Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 32

Sponsored Links

Chapter 32

Tana tunkarar waje ta aro jarumta ta yafawa kanta dan gudun zargi har ta isa makarantar su khadija bata sha wani wuyan ba wajen batasu su fita a ƙafa suka doshi gidan haj ikilima.

Duk yanda ƴan ƙannen nata sukaso ta fadamusu ina zasuje bata amsa musu ba.

Saima kara ƙami da take wajen yin sauri sun gaji sun kuma galabatu kafin su isa anguwar da haj ikilima take basu sha wahala ba mai gadin yabude musu ƙaramar kofa dake jikin get ɗin suka shiga dayake yasan fuskar Aisha.

Sallama dauke a bakunan su suka shiga falon gida haj ikilima da itama dawowar kenan daga gidan yarta,ta amsa musu da sallamar fuska sake”lale marhabin da manyan baƙi Aisha yau kece a gidan namu kushigo ku kushigo ta kama hannun mubaraq tana cewa maigida ba cefane yayade?

Aisha ina mamar taku fatan tana lafiya sai a sannan tasamu tasake kukan da take ƙokarin riƙewa tun daxu ya kubce mata a rikice haj ikilima ta juyo tana tambayan ta,

Lafiya Aisha?

Mesamu Anna?

Kimun magana mana
Duk tabi ta kiɗime dawowa tayi da tambayar ta kansu khadija dasuma kukan suke ganin Aisha nayi yasasu,wai meyake faruwane khadija meyasamu mamarta ku?

Cikin kuka tace”haj wallahi muma bamu sanin abunda yafaru ba kawai de Anty taxo ta daukemu a makaranta mun dawo nan amma ki tambayeta ko zata iya faɗa miki.

Jinjina kai kawai haj ikilima tayi taciro wayanta daga cikin hand bag dinta ta dannawa faisal kira lokacin suna zaune Ahmad yasoma faɗa masu abunda basma ta aikata na son kashe kantakanta.

harda barazana data masa harda da amincewar da yayi kan wannan auren da yake gani kaman a shirin film wai shine zai tare gidan su amarya saide shi yatare can kaman wani mara galihu ko mara gata.

Wayan hajiar sa shiya dakatar dasu daga tattaunawa da suke”duk abunda kake kabari kazo gida yanzu shine abunda kawai tace dashi ta kashe wayan hankali tashe yamiƙe yana tace dasu”ni zan wuce gida hajia ce tayi kiran nakuma ji muryarta kaman arude tayi magana.

“Ya salam suka ce a tare kode zamu tarene Ahmad yafaɗa yana kokarin fita waje”da kabarshi kawai zamuyi waya duk yanda ake ciki kasan halin antyn taka abu kaɗan yake sata rikice.

“Ok kawai yace yana dan bubbuga kafadan sa sai najika.

Daga haka sukai sallama har bakin mota sukai masa rakiya da khalid sannan suka juya zuwa ciki khalid nufar hall ɗin ɗinkin yayi tunkan yakarasa shiga ya hango bata nan.

Time ya duba har sha biyu ta gota laila ya kwallawa kira”na’am yaya khalid ta amsa tana karasowa inda yake saida suka gaisa sannan yake tambayarta”Aisha fa?

“Wallahi nima najita shiru yau ko lafiya?amma bata saba kaiwa wannan lokacin haka ba,saide jiya tayi magana kaman mamarta bata batada lafiya Allah de yasa bajikin bane.

“Amin ya rabbi
Kinsan gidan nasu kuwa?
Ɗan jim laila tayi sannan ta amsa tana cewa”gaskiya bansan gidanna su ba amma nasan nguwar su sannan idan ka tambaya kace gidan su malama Aisha ta Nurul huda ba wanda baisanta ba ko ƙaramin yaro ka tambaya.

“Nagode yace da ita yana barin wajen.

Alh sunusu
Lokacin da yayi tozali da Anna yashiga tashin hankalin iya tashin hankali saboda girgita da ganin ta da yayi har wayan da ke ƙange a kunnesa saida tasubuce ta faɗi ƙasa kasa nutsuwa yayi har saida ya kira sunan ta cikin rawar murya.

Ganin taƙi tsayuwa yasa yaransa subita su ɗauko masa ita yana bukatar ta a raye,yasan muddin yasame ta to lalle yagama da ishaq duk inda yashiga koda karkashin ƙasa yashiga tabbas zefito.

Motan sa yashiga cikin rashin nutsuwa yabi bayan yaran nasa saide neman duniya sukai mata basu ganta ba kaman wata mai rufa ido ta ɓace musu ɓat.

Suhail
Kiran khalid yayi daga jiya zuwa yau besan adadin kiran da yamasa ba,yanzu ma cikin rashin nutsuwa zuciya data ruhin rashin jinta yasake kiran khalid ɗin,yana ɗaga wayan ko sallama be barin sunyi ba yafara cewa”nasan warhaka tazo dan Allah khalid bata wayan naji muryarta ko zuciyata zata samu nutsuwa.

Dafa goshi khalid yayi kaman yana ganin sa yace”ok maida kira video sai kaji dadin kallon,ba musu ya maida shikuma khalid beyi ƙasa a gwiwa ba yasake komawa hall ɗin har sannan batazo ba.

Hasko masa da wajen zamanna ta yayi yakuma sake tambaya akace masa bata dazo ɗin ba”kade gani ko wallahi tun safe nake zarya daga office dina zuwa nan amma bata zo ba in sha Allah zuwa anjima zan binciko maka gidan su”promise suhail yace a sanyaye”sure khalid ɗin ya amsa masa.

*****
Aisha yini tayi tana kuka tambayan duniya haj ikilima ta mata amma ba wani amsa dan koda faisal ya karaso gidan dan kiran da hajiar tasa tamasa,shima tambayan yayi amma ganin ta kasa bude baki tayi magana da zaran tabude baki da niyar basu amsa sai kawai taji sabon kuka ya kubce mata.

Faisal ya kalli hajia ikilima da duk ta damu yace”hajia ina ga a barta kawai tasamu nutsuwa kila ta iya faɗin koma menene ke faruwa dasu,amma yanzu idan ance sai tabude baki tayi magana ze iya zama kaman taƙurata ake.

Aisha tashi kishiga ɗaki kikwanta ki huta dan Allah kibar kukan nan haka karwani ciwon yakamaki.

Ɗaga kanta kawai ta iya yi gashi kanta yayi wani irin nauyi dakyar take iya bude idanunta saboda nauyi da sukai mata,miƙewa tayi harwani irin dish dish take gani saboda jiri data ke gani miƙewa tayi hajia ikilima da duk tadamu ta taimaka mata wajen mikewar album din da tadauko dakuma diary ne suka faɗo daga saman cinyarta ƙurawa bangon littafi dake rubuce da DESTINY faisal yayi kan yayi yunkurin kai hannu Aisha ta duƙa a sanyaye ta ɗauki abunta.

BAYAN SATI ƊAYA
___________________

Aisha ta dan sake a gidan dan hajia iklima da mijinta dama yaran baki daya suna zaune a falo ranan da suka ciki sati a gida,Alh auwal yabude da addu’a sannan yayi musu nasiha sosai akan riƙe gaskiya da amana yakalli ƴaƴan sa faisal shine babba sai malik da malika ƴan biyu sai fadil da sa’id sai autar su ummu salma,yace faisal ganan Aisha da kannenta cikin mu Allah ne yakawo ta cikin ku kuriƙeta tamkar ƴar uwarku ta jini kutsaya mata duk abunda take da bukatar a tsamatan babu ƙyara ko tsunguma itama dayace cikin mu.

Kallon Aisha yayi dakan ke duƙe yakira sunan ta amsawa tayi cikin sanyi murya yace”inason ki kwantar da hankalin ki kuma kidawo da nutsuwarki ki karfafa gwiwanki gaduk abunda kika saka gaba karki kalli faɗiwa a rayuwa kullum ki kalli nasara wannan shi zai kaiki ga nasaran sannan ganan ƴan uwanki duk wani abu daya taso miki ki samesu zasu tsayamiki ki daukemu tamkar iyayenki waƴan nan kuma ƴan uwanki hajia kuma mahaifiya.

Tuni kuka ya kubce mata tana fadawa jikin hajia iklima.

Alh sunusi jin Anna taɓace musu yakai gwaro yakai naushi sai cizon hannun yake kawai yakira su goga da gaja a waya yana cewa su shirya yau garin ƴar daje zasu”lafiya de ko gaja ya tambaye shi”eh kawai ya amsa mishi a gajarce.

Da yake tafiyar gaggawace be koma gida ba kawai waya yayi yasanar da hajia mariyah duk da bata garin suka dauki hanyan daura tunda suka dauki hanyan waya kawai yake akai akai duk bayi da nutsuwa sun fita garin kano sunyi tafiya mai nisan zango kaman daga sama yaji motar da yake ciki tadaki wani dotse dake gefen titi wani irin ihu ya saka yana kiran goga na mutu..

Leave a Reply

Back to top button