Hausa NovelsSakayyah Book 2 Complete

Sakayyah Book 2 Page 4

Sponsored Links

 


By

Related Articles

      *GARKUWAR
MARUBUTA**SAKAYYAH book 2… Page 4*

             Na

*Aysha Aliyu Garkuwa*

 

Zare ido Hajja Nana tayi cike da matsanancin mamaki al’ajabi
haɗi da alhini.

Tayi salati tare da tafa hannu.

Muryanta na cike da mmki, takaici, haɗi da fusata  ta cigaba da cewa.

“Ohh Allah ya kawo mu ƙarshen duniya, yarinya babu tsoron
Allah bare aje ga babin kunya ki dubi tsabar Idona ki kuma dubi tsabar idon
Mutumin dake matsayin Mahaifinki, sannan ki dubi tsakar idon Mahaifiyarki kice
wai wane kike so!”.

Cikin raunin Khausar tayi ƙasa da kanta tana mai rumtse
idonta tana jin wani irin yanayi mai cike da rauni azuciyarta.

Wani shegen kallo Hajja Nana ta watsa mata cikin tsananin
fushi da ɓacin rai tace.

“Wanene shi Moddibo? wani gantalellen yadine Moddibon? shin
inane tushensa su waye ne Asalinsa dame yafi ɗan uwanki da har kika zaɓe sa
kika ƙyale ɗan Uwanki dame yake taƙama!?”.

Ta ida maganar tana me tsare Khausar da ta ɗan ɗago kanta
fuska cike da rauni, ita Hajja Nana da idanun fusata ta banka mata harara.

 

Ita kuwa Khausar ahankali ta sake sunkuyar da kanta ƙasa
batare da tace. Uffan ba yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke tsuma.

Cikin sanyi Lamiɗo ya sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi tare da
jinjina kansa kana ya maida kallonsa kan Khausar da kanta ke ƙasa.

Mommy kuwa cikin yanayin mamaki da yadda maganar tazo mata
abazata ta tsirawa Khausar Ido tana maimaita abinda Khausar ta faɗa aƙasan
ranta.

 

Girgiza kai Hajja Nana tayi tare da juyawa ta kalli Mommy
tare da sakin kuka kana tace.

“Yanzu Aysha Ina magana kema kinyi min banza, baza ku bani
amsaba, wato ni zaku mayar gantalalliya ga tsohuwar banza tana magana dole ku
shareni tunda kun mayar dani bansan abinda nake ba”.

Sai kuma ta maida kallonta kan Khausar cikin matsanancin ɓacin
rai da kuka tsufa tace.

“Yanzu abinda kika zaɓawa kanki kenan Khausar!?.

Yanzu abinda zaki yimin kenan? Kice ba kyason ɗan Uwanki?.
Wannan dangin Mayu da kika ce bakyaso ai ban damu ba amma ki dubi tsabar Idona
kice bakyason jininki ɗan uwanki yaro mai mutunci da kamala?”.

Mommy, Lamiɗo, da Dije baki ɗaya Idanu suka zubawa Hajja
Nana suna kallon yadda take kukan tsakaninta da Allah Khausar kuwa still Kanta
na ƙasa ita kadai tasan abinda take ji.

 

Cikin fushi da tsawa Hajja Nana ta kalli Khausar data ƙi ɗago
kanta tace.

“Waye shin dame yafi Aliyu?.

Wato dai ya tabbata babu tsoron Allah acikin waɗannan
tsayayyun idanun naki, banda lalacewa da taɓarɓarewar tarbiyarki shin har kina
da bakin da Iyayenki na maganar aurenki zaki sanya naki aciki da masifar
tijara?”.

 

Cikin sanyi Khausar ta ɗago kanta, tare da buɗe idanunta
wanda tuni suka sauya launi daga farin madara zuwa jan rushi, cikin rauni ta
kalli Hajja Nana dake zazzaga bala’i kamar ba gobe.

Sai kuma ta lumshe idanunta kana ta buɗe,   amma ko ƙala bata ceba.

Afusace Hajja Nana dake kuka tace.

“Maza ki daina kallona da wannan.

 Fitsararrun idanunki
dake tsaye kamar Nonon maza tunda kin shafawa Idanunki baƙin kwalli, adole gaki
ƴar tijara.

Ohoɗijam kai ni wallahi tallahi billahil-azem tunda nake ban
taɓa kallon abinda ya gigitani ya ratsa ƙwaƙwalwa ta irin wannan maganar taki
ba!”.

Sai kuma ta sanya bakin zaninta tare da sharce hawaye da yar
majina still tana kuka tace.

“Yanzu Khausar me kike nufi dani?, kina nufin Baffanki da
yayi tattaki tun daga Adamawa yazo nan yazo abanza mu taso tun daga Jauro yaya
da sanyin safiya munyi a wofi kenan?.

Ki dubi tsabar Idanun mu saboda baki da kunya kice bakyason
Jikana sannan ki dubi tsabar idon Baffanki kice bakyason.

 Ɗansa  bayan shi zai bada Aurenki?”.

Kasa ɗago kai Khausar tayi ta kalleta sabida wani irin abu
take ji azuciyarta yayin da hawaye suka shiga bin kuncinta.

Mommy Kam ta gumi tayi baki ɗaya kanta ya kulle da lamarin ta
rasa ta yanda zata fara misalta abin.

 

Lamiɗo kuwa ganin yanda Hajja Nana ke kuka haiƙan ƙadaran
tana surutai yasa ya sassauta muryarsa tare da cewa.

“Dan Allah Hajja Nana kiyi haƙuri ki daina wannan kukan”.

Saurin ɗaga masa hannu tayi still tana kuka tace.

“A’a barni idan banyi kuka ba me kake so inyi tunda Allah ya
haɗani da gantalalliyar jika dake son kunyatani a Idanun duniya anya yarinyar
nan tana da hankali kuwa kodai akwai abinda ke damun aƙwaƙwalwar , hegiya
fitsararriya”.

Cikin rauni da alamun damuwa Khausar ta ɗago Idanunta dake
jiƙe da ruwan hawaye ta kalli Hajja Nana muryanta na rawa cikin sanyin tace.

“Dan Allah ni. Ki daina zagina Hajja Nana ki daina Sheganta
ni ke kinfi kowa sanin cewa niba Shegiya bace kuma ki daina zagin Ubana ki
daina saka shi acikin wannan maganar ki barshi ya kwanta akabarinsa cikin
nutsuwa da salama tun da dai ba wani mugun abu na aikata ba bare kiyita ihu
kina son tara mana mutane”.

Cikin fushi da takaici Mommy ta Kai hannunta na dama tare da
kwaɗawa bakinta mari kana ta watsa mata Harara tare da cewa.

“Rufe min baki fitsarariya mara kunya. Wallahi Khausar kin
bani mamaki sam ban taɓa zaton haka daga gareki ba agaban idanun mu Khausar
yaushe kika zama haka ni zaki kunyata?”.

Da sauri Khausar taja baya tare da fashewa da matsanancin
kuka me tsuma zuciya.

Cikin sanyi Lamiɗo ya kalli Khausar dake kuka tamkar ranta
zai fita kana yace.

“Khausar tashi ki tafi ɗaki”.

Da gudu ta miƙe ta nufi ɗakinta, kana Dije ta mara mata
baya. Khausar na shiga ɗaki ta faɗa kan gado tare da fashewa da matsanancin
Kuka me tsuma zuciya da ban tausayi yayin da hawaye wani ke bin wani suna
kwaranya daga Idanunta.

 

Acan Falon kuwa ta inda Hajja Nana ke shiga ba tanan take
fita ba, baki ɗaya Idanunta sun rufe sai Masifa take zazzaga musu musamman Mommy
ganin yanda take zazzaga Masifa ba Full stop bare commer yasa Lamiɗo kasa fadar
abinda ke ransa cikin sanyin murya da ladabi yace.

“Dan Allah Hajja Nana kiyi haƙuri, muyi mgnar a tsanake,
kinfa san shi Aure fa rabone, sannan nufi ne na Ubangiji sannan matar mutum
kabarinsa, idan har Allah ya ƙadarta cewa Aliyu shine mijin Khausar to fa duk
duniya idan za’a haɗu babu wanda ya isa ya raba wannan auren”.

Wani irin kallo Hajja Nana ke binsa dashi tana mai tafasa
dan masifa.

Cike da ladabi da kuma sanyin murya Lamiɗo ya cigaba da
cewa.

“Idan kuma har Allah bai ƙadarta cewa Aliyu shine mijinta
ba, tofa babu wanda ya isa yasa hakan ya kasance, dan haka dan Allah kiyi
haƙuri Insha Allah komai zai dai-dai ta”.

 

Girgiza kai Hajja Nana tayi tare da juyawa ta kalli Mommy da
kanta ke ƙasa cikin fushi tace.

“Lallai Aysha dama irin wannan tarbiyyar kika bawa ƴarki
kenan?

Yanzu mu awajen mu wace yarinya ce ta isa ta kalli tsabar
idon magabatan ta tace wai ga wanda take so wannan abin kunyar har ina?”.

Cikin sanyi da alamun damuwa Mommy ke kallonta baki daya ta
rasa wani kalma za tayi amfani dashi wajen bawa Hajja Nana haƙuri.

 

Hajja Nana kuwa ƙwaffa tayi cikin rawan murya ta cigaba da
cewa.

“Tirrr da wannan rayuwa wai yarinya ƙarama kamar Khausar har
tasan ta tsaya agaban manya tace ita ga wanda take so, watoma kenan itace
zatayiwa kanta zaɓin mijin da zata aura.

To mu azamanin mu koda ya rinya itace Sarauniyar kyau idan
magabatan ta suka zaba mata miji koda kuma shine Sarkin munin duniya haka zata
zauna dashi bare me Khausar zata nunawa Aliyu?Mutumin da koda kyaune ya fita”.

 

Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauke tare da gyara zaman sa kana ya
tsira mata idanu yana mamakin yanda ta ɗauki al’amarin da zafi kawai dan
Khausar tace Moddibo take so shine ta kafa aƙota sai kace wacce akace tayi
cikin shege shi kam baiga abin tada jijiyoyin wuya akan maganar ba.

Numfashi ya fesar tare da sassauta muryarsa yace.

“Dan Allah Hajja Nana kiyi haƙuri Insha Allah komai zai
dai-dai ta akwai yarinta atare da Khausar har yanzu bata mallaki hankalin kanta
ba, amma bawai dan baki isa da ita bane yasa tayi magana”.

Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da ɗago kanta kana cikin
sanyin murya ta kalli Hajja Nana dake matsar kwallar da taƙi fitowa tace.

“Dan Allah Hajja kiyi haƙuri wallahi Ni kaina ban taɓa jin
wannan kalmar abakin Khausar ba, sai yau da ace tun farko naji to wallahi bazan
bari ya fito fili ba zan dakatar da ita”.

Wani irin kallo Hajja Nana ta watsa mata tare da ƙankance
ido tace.

“Wallahi ƙarya kike Aysha Babu ta yanda za ayi ƴarki na
soyayya da wani amma baki sani ba, kawai dai so kike kinuna min iyakata akan
Khausar kuma kisani duk abinda zakiyi ke dai baki  isa ki canza matsayina ba”.

Kai Mommy ta girgiza cikin sanyi da ladabi ta cigaba da bata
haƙuri haka zalika Lamiɗo hakuri kawai suke bata.

 

Miƙewa Hajja Nana tayi tare da ƙankance Ido ta kalli Lamiɗo
da Mommy kana ta ya mutse baki tare da cewa.

“Ni dai Wallahi Allah wannan maganar jinta nake kamar saɓon
Allah”.

Cike da damuwa Mommy tace.

“Dan Allah kiyi haƙuri ki zauna. Khausar tayi kuskure amma
zamuyi wa tufkar hanci”.

Cikin sauri Hajja Nana ta kalli Mommy tare da faɗin.

“In zauna fa kika ce? Inani ina zaman nan? Ina sam nikam
banga wajen zama ba. Subhanallah Allah ya tsareni ai sai Girgiza ƙasa ya rufta
dani aciki yarinya budurwa yarinya ƙarama har tanada tsaurin idon da zata zauna
tsakanin magabatan ta masu aurar da ita, ta iya buɗe baki tace bata son zaɓin
su sai zabinta”.

Ta ida maganar tare da ficewa tana mita, da korwa da
kororowa haɗi da kormoto.

Cikin sauri Lamiɗo da Mommy suka bi bayanta cike da
girmamawa suke bata haƙuri amma firr wannan fitinenniyar tsohuwa taƙi
sauraronsu tafiya kawai take tana kumfar baki, har ta isa Farfajiyar gidan.

Dai-dai lokacin Hajiya Bunayya ta fito tare da kallon Hajja
Nana sai kuma ta maida kallonta kan Mommy dake aikin rarrashin Hajja Nana tana
bata haƙuri tace.

“Aysha lafiya kuwa yau nakeji hayaniya naga kamar ran Hajja
Nana aɓace”.

Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe cikin sanyin murya tace.

“Dan Allah Hajiya ki tayamu bata haƙuri fushi tayi”.

Kallon Hajja Nana. Hajiya Bunayya tayi da murmushi afuskarta
tace.

“Ayyah Hajja Nana kiyi haƙuri dan Allah”.

Ko kallonta Hajja Nana ba tayi ba bare ta tanka ta ta nufi
jikin mota.

 

Baffa Jimeta da Baffa Liman dake zaune Falon Lamiɗo kuwa
jiyo hayaniyarta yasa sukayi saurin miƙewa tsaye, sai kuma suka nufi wajan jin
Muryan Hajja Nana na tashi cikin sauri suka fito tsaye suka hangota jikin motar
tana ta sababi kallon Baffa Liman Baffa Jimeta yayi cike da mamaki yace.

“Yau kuma waya taɓo Hajja Nana haka?”.

Girgiza kai Baffa Liman yayi tare da faɗin.

“Allahu a’alam amma dai baya wuce Khausar ba”.

 

Suna isa jikin Motar Baffa Jimeta ya matsa kusa da ita tare
da sassauta murya yace.

“Hajja lafiya kuwa me yafaru?”.

Kallonsa tayi cikin fushi tace.

“Wuce mu tafi ina Liman maza ku wuce mutafi wannan gida ba
gidan zuwa bane gidan fitsararru da rashin tarbiyya”.

Dai-dai lokacin Gimbiya Dadu ta fito daga sashen ta jin
hayaniyar babu walwala afuskarta ta kalli Hajja Nana tare da cewa.

“Dakata!, Mukam ba fitsararru marasa tarbiyya bane Jikar
kice dai fitsararriya mara tarbiyya”.

Afusace Hajja Nana ta kalleta tare da ɗaga mata hannu cikin
fushi da ɗaga murya tace.

“Keee dakata kada kice zaki faɗa min magana”.

Cikin sauri Lamiɗo ya juya ya kalli Gimbiya Dadu cikin
sanyin murya yace.

“Dan Allah Mama kada kiyi magana, ki taya mu bata haƙuri
baki san meye ɓata mata rai ba”.

Taɓe baki Gimbiya Dadu tayi kana tace.

“Yo aiji nayi tana haɗa mana Jami’n zuriya gaba ɗaya ne tana
aibanta mu”.

Tafe hannu Hajja Nana tayi tare da ƙankance ido kana tace.

“Toh Zuri’ar taku ta arziƙi ce? Nace zuru’ar taku har wata
kayan gabas ce? Kin sani dai na sani. ko kuma wata tsiyace da ita zuri’ar
Mayu”.

 

Girgiza kai Baffa Jimeta yayi tare da cewa.

“Inalillahi Ash’sha haba Hajja Nana dan Allah kiyi haƙuri
mana”.

Kusa da ita Baffa Liman ya matsa cike da rarrashi yace.

“Dan Allah Addah Hajja am kiyi haƙuri ki kwantar da hankalin
ki kizo muje mu zauna”.

Girgiza kai tayi tare da faɗin.

“Inaaa zan zauna mutafi kawai nifa bazan zauna awannan gidan
ba wallahi banga wajen zama ba wannan abin kunya da tashin zuciyar ba dani ba”.

Ganin yanda ta tashi hankalinta yasa Baffa Jimeta ya buɗe
mata bayan mota tashiga sannan ya zagaya yashiga mazaunin Driver Baffa Liman ya
zauna gefensa.

Ahankali Lamiɗo ya matsa jikin motar ta Side din da hajja
Nana ke zaune cike da ladabi yace.

“Dan Allah Hajja kiyi haƙuri akan abin da ya faru”.

Girgiza kai tayi tare da cewa.

“Ba komai Lamiɗo ai ba laifin ka bane, ai kai baka da laifi
aciki laifin uwarta ne da ita kanta”.

Mommy Kam da kallo tabi motar har ya fice daga gidan.

 

Bayan sun fita Baffa Jimeta ya juya tare da kallon Hajja
Nana da tayi kicin-kicin da fuska kana yace.

“Toh Hajja yanzu gida zamu tafi kenan?”.

Girgiza kai tayi tare da cewa.

“Kaini gidan ƙawata Innare”.

Jinjina kai yayi kana yace.

“Toh”.

Kai tsaye gidan su Moddibo ya nufa da motar.

 

Acan gidansu Abba kuwa zaune yake afalonsa cikin yanayin
shiru-shirun daya saba ya tallafe haɓarsa da hannunsa na dama baki ɗaya ya rame
dan bai cika Lafiya ba ahankali ya kalli center table dake gabansa jin wayarsa
na ruri ɗauka sunan Manager company sa dake Marocco ne ya bayyana Picking Yayi
tare da kaiwa Kunnensa sannan yayi sallama.

 

Bayan sun gaisa Manager ya fara mishi mgn da larabci kamar
yadda suka saba yace.

“Yallaɓai sabbin kaya da mukayi Order daga Chaina sun iso
gaba ɗaya sannan ana bukatar kai ko ni wani ya zamana yana wajen domin aikin
sabbin na’uran sarrafa  Arabia Gawn da
mukeson fara sabbin samfurin.

To gashi kuma ni yanzu ba na nan, kasan ina India naje aduba
min lafiyar ƙafana to dole since sai an wakilta wani kafin asauke kayan aga
yanayin da abubuwan suka iso lafiya”.

Jingina kai Abba yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya kana yace.

“Toh kuma gashi nima kuma ban cika lafiya ba kullum ina fama
da matsanancin ciwon kai, dama can a tsarina Jameel ne zai wakilceni aiyi
aikin”.

Cike da tausayawa Manager yace.

“Ayyah Allah Ubangiji ya sawwaka.

 Yallaɓai sai dai a
cigaba da haƙuri Jameelu kuwa Allah yajiƙan sa ya gafarta masa, amma ya kamata
asamu awakilta wani tunda bana nan ga kaya sun iso gashi audugar da aka tura da
Nigeria ta iso, kuma tunda tazoma bamuyi mgnar ba sabida wannan iftila’in ɓatan
Jameel”.

Jinjina kai Abba yayi tare da cewa.

“Toh shikenan, amman bazan samu zuwa ba, domin nima kaina ba
lafiyar bace dani amma Insha Allah zan turo Aliyu yazo zaiyi dukkan abinda ya
dace”.

Kai Manager ya gyaɗa kana yace.

“Toh Allah ya bada iko dan kaya sun iso tun jiya suketa
ƙoƙarin za afara aikin sauƙe kayayyakin da ayyukan su masu motocin ma sun matsa
min don suna so su fita cikin Company’n dan sunce basu son su wuce kwana biyar
zuwa takwas, in sun wuce haka kuma sai in za’ainta biyansu ne”.

Cikin sanyin murya Abba yace.

 “Toh shikenan ba
komai Insha Allah zanyi wa Moddibo magana zai zo yanzu zan kira shi in sha
Allah in this week zai shigo Marocco”.

 

Acan gidan su Moddibo kuwa abakin ƙofa Baffa Jimeta yayi
Parking din motarsa cikin sauri Hajja Nana ta buɗe Murfin motar ta fita tare da
buɗe gate din gidan tashiga.

Da kallo Baffa Jimeta da Baffa Liman suka bita har ta shige
cikin gidan.

 

Ita kuwa tana shiga tun daga ƙaramin gate da zai sadata da ɗaya
sashen   ta fara doka sallama tare da faɗin.

“Innare! Innare!! Innare!!!Bakya Nan ne!?”.

Cikin sauri Innayi ta fito daga ɗakinta da murmushi
afuskarta tace.

“A’a wannan muryar wa nake ji kamar Hajja Nana”.

Kai Hajja Nana ta gyaɗa tare da cewa.

“Eh Innare nice dai”.

Murmushi Innayi tayi tare da ƙarasawa kusa da ita tace.

“A lale maraba Barka da zuwa Maraba maraba mu shiga daga
ciki”.

Kai Hajja Nana ta gyaɗa sannan suka shiga ciki cike da
kulawa Innayi ta ajiye mata ruwa da abin taɓawa Sannan ta kalli Hajja Nana dake
ta cika tana batsewa tace.

“Hajjia Nana mutan maka da Madina Bismillahi”.

Girgiza kai Hajja Nana tayi kana tace.

“A’a bazan iya cin komai ba barshi kawai Nagode”.

 

“Meye faru kuma?”.

 

Girgiza kai  tayi cike
datakaici tace.

“Ƴaƴan zamani kai Allah ya kyauta”.

Zama Innayi ta gyara tare da cewa.

“Waya taɓoki?”.

Ƙwaffa Hajja Nana tayi kana tace.

“Hegiyar yarinyar nanne fitsararriya gantalalliyar yarinya
da batasan abin da ya dace da kanta ba, ana nuna mata gabas tana ga yamma.”

Sai kuma ta fesar da numfashin kana taci gaba.

“Uyumm yarinya har an kai matakin da yarinya ƙarama ana
magana tana mgna ta fetsare Idanunta ta kalli idanun Magabatan ta tace wai
tayiwa kanta zaɓin mijin Aure”.

 

Ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe tare da kallon Hajja Nana kana
tace.

“Wace yarinya ce haka”.

Cike da takaici Hajja Nana tace.

“Khausar mana”.

Cike da Mamaki Innayi tace.

“Ha’a Khausar kuma wace Khausar ɗin?”.

Jinina kai Hajja Nana tayi tace.

“Eh Khausar jikata”.

Gyaɗa kai Innayi tayi tare da cewa.

“Eh na fahimta.”

Kallonta Hajja Nana tayi kana tace.

“Yanzu na fito daga gidan Lamiɗo ai”.

Cike da mamaki Innayi tace.

“Dama Khausar ɗin gidan Lamiɗo itace jikar ki?”.

Kai Hajja Nana ta gyaɗa tare da cewa.

“Eh itace jikata ɗin mana”.

Numfashi mai nauyi Innayi ta sauƙe tare da gyara zamanta
kana tace.

“Toh ki kwantar da hankalin ki me yayi tsanani aciki?”.

Ƙwaffa Hajja Nana tayi tare da kallon Innayi tace.

“Mun zo da batun Aurenta da ɗan Uwanta, sannan dama anan
cikin zuri’ar gidan Lamiɗo kin sansu Zuri’ar Mayune to wai akwai wani yaro
Naseeru da yake sonta”.

Gyara zama Innayi tayi tana kallonta.

ita ko Hajja Nana ta cigaba da cewa.

“To Ni duk atunanina ma idan batason Aliyu Naseeru zata ce
tana so amma wai.

 Yarinya nan tace wai
wani take so, saboda rainin hankali wai Uwar ma batasan da batun ba”.

Ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe tare da fuskantar  Hajja Nana tace.

“Toh me abin tashin hankali kinsan zamanin da dana yanzu ba ɗaya
bane, abinda aka mana muka jura na yanzu ba zasu jura ba, bama a isa ayi musu
ba, bare kuma har aje matakin su ɗauka, amma yanzu kisha ruwa ranki yayi sanyi
tukun”.

 

Numfashi Hajja Nana ta fesar kana tace.

“Wallahi baki daya a fusace nake  yarinya tayi matuƙar ɓata min rai ta fusata
min zuciya ni zata wa tsawa ƙasa a ido.

 Baffanta yayi tattaki
gari ya garara yazo amma tace bata son ɗan sa saboda bata da mutunci”.

Innayi kuwa ruwa ta miƙa mata tare da cewa.

“Ke dai kisha ruwa zuciyarki yayi sanyi”.

Karɓa tayi tare da kafawa abakinta ta fara sha

 

Acan Falon Moddibo kuwa zaune yake akan Sallaya bayan ya
idar da sallar Walha hannunsa riƙe da Alkur’ani yana karanta suratul Tauba yana
Aya ta ɗari da ashirin da bakwai yaji wayarsa na Vibrating Kallon screen ɗin
wayar yayi ganin sunan Abba yasa ya cigaba da karatun kasancewar saura Ayoyin
biyun ƙarshe yasa ya cigaba yana ƙarasawa ya shafa addu’ar dai-dai lokacin wani
sabon kiran ya sake shigowa.

 

Anutse ya ɗaga wayar tare da kaiwa Kunnensa yayi Sallama.

Cikin sanyin murya Abba ya amsa tare da cewa.

“Aliyu”.

Ahankali Moddibo yace.

“Na’am Abba ina kwana ya ƙarfin jikin naka?”.

Cikin sanyin murya Abba yace.

“Lafiya lau Alhamdulillah ya gida? Aliyu ya kwana biyu duk
ban jika ba”.

Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauƙe kana yace.

“Wlh kuwa Abba ya ƙarfin jikin naka?”.

Ahankali Abba ya sauƙe numfashi kana yace.

“Jiki da sauƙi”.

gyara zamansa yayi tare da cewa.

“Toh Abba Allah ya ƙara sauƙi amma lafiya kuwa?”.

 

“Eh lfy lau. Yanzuma nayi waya da.

Mgnar Company na dake
Marocco, to dama akwai kayan da mukayi Order sabbbin Injuna, sabida
tsoffin sun fara samun matsala kasancewar sun kwana biyu to an kawo sabbin  kuma Manager baya nan yaje duba lafiyarsa,
kuma yanzu dole ana buƙatar sai akwai sahalewar wani da kuma sa hannu na kafin
afara sauƙe kayan dole kuma akwai buƙatar tsayeyye da zai sa ido kan aikin kafa
musarrafan da za’ayi”.

Tunda Abba ya fara magana Moddibo ya lumshe idanunsa yana
cigaba da sauraron sa.

Abba ya cigaba da cewa.

“To yanemi da Inje, to ni kuma bazan iya ba, kullum ina fama
da ciwon kai kuma kaga  ga yanayin da
nake ciki har yanzu ana zuwa min gaisuwa, shiyasa nake so ka shirya ka
wakilceni, kaje ka fuskanci aikin idan yaso idan komai ya dai-dai-ta aka fara
aiki in anyi rukunin forko saika dawo ba zaka daɗe ba”.

Moddibo kuwa shiru yayi tare da jingina bayansa da jikin
Cushing.

Daga ɗaya ɓangaren Abba yace.

“Hello! Aliyu Hello!!, Hello!!! Aliyu kana jina kuwa?”.

 

Shi kuwa Moddibo cije Lip ɗinsa na ƙasa yayi Aransa yace
bana son garin Gembila baki ɗaya jihar Taraba ta fitar masa ji yake tamkar wuta
ake watsa masa aduk lokacin daya tuna shi kaɗaine ke  rayuwa babu J ɗinsa, babu wani akusa dashi
idan zai tafi masallaci shi kaɗai sannan idan zai dawo shi kaɗai kana idan
zaici abinci shi kaɗai baki ɗaya ilahirin garin ya masa duhu kana ya masa ƙunci
sam baya son zama acikinsa Nigeria kanta ta fice masa arai.

To amma kuma idan ya tafi Ummi ya zatayi.

Cikin sauri ya buɗe Idanunsa dake lumshe jin Abba na cewa.

“Aliyu ya dai kayi shiru baka ce komai ba?”.

Numfashi mai tsayi yaja kafin ya sauƙe ahankali cikin sanyin
murya yace.

“Abba Ummi idan na tafi nayi nesa da Ummi ba zata ji daɗi ba
sannan Innayina, da waye zan barta?”.

Ahankali Abba ya sauƙe Ajiyar zuciya tare da sauƙe dogon
numfashi kana yace.

“Ba komai Aliyu Insha Allah za ayi ƙoƙari akula da duk kan
al’amurran su sannan ba daɗewa zaka yiba”.

Cikin raunin murya Moddibo yace.

“Abba Ummi tace idan banje wajenta ba hankalinta na tashi
damuwarta na tsananta. Abba bana son ganin Ummi cikin wani yanayi, Innayi na
kuma bata da kowa a duniya saini in nayi nesa da ita ya zataji”.

Ajiyar zuciya Abba ya kuma sauƙe kana yace.

“Bakomai Insha Allah za muyi magana da Malam Ahmad za’a
kwantar mata da hankalin ta, sannan dama inaso zamuyi magana dakai Innayi kuma
kada ka damu zata iya dawowa gidana kafin ka dawo ko gidan Ummin”.

Ahankali Moddibo ya gyara zaman wayar akunnensa.

Yayinda Abba  kuma ya
cigaba da cewa.

“Akan kuɗin da aka har haɗa aka turo wanda Fatima ta saida
Sarƙoƙinta da kuma motarta kazo zamuyi maganar ka karɓi kuɗin Asiya mata wata
motar sannan sauran ta ajiye  idan zata
sai wasu kadarorin ma ta ajiye”.

A hankali ya gyara zamansa tare da rintse idanunsa kana ya
cigaba da cewa.

“Sannan kaima naga motar da kake Amfani da ita tsohuwar mota
ce ya kamata ka siya wata sabuwar motar ka riƙa hawa”.

Girgiza kai Moddibo yayi cikin raunin murya yace.

“Abba me zanyi da wata sabuwar mota Abba bana son Kuɗin dan
Allah kadaina maganar Abba ni dai bana son Kuɗin Abba bana son su”.

 

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da girgiza kai kana yace.

“A’a Aliyu ya za ayi kace haka?”.

Moddibo kuwa rumtse idanunsa yayi tare da taune Lip ɗinsa na
ƙasa kana yace.

“Toh Abba me zanyi da kuɗin da suka kasa ceton min J me
zanyi da kuɗin da suka kasa temakon ceto mun rayuwar J Abba bana son Kuɗin Abba
dan Allah kada kayi min maganar kuɗin”.

 

Numfashi Abba ya fesar cikin sassauta murya yace.

“Aliyu kayi haƙuri dole muyi maganar kuɗin nan kaima kace
baka son maganar kuɗin nan to ni kuma me zanyi dasu Aliyu kayi haƙuri kaji
sannan dan Allah kayi ƙoƙari ka shirya ka tafi Marocco E PASSPORT naka zaka
fitar dan Allah, mu fara neman damar fitan ko ta online zakayi komai, cikin
makon nan nakeso ka tafin in Allah yasa ka samu buse”.

 

Shiru Moddibo yayi lokaci
da yaji maganar Bashir ya dawo masa kunne na cewa yayi mafarki da M
Jameel sannan yace ya faɗa masa cewa ya taya Abba harƙan kasuwancin sa dogon
numfashi yaja mai sanyi duk da cewa baya so ya tafi ya bar Ummi da Innayi amma
ji yake ya tsani zaman cikin Taraba da Gembila baki ɗaya Jahar Jaligo ta fita
Aransa ga kuma tuno da abinda Bashir di ya faɗa ya sauƙe numfashi cikin sanyin
murya yace.

“Toh shikenan Abba bari nayi magana da Innayi da Ummi”.

Kai Abba ya gyaɗa kana yace.

“Toh shikenan idan kunyi maganar dan Allah ka kirani yanzu
yanzu ina jiranka”.

Cikin sanyin murya Moddibo yace.

“Toh shikenan ba matsala”.

Sannan ya katse kiran ya miƙe.

 

Acan ɗakin Innayi kuwa Hajja Nana na gama shan ruwan ta
ajiye Cup ɗin tana sakin ajiyar zuciya.

Ahankali Innayi tace.

“Toh kici abinci”.

Girgiza kai tayi tare da faɗin.

“A’a bazan iya cin abinci ba barni kawai”.

Kallonta Innayi tayi kana tace.

“Toh Wai me ya tsananta ne har ya tayar miki da hankali
haka?”.

Ƙwaffa Hajja Nana tayi tare da riƙe haɓa cike da takaici
tace.

“Wai fa Khausar cewa tayi bata son Aliyu wai wani take so”.

Gyara zama Innayi tayi kana tace.

“Wai wani waye shi wanda take son?”.

Cikin fushi Hajja Nana taja dogon tsaki tare da cewa.

“Wai wani wai shi Moddibo take so Malamin Makarantar su inji
Lamiɗo”.

Cikin sauri Innayi ta kalleta tare da jan dogon numfashi
kana ta lumshe Idanunta tare da buɗe su cikin sanyi ta kalli Hajja Nana kana
tace.

“Moddibo?”.

Kai Hajja Nana ta gyaɗa tare da faɗin.

“Eh Moddibo?”.

Jinjina kai Innayi tayi kana tace.

“Kuma wai malamin su?”.

Still Kai Hajja Nana ta gyaɗa mata.

 

Dai-dai lokacin Moddibo ya isa bakin barandar ɗakin
Innayi  yana son ya mata bayanin Abba ya
kira sa akan yaje yasa yazo wurinta, yana taka step ɗin firko ne.

Ya jiyo sautin Muryan Innayi na cewa.

“Toh Moddibo ai jika nane Hajja Nana.”

Sai kuma tayi murmushi mai cike da jin dadi kana taci gaba
da cewa.

“kinga shikenan faɗuwa tazo dai-dai da zama Aliyu jikana
aishine Moddibon kinga sai muyi tuwonmu manmu”.

Cikin sauri Hajja Nana ta miƙe tare da kallon Innayi kana ta
zare ido sannan ta buga hannunta aƙirji tare da cewa.

“Ji kanki?”.

Jinjina kai Innayi tayi tare da faɗin.

“Eh jikana ne Aliyu”.

Still Hajja Nana na tsaye cikin zare ido tace.

“Shine Moddibo kenan?”.

Kai Innayi ta gyaɗa mata cikin tabbatarwa.

Ita kuwa Hajja Nana cikin wani yanayi tace.

“Sannan kuma shine Malamin nasu?”.

Kai Innayi ta kuna gyaɗa mata kana cikin sanyi tace.

“Tabbas shine jikana Moddibo”.

Cike da mamaki Hajja Nana tace.

“Kenan jikanki ne Moddibo wanda Khausar ke so?”.

Still Kai Innayi ta gyaɗaa karo na barkatai tare da cewa.

“Eh”.

Cikin wani irin masiyacin kallo Hajja Nana ta kalleta tare
da cewa.

“Aikuwa baza ta saɓu ba bindiga aruwa, ai wannan ma ta
tsuniyace mara wanzuwa ai wannan ma zancen banza ne, wannan ƙarya ne wlh.
Khausar bata isa ba mu zata lalatawa tushe da asalin zuri’a”.

Cikin sauri Innayi ta mike tare da zare ido ta kalli Hajja
Nana cike da mmki tace.

“Wannan wace irin kalma kike faɗa?”.

Gyara tsayuwa Hajja Nana tayi kana tace.

“Toh Innare waye bai san cewa jikanki bashi da asali ba,
wani mahaukacin ne zai ɗauki ƴa ya baku? waye zai so haɗa zuri’a da jikan ki da
bashi da asali! ɗan shege da kika samu akwararo ɗan da ba’asan tushe da
Asalinsa ba!!!”.

Cike da matsanancin mamaki Innayi ke kallonta Hajja Nana ta
cigaba da cewa.

“Ɗan da ba asan tabbacinsa ba asan asalinsa ba. Yaron da ake
da tabbacin cewa ba ɗan sunna bane ɗan zina ne. Shine za ahaɗa zuri’a ta
dashi  ai wallahi wannan ba zata yuba”.

Ta ƙarashe mgnar cikin yanayinta na ba shina ba sabo.

Cikin fushi da ɓacin rai Innayi ta watsa mata wani irin
kallo tare da cewa.

“Ke dakata Hajja Nana ki kama kanki”.

Dogon tsaki Hajja Nana taja tare da cewa.

“Bazan kama ba, tabbas abinda na faɗa gaskiya ne, idan har
yana da uba to waye Ubansa tun da kuka zauna tsawon rayuwarku shekaru talatin
da  acikin Garin Gembila waya san
Asalinsa wayasan Ubansa wayasan tushensa na faɗa na ƙara fada da ƙarfi shi ɗan
shege ne ke kuma magajiya”.

Moddibo dake baranda atsaye ne, yayi wani irin jan numfashi
tare da rumtse idanunsa domin tamkar sauƙan aradu haka maganganunta suka ratsa
ƙwaƙwalwarsa zuwa dodon kunnensa.

Hajja Nana kuwa cikin fushi da ɓacin rai tace.

“Shegene jikan naki na faɗa zan kuma faɗa”.

Wani irin kallo Innayi ke binta dashi zuciyarta na wani irin
tafarfasa ta kalli Hajja Nana kana tace.

“Tabbas babu wanda yasan asalin Jikana sannan babu wanda
yasan ina ne tushen jikana amma ke dai baki isa ki jefe mu da mugayen kalamai
irin wannan ba”.

Taɓe baki Hajja Nana tayi tare da watsa mata Harara kana
tace.

“Na nawa kuma ance da kuturu Allah ya la’ance ka, jikan ki
dan kwararo ne ɗa mara tushe da galihu”.

Cikin tsanananin tashin hankali da ruɗu da wani irin
tsinkewar zuciya mai tafiya da nunfashi Moddibo ya dafe kansa da hannu bibbiyu
tare da rintse idanunsa…!

 

 

Littafin SAKAYYAH dai na kuɗi Hajia ba free book bane dan
haka ki saya ki karanta cikin Aminci da salama 1k ne kacal kuɗin samun damar
karantawa 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar

biyanki ta WHATSAPP 09097853276

Leave a Reply

Back to top button