Furar Danko Book 2 Page 55
‘…..!!
5️⃣5️⃣
……… Da kayan data haɗa na tafiya ya fara cin karo. Yay ma kayan kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Har ya gama wanka ya kimtsa bata shigo ba, duk da yaji hakan babu daɗi sai ya daure. Ganin bata da niyyar shigowa shi kuma yana bukatar shayi ya sashi mikewa ya fita da kansa. A falo ya sameta zaune ta zubama tv ido. Ɗan tsai yay yana kallonta na wasu sakkani, sai kuma ya ɗauke kansa ya wuce kitchen. Babu daɗewa ya dawo ɗauke da cup ɗin shayi, wucewarsa yay nan ma ya barta da ƙamshin turarensa. Takaicinsa ne ya turnuƙe mata zuciya, taji kamar ta fasa ihu. Sai kawai ta ɓige da sakin kuka mai cin rai. Wayarta ta ɗauka, tai tsai tana kallo da tunanin wanda zata kira ta sanarma damuwarta, sai kuma zuciyarta ke kwaɓarta da yin hakan. Wani gefe na bata shawarar gara taje suyi duk wacce zasuyi ita da shi amma karta yarda sirrinsu ya zama abin kasawa a fai-fai. Sannan ba lallai ne ba ta samu goyon bayan wani, musamman idan tai la’akari da yanda mutanenmu suka ɗauki haihuwa abu mai matuƙar muhimmanci. Wayar ta yarfar a kujera wasu hawayen masu zafi na silalo mata. Ita da wannan shariyar da yake mata gwara ya balbaleta da masifa kawai, idan yaso ma ya haɗa harda duka yafi sauƙi. Batun yanzu ba ta tsani ta samu saɓani da mutum ya mata shiru, gara a sanar mata ayi hayaniyar da za’ayi komai ya wuce, saboda ita bata iya riƙo ba sam. Shiyyasa tafi yarda da da’an mata ta rama kawai a wuce wajen sai wata kuma ta taso.
Aunty Bilkisu da ke karance da yanayinsu a kwanakin nan leƙowarta biyu tana ganin Lulu zaune a falon. Ana ukun ne ta sameta tana kuka. Shiru tai tana kallonta cikin nazari, kafin ta ƙaraso cikin dakin ta kai zaune a kusa da ita ta zari tissue ta miƙa mata. Lulu bata musa ba ta amsa ta share hawayenta. Sai dai duk da haka basu daina zubowa ba. Lokaci sosai ta bata ta rage nauyin zuciyarta da kukan kafin ta fuskanceta. Cikin tausasa harshe ta ce, “Wannan shine auren! Shine kuma haƙurin da iyayenmu ke yawan jaddada mana akan muyi idan za’a kaimu gidan aure da bayan an kaimu. Su maza haka suke zuma ne ga zaƙi ga harbi. Zaka iya kuma cin karo da kowanne a garesu a kowanne irin lokaci koda babu wani ƙwaƙwƙwaran laifin da kai musu. Mawaddat kada ki kalleni a matsayin yayar miji, kalleni a matsayin yar uwarki mace da tasan zafinki da sanin ma’anar kalar raɗaɗin da kike ciki. Minene ke faruwa tsakaninki da shi?. Karki damu ki faɗa min, zan koya miki dabarun da zaki cimmasa, dan nasan Hydar nada zuciya, kafiya, da taurin kai akan abinda yake ra’ayinsa.”
“Aunty ni ban san mina masa ba. Na tambayesa amma yaƙi faɗa. Har roƙonsa nayi bai saurareni ba. Ni gaskiya ina son na wuce gida bazan iya ba….”
A bazata batare da sun san yana a bayansu ba suka ji saukar muryarsa a kansu, “Ai dama bazaki san mi kikamin ɗin ba, gida kuma ga hanya nan a buɗe tunda dama shine burinki tun ba yanzu ba!!”.
A zafafe itama Lulun ta ɗago zatai magana aunty Bilkisu ta jinjina mata kai tare da jimƙe hannunta cikin nata alamar kar tace komai. Shirun tayi sai dai ta fashe da kuka. Tsaki yayi da juyawa zai koma dan dama kofin da ya sha shayi ya fito maidawa kitchen, da sauri aunty Bilkisu ta dakatar da shi da faɗin, “Hydar dawo ka zauna”.
“Aunty ni mizan zauna na mata, kina jin fa abinda take cewa. Dan taga na ƙyaleta bance komai ba har tanada bakin faɗama mutane zata wuce gida. To zuciya take tunanin ta fini ko mi?…”
“Hydar Please cool dawn mana. Nace ka zauna. Idan kuma Ammah kuke son na kira muku nikam sai na kirata. Maybe ita kufi jin maganarta”.
Ransa a ɓace ya dawo ya zauna. Sai faman sauke huci yake. Yayinda ita kuma Lulu take kuka. Sai da aunty Bilkisu ta basu mintina kamar uku zuciyoyinsu suka ɗan risina kafin tai gyaran murya kaɗan tana fuskantar Smart. “Aliyu mike faruwa? Kasan dai Mawaddat amana ce a hannunka, sannan ni shaida ce tanada haƙuri da ƙoƙarin ganin ta ƙyautata maka a matsayinka na mijinta da kiyaye duk wani ɓacin ranka. Shin miya kawo wannan fitinar a tsakaninku haka babu daɗi? Kuna ganin kunmin adalci abu ya faru kuna irin wannan tashin hankalin ina a tsakkiyarku. Wane laifi ta maka? Miya faru kake fushi da ita? Tunda ita ta tabbatar min bata san abinda tai maka ba…”
“Ai bazata sani ba tunda ta ɗaukeni wawa da bai san ciwon kansa ba….”
Cikin kuka Lulu da ke kallonsa ta ce, “Toni ya kake so nayi maka ne Aliyu. Na tambayeka kace ban maka komai ba. Amma kana fushi da ni. Ko magana baka son kayi dani, idan ka gaji da zamanmu ne ka sallaman na wuce tunda ai ba dole bane. Ni dama bance inayi ba balle kaji su bini da tsatstsaga….”
“Oh nine kazar kenan? Ai ba sai kin faɗa ba dama nasan ba ƙaunata kike ba. Dan baki da yanda zakiyi da ni ne kawai kike zaune. Sai dai ban san ƙiyayyar da kike min ɗin takai girman haka ba, har ki guji haihuwa da ni. Na farkon dama ALLAH ne yayi maganinki ya samar da shi a lokacin da bakiyi zato ko tsammani ba, shine yanzu kika bi hanyar takaita ni. To sai ki sake ɗaura ɗammara dan wannan batai dai-dai da ke b…..”
“Ya ALLAH Aliyu…”
Aunty Bilkisu ta katseshi cikin tashin hankali. Dole yay shiru shima yana hucin. Yayinda Lulu ke kukanta ita dai. Shiru falon yayi kusan mintuna biyu sai ajiyar zuciyoyinsu sannan aunty Bilkisu ta sake dubansa. A nutse ta ce, “Kai waya gaya maka bata son haihuwa da kai Hydar? Banji daɗi wannan furucin naka ba sam gaskiya”.
“Gaskiyar kenan ai aunty, inda tana son haihuwa dani bazataje tai planing babu sanina ba. Da haka zamuyita tafiya ni ina tunanin akwai matsala ita kuma tana cutar dani. Da yake bani da hakkinta sai gashi ALLAH ya sanar dani ta hanyar likitar da taje ta dubata. Ni na taɓa cemata bana son yarane? Gidanmu mu kusan talatin aka haifa, yanda na tashi na gammu nima haka nake fatan tara zuri’a. Amma shine zata zaluntan….”
“Niba azzaluma bace, kuma nima bance bana son haihuwar ba ai…”
“Ƙarya kike yi wlhy, idan ba zalunci ba mi kikayi? Da lafiyata da ƙuruciyata ki cutar dani ta hanyar katangeni da ganin jini na. Ke wlhy kika sake maidamin magana zan fasa bakinki ne har sai haƙoranki sun zuba. Bana son raini ki shiga hankalinki kar kiga ina ƙyaleki ki ɗaukeni wani banza can!!….”
A hargitse Lulu take dubansa. Zatayi magana Aunty Bilkisu ta hanata. Shiko sai huci yake yi dan ya gama kaiwa wuya. Abinda Lulu bata sani ba Smart ya tsani yana magana ana maida masa. Musamman idan shi akaima laifin yana sake harzuƙa ne. Duk yaran gidansu sun san wannan halin nasa, shiyyasa suke kiyaye wa. In ko kai kuskuren dagewa akan dole sai ka masa bayanin da zaka fidda kanka zai iya maka dukan hauka ne ya bar uwarka da jiyya. Wannan itace babbar matsalarsa, idan yay ƙololuwar fushi baya iya controlling temper ɗinsa sam. Shiyyasa yake da ƙoƙarin kauda kansa akan abubuwa. Ganin yanda ya fusata ya saka aunty Bilkisu cewa suje su kwanta da safe sa ƙarasa. Shi ya fara tashi fuuu ya wuce, dan haka ta hana Lulu tashi. Nasiha ta fara mata da sanar mata halinsa na son rashin maida murtani ko bama kai kariya. Dan shi idan akai masa laifi ko bayani wani lokacin baya buƙatar ai masa. Gara ka masa banza idan ya gama hawa da saukar zai huce da kansa ya dawo ya binciki gaskiya in ma hukuncinne ya maka. Ta nuna mata kuskurenta tare da bata shawarar taje ta cire abinda ta saka ɗin. Haihuwa ai komai na ALLAH ne. Ayi fatan kawai ALLAH ya bada masu albarka. Lulu taji daɗin nasiha da shawarar aunty Bilkisun, dan haka ta ɗan ji zuciyarta ta rage mata nauyi.
Koda ta shigo ɗakin kwance ta samesa. Batai magana ba ta shiga toilet tayi wanka ta gyara jikinta. Kamar yanda sukeyi a tsakanin nan kwanciyar kai da ƙafa haka ta kwanta yau ma. Ta lulluɓa da bargon data ɗakko. Duk abinda take yana jinta, amma ko motsawa baiyi ba. Sai can cikin dare sosai ya tashi yayo alwala ya zo ya kama salloli. Sai da ya ji zuciyarsa ta samu nutsuwa da karatun Alkur’ani sannan ya tsagaita. Ganin asubahi ta gabato ya haƙura bai kwanta ba har sai da yay sallar asubahi. Alerm ne ya tada Lulu, dama haka yake mata tunda suka samu saɓanin. Kafin ta fito bayi ya haye gadon yay kwanciyarsa…
Ranar yini yay barci, dan sai azhar ya tashi. Babu kowa a ɗakin sai shi kaɗai. Yay wanka ya shirya cikin ƙananan kaya marasa nauyi. Suna falo zaune Iya Tabawa na basu labarin sanda suna ƴammata Lulu na kwasar dariya kamar ba ita tasha kuka jiya ba ya fito, sam ita bata da riƙe abu, shiyyasa idan aka riƙeta take jin zafi. Da gudu AA dake wasa ya nufosa. Cak ya ɗaga yaron sama yana mai sumbatarsa cike da jin ƙaunarsa. A haka ya kai zaune cikin kujera suna dariya shi da AA ɗin da yakema cakulkule. Iya Tabawa ya fara gaisarwa sai aunty Bilkisu. Ya tambayeta yaya jikin tace Alhmdllh sai fatan komawa gida lafiya. Murmushi yay da faɗin, “Ai keda Nigeria sai nan da shekara ɗaya”.
Idanu ta waro sosai da faɗin, “Shi kuma mijin nawa kuyi yaya da shi?”.
Cikin kauda kai da taɓe baki ya ce, “Uhm su miji”.
Kafin aunty Bilkisu ta sake cewa wani abu a fisge Lulu tace masa “Good Afternoon”. Kallonta yayi shima a karo na biyu cikin ɗauke kai yace, “Afternoon” a taƙaice. Daga haka babu wanda ya sake kula ɗan uwansa. Abinci ma sai da aunty Bilkisu ta zungureta ta tashi ta kawo masa. Batai zaton zaici ba, amma sai taga yaci sosai yana bama AA. Bata san yayi matuƙar kewar girkin nata ba ne. Basarwar da yake ɗin ma ta dole ce. Haka ya ƙarasa yinin nan a gida yau ko waje bai leƙa ba har washe gari. Washe garin ma sai zuwa yamma ya fita training center ɗinsu……..✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
Zafafa
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*