Limaman da za su jagoranci Sallar Taraweeh da Tahajjud a Masallacin Harami a bana .
Hukumomin Saudiyya sun fitar da jerin sunayen limaman da za su jagoranci sallolin Tarawi da Tuhajjud a Masallacin Harami da ke birnin Makka a lokacin azumin bana.
Shafin intanet na Haramain Sharifain ya bayyana cewa limamai shida ne za su jagoranci gudanar da sallolin a bana.
Ana sa ran za a fara Azumin wannan shekarar a cikin wanan watan Afirilu nan.
Har wa yau, hukumomin Saudiyya sun ce bana babu wasu limamai da za a gayyato domin limancin sallolin, kamar yadda ake gani a shekarun da suka wuce.
Babban limamin masallacin Ka’abah Sheikh Abdul Rahman al-Sudais na daga cikin limaman da hukumomin suka ce za su yi jagorancin sallolin.
Ga hotunan limaman da za su ja ragamar
Sallolin Tarawi da Tuhajjud 2021
1- Sheikh Abdullah Awad Al Juhany
2- Sheikh Abdul Rehman Al Sudais
3- Sheikh Maher Al Muaiqly
4- Sheikh Saud Al Shuraim
5- Sheikh Yasir Al Dossary
6- Sheikh Bandar Baleelah
Domin Karin
Domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu,
Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.
by
musa s zage