Cinikin Rai Book 2Hausa Novels

Cinikin Rai Book 2 Page 9

Sponsored Links

Volume: 9 The trued behind illegal
Sai da suka iso kofar gidan ta fito shima ya fito, yana karewa unguwar kallo, sannan ya ce mata.
“Zainab baku da makaranta ne a unguwar nan?” Hararanshi tayi ta ce mishi.
“A matsayinka na Mayor me gari, baka san aikinka ba, babu asibiti babu makaranta, sannan kaga yadda unguwar take da manyan lambatu ka tambaye ni, kai abin da ka sani niman kudi baka san yadda rayuwar mutane suke ba, kada ka sake Allah ta tambaye ka, da hakkin talakawan unguwar nan!”
“Gaskiya ban kyauta ba, amma ai laifin ba Ni daya ba ne?”
“Na ka ne mana, kai ne shugaba kuma kai kake da hakkin sanin su waye suka zabe ka. Ni zan tafi na kwanta.”
“Na zata zaki ce dan gurgu muje ka taya ni kwana, sai na daka tsalle!”
Wani yatsuna fuska tai tare da juyawa, bata kuma cewa cikanka ba. Baki daya ta ta manta da jacket dinshi da ta rufa sai da ta shiga cikin gidan, Elbashir da wasu security suna leke-leke, saka yatsa Elbashir yayi ya ce.
“Ta shiga cikin dakinta!”
“Tana barandar ɗakinta!”
“Weldone ”
“Sir ta shiga!”
“Ok” ya dan dukka kaɗan ya ce. “Malik ta shiga ɗakinta.” “Ok, ina son nan da kwana uku a hada connecting Cctv footage din unguwar nan da master room dina. Sannan a saka Idanun akan motsi Shatima!”
“Kana zarginshi be?”
“Kula da kai bada sako.”
Shiru Elbashir yayi yana fadin, “kuma gaskiya ne, domin ya tunzuro Lalla salmah da Jalilah.”
“Kome aka yi da jaki sai ya ci kara, manta da su.”
“Hmmm! Kyale su, ina jiransu.”
Iya haka ya fada ya shiga motar, Elbashir ya nad’e mishi keken ya saka a bayan motar, suka bar unguwar.

Dakyar ta iya wanke fuskantar, ta cire kayan ta kwanta. Idanunta a rufe tayi addu’ar barc, daga nan barci yayi gaba da ita.
★★★
Washi gari
Lalla salmah ta shigo Keivroto da misalin karfe takwas na safe, bata tsaya ko ina ba, sai whiter town. Kai tsaye gidan Malik ta nufa. Wani abin dariya koda ta isa ku kwarjinin Malik ya hanata ko tari. Asalima sai ta shiga raba idanun tana sunkuyar da kanta. Malik yayi bala’in cika mata idanun.
Ai masu iya magana sun ce wargi wuri ya samu. Kuma hakan ce domin bata iya ko tari ba, Malik da ta kai sama da wata huɗu tana son ganin shi amma sai gashi a banza ta samu ganin shi.
“Malik dama nazo maka da wata magana ne.”
“Ina jinki;” ya fada hankalinsa yana kan tap dinshi.
“Wai ko zaka duba Maidah ce, bata da matsala.”
“Na riga na zaɓi wacce nake so, Don haka babu kome Allah ya bata wanda ya fini”
“Amma Malik wace ce haka ne Sa’a?”
“Wata marainiya ce daga cikin gari!”
“Marainiya kuma? Ba yar kowa ba?”
D’ago fararen idanu yayi ya zuba mata ya ce mata. “Dole sai Yar wani zan aura ne?” Girgiza kai tai, ya ce mata. “Kin ga kuwa bai zama dole sai nayi abin da zai faranta ran kowa ba, matukar raina zai min dad’i bana bukatar amincewar kowa da kowa, kin fahimta?” Ya kuma tambayar ta, gyad’a kai tai, ajiye tap din. “Ki nutsu akan goben yarki, bana son fitina da tashin hankali, i choice Zainab ne domin wani dalili na kashin kaina, don allow me to be angry!”
Gyada kai tai domin bata da bakin magana.
Ganin haka yasa ta mike tssm tare da mishi sallama.
Tabbas izuwa yanzu ta fahimci Malik ɗin da ta sani ba shi ne a gabanta, wannan sakakken Malik ne domin wancan babu ruwanshi maganar da zata fito bakinshi akan kuɗi ce ko harkan siyasa.
Amma wannan kiri-kiri ya gaya mata ya fara soyayya da wata yarinya ba yarta ba, sannan ba ita kanta ba, asibiti ta wuce wurin shatima da yake kwance ta ce mishi.
“Wai meye ya maka ne ka koma haka? Ya batun aurenshi da Nadrah!” Dakyar ya tashi zaune sai da Faruq ya taimaka mishi. “Hmmm! Batun aurenshi da Nadrah ai tuntuni ya rushe baki da labari ne? Nasan waye munafukin Elbashir ne. Don haka abin da zance ke ki jaraba hada shi da yarki mana!”
Zama tai sannan ta ce mishi.
“Malik ɗin da na gani yau, ba Malik ɗin da na sani ba ne, Malik ɗin da na sani babu harkan mace a gaban shi, amma yau da idanuna naga wannan Malik ɗin idanun shi naga much of love and affection!”
Murmushi yayi sannan ya ce mata.
“Exactly what I see, idan mutum ya taba yarinyar tabbas dukar mutuwa Malik zai yiwa mutum!”
Ajiyar zuciya suka cike da damuwa, can Lalla salmah ta ce mishi. “Hmmm ya kake ganin muyi tsayayya magana.”
“Kamar ya?”
“Mu ingiza Jalilah mana!” Kallonta yayi sannan ya ce mata. “lallai mata dole shaidan ya sallama muku, kaidinku tafi tashi.”
Juyar da kai tai tana faɗin. “ta wannan hanyar ne zamu turo yarinyar daga jikinshi. Sannan zamu dragging Jalilah itama. Yanzu zata iso nan da karfe daya na rana, zata sauka a gidana!”
“Allah ya kai mu!”
“Amin,amma kai meye matsalar da ya haɗa ku!’
“Yarinyar ina sonta, amma lokaci guda Malik ya juyar mata da tunaninta, sannan ya saka ta butulce min!”
“Kai fa yautai ne mugun tsuntsu ne, ka hango wani abun ne yasa ka nacewa yarinyar.”
“Gaskiya ne, yarinyar karama ce amma yar jagaliya ce, sai dai duk da wanan harkan tana da mugun kamun kai, kome nata a rufe yake, nayi kokarin nimanta da shashanci ya akan idanuna ta mari wani matashin mai kuɗi, shi kuma yayi alƙawarin sai yayi yadda yake so da ita, karshe na saka aka bi min shi har kasar shi, aka mishi kakkauran kashedi bayan sun karya mishi kafa da hannu, idan ya kuma zuwa gawarshi zata dawo ƙasar shi ba a gane shi ba.”
“Yanzu don wannan yarinyar kayi wannan aikin, na zata a film ake irn wannan aikin ashe har a duniyar zahiri ana aikatawa!”
Gyad’a kai Lalla salmah take, domin taga wanda ya ci ubanta a rashin mutunci. Kuma a haka aka samu wanda ya kwantar da shi, gyad’a kai tayi sannan ta ce mishi.
“Yanzu meye matsalar ka da Malik?”
“So nake na wargaza shi, na ruguza duk wani aikin shi na tukuru!”
“Ai kuwa ka dauki dala ba gammo, ruguza Malik ba sauki, domin babu hanyar da zaka iya ruguza Malik, babu shi har duniya ta tashi!” Inji Elbashir yana ajiye mishi kayan dubayya.
“Nazo nan ne, domin Malik ya bukaci haka, ka da zuwa na ya saka ku fara tunanin da wata manufa nazo. Lalla salmah har dake?”
“Ni kuma? Allah ya min tsari, kawai nazo duba shi ne da jiki.” Daga haka ta dauki jakarta tabar dakin,jan kujerar da yake gaban gadon Elbashir yayi ya ce mishi. “Zan baka shawara, a matsayin wanda ya fara zama da Malik. Ka sassauta kiyayyr da kake nuna mishi. Malik bai maka kome ba sai tarin alkhairi, wallahi idan ni ne kai ba zan yarda wani ya san meye matsalata da shi ba, tunda Malik ya rike hannuna, har kwanan gobe bana fatan ya sake ni, daga bayanka nazo amma yadda nasan Malik ko kai da ka sanshi tsawon shekaru albarka, don haka ina baka shawarar ka tuna me ka mishi ya juya maka baya?”
Shiru yayi sannan ya mike yana fadin.
“Indai akan Zeenobia ce, Malik ba zai ragawa kowa ba, yana da kyau ka san wace ce ita a rayuwar Malik duniyar shi yake son ginawa da ita;”
“Idan ka gama zaka iya tafiya, kare mara zuciya.”
“Duk abin kace daya ne;”
Daga haka ya juya ya fita,. Ba zai tab’a fahimta ba, ya barshi da halin shi, Allah yana ganin ya fita harkokinsu da Malik gashi ga Malik ɗin.
***
01:07pm
Jalilah ta sauka, Elbashir ya tafi daukota. Daga nan wani gidan Malik da yake cikin gari ya kaita. “Na kawo ki nan ne, domin Malik ya ce haka idan kuma sake kika biyewa Lalla salmah da Shatima kwabarki zata yi ruwa. Malik bai san kin zo ba. Ki gama kwanakin ki koma gida.”
Daga nan ya juya yayi tafiyar shi. Bayan tafiyar shi, ta kira Lalla Salmah, ta ce mata tazo maza. Kafin wani lokaci ta iso. Wanka Jalilah tayi, suka fita cin abinci. Suma gidan cin abincin da Malik ya ci suka je.
Can bayansu wata ta ce.
“Ke kin ga wani labarin da yake trending?”
Girgiza kai ɗaya tayi, “duba Mayor Malik Menk Jordan tare da wata yarinya suka ci abinci jiya anan gidan cin abincin.”
Kallon juna Jalilah da Lalla Salmah. Juyawa Lalla Salmah tai ta ce musu.
“Don Allah muga yarinyar?”
Mika mata suka yi, tayi zooming hoton Zeenobia bai fito ba. A saman hoton aka rubuta.
#girlfromgettoarea#keivrotoinhell#datingorbadside.
“Mika musu wayar” tana fadar haka ta mike daga kujerar suka fita a cikin gidan cin abincin. Kai tsaye ta ce. “Kai ni gidan shi;”
“Tow! Ai wallahi idan nice ba xan yarda ba zan yarda ba, ka lalata min rayuwa ka ajiye ni for while.” Haka tai ta zugata tana nuna mata ai Malik bai da amana, tunda yaci moriyar ganga shi yasa ya watsar da ita.
Ai da mutumin kirki ne d sun taru sun rufawa juna asiri.
Waye ya mutu waye ya dawo. Dakyar suka isa gidan, bata tsaya ta gama parking me kyau ba, ta fito daga motar ta shiga cikin gidan. Lokacin Malik yana tare da baki. “Ina maciyi amanar, bayan lalata min rayuwa da kayi ka ajiye ni for long time kana da zarar niman wata mace? Har kana da ikon auren wata mace? Tow wallahi sai duniya tasan abin da ka aikata ya bika kaji na rantse da Allah! Tun wuri ka gaggauta rabuwa da shegiya kwadayayyar yarinyar nan”
“Bashir yi min waje da mahaukaciyar nan” ihu ta shiga yi da tara mishi jama’a. Tare da fadar miyagun kalmai akan shi, kuma ta tabbatar da cewa sai ta yi taron manema labarai ta gaya musu abin da yake aikatawa.
Duk da baya son magana, bai wani ko dar ba. A wanan gaɓɓar Malik sam baya tsoro ko karya, abu daya ya sani koda maganar tafito mutanen da suke kewaye da Zainab zai yi wuya su barta ta juya mishi baya, don haka ya cigaba da tattaunawar shi. A bangaren ilimin da kuma cigaban al’ummar Keivroto City.

Bayan tafiyarsu yayi tsam yana nazari, kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
“Elbashir! Bana son al’amarin ya kai ga haka, amma Salmah da Shatima sai da suka kai ni bango!”
“Kayi hakuri zasu daina.” “Hmmm!” Ya
Fada tana sunkuyar da kanshi, asibiti suka nufa daga Shatima har Lalla Salmah babu wanda yace mata ka da ta tunkari Malik, kowannensu kawai amfani yake da ita domin biyan buƙatar ranshi.
Dake bata da lissafi, kawai ta shiga taron manema labarai.
Wurin karfe biyar na yamma, suka taru kofar asibitin, ta fito idanunta dauke da hawaye tana kuka, “Na tara ku ne anan ba don kome ba, sai dun a nima min hakkina.”
“A wurin waye?” Yan jarida suka tambaye ta,
“A wurin Malik Menk Jordan! Shekaru goma shatara ya lalata min rayuwa da sunan zai aure ni, ƙarshe ya buge da cewa na cutar mishi da Yarinyar da zai aura itama cikin yayi mata karshe ta haifa mishi yara biyu tagwaye.”
Kashe Cameras dinsu suka yi.
“Madam Jalilah! Wannan labarin ba zamu iya dauka ba, domin kuwa kema ana zargin ki da aikata miyagun laifuffukan safarra yara da mata. Ban ki Wannan labarin yayi trending a social media amma a zahiri babu haka. Amma kai tsaye an aika labarin. Wanda nasan gidajen jaridun mu sun tsayar da watsa shi duniya.”
“Babu me zarran tayani kwato hakkina?”
“Sai dai ki gwada sa’ar ki a internet, amma Malik ba kanwar lasa ba ne!”
Wato har abada tsoron Malik halittace ne a zukatan al’ummar Keivroto. Amma maganar gaskiya babu me zarran yakar shi, haka ne babu shi ba a haifi namijin ba, akwai maza.
Akwai mazaje.
Amma shi Namijin duniya ne,……
#500₦
#+234 703 513 3148
[9/10, 9:17 PM] Yan Mata:

Leave a Reply

Back to top button