Hausa NovelsSakayyah Book 2 Complete

Sakayyah Book 2 Page 12

Sponsored Links

 

GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2… Page 12*

Related Articles

 

          Na

*Aysha Aliyu Garkuwa*

 

 

 

*TSAYA! TSAYA!!! NACE ki TSAYAKO Sister’s* duk wacce batayi
anfani da sabulun mg’s ba  ko kit dinsu
inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg’s sai sanbarka
duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg’s domin
yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk
Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark
dama dukkan wani prblm yajaraba mg’s bi’iznillah komai zaizama labari bayan
jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,  gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using
mg’s batare da kunbukaci wani Mai ba🤗nd wanan new soap din💣ne,😯
bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku, domin ance gani yakoriji Kuma siyan
nagari maida kudi gida

You can check pic👇for the soap reviews🥰

Soap price:4k

maiso ga number’s ɗin da zakuyi mgn bani AYSHA ALIYU
GARKUWA, zakuyiwa mgn ba, gaban 👇🏻👇🏻👇🏻Ga
ta inda zakuyi magana Whatsapp

08062991549

07046881166

07067210195

Call 08064532391

Instagram:glow_with_mgs

Facebook: mg’s skincare

 

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set
nagyaranjiki sannan akwai na amare special Wanda inkinyi using baki Kuma
bukatar kiyi Wani gyaranjiki domin keda kanki zaki shaida cewa fatar taki ta
wanku tarwai😍08062991549

 

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is
not free

 

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏

 

 

Cike da matsanancin mamaki Moddibo ya tsirawa ƙofar da suka
rufe ido, toh shin me hakan yake nufi, gwauron numfashi ya fesar yayin da
abubuwa da yawa suka riƙa dawowa cikin ƙwaƙwalwarsa, cikin kasala ya jingina
bayansa da jikin kujeran kana ya buɗe manyan idanunsa da suka sauya launi.

Ahankali ya shiga ƙarewa tsarin falon kallo, falone mai
masifar girma da kyau tun daga farkon falon yake ɗauke da wasu lumtsa-lumtsan
kujeru 4couner tun daga farkon Falon har ƙarshesa kujerune zagaye dashi ya
kasance kalan Golden ne da ratsin milk kana da ɗigon Coffe ga wasu trust pillow
kalan Golden da suka sake ƙawata kyawun kushin ɗin yayin da ƙasan falon ke
mamaye da wani lallausan Darduma kalar Golden da ratsin milk kana da ɗigon
Coffe daga can saman P.o.p kuwa wasu irin Gloves ne da akayi musu dising na
ƙawa da alfarma, yayin da Labulayen suma suka kasance kalan Golden ɗin, daga
tsakiyar Falon kuwa wasu stool ne masu azabar kyau guda  biyu ɗaya daga farkon falon ɗaya kuma daga
ƙarshe kuma jikinsu duk akwai ƴan ƙananan stoll guda huɗu, wanda za’a iya
jansu, iya tsaruwa falon ya tsaru kana sai can gefen daga gefe kuma dinning
area ne mai ɗauke da dining table shima komai goldie ne, sai daga gefen dama
can wata ƙoface dake da ƙawanyar labule, hakama gefen hagu falo ne na al’farmar
kai da ka gani kasan babu ƙaranta a cikin lamarin tsarin komai a fili zai nuna
maka anci uban kuɗi a Masaarautar daga can tsakiya wani shunfiɗeɗɗen steps ne
mai faɗi wanda ake shimfi tattausan Carpet na al’farmar busa alamun akwai wuri
na musamman a saman.

 

Cikin fesar da numfashi ya riƙa juya idanunsa lungu da saƙo
na cikin falon, kafin ahankali idanunsa suka sauƙa akan wasu jerin hotuna masu
yawa.

Ware idanunsa yayi ganin wani kyakykyawan Matashi mai
masifar kama da shi tamkar an tsaga kara babu abinda ya raba sa dashi yana cikin
shiga ta al’farmar dake nuni da rainon masarautar ce.

 A hankali kuma ya
dire idanunsa bisa hoton dake gefen.

Wannan mutumin daya gani a fada ne amatsayin Sarki sai kuma
wata kyakykyawa mata mai matsakaicin shekaru.

   Zazzafan Ajiyar
zuciya ya sauƙe tare da maida idanunsa dake lumshe kan wasu kyawawan mata su
uku  biyu daga ciki zasu girmeshi ɗaya
daga cikin kuma da alamun itace ƴar auta sai kuma hoton wani Kekkyawan jariri
da aka ɗaura saitin cinyar Sarki, sai dai bisa alamu haɗa hoton akayi.

Suna zagaye da iyayen nasu,
sai kuma ya maida idanunsa kan hoton dake gaba…

Cikin sauri ya miƙe tsaye murya ɗauke da tsananin mamaki da
kaɗuwa gami da al’ajabi ya motsa Pinch lips ɗinsa tare da faɗin.

“Innayi”.

Ganin hoton Innayinsa ɓaro-ɓaro tare dana wannan ahalin duk
da kuwa cewa alokacin tana da ƙarancin shekaru bai hanashi ganeta ba, ko dan
yasan hoton a wurinta ne, dan tabbas tana da hoton wanda kuma hannunta ke riƙe
da jariri fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi wanda kuma ta sha faɗi mishi
shine a hannunta a ranar da anka haifeshi akayi musu hoton.

Yatsunsa biyu na  yasa
ya murza idanunsa ganin ko mafarki yake.

Cikin bugawar zuciya yace.

 “Wannan fa innayi ce
ba gizo idanuna kemin ba”.

 Cikin tsananin
al’ajabi ya furta.

“Ya salam Abun Al’ajabi”.

Kafin ahankali ya ɗaga ƙafafunsa da yaji sunyi masa mugun
nauyi ya nufi jikin hoton, yayin da ƙwaƙwalwarsa ke tariyo masa cewa tabbas
Innayi nada wannan hoton awajenta.

Da sauri ya dafe kansa tuno kalmarta agaresa da take cewa
Kaje sai nazo.

Hannunsa duka biyu ya Sanya tare da dafe kansa lokaci ɗaya
abubuwa da yawa suka shiga dawo masa ƙwaƙwalwarsa kama daga abubuwan da yake
yawan mafarkinsu, atsawon rayuwarsa wanda tunda ya shigo masarautar nan yake
ganinsu ra’anul ayn.

 da kuma irin kalaman
da Innayi ke masa wasu lokuta kana da tsananin kamanninsa da yaron dake jikin
hoton da kuma Sarki wanda Babu bancin dake tsakaninsu wanda zai iya nuna cewa
ba mutum ba ɗaya bane, sai dai shekarun da Sarkin yake dashi wanda shi kuma
nashi basu kai haka ba kana hatta ƴan matan dake zagaye da hoton suna tsakanin
kama dashi.

 

Zazzafan Ajiyar zuciya ya sauƙe akaro na barkatai kana ya
tsirawa farcen hannun mutanen dake jikin hoton idanu wanda baiyi fari tasss ba
yayi kalan ruwan ƙasa-ƙasa wanda haka shima nashi yake.

Kansa ne ya shiga juyawa cikin tsananin tarin mmki a zuciya
yashiga jada baya yana tafiya da baya da baya har ya isa jikin kujeran da aka
ajiyesa da farko kana ya runtse idanunsa kansa ya dafe da hannunsa na dama ya
fara tunani.

“Shin me yake faruwa dani? Me hakan yake nufi? Ina ne nan?
Toh menene haɗina dasu? Meyesa suka kawoni nan suka rufe ni? Meye nufinsu? Shin
ko dai mafarkaina gsky ne?.”

Tambayoyin da yake yiwa kansa kenan.

Cikin sauri ya janye hannunsa dake kansa ya shiga laluma
aljihunsa da niyyar ciro wayarsa dan ya kira Innayi. sai yaji wayam iska ya
furzar mai zafi tuno cewa ya barsu acikin amota…

 

Acan cikin gida kuwa wani hamshaƙin falone me masifar kyau
da tsari wanda yaji komai na more rayuwa daga can tsakiyar falon kuwa wata
kyakykyawar Matace wacce take cikin hoton da Moddibo ya gani Hakimce akan wata
kujera ta alfarma.

Yayinda ƴaƴanta ke zagaye da ita a hoton, sunlma suna
gefenta sai dai Ba Ibrahim kana babu Rahma, bisa alamu hira suke cike da
shaƙuwa.

Cikin nutsuwa Dr Jameel suka kutsa kai cikin falon da sauri
yaron da Dr Jameel ke riƙe da hannunsa ya janye kana ya nufi gaban matar tare
da riƙo hannunta da cewa.

“Didi kin san wani abu kuwa”.

Cikin kula da so irin na kakannin a kan jikokinsu ta girgiza
mishi kai tare da cewa.

“Toh Sarkin fada, me ka gano kuma, dan na lura in kunzo dai
kana son zaman fada”.

Da sauri ya zauna gefenta tare da cewa.

“Didi wlh yanzu na ga wani mai kama da Uncle Ibrahim sai
kingani kamarsa ɗaya da Uncle Ibrahim.

Sai dai shi yafi Uncle Ibrahim tsawo da kyau amma Didi babu
abinda ya raba su da ace Uncle Ibrahim zai ɓata toh wlh  wannan za’a ɗauka ya maye gurbinsa”.

Cikin sauri da bugawar zuciya. Didi ta kalli Dr Jameel kana
tace.

“Jameel waye shi?Akan wayake Hakim ke magana?”.

Ajiyar zuciya Dr Jameel ya sauƙe tare da zama akan Lallausan
Darduman dake malale ƙasan tiles ɗin kana yace.

“Kai Didi gsky nima abin nan yaban mamaki.

Didi yau tsawon kwana huɗu kenan yake bibiyata bansan shiba
amma tun ranan farko dana fara ganinsa yana min kama da wani sai dai na rasa da
waye yake min kama ina ta tunani na rasa ganowa sabida gaba ɗaya lamarin shi ɗauremin
kai yadda yake ta nuna ya sanni”.

Sai kuma ya ɗan fesar da numfashi tare da gyara zamansa kana
ya cigaba da cewa.

“Na rasa dawa yake min kama baki ɗaya abin ya kwanta min
akaina, sai yau da muka zo nan naga na kalli Fuskar Abualeey, sai na ga suna
tsananin kama, sai kuma na tuni Ibraahim ashe dasu yake min kama kai kamanninsu
da Ibraahim ya ƙazanta  Didi shin wanene
shi”.

Cikin wani irin yanayi na tsananin al’ajabi da tsuman
zuciya. Didi ke sauraransa yayin da
ƴaƴanta Lalla Khadijah, da kuma Lalla Hafsat mahaifiyar Hakim wacce take
aure a Mexico wanda zuwan kakansu Sheiyk Jabeer Nuruddeen Gwadabe Joɗa, ne yasa
su zuwa dan ganawa da kakansu.

Ido suka tsira Dr Jameel cikin son fahimtar wani abu.

kana hadiman Didi kuwa dake can gefe sunkuyar da kansu
sukayi

 

Dr Jameel kuwa ahankali ya cigaba da faɗin.

“Sannan kuma ashe ban sani ba yana bibiyata, har muka shigo
gidan nan”.

Nan ya kwashe komai tun daga haɗuwarsa da Moddibo har zuwa
yau ya sanar mata…

Kana ya ɗaura da cewa.

“Sannan kuma Didi ɗazun da Abualeey ya kirani kan inzo in
duba jikin Rahma ciwon cikinta ya tashi. Ashe ban sani ba yana biye dani sannan
kuma shigowar da zamuyi *Rinƙas* ya ƙwace ya shigo cikin Masarauta Didi.

 zakisha mamaki idan
kika ga yanda yake sarrafa Dokin nan”.

Lokaci ɗaya Lalla Khadijah da Kalla Hafsat suka kalli juna,
kana suka juyo cike da mmki suka kalli Didi.

Da bugun zuciyar ta ya sake nunkuwa fiye da kaso tamanin
cikin ɗari.

Cikin fesar da numfashi ya cigaba da cewa.

“Kuma kinfi kowa sanin mutum biyu ne ke kaɗai ke iya,
sarrafa Rinƙas, ko Ibraahim baya iya zuwa ko kusa dashi.

Amman shifa kai tsaye ya fuskanci dokin. Didi wlh al’amarin
mutumin yayi masifar ɗaure min kai fiye da yanda kike zato”.

 

Didi kuwa tun daga lokacin da Hakim ya faɗa mata yaga mai
kama da Ibraahim zuciyarta ke bugawa har zuwa yanzu da Dr Jameel ya dasa ayar
mgnar, cikin sauri ta juya ta kalli Lalla Khadija da Hafsat, sai kuma Rahma
data fito yanzu ta kwanta gefenta Lalla Hafsat tana damƙe cikinta.

 cikin sauri Hafsat da
idanunta ke waje ta kalle Didi kana tace.

“Didi”.

Murya cike da sanyi da bugawar zuciya Didi tace.

“Na’am”.

Sai kuma suka shiga kallon juna alamar maganar ta ratsasu.

Dr Jameel kuwa batare daya lura da yanayin da suke ciki ba
ya cigaba da cewa.

“Allah Didi kamannin nasu har ya ƙazanta kamanninsa da
Ibraahim is too hight har Abualeey da kansa abin ya jijjigasa kin kuwa ga Fada?
yana shiga fa sai da kowa ya tashi tsaye”.

Didi kam kallonsa kawai take bako ƙyaftawa shi kuwa Dr Jameel
cigaba da cewa.

“Kinga Jabeer bin Jabeer shima sosai yayi mamaki saboda naji
yana cewa wai sun haɗu dashi ajirgi, dan sai cewa Abeey yake, Abeey ka ganshi
ko babu abinda ya raba shi da Ibraahim kamannin yayi yawa, nacema zan faɗawa
Didi kace kar in faɗa mata hankalinta zai tashi, gashi yanzu yazo har inda take
Abeey wlh jininmu ne. Haka yake ta faɗa yana can yana ruɗe”.

Cikin sauri da yanayin zabura Didi ta miƙe tare da kallon
Jakadiyarta da kanta ke ƙasa kana tace.

 “Jakadiya maza je ki
duba idan Mai Martaba na nan. Kice Ina son ganinsa cikin gaggawa. In kuwa
yanada uzuri a fada, ina fatan ayi min iso”.

Cike da girmamawa Jakadiya ta gyaɗa mata kai kana ta furta.

“Toh”.

Sai kuma ta juya cikin sauri ta juya ta fita Ahankali ta
riƙa ratsa tamfatsa-tamfatsan falon har ta isa bakin ƙofar fadan wayam ba kowa
alamar duk an watse.

Cikin Sassarfa ta juya ta koma falon domin sanar mata…

 

Acan ɓangaren Moddibo kuwa jin ana ƙwala kiran sallar
Maghriba yasanshi motsa laɓɓansa yashiga bin kiran Sallar kana yayi addu’ar da
Manzon Allah (S.A.W)ya koyar sai kuma ya furta.

“Ya Salam, shin Mutanen nan me suke nufi dani, suna nufin ba
zanyi Sallah acikin jam’i ba?”.

Ahankali ya juya idanunsa akan wannan Corridor dake gefen
damansa cikin nutsuwa yabi hanyar yayi tafiya mai ɗan tsayi ya hango wasu
ƙofofi guda biyu gefen hagu da dama ahankali ya murɗa ƙofar dake gefen dama.

“Ya Salam”.

Ya furta asaman laɓɓansa ganin wani tsarerren falo ahankali
ya taka ya shiga ciki.

Sai kuma ya ɗan jujjuya kai, ƙofar dake kusa dashi ya nufa.

 Wanda bedroom ne a
hankali ya murɗa ya shiga.

Ƙofar bathroom  ya
sake murɗa yashiga, alwala kana ya fitowa.

Jujjuya ya kai yayi cikin sa’a yaga darduma a shimfiɗe a
wata ƴar kusurwa awajen alamar ana sallah awajen anutse yayi sallar Maghriba
awajen kana ya cigaba da addu’oi har aka kira Isha’i, bayan ya idar ya fito
falon farko da aka fara ajiyesa.

Yana isa Idanunsa suka sauƙa akan dining da aka jera abinci
kala-kala sai kuma ya juya kanshi hanyar shigowa nan yaga wasu hadimai guda uku
maza suna tsaye.

Ganinsa yasa sukayi saurin sunkuyar da kansu ƙasa kana suka ɗaura
hannunsu aƙirji alamar Barka da fitowa.

Cike da girmamawa ɗaya daga cikin su yace.

“Ranka ya daɗe ga abinci”.

Numfashi ya fesar kana ya tsira musu ido na second biyu tare
da cewa.

“Shin meyesa aka tsareni anan?”.

Cike da ladabi da kuma Mutuntawa suke sake sunkuyar da kansu
ɗaya daga cikinsu yace.

“Kayi haƙuri Ranka ya daɗe Umarni ne daga mai martaba yace
kada mu bari a buɗe maka ƙofa dukkan abinda kake buƙata akwai shi anan basai ka
fita ba”.

Cike da mmki ya kallesa kana ya lumshe idanunsa tare da
fesar da iska mai zafi yace.

“Akan me za’a rufeni a hanani fita bayan ina da abubuwanyi”.

Cike da ladabi Hadimin ya sake sunkuyar da kansa wanda da
alama shine babban su kana yace.

“Kayi haƙuri In Sha Allah Mai martaba yana nan zai zo
wajenka”.

Batare daya sake furta komai ba ya koma ya zauna akan
kujeran.

Allah ya sani shi yama rasa shin wani irin tunani zaiyi abu ɗaya
dai yana jin wata nitsuwa ta musamman a jikinshi da zuciyarsa.

Anutse Hadimin ya sake biyo sa tare da cewa.

“Bismillah ka matso ga abinci”.

Kai ya girgiza duk da kuwa yunwa da yake ji amma yanayin da
yake ciki bazai iya bari yaci abinci ba.

Ganin haka yasa ɗaya daga cikin hadiman ya nufi jikin Frigde
kana ya kawo masa Fruits tare da ajiyewa akan stool agabansa.

 Sanyayyar iska ya
fesar daga bakinsa kasancewar sa mai son ƴaƴan itatuwa yasa ya miƙa hannu ya ɗauki
apple ya ɗan fara ci ahankali…

Yayin da hadiman suka koma baya suka ci-gaba da tsayuwar
anutse ya ɗago manyan idanunsa dake lumshe ya kallesu kana yace.

“Ku zauna mana”.

Murmushi sukayi tare da faɗin.

“A’a yallaɓai babu matsala kada ka damu wannan ai aikin
mune”.

Da mamaki yake kallonsu kana yashiga tunanin wannan
al’amarin ya yake.

Yana zaune yaga wani Hadimin
ya turo ƙofa ya shigo yayin da wasu hadimai uku mata ke biye dashi
hannunsu riƙe da manya-manyan Trolley suna shiga suka gaishesa cike da
girmamawa kana suka nufi bedroom ɗin suka buɗe Weldrop suka shirya masa kayan
kana suka fito Hadimai matan suka tafi suka bar namijin.

Shi kuwa namijin cike da ladabi ya durƙusa gabansa tare da
faɗin.

“Mai martaba yace ayi maka sannu da zuwa, sannan yace afaɗa
maka ka kwantar da hankalin ka ka shiga kayi wanka ga kaya an kawo maka ka huta
zuwa anjima zai zo kugana”.

Tunda ya fara magana Moddibo ke kallonsa jin ya dasa aya
yasa shi faɗin.

“Ina buƙatar wayoyina suna cikin mota akawo min ko kuma suzo
muyi duk maganar da zamuyi zan tafi ina da abubuwan yi”.

Cike da girmamawa Hadimin ya furta.

“Kayi haƙuri In Sha Allah zan isar masa da saƙonka”.

Kana ya miƙe ya fita…

 

Acan cikin gida Side ɗin mai Martaba kuwa Didi ce ke tafiya
cikin sasarfa yayin da hadimai biyu ke biye da ita hannu ta sanya ta buɗe ƙofar
falon yayin dasu kuma suka tsaya daga gefe.

Cikin Sassarfa ta ƙarasa shiga cikin falon Idanunta suka
sauƙa akan Mahaifinta Sheikh Jabeer, Mijinta Sarki Youssef Muhammad Mouley,
Waziri, Jakadiyar Sarki, Galadima cikin sauri da girmamawa Jakadiyar Sarki ta
miƙa mata hannu alamar tazo ta zauna

Kai ta gyaɗa kana ta zauna tare da kallon Mahaifinta wato
Sheiykh Jabeer cikin sanyi da yanayin damuwa ta furta.

“Abiey meke faruwa? Me nakeji? Kufahimtar dani na kasa
fahimtar abinda Dr Jameel da Hakim ke faɗa min shin gaskiya ne”.

Cikin sauri Jabeer bin Jabeer ya matsa kusa da ita tare da
riƙe hannunta cikin ƙauna da shaƙuwa ta Yah da ƙani yace.

“Didi ina ji ajikina ɗankine kuma tsatsonkine, ina ji
ajikina wannan mutumin dana gani ɗankine wallahi domin babu abinda ya raba shi
da Ibraahim kamanninsa da Ibraahim da kuma Mahaifinsa har ya ƙazanta.

Didi dai-dai da faratunsa irin na ƴaƴan kine”…

 

Aƙage ta matse hannunsa dake cikin nata kana idanunta cike
da ruwan hawaye tace.

“Toh waye shi? A ina yake? kununa min shi?, dan Allah kuyi
gaggawan kaini garesa domin idanuwa sun ƙagu suyi tozali dashi haka zalika kunnuwana
su ƙagu suji sautin Muryansa”.

Gyaran murya da Sheiykh
Jabeer yayi yasa ta dawo cikin nutsuwarta cike da kamala da tarin
nutsuwa ya furta.

“Fatima ki nutsu mana, ai komai yazo da sauƙi Bi’iznillahi
ta’ala ɗan da muka rasa tsawon shekaru, in Sha Allahu yazo garemu nima kaina na
gamsu wannan ɗankine tsatsonkine”.

Numfashi mai martaba ya fesar tare da muskutawa kana ya
furta.

“Nima inaji ajika babu haufi babu shakka ko tsoro wannan ɗana
ne jini nane Abeey yaron nan Aliyu nane babu haufi jikina da jinina da zuciyata
sun shaida min”.

Sai kuma ya maida kallonsa kan Sheykh Jabeer kana yace.

“Tabbas wannan al’amari ya girmama sai dai kuma yanzu saboda
idon Fada da kuma yadda al’amarin yaja hankalin mutane yana buƙatar sirri”.

Kai Jabeer bin Jabeer ya jinjina tare da sake tuno kamannin
Moddibo da kuma Ibraahim Sarki Youseep Muhammad Mouleey kuwa numfashi ya fesar
kana ya cigaba da faɗin.

“Ga kuma yanda ya shigo ya iya sarrafa *Rinƙas* yaja
hankalin mutane gaba ɗaya sannan kuma muna buƙatar tabbatarwa da shi kan
al’adun masarautar da sanar dashi dukkan abinda ya dace, dan haka sai zuwa
tsakiyar dare yanda hankalin mutane duk ya kau zamu shiga wajensa dan bincike
da tabbatar wa”.

Kai suka jinjina cike da gamsuwa da kalamansa sai kuma ya
maida idanunsa kan Sheykh Jabeer tare da faɗin.

“Abeey Wallahi wannan yaron ɗanane babu ma wani batun
tabbarwa inaji ajikina ɗanane tsatsonane ɗanane da muka rasa tsawon lokaci”.

Cikin fesar da numfashi Sheikh Jabeer yace.

“Ka kwantar hankalinka Youseep na sani amma akwai buƙatar bincike
akwai buƙatar mu san wani abu”.

Kai ya jinjina kana yace.

“Toh shikenan”. Kasancewar Sheykh Jabeer abokin Mahaifinsa
Muhammad Mouley ne yasa baya iya yi masa musu.

Galadima da tunda aka fara magana bai ce komai ba, sai yanzu
ya fesar da numfashi kana yace.

“Tabbas nima inaji ajikina wannan tsatson mune saboda inba
haka ba bai isa ya sarrafa *Rinƙas* ba sannan kamannin nan yayi yawa kana ku
kalli yanda yake bin taswiran gidan nan tamkar yasan wuraren, wannan yasa
nakeda tabbacin da wuya ace akwai wani abinda bai saniba na al’adunmu sai dai
abin tambayar shin taya hakan yakasance”.

Kai suka jinjina cike da gamsuwa kana suka cigaba da
tattauna maganar daga haka suka tashi daga taron.

Yayin da Didi kam daren wannan ranan haka ta suku-ku baki ɗaya
zuciyarta da nutsuwarta ya tafi izuwa ga ɗouki da kuma mararin son ganin yaron
da akece yana tsananin kama da Ibrahim ɗin ta koda kuwa abincine ta kasa ci.

 

   Acan ɓangaren
Moddibo kuwa yana zaune a inda yake batare daya motsa ba bare kuma yaci abinci
baki ɗaya abin duniya ya ishesa abubuwa goma da ashirin sun haɗe masa, tarin
tambayoyin a kansa sama da dozin wanda innayi kaɗai yakeson ji da ganin yayi
mata su, ahaka ya cigaba da zama kafin daga bisani wata zuciyar ta yanke
shawarar ya tashi koda zai iya samun wata ƙofa ta baya da zai fice.

 Ahankali ya miƙe tare
da kallon gefen daman sa inda ya shiga yayi alwala kana ya kalli falon daga
gefe ya hango wata ƙofa ahankali ya fita idanunsa suka sauƙa akan wani falo na
daban shima still yana ɗauke da ƙofa hagu da dama murɗa ƙofar yayi ya fita anan
yaga wani ƙofa hagu da dama sai kuma wani step daga tsakiyarsu daga can sama
shima kofa ce hagu da dama…

Hadimansa kuwa ganin ya fita yasa suka shiga taka masa baya
tunda basu da ikon hanasa cikin tsuke fuska ya kallesu, su kuwa cike da
girmamawa ɗayansu yace.

“Ranka ya daɗe ko akwai abinda kake buƙata?”.

Girgiza kai kana yace.

“Um-um babu abinda nake buƙata”.

Kai suka gyaɗa tare da faɗin.

“Toh”.

Tunda basu da ikon hanashi tafiya.

Cike da a nitsuwa yake tafiya har ya haura step ɗin yanda
ƙasan yake haka zalika saman yake komai na ginin iri ɗaya ne sai dai tsarin
Furnitures ɗin ne suka banbanta.

Kasancewar suna saman daga gefen dama komai White & Sky
blue kalar Sararin samaniya sai kuma daga can gefen Hagu komai na cikinsa ya kasance
Jane da ratsin fari haka nan yakeji kamar anayi ma shi jagorane.

 

Cikin fesar da numfashi ya koma kan step ɗin ya tsaya a
Balcony yana mai cigaba da kallon tsananin kyau da tsaruwan wajen tun da yake a
iya tsawon rayuwarsa bai taɓa kallon falo mai masifar girma da kyau irin wannan
ba.

Ahankali ya ɗaga idanunsa sama anan ya hango ainihin
tsakiyar Fadan.

Babbar Fadace mai masifar kyau da girma akwai wurare
daban-daban yayin da Part-part sunfi aƙirga iya inda idanunsa ke iya hangowa
Part-part ne ashimfiɗe sai kuma hadimai da yake hangowa suna zirga-zirga wanda
bazai iya ƙiyasta yawansu ba, ga wani irin wuta mai haske da ƙyalli daya haske
ko ina na cikin fadar tamkar rana kana ga bishiyoyin dabino da mijin gwanda
wanda duk ta inda ka cilla ido suke rausayawa sai zurga-zurga Hadimai keyi.

  Ahankali ya juya
bayansa daga gefe nan idanunsa suka hango wani garden Mai azabebben kyau daga
can bayan Garden ɗin kuwa wani Swimming pool ne dake ɗauke da ruwa Sky blue ga
wasu fararen kujeru kaman resting Chair dake gewaye da wajen kana daga ƙasa su
kuwa Grass Carpet ne da yayi dark blue Mai azabar kyau yayin da wasu irin
tsuntsaye masu kyan gani da daɗin sautin murya ke shawagi awajen wanda da alama
saboda ƙayatarwa aka ajiye su…

 

  Ya ɗauki tsawon
lokaci yana kallon wajen haka nan ya tsinci kansa da son ganin wajen domin
kallon wajen yatuno masa da Gembilan sak yanayin tsarin gidansu haka wajen yake
sai dai tsarin wannan ba suda yalwan Furanni haka kawai aransa yaji da ace za’a
bashi dama zai ƙawata Ilahirin Fadar da Furanni saboda arayuwar duniya babu
abinda ke sashi farin ciki kamar yai ta kallon Furanni har misalin 11:30 yana
tsaye awajen kafin ahankali ya motsa ƙafafunsa jin sun gaji da tsayuwa kana ya
gangaro ya dawo cikin ainihin falon da aka kawo sa…

 

Yana shiga falon ya zauna akan kujera tare da lumshe manyan
idanunsa dake lumshe yana mai sakin ajiyar zuciya akai-akai.

Zaman sa babu daɗe wa kamar misalin 12:00 yaji ƙaran ƙofa an
buɗe.

Jin ƙaran buɗe ƙofa yasa ya buɗe Idanunsa dake lumshe kana
yabi wajen da kallo…

Da mamaki yake kallon Jabeer bin Jabeer da suka haɗu ajirgi
kasancewar shine agaba.

Jabeer bin Jabeer kuwa cikin ƙaguwa ya maida idanunsa kan
Didi da Lalla Khadijah da Hafsat ke gefenta,
tare da cewa.

“Didi shigo kiganifa, Didi dan Allah ki ganshi da kyau fa”.

Sheikh Jabeer, Sarki Youseep Muhammad Mouleey, Waziri
Galadima, Sarkin Dawakai, Jakadiya, Mahaifiyar Sarki Niyna Lalla Khadijah da
Lalla Hafsat sai kuma Rahama dake can biya tana biyosu da sassarfa tare da faɗin.

“Didi ku jirani mana”.

Su kuwa cikin nutsuwa suka
shiga cikin falon.

Suna shiga Moddibo ya zuba musu ido cike da mamaki yake bin
Didi da Abualeey da wani irin amintaccen kallo yana mai jin wani irin yanayi na
ratsa mishi zuciya a kansu haka nan ya gaza janye idanushi a kansu sai bugun da
zuciyarsa keyi.

Lalla Khadijah da Hafsat kuwa ruggumeshi sukayi tare da
sakin wani sassayyan kuka, wannan na gefen dama wannan na gefen hagu,

Rahama kuma na isa, sai kawai ta kifen kanta bisa guiwowinsa
tare da faɗin.

“Yah Aleey laisa leeh misluka abadan, ana uhubbuki hubban
azeeman”.

wani irin amintaccen nitsuwa ne yaji yana ratsashi, wanda
yasa baisan lokacin da yasa tafukan hannunsa yana sharewa Lalla Khadijah da
Hafsat hawayeba.

Su kuwa Khadijah da Hafsat sai kuma suka ɗan janye jikinsu
tare da ruggume juna cike da tsananin farin cikin.

Ita kuwa Rahama cikin yanayin shogwaɓar ƴan auta take ɗan
kuka tare da cewa.

“Yah Ibraahim ina kake kazo kaga Yah Aleey na ya fika kyau
daga yauma niba ruwana da kai”.

Dan fesar da numfashi Modibbo yayi tare da sa hannushi yana ɗan
shafa bayan Rahama alamun tayi shiru.

 

Sarki Youseep Mouleey kuwa cikin kamala ya zauna bisa kujera
kana Sheikh Jabeer ma ya zauna gefensa yayin da Galadima, Waziri, Sarkin
Dawakai,  suka zauna a ƙasa.

 Amintattun Hadiman
dake biye dasu kuwa daga can baya dasu suka zauna.

Jakadiya kuwa idanunta akan Moddibo ta saki yalwataccen
murmushi mai cike da zallan farin ciki kana tace.

“Masha Allah nesa ta matso kusa abin nema ya samu”.

Moddibo kuwa idanu ya zuba musu baya ko ƙyaftawa ganin
Jabeer bin Jabeer ya zauna aƙasa gasu Galadima sai shima ya zamo daga kan
kushin ɗin ya zauna akan Carpet tare dasa hannunsa yana sharewa rahama hawaye.

Yayin da yake kallon Sheikh Jabeer cike da mamaki kasancewar
ya masa farin sani domin yasha zuwa wajensa a Adamawa sai dai baya samun haɗuwa
dashi cikin tsananin mamaki ya motsa laɓɓansa tare da faɗin.

“Sheikh Jabeer”.

Sheikh Jabeer na kallonsa tare da mamakin kiran sunan sa ya
furta.

“Na’am. Ka Sanni ne?”.

Ware idanu Moddibo yayi kana ya jinjina masa kai cikin sanyi
Murya da yanayin nutsuwarsa yace.

“Farin sani ma kuwa shekaran Kur’anin dana rubuta na farko
kusan uku awajenka wanda na rubuta daga baya kuma yayi cika shekara ɗaya
awajenka amma har yanzu ban samu an dubasuba.

Batare da Sheikh Jabeer ya janye idanunsa daga kansa ba
yace.

“Menene sunan ka”.

Moddibo kuwa ahankali yace.

“Sunana Moddibo daga Taraba nake tura maka wanda aminina
Jameel Bashir Mai Dala yake kai maka”.

Baki ɗaya falon ya sake yin shiru baka jin muryan kowa sai
na Moddibo da Sheikh Jabeer yayin da Didi da Sarki Youseep Mouleey kuwa jikinsu
ke wani irin tsuma aduk lokacin da Muryan Moddibo ya ratsa kunnensu.

Kai Sheikh Jabeer ya jinjina kana yace.

“Toh menene cikekken sunanka ai Moddibo ba sunan yanka
bane?”.

Lumshe idanu Moddibo yayi tare da buɗe su kana ya shafa
sajensa a hankali yace.

“Sunana Aliyu Youseep Muhammad Mouleey”.

Cikin matsanancin mamaki daya sake mamaye zuciyoyinsu da
tabbatar musu lallai babu haufi jininsu ne, akaro na barkatai suka juya suka
shiga kallon junansu da ƙyar Sheikh Jabeer ya furta.

“Kace me sunan ka?”.

Ahankali Moddibo ya kuma motsa laɓɓansa tare da faɗin.

“Sunana Aliyu Youseep Muhammad Mouleey”.

Cike da matsanancin mamaki daya daki zuciyoyinsu suka haɗa
baki wajen faɗin.

“Ikon Allah sunan ka kenan?”.

Kai ya gyaɗa yana ɗan ciza lips ɗin sa na ƙasa ya furta.

“Eh sunana kenan?”.

Ahankali Sheikh Jabeer ya furta.

“Ikon Allah toh waye mahaifinka”.

Araunane ya jingina bayansa da jikin Kujeran kana ya girgiza
kai tare da lumshe idanunsa yace.

“Babana ya rasu!”.

Da sauri Lalla Khadijah tace.

“Wlh mahaifinka na raye gashi nan a gabansa kusa da kai”.

 

Cikin Sauri Didi ta katse Khadijah ta hanyar daga mata
hannun, kana ta juyo ta kalli Modibbo zuciyarta na cigaba da bugawa da karfi
tamkar zai fasa ƙirjinta ya fito ta tace.

“Toh wacece Mahaifiyarka!?”.

Idanunsa cike da rauni ya buɗe ya kalleta kana yace.

“Mahaifiyata ma ta rasu”.

Cikin sauri Rahama tace.

“Ga Didi nan a gabanka a raye waya ce maka baka da mama”.

haka nan yakejin baya son kukan Rahma har ransa, ya kuma
lura ta ƙoshi da sakalci cikin sanyi yake jujjuya mata kai alamun kada tayi
kuka.

Sarki Youseep Mouleey kuwa cikin sauri yayi gyaran murya
tare da faɗin.

“Toh waya faɗa maka Iyayen ka sun rasu?”.

Moddibo kuwa cikin sanyi da fesar da numfashi ya kallesa
kana ya gyara zamansa tare da faɗin.

“Kakata ce ta faɗa min”.

Aƙage Sarki Youseep Mouleey ya kuma cewa.

“Shin wacece kakar ta ka?”.

Ahankali ya ɗaga yatsarsa tare da nuna musu hoton dake manne
jikin bango kana yace.

“Gata can Kakata na rasa ya akayi nazo na samu hotonta acikin
wannan Fadar taku”.

Cikin jin dadi Jabeer bin Jabeer yace.

“Aha bana faɗa mukuba, ai wlh dama na sani wannan daga gani
babu tambaya Aliyu ne”.

 

Da sauri Didi dake kuka ta matso kusa dashi tare rungumesa.

Shi kuwa Moddibo shiru yayi, sai idanunsa daya lumshe yayin
da lokaci ɗaya wani irin yalwataccen farin ciki ya lulluɓesa alokacin data
rungumesa tsintar kansa yayi da ɗaura tafukansa abayanta ya rungumeta lokaci ɗaya
kuwa yaji ruwan hawaye na cika masa idanunsa wanda bai san dalilin zuwan suba
kawai dai yasan yanajin wannan matar da yaranta har cikin ƙahon zuciyarsa
hakanan yakeji ya aminta da ita fiye da aminci da yayiwa ko wacce uwa a duniya.

 Haka zalika rungumar
da tayi masa ji yayi kamar Innayi ce ta ruggumeshi amman sai yakejin aminci da
son fiye yadda yake ji tare da innayi wannan ruggumar jinsa yayi ruggumace ta
mahaifiyar data ɗauki cikinsa tsawon wata tara da kwana tara ce ta kuma yi
naƙudarsa so a matsayin uwa zuciyarsa da jininsa suka amshi rungumesa da tayi
kamar yadda jikinsa zuciyarsa suka amshi Khadijah da Hafsat da Rahman a
matsayin tsotsonshi muharamansa, sabida jini baya ɓuya.

   Ji yake tamkar
rungumar da yake nemane tsawon shekara da shekaru ne wanda  bai samu ba.

 

Didi kuwa kuka ta saki hadda shesh-sheƙa batare data raba
jikinsu ba tace.

“Abeey wallahi wannan ɗana ne. Abba wallahi ɗana ne ku gani
taya za’a yi kuce sai kunyi wani bincike? ɗana ne Aliyuna ne fa Abba ɗana ne
fa”.

Kalmar da take maimaitawa kenan tana cigaba da kuka.

 

Da sauri Sheikh Jabeer ya riƙo hannunta kana yace.

“Fatima kada kiyi kuka na gamsu na kuma yadda ɗan kine kuma
tsatsonki ne nima ina ji ajikina tabbas tsatsonki ne kuma jikana”.

Ya ida maganar yana share mata hawayen daya ƙi tsayawa a
idanunta.

 

 Sarki Youseef Mouleey
kuwa cikin sauri ya buɗe wa Moddibo hannunsa kana cikin raunin murya da
tsantsar bege yake faɗin.

“Zo ɗana”.

Moddibo kuwa tsintar kansa yayi da gaza yi  musu gardama, kana zuciyarsa ta gamsu da
kalaman da suke faɗa.

Yayin da yake jin su ɗin wani sashe ne na jikinsa.

Da wani irin bege da shauƙi ya faɗa jikin Sarki Youseep
Mouleey ya rungumesa yayin da shima sarki Youseep Mouleey ya ƙanƙamesa ji yake
kamar idan ya sake sa tamkar zai sake nesa dashi ne ciki rauni yake faɗin.

“Shakka babu wannan Aliyu nane”.

Kallonsa ya mayar kan Sheikh Jabeer kana yace.

“Abeey wallahi wannan ɗana ne.

Allah sarki rayuwa. Allah ya ɗauki ran Mahaifina yau da yaga
jikinsa da zarrar da bai taɓa tunani da zato ba”.

Baki ɗaya kallonsu mutanen falon keyi cike da tarin
tausayinsu.

Sarki Youseep Mouleey kuwa cikin rauni da farin ciki ya sake
rungume Moddibo tare da kallon mahaifiyarsa Niyna yana  faɗin.

“Niyna yau da Abbana na raye da yaga Jikinsa da Zarrar da
zata girgiza Maƙiya, Da yaga jikinsa da zarrar da zata sa zuciyoyin maƙiya
cikin tashin hankali da firgita tabbas Aliyu ɗana ne Niyna kalleshi fa”.

Kai Niyna take jinjinawa cike da gamsuwa tana mai shafa kan
Modibbo.

 

Moddibo kuwa mamaki da al’ajabi ne ya cika masa zuciya
ahankali ya janye jikinsa daga na Mahaifin nasa kana ya koma ya zauna yana
binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.

 

Ahankali ya maida idanunsa kan hoton Innayi kana ya dawo da
kallonsa garesu cikin nutsuwa ya furta.

“Wacece wannan awajen ku? Kakata ce wacce da ita nake
rayuwa, Kuma ita kaɗai nake da ita a duniyata”.

Cikin sauri Didi ta girgiza masa kai tare da faɗin.

“Kana da kowa aduniya. Kana da ƙanne, kana da Yayu, Kana da
Mahaifi, Kana da Kakanni kakan ka ɗaya ne ya rasu Mahaifin Babanka, Kana da
zuri’a zuri’arka mai tarin yawa gaba ɗaya wannan masarautar family’nka ne.

Aleey a ina kuke rayuwa?”.

Tun da ta fara magana ya tsira mata idanu yana sauraren ta
har sai da tadasa aya kafin yace.

“A Nigeria muke rayuwa acikin Jahar Taraba Gembila” .

Da mamaki ta kallesa tare da faɗin.

“Allah sarki Innayi tana raye?”.

Da sauri ya kalleta jin Sunan Innayin sa abakinta sai kuma
ya jinjina kai kana yace.

“Eh Innayi tana raye”.

Still idanunta na zubda hawaye ta furta.

“Allah sarki Innayi tayi min halarci mai yawa ashe wasiƙar
data ajiye min da gaske ne ta kular min da ɗana kula mafi kyawu da inganci”.

 Zazzafan Ajiyar
zuciya ya sauke kana yace.

“Kin santa ne?”.

Kai ta jinjina masa tare da cewa.

“Na santa Hadima tace da aka haɗani da ita.

Jakadiyata da aka haɗani da ita tun daga lokacin da aka kawo
ni ƙasar Marocco, ashe data tashi ƙasata ta koma da ɗana kusa da Jahata dan ta
kular min da ɗana”.

Sai kuma ta lumshe idanunta akan Moddibo kana ta cigaba da
faɗin.

“Sannan sai da tayi sanadin yanda ɗana zai kasance mutumi na
gari har Alkur’ani mai girma ka rubuta ka kaiwa Mahaifina ya duba maka”.

Sai kuma ta mai da kallonta kan Sheikh Jabeer kana tace.

“Abeey Ya akayi baka taɓa kallonsa ba?”.

Sanyayyar numfashi Sheik Jabeer ya fesar cike da kamala
yace.

“Fatima wannan abubuwane da tattaunawarsu sai ahankali kiyi
haƙuri yanzu dai mu fara godewa Allah”.

Kai ta jinjina tana mai yin tasbihi azuciyarta…

 

Jakadiya kuwa cike da tsantsar farin ciki tace.

“Ai wannan ma babu bukatar wani bin cike ko wani abu tsatso
ne na gidan nan, jinine na gidan nan, haihuwa ne na gidan nan,Tarbiyya ce ta
gidan nan,Masha Allah”.

Ta sauƙe Ajiyar zuciya tare da cigaba da cewa.
_“Fatabarakallahu Akhsanul Khaliƙin_, Halittace ta gidan nan daga gani ma babu
tambaya tsatsone namu, ina Ibraahim yazo yaga ɗan uwansa da yake cewa yana haɗuwa
dashi acikin mafarkai”.

Haka nan suka ci-gaba da tattaunawa cike da al’ajabi da mamaki
wanda mgna ce ta gsky da gsky wacce gskyarce tayi aikin da dole Modibbo yaji
zuciyarsa ta gamsu da kalamansu koda suka fara yi mishi tambaya kan yadda ya
sarrafa Rinƙas ya shaida musu yasan Rinƙas a mafarkine ga mamkinsu dukkan wasu
al’adu ko wani abu na sittin masarautar duk ya sani.

 

Cike da kulawa Sheikh Jabeer ya kalli Moddibo kana yace.

“Moddibo ka shiga ka kwanta in Allah ya kaimu da safe zamu
ƙarasa magana”.

Kai ya jinjina kana yace.

“Wayoyina suna cikin mota ina so akawo min su ina buƙatar
mgn da innayi inada tarin tambayoyin da nakeso inyi mata”.

Kallonsa Sarki Youseep Mouleey kana ya girgiza masa kai tare
da faɗin.

“Kada ka damu duk abinda kake buƙata ga hadimanka za’a yi
maka sannan duk tambayoyinka ka tarasu lokacin amsasu nan tafe”.

Kai ya gyaɗa yana mai cigaba da jin nutsuwa su kuwa sallama
suka masa kana suka fice.

 

            Nigeria
Gembulan

Dai-dai lokacin kuma Naseer ne, zaune tsakiya falonshi wasu
hawaye masu zafin gaskene wani ke korar wani, tunda yaje gidan Lamiɗo, hira
wurin Amina da Lamiɗo da kanshi ya sanar masa an daura auren Khausar da Modibbo
ya kasa ƙara sawa cikin gidanma ya juyo ya dawo, kuka yayi tayi tamkar mace har
yanzu ɗaya gaza bari kife kansa yayi bisa guiwowinsa a fili yake faɗin.

“Khausar ya za’ayi jinin haka, duk wani burina da sha’awata
a kanki ne, na soki tun baki san kanki ba, rana tsaka ba zato ba tsammani inji
wai an aura miki Modibbo, shike nan na rasaki kenan, domin na sani yafi ƙarfin
iyawata, bani da abinda zan iyayi a kanshi, yayi min zarrar rayuwa ya kwace min
ke”.

Sai kuma ya ɗan tsagaita kukan tare da kallon wayarsa da
kiran Amina ya shigo, cikin tarin takaici ya kashe wayar a fili yace.

“Khausar ne kaɗai a raina Amina zan dai aureki ne dan biyan
buƙatar rayuwata, da kuma rage jarabar rashin malakar Khausar ne”.

Haka yaci gaba da surutai kamar zautacce, Allah ya sani
baiyi zaton hakaba.

 

            Rabat
Marocco

Washe gari tun shida da rabi na safe  ƴan uwanshi mata suka shigo a jere, Lalla
Hafsat ce riƙe da wani tray mai ɗauke da wasu ƴan ƙaran kwanuka masu kayan
gani, Ragama kuwa wayace makale a kafaɗarta. inda yake suka nufa, jawo stoll
Hafsat tayi tare da ajiye trayn kana ta fara haɗa mishi tea.

Lalla Khadijah kuwa hannun ta miƙe mishintare da yimishi
sallama alamun musabaha takeso suyi.

a hankali ya ɗago hannunsa na dama ya miƙa ta, dai-dai
lokacin kuma Rahama ta manna mishi wayar dake hannunta a kunne, tare da cewa.

“Yah Aleey ga Yah Ibraahim daga jiya zuwa yau ya kirani yafi
sau goma, wai in ban haɗuka ba yaji muryarka in ya dawo bazai min mgn ba”.

Ɗan murmushin gefen baki yayi tare da sa hannushi na hagu ya
amshi wayar.

It kuwa Rahama cikin jin dadi ta kalli askin kan Modibbo
tare da cewa.

“Lah Yah Aleey ko askinkafa irin na ahlin masarautar Mouley
ne”. sai kuma ta ƙara sunkuyowa kanshi tare da cewa.

“Lah Adda Khadi zoki gani, wlh shima yanada naɗeɗɗen gashin
irin na Abualeey”.

Numfashi me ɗan tsawo ya fesar ganin Hafsat na miƙa mishi
cup ɗin tea da kuma turo masa stoll din gabanshi tare da cewa.

“Bisimillah Didi tace ka ɗan taɓa wannan kafin ta ƙarasamaka
breakfast inka”.

Longwaɓar da kai yayi tare da ɗan yamutsa fuska kana a
hankali yace.

“Toh me ɗaya zanyi mgn a waya ko cin abinci ko gaisuwar ku,
ko kuma kallon kaina zan bari Rahama tayi tayi”.

Ya ƙare mgnar da amsa sallamar da yaji anyi mishi da muryar
da ta kasance irin tasa sak.

Sai kuma ya ɗanyi murmushi jin Ibraahim na cewa.

“Yah Aleey ka koresu in ba hakaba bazasu Barka ka huta ba fa
more especially Rahama Bata da aiki sai suru”.

Cikin sanyi yace.

“Kana ina yanzu Ibraahim kai ban gankaba”.

Cikin jin daɗi Ibraahim yace.

“Ina Istanbul, nima jiya na tafi da safe kai kuma ka isa da
yamma”.

Kai ya gyaɗa tare da kallon Hafsat dake miƙa mishi tea ɗin
amsa yayi da hannunsa na dama. Ya lura kusan halinta iri ɗaya ne da nashi bata
da yawan surutu da fara’a sosai sai dai kuma tana da kula.

Lalla Khadijah kuwa miƙewa tayi tare da cewa.

“Bari inje in taya Didi aiki”.

Kai ya gyaɗa mata kana ta fita.

Daga nan yaci gaba da mgn da Ibraahim, tare da kallon Hafsat
dake ƙara mishi siymil wani abinci su ne na larabawan can da fulawa akeyishin
sai dai ya wadatu da nama.

 

Cup din ya miƙawa Rahama tare da kallon Hafsat kana yace.

“Alhamdullah na ƙoshi, kai ta jinjina kana ta tattara wurin
tare da cewa.

“Toh kaje ka ɗan kwanta ka huta, ke kuma Rahana zomi
tafi”.

Kai jinjina mata, daga nan suka fita suka tafi.

 

Sai misalin ƙarfe 9:30 Didi ce da Sarki Youseep Mouleey suka
shiga falon suna shiga suka ji falon shiru alamar baya nan yayin da suka fara
jiyo wani sautin murya mai daɗi da sanya nutsuwa na karatun Alkur’ani na ratsa
kunnensu.

Cikin nutsuwa Sarki Youseep Mouleey ya fara bin direction ɗin
da  yake jiyo sautin karatun Yayin da
Didi ke biye dashi.

Akan darduma suka hango sa da alama Salatul duha ya idar
kana idanunsa na lumshe yana karatun akansa.

Daga gefensa suka zauna lokaci ɗaya hawaye ya shiga bin
kuncinta cike da farin ciki ta ɗaga hannunta sama kana tace.

“Alhamdulillah Innayi kinyi min duk kan gatan duniya kin
bawa ɗana Ilimi mafi girman ilimi mafi tsada da daraja wanda zai amfanesa
duniya da lahira sannan zai amfanemu”.

Sai ta kuma kalli Moddibo still hawaye na kwaranya daga
idanunta ta cigaba da faɗin.

“Wannan ɗana ne yake karatun Alkur’ani tamkar acikin harami
wanda koda acikin harami sai an jinjina masa”.

Moddibo kuwa jin sautin Muryanta da kuma motsin Mahaifinsa
yasa ya buɗe Idanunsa jin tana cigaba da cewa.

“Innayi Allah ya biya ki da mafificin Al’khairi Ubangiji
Allah ya sadamu inyi miki *SAKAYYAH* da mafi kyawun abinda ki kayi min sannan
inyi miki godiyar da ban san da wani irin baki zan miki ba”.

Ahankali Moddibo ya shafa addu’a kasancewar yazo ƙarshen
surar da yake karantawa.

Anutse ya juya ya kallesu haka nan zuciyarsa ta aminta da
cewa Tabbas suɗin wasu ababene na jikinsa da Zaran ya kalli Mahaifinsa zai ga
tsananin kamanninsa dashi babu abinda ya raba su shi kansa kamanninsa da
mutumin yana bashi mamaki babu abinda ya rabasu sai dai shi Modibbo yawan
shekarun sa bai kai nasa ba zuwa yanzu ya gama gamsuwa iyayensa ne su.

Cike da ladabi ya gaishe su kana suka amsa cikin sakin fuska
da tarin ƙaunarsa.

 

Didi kuwa ahankali ta janyo basket data shigo dashi ta ajiye
agabansa, tare da fitar da kulolin, kana ta ɗauki plate ta zuba masa abincin da
ta dafa mishi da kanta, kana ta kalleshi cike da so da ƙauna tace.

“Wannan abinci da kaina na shiga kitchen na dafa maka dan
kaci da kyau”.

Cikin gamsuwa da kalamanta ya jinjina kai ya tabbatar
nutsuwa da kamalarta da kuma kimarta tafi ƙarfin tayi masa ƙarya maganganun da
take faɗa daga zuciyarta ne kuma gaskiya ne babu shakka ko haufi aciki shi
kanshi ya gamsu mahaifiyarsa ce ita Abualeey kuwa mahaifinsa ne masarautar
Mouley kuwa tabbas mahaifarsace…

Fuska ɗauke da yalwataccen murmushi Sarki Youseep Mouleey ya
janyo Cup tare da faɗin.

“Ni kuma da kaina zan haɗa maka tea in baka duk kan kulawar
daka rasa atare damu na tsawon shekaru, in Sha Allah sai mun haɗa ta mun baka a
iya tsawon sauran Rayuwar da Allah ya ƙadddara mana anan gaba”.

Cikin wani irin tattali da kulawa suka ci-gaba da faɗa masa
maganganu masu sanyi da ratsa ƙwaƙwalwa wanda ko wani ɗa yake fatan saurara
daga iyayensa.

Moddibo kuwa tamkar amafarki haka yake jin abubuwan sai dai
wani lokaci wani abu ya taɓa ganinsa amafarki sa.

Haka suka cigaba da kulawa dashi suna hira da kara fahimtar
yasan komai ma masarautarsu, yinin wannan rana suna tare dashi koda motsi yayi
zasu tambayesa me yake so ko kuma me yake buƙata sai gab Azahar suka yi masa
sallama suka fita suna tafiya aka kira sallar Azahar…

Anan yayi Sallar Azahar ɗin sa yinin wannan ranan ma ba’a buɗe
sa.

Haka yayi kwanaki biyu anan batare daya fita koda ƙofan
falon ba sai dai akawo masa abinci sai dai kuma su shigo suyi hira dashi…

Yau ta kasance Asabar inda ya zama kwanakinsa uku kenan a
Masarautar Mouleey bayan fitar Mahaifiyarsa, Mahaifinsa da kuma Sheikh Jabeer
yana zaune a falon kamar daga sama ya fara jiyo shesh-sheƙan kuka.

Cikin sauri ya juya ya kalli Hadiman dake tare dashi sai
kuma ya kauda kansa ganin basu bane cikin yanayin mamaki da al’ajabi ya juya
gabas da yamma kudu da Arewa  yaga dai
duk basu bane keyi kukan. Bisa alamu kuma kamar su basujiba, ahankali ya miƙe
ya nufi Corridor har ya isa falon nan ma ba kowa sai dai yana jin shesh-sheƙan
kukan daga cikin bedroom cikin sassarfa ya nufi bedroom ɗin yana shiga ya hangi
Jalaluddeen ne zaune agefen gadon yana kuka tamkar ransa zai fita.

Cike da matsanancin mamaki gami da al’ajabi yace.

“Jalaluddeen k…”…..

Leave a Reply

Back to top button