Hausa NovelsHausa NovelsTabarmar Kashi Book 2

Tabarmar Kashi Book 2 Page 35

Sponsored Links

TABARMAR KASHI

Book 02 Page 35

Shuru sãahar tayi tana gyada kai, idanunta dauke da qwalla,tausayin masu ciwon yana ratsata

“Surgery shine best hanya nake tunani da fadeela zata rabu da ciwonta,saboda kamar nata ciwon hakan ya nuna a yadda naji daga bakin nadeeya,hajiya qarama ta gara iza wutar ba za’a tabata ba,ba za’a yi mata aiki ba….yanzu kuwa lokaci yayi,ko tanaso ko bataso” sãahar ta fada with confidence.

“Bestie,please nan da sati daya ki bincika min best asibiti a kowacce qasa yake da zasu iya yiwa fadeela aiki, zanji da komai,ko sajjad banaso ya sani sai an gama” kai afifa ta mirgina

“Anya bestie?,bakya gudun faruwar komai?” Kai ta girgiza

“‘Na yarda da Allah, kuma nayi imanin bazai tozarta ni ba,kyakkyawar niyya sa tsarkin zuciya shine a gaba da komai” ta qarasa fada tana daukar wayarta, ta bude calendar na period dinta don ta duba kwana nawa ya rage, saboda ciwo da taji mararta tana mata kadan kadan. Qatoton circle ta gani tare da manyan rubutun
OVULATION DAY,sai ta sauke wayar tana dan yatsina fuska

“‘Kina experiencing wani pain ne?” Kunyar afifa kadan tadan kamata,saita kau da kai tana girgizawa
“Na sha magani” murmushi afifan tayi, qasan ranta tana jin dadi da hakan ta faru, tana kuma sake ganin kima da martabar toufeeg, don wanna abun da yayi a wajenta ya tabbatar mata yasan abinda yakeyi,kuma shi ba shashasha bane,hakanan ya tabbatar mata cikakken namili ne da tunaninsa ya saba da na diya mace.

********Kamar ko yaushe,qarfe takwas saura minti biyar ta kammala shirinta,har ta fiddo mayafi zata yafa ta tuna da hijaban da ya aiko nadeeya ta kawo mata guda goma sha biyar a jiya. Tun ranar da su afifa suka tafi tunda ta rakasu bata koma sashen nata ba,tayi zamanta a sassansu,kwanaki biyu yau kenan ko fuskarta bata sake bari ya gani ba,ko hijaban ma sai nadeeya taga ta shigo mata dasu

“‘Inji yaa moha, ki fara using nasu on Monday” tayi maganar tana hadiye dariya. Da kallo ta bita,nadeeya da afifa sun hade kai,sai suyita mata magana suna boye dariya,sun maidata kamar wata ‘yar tsanar wasansu,amma taci alwashi itama duk ranar data kamasu ba zasuji da dadi ba.

Qaramin tsaki ta ja, batasan meye nufinsa da yin hakan ba,zama tayi ta zazzagesu,ta kuma cire color din da zai shiga da atamfar jikinta,ta qarasa gaban madubi ta saka tana daure igiyar kai data hannun hijabin. Lokacin fadeela ta shigo wadda ta barta ne tana qarasa yin breakfast a dining.

“Anty na gama”

“That’s good girl,oya let’s go” ta fada tana goya school bag din fadeelan a bayanta kamar yadda suka saba.

Tun daga nesa taga parking space din da yake cin motocin nasa wayam ba kowa, ba kamar yadda suka saba ba,a safiya irin wannan gurin zaka sameshi jere da motocinsa da kuma su jibril suna tsaye suna jiran garasowarsu. Yau din shi daya ta hanga,tsaye jikin BMW dinsa fara sol, wadda a wancan satin ta iso,sai daukan idanu takeyi tana tabbatarwa da me kallonta tsadar da take da ita.

Yau din sassaugar shiga ce, amma yadda kayan suka karbeshi sun maidashi wani so hot,ya koma balarabe sosai amma mara yawaitar haske sosai, cikin taupe color button up shirt yake da slim fit trouser medium gray, gafarsa wani tsadadden sneakers ne da ya kwanta sosai a lafiyayyar qafarsa da take qal kamar baya taka qasa. Wayarsa na hannunsa yana dannawa,tamkar hajiya qarama dake tsaye gabansa tana fuskantarsa ita da haseena baya jin abinda ma suke fadi,yayin da haseenan dake rungume da hannayenta ta zuba mishi idanu,sirrin tasirin kyan dake fita tattare da kamilar fuskarsa me yawan kwarjini suna sanyata jin kamar ta rungumeshi a yanxu haka,tana jin kamar ta bude idanu ta ganta ta zama mallakinsa matarsa, kishinsa na sake hauhawa cikin zuciyarta, tana ji a ranta zata iya vin komai zata iya rasa komai muddin shima ta rasashi, ciki kuwa harda rai da rayuwarta.

Kai säahar ke gogarin daukewa bayan idanunta sun gama qarewa kowa kallo a cikinsu,wani abu taji na neman tsaya mata a wuya,tsaiwar meenal tayi mugun yin kusa da toufeeq din, ta tabbatar da zaiyi wani wawan motsin tsaf zai iya taba jikinta, qoqarin gayawa kanta takeyi

“Ba huruminki bane,meye naki?” Amma ga mamakinta zuciyar taqi karba,kai ta sake kawarwa tana fadin
“Wataqila tana tuna cewa dukkansu musulmai ne masu amfani da yaren hausa, bai kamata kuma a samu hakan daga garesu ba”

Kamar wanda aka yiwa wahayi da tahowarta,ya cira kansa a hankali idanunsa suka sauka a kanta

“Ya salam,ya Allah” ya furta a fili qasa qasa. Idanu ya kafeta da shi yanason banbamce shigar mayafin data hijabin

“Ba abinda ya buya” wata zuciyar ta gaya masa,wannan kyan yana nan a muhallinsa d gurbinsa,cikakkiyar halittar da a yanzu yasan ainihin cikarta da zatinta sai yake ganin tamkar kiwa na iya ganinta ta cikin hijabin nata,boobs din da yake qoqarin ganin sun buya sai idanunsa ke nuna masa su muraran,wani abu ne nauyi yaji ya sauka aqirjinsa ya sauke hannunsa yana yarfar dashi sannan ya ratsa ta tsakanin hajiya qaraman da meenal ya nufesu.

A hanya sukayi kacibus, kowa idanunsa cikin na dan uwansa,fadeela ta wuce gaba abinta ta tafi gaida hajiya qarama,wadda a yanzu sai zata fita school suke haduwa,sabanin lokutan baya da duk safiya sai an kai mata ita kafin ta wuce makarantar.

“Babu ta yadda za’a iya boyesu ne?” Yayi mata tambayar yana riqe qwayar idanunta cikin nasa,wanda taketa shirin gocewa hakan. Cikin rashin fahimta da dan hadewar fuska tace

“Me?” Idanunsa ya sauke akan qirjinta, da sauri takai dubanta kai,sai tasa hannu tana daga hijabinta ta saitin gurin hadi da ja baya tana kuma sake hade rai

“Ummmm?” Ya sake fada da sigar tambaya.

“Bana so” ta fadi cikin jin haushi,taku biyu yayi gabanta yana qare hade tsakaninsu

“Nine dai bana so, banason kowa ya kallesu Allah zan iya hadiye zuciyata, they’re mine” A mamakance ta kalleshi tana zare ido, tanason tace wani abu ma ta kasa, bai kuma bata dama ba,sai ya sake matsawa gabanta,a hankali yasa hannunsa ya jawo hijabin saman habarta wai ko hakan zai rage mannuwarsa a jikinta yana sake kallon girjin nata

“Damn it!” Ya fada gasa gasa,sai ya zura hannu ya karba lunch bag din fadeela,ya sake saka hannu ya zare school bag din nata sannan ya juya ya fara tafiya. Juyowarsa ta sanya hajiya qarama dauke kai daga kallonsu wani abu yana bugun zuciyarta was canje canje take gani a tsakaninsu wanda batasan meye silar afkuwar sa ba.

Meenal kuwa kuka takeson saki hajiyan na mata nuni da kada ta sake tayu,haka ta dinga hadiyeshi tana ji kamar tana hadiyar zuciyarta,zuciyar tata kamar zata fashe.

“Barka da safiya” sahar tace da hajiya qarama,sai da tayi namijin qoqarin dai daita kanta sannan ta jefa mata wani kallo

“Barkanki dai,ya ayyuka?” Yadda ta kira ayyukan ya yiwa säahar kama da gatse, sai tayi kamar bata jita ba, tayi gaba dai dai lokacin da ya bude mata seat din gaba. Sai data kalleshi cikin mamaki ya dage mata dukka girarsa biyun,bata ce komai ba ta shige ya tattara mata hijabinta ya rufe mata motar.

“If you are not ready to go ki koma ciki” yace d meenal da takaici va sanyata tsaiwa a gurin, tabota hajiya qarama tayi sai ta taka ta bude murfin motar ta shige. Sahar na kallonta ta cikin madubi, haka kawai yau din taji kanta ya fashe, gyara zamanta tayi tana kauda kanta gefe.

“Set your belt” ya furta a nutse yana gyara zamansa.
Kasa jira yayi ya miqa hannunsa da nufin jawo belt din ya daura mata,wanann ya bawa hannnun nasa damar shafar qirjinta. Daga shi har ita ba wanda jikinsa bai amsa ba,haushi ya kamata,tana tsammanin zai janye,sai taji ya garasa kwantar da fin rabin jikinsa a kanta. Da sauri ta daga kanta ga hajiya qarama dake tsaye saitin window din nasu,idanunta fes a kansu tana gain komai,ta dauke kan nata da sauri ta maida gareshi, tanason magana ma amma ya matseta sosai jikin seat din, yanata kokawar sanya belt din amma har yanzu baikai ga sakawa ba.

Bugun zuciyarta ya fara qaruwa saboda gaba daya kusan a fakaice rungumeta yayi, saita sanya hannunta tana son tureshi, saidai kafin takai ga aikata hakan ya saka belt din da wani irin hanzari,ya kuma kama dukka hannuwan nata ya rige cikin nasa va sauke mata tattausan kiss saman lips dinta abinda ya sanya hajiya garama rufe idanunta da sauri ba tare data shirya ba

“Kwana biyu,kwana biyu ko?”‘ Ya fada qasa qasa, tasan me yakeson fadi ,yanason sakayawa ne saboda meenal dake cikin motar. Da sauri sukaji an bude murfin motar kuma a wani irin fusace,bata iya tsaiwa ba ta kwasa tayi cikin gidan da mugun gudu, abinda ya yanke tsaiwar hajiya qarama a gurin,tabi bayan meenal din cikin sassarfa.

Tashi yayi ya koma mazaunin driver yana sakin murmushi
“Ko kishin kanki baki dashi? a gaban idonki na bawa wata lift?” Ya fada with softness yana shirin kunna motar
“Kishi? god forbid” kadan ya waiwaya ya kalleta, kaman zaiyi magana sai ya fasa murmushi ya sake kubce masa
“Alright,zamu gani, amma dai yanzun ai na taimakeki da korar miki ita,ko banza kya shaqi numfashi me kyau” kasa amsa masa tayi saboda gaba daya ya yamutsa ta a fakaice,kuma batason taci gaba da amsa masa fadeela ta fahimci wani abun. Kawai dai abu daya ya bata mamaki driving da yakeyi yau da kansa abinda bata taba gani ba, sai daya fita sauran motocin suka taso suka rufa musu baya,biyun kuma sukayi gaban tasu.
A yau din bayan sun isa company,su biyu kadai suka wuce zuwa ciki. Dukka ma’aikatan kowa goqarin gaidashi yakeyi cikin girmamawa,abinda yadan basu mamaki shine yadda yake amsa gaisuwar tasu a yau kadan kadan, musamman ma’aikata mazan. Hatta cikin elevator su kadai ta dauka har zuwa building dinsu. Baya yaja yana kallonta,fa fahimci abinda yake nufi tayi gaba kenan, dauke kai tayi gami da noqewa kamar bata fahimci abinda yake nufi ba. A nutse ya tako ya garaso kusa da ita,ya sanya hannunsa ya rigo nata hannun yana hade tafukan hannayensu guri daya. Cikin sauri ta daga kanta ta kalleshi,ta kuma fara yunqurin zare hannunta daga nashi. Jifanta yayi da wani irin kallo sannan ya girgiza mata kansa alamun a’ah,bai sake saurararta ba ya jata a tausashe suka fita daga elevator din.
Kusan duk inda suka gifta sai idanun jama’a sun bisu da kallo,wani irin mugun matching sukayi a safiyar tare da wani sassanyan kyau dake cakude da annuri saman fuskar kowannensu. Wanna kallon da ya lura ana binsu da shi ya sake jagula masa lissafi,sau uku yana canza mata side,from left to right, from right to left.
Cikin kamalarsa yayi sallama cikin lobby na office din nasa, mazaunin saima kenan. Da kuxarinta ta dago tana amsawa, harda gyara zamanta, saidai kuma kafin takai ga garasa amsa sallamar komai ya magale mata a wuya,da qyar ta tattaro kalmomin
“Good morning sir”
“Morning” ya amsa mata yana wucewa kai tsaye ga office dinsa,har a lokacin kuma bai sake mata hannu ba “Sir,kowa kai yake jira,dukka suna hall din” saima tayi qarfin halin fada tana jin wani abu me daci saman harshenita. Sai a wanna karon ya waiwayo,kallo yayi mata irin wanda ya saba yiwa kowa, amma sai taji wani dadi a ranta,saboda takan jima bata samu wannan damar ba
“Monday ne dama?” Ya tambayeta cikin kokwanto. Sai data hado wani murmushi saman fuskarta sannan ta gyada masa kai tana lumshe idanu
“Yes sir” tana gama fada jibril yayi knocking ya nemi izini sannan ya shigo
“Sir, kowa yana jiranka”
“Okay” ya amsa yana gyada kai

[28/09, 9:21 am] +234 903 576 5837: “HUGUMA*

 

Leave a Reply

Back to top button