwa lokacin ke durƙushe kansa ya buɗe idanunsa cikin wani irin sauri ya yunƙura ya zauna Atsakiyar gadon kana ya janyo Dr Jameel ya fashe da wani irin kuka yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ke rawa.

Lokaci ɗaya kuma jikin Norses dake ta faman rawan kai da zumiɗin ganin kyawunsa jikinsu yayi masifar sanyi ganin yanda Kamilin mutum kana Matashi mai jini ajiki ke kuka Dr Jameel ma Baki ɗaya jikinsa ya mutu ganin yanda mutum dake kiranshi da J ke kuka tamkar mace.

 

Cikin rauni da tarin damuwa kana da kuka da yaci ƙarfinsa ya cigaba da cewa.

“Alhamdulillah Allah Nagode maka Ubangiji ya cika min burina Allah na gode maka dama J kana raye?”.

Ya ida maganar tare da janye jikinsa daga na Dr Jameelu ya tallafe kuncinsa still hawaye na bin fuskarsa kana muryarsa na rawa yace.

“J”.

Cikin sauri ya sake Rungume Dr Jameel Araunane yace.

“Ummi! Ina kike? Yau ina Abbana? Ummi ina kuke ga J ɗina Ummi J ɗina bai rasu ba Ummi gawar wani aka nuna mana akace J ne Ummi J ɗina bai rasu ba Ummi”.

 

Dr Jameel kuwa cikin sauri da tsoro ya janye jikinsa daga na Moddibo kana ya nuna sa da yatsa muryarsa na rawa yace.

“Bawan Allah ni ban sanka ba nifa ba J ɗinka nan da kake faɗa bane”.

Miƙewa Moddibo yayi ido cikin ido ya kallesa kana yace.

“J nine kake cewa baka sani ba!?,A.J ɗin ka nefa”.

Ya ida maganar kana baki daya ilahirin jikinsa rawa yake yayinda maransa ke cigaba da damƙarsa cikin rauni ya kalli Dr Jameel daya zuba masa ido kana yace.

“A.J ɗinka nefa Amma kake cewa baka sani ba”.

Ajiyar zuciya Dr Jameel ya sauƙe tare da fesar da numfashi cikin gaskiya da gaskiya yace.

“Wallahi ban sanka bani ban taɓa ganin ka ba”.

Cikin tsanananin tashin hankali tsoro da kiɗima Moddibo yace.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n J kaji tsoron Allah ka daina rantsuwa nine kake cewa baka sani ba J Moddibo kane fa Jameelu Nine zaka ce baka saniba!?”.

Cikin yanayin rashin fahimta Dr Jameel ya Girgiza kansa kana yace.

“Wallahi ban sanka ba ni ban taɓa ganinka ba”.

Araunane Moddibo ya tsira masa idanu kana yace.

“Baka Sanni ba J kace baka taɓa kallona ba?”.

Ya ƙarasa maganar tare dasa hannu ya shafa jikinsa jin babu waya yasa yayi saurin kallon Dr Jameel yace.

“Ina wayata?”.

Araunane ya sake kallon yace.

“J naji baka sanni ba domin Ni Aminine daya cancanci ka wurgar ko? to amma J Ummi fa Ummi ma baka santa ba?”.

Kai Dr Jameel ya girgiza kana yace.

“Wacece Ummi kuma?”.

Zare ido Moddibo yayi Aƙiɗime yace.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n J Ummi mahaifiyar kace baka sani ba!?”.

Ahankali Dr Jameel ya sunkuyar da kansa ƙasa kana ya ɗago ya kalli Moddibo yace.

“Ni kuma Mahaifiyata?,Gaskiya dai inaga wannan kana da Lalurar ƙwaƙwalwa!”.

Cikin sauri Moddibo ya zauna abakin gadon ya dafe kansa da hannu bibbiyu muryarsa na rawa yace.

“J ni kake cewa ina da matsalar ƙwaƙwalwa yayi kyau J shin wani irin laifi muka yi maka aduniya da muka cancanci irin wannan hukuncin agareka me muka yi maka mai tsanani da zaka hukunta mu ta wannan hanyar”.

Kallonsa kawai Norse din keyi cike da tausayawa.

Cikin rauni ya cigaba da cewa.

“J Ni kake jifa da kalmar cewa ƙwaƙwalwa ta ba ɗaya bane, to koma ƙwaƙwalwa ta takasance tana da matsala J rashinka akusa damu ne da kalmar da aka faɗa mana cewa ka rasune ya jefamu cikin wannan halin”.

Kallon ikon Allah kawai Dr Jameel yake kana yana kallon yanda hawaye ke bin kuncin Moddibo.

Cikin sanyi da rauni Moddibo ya cigaba da cewa.

“J sannan koda na kasance mai taɓin hankali katari da gawarka da akayi da gawarka akace ka rasu shiya jawowa ƙwaƙwalwata matsala!”.

 

Ahankali Dr Jameel ya matsa kusa dashi Asanyaye yace.

“Bawan Allah ka nutsu ni bansan kaba ban san mekake nufi ba”.

Cikin fushi Moddibo yace.

“J ƙarya kake”.

Miƙewa Dr Jameel yayi tare da ɗage kafaɗa yace.

“Ok toh shikenan”.

Ya ƙarasa maganar tare da ficewa Norses suka mara masa baya.

 

Cikin sauri Moddibo ya mike ya fita kai tsaye wajen motarsa ya nufa ya ɗauki wayarsa ya dawo reception din ya kunna wayarsa dake ɗauke da hotonsa dana M Jameel ya nuna masa kana yace.

“Yanzu wannan ka mantani ai gaka gani”.

Kallon fuskar wayar Norses ɗin sukayi Wacce Dr Jameel ya Kira da Baby tayi saurin buɗe baki cike da Mamaki ta kalli Dr Jameel kana tace.

“Iyee Dr da gaske fa kaine”.

Harara ya watsa mata kana yace.

“Kuma dai baku da hankali”.

Ahankali Moddibo ya juya da fuskar wayarsa nan yaga takwas tara cikin sauri yace.

“Yah salam banyi maghariba banyi Isha’i ba”.

Sai alokacin Dr Jameel ya tuna da batun sallah kallon Moddibo yayi da duk kiɗima da ruɗu kana da gigita dake jikin mutumin amma ga mamakinsa sai ya juya ya nufi Masallacin dake cikin Hospital Kai tsaye Tap dake wajen Moddibo ya nufa ya ɗaura alwala har zai shiga Masallacin ya tsaya ya juya tare da kallon Dr Jameel da still Idanunsa ke kansa.

Kai ya jinjina muryarsa na rawa yace.

“Yayi kyau J nine kake cewa baka gane ba zan shiga Masallaci in faɗawa Ubangiji duk abinda ke damuna”.

Ya ida maganar tare da shiga Masallaci nunfashi Dr Jameel ya fesar kana shima yayi  alwala ya nufi masallaci.

 

Yana shiga Masallaci yayi maghariba da Isha’i  yana idarwa idanunsa suka sauƙa kan Moddibo daya tsira masa ido.

Cikin sanyin murya da rauni Moddibo yace.

“J Nine kake cewa baka gane ba”.

Kai Dr Jameel ya Girgiza cikin gaskiya da gaskiya yace.

“Wallahi bawan Allah Ni bansan kaba ban kuma gane kaba kadena cemin J Ni sunana Jameel”.

Cikin sauri Moddibo ya katsesa kana yace.

“Aina sani dama sunan ka Jameel ne”.

Dr Jameel kuwa jin wayarsa na ringing yasa ya Mike ya fita kai tsaye cikin Hospital ya nufa duba matar daya mata Theater Yana shiga Moddibo yabi bayansa bayan ya gama duba ta yafita ya kalli Moddibo kana yace.

“Yanzu ko inda zanyi aikin ma sai kabini har ciki?”.

Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.

“Eh dole sai na bika J”.

Cikin alamun gajiyawa Dr Jameel yace.

“Toh kabarni mana ina sarara”.

Kai Moddibo ya Girgiza cikin tsaresa da ido yace.

“Ai tsakanina da kai babu sararawa sai lokacin dana danƙa ka ahannun Ummi da Abba”.

 

Siririn tsaki Dr Jameel yaja kana ya juya yabar wajen kai tsaye Office ɗinsa ya nufa dai-dai lokacin Baby ta shiga.

Tana shiga ta tsaya daga bayansa bayan ya zauna akan kujera cike da salo ta sanya tafin hannunta tashafa sajensa zuwa kan Lips ɗinsa.

Cike da shu’uman ci ya lumshe Idanunsa cikin wata narkakkiyar murya mai tarwatsa lissafin mata yace.

“Ohhhh My Baby don’t kill me. Cikon Office muke fa, mu tafi gida Please I need you”.

Shagwaɓe Murya tayi tare dayi masa fari da ido tace.

“But Dr Ina da Nightduty”.

Wani kallo ya bita dashi yana shinshina wuyarta kana yace.

“Toh yanzu yakike so inyi”.

Ido ta kashe masa tare da ɗage gira tace.

“Duk yanda kace haka za ayi?”.

Cike da tsanananin Mamaki Moddibo ke kallonsu Aruɗe yace.

“J wacece wannan kuma kasan abinda kake yi kuwa?”.

Cikin tsawa ya kalli Baby kana yace.

“Ke ki sake shi baki da hankali ne?”.

Juyawa Dr Jameel Yayi tare da kallon Moddibo Up anda down Cike da takaici yace.

“Ya dai bawan Allah Meyesa kake shige min rayuwa da ƙudundunai ne?,Ko kuma dan kaga bansa security sun jefa ka waje bane?Ina ruwanka da ita?”.

Araunane Moddibo ya kallesa kana yace.

“J baka da hankali ne J mekake yi haka? Shin wace rayuwa ka jefa kanka aciki J?”.

 

*Gembila*

 

Acan Gembila kuwa adai-dai wannan lokacin Mommy ce zaune abakin gadon Khausar yayinda Khausar da Asma’u ke tsakiyar gadon cikin dariya Mommy ta gyara zaman wayar dake kunnenta kana tace.

“Yau dai Ummi kiyi haƙuri nice na hana Asma’u dawowa kuma Khausar ce ta hana dan Allah kiyi haƙuri ki barta ta kwana, kinsan abokin kuka shi ake faɗawa mutuwa”.

Murmushi Khausar tayi tana kallon Mommy.

Still Mommy na Dariya tace.

“Shiyasa nace bari in kiraki in Faɗa miki kuma ɗazu nayi ta kiran wayarki yana shiga ba’a ɗauka sai yanzun”.

Acan ɓangaren Ummi kuwa murmushi tayi cikin yanayin sakin fuska da jin daɗi tace.

“Laa bakomai ai lokacin da kika kira ina tare da Babansu ne kuma nabar wayar aɗakina muna tatauna batun Khausar ne sai yanzu dana shiga ɗaki naga miss call ɗinki na kira”.

Murmushi Mommy tayi cikin jin daɗi tace.

“Toh Nagode Insha Allah zamu kwana gobe zata dawo”.

Khausar dake gefe tayi ƙasa da murya kana tace.

“Mommy kice mata dan Allah goben ma sai da daddare zata dawo zamu sake yini”.

Dariya Ummi dake jiyo sautin muryar Khausar tayi kana tace.

“Ai kwana ya isa basai anyini ba”.

Karɓan wayar Khausar tayi tare da langwaɓar da kai tace.

“Dan Allah Ummi idan mun kwana mu yini”.

Murmushi Ummi tayi tare da gyara rikon wayar tace.

“Ku kwana dai sannan kuzo da wuri Ina son tattaunawa dake”.

Kai Khausar ta gyaɗa kana tace.

“Toh Ummi”.

Sannan ta katse wayar.

Miƙewa Mommy tayi kasancewar girkinta bisa duk kan Alamu cikin shirin tafiya side ɗin Lamiɗo take kallon Khausar tayi kana tace.

“Toh kizo ki rufe muku ƙofa”.

Kai suka gyaɗa atare suka miƙe da Asma’u suka bi bayanta kana suka rufe kofar.

 

Zama Asma’u tayi akan 2sitter kallonta Khausar tayi ta shafa cikinta kana tace.

“Asma’u mai za muci ne?”.

Kai Asma’u ta girgiza kana tace.

“Wani abinci zanci Khausar bayan kinsan Maganar daya kawoni nake so muyi amma tun yamma kin ƙi ki zauna muyi”.

Langwaɓar da kai Khausar tayi cikin sanyin murya tace.

“Shiyasa nake so mukwana kinga yanzu ma Mommy Bata nan zamu sake muyi maganar mu”.

Jinjina kai Asma’u tayi tare da cewa.

“Toh shikenan”.

Ahankali Khausar ta shafa cikin tace.

“Gaskiya yunwa nake ji kema kuma naga ɗazu bakici abincin sosai  ba”.

Ajiyar zuciya Asma’u ta sauƙe kana tace.

“Toh shikenan muje kichen ɗin muga mai zamuyi”.

Suna shiga kichen Asma’u ta buɗe freezer Khausar kuwa na tsaye gefenta ganin ɗanyen kifi yasa Asma’u juyawa ta kalli Khausar kana tace.

“Toh muyi Marghi special mana”.

Kai Khausar ta gyaɗa cike da gamsuwa tace.

“Toh shikenan muyi”.

Suna aikin suna taɓa hira cikin awa ɗaya suka gama kana suka soya chips aplate Asma’u ta zuba musu sannan Khausar ta zuba musu Tea cup biyu afalo suka zauna suna ci suna kurɓan tea suna cikin ci suka ji Knowking ahankali Khausar ta kalli ƙofar tace.

“Waye”.

Haiydar dake tsaye yace.

“Nine”.

Kurɓan tea Khausar tayi tace.

“Toh lafiya har mun rufe kofa zaka zo kana mana Knowking?”.

Murmushi yayi kana yace.

“Naji ƙamshi yana ta buɗewa ne ta ko ina shiyasa nasan wani abu kuka girka Ni dai Ku sammin kawai yunwa nake ji dan nayi dogon hira”.

Hararan ƙofar Khausar tayi tare da cewa.

“Shegen kwaɗayi mutum yana nan da hanci kamar Mage duk abinda akayi baka ciki ma sai an baka”.

Dariya Asma’u tayi tare da miƙewa tashiga kichen ta ɗauki Plate ta zuba masa sauran kana ta buɗe ƙofar  ta miƙa masa har ta juya yayi saurin cewa.

“Toh ni baza abani shayin bane”.

Harara Khausar ta watsa masa kana tace.

“Ohh Haiydar kinga Ni Ko Asma’u da ba kin fara bashiba”.

Murmushi Asma’u tayi tare da juyawa ta koma kichen Haiydar kuwa gwalo yayiwa Khausar kana yace.

“Oho dai abani”.

Miƙa masa Asma’u tayi bayan ta zuba.

 

Bayan sun kammala Asma’u tace.

“Khausar mu dan watsa ruwa mana”.

 

“Eh to ki fara shiga”.

Cewar Khausar dake gyara zamanta.

 

Miƙewa Asma’u tayi tare da tattare Plate ɗin ta kai kichen kana ta dawo ta watsa ruwa bayan ta fito Khausar ma tashiga ta watsa tana fitowa ta bude Siff ta ɗauka musu sleeping dress riga da wando masu duhu ta miƙawa Asma’u ja sannan ita ta sanya fari.

Kai tsaye falon suka fito Khausar ta kunna Tv ta rage Volume Anutse Asma’u ta juya ta kalli Khausar kana cikin sanyin Murya tace.

“Khausar”.

Ahankali Khausar ta juya tare da tattara duk kan nutsuwarta zuwa gareta tace.

“Na’am”.

Ajiyar zuciya Asma’u ta sauƙe kana tace.

“Khausar wai Maganar da naji gaskiya ne abu ya kankama wai har an ɗaura aurenku?”.

Numfashi Khausar ta fesar kana ta sunkuyar da kanta ƙasa cikin rauni ta riƙo hannun Asma’u ta mannasu da kumatunta ga mamakin Asma’u sai taga hawaye na zuba Shar-shar-shar akuncinta.

 

Cikin sanyi da rauni Asma’u tace.

“Haba Khausar daga na miki magana sai ki fara kuka ai mu abun farin cikine”.

Ƙasa cewa komai Khausar tayi sai hawaye da take ahankali ta fara sheshsheƙa dake fita daga ainihin zuciyarta.

Araunane Asma’u tace.

“Haba Khausar kina kuka Ni kuma ya kikeso inyi kawai daga nazo muyi magana ta tsakanin mu sai ki fara kuka ai wannan abin farin cikine ba abin kuka ba”.

Kai Khausar ta girgiza cikin rawan murya tare da ƙoƙarin hana kanta kuka tace.

“Asma’u na amince ne saboda wasiyyar da Yah Jameel ya barmin kenan, amma ke kinsani kinsan waye Moddibo kinsan yanda tsakanina dashi yake kuma ni wlh banyi zaton da sauri-sauri haka zasu liƙa mishi niba”.

Hawaye na bin kuncinta  ta cigaba da cewa.

“Bansan wace irin rayuwa zanyi atare dashi ba bansan wani iri zama zanyi ba bansan wani irin ƙakubalen zan fuskanta ba amma ina cikin taraddadi da tashin hankali Asmau”.

Atake idanun Asma’u suka cika da hawaye cike da tausayin Khausar.

Araunane Khausar ta cigaba da cewa.

“Ranar  ma abinda ya kaini gidanku kenan naje ne muyi maganar amma sai in rasa ta yanda zan fara maganar ta ina zan kama mgnar ma”.

Cikin matsanancin kuka da tashin hankali tace.

“Asma’u shin menene makomata Yah Jameel ya barni da nauyi mai tarin yawa inaso in wanzar masa da wasiyyar sa gashi ya kasantu to amman ni menene makomata”.

Cikin rauni da tarin damuwa Asmau tace.

“Khausar ki daina kuka in dai kin gamsu Saboda farin cikin Yah Jameel amakwancinsa kikayi to ki daina kuka na tabbatar da Yah Jameel yana raye ba zaiso kukan kiba”.

Kasa da kai Khausar tayi hawaye na cigaba da zuba daga idanunta cikin zubda hawaye Asma’u ta cigaba da cewa.

“In dai har kinyi haka saboda farin ciki da kuma Wasiyyar Yah Jameel ya bar miki toh kada kiyi Kuka Yah Moddibo ai Namiji, ke kuma macece, kuma zuciya tana son mai kyau tata mata ke kuma mace cefa cikekkiya mai ababen muradin dukkan namiji”.

Ta sauƙe Ajiyar zuciya still Hawaye na bin fuskarta ta cigaba da cewa.

“Ina da tabbaci Khausar ko Yah Moddibo muddin yaji wasiyya ce Yah Jameel ya bar miki sannan saboda wasiyyar sa kika ce kinji kin gani zaki auresa nasan bazai zalunceki ba muddin bai kyautata miki ba to bazai zalunceki ba”.

 

Kai Khausar ta girgiza ta tare da ƙara danne sheshsheƙan Kukan ta haka ma Asma’u cikin sauri Khausar ta fara share mata hawayen fuskarta murya na rawa Asma’u tace.

“Khausar ban san da wani irin baki zan miki godiya ba, Ubangiji Allah ya biya ki da mafi kyawun sakamako saboda wasiyyar ɗan uwana kika amince da mgnar duk da ba yayanki bane”.

Cikin sauri Khausar ta sa hannu ta rufe mata baki muryan ta na rawa tace.

“Asma’u meyesa zaki ce haka  Yah Jameel kike cewa ba Yayana bane?”.

 

Kai Asma’u ta girgiza kana cikin raunin murya tace.

“Ba haka nake nufi ba Khausar”.

Araunane Khausar tace.

“Toh meyesa haka Yah Jameel Yayana ne kuma Malami nane sannan Al’farma ya nema ya haɗani da Allah da Manzon ranan rabuwa ta na ƙarshe da Yah Jameel”.

Sai kuma tayi saurin rufe fuskarta da tafin hannunta kana cikin rauni ta cigaba da cewa.

“Yah Jameel Yana Kuka fa Asma’u yake cemin Khausar nasa zaiyi wuya inyi tsawon rayuwa alokacin daya faɗa min hankalina ya tashi na gigice bansan lokacin da hawaye ya fara zubo minba”.

Asma’u kuwa lumshe idonta tayi tana mai jin ƙaunar Khausar aranta.

 

Cikin sheshsheƙa Khausar ta cigaba da cewa.

“Ganin ina kuka sai ya fara yimin dariya yana cewa dan yace min zai mutu shine xan fara kuka ai bawai dan ya faɗa yana nufin mutuwa zaiyi ba, sannan yace min akwai Alfarma da temakon da yake nema awajena”.

Ta lumshe Idanunta hawaye masu zafi suka zubo kana ta cigaba da cewa.

“Yasa na mishi al’ƙawari koda bayan ransa zan cika masa wasiyyar Asma’u kuma nayi nasa al’ƙawarin idan har ban auri Moddibo ba kenan ban cikawa Yah Jameel Wasiyyar sa banyi masa taimakonba shiyasa nace Moddibo zan aura amma ke kin sani tsoron Moddibo nake hasalima babu wacce Moddibo ya tsana arayuwar sa sama dani kinsan shi baya sona ni kuma ina tsoronsa”.

 

Cikin sanyi da son ƙarfafa mata gwiwa Asma’u tace.

“Insha Allah ba zaki taɓe ba Ummi ma tayi farin ciki da wannan auren kowa kin sashi afarin ciki Insha Allah Ubangiji zai dawwamar miki da farin ciki agidan Auren ki”.

Ajiyar zuciya mai nauyi Khausar ta sauƙe kana yace.

“Ni dai zanyi wannan al’amarin saboda Yah Jameel ne kuma na yarda zan jure duk kan ƙunci, Haranta, Cin fuska, Tozarci, Cin zali da duk wani salon wulaƙanci da Moddibo zai min saboda cika burin Yah Jameel”.

Asma’u kuwa kai ta girgiza kana tace.

“Insha Allah ma ba zai miki ba da yardan Allah ba zaki ƙuntata ba rayuwa ba zata miki ƙunciba tunda Mommy ta sanya Albarka aciki komai zai tafi dai-dai”.

Ta ida maganar tare dasa hannu tana share mata hawaye murmushi tayi ko kaɗan bata son ganin hawayen Khausar cikin son ƙawar mata da damuwarta tace.

“Keda kike amarya wayasan amarya da kuka kuma amaryar ma ango mai tsada matar Yah Moddibo?”.

Harara Khausar ta watsa mata da jiƙaƙƙun Idanunta da Eyelashes ɗinta suka sake zara-zara dasu sai kuma ta tura baki tace.

“Ba wata amarya amarya ko kuma wahalalliya dai!?”.

Dariya Asma’u tayi kana tace.

“Ba wata wahalalliya amarya dai”.

Cikin sanyi Khausar tace.

“Hmmm Asma’u Ni dai hankalina atashe yake ina tsoron Moddibo bansan wani irin zama zamuyi ba”.

 

A dai-dai lokacin kuwa Samira Sani ce, da Amina ke waya tana gaya mata batun auren MODIBBO DA Khausar, Ya Salam wannan labarin ya girgiza Samira, haka yasa bta cilla wayar bisa gado ma tare da ta katse kiranba.

Da gudu ta nufi ɗakin Hajia Lami, tana shiga ta ganta zaune bakin gado da waya a kunne tane cewa.

“Haba dai Hajia Bunayyah wanne irin aure kuma, innalillahi ya za’a mana haka muna nan muna shiri mun rasa nitsuwa dan jawo hankalin wannan yaro kuma azo ace wannan shegiyar yarinyar ya aura, ya zasu fito mana a bazata”.

Sai kuma ta katse wayar tare da ruggume Samira da ta faɗa jikinta tana kuka wui-wui tare da cewa.

“Mommy shike nan ni kam nayi batam ɓaka tamtam, ni ba budurcinaba, ni ba Modibbo ba, ni ba lafiyata ba ni da zunubin zina da boka, ga ruwa mai wari da ke bibiyata”.

Ta ƙare mgnar da fashewa da matsanancin kukan da yasa Hajia Lami ruggume mata cike da takaici ta fara lallashinta.

 

Acan Falon Lamiɗo kuwa kallon Mommy dake zaune gefensa yayi ahankali ya sauke ajiyar zuciya kana yace.

“Ɗazun Alh Bukar suka zo maganar Amina da Naseeru to kuma har angama magana anbawa Naseer Amina  since Ashirye suke nan da kwana goma suke so dan Ashirye suke”.

Murmushi Mommy tayi kana tace.

“A’a Masha Allah Abu yayi kyau Allah yasanya al’khairi”.

Anutse Lamiɗo ya gyara zamansa kana yace.

“Toh kuma tunda sakaranar yazo abakin gaba kawai za ahaɗa da ɗaurin bikin Khausar”.

Saurin Kallonsa Mommy tayi Asanyaye tace.

“Mai martaba da sauri haka?”.

Kallon yanda tayi da fuska yayi kana yace.

“Toh ke Meye damuwarki aciki?”.

Cike da damuwa tace.

“Toh Babu abinda muka shirya wa bikin nan fa”.

Numfashi ya fesar kana yace.

“Toh na saki ne ko kuma nace kishirya ne?,Ko cokali bansa ki siyawa Khausar ba kibar min ƴata Ni zan mata komai”.

Ya ƙarasa maganar cike da kara, mutuntaka, da kuma dattako.

Cike da kunya da jin daɗin karansa Mommy tayi murmushi kana tace.

“Nagode Allah yasanya musu al’khairi duk abinda kace haka za ayi”.

Murmushi yayi kana yace.

“Haka nake son ji ke dai ki sanya Albarka acikin wannan al’amarin”.

Jinjina kai tayi cikin sanyin murya tace.

“Allah yasanya alkhairi”.

 

*Morocco*

 

Cikin fushi Dr Jameel ya watsa wa Moddibo Harara kana yace.

“Haka kawai zaka zo kana takura min rayuwa dan bansa ankore kaba?”.

Cikin wani irin yanayi Moddibo yace.

“Korana?,Kasa akoreni J ni kake cewa zaka kora?J Bismillah in baka koreni ba baka amsa sunan ka Jameel ba”.

Afusace Dr Jameel yaja hannun farkarsa yace.

“Mu tafi Baby”.

Cikin sauri Moddibo yabi bayansa kafin ya fita tuni Dr Jameel yashiga mota, Cikin sauri yashiga motarsa zaiyi reverse yaga wasu motoci biyu sun taresa dole sai anja daya daga ciki kafin ya samu ya fita Dr Jameel kuwa tuni yaja motarsa ya tafi.

Da sauri Moddibo ya fito daga motarsa yace.

“Waye wannan yazo ya tare min mota ta ina zan fita”.

Dai-dai lokacin mamallakin Motar yazo cikin sanyin murya yace.

“Ayyah Bawan Allah kayi haƙuri na ajiye mota abayan naka banyi tsammanin zan daɗe ba abu kawai zan karba”.

Uffan dai Moddibo bai ce da mutumin ba yashiga motarsa yaja ya tafi sannan Moddibo ya shiga nasa yaja ya fita sai dai ba motar Dr Jameel ba labarinsa gefe da gefen Asibitin ya zagaya amma koda wasa baiga alamunsa ba.

Komawa yayi da niyyar shiga asibitin security suka hanasa duk yanda yaso shiga sunƙi barinsa cikin takaici ya juya akalar motarsa kai tsaye Mouley Youssef Hotel Rabat ya nufa cike da tunani iri-iri, yana isa yayi Parking kana ya fito yashiga cikin harabar Hotel ɗin ya shiga reception kai tsaye ya wuce masauƙinsa yana  ya sa key ya buɗe ya shiga bakinsa ɗauke da sallama

 

Zama yayi akan 1sitter ya dafe kansa da hannu bibbiyu cikin sauri ya janye hannu ya ɗauki wayarsa ya kira Number Abba amma har ya katse ba adauƙa ba.

Lokacin da kiran yashiga wayar Abba tuni yayi bacci miss call uku Moddibo yayi ganin bai ɗauka ba yasa ya haƙura ya jinginar da kansa da jikin kushin yasani koda ace J zaiyi ko wani irin basaja ne aduniya ba zaiyu ace anyi masa Aure Iyayensa basu sani ba kuma ga duk kan alamu ma wancan karuwa ce domin tafi kama da karuwai wannan ne ya fara ɗarsa mishi shakku anya wannan J ɗin shi ne kuwa a fili yace.

“Ina inada tabbacin J na ba mazinaci bane, kuma bazai aikata zinaba, shin toh in ba J na bane waye wannan”.

Kanshi ya daddafe da duka hannunsa yana mai rumtse idanunsa da ƙarfi da kuma ƙarfin yace.

“No J bazai kasance haka, ina ba J ɗina bane kuma J na ko allura bai iya yiba  ba abinda ma ya haɗashi da likitanci”.

Yayi mgnar da cikekkiyar yaƙini da yarda da hakan sabida yanzu ya fara samun nitsuwa, ya gamsu kawai tsananin kamannine mutumin yake dashi da Jameel ɗinsa wanda hatta sautin muryarsu iri ɗaya ne da J dinsa.

“Yah Salam. Allah mai iko to waye wannan ɗin”.

Yayiwa kansa tambayar da yake masifar son sanin amsarta”.

 

*Gembila*

 

Ɓangaren Asma’u da Khausar ma haka suka raba dare wajen hira har misalin ƙarfe uku suna zaune suna hiransu ta Aminai daga baya suka koma hiran makaranta wani abin idan sun tuna suyi dariya wani suyi murmushi musamman rigimar kwausar da Modibbo, rayuwa kenan shikenan rayuwar makaranta ta wuce kamar ba ayiba cikin murmushi Khausar ta gyara zamanta tare da kallon Asma’u kana ta ɗan tsuke fuska sai kuma tayi kasa da kai cikin juya murya zuwa irin ta Modibbo tace.

“Ke uwar rawar kai”. Sai kuma taja tsaki tare da cewa.

“Ko sunanafa baya kira wai ke”

Dariya sosai Asma’u keyi tare da riƙe ciki, ita kuma Khausar baki ta ɗan taɓa kana a hankali tace.

“Da jajayen lips inshi a wurin kamar balarabe da dunduniyarsa laushi kamar ta jariyai, gashin ƙeya kamar jikin Mage.”

Cikin nunata da yatsa Asma’u tace.

“Yah Salam ashe har haka akeson Ƴaƴana ban saniba”.

Harara ta watsawa Asma’u tare da cewa.

“Kamar yaya so”.

Tafa hannu Asma’u tayi tana faɗin.

“Toh fisabilillahi in ba soba mai ya kai hankalin da idanunki kan lips inshi harda ƙeyarshi duk yawan sa hulanshi, shin tukun nama ya akayi kika san dunduniyarsa da taushi, na shiga uku ashe Allah ya tsare bawan Allah da kin fyaɗeshi”.

Cikin kauda kai dan sai yanzuma taji kunyar kalamaanta a hankali tace.

“Ba wani nan kin dai san kawai ni ina son mai kyau, haka Allah yayini”.

Ta ƙare mgnar tana lumshe idanunta, a hankali ta buɗesu ganin yadda lips enshi ke motsawa in yana mata masifa.

Haka dai sukayi ta hira mafi akasari kan Modibbo ne yanayi tana kusheshi kushen da yake naɗe da cikekken yabon halittarsa da ɗabi’unsa.

 

Washegari da safe Misalin shaɗaya bayan sun gama yiwa Mommy Komai suka shirya suka tafi gidan Ummi suna isa suka samu komai fes-fes ta gyara har ta gama girki.

 

Ummi kuwa murmushi tayi ganin su yasa tace.

“Yawwa ƴan al’barka tun ɗazu nake son zamu tafi gidan Abban Jameel nida Innayi, kuma gidan shiru Bashir ya tafi sabgogin gabansa”.

Khausar na zama tace.

“Ai haka suke Ummi haka ma Haiydar shegen yawo ne da yaran nan”.

Kai Asma’u ta jinjina tace.

“Haka suke kuma idan mutum ya fita na minti biyar su riƙa cewa shine yake yawo.

Murmushi Ummi tayi kana tace.

“Yau ɗauki wannan Asma’u ki ƙaiwa Innayi yanzu na leƙa na samu tana walaha”.

Zare ido Khausar za tayi cikin sauri tace.

“Innayin tana nanne?”.

Da sauri Asma’u tace.

“Ai tunda Yah Modibbo ya tafi Marocco ta dawo nan”.

Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe ta koma ta zauna tare da faɗin.

“Au”.

Ahankali Asma’u ta jawo kular dake gaban Ummi tana buɗewa tace.

“Yau kuma mai akayiwa Innayi?”.

 

Kallon kulan Ummi tayi kana tace.

“Tuwo nayi mata nasan tanason tuwo”.

Kai Asma’u ta gyaɗa kana tace.

“Ayyah aikam dai”.

Ta ƙare mgnar tare da nufar ɗakinta da kular don nan innayi take.

Anutse Ummi ta maida kallonta kan Khausar cike da kulawa tace.

“Khausar”.

Cikin sanyi ta ɗago kanta tace.

“Na’am Ummi”.

Ido Ummi ta tsira mata kana tace.

“Ahaka za ayi zaman auren?”.

Khausar kuwa da sauri tayi ƙasa da kanta batare da tace Uffan ba yayin da hawaye ke cika mata kwarmin ido.

Ahankali Ummi ta sake kiran sunan da faɗin.

“Khausar”.

Shiru Khausar tayi sake kiran sunanta ta kuma yi.

Still Bata dagoba numfashin Ummi ta fesar tare da cewa.

“Khausar ɗago mana ki kalleni”.

Ahankali ta ɗago Idanunta dake cike da ruwan hawaye cikin sauri Ummi ta girgiza mata kai kana tace.

“Kar kiyi kuka Khausar insha Allah  inaji Ajikina akwai al’khairi a alaƙarki da Moddibo Ubangiji Allah ya miki albarka”.

Cikin rauni da zubda hawaye ta amsa da Ameen asaman laɓɓanta.

Cikin rarrashi da son kwantar mata da hankali Ummi ta cigaba da cewa.

“Sai kuma batun tsoro ki daina mutumin da kike ƙoƙarin kasancewa ƙarƙashin inuwar Aurensa ai bai canci irin wannan tsoronba, shi ba Dodo bane Aliyu da kike ganifa yana da mutunci, Kara, tausayawa, da kuma karamci tsoron da kike nunawa akansa ya tsananta”.

Cikin sanyi ta girgiza kanta muryan ta na rawa tace.

“Ummi baki sanshi bane ba fa”.

Itama Ummi cikin sanyi tace.

“Nasan shi mana Khausar”.

Araunane Khausar ta girgiza kai cikin son Hana kanta kuka tace.

“Ummi baki san saba yana da mugunta fa”.

 

Kai Ummi ta girgiza kana tace.

“Ba zai miki mugunta ba Khausar in Allah yaso ya yarda Babana bazai miki mugunta ba saboda kin masa duk kan halarcin duniya”.

Lumshe Idanunta tayi cikin raunin murya tace.

“Ummi baya sona ya tsaneni koda kallon fuskatane baya so tunda muke tare Amakaranta da zaran mun haɗu zai nemi laifin da zai lika min kawai dan ya dake ni”.

Ta share hawayen da suka zubo mata cikin sanyi ta cigaba da cewa.

“Ummi ina tsoron rayuwa dashi sannan kuma Ummi ina so in cikawa Yah Jameel burinsa Ina so ciki wannan al’ƙawarin dana ɗauka”.

Ahankali Ummi ta matsa kusa da ita ta janyota jikinta ta Rungume cikin ƙarfafa mata gwiwa tace.

“Kar kiyi kuka Khausar! Kada jiki tsoro! Kada ki damu ki daina tsoron Babana babu abinda zai Miki”.

Ta ƙare mgnar dasa hannunta, amshi wayar Khausar tare da cewa.

“Yanzu bani wayarki in sa miki number’s, ko kinada ita?”.

Cikin sauri ta jujjuya kanta.

Ita kuwa Ummi cikin kulawa yace.

“Toh bani wayar, in sa miki,  yanzu dai kin san ke matar aurece, igiyoyin aurensa na kanki, banda yawan yawo, dukda dama nasan baku da yawan yawo”.

Ta ƙare mgnar da fara sa mata number Modibbo dan wayarta ba pin, tana gama sa number’s ɗin ta miƙa mata waya.

Amsa tayi tare da kife wayar bisa cinyarta. Ita kuwa Ummi da sauri ta kalleta jin tana cewa…

 

 

 

Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER’N na 09097853276. Kana in tura miki shi kisha karatunki cikin aminci.

 

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Reply

Back to top button