SOYYAYYA

YAUDARA IRI UKU DA MAZA SUKE YIWA MATA DA KUMA IRI SALON MUGUN TAR SU DA SUKE YI…..

Sponsored Links

  YAUDARA IRI UKU DA MAZA SUKE YIWA MATA DA KUMA IRI SALON MUGUN TAR SU DA SUKE YI…..


Duk wata mace a rayuwa matukar ta kai munzalin girma Kyakkyawa ce ko akasi ba ta rasa masoyi wanda zai ce yana sonta, musamman a lokacin girma kamar 16-17-18- 20 22, kuma a wannan lokacin ya’ya mata sunfi farin jini, shiyasa duk wata mace da ta tsaya ruwan ido ba tayi zaɓi ba a wancan lokacin takan yi nadama.

shawara ga kowacce mace ta yarda da kaddarar ta ta zaɓi mutumin kirki ta cire son abin duniya matukar akwai sana’a da halayya nagari mai son Adini da sallah
lokaci biyar.

Mace musamman budurwa kar ta yarda ta yi soyayya da wanda bai nemi iznin iyayen ta ba, ko wai hira sai dai su tafi wani wuri ko sai a makaranta da dai sauran su.

1: Wani namiji zai ce yana son mace ne saboda kawai tana burge sa, shi ba yi ma da burin aure yanzu sai dai kawai ayi ta soyayya a bata wa juna lokaci, wannan
irin soyayyar kada ki yarda da shi ki kame kanki ki fuskanci karatun ki in kina wata sana’a shima ki fuskanta domin irin wannan soyayyar sau da dama mazan ba sa gayawa mata gaskiya ke ga ki kina ta
zaton zai aure ki amma shi kawai yana tare da ke ne don ebe kewa waya chatting dss, amma koda ba zai kaiki ga sabon ALLAH ba.

2: Wanda kawai shi don gidan ku akwai dukiya ko sarauta don ace yana soyayya dake abin alfahari ne ko don kwadayin irin kina kashe masa kudi da dai sauransu, amma ba don auren ki ba.

3: Shine mafi munin yaudara wanda zai nuna miki matukar so da salo iri iri amma shi daman kawai burin sa sha’awa kike ba shi, ya yaudare ki ya ta’ka ki wato yayi zina dake, irin su sukan kasance mayaudara
masu salo salo, shiyasa duk wani namiji musamman ke

BUDURWA da ya fara kawo miki maganar banza ki fita daga harkar sa na har abada, duk irin soyayyar da kike masa duk tsanani da za ki shiga mai sauki ne akan wanda za ki shiga in kika saɓawa ALLAH da shi, rabuwa dai daman dole ku rabu shi irin wannan
namijin daman ba auren ki bane a gaban sa, kuma wulakanci da tozarci ne zai biyo bayan yarda da shi.

Leave a Reply

Back to top button