Cinikin Rai Book 1 Page 20
CINIKIN RAI….20
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
*Wannan shafin na ku ne, Aunty Halima da Habibay ku more!*
<<<<<<<|=|>>>>>>>>>
Wato dukkan hankalinta ta daura akan shi, har ya fito falon baki ɗaya. *Wheelchair!* Ta furta a kasar zuciyarta. Dauke kai tayi tana dariya ƙasa ƙasa, d’ago idanu yayi ya zuba mata. Sake kallonshi tayi ta kunshe dariyarta, baki daya sai yaji ya muzanta. Jikinshi ya wani irin sanyi. “Ke meye haka?” Dake bata iya boye abin da yake ranta ba ta ce mishi.
“Malik Menk Jordan! Ya kare akan keken guragu. Wai dama wannan shi ne dalilin da yasa shi nisanta kanshi da Al’umma?” Ta kuma kwashewa da dariya, sannan ta dan durkusa akan gwiwarta kamshin turaren Imperial Majesty ya daki hancinta. Sau daya ta tab’a jin kamshin nan, a rayuwarta sai yaui. “Ko a yaya nake bana kunyar haduwa da mutane, sannan maganar pmutane bata gabana. Ni mutum ce me ra’ayin kaina. Ban zo nan domin Kasuwancinmu ba, nazo na ga waye ya firgita mutane da Gwamnatin kasa baƙi daya.
Ka ji da kyau, bana tsoron tunkarar kowacce matsala, amma a karon farko na rayuwata da na ga makirkirin matsala ya koma gefe yana gudun matsala, shi yasa na mishi dariya. Da nasan cewa Malik Menk Jordan ya gudu daga cikin al’umma saboda nakasarshi da ban tako nan ba!”
A karon farko da yaga macen da ta saka shi ya ji ashe, shi in matsoraci h ne. Ashe tsoro ne ya saka shi boye kanshi. Kasa magana yayi ya kalli Elbashir. “Coffee take bukata ko Tea?” Wani dariyar takaici ne ya kamata, wato shi a haka har wani izza ce da shi. Haka kawai zuciya ta ingizata ta kai mishi naushi. Kafin ta idda nufinta, ya ja kekenshi. Sai da ta fadi can.
“Ke baki da hankali ne?” Elbashir ya fisgota zai kifa mata mari.
“Kyaleta mana, bakuwar mu ce tana buƙatar karramawa ko wacce iri ne!” Gyada kai yayi. Fita yayi kallon Malik tayi yana tafiya a keken shi har gaban wani table. Zaman shi ya gyara yana kallonta. Nuna mata kujeran da yake facing ɗinshi yayi.
Hadiye yawu tayi tana me zama dakyau ta ce mishi. “Da gurgunta kake niman maza?” D’ago kai yayi ya kalleta, kasa tayi da kanta tana wasa da file din hannunta. Kwarjini ya mata lokaci guda, yadda ya kura mata idanu, tana jin ba dadi domin tsakani da Allah idanunshi na da kaifi. “Me kake so?” Ta tambaye shi muryanta a shake. Murmushi yayi yana me juya kekenshi. Shigowa aka yi da tiren tea. Elbashir yana biye dasu, duk maza ne kuma matasa.
Ajiye a gabanta suka yi, Elbashir ya koma gefenshi ya tsaya a gefenshi. “Sha!” Ya fada a sassanyayye. “Ba na shan ruwa ko wani abu a inda ban yarda dasu ba!” Murmushi yayi ya ce mata. ” “Sugar nawa kike so.?” “Guda bakwai!” “Bakya tsoron ciwon sugar ne?”
“Waye ya damu idan na mutu? Don haka zanji dadina kafin na mutu.” Duk da tarin yarintar da ya hango a tattare da ita, amma kuma ya fahimci tana fadar duk abin da ya fito daga zuciyarta ne. Sai da ya zuba mata sugar hudu, ya juya kafin ya d’an diba a cokali ya sha kaɗan, ya tura mata. Da wutsiyar ido ta kalle shi ta ce mishi. “Duk da haka ba zai saka na sha ba “”Ok” ya kai spoon zai diba Elbashir ya ce mishi. “Malik ka manta baka shan sugar!”. Juyawa yayi ya kalli Elbashir ya ce mishi. “Kai haba dole mu karrama bakuwar mu”
Sai da ya sha sau uku kafin ya tura mata har da cookie ɗin. A hankali ta dauka tana kallon coffee ɗin. Kurba tayi a hankali, “Idan kuma da mun saka, guba fa?” “Tunda ya sha ai zamu mutu tare ne!”
Murmushi Malik yayi yana kallon ɗan bakinta yayi, yana girmama maganar da yake fitowa sam babu mara ma’ana sai dai rashin da’a. Ajiye kofin tayi tana faɗin. “Ya ishe ni” “Muje ji ga gidan!” “Tab! Ba ji ya kawo ni ba.” Ta mika shi file ɗin. “Da dai kin tashi kunje!” A fusace ta kalli Elbashir.
“Ban zuwa wani abu ne?” Ta tambaye shi, “ko daya”
“Ok Ina file ɗin!” Mika mishi tayi ya dauki medical glass ya saka sannan ta ce mata. “Su mutanen da suka baki aikin me yasa basu, bawa Yaransu ko su kansu ba?”
Shiru tayi tana kallon shi, sam bai yi kama da wanda yake dogon magana ba, amma yadda yake magana. Yana kara saka mata mamakinshi.
“A Kasuwancinmu, cinikin rai yafi kome armashi da me zaki biya asarar da aka min?”
Kallon shi tayi, sannan ta ce mishi, “Na sani rayuwa ita ce fansar, tsinannen dukiyarka”
“Ke ki iya kalamanki!” D’aga hannu yayi alamar Elbashir yayi shiru. “Hmm! Ina jinki.” Ganin babu ɓacin rai ko muzanci a kan fuskarshi yasa ta sake wani lalacin murmushi ta ce. “Ba fa ni ce ba fada ba, abin da naji mutane na fada ne, me yasa ba acin dukiyarka?”
“Saboda gumina ne, babu gumin kowa a cikinshi.”
“Kana cire hakkin Allah kuwa a cikin gumin naka?” Rintsa idanu yayi ya ce mata. “Bana cirewa ko zaki cire min ne?”. Kallon shi tayi sannan ta ce mishi. “me yasa kake jin haushi?” Nuna kanshi yayi sannan ya ce mata. “Bana jin haushin!” “Kana jin haushi mana, kokarin boye fushin zuciyarka kake, amma kafi wancan sikagon fusata!” Ta kalli Elbashir.
Matse hannunshi yayi sannan ya ce mata. “bana jin haushi, baki gani ba ne!”
“Kana jin haushi tunda gashi kamar zaka karya kashin hannunka, Malik” ta kira sunanshi a hankali, ta fuskance shi. “Kasan me? Nayi abubuwa dayawa a rayuwata, kama manyan laifuka zuwa kananu. Amma na iya saita kaina, kai kuma tunda nazo naga fushi da ɓacin rai a kan idanunka, idan baka manta ba kasan dalilin da yasa na kai maka duka? Domin na kara yarda da cewa kana cikin fushi ne, and saka hannu zan tafi”
Ya kai tsawon shekaru sha uku a wurin zaune, amma babu me zarrar gaya mishi magana ko wacce iri sai an sunkuyar da kai amma yarinyar da yasan da yayi aure da wuri da ya haifi wadanda suka haife ta , take gaya mishi magana son ranta.
“Saka min hannu?” Shiru yayi yana nazarin abun da ta fada, a fusace yake? Yes a fusace yake na tsawon shekaru arba’in yana cikin fushi da fushin wani. Amma kuma me yasa yarinyar ta zo har niman shi? Shin Ishara ce tazo ta mishi ko kuma tazo ganin sirrin shi ne ta gaywa duniya.
Kamar ta san me yake tunani ta ce mishi.
“Ka da ka damu, ban tab’a tsurku ba, sannan ban iya saran kowa ba, bana yin ka domin na fallasa asirinka, bana zama da kai domin dukiyarka, abu daya na sani idan kayi min halacci, zan maka biyayya kamar kare amma ba zan dauki cin mutunci ba, domin ina da saurin hannu. Abu daya nake son na gaya maka, a matsayinka na Mayor mai gari, ina son ka fito cikin al’umma ka, su san waye shugabansu ba ka zauna a tsibiri kamar wani namun daji ba.”
“Hmm! Kin ga?” Tab’e baki tayi tana faɗin. “Yo kwana zan yi ina surutu? Saka min hannun?”
“Zan saka hannu amma da sharadi!” Tsam tayi da ranta, kafin ta ce mishi. “Hmm! Bayan ka saka hannun kenan sharadin zai biyo baya, amma yanzu ratab’a kawai.”
“Ki tsaya ki shi sharadina!”
“Ina fa, kawai saka min sai ka faɗa min!”
“Kamfanin da zan saka miki hannu akai, basu da.”
“Wannan daga baya zan ji da shi, saka min hannu!”
“Mutanen da suka turo ki.”
“Malik Menk Jordan!” Tun daga tsakiyar kanshi ya ji sunan har sai da yaji tafin kafarshi tana kaikayi.
“”Please saka min hannun.” Kura mata idanu yayi ya ce mata.
“Me yasa ba.”
Dan mikewa tayi ta zago bayanshi, ta dan rankwafa kadan daidai kunnenshi.
“Ka saka min hannu, duk wani abin da zai faru. Zan magance shi bana son jan rai ina da wutar ciki.!”
Yadda take maganar daidai kunnen shi ya haifar mishi da mutuwar jiki.
Pen din hannun shi ne ya fara kokarin fadi, Elbashir ya fisgo ta, tare da dawo da ita kan kujeranta.
“Ke wacce irin mutum ce?” Murgud’a mishi baki tayi, ta ce mishi..
“Dan bakinciki ina ruwanka da mu? Koma meye matsalarka da mu? Yau naga hassada. Gaskiya Uncle Malik ka gaya mishi ya daina saka min idanu.”
“Elbashir!”
“Na’am Ubangidana!”
“A kiyayye!”
“An gama”
“Haka ya miki?!”
“Dama-dama, dan sarki akan jaki.”
“Kamfaninku tana da license?”
“Wai duk akan saka hannun kake wannan bididdigin?” Ta fada tana kokarin kwashe file din, tunda ya kasa saka mata hannu.
Rike file din yayi ya ce mata, “zan baki cheque, ki tafi ki kwashe duk yawan abin da kike so, amma ki sani da shar”Ka cinye sharadinka, na fasa.”
“Gashi nan ki saka iya adadin kudin da kuke so.”
“Kace na saka iya adadin kudin da ya mike?”
“Yes!”
“Ko ba Yes ba!” Ta karbi takardan cheque, sannan ya juya banki daya suke.”
“Golden bank?”
“Kin san banki ne?”
“Eh anan nake ajiye kudina!”
Yadda suke jira zaka dauka sun shekara guda da sanin juna, hiran ba wai na arzikn bane, saka iya adadin kudin da suke bukata tayi, ta mika mishi. Kallon kudin yayi sannan yayi sign.. “ka duba yayi ko?”
“Eh Malik na saka a cikin littafin amsar Cinikin rai ne?”
“A’a” ya fada yana sign a jikin file din da ta zo da shi.
“Me kike so yanzu?”
Mikewa tayi tana murmushi, “me kuwa zan bukata, bayan wanda na samu? Kawai na gama sai an fara juya kome.”
“Idan wani abu ya samu dukiyata, sai kin biya.”
“Idan ban biya ba, a rataye ni. Kuma ka gayawa Awakin da suka kawo ni ahir
dinsu, a kuma rufe min fuska idan ba haka ba, hukumar kare hakkin dan Adam zata shiga tsakanin mu.”
Karfin halinta kawai suke gani, “eyeee haka kuke barin abokin cinikayyar ku, ya tafi shi daya babu dan rakiya?” Kallon juna suka yi. “Ke dalla tafi can, tunda Malik ya dawo nan bai.”
“Muje a rakata ai bakuwar mu ce!”
“Tow Malik!” Inji Elbashir, wani gatsina fuska tayi ta ce. “Kai wallahi baka da hali, wato aikin kwarai ba zaka saka shi yayi ba, kana nan a bayan shi kamar bindi. Wallahi ka ji tsoron Allah, ka daina hana shi aikin alkhairi ba halin musulmin kwarai ba ne.”
Haka suka rakota har waje. Kallon Malik tayi ta ce mishi. “Turarenka yana min kama da kamar mun tab’a haduwa, a wani wurin but i can say ga inda muka hadu ba.” Ta fada tana kallon security na cikin gidan baki daya. “Kana kula da rayuwarka sosai.” Ta dan dukka kaɗan. “Kamar yadda kake kula da dukiyarka, da kuma.” Kasa jan numfashi yayi, domin abin da yake mugun gudu kusanci. Baya yayi da keken shi ya ce mata.”ki kula da rayuwarki da mutanen da suke zagaye dake!” Sake baki tayi sannan ta d’aga kafad’arta ta cigaba da tafiya.
“Malik me yasa ka amince ka saka hannu, bayan kasan ita kanta ba ra’ayin kanta ba ne?”
“Babu kome, domin ko na maka bayani ba zaka gane ba ne!”
“Zan gane mana, ka min bayani yadda zan fahimta. Mutanen mu suna ta bibiyar alamarinka zaku gana, kaki amma ita lokaci daya ka bata damar ku gana!”
“Hmmm! Zak fahimci dalilin sai nan da yan lokaci ƙalilan.”
Daga haka ya juya da kekenshi. *Gudu kai saboda nakasarka?*
“Elbashir yarinyar nan tayi gaskiya, a gyara min gidana na whiter town!”
“Malik tunda nake da kai, tsawon shekaru arba’in baka tab’a canza maganar ka ba, yau kai kace cewa zaka koma whiter town?”
“Na yanke shawarar haka, a maida ni whiter town!”
★★★
Kamar yadda suka daukota haka suka mai da ita, bata zame ko ina ba sai kamfanin Amjad.
“Ajiye mishi tayi a gabanshi.”
“Gashi nan na samo kome!”
Kallon cheque din yayi, ya ce mata.
“Are you sure kin ga Malik?”
“Kai baka.tab’a ganin shi ba ne?”
“Ko hoton shi kuwa ban tab’a gani ba!”. .”tow gashi nan, zan tafi gida.”
“”Da wuri haka?”
“Eh ta saka kai zata fita!”
“Zeenobia na gode sosai!”
“”Ba kome”
Ta fada tana me barin Office ɗin, ko minti biyar bata yi da barin kamfanin ba, MD da Salim suka shiga kamfanin aka shiga kwashe kome, kafin karfe shida na yamma sun kwashe kome sun sallami ma’aikata.
Karfe tara na dare, ginin kamfanin ya ruguje ya zube kamar ba a tab’a ginin shi a tsaye ba…..
*Zan kara muku page daya ya zama last free page in sha Allah idan na gama book one, book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[01/09, 9:04 pm] usmanlauratu71