Hausa NovelsSakayyah Book 2 Complete

Sakayyah Book 2 Page 14

Sponsored Links

 


By

Related Articles

 *GARKUWAR
MARUBUTA**SAKAYYAH book 2… Page 14*

 

       Na

*Aysha Aliyu Garkuwa*

 

*Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn,
masu cewa wai sun goda suga number’n nayine, ko kuma a’a bari dai in na shirya
zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuɗin bai cikaba tukun sai sun cika, ko
kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh in ba iyayiba ai duk nisan state da
kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen wajema.
Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba ku daina
min mgnar ku bari sai kun shirya,kada kizo ki ɓata min lokaci a banza, wlh ni
na tsani harkar karanta, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuɗin kaya
ga account no ga numberta ai sai ki biya kawai kafin kimin mgn. Tunda dai ga
alamominshi da duk illar da yakeyi na faɗi in kina dashi faƙat in babu kada ki
wani zo kice min bayani dan ko kinzo iya bayanin da zan miki kenan*

Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha’awa. Ƙaiƙayin
gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin.
Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya,
melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni’ima. Buɗewar gaba,
domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi
al’ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin
wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa,
da dai sauran abubudann ban  lissafa.
Sune manyan alamomin infection.

Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman
kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari
kiji illolin infection wato cutar sanyi.

Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin
kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi
bare wata ni’ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta
lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya,
zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk
tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki
nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.

KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA
BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya
dauke miki dukkan sinadaran ni’imomin ki, da sha’awarki, duk kayan matan da
zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki
magunguna GARKUWAR MA’AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau,  duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji
sha’awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta
gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai
kiji Doctor’s suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic
infection ne yar uwa.

INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara,
Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar
komai Maganin na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk
nacin infection koda na cikin mahaifane bi’izinillahi ta’ala zaki rabu dashi,
cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da
maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki
ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da
mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da
shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma’ana zai
sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a
jikinsu musamman ya’ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita
miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin
garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin
10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz
bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER’N
na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau
kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya.
Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso
in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada
kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA’AURATA.

 

Da sauri Hajia Bunayyah ta zubawa Didi, idanu sabida a
zatonta, lamarin zai zo da gardama ne, ta yadda zasu koma Nigeria da Khausar,
ga mamakinta sai taga Didi ta gaza ƙarasa kalmar bakinta, sai juyawa tayi ta
fuskanci alƙibla, tare da yin sujudul Shukur cike da yalwataccen farin ciki da
yasa hawaye fara zubomata.

Wani irin malolon bakinci ne, ya takari ƙahon zuciyarta, sai
kuma tayi ƙasa da kanta, jin Didi na cewa.

“Alhamdulillah wannan mgnar itace mafi daɗi a cikin dukkan
bayanan da kikayi mana Innayi kin gama min komai a rayuwata”.

Lamiɗo kuwa sassayyan numfashi ya fesar hakama Bappa Jimeta
da kuma Abban Jameel. Hajja Nana kuwa ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe tare da
gyara zamanta cikin jin daɗin nagartar ahlin Modibbo, yanzu matsalarta ɗayace,
ta yaya Modibbo zai karɓi Khausar wacce irin tarba zaiyi mata a matsayinta na
matar da aminshi ne yayi mishi zaɓinta, bawai dan ita ɗin zaɓin rashi bane,
gouron numfashi ta kuma fesarwa tare dayi mgnar zuci.

“Dole in sa ido kafin komawarmu inga irin tarɓa da kuma
yanadin da yaron nan zai amshi Khausar a matsayin mata, muddin naga abinda bai
minba, ko alamu. Tozarci ko cin fuska, Allah shine shaida wlh bazan bar jikata
a wulaƙanta min ita a ƙasar da bata da kowa nata ba.”

Sai kuma  ta juyo
kanta ta kali Niyna kakar Modibbo kenan mahaifiyar Abualeey, cikin kamala
kawaici mutuntaka gami da aminci tace.

“Ku shirya idan Allah ya kaimu gobe da yamma akwai taro na
musamman, wanda dama an shiryashi tun kwana uku baya, don zamu gabatar da Aleey
a gaban family’nsa, tuni Fada take amsar bakunar ƴaƴanta da jikokinta na nesa
dana kusa, domin wannan shine buri da fatan dukkan ahlinmu. Toh Alhamdulillah
gabatarwa ta ƙara armashi tunda da matar Aleey ta aure ta sunnan ma’aki S.A.W.
za’ayi taro”.

Sai kuma ta kalli Jakadiya tare da cewa.

“Jakadiya a sanarwa sarki shiri a shirya gangamin gabatarwar
da na aure. Kana ki gayawa Gimbiyya Lailai ta tanadi kayan amarya dana ango, a
kuma fidda ƙoren al’ada”.

Cikin biyayya da girmamawa Jakadiya ke amsawa da.

“An gabama Gimbiya Shatu”.

Sai kuma ta kalli Sarki Youseep Mouleey tare da cewa.

“A sanarwar faɗa gobe babu zama, kana taron na family ne,
idan Allah ya kaimu jibi kuwa za’a gabatar da Aleey a Fada, da kuma bayyanenne
matsayinss”.

Yah Salam Didi kam sai wasu hawayen farin cikin ne ke zuba
mata wani ba korar wani.

Galadima kuwa da Waziri kawai murmushi sukeyi kai kace anyi
musu bushara da al’jannane.

 

Sheykh Jabeer kuwa a
gyaran murya yayi tare da kallon matar amininsa Marigayi Sarki Muhammad
Mouley, da ɗan murmushi a fuska yace.

“Da dai kada a yawanta bidi’a a lamarin, kuma da an sirranta
shi ko”.

Cikin sauri Galadima yace.

“Yah Sheykh ai Aleey ya sirrantu tsawon shekaru talatin ai
yanzu kam lokacin bayyanar sa ce tayi, dole ya fito ko domin girgiza zuƙatan
sauran  ɗan burbushi magauta duk da dama
suna zaton haka tunda kowa yasan labarin wasiƙar da Innayi ta bari kafin
tafiyar kuma a san shi ba a tsinci gawarsa ba kamar yadda ake tsinta na
yayunshi da suka gabata, masu fariyar dole sarauta ta bar hannun ahlin Aliyu
Mouley, su san cewafa ga wani Aleey mazan”.

Murmushi mai ɗan sauti Sheykh Jabeer yayi dan shi kansa
al’amarin yana tsumashi yana tuna mishi irin magautan da suka fuskanta a
masarautar Joɗo, shida har tsuntsuwa aka meda mahaifiyarsa. *A Littafin GARKUWA
sai gashi kuma ƴar shima ta faɗa irin gidan*

Innayi kuwa cikin yaƙini tace.

“Da izinin Allah su da Aliyu na sai dai kallo basu da zarrar
iya cutar dashi”.

Cikin gamsuwa Sarki Youseep Mouleey ya gyara zamansa tare da
fuskatarsu kana yace.

“Aje a fara shiri”. Daga nan aka watse taro cike da jin daɗi.

 

Didi ce zaune a bakin gadon ta na alfarma yayinda

Lalla Khadijah da Hafsat dake zaune a gabanta cikin tsananin
happy tace.

“Didi kin ko tuna cewa gobene birthday ɗin Aliyu”.

Kai ta jinjina tare da kallon Rahama da ta miƙe zaune tana
mai danna wayarta tace.

“Didi kice inyi gayyata ta mu samman”.

Ta ƙare mgnar tana shiga group ensu na  Mouley family.

Didi kuwa cikin jin daɗi tace.

“Ai kuwa Rahama ki gayyata ta musamman domin bikine na
musamman.

Sai kuma ta kalli Hafsat tare da cewa.

“Ki kira ƙawarki Islam kuje
Ryad square shopping mall. Ku ɗebo dukkan abinda ya dace, kama daga na
amarya da shi Aleey.

Daga nan in kun taso ku biya Marocco Mall ki ku zaɓo dukkan
abin buƙata na al’adun amaren masarautar Mouley, Hafsat so nake komai ya zama
na musamman ne”.

Cikin sanin manufar mahaifiyar tasu ta ce yanzuma kuwa Didi.

 

Khadija kuwa da sauri tace.

Amman sai munje munga amaryar kafin mu tafi”.

Gyaɗa musu kai Didi tayi tare da cewa.

Nima yanzu zan tafi sashin Niyna dan ance min su Goggonku
Salma da Zakariyya sun iso”.

Daga nan ta miƙe ta fita.

Rahama kuma tana gama fesa labarin hidimar da za’ayi a
masarautar tasu gobe misalin ƙarfe huɗu na yamma.

Ta kuma shiga group ɗin na ƙawayenta.

Nan ta fesa musu.

 

A masauƙinsu Khausar kuwa bayan su Ummin da Innayi sun dawo
cikin farin ciki Ummu ta zauna kusa da Khausar dake riƙe da kwanon
ƙasaitacciyar mace da Ummin ta dama mata tun kafin su tafi.

Ƙwaffa tayi tare da cewa.

“Wai Khausar har yanzu baki shanye damun nan ba?”.

Fuska ta ɗan kwanɓe tare da cewa.

“Allah ko Ummi abun babu daɗin”.

Da sauri Asma’u tace.

“Ni dai Wlh yayi min daɗi gaba ɗaya gumbunan da da garukan ɗaɗine
dasu, wani garɗi kamar na dabino da aya da kwakwa harda ɗanɗannon zumafa a
ciki, Ummi gashi da zaƙin su ƙungiyar alewa da kuma mazarƙwaila”.

Da sauri Ummu tace.

“Toh sha zumami kice mana wanda aka ɗan sha ɗin ma kece kika
shanye. da kike koro jawabi haka”.

Yar dariya tayi tare da rufe idonta kana tace.

“Sai daifa gsky kuma duk da kayan dadin akwai itatuwa da
jijiyoyi dan naji ƙamshi jijiyar ilanwaddihi ma da ma kwaranyi wanda kike yawan
aikena in amso miki wurin Innayi”.

Harara Ummi ta cilla wa Asma’u tare da cewa.

“Dama ai mgni kam bazai yi ɗaɗiba, maza Khausar kafa kai ki
shaye”.

Cikin rumtse idanun ta kafa kanta ta fara sha.

Saida tasha kusan rabi kana ta janye kwanon tare da kwaɓe
fuska tace.

“Wlh Ummi ni dama can kayan zaƙi bai cika dakuna ba, nafi
son abun yaji-yaji kiga mana kazar nan da kika dafa min duk da babu daɗi  amman dana zumbuɗa yaji na cinyeshi fes. Kuma
Kinga Wanda Aunty Hajara ma ta kawo min na cinyeshi. Shi kam ma yafi rashin daɗi
dan da ƙyar naci tanata zagina wai dubu ashirin da takwas ta biya AYSHA ALIYU
GARKUWA ta dafa minshi wai zuciyar farin ragone”.

Haɗe fuska Ummi tayi tare da cewa.

“Kuma wannan ɗinma sai kin shanyeba”.

Jin haka yasa ta kafa kai ta shanye, tare da ajiye kwanon
kana tace. “Alhamdulillah na gama”.

Cikin sauƙe numfashi Ummi tace.

“Yanzu muka dawo daga sashin kiran da akayi mana, munje bisa
jagorancin innayi”.

 

Da sauri Asma’u tace.

“Ummi kunga Yah Modibbo?”.

Kai ta jujjuya mata tare da cewa.

“Bamu ganshiba, baima san munzoba, innayi ma sunce ta bari
sai gobe zata ganshi”.

Taɓe baki Khausar tayi tare da cewa.

“Uhmm me ake ta ɓoyeshi sai kace kuɗine shi ko zinari”.

Zura mata ido Asma’u tayi tare cewa.

“Yoh ba doleba, sun san akwai mai ƙar mishi kallo har gashin
ƙeyarsa ta iso”.

Harara ta cillawa Asma’u tare da cewa.

“Waya ma damu da dashi”.

Murmushi Ummi tayi
tare da faɗin.

“Yanzu dai tashi kiyi Wonka, tunda dilken ya kai awa biyu a
jikinki”.

Da sauri tace to, tare da miƙewa ta nufi bathroom din.

 

Asma’u kuwa falo ta nufa jin innayi na kiranta.

 

Zaune ta sameta dasu Hajia Bunayyah da kuma su Aunty Hauwa
duk dai waɗanda suka zo tasu.

Gyara zama tayi tare da kallon su ɗaya bayan ɗaya kana tace.

“Idan Allah ya kaimu gobe za’a fara hidimar bikin Khausar da
Modibbo kamar yadda al’adar masarautar Mouley takeyi.

Dan haka ku shirya karfe huɗu na yamma ne za’a fara.

Zuwa Maggarib an gama na gobe sai kuma zuwa jibi.

Cikin tsinkewa da lamarin cigaban da Khausar ta samu Hajia
Bunayyah tace.

“Uhmm Allah ya kaimu”.

Sai kuma ta yunƙura zata tashi.

A hankali ta koma zaune jin muryar Hajja Nana na cewa.

“Bisa alamu dai Khausar taci ribar ƙin auren ɗan mayu, abu
ya haɗu, sunna ta haɗu da farilka, sakekke ya haɗu da sakekkiya, wato bazawari
ya samu bazawara ɗan maye da ƴar Mayu, jikar tsarki da jikan sarki”.

Cikin takaici Hajia Bunayyah tace.

“Kamar yaya kuma Sunan ta hadu da farilla?”.

Kai Hajja Nana ta jinjina cikin isa kasaitar data motsomata
yau tace.

“Eh ɗan babban Sarkin Mouley na kasar Marocco ya auri jikar
babban Sarkin Gombawa na ƙasar Nigeria jihar Gombe, kin san su dama su Khausar
kirarinsu Gombawa ɗiban fari ba’a kwana dasu ba a tashi dasu, Gombe doma
hamadar sarki lahirar sulaimanu”.

Da sauri Innayi ta kalleta cikin rashin fahimta ita kuwa
Hajja Nana cikin ƙasaita tace.

“Yoh da ji kikeyi ku kadaine keda masarauta, to idan baki
saniba, Sarki  Buba Yero shine tsohon
mijina kuma kakansu Khausar,  barina  Gombe da mahaifin Khausar da bappanta
Muhammad, ne yasa masarautar ta koma hannun kaninsu ɗan abokiyar zamata, kuma
shi har yanzu jira yake Yayanshi bappan Khausar yaje ya karɓi ragamar mulki dan
su masarautarsu sunada imani da ƙaunar juna babu wani tsaface-tsaface, nice na
hana sabida ni kwanciyar hankali ƙannena yafi min”.

A hankali Ummi dake jiyo Hajja Nana ta fesar da numfashi
tare da cewa.

“Haba sai haka mana ƙasaita da isar Hajja Nana tayi yawa,
ita kanta Khausar ƙasaitarta da kwarjinin ba irin na normal mutane bani,
kwarjinin ta yawa gareshi.

 

Sai kuma ta kalli Khausar da fitowar ta kenan daga Bathroom.

“Masha Allah”. Shine abinda Ummi ta faɗa sabida ganin wani
irin sheƙi da ƙellin da fatar Khausar keyi kai kace tarwaɗace, tsabar farin da
tayi kace balarabiyace.

 

Gashin kanta dake tubke ta zubawa ido.

Sai kuma ta kalli Khausar ɗin dake tsane jikinta tare da
miƙa mata.

Man shafawa, da dauko handdryer kana ta dawo ta bayanta.

Tare da fara busar mata da gashin dan ya ɗan jike. yaje mata
tayi tare shafa mata mai.

Ita kuwa Khausar mai take shafawa a jikinta kusan a tare
suka gama.

Ajiye handdryer ɗin Ummi tayi tare da juyowa gefen gadon
inda akwatuna set ke jere,  ɗaya pink ɗaya
blue, wanda Ummi ce ta bada aka haɗawa Khausar ɗin Kayan lefe, kana kuma shine
aka kai gidansu dangi da abokan arziƙi suka gani.

Wanda suma Hajia Bunayyah dai bata samu abin kushewa ba.

 

Na forkon ta buɗe wanda tun a gida Asma’u ta haɗa dukkan
abin buƙata da kuma kayan da Khausar ɗin zata saka har gama bikin.

Wata Dubai Abaya Ummi ta zaro mata, Black color sai kuma
zare golding color da aka yiwa rigar aiki zuɓi na musamman mai masifar kyau da
ratsin fari kaɗan  rigar irin mai ɗan faɗin
nanne musamman daga sama. sai kuma ta zaro mata wani tattausan mondo Wanda
bazai wuce iya guiwarta ba, sai bra su duka fararare, turare ta zaro kusan kala
uku ta feshesu dashi. Kana ta ɗauko Kulaccar sirri wacce ta saya wurin AYSHA
ALIYU GARKUWA, miƙa mata tayi tare da cewa.

Gashi ki shafa wannan.

Amsa Khausar ɗin tayi tare da cewa.

“Ayyah Ummi a tubke min gashin nan”.

To Ummin tace tare da fara tubke mata shin.

Tana gama ta nufi falo tare da cewa.

In kin gama kizo, kai kawai Khausar ɗin ta gyaɗa mata.

 

A can Falo kuwa Hajia Bunayyah ce ta miƙe jiki a salube ta
shige ɗakin da nanne masauƙinsa inta da Aunty Hajara da kuma Aunty Ruƙayya.

Da sauri ta maida ƙofar ɗakin ta rufe tare da dannawa Hajia
Lami kira a wayarta.

Bugu ɗaya ana biyu Hajia Lami ta ɗauka tare da cewa.

“Mutanen Marocco yaya akayi?”.

Cikin fesar da numfashi mai zafi Hajia Bunayyah tayi kwafa
tare da cewa.

“Wllhi Allah Hajia Lami munyi babbar asara daba Samira
wannan yaron ya auraba. Na rantse miki da Allah munyi asarar samun daular
duniya.

Wannan shegiyar yarinya
mai idanu kamar na mujiya ko yaushe suna lunshe kamar mai jin bacci anya
ma kuwa ba idanun dunane da ita ba.

Kinga tayi nisa ta barmu da Naseer ɗin da ubansa ko Sarkin
tasha bai taɓa samuba, ke kuwa ta bar miki ƴa da wari da yoyon ƙazanta”.

Nannauyan numfashi Hajia Lami ta fesar tare da cewa.

“Toh yanzu me abinyi?”.

Cikin tsananin hasada Hajia Bunayyah ta buga hannunta da
jikin gini tare da cewa.

“Wallahi Allah ni dai na rantse da Allah, sai na kashe auren
nan, koda zan tafi tsirarane sai na watsa aurenan, muddin ina raye wlh Khausar
bazata ji daɗin rayuwarta a gidan nan ba, idan zaki zo mu haɗa hannun da ƙarfe
mu tumɓuke auren nan, mu shiga da Samira gidan to ki fara shiri, domin ina
dawowa zamu bazama”.

Cikin ƙeƙashewae zuciya Hajia Lami tace.

“Ai ke dai Allah ya dawo dake lafiya, Ƙawata na sama mana
labarin wani ƙasurgumin boka a ƙasar Niger cikin dajin Damagaran ance min
aikinshi kamar yankan wuƙane, babu haufi shi bazama ka biyaba sai buƙatar ka ta
biya”.

Cikin yaƙini tace.

“Ke dai ki shirya ina dawowa zamu tafi”.

Daga nan suka katse kiran kana ta fito.

 

A falon kuwa da sauri su Ummi suka ƙali ƙofar falon jin
sallamar Jakadiya da kuma su Lalla Khadijah da Hafsat.

Cikin sakin fuska Ummi da Innayi suka amsa tare da nuna musu
wurin zama.

Zama sukayi cikin sakin fuska da cikekken fulatancinsu da
suka iya ta sanadin Didi suka kalli su gaisa cikin mutumtaka.

Jakadiyace ta kalli Lalla Hafsat tare da juyowa ta kalli
innayi kana tace.

“Dama yayun Aliyu ne suka zo ganin ƙanwar tasu tare da
marabtanta.

 Cikin jin dadi Ummi
tace.

“Ayyah to babu laifi barin in kirawota”.

Sai kuma ta mike ta nufi dakin da Khausar take.

“Masha Allah diyata kinga yadda kikayi kyau kuwa”.
Murmushi tayi tare da rufe fuskarta da tafukan hannunta.

Ita kuwa Ummi kamo hannunta tayi ta ajiyeta tare da cewa.

Zo mu je ki gaisa da yayun Modibbo.

Da sauri ta sunkuyar da kai ganin yadda Ummi ke gyara mata
tarhan da tayi da gyalen abayar sosai tayi masifar kyau ta fito cas da ita a
matashiyar budurwar yar kimanin shekaru 19 zuwa 20. Duk da rigar nada faɗi bai
hana kyan surar jikinta bayyana ba.

 

A hankali suka fito falon.

Khausar kam kanta a ƙasa take wani irin amintaccen taku mai
cike da nitsuwa.

 

Da sauri Lalla Khadijah ta miƙe tsaye lokacin da suka iso
tsakiyar falon.

Hannunta ta buɗewa Khausar tare da faɗin.

“Wow  Masha Allah, Didi
dai ta samu ƙarin diya wannan ai in an ganta da Rahama kai kace
tagwayene”. Murmushi mai yelwa Lalla Hafsat ma tayi tare da miƙawa Khausar
hannun a hankali Khausar ta ɗan janye jikinta dan jikin Lalla Khadijah ta ɗan
saketa.

 

Ruggumeta Hafsat tayi tare da cewa.

“Masha Allah,  Khausar
muna farin ciki da shigarki Mouley family. Allah ya baki hikima da basirar zama
tsakiyar wannan Fada”.

Kusan a tare suka amsa da Amin ita kuwa Khausar yatsun
hannunta take ɗan murza tare da ɗan rusunawa kana ta gaidasu.

Amsawa sukayi suna mai ƙare mata kallo. Cikin ɗan sakin
fuska Hafsat tace.

“Ai wannan  komai nata
kamar na Rahama zaiyi mata dai-dai”.

Cikin girmamawa Jakadiyarsu tace.

“Sosai ma kuwa”. Ita kuwa Hafsat hannun Khausar ta kamo tare
da cewa.

“Takalmi sise nawa kike sawa”.

Cikin sanyin murya tace.

“37”. Da sauri Khadijah tace.

“uhm jinjina sise ɗin Rahama kenan”.

Sai kuma ita Khadijah ta kamo hannun Khausar tare da ajiyeta
gefen Innayi kana tace.

“Zauna abinki. Didi da Niyna sunyi miki Barka da zuwa,
masarautar Mouley. Yanzu mu zamu fita ne.”

A hankali tace.

“Allah ya kiyaye hanya.”

Amin sukace a tare sai kuma suka ɗan kalli Asma’u tare dayi
mata murmushi suke.

“Ke me sunanki?”.

“Asma’u”.

Murmushi Khadijah tayi kana tace.

“Yauwa toh in ba matsala innayi zamu tafi da ita, ai kin san
sise ɗin Khausar da kalanta ko?”.

Cikin fara’a Asma’u tace.

“Sosai ma kuwa, Nama fita sanin abinda yake mata kyau”.

Dariya sukayi ganin hararar da Khausar ta cilla mata..

Ummi kuwa murmushi kawai tayi.

 

Daga nan suka fita da Asma’u.

 

Sune basu dawoba sai gab da Maggarib.

 

Acan Side din da Modibbo yake kuwa.

Zaune yake shi da Ibrahim da Dr Jameel.

Cikin tsuke fuska ya kalli Dr Jameel dake zoro wayarsa daga
aljihu.

“Baby”. Ya faɗa a saman lips enshi.

Sai kuma ya tsaida idonsa kan Modibbo da ya wani irin
tsaresa da idanu.

A hankali yace.

“Yah dai Malam kallon nan fa?”.

Fuska Modibbo ya kuma tsukewa tare da cewa.

“Kaji tsoron Allah, Dr J kasani. Abinda kakeyi kana tafiya
cikin fushin Ubangiji ne, kuma masifar zunubinka zaiyi ta bibiyarka tun anan
gidan duniya, kasan cewa abinda kayiwa ƴaƴan wasu za’ayiwa ƴaƴan ka, shin me
ribarka a cikin in har ka jazawa ahlinka. Ka tuna shifa zina tsananin muninsa
yasa Allah baice kada kuyi zinaba,  cewa
yayi kadama ku kusaceshi fa. Shifa mazinaci baya zina har sai an zare mishi
imaninshi. Kasan kuwa abinda Allah ya tanadarwa mazinata abinsha a cikin
jahannama?”.

Cikin tsananin sanyin jiki Dr Jameel ya rumtse idanunsu tare
da cewa.

“Nifa shiyasa badon Abualeey da kansa yace min dole in
kasance kusa da kaina wlh bazanzoba sabida na lura kai mutumne mai tsaraɓe-tsaraɓen
halal da haram”.

Cikin takaici Modibbo yace.

“Koda baka zo inda nakeba kasa a ranka in dai ina cikin
ƙasarnan, sai na kasance tare da kai, na kuma yi al’ƙawari zan ƴaƙi shsiɗanin
dake tare da kai, in Sha Allah sai ka dawo managarci tamkar J na”.

Murmushi Dr Jameel yayi tare da kallon hadimai guda huku da
suka shigo da manyan jakukkuna guda biyar
masu ɗauke da tambarin Anfaplace mall Marocco.

Da sauri Ibraahim ya miƙe tare da cewa.

“Ku shigo dasu cikin bedroom kada ku barsu a nan”.

Jin hakane yasa suka bishi a baya.

Kusan a tare suka shirya kayan cikin wodurob.

 

Daga bisani suka fito falon, a tsaye ya samu Dr Jameel.

“Mujeko  Ibraahim”.
Cewar Dr Jameel.

Kai Ibraahim ya gyaɗa tare da bin bayanshi sai kuma ya juyo
ya kalli.

Moddibo dake cewa.

“Wai dan Allah Ibraahim sai yaushe za’a buɗeni in samu zuwa
jam’in salla, wlh abinfa yana damuna.

Sassan numfashi Ibraahim ya fesar kana a hankali ya juyo ya
dawo gaban Modibbo tare da cewa.

“Kayi haƙuri Yah Aleey in Sha Allah gobe dai a jam’i zakayi
sallan magarib. Akwai babban dalilin ne da yasa ba’a barka ka fitoba.

Ƙwaffa Modibbo yayi tare da lumshe idonsa Allah ya sani suna
ƙona mishi rai da batun hanashi jam’i da wotoyinsa.

 

Shi kuwa Ibraahim juyawa yayi yabi bayan Dr Jameel suka
tafi.

 

Washe gari tun safe Dr Jameel da Jabeer bin Jabeer da kuma
Ibrahim suka shigo wurin Modibbo.

Tare da wani Kekkyawan matashi wanda bazai wuce sa’an
Modibbo ba.

Cikin sakin fuska matashin ya bawa Modibbo hannu tare da
cewa.

“Sunana Zakariyya Khallin”.

Cikin ɗan sakin fuska Modibbo yace.

“Masha Allah”.

Ibrahim ne ya amshi mgnr da cewa.

“Yah Aleey Wannan ɗan Goggo Salma ne  ƙanwar Abualeey. Shi a India yake shima
likitane, taron gabatar da kaine ya kawoshi.”

Murmushi Modibbo yayi tare sake bashi hannun, shi kuwa
Zakariyya ruggume Modibbo yayi tare da faɗin.

“Duk da zumuɗin Mami na rigata ganin ɗan yayanta”.

Shi kuwa Modibbo Ibraahim ya kalla jin yana cewa.

“Dr Jameel ma ɗan Goggonmu ne Aunty Sahrah itake bin Goggo
Salam, kuma babanshi Aminin Abualeey ne ɗan ƙasar Turkey, duk dangin babanshi
suna can”.

Dr Jameel kuwa numfashi ya ɗan fesar kana yace.

“Ni ya labarin Yusuf ne, kwana biyu bamuci wayaba”.

Da sauri Zakariyya yace.

“Ya tafi Mexico kasanshi ya nacewa Zeeyada yar Lalla Hafsat”.

Sai kuma ya kalli Modibbo tare da cewa.

“Yusuf ɗan Unclee Haroon Mouley ne, ƙanin Unlee Youseep
Mouleey”.

Cikin fahimta Modibbo yace.

“Na fahimta, toh amman kuma tunda nazo banga Unclee Haroon ɗinba”.

Cikin sanyi Dr Jameel yace.

“Dashi da Mamina, da Abbana duk rana daya sukayi haɗari, su
sun rasu shi kuwa har yau baida lfy tsawon shekaru ashirin da biyar kenan”.

Cikin sanyin jiki da tsananin tausayi Modibbo yace.

“Allah sarki Jameel Allah ya jiƙansu da rahama yasa sun huta
shi kuma Unclee Haroon Allah ya ya bashi lfy”.

Da Amin suka amsa baki ɗayan su.

Shi kuwa Modibbo cikin sanyi ya kalli Dr Jameel tare da
cewa.

“Dan J kabar abinda kakeyi ka zamewa Aunty Sahra da Abba
al’waladussaliha ko dan basa raya ka zame musu sanadin samun lada”.

Cikin sanyi jiki Dr Jameel yayi ƙasa da kansa yana mai
taunan lips inshi na ƙasa.

Shi kuwa Modibbo a raunace yace.

“Mu kuwa zamuci gaba dayi maka Addu’o’i Allah ya shiryeka”.

Amin suka amsa a tare.

Sai kuma Ibrahim yace.

“Yauwa mu shiga daga ciki masu gyara zasu shigo gyara nan ɗin”.

Toh sukace kana suka shiga Corridor nan tare suka shiga
ƙofar nan ta dama inda Modibbo yake, a falon suka zauna.

Zamansu ba jimawa Rahman ta shigo da hadimai da sunka kawo
musu breakfast.

 

Acan Side ɗin dasu Khausar suke kuwa, suma tuni an kawo musu
breakfast, dama dukkan abin buƙata.

 

A nan wannan falon kuwa, zuwa bayan an isar da sallam
la’asar  duk an gama ƙawatashi da
shiryashi irin shirin nan na al’farmar da kamala.

Kujerun gaba ɗaya an mannasu da ginin duk da girman falon
wai dan a samu ya ƙara girma.

Wata kujera mai zaman mutum biyu aka ajiye daka san tsakiyar
falon. Sai kuma wasu datsa-datsan Turkiy Carpet masu masifar kyau da taushi. Da
aka shimfiɗa a gaban kujerar, wacce duk ta inda ka shigo zaka kalli waɗanda ke
ka kujerar. Sai kuma wasu tukwanen kasa masu zanen ɗawisu da aka jere gefe da
gefen kujerar yayinda daga sama tukwanen kuwa, gashin gezan ɗawisunne a cikin
mai cikekken launi daban-daban, sai kuma wani tim-tim da aka ajiye a guda biyu
a gaban kujerar wanda da bisa alamun anan waɗanda zasu zauna kan kujerar zasu
daura sawunsu.

Sai kuma hadimai guda uku ɗaya na bayan kujerar ɗaya na
gefen dama ɗaya na gefen hagu.

Kana duk inda ka wulga idanunka a falan kaskon turaren
wutane mai fasar da sassayan kanshi.

Sai kuma sanyin ac dake ratsa ko ina, an sassake labulayen,
tare da kuna wutan falon baki ɗaya a ƙalla falon zai iya ɗaukan mutun settun
zuwa tamanin.

 

A nan sashin dasu Khausar suke kuwa.

Wasu matane guda biyu, aka kawo dan shirya kausar,
Kasancewarsu ƙwararrun masu shirya amare, wanda suke zaune acikin masarautar
musamman domin gyara da kuma ƙyale amare.

Wata Haɗaddiyar rigar Caftan and Takchitas suka sanyawa
Khausar din, wacce ta kasance farace ƙal, mai ɗauke da ratsin adon gold da kuma
sky blue wato kalan sararin samaniya.

Rigace me tsananin kyau da takasance traditional wedding
dress wanda ƴan masarautar Mouley morocco ke sawa lokacin biki, sosai rigar ta
zauna ajikin kausar, tayi mata ɗas tare da k’ara bayyana tsantsar kyaunta,
musamman da suka ɗaura mata tsadadden sarƙan gold da kuma ƴan kunne haɗi da
awarwaro da kuma zobunan gold, wanda suka ƙara cika adon nata, babban mayafin
daya kasance fari ƙal, wanda aka kewaye bakinsa da tsararren ado me kalan sky
blue, suka sanya mata akanta, wanda ya sauko har yakai ga ya rufe kyakkyawar fuskarta.

Masha Allah da wannan tsananin kyaun da kausar tayi, wanda
kallo ɗaya zakayi mata kasan ta cika mace har mace, saboda tsananin kyaun da
traditional wedding dress din yayi mata, a kyawawan ƙafafunta kuwa wani haɗadɗen
takalmi irin nasu na sarauta me kalan sararin samaniya suka sanya mata, daya
sake k’awata shigan nata. Duk da kafafun nata ba lalle dan innayi ta hana a
saka mata.

 

Su kansu sun yaba da kyaun yarinyar domin tunda suke shirya
amare basu taɓa shirya amaryar da tayi kyau sosai kamar wannan ba, kai kace
asalinta balarabiyar Morocco’n ce, musamman yanda jikinta ke fitar da
sihirtaccen k’amshi kulaccar sirri da me matuk’ar ratsa zuciya haɗi da daɗin
shaƙa.

 

“Masha Allah, tsarki ya tabbata ga Ubangiji me tsara
kyawawan halittun da yayi wannan halittar da ta kasance tamkar farin fure
acikin tarin jajayen furanni, Allahumma Barik.”

 

Cewar Lalla Khadija da shigowarta kenan, cikin shigar
ƙasaita.

 

“Masha Allah.”

Ta kuma faɗa tana me miƙawa su Asma’u, Dija da kuma Asiya
kayan dake hannunta, wanda suna ɗaya daga cikin kayan da aka kawowa kausar
jiya, dogayen riguna ne guda uku masu matukar kyau.

“Ga wannan kuma ku sanya, domin naga kaman kune ƙawayen
amarya.”

Amsa sukayi suna godiya..

Leave a Reply

Back to top button