Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 33

Sponsored Links

Chspter 33

Diro a motan da su goga sukayi suka nufo wanda Alh sunusi ke ciki suka bude masa kofa gaja yace”Alhajin Allah fito fatan ba abunda ya sameka ko?

Eh eh yace duk ya rudewa iya ruɗewa idan akwai abunda ya tsana a duniya shine mutuwa”Alhaji wannan tafiyan batada sana’a kawai mukoma abari zuwa wani lokacin idan ka matsa bamusan abunda zamu tadda gaba ba.

Ya gamsu da bayanin gaja dan haka sauya mota yayi yashiga nasu sukuma suka shiga nasa daya bige suka juya baya.

Basma da ke zaune tsakanin ƙawayen ta wasu nashan syrup wasusun na afawa dan kunsan yawancin matasan mu nayanzu wasu suna ganin hakan kaman wani wayewa ne.
Allah ya shirye mu baki ɗaya.

Nan sukai ta tattauna yanda zasu shirye party bikin sun tsara taron da zasuyi har tsawon sati zasuyi suna shagalin bikin su,wanda wasu a cewar su dole sai ango ya halarci shagalin.

Ahmad cikin sati ɗayan nan duk ya faɗa damuwa fal ransa yanaji ajikin kaman yayi kewar wani abu amma kewan menene de besanin ba saide tabbas yana jin yayi kewa acikin zuciya da ruhin sa.

******
Aisha yanzu de tazama ƴar gida saboda yanda kowa yake ƙoƙarin sa dan ganin sun sake dasu Alhamdulillahi ta ɗan sake saide abun da ba’arasa ba,kullum daren duniya sai tayi mafarkin Anna saide takanyi mafarkin ne tana ganin ta cikin kyakkyawar yanayi tsaɓanin da datake yawan mafarkin abin tsoro ko kuma ana azabtar da ita.

Taɗan sake ba lefi amma haryau jiknta akame yake dasu kwara ummu salma tafi sakewa da yarinyar saboda akwai da shiga rai gata da ɗan banzan surutu irin yaran nan ne masu suturu.

Kitchen ta nufa nan ta iske hajia ikilima da ɗiyarta malika suna ta kiciniyar haɗa abun kari,gaida hajia tayi sannan ta gaida malika amsa mata sukai fuska sake.

“Amm hajia me zankama miki?
fuska dauke da murmushi hajia ikilima ta kalle ta tace”amma ai saikin cire wannan hijabin naki dariya malika tayi tace”wallahi ni Anty hajia mamaki ma wannan ɗiya taki take bani mutum kullum kumshe a ɗaki idan anyi sa’a ta fito saide da zumbuleliyar hijabi wannan mijinta zesha fama duk tabi ta ɓoye abubuwa.

Dukanmu dariya mukai atare jin abunda malika kecewa”kai Anty malika nace ina ƙoƙarin cire hijabin dan saka musu hannu a aikin nasu sannan nikaina ina da bukatar koyan kalolin girke girke tunda ban iya abu dayawa ba saboda matsalan rayuwa da muka taso.

Wanke wanken farayi inayi ina ɗan kallon yanda suke sarrafa komai nasu cikin gwarewa”Anty malika inaso fa ki koyamun girki irin taku ta ƴan gayu yanda nakare maganan saida ya basu dariya”to ai gidanta kikazo inde koyan girkine ganan oganniyata nan tafaɗa tana nuna hajia.

Koba komai na ji daɗin yanda suke jana aji ba nuna bambanci su ƴaƴan masu kuɗine,komai ake agidan sai an sako dani dan son nakara sakewa dasu.

Da yamma ina zaune can bayan gidan cikin wasu furanni wajen yana da daɗin zama musamman ga irin waƴan da suke bukatar keɓewa,nayi zurfi cikin tunanin ta inda zanfara.

Zumbur na miƙe kaman wacce ta mitsina ɗakin da aka ware mana nida ƴan kannena na nufa,wani baƙin riga da wando da malika tabani nasaka na daure gashin kaina baya,nasaka hijabi har ƙasa sannan na nufi falo na tadda Anty hajia ita kaɗaice zaune tana kallon tashar saudiyya a tv har kasa na duka nace”barka da yamma Anty hajia.

“Barkade Aisha ina kika shiga dazu na leka ɗaki bakya nan?

“Eh wallahi ina can bayane na amsa mata.

Maida hankalinta tayi kaina tace”Aisha inaso kisawa ranki salam kuma in sha Allah ba abunda ze faruda mamartaku sai alheri Alh yasaka jami’an sirri suna yin aikinsu ba dare ba rana mukanmu addu’a ya kamata mubisu dashi Allah ya bayyana mata da ita duk inda take cikin ƙoshin lafiya”Amin na amsa idanuna na tare kwallah.

Ba kuka zakiyi ba Aisha lokacin kukanki ya wuce yanzu lokacine da zaki zama jaruma ki koyi juriya sannan ki karfafawa kanki gwiwa wata zuciyar ta bata amsa.

“Share hawayenki kinji karki bari hawayenki ya zube abanza idan da wanda kike zargi ko tuhuma ki faɗamun zan sa ayi mana binciken sirri dan yayanku faisal jami’in sirrine na farin kaya kina iya tuntuɓan sa ze tamaka miki dari bisa ɗari bani da haufi kansa.

“Babu Anty hajia kuma nagode da kulawarku kanmu ba abunda zance dakun sai fatan Allah yasaka muku da mafificin alheri yabiyaku da gidan aljanna”amin ta amsa tana maijin daɗin addu’ar har cikin ranta kuma take tausawa yaran nan da mahaifiyarsu tuntuni take da niyar daukan dauwayniyar karatun su dakuma bukatunsu na yau da kullum Allah ne be nufeta wancan lokacin ba dan komai baya faruwa sai da nufin sa.

“Anty hajia inason nazan ɗan leƙa anguwar mu ingani wala Allah ko wani yaga Anna nayi maganan cikin sanyin murya da mutuwar jiki.

“Ok Aisha amma dole ki canza taku dan bazaki fita haka ba,faisal ne ke magana dan shigowarsa falon yaji ina tambayan fita,kallon kaina nayi nagade shigar da nayi bata da wani aibu tattare da ita maida kallon nayi kansa ga mamakina sai cewa yayi cire hijabinki.

“Wai me haka faisal?
Hajia tayi tambayar tana kafesa da ido shima kallon nata yayi yace”come Anty hajia wani aiki zamu fara da ita daga yau yanzuma kuwa dole saita canja takunta tatashi a wannan amai sanyin takoma mai zafin.

“Aiki na maimaita maganan a fili?”yes aiki dan haka kisameni a garden zamuyi magana yana kaiwa nan yamiƙe yayi waje a sanyaye nakime jiki ba kwari,karfamun gwiwa Anty hajia tashiga yi tana cewa”ki daure Aisha nasan zaki iya kuma na yarda da faisal bazai saka rayuwarki cikin hatsari ba.

Kowace rayuwa dakike gani tana da irin tata kalubale harda ma masu kuɗi dakike gani wasu tasu ƙalubalen idan an daura miki akanki ko an fayyace miki sai kin kwana sallah kina godewa Allah da ni’ima da yayi miki,jinjina mata kai kawai nashiga yi dan bani da wani karsashi daya saura mun ajikina.

Ina isa garden ɗin na hangosa tsaye yana goye da hannun sa a kirjinsa,sallama nayi ya amsamun fuska sake yana karemun kallo yace”zamu fara wani atisaye dake mai suna CIKAN BURINA.

“Cikan burina na nanata”yes ya amsa or operation AS ko ince dake operation Alhaji sunusi,wani irin wuntsulowa nayi idanuna suka firfito idona masu haske da girma barakallah waje ina mai dafe kirjina wacce take mun wani irin lugude kaman zata faso girjina ta fito,kallon sa nake saboda tsaban mamakin yanda akayi yasan wannan shine cikan burina kasa magana nayi saboda yanda bakina yayimun nauyi ƴawun bakina yakafe sai ido wirkil warkil danake binsa dashi nazama kaman wata mutum mutumi.

Leave a Reply

Back to top button