Hausa NovelsSakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 9

Sponsored Links

 

📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

 

*SAKAYYAH*

_Page 9_

 

NA

*AYSHA ALIYU GARKUWA*

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

*FREE PAGE NE ƴar uwa ki biya ki karanta abinki cikin Salamah, littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Kana in saki a Groups da na buɗe ba SAKAYYAH in da zaki karanta abinki salamun ƙaulum min rabbil rahim. Nama lfy fata lfy. Ba ruwan ki da jiran na sata na Allah ya isa*

 

 

Cikin nitsuwa yake tafiya, tare da taka steps ɗin a hankali, yana  sauƙa ƙasa, yayinda hankalishi baki ɗaya ke bisa system nashi dayake kan hannunsa na dama yana daddanashi da hannun hagunsa, bisa dukkan alamu.

Abu mai mahimmanci ne yakeyi.

 

A dai-dai lokacin kuma Khausar ta iso bakin steps ɗin, cikin sauri take tafiya, da alamun tsoron kada malami ya rigata  shiga aji ne.

Da sauri take tattaka steps ɗin tanayi sama.

Steps biyu ta taka ana uku, taji juyo da kanta da sauri dan jiyo muryar M Jameel na ce mata.

“Khausar sai yanzu?”.

Ba tare da ta tsaya ba, kana bata kuma juyo kanta ba taci gaba da tafiya a haka, hannunta na kan da ƙarfe dake gefen steps ɗin cikin yanayin sakewarta da M Jameel ɗin tace.

“Wallahi tun ɗazu muka iso fa Malam”.

Yana mai binta da ido yace.

“To kuma meya hanaki shiga class?”.

Still bata janye kanta daga kallonsa ba, kana bata tsaya daga haurawa saman da takeyi ba tace.

“Raudat ce ta tsaidani a side ɗin su”.

Da sauri yace.

“Da me ta tsaida ki?”.

Ɗan guntun murmushi tayi tare da cewa.

“Wai ƙwarone ya shiga idonta, shinefa tai ta ihu taƙi sakina dole saida aka cire matashi Allah sai kaga yadda idonta yayi jazir”.

Kanshi ya sunkuyar yana ɗan murza zaɓen azurfan dake yatsar  yace.

“Ayya kwaro bai kyauta ba ya shiga idon Gimbiya Raudat”.

“Ai dai kam fa”.

Ta faɗina tana mai ƙoƙarin juyo kanta.

Cikin tsokana yace.

“Gashi kuwa har Malam Moddibo ya shiga ajinku”.

Cikin sauri ta kuma juyo kanta da dama bata gama juyashi ba cike da kaɗuwa tace.

“Da gaske?”.

Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.

“Tun ɗazuma kuwa”

Cikin yanayin tsoro ta ɗan zaro manyan udanunta tare da cewa.

“Na shiga ukuna”.

Murmushi M Jameel yayi tare da cewa.

“Ato kiyi sauri ki hau, in kinyi sa’a ya barki ki shiga”.

Jin haka yasa ta juyo da sauri tare da taka step ɗin gaba kana tayi kwanan haurawa kam steps ɗin da zai sadata da sama.

Wanda kuma dai-dai lokacin Moddibo ma ya taka step na ƙarshen kwanan.

Unexpected taji tayi karo da mutu.

Shi ma Moddibo ba zato ba tsammani yaji kanta ya bugi ƙirjinsa yayinda hannunta ya bugi System ɗin dake hannunsa ya subce ya tafi ƙasa da sauri ya sunkuyo ya cafe system ɗin da kana ya miƙe tsaye,

 

Ita kuwa Khausar cikin sauri ta ɗago kanta dai dai lokacin kuwa ya ɗago kansa shima ido cikon ido suka kalli juna kamar a fuzge ya furta.

“Again?”. a lokacin guda kuma, cikin tsananin takaici da zafin rai ya ɗaga tafin hannunsa na hagu ya yarfa mata wani irin gigitaccen mari mai masifar zafi gami da raɗaɗi.

 

M Jameel kuwa jin sautin sauƙan marin ne yashi ɗago kansa da sauri.

 

Ita kuwa Khausar wani irin gigitaccen ihu mai cike da rauni tare raɗaɗi ta saki, tare da dafe kuncinta kana ta rumtse idonta wanda duhu mai tarin yawa ya mamaye mata gani, kana tayi taga-taga ta koma baya zata faɗi, jin ta tafi suuuuu ƙafarta ta sule yasa takuma sakin wani ƙaran tare da buɗe idanunta, sai kuma tayi sauri ta medasu ta rufe sabida ganin wasu irin taurarin masu wutsiya da tartsatsi suna gilmawa ganinta sabida zafin marin da yasa suka mamayewa ganinta.

 

Gaba ɗaya ta sadakar domin tasan muddin ta faɗo nan to ita da karaya sun zama aminan juna.

 

M Jameel kuwa kanshi ya riƙe da hannu bibbiyu tare da faɗin.

“Innalillahi!!”.

Wanda faɗin hakane ya jawo hankalin Malam isa da yazo wucewa ta gefensa.

Shima ma Malam isa idonsa ya rumtse da ƙarfi tare da cewa.

“Yah Salam”.

 

Shi kuwa Moddibo cikin takaici yayi sauri miƙa hannunsa da nufin kamo hannunta amman ina tuni tayi nisa.

Sai yatsunta biyu ya samu ya riƙe da masifan ƙarfi.

Wanda saida suka bada sautin ƙas-ƙas.

Cikin zafin nama ya fincikota da ƙarfi wanda hakan yasa ta afka jikinsa.

 

Ita kuwa Khausar jinta a jikin mutum ne yasa tayi masa wani irin sahihin rugguma mai cike da razani dan gani take kamar dai har yanzu bata tsira ba.

Kanta ta cusa cikin ƙirjinsa tana mai shaƙan turarensa mai masifar ƙamshi.

Wanda a take nitsuwarta ta fara dawowa.

 

Shi kuwa Moddibo cikin tsoro da wani irin masifeffen abu da yaji ya soƙi tsakiyar kansa har zuwa cikin ƙahon zuciyarsa kana ya harba masa wasu irin masifaffun baƙin al’amuran a cikin jijiyoyin jikinsa da suka sa jikinsa sakin wani irin masifeffen karkarwa da sabauta aniyarsa, ya ware hannunsa tare da rumtse idanunsa da masifan ƙarfi.

 

M Jameel kuwa ajiyan zuciya mai ƙarfi ya sake tare da jingina bayansa da jikin ƙarfen.

a hankali ya kuma sakin numfashi tare da kallon yadda Moddibo ya buɗa hannayensa duka biyu kana ita kuma Khausar tana kwance bisa ƙirjinsa tayi lip tana ruggume dashi da masifan ƙarfi.

 

Wani irin shu’umin dariya mai sauti M Jameel ya sake.

Wanda hakan yasa Moddibo buɗe idanunsa kana dai-dai lokacin yaji gaba ɗaya tsikar jikinsa na tashi.

 

Malam isa kuwa sunkuyar da kansa yayi yana murmushi.

 

M Jameel kuwa dariya yake tare da nuna Modibbo da Khausar ɗin wacce tuni fuskarta tayi jazir shatin yatsun hannunsa sunyi ruɗu-ruɗu a farar fatarta.

Cikin sauri Moddibo ya ɓalle hannunta daga jikinsa tare da matsawa gefe da sauri.

Wani irin tsuke fuskarsa yayi tare da watsa mata kallon da yasa hantar cikinta kaɗawa.

Wanda cikin rawan jiki da rawan murya cike da rauni tace.

“Ana Aspet ya Mu’allim Allah mi larai ma on! Please! Kayi haƙuri”.

Ta ƙare mgnar cikin tsoro tare da gwamusa yaruka hudu duk a wuri ɗaya dan neman afuwa.

Shi kuwa Moddibo juyawa yayi tare da ratsa gefenta ya wuce kana cikin wata fusatacciyar murya mai matuƙar firgitarwa yace.

“Biyoni!”.

Cikin ɓarin jiki tace.

“Toh”.

Sannan ta miƙe tabi bayansa.

 

M Jameel dake riƙe da System ɗin yana juyawa yayi saurin bin bayansa da faɗin.

“Alhamdulillah kamar babu abinda ya samu System ɗin”.

Shi dai Moddibo ko juyawa baiyi ba bare kuma ya tankawa M Jameel.

 

Malam Isa kuwa dake ƙasa ido ya zirawa Khausar dake sauƙwa dafe kuncinta da kunne ya da tun da tasha marin ya bada sautin kauwww har yanzu ƙaran takeji, kana ga idanunta da suka kaɗa sukayi jawur asanda ta saƙƙo yace.

Fattanah sam bakya yin abinda ya dace a rayuwarki”.

 

Cikin zafin raɗaɗin marin da fuskarta keyi ta ɗago Idanunta da suke sake girma da ja ta kalli Malam Isa sai kuma tace.

“Wallahi bansa niba ne na juya ina kallon Malam Jameel ne dake yimin magana ne mukayi karo”.

Bata jira jin abinda zai ce ba tabi bayan M Jameel dake biye da Moddibo.

 

Cak Khausar ta tsaya daga bakin Office ɗin, karo na farko kenan arayuwarta da zata fara shiga Office ɗinsa, duk da cewa da basu da office da yawa, amma yanzu gyaran da akayi an haɗa Malamai biyu akan Office  ɗaya Office din ba wasu masu girma bane, haka zalika ba ƙanana bane, sannan duk kusan ajere suke.

Ahankali Khausar ta maida Idanunta bakin office ɗin da akasa wasu irin flowes masu launi mai kyau da ɗaukar hankali aka jera suna fitar da wani irin sanyayyan ƙamshi.

Cikin Office ɗin kuwa Madaidaitan deks ne da kujeru ɗaya na fuskantar gabar ɗaya na fuskantar yamma daga gaban ko wanne kuma akwai kujeru guda biyu daga kan deks ɗin daga gefen damar sa akwai wani Cubet kamar kanta dake ɗauke da tarin littattafai na addini da kuma na boko cikin wajen kamar dai Library haka wurin yake.

Daga gefen hagunsa kuma flowes ne masu  kyau da tsari daga jikin bangon kuma Room hitane ne maƙale abango yana fitar da ɗumi mai daɗi a jiki,

Sai kuma labulayen window da suka kasance farare sol Sanyayyan iska na kaɗawa daga bangon kudu dake kallon yamma TV ne maƙale abango daga tsakiya kuwa wani irin dakekken turkey carpet mai yawan gashi fari sai ratsin maroon kaɗan. sosai Office ɗin yayi kyau.

 

Shi kuwa Moddibo cikin nutsuwa da kuma zafin da zuciyarsa keyi masa ya zauna akan kujeran dake gabar yana fuskantar yamma yayin da M Jameel ya zauna akan kujeran dake yamma yana fuskantar gabar kana da sunan ko wannensu ajiki kujerarsa.

 

Ita kuwa khausar cikin tsananin tsoro ta ƙarasa shiga office ɗin tare da tsugunnawa agaban table ɗin da Moddibo ke zaune.

Ta riƙe kunnenta Muryanta Araunane wanda ke nuni da tsantsar tsoro da tashin hankali tace.

“Malam kayi haƙuri bansan kana tahowa ba”.

Shi kuwa Moddibo ko kallonta baiyi ba saboda yanda zuciyarsa ke tsananin ta farfasa ya tabbata idan yace zai daketa to zai iya karyata ko kuma ya sumar da ita hakan yasa ya janyo kujeran dake kusa dashi ya ɗaura ƙafafunsa akai kana ya lumshe idanunsa tare dasa hannu ya janyo Hiramin dake kansa ya rufe saman Idanunsa.

 

Cikin tsantsar nutsuwa da kuma sanyayyan sautin muryarsa mai zaƙi ya fara rara Ƙira’a acikin suratul Rahman yasan hakan shine kaɗai zai sanyaya masa ransa da zuciyarsa yasan muddin yace zai daketa ayanzu zai iya sumar da ita ko kuma karyata.

Saboda abubuwan da yarinyar ke masa yayi yawa.

Sabida tsabar raini da rashin kunya fa har gidansu ta bisa tayi masa rashin kunya sannan ta jima sa ciwo ayatsun ƙafansa wanda ya ɗauki tsawon kwanaki yana fama da ciwo.

Kana  yaje ƙauyen su nan ma bata barshi ba saida ta bisa tayi masa rashin kunya ta nemi jefa shi acikin ruwa da wannan masifeffen sanyin garin nasu,

kana amakaranta ma bata barsa ba shin tsaranta ta mayar dashi kome?.

 

Ita kuwa khausar cikin Sanyayyar Muryanta me cike da tsoro tace.

“Ayyah malam na tuba kayi haƙuri wallahi bansani bane”.

Ƙin tanka mata Moddibo yayi ya cigaba da rera karatunsa cikin zazzaƙan muryansa.

Shi kuwa M Jameel Gyaran murya yayi hakan yasa Khausar tayi saurin Kallonsa da manyan Idanunta da suka kaɗa sukayi jawur.

Da ido yanuna mata Moddibo alamar ta cigaba da basa haƙuri.

Kai ta gyaɗa sannan ta cigaba da cewa.

“Ayyah Malam na roƙeka kayi haƙuri bazan sake ba”.

 

Acan sama ajinsu Khausar kuwa wani irin tsarin gini ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali wasu irin windon Glass ne tsala-tsala masu tsayi da kyan tsari sannan ga flowes masu fitar da sanyayyan ƙamshi kana ga Room hita  guda biyu gaba da baya daga farkon shiga class ɗin kuwa wani irin Black Board ne mai tsari irin wanda ake amfani dasu a manyan makarantu, kana ga wasu irin kujeru na zaman ɗalibai masu taushi da kyau, agaban ko wani kujeran ɗalibi akwai sunan sa ajiki, hakan yasa duk ɗalibar data shiga baza tasha wahala neman wajen zamanta ba wanda kuma manna sunan ake bisa alamu in an tashi kawai ɓarewa za’ayi a saka sunayen sabbin waɗanda zasu shigo ajin, kujeran Khausar shine na farko acikin jerin kujerun dake gaba da sunanta manne kamar haka _Khausar Usman Abubukar Lelewal._

Samira Sani ce ta ɗan juya Idanunta kan kujerar dake gefenta.

Wanda sunan Khausar dake manne kujerar afarkon.

 

Wani irin ya mutsa fuska tayi tamkar wacce taga wani abin ƙi cikin taɓe baki da tsanar mamallakiyar sunan tace.

“Ikon Allah wannan shine suna mai buƙatar hadda sunaye huɗu duk masu tsawo!”.

Ta Ida maganar tare da bankawa kujeran harara tamkar Khausar ɗin na kai, kana ta zauna daga baya inda sunan ta ke kai.

 

Asma’u dake gefe azaune tace.

“Ha’a sunane de ai ba wani abu ba kuma duk sunayene masu inganci da Kekkyawar nasaba naga dai sunanta sunane na ɗiya ga Annabi  Muhammad (S.A.W) sannan sunan mahaifinta sune na sahabin Manzon Allah (S.A.W) haka zalika sunan kakanta sune na sahabin Manzon Allah (S.A.W).

Lelewal kuwa naga suna ne da kowa ke fatansa”.

 

Abeeda Sule ne ta watsa wa Asma’u harara tare da faɗin.

“Ke kuma wayasa bakin ki?”.

Taɓe baki Asma’u tayi kana tace.

“Ai gaskiyane daga kallon sunan baiwar Allah zata fara ƙanan magana”.

Ɗaya daga cikinsu manyan matan ajin nasu ne wacce bata fiye magana Hajia Khadija tace.

“Da wannan hatsaniyar da kukeyi tunda Moddibo ya fita tun ɗazu akan zaije ya dawo bai dawo ba aigwara kuje ku duba ko lafiya mai ya tsaida shi aji ba kowa kuma shine muke da First period?”.

 

Cikin zumuɗi Samira Sani tace.

“Gaskiya ne kam bari naje na kirasa”.

ta ida maganar tare da ficewa ta sauƙa ƙasa.

Cikin yauƙi ta nufi Office

 

Tana isa idanunta suka sauƙa akan Khausar dake riƙe da kunnenta, ga kuma Idanunta da suka sauya,

yayin da shi kuwa Moddibo idanunsa ke lumshe yana rera karatun Alkur’ani cikin Sanyayyar sautin muryansa daya haɗu da ɗumin room hita ga ƙamshin daddaɗan tularensa.

Numfashi mai nauyi ta fesar  tare da tsirawa yalwataccen sajensa daya ƙawata kyawun fuskarsa idanu sai kuma ta maida kallonta kan zara-zaran yatsun hannunsa dake kan table yana ɗan bubbugasu ahankali cike da shauƙi tace.

“Wowww”.Faɗar hakan da tayi shi ya janyo hankalin M Jameel yayi saurin juyawa ganinta tsaye acikin Office din yasa shi faɗin.

“Lafiya?”.

 

Sai asannan ta dawo cikin nutsuwarta still Idanunta na kan Moddibo tace.

“Malam Barka da safiya”.

 

“Barka dai”.

 

Still idanunta na akan Moddibo tace.

“Malam dama munzo kiran Malam Moddibo ne, shine muke dashi tun ɗazu ya sauƙa, akan cewa zai zo ya ɗauki wani abu sannan kuma bai koma ba”.

 

Da ido M Jameel ya nuna mata Moddibo da har zuwa lokacin idanunsa ke lumshe yana karatu sai dai ya rage sautin muryansa ya koma fita asaman laɓɓansa.

 

Shi kuwa Moddibo jin Muryanta yasa ya janye Hiramin dake fuskarsa kana ya buɗe idanunsa da har zuwa yanzu akwai alamun ɓacin rai acikinsu, kallo ɗaya ya mata ya kawar da kansa gefe.

Ita kuwa Samira gefe ta koma ta tsaya.

Khausar kuwa lumshe Idanunta da suka kaɗa sukayi jawur tayi sai kuma ta buɗe su still Hannunta nakan kunnenta tace.

“Ayyah Malam kayi haƙuri”.

Shi kuwa Moddibo juyawa yayi tare da kallon M Jameel yace.

“J ka da keta”.

Da sauri M Jameel ya juya tare da nuna kansa da babban yatsa kana yace.

“Ni!?”.

 

Cike da tsuke fuska Moddibo ya gyaɗa masa kai kana yace.

“Eh ka daketa!”.

Zare Ido M Jameel yayi tare da cewa

“Meyesa?”.

A kufule Moddibo yace.

“J kadaketa nace!”.

Kallon mamaki M Jameel yake masa tare da cewa.

“Akan me zan daketa?”.

Cike da ɓacin rai Moddibo yace.

“Idan fa ka bari nace ni zan daketa zan sumar da ita fa!, zan karyata fa!!”.

Cikin tsananin fusata ya ida maganar.

 

Ita kuwa Khausar tuni jikinta ya hau rawa Allah ya sani bata son duka, sannan mari ɗaya daya mata ya mugun gigita mata ƙwaƙwalwa wanda har zuwa yanzu take jin raɗaɗin sa asaman fuskarta.

 

Fuskarsa babu walwala yace.

“Idan har nace zan daketa zan sumar da ita”.

Ita kuwa Khausar jin azaban mari ɗaya daya mata, aranta tace Ashe Allah ya rufa min asiri da yasa duk lokacin da nayiwa Moddibo laifi baya duka na yake sa Malam Adam display master ke dukana na tabbata dashi yake dukana kullum da tuni ya kasheni!.

 

Cikin hanzari ta juya tare da kallon M Jameel ta miƙa masa hannu Muryanta na rawa tace.

“Malam ka dakeni!”.

Girgiza kai M Jameel yayi cikin sanyin murya yace.

“Ni dai kam bazan iya ba bazan iya dukanta ba Moddibo, ka dubi fuskarta fa mari ɗaya da ka mata kalli fuskarta fa ai ya wadatar wani hukunci ya rage bayan wannan?”.

Ya kare mgnar a hankali

Moddibo kuwa cikin fushi yace.

“Kada keta in kuma baza ka daketa ba zan daketa da kaina fa”.

Cikin sauri M Jameel ya fara girgiza kai  yayi cikin wata Sanyayyar murya me cike da zallar jin ƙai tare da tarin tausayi gami da rauni yace.

“La! La!! La!!! A.J  bazan iya ba! Wlh Bazan iyaba ba wannan ba hurumina bane hurumin taɓa ta awajenka yake bani da karsashi ko ƙwarin gwiwar da zan iya taɓa ta!”.

Ya ida maganar cikin wani irin salo na daban, kana dai-dai lokacin  Amina tazo Office ɗin domin kiran M Jameel ya shiga ajinsu wani irin sarawa kanta yayi jin yanda yake cewa bazai iya ba.

Da sauri ta dafe ƙofar office ɗin jin jiri na ɗibarta kadde ace dokon soyayyarsa za tayi abanza, kadde Khausar yake so yanda ya ƙarashe maganar na nuni tamkar itace rayuwar sa.

 

Da sauri Moddibo ya juya ya kalli M Jameel jin yanda yayi magana da kuma yanda ya lanƙwasa harshensa abun ya bashi mamaki.

Azuciye Moddibo yace.

“In daketa kenan?”.

 

Langwaɓar da kai M Jameel yayi cikin sanyin murya yace.

“Kayi haƙuri ina mai bada haƙuri amada dinta ka nemi wani punishment ɗin ka bata amadadin wannan, amma nikam bazan iya dukan taba sannan kaima banaso ka daketa!”.

Baki ɗayan su kallon Mamaki suka bi M Jameel dashi ganin yanda yake lanƙwasar da murya tare da nemawa Khausar ya fiya, ita kuwa Amina wasu hawaye ne masu zafin gaske ne na tsananin kishi da baƙin ciki, suka zubo mata  saurin ta sanya hannu ta share.

Kwantar da Murya M Jameel ya kuma sakeyi ya cigaba da cewa.

“Kallifa A.J mari ɗayan nan da kamata kalli fuskarta fa ka daketa awaje mafi daraja”.

 

Moddibo kuwa  lumshe idanunsa yayi kana ya buɗesu akan M Jameel tare da cewa.

“J kadaketa ni idan nace zan daketa bazai mata daɗi bafa”.

Sake Langwaɓar da kai M Jameel yayi kana yace.

“Kayi haƙuri Moddibo ni bazan iya dukanta ba!”.

 

Ita kuwa Samari Sani na tsaye agefe ta harɗe hannayenta aƙirji yayin da ta zubawa Moddibo ƙananun Idanunta ko ƙyaftawa ba tayi.

Ita kuwa Amina Idanun ta nakan M Jameel da idanunsa ke kan Khausar zuciyarta nayi mata zafi.

 

Khausar kuwa kallon M Jameel ta sakeyi akaro na barkatai tace.

“Malam Jameel ni dai ka dakeni”.

Kai ya girgiza mata tare da faɗin.

“Bazan iya dukan ki ba Khausar!”.

 

Shi kuwa Moddibo cikin tsananin ɓacin rai ya juya ya kalleta a kufule yace.

“Toh inda keta da kaina!?”.

Girgiza kai M Jameel yayi sai kuma yace.

“A’a asassauta mana dan Allah”.

Ƙwafa Moddibo yayi da faɗin.

“Shikenan kije ki kaɗe ɗan kwali sau ashirin”.

 

Cike da tsoro ta zaro ido domin kaɗe ɗan kwallon da yace  yana nufin ta cire ɗan kwalinta tasa abokitin ruwa ta matse kana ta kaɗe har sai ya bushe,

sannan ta sake sakawa cikin ruwa ta matse kana tayi ta kadewa har sai ya bushe.

Tofa jin haka ne yasa a tsorace ta zare Ido Jin hukuncin daya yanke mata ba zata manta lokacin daya sata kaɗewa sau goma ba awannan lokacin ma saida tayi sati biyu gaɓɓanta na ciwo ko abu zata ɗauka da ƙyar take iyawa.

 

Cikin yanayin neman alfarma M Jameel ya sake langwaɓar da kai kana yace.

“Dan Allah ka sassauta mata karage mata”.

Jin Muryan M Jameel yasa ita ma ta kalli Moddibo cikin wata raunatacciyar murya tace.

“Dan girman Allah Malam kayi haƙuri karage min”.

 

Shi kuwa Moddibo wani kallo ya watsa mata cikin haɗe girar sama dana ƙasa yace.

“Kada ki sake haɗa ni da girman Allah da kinsan darajar girman Allah da zaki mutunta Malama ki,

kije kiyi shabiyar kinci darajar girman Allah.

idan kika sake cemin dan Allah in rage miki kuwa nida ke bibbiyu!”.

Gyaɗa kai tayi kana tace.

“Toh shikenan”.

Shi kuwa M Jameel kallon Moddibo yayi cikin jujjuya  ido  yace.

“Ina neman alfarma abarta tashiga aji tayi karatu idan antashi Break sai tayi”.

 

Shi kuwa Moddibo Ɓata fuska yayi yace.

“Bana son ganinta a aji Idan naganta a aji zan kakkaryata in wurgar ta window”.

Ita kuwa Samira Sani cikin lanƙawasa harshe tace.

“Malam Moddibo mu tafi”.

Sake tamke fuska yayi tare da juyawa ya watsa mata wani bayyane  harara sai kuma ya nuna mata ƙofa alamar ta ɓace masa da gani.

 

Sum sum ta  juya da sauri  ta fice.

Da harara yabi bayanta Aransa yace.

Shegiyar yarinya mai kama da Mayya,

sai shegen kallon jaraba tasani gaba zakiyi dan rashin kunya.

 

Samira Sani kuwa tana shiga ajinsu ta lumshe Idanunta tare da kallon gefen ko wannen kujera dake ɗauke da flowes ta saki murmushi mai cike da jin daɗi,

tasan wannan aikin Moddibo ne domin kaf cikin Malaman shike son flowers.

Hajia Ruƙayya ce ta dubi Samira data shigo kana tace.

“Ni kam ya banga Khausar ta shigo ba har yanzu kuma ɗazu na hangota kafin na haura”.

Juye Ido Samira tayi tare da faɗin.

“Tana can tayiwa Moddibo rashin kunya yana cin Ubanta, shegiyar yarinya fitsararriya ‘yar marasa tarbiyya!”.

 

Asma’u ce ta juya ta kalleta rai a haɗe tace.

“Haba Samira meyesa zaki zagi iyayenta ai bai kamata ki zagi iyayenta komai yaya iyaye nada daraja”.

Harara Samira ta wurga was Asma’u kana ta buɗe baki da niyyar magana ta fasa sakamakon shigowar Moddibo.

 

Ganin shigowar Moddibo yasa ta tsuke bakinta tare da neman waje ta zauna cike.

Cike da ladabi suka gaishesa cikin harshen larabci tare da faɗin.

”صبحل خير ىاعثتذ“

Ya Amsa da.

“صبحل نور كىفل قراء“.

Suka amsa da.

”الحمد الله“

Kasancewar Tafseer zasuyi dake yanzu lokacin Islamiyya ne yasa yace.

“Kuyi muraja”.

Cikin bawa ko wanne harafi hukuncinsa suka shiga karanta suratul Muhammad har zuwa karshe.

Bayan sun gama kawo haddan ya jinjina kai tare da faɗin.

“Sai gobe Insha Allah zamu fara tafsirin sa”.

 

Aɓangaren M Jameel kuwa tare suka jera da Amina suka nufi ajinsu yayin da azuciyar Amina yayi baƙiƙƙirin data tuna yanda M Jameel ke karyar da murya akan Khausar har suka isa ajin tunanin da take aranta kenan yanayin yanda tsarin ajinsu Khausar yake haka ko wanne aji yake cike da ƙwarewa M Jameel ya shiga yi musu ƙarin Mi’atu Hadith daga na Arba’in bayan sun karanta masa.

Ko wanne aji da Malami aciki suna darasi.

 

Ita kuwa Khausar ita kaɗai ce tsaye aharabar Makarantar cikin gajiyawa ta ɗaga boket ɗin ruwan ta koma rana wai ko zata samu yafi bushewa da wuri, tsoma ɗan kwalin tayi aciki kana ta matse sannan ta fara kaɗewa.

Nannauyan ajiyar zuciya ta saki tun akaɗewa na uku taji hannunta ya sage aranta tace.

“Insha Allah Ina komawa gida zan nemi ɗankwali mai shara-shara mara nauyi wanda kodan irin rana ta yau ta faru zaimin sauƙi.

Cike da gajiya ta miƙe  ta riƙe ƙugunta da hannu ɗaya ta lumshe idanunta sosai ta gaji.

 

Shi kuwa Moddibo daga can sama acikin ajinsu Khausar yake kallonta tana kaɗe-kaɗen ganin ta tsaye ta riƙe ƙugu gaban ƙirjinta duk ya jiƙe da fuskanta, ganin ta tsayanne yasa ya buɗe glass ɗin window dake saitin ta tare da ziro hannunsa ya ƙyasta yatsunsa da ƙarfi wanda hakab yaja hankalin Khausar da saurin ta ɗaga kanta.

Ganin abinda yayi yasa da sauri ta cigaba da kaɗewa tana mai rintse Idanunta.

 

Har Moddibo ya gama teaching ɗinsa ya fita Khausar nakan punishment Koda ya saƙƙo ya ganta Harara ya watsa mata kana a kufule yace.

“Ba zaki shiga ajiba yau har sai kin gama abinda nasaki”.

Fuska ta Shagwaɓe  tare da langwaɓar da kai tace.

“Ayyah Malam dan Allah kayafemin duk ɗan Adam ajizine!”.

Harara ya watsa mata ya wuce batare daya bata amsa ba,

bayansa tabi da kallo tana tura ƙaramin bakinta, to har wani malami ya sake shiga yayi darasi Khausar bata gama ba sai sha biyu dai-dai lokacin tashin matan Aure sannan Yara da ‘Yan mata suyi suci abinci su koma ajin boko.

 

Hajiya Ruƙayya ce da Aunty Khadija ne suka  fito tare da ƙarasawa kusa da Khausar dai-dai lokacin da Khausar ke faɗin.

“Wayyo hannuna”.

Ta faɗa tana matsa yatsunta dake raɗaɗi.

 

Dafata Hajiya Ruƙayya tayi kana tace.

“Ayyah sannu Khausar kece bakyaji me kika yiwa Moddibo!?”.

Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da marairaice murya tace.

“Allah babu abinda na masa kawai ina tahowa ne mukayi karo dashi har System ɗinsa ya faɗi kuma ma naji malam Jameel yace System ɗin beyi komai ba amma sai da ya sani wannan kaɗe-kaɗen sabida in baici zalina ba baya jin daɗi rayuwarsa ta duniya”.

Ta ida maganar da faɗin.

“Affan zo”,tare da miƙa masa hannu.

Murmushi Aunty Khadija tana mai jujjuya kai.

Ita kuwa Hajia  Rukayya

Miƙa mata yaron dake ta faman ƙyalƙyala mata Dariya Aunty Ruƙayya tayi Sai kuma tayi saurin janye hannunta tana cewa.

“Wayyo Aunty Ruƙayya hannu na ya gaji yaukam bazan iya riƙe sa ba”.

Ta ƙare mgnar tana ƙara matsowa  kusa da Aunty Ruƙayya kan kumatunsa ta sumbata tana faɗin.

“Affan gaye”.

Shi kuwa yaron sai dariya yake ƙyalƙyala mata tare da miƙa mata hannu alamar yana so ta ɗauke sa dan sosai yaron ya saba da ita saboda Aunty Ruƙayya na zumunci da Mommy Khausar sannan Khausar na shiga lokaci zuwa lokaci.

 

Samira Sani da Abeeda Sule ne suka ƙaraso wajen Kallon Abeeda Sule Samira tayi da faɗin.

“Ai Moddibo shike maganin tantirai marasa mutunci ’ya’yan Fitsararru awannan makarantar yana min dai-dai!”.

 

Sake hannun Affan Khausar tayi ta juya ta kalli Samira da kyau tace.

“Waye ‘Yar marasa mutuncin?

Akwai ‘Yar marasa mutunci daya wucike ne ‘Yar magulmata Munafuka kawai! Inbanda munafurci da gulma da biye-biyen bokaye Me kuka iya!?”.

Afusace tace.

“Ke Khausar zanci Ubanki fa!”.

Wara ido Khausar tayi kana tace.

“Ubana kuma, uhmm saide Kici naki uban domin ni kam nawa Ubana tuni Ubangiji ya daɗe da yimasa sutura sai dai kije kici naki ‘Yar matsiyata?”.

Ta ida mgnar cikin tsiwa,.

 

Abeeda Sule ne tace.

“Ke akwai ma ƴar matsiyata irinki, kina tsammanin bamu san cewa munsan ke Agwola bace acikin gidan sarki da kike nunawa kamar gidan ku ne?”.

 

Dariya Khausar tayi kana tace.

“Dan Allah rufe mana baki ‘Yar Alhaji sule baka layya kibari tukunna in Babanki ya fara layya saiki faɗa wa mutane Magana?”.

 

Zare ido Abeeda tayi tare da hayayya ƙowa tace.

“ ‘Yar iska ni zaki cewa Ubana baya layya”.

Taɓe baki Khausar tayi tare da faɗin.

“Ke rufe min baki ai bani na faɗa ba Inkiyarsa ce hakan, ko ba sunan sa bane? Alhaji Sule baka layya!! ko kuma ni nasa masa ko kuma dan tsoronki sai inki kiransa da sunan da aka sa mishi”.

 

Hajiya Ruƙayya ce tace.

“Khausar rabu dasu”.

Gyaɗa kai tayi.

Ita kuwa Samira cikin takaici tace.

“ ‘Yar banza kawai agola”.

Dariyar rainin hankalin Khausar tayi sannan tace.

“Eh koma menene inma ni Agolace inada daraja sannan ina da tushe dama ni ban ɓoyewa cewa Agola bace Ni saboda idan kinga sunan su Amina da sunana kin san ba yar gidan bane,

Ni sunana Khausar Usman Abubukar Lelewal sukuwa kinga ba haka sunan su yake ba daga nan ma mutum yasan Ni Agola ce ko dama anɓoye miki ne?”.

 

Hannunta Hajiya Ruƙayya taja suka bar wajen zuwa gefe tace.

“Khausar kifita har ƙansu  kiyi abinda ke gabanki kinga duk yau baki samu karatu ba”.

Kai Khausar ta gyaɗa mata sannan tayi mata Sallama ta tafi.

Asma’u ce ta ƙaraso wajen Idanunta akan Samira da Abeeda dake zagin Khausar cikin yanayin sanyin muryanta tace.

“Khausar kifita sabgar wa’annan yaran dan Allah keda su ba ɗaya bane kada ki ringa biye musu muta nen da ƙwaƙwalensu basa ja, kinga fa yanzu da ya kamata suna SS 3 nefa daƙiƙancinsa kesa kullum basa gaba sunan a jaɓe har muka isosu”.

Yamutse fuska Khausar tayi kana tana matsa yatsun hannunta tace.

“Kinsan Allah Asma’u Indai basu fita sabgata ba zan basu mamaki zan nuna musu Khausar Usman Abubakar Lelewal ba kanwar lasa bace”.

 

Hannunta Asma’u ta riƙe tace.

“Ni dai dan Allah ki fita sangarsu ai ko kare bai haushi shi kaɗai tukunna wai me kika yiwa Moddibo ya saki Punishment?”.

 

Rau-rau da ido Khausar tayi sai kuma ta ya mutse fuska tare da jan tsaki kana tace.

“Mutum yana nan kamar wani sabon boss sam fuskarsa babu fara’a yana nan sai baƙin mugunta.

Kuma wallahi Wuta bal-bal ban yafe masa ba, ai bani kaɗai nayi kuskuren ba shima yayi yana tafiya kamar makaho, kuma yaseen saƙo na baki ki faɗa masa ehe”.

Ta ida mgnar cike da tsiwa da murguɗa baki

Asma’u kuwa  dariyar  dake cinta ta danne kana tace.

“Aikuwa gashi nan abayanki yana ma jinki ba sai na faɗa masa ba”.

Arazane Khausar ta saki ihu  tare da rintse Idanunta cikin tsananin tsoro da rawan jiki ta juya tana mai faɗin.

“Dan Allah! Dan Allah!! Dan Allah!!! kayi haƙuri Allah bada kai nake ba kuskuren harshene ni da kainama nakeyi”,

Ta ida maganar tana buɗe Idanunta jin be tanka taba ga mamakinta bata gansa ba.

Kallon Asma’u tayi wacce zuwa lokacin ta saki dariyar ta tace.

“Fattanah sarkin tsiwa dama gwada ki nayi inga da gaske saƙon kika bani”.

 

Harara Khausar ta zabga wa Asma’u amma batace Komai ba.

Murmushi Asma’u tayi tare da jan hannunta zuwa resting chair dake cikin harabar makarantar suka zauna Asma’u ta fito da kula da ɗauke da pride rice da yaji kayan hadi da namar kaza suka ci.

Bayan sun gama cin wannan Khausar ta buɗe bata kukan.

Peper checking ne guzurin zabbin data dawo dasu.

Sunaci suna ɗan hirarsu dai har suka gama,  suka mike tare da zagaya classes din makarantar suna kallon yanda aka tsara makarantar kamar ba shiba.

12:10  suka koma aji.

Bayan komawar su Malam Isa dake ɗaukar su Economist ya shiga ya koyar musu sosai Khausar da Asma’u ke fahimtar karatun 1:15 dai-dai suka fita sallah.

 

Bayan sun fita Al’wala sukaje wajen da aka tanada dan alwala sukayi gefen maza da ban na mata da ban Amma masallacin guda daya ne saidai anraba daga tsakiya anyi katanga mata zasu shiga ta gefen dama maza tagefen hagu.

Bayan sun idar da Sallah ƙarfe 1:30 suka koma aji wasu Malaman suka sake shiga.

Sosai Malaman suka dage wajen koyar dasu domin anƙara musu Salarie sannan ankawo sabbin Malamai hakan yasa babu period din dake wucewa ba tare da anshiga ba  5:00 dai-dai suka tashi motar su Khausar tazo ta ɗauke su.

 

Washe gari.

Ma haka suka gudanar da karatunsu kamar na jiya.

Acikin satin karatu suke gadan gadan babu kama ƙafar yaro saboda suna son dai-dai-ta komai na lokacin daya wuce ahutu koda wasa Khausar bata sake yin ganganci wani abu ya haɗa ta da Moddibo ba bare tayi masa laifi da zaran ya shiga ajinsu zata tattara duk kan nutsuwarta akansa tana sauraron abinda yake koyar musu kuma sosai take fahimta yayin da ita kuma Samira Sani zata tsaya aikin Kallonsa aduk sanda ya shiga musu shikuwa Moddibo duk yana lura da yanayin ko wannensu.

 

Yau Alhamis ya kasance babu makaranta suna hutu.

Khausar ce zaune a falon Mommy ta tana duba Mi’atu Hadith,Mommy dake Bedroom ta ƙwala mata kira Amsawa tayi tare da ajiye Hadith ta fita.

Bakinta ɗauke da Sallama tashiga Bedroom din Kallonta Mommy tayi tace.

“Khausar ɗibi wannan kayan ki kaiwa Hajiya Bunayya kala ɗaya nasiya mana”.

Kallon mamaki Khausar ta yiwa Mommy anma wannan basabon abu bane ko yaushe Mommy na zaune zuciya ɗaya da ita tana kyautata mata, amma ita Hajiya Bunayya ba da zuciya ɗaya take zaune dasu ba.

Gyaran Murya Mommy tayi tace.

“Khausar tunanin me kike?”

Murmushi Khausar tayi tare da ɗiban kayan tace.

“Toh”,Mommy sannan ta fice.

 

Bakinta ɗauke da Sallama ta shiga falon Hajiya Bunayya kana ta nemi waje ta zauna aɗaya daga cikin kujerun dake falon tace.

“Ummah gashi Mommy na ta siya musu iri daya”.

Washe baki Hajiya Bunayya tayi tare da kallon turamen Zannuwa da tsadaddun less ɗin tace.

“Aaaa lalle kam Khausar Nagode Allah yayiwa ƙanwata al’barka muje inyi mata godiya”.

Kai Khausar ta gyaɗa tare da miƙewa dai-dai lokacin Hajiya Lami mahaifiyar Samira Sani tayi sallama suka shigo atare.

Kallon Khausar Hajiya tayi tace.

“Khausar jeki nayi baƙi kice mata Nagode zan shigo anjima”.

 

Kai Khausar ta gyaɗa tare da ficewa yayin da Samira ta bita da mugun kallo.

Kallon Hajiya Lami Hajiya Bunayya tayi kana ta mika mata hannu suka tafa Dariyar ƙeta Hajiya Bunayya tayi tace.

“Kalli Sokuwarki wai kaya ta saya mana iri ɗaya”.

 

Dariya Hajiya Lami ta fashe dashi tare da cewa

“Aaaa Ikon Allah sokuwa ta ƙarshen zamani kuwa wato hadda siya muku anko”.

Tsaki Hajiya Bunayya tayi tace.

“Bar ‘yar banza mai kama da ‘ya‘yan mayu tazo ta liƙewa mijina”.

 

Hajiya Lami tace.

“Aikam wa’annan mutanen sai Allah aike kika sake kika basu dama, kika bar mijinki ya ƙara aure ni yanzu Baban Samira ya isa yace zai ƙara aure ne, sannan bayan kin bari yayi auren ma kika barta tahaifi santalelen yaro me jikin girma bayan shi hadda ‘yan biyu da kawunansu kamar ‘Ya‘yan ruwa ga shegen gashi kamar ‘ya‘yan Aljanu”.

 

Ƙwafa Hajiya Bunayya tayi kana tace.

“Ai wallahi nayi sake amma daga ‘yan tagwayen babu ita ba sake haihuwa ina lura da ita kwannan kamar cikine da ita to bazan bari ta haife sa ba zanje wajen boka Kar’uzu azubar dama duk cikin ta uku kafin ’yan biyu ni nake sawa azubar  shegiya ai bazan barta ba kenan yanzu ma inada  niyya zanje wajenki jibi muje wajen Malami”.

 

Gyara zama Hajiya Lami tayi tare  da faɗin.

“Aini ma abinda ya kawoni kenan Hajiya Bunayya in sanar miki”.

Kallonta Hajiya Bunayya tayi tace.

“Toh Meye faru?”.

Ajiyar zuciya Hajiya Lami ta sauƙe tace.

“Akwai wani Malami ne amakarantar su Samira take sonshi”.

Cikin don jin ƙarshen zancen Hajiya Bunayya tace.

“Toh wani Malami?”.

 

“Wai shi malam Moddibo tana masifar sonshi shi kuma yana nan kamar Waliyi ko ta kanta bayayi”.

 

“Ikon Allah”.

Cewar Hajia Bunayya

 

“Toh fa shine nake son zamu kai sunansa wajen Malami ya jawo mana hankalinsa da tunaninsa”.

Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi kana tace.

“Eh hakan ma yayi shine dai-dai, gwara ajashi ya dawo yana binta, nima dama abinda zai kaini kenan harda batun Amina itama wani Malamin su take so”.

 

Cikin mamaki Hajia Kamu tace.

“Ita kuma wani Malamin take so?”.

Da sauri Hajiya Bunayya tace.

“Eh wani Malami take so wai shi M Jameel shi kuma baki ɗaya hankalinsa nakan wannan ‘yar matsiyatan!”.

 

Cikin zato ido Hajiya Lami tace.

“Wa kenan?”.

 

“Khausar mana”.

 

Hajiya Lami kam baki ta saki  tare da riƙe haɓa kana ta saki salati tace.

“Ikon Allah Uwarta ta hanaki rawan gaban hantsi, sannan itama Khausar tun yanzu zata hana ‘yarki rawan gaban hantsi, ta hana ta samun abinda take so, to ko lallai kinada aiki ja a gabanki

Yakamata muyi aggawan zuwa mu ɗauki mataki dan bata isa ba amma shi Jameel din ɗan gidan waye!?”.

 

Murmushi Hajiya Bunayya tayi kana tace.

“Ɗan gidan Alh Bashir Mafindi.

Ko da yake yanzu anfi saninshi da  Maidala ne”.

Kai Hajiya Lami ta jinjina tace.

“Kai-kai lallai kice babban kamu ne ina zamu yarda muyi wasa dashi waye bai san Alhaji Bashir Maidala ba”

.

“Ai dai kam  ɗan masu kuɗi ina zamu bari muyi wasa da wannan damar tamu.

Ai wlh koda zan tafi tsirara bazan taɓa bari ya auri Khausar ba, sannan Insha Allah zanyi kokarin ganin anja mana hankalinsa yaji ya tsaneta ya riƙa cin Ubanta kamar yanda Moddibo keyi mata amakaranta shine abinda yafi mana a’ala da kwanciyar hankali”.

 

Acan waje kuwa Khausar ce tsaye aƙarshen Barandar Hajiya Bunayya cikin tarin al’ajabi da mamaki ta jinjina kanta bayan ta gama sauraron abinda suka faɗa…..!

 

 

 

*GARKUWAR* taku ce dai MA’AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*

 

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

 

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

 

Ga masu buƙata ga number’ wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu,  ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.

0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki Ka mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nane🤝🏻sayan na gari meda kudi  gida.

 

 

GARKUWAR MA’AURATA

 

 

 

 

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Reply

Back to top button