Mu'ujizar Alkur'ani

ALLAH YA SANYA DUWATSU SU ZAMA TURAKU GA KASA.]

Sponsored Links

 1- A Yau Masana na geology suna gano aikin DUWATSU ga KASA yadda suke kakkafeta don kada ta dulmiye . 

Kuma Masana a bangare da dama na duniya sun tabbar da cewa DUWATSU kasansu da nutse acikin kasa yafi Abin da ya bullo tsayi kusan ninkinsa sau uku har zuwa sama da haka tamkar ka kafa turke ko kusa ta nutse kasa . Wanna shine Abin da kur’ani ya fada tun shekara dubu daya da Dari hudu da wani Abu inda Allah SWT Yake fada : ( ﻭﺍﻟﺠﺒﺎﻝ ﺍﻭﺗﺎﺩﺍ ) mum sanya duwatsu su zama turaku ga kasa. Allahu Akbar. A wani wurin kuma Allah Yana bayyana aikin duwatsu da yadda suke kafe kasa kada ta dulmiye cewa: ( ﻭﺟﻌﻠﻨﺎ ﻓﻴﻬﺎ ﺭﻭﺍﺳﻰ ﺍﻥ ﺗﻤﻴﺪ ﺑﻬﻢ )
Don haka kur’ani kullum Shi Yake fara fadar Abu daga baya Masana su gano.

 2- ALLAH (SWT) Yana fada a cikin Alkur’ani:

        (ﻭَﺟَﻌَﻠْﻨَﺎﻓِﻴﻬَﺎ ﺭَﻭَﺍﺳِﻲَ ﺷَﺎﻣِﺨَﺎﺕٍ ﻭَﺃَﺳْﻘَﻴْﻨَﺎﻛُﻢ ﻣَّﺎﺀ ﻓُﺮَﺍﺗﺎ ‏)
‏[سورة ﺍﻟﻤﺮﺳﻼﺕ 27 : ]

KUMA MU KA SANYA DUWATSU
( MASU KAFE KASA ) MASU TSAHO
ACIKINTA KUMA MUKA SHAYAR DA KU RUWA MAI DADI .

       

  Wannan aya ta alkanta duwatsu masu tsaho da kuma ruwa mai dadi abinda masana a yau suke ganowa. ta yadda suka bayyana cewa duwatsu masu tsaho suna bada gudummowa wajen taruwar giza gizai da kuma saukar ruwan sama.
   kamar yadda suke taka rawa wajen tace ruwa da kuma samar da ruwan dadi. shi yasa za kaga yawancin dogwayen duwatsu akwai koramu a kusa da su.

 IN Banda ( Alkur’ani) wanne littafine zai fadi abin da za ai tun kafin shekaru 1436 da suka wuce a lokacin da babu wasu na’urori da za’a binciko ko a leko ko a gano. Don haka kur’ani kullum Shi Yake fara fadar Abu daga baya Masana su gano.

   Allah ka Bamu Albarkar wannan Littafi. Ameen summa Ameen

ALLAHU AKBAR.
DAGA NAKU
    MSZ.

                Domin Neman Karin Bayani Zaka Iya Tuntubarmu Ta Wayannan Hanyoyi Kamar Haka

                 WhatsApp: +2348135986732

                     Facebook: musa s zage

                         Twitter: musa s zage.

                 

                 

Leave a Reply

Back to top button