Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 37

Sponsored Links

 

 

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/16, 7:57 AM] +234 803 800 7509: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

3️⃣7️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

  Zaune yake gidin
iccen mangoron dake kofan gidan a zahiri zaka dauka dabbobin dake killace a
wuri daya yake kallo a lokacin don fuskanshi dake kallon dabbobin dake kiwo.

   Saidai a can kasan
zuciyar shi tunanen halin da rayuwan shi ke ciki yakeyi idan bayi karya ba yau
kwanan shi biyar ke nan a garin tsohon wanda kuma a kullun ana dan cigiyartawa
koda Allah zaisa a samu wanda yasan waye mahaifin nasa a kasan.

   Saidai sunyi abune
a dunkule don basu sanar a zamanance ba ko su cigiyarta ta hanyar daya dace
subi na zamani koda ace sukai cigiya wurin uban kasan da haka zai iya taimaka
masu har su kawo ga mutumin da suke nema din.

    Bakon malam musa
kana jin dadin zama kai kadai baka sha,awan zuwa majalissane kayi hira ko baka
da sha,awan hakane muyi sabo dakai sai zama kai kadai.

   Murmushi yaiwa
saurin dake kaiwa zaune gefen shi saman dan iccen dashi Ahmed din yake zaune a
kai yace ko naje majalissan ku ban san komai da zakuyi magana a kai ba yanzu
zamana a nan ni kadai shine alherina don banji bangani daga abin ki.

    Kumafa kayi
gaskiya don zaman majjalissa bai bar yaro ba baibar tsoho ba balle matar aure
ko makaho duk wanda ya gitta sai an aza mashi ayyah a kai kafin yakai inda zai
tafi din.

   Kaga ke nan kana
muna wayau daka kebe nan kai kadai kana nazarin ka duk da dai wani lokacin zama
a cikin mutanen yana da dadi don mutum na samun abin karuwa sosai.

    Dan bayaro kaine a
nan kuma yau tare da bakon malam musa wani farin saurayi mai zubin fulanin
asali ya fada yana karasaowa wurin su.

   Shima wuri ya samu
ya zauna suna gaisawa kafin yace wai bako kai mutumin inane naji hausan ka
daban da namu sosai yana kallon idon Ahmed din dake kallon su.

   Ni mutumin
zamfarane wajajen sokoto hodi jam kace ka fito danisa kai bako aradu niko kano
ban taba sani ba balle wanan garin sokoto ina dai jin sunan garin sosai a redio
da waya kuma.

   Ashe Malam musa ba
kusa ya fito ba dama harda yan uwa a wanan garin mai nisa haka gaskiya kayi
tafiya sosai kafin kazo nan na farkon ya fada.

   Tafiyan kwana biyu
da wuni ya kawoni nan garin ku kaga kuwa ai ba wani nisa mai yawa ga tafiyan ke
nan Ahmed din ya fada cikkn zolaya don koshi da yayi tafiyan duk da tafiyan
tana da muhinmanci a gareshi saida yayi nadaman yin hakan a zuciyarshi.

  Musanman yadda ya
baro gida bai sanarwa kowa inda ya dosa ba wanda yasan hakan ba karamin tayarwa
Dije da hankali hakan zaiyi ba.

   Amma shi hakan ya
kama dole gareshi sai yayi wanan tafiyan don ya tserar da kanshi daga samun
mutuncin shi da asali da aka fara kira mashi baida shi.

   Idan ya tsaya daka
ta Dije da yan uwa ba zai taba samun hakan ba don sun tsaya akan dole shi
mahaifin nasane zai kawo kanshi garesu idan har ya damu da danshi.

   Alhalin gaba dayan
su kaf sun janye sun saka masu ido a yanzu ba wani wanda ke daukan kwandalanshi
ya taimaka masu dashi duk da sunsan suna bukatan taimako a lokacin.

  Kowa yaja diyanshi a
jiki sun waresu a gefe suna nasu lamari a tsakaninsu bayan shi malam ladan a
baya lokacin da yake raye ya taimakawa yan uwa da abinda yake dan samu a
aljihunshi lokacin.

   Yanzun ko kasa ya
rufe ido tun mutuwanshi suka sakasu a gaba da wani surfan cewa ai gonan malam
ladan din akwai kudin mshaifiyarsu ciki data kwashi adashe lokacin ta kara mai
ya sayi gonan dashi.

  Dole aka saka gonan
cikin na gadon su suka dawo kuma sukace ai sun tuna cewa gidan nan ma dasu Dije
din da jikanta suke ciki yanzu da kudin tsohuwan su aka sayi filin har yai
ginan.

   Wanan ne hukuma
basu yarda da dashi ba kuma don angane suna son su wullakanta ahalin mamacinne
kawai a duniya suke wanan kirkire kirkiren a yanzu din.

  Tun wanan case din
suka dauki tsangwama suka sakawa Dije da ahalinta haka yasa karshe danta namiji
daya tilo ya bar garin yai kaura ya koma garin ibadan da zama.

   Saidai kuma ko can
din ma ba wani sana,an kirki yakeyi ba ana dai zaune hakanane sunan ba a garin
ana wurin neman kudi don bai iya yiwa kanshi maganin dubu goma balle wanin shi.

    Haka yasa yakan
dade bai leko gida ba don koda yazo din ma karshe idan zai koma   na mota ma wuya yake masa yasa yanzuma ya
daina zuwa ga baki daya garin.

    Su kuma diya matan
na dije ita mahaifiyar Ahmed din tayi aure tabi mijinta kasan Niger state inda
yake noma har zaman ya mayar dasu can na dindindin a yanzu sai can ba a rasa ba
ta kan dan lekosu nan zamfara din.

   Haka ita kuma
kanwarta a wani kauyen zamfara ne da ake kira silami take aure itama ba wani
halin da zata iya tallafawa wanin ta don mijinta tallakane tilis.

    Wanan yasa suke
zaune tsiya tsiya ita da dan jikanta a cikin rubaben gidan su da malam ladan ya
mutu ya barsu a cikinshi.

   Saidai  saboda gidan don rashin samun gyaran da baiyi
lokaci lokaci saidai dan facin da Amadin ke yawan yiwa gidan tun yana karami
har tasowa yanzu din daya girma don hali bai kai ba yasa suke zaune a cikinsa.

   Ko karatun boko da
yayi Allah dai ya nufa sai yayi da taimakon Allah dana jama,a ya samu yakai
secondary nan ma da kyar ya samu Allah ya rufa mai asiri gwanati na biyan kudi
haka ma daya dauko karatun zuwa jami,a.

  Yasha korafi da ayi
mugani na yan uwan kakan shi dana Dije din kowa ya dare ya zuba mai idanu shine
ya hadu da madam na neman dan aiki yace zai iya da wanan taimakon ya samu har
ya hada karatun shi na jami,a yanzu.

    Wai amma dai kai
bako dama kasan ta kan shanuwa sosai ko dan naji iyayyen mu na maganan cewa duk
yadda akayi kai din ka fito daga gidan manyan fulanine da suka san kansu da
kuma sanin dabarun kiwo.

   A,a haaa nikan ai
baffa shewa yayi yaron manya ne da ganinshi wata kila wani dangantaka ne ya
hadashi da malam musa har yazo nan ya zauna dashi ?

    Dan uwan
mahaifiyanane shi amsan da Ahmed yabawa samarin biyu ke nan da yake ganin sunzo
don bugun cikin shine su san wani abu a game dashi dama.

    Haka kan don
gaskiya baka da kama dashi don naji suna fadin dakai dan kasan nan ne sai suce
kai jinin wurichedine don sune dabi,unsu yake irin naka sak naji baffana ya
fada.

   Gaban Ahmed ne ya
fadi don jin abinda dan bayaron ya fada amma saiya dake bai nuna komai a fuska
ba sun dauki lokaci a tare dashi da suka fito sallah la,asarne suka rabu kowa
ya kama gaban shi daga can din.

    Mamaki nayi kwarai
lokacin da hjy karima ta kira layin wana tana sheda min cewa na fito na tari
mutanen garin mu gasu nan sunzo daga zamfara din mu.

    Har na gama
kimtsawa na fita zuwa inda suke ban gama mamajin hakan ba wanda ba wani abu
nakewa mamaki ba sai yadda akayi wasu yan zamfara zasuzowa hjy karima buki
tundaga can.

   Don naga ai buki
idan bana mama ba basu zakewa haka har su kwaso jiki su zo idan buki ya sami
ummah katsina koda sunce zasuzo karshe bamu ganin kowa har muje mu dawo saidai
suba da excuse din karya suce shine ya hanasu zuwa.

   Daga karshe kuma
muka gane saboda mamace don kada suyi laifi a wurinta dan abinda suke samu a
daina basu yasa basu zuwa wani sha,ani na ummah din.

   Sallama nayi nasa
kai dakin dasu na fara arba suna zaune a kasa sun baje sai abinci sukeci gashi
an loda masu abincin a gabansu sai kwasa sukeyi kamar masu yunwa a ciki.

  Sai hakan ya bani
kunya amma haka na daure na karaso ina fara,a a fuskana ina fadin gwaggo ashe
kuna hanya sannuku da zuwa.

   Suka juyo tare da
fara,a suna fadin a,a maamahce an zama mutanen kano ashe kina nan tare da maman
ku amarya ?

  Eh daga Abuja danaje
hutu mukazo nan din tare dasu au ashe dama kina can wajensu Abujane nace eh
tunda akai hutu nake can ai ya hanya ya mutanen gida nayi saurin kawar da
zancen a lokacin.

  Kowa lafiya kalau
ummah kima jiya muna tare gidan ya
mamman nake fada mata zancen zuwan mu saidai lokacin ba a gama tsayar da
maganan ba don na daukama da wata cikin su zamuzo ashe ba wanda zaizo a
cikinsu.

   Aiko za a zo ita
kan hjy salma dake da yara kanana bata samun zuwa don makaranta gwaggo Ai ta
fada tana kai loman abinci a bakinta.

    Hakane gaskiya
yanzu ita bata faye zuwa wuri ba don yaranta ita dai yar mulkin daine kuma
kunsan bata zuwa koda alama .

    Mommy ce ta fito
take fadin yauwa Zahra kin fito nace kizo gasu gwaggon ku sun iso ku gaisa dasu
dan dariyan yake na sake a fuskana nace.

    Wallafa ashe suma
suna hanya ga tafiyan da dan nisa sai naji gwaggo shafa tace ai ma tafiyan
kamar girshi yazo muna don masu son zuwa suna da yawa motar da yaya ya bayar
kuma iyakan mu zata dauka.

   Ke nan ma ashe da
babban mota Abba ya basu dasunfi nan yawa ke nan da basuzo su biyar ba sai
ashirin tunda wurin kwadaine don suna ganin wurin samune nan.

    Duk a zuciyana
nake wanan zancen ni kadai dan dama ance diya mace tasan zafin uwarta fiye da
da namiji wani lokaci don haka ke nan ina jin zafin yadda dangin Abba kewa
mahaifiyar mu nima.

   Badon komai ba sai
don kawai suna ganin cewa ita ummah bazata iya masu wani hanya har su samu
komai daga mijinsu ba ma,ana dan uwansu.

    Ina nan dai zaune
dasu a dakin idan suna son wani abu zan tashi naje na dauko masu duk da mimmy
ta kama kanta tana can tana sha,anin bukinta su kuma suna zaune kamar wasu yan
kauye dole na koma saini ke kula dasu a lokacin.

   Ina nan zaune wurin
su duk da hankalina yana kan waya amma ina sauraren hiran da sukeyi jefi jefi
wanda gulman mama sukeyi kan cewa wai mama ta nuna bakin ciki da zuwan su a
fili.

  Naji gwaggo shafa
tace ai ba zamubi ta nata bamu don dan dan uwanmu mukazo ai ba don wani abu ba
shi ya nuna yana son azo ayiwa matarshi kara a nan.

    Duk ina jinsu suna
dan hiransu jefi jefi kawata maryam dana samu a nan yar yar mommy da muke kwana
dakin tsohuwar a tarece ta biyoni.

   Kwance ta sameni a
daidai kan gwaggo shafa saidaini ina saman digon kujera a kwance da wayata a
hannuna ina duba.

  Take fadin au nan
kike kinga yan garin ku yau kin manta damu ki tashi muje mu shirya za a tafi
wurin kauyawa da andawo  za a fara shirin
dinner kuma .

   Kafin nayi magana
gwaggo Ai tace keko taga uwayenta ai dole ta dawo wurin mu ta zaunamana wa take
dashi nan wanda yafimu ai zamanta yayi rana garemu nan tunda ita karima bamu
ganta ba tun dazun .

   Suna can sun tafi
gidan da za akai amaryan ne amma zasu dawo yanzu ai tunda zasu wurin wasan suma
maryam ta fada.

  Mikewa nayi na fara
fita bayan nacewasu gwaggo su shirya muje can mu hadu da mommy din a wurin
sukaji dadin hakan suma nan na barsu sun fara shiri.

   Wanka na fara shiga
nayi na fito na samu maryam tana shiri take fadin wai wanan ne za a saka a
wurin ni sam bai mun ba wallahi.

   Ai kinsan anko ba
sai ra,ayinka ba abune na kowa don haka ko bai maka ba saikayi hakkuri ka saka
a jikinka kawai hakane ta fada balle kinsan duk wanan kayan ai mommy kice ta
zabosu can Abuja .

  Kinsan ita tanada
wani ra,ayi na daban dake hadasu da yan uwa halan ku baku gama sanin halinta
bane a gidan ku ?

   Don itafa mama
karima idan ta zauna a wuri dolene a bita ko kuma ta hada mutanen fada ko tasa
dole ku tsani juna a tsakanin ku .

   Bari kawai basai na
fada maku halinta ba kuda kanku zaku sani nan gaba don duk wanda yayi kokarin
nuna cewa ya fita nan take zata tsaneshi.

  A yanzu duk amfani
takeyi daku hakan dole tana da wani manufa akan ku da takeson ta aiwatar nan
gaba don haka take kwanta maku a yanzu.

   Shigowan dayan
kawarmu dakin yasa tayi shiru ga abinda take fadi din a lokacin don kada wanan
din taji me muke fadi a lokacin.

  Niko da tasan
halinda zancen ta ya sakani a lokacin da bata fada min wanan zancen ba gaskiya
don gaba daya hjy karima ta fice min a rayuwana harma na koma tsoronta ko a
lokacin.

   Haka muka shirya da
kyar na samu motan daya daukemu tare dasu gwaggo zuwa inda ake kauyawa din har
mukaje muka dawo nice ke fama dasu lokacin.

   Sai dare mommy ta
dawo lokacin har an fara shiri wai zuwa wajen dinner da za,ayi a ranan saidai
banda niyar hakan don na fadawa su maryam cewa ba zanje bani saboda dare .

   Don haka tunda naga
su gwaggo sunci abinci sun kwanta a inda muka gyara masu nida maryam na dawo na
kwanta abina a dakin tsohuwar nan.

   Bayan mommy ta
dawone ta samu sun kwanta take fada don me zasu kwanta a falon ni ina ina dana
barsu a nan kwance gwaggo shaface tace aiko tayi kokarinta damu.

  Don ko nan din ma
itace ta gyara muna muka kwanta to ai sai ku tashi muje wurin dinner ta fada da
sunso suki amma kuma suka shirya suka tafi.

   Basu dawo ba sai
karfe daya da wani abu na dare kowa ya samu wuri ya kwanta maryam ma bansan
dawowanta gidan ba lokacin don na dade da tin barci ko ni.

Leave a Reply

Back to top button