Cinikin Rai Book 2 Page 26
Yan Mata: 26-
Dukkansu suna falo ya fito, bai saurari kowa ba yayi tafiyarshi, Elbashir ya rufa mishi baya. Tunda ya shiga motar yake cirra kamar wanda zai tashi sama. “Kayi hakuri!” “Ba kome!” Ya faɗa yana cigaba da cire, tabbas lalacewar bata kai da Zeeno zata mishi haka ba.
“Kayi hakuri ka mata uzuri” murmushi yayi ya ɗauke kai yana fadin.”Muje ka ji” “Ok!” Daga haka suka yi tafiyarsu. A can kuwa baki daya aka rasa me mara fada, ita da laifi ita da kuka. Mikewa Zulfah tayi ta tsaya a bakin kofar tana faɗin. “Kukan uban me kike? Idan kika sake wani abu ya kuma samun cikin wallahi ni zan tsayawa Malik da gayya kika zubda cikinki. Wawuya mahaukaciyar banza” a fusace tayi yunkurin mikewa ta ce mata. “Dan ubanki tashi zaki yi ki zubda cikin? Idan shi ne ya rage miki a duniya fa? Idan kin so ki zubar yar iska jaka, wallahi sai na gayawa Hajja Mama iskancin da kike mishi wawuya kawai”
“Eh nayi din!” Ta faɗa da karfi tana ihu, “mahaukaciyar banza” daga ta fita ta bar bakin kofar, haushi ya cikata, ba abin ta zane ta, ta zane cikin jikinta, domin ko wannan ihun da take, jini ne ya fara zuba. Don bakin hali bata fada ba, sai da ta fara jin qarfinta ya fara karewa ta shiga niman a gajin mutane, ko kafin a nimo Malik ta suma yafi a kirga, domin ba karamin jini ya zuba mata ba. Lokacin da suka isa asibitin bata ma san waye a kanta ba. Haka suka yi ta kokarin tsayar da jinin. Dakyar ya tsaya. Zuwa lokacin ran Malik kamar ya ficce a jikinshi don b’acin rai. Da aka ce za a mata karin ji, kin yarda yayi a saka mata wani ya bada na shi aka.saka mata, bayan ya huta na tsawon awa hudu, suka koma wurin likitan. “Sir cikin yana nan, amma watanin ya koma baya, sannan yawan damuwar da take shiga yasa jinin ya zuba, amma kome ya daidaita. Cikin a kula da shi domin munso mata wankin cikin sai muka samu yana bugawa bai mutu ba, don Allah a kula da lafiyar uwar da dan cikin!”
“Mun gode!” Elbashir ya furta yana me fita Malik ya bi bayanshi. “Yanzu ya zamu yi da ita?” Elbashir ya tambaye shi, yana kallon dakin da take. “Ina ga a kyaleta da zancen cikin, matukar ta san cikin yana raye a jikinta, zata iya zubawar”
“Haka shine mafita!” Don haka suka samu su Ammyn da maganar a bar batun cikin a barta da halinta, duk suka amince aka zuba bata idanu, sai da ta kwashe kwana uku tana kwance kafin ta farka, a lokacin ta ga dakin da take ciki. Lumshe idanunta tayi tana son tuno abinda ya faru, a hankali ta tashi zaune, jikinta babu kwari ta kalli bakin kofar babu kowa, komawa tayi ta kwanta tana jin wani irin rashin karfi, turo kofar nurse tayi. “Har kin farka?” Gyada kai tayi tana kallon matar da uniform. Sai da ta gama mata tambayoyi kafin ta fita ta can sai ga ta tare da su Ammyn. “kin tashi Zainab?” Gyada kai tayi tana kallon su. Brush da toothpaste ta kawo mata, sai ruwa a kofi ta bata, tana sha kaɗan. Bayan ta wanke bakinta. “Ammyn yunwa nake ji!” “Tow bari na baki abincin ko” hada mata tea tayi, sai doya da kwai, ta fara ci a hankali. Tana kallon Ammyn. “Ammyn babu su Abbas ne?” “Eh yana tare da Black sun fita!” “Hmmm! Dama Black yana nan yaki zuwa inda nake.”
“Tow waye zai zo inda kike? Bayan kin san halin da kike ciki? Kawai kowa yana gudun abin da zai janyo ki ci zarafin Malik ne yasa kowa ya kama gabanshi.” Daga haka Ammyn ta fita, tabarta ita ɗaya a dakin kamar mayya, taji haushin Malik ta kara kamata, ko da Ammyn ta koma dakin ta samu ta gama har tayi wanka. “Ammyn cikin yana nan kuwa?” “Cikin da kika ce baki so ne za a bar miki? Cewa kika yi baki san cikin waye yake da zarar cewa a bar cikin a jikinki? Shi yasa da aka bukaci wanke shi na ce e ai baki son shi a cire shi, kada ki farka ki mutu bayan ana sonki.”
Wani irin kaunar cikin ya tsarga mata, ta ware idanu waje. “Ammyn kuka ce a wanke cikin?” “Eh yo me kike so muyi? Muce a bari ki ji haushin mu?” Fashewa tayi da kuka tana faɗin. “A ƙalla a jira a ji ra’ayina, nima ina da hakki akan cikin sai a wanke mishi shi?” Girgiza kai Ammy tayi tana faɗin. “Abin da kike bukata ne aka miki sai ya zama laifi?”
“Baki son cikin an zubda laifi ne? Cewa kika yi baki so me za a miki da shi? Kin ga rayuwarmu nan tana da muhimmanci, kowa tattalin abin da yake da shi yake, amma e cewa kika yi zaki watsar da shi, don haka kiyi addu’a Allah ya kawo wani idan kina so!” Yadda take kuka kamar da gaske cikin ya tafi yasa Ammyn tsammanin ta nutsu, don haka ta kara mata da nasiha, ko zata kara jin nutsuwa a ranta, har na wani lokaci. Tunda Ammy ta tafita take kuka tana jin wani bala’in kaunar Babynta, as a mother she never protect he own child, Babyn da baby ruwanshi. Bai dauki hakkin kowa ba, amma tayi curse dinsa har ya mutu tun bai zo duniya ba, ta zubda shi. Haka tayi ta kuka tana karawa.
Koda nurse tazo, ta ga halin da take ciki allurar barci ta mata domin jininta yayi mugun hawa, dole barci yayi gaba da ita, lokacin da Malik ya ji labarin yazo har dakin tana barci. Yana ganin yadda bakinta yake motsi. Ya kai kunnenshi.
“Na gaza ceton yarona, na gaza zama uwa!” Abinda take nanawata kenan har barcin yayi nauyi sosai. Daga nan ya koma ya zauna, tare da riko hannunta ya daura a saman cikinta. “You never give up! Har yau ke uwace, laifina ya shafe shi natural and pure love kikewa little Malik” ya sumbaci goshinta yana shafa kanta a hankali yana kallon yadda duk ta lalace, dama ba auki ne da ita ba, sai kuma ta kara figewa.
Tashi yayi ya bar dakin, yana kallon Elbashir. “Jirgin yaushe muke da?” “Jirgin karfe goma na dare, saboda yanayin Keivroto akwai yanayi mara kyau.”
Kallon agogon hannunshi yayi, yana me jingina bayan shi da bango. “Me yasa take damuwa da rashin kare Yaron?” “Saboda tana sonka, tana son abin cikinta, shi yasa take kuka kamar yadda take sonka take sonshi.” “A’a ba sona take ba, kawai na mata dole ne dolen da na mata, yasa take jin haushina da cikin. Har take ganin a matsayinta Na uwa ta fadi da ta gaza kare dan danta.”
Shiru Bashir yayi yana mamakin, yadda Malik ya sauya baki daya, tun daga ranar da suka fara ganin Zeenobia tun ranar Malik yake cewa ya samu mace. Wacce babu ruwanta harkan gabanta yafi mata kome. Ashe ba haka ba ne, ashe ita nata goben daban. Na shi daban. “Bashir ka daina tunani!” “Malik idan ban yi ba me zan yi? Yarinyar nan ta sauya maka rayuwa daga yadda na sanka. Ta saka ka zamo wani irin mutum a cikin al’umma. Malik be yourself ka dawo hankalinka mana” Murmushi yayi yana tafiya a hankali yana biye dashi. “Kasan meye banbancin mu da kau?”
Girgiza kai Bashir yayi, ya juyar da kanshi yana kallon waje. “Ina sonta, kuma ina soyayya. Kai kuma baka soyayya baka san meye soyayya ba, shi yasa da kasan meye soyayya ba zaka ga laifina don na biye mata ba, sai mq tausaya min da zaka yi. Idan har mace ta kai namiji wata duniyar da bai tab’a isa ba, yana mata uzuri a duk abin da zata mishi. Bashir kayi aure ka gane me nake nufi!”
“A’a Malik ba zan iya ba, yarinyar da bata wuce sa’ar hanjin cikina ba, tana min yelling ballata zan yi na kai gidan uwareta.”
“Ba zaka iya ba, ko ni da can baya aka min abinda Zainab tayi sai yanke mata harshe, amma a yanzu lafiya lau sai ma tausayi take bani!”
“Allah ya kyauta, amma ba zan yarda da auren yarinya karama tana min tsawa ba” dariya Malik yayi ya ce masa. “Ai na yafe mata, abin da zata min da wanda na sani da wanda ban sani ba, da wnada zata yi gaba na yafe mata baki ɗaya. Bana fatan Allah ya kamata da laifin da ta min, bari na gaya maka wani sirri! Ban sani ba ko lafiyarka tayi rauni ce, amma idan kana son gyara shekarunka da tsufarka, ka auri budurwa wacce kome nata yake tsaye, zaka more rayuwa. Zaka kuma gyara kaifin haddarka faɗin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne, ba fadar Malik Menk Jordan ba!”
Shiru Elbashir yayi, yana sauraron shi. Can ya ce. “Kana ganin na nimo auren Hafsah kenan?” “Idan har zaka iya ka nima mana, ai zaka ji dadinka ne” suna tafe suna hira, har suka isa gidan Sayyada Quddisiya. Da Wahiba ya hadu ta ce mishi. “daga wurin wancan mahaukaciyar ka dawo?” Ya rasa yadda zai yi da ita, domin jin haushin Zeeno take. “Daadi wurinta ka tafi?” “Wahiba me yasa kike haka ne?” “Me yasa ba zan yi ba? She driving Daadi crazy!” Ta fada kamar zata yi kuka. “And ta zubar da dan uwanmu, kin san da Daadi ya gaya min she’s pregnant hatta kawaye sai da na gaya musu, second Mommy she got baby for us! Akan me ba zan tsane ta ba!” Ta faɗa da karfi tana kuka. “I love my siblings tun ban ganshi ba, na.ji ina masifar kaunarshi.” Rungume ta Malik yayi yana shafa bayanta, “Sorry my twins, kukan ya isa haka, kin ji zan tafi Keivroto ku kula da ita, please ban da fushi da rashin kunya she still my wife!” Cikin kuka da ihu ta ce. “Ka sake ta mana! Dole ne sai ka zauna da matar da bata dace da kai ba. Akwai masu sonka mu ma muna sonka.” Zaunar da ita yayi sannan ya ce mata. “A matsayina, mahaifinku dole na nime macen da zata kula da damuwa ta, babu kyau kadaici shi yasa na kawo ku nan, idan kome yayi daidai zan ce ku dawo wurina a Keivroto;”
“Daadi kayi hakuri” murmushi yayi yana rike hannunsu, gani yake kamar Nuratu ce a gabanshi, gani yake kamar yana tare da ita. Rungume su yayi baki daya yana mai da kwallqr da ta cika mishi idanu. “Ban da rigima da faɗa.” Haka yayi ta jansu da hira. Sannan ya bar su, ta tafi wurin Sayyada Quddisiya da take kitchen, ya zauna a kujeran da yake fuskarta ya ce mata. “Anne zan tafi na barku da aiki don Allah a duba lamarinta!” “In sha Allah babu abunda zai kuma faruwa, sai alkhairi.”
Haka suka yi ta hira tana mishi nasiha, sannan ya shiga ya dauki kayanshi suka bar gidan, da kasar baki daya.
A can asibiti su Black, Abbas, Adnan da matarshi sun hadu a can asibitin. Sai can dare suka bar asibitin. Wayarta ce a hannunta, tana chatt da Hafsy sai dariya take mata tunda ta bata labarin cikin da ya zube.
*Ke Yar kunama, yaushe har aka yi abin haka da sauri, sau nawa aka yi da har kwallon ya faɗa raga?*
_Ke dai banza ce, na gaya miki mun yi kusan wata biyu a wani garin ruwa kuma ai a lokacin anyi ya fi sau biyar, tun a hanya na fara rasa isasshen lafiyata._
Dariya ta saka har da emoji. *Da gaske an yi ya fi sau goma kenan?*
_Mahaukaciya! Ba zan gaya mikin ba_
Dariya hafsy ta saka tana gaya mata. *Allah kin bani dariya, wato daga dauke ki sai aka yi abin da Sayyadi yayiwa Nazneen! Daga nan sai labari ya sha banban ko?*
_Ke bana son iskanci wace ce Nazneen da Sayyadi?_
*Banza labarin novel din Addah Ramlat nake gaya miki*
_Allah ya kyauta wallahi na zata wani abun arziki ne_
*Allah abin arziki ne, ke dai da baki karanta hausa novel!*
_Zan rufe data na, tunda na zaki min taaziyar Babyna!_
*Allah ya sa me ceto ne ya baƙi na mora, zan saya miki littafin kina so ko baki so?*
….
______
*Kuyi hakuri da abin da yake, nima ba son raina ba ne. Amma zan kokarta mu tafi yadda ya dace, idan kuma kuna son ayi rushing mu gama shi nan da kwanaki idan zaku iya hakuri labarin yana nan kan domin yanzu muka yi tsakiyar rigimar Zeeno da Malik na gode sosai*
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM]