GUZIRIN MAI HAILA

GUZIRIN MAI HAILA KASHI NA UKU

Sponsored Links

                          بسم الله الرحمن الرحيم    

              { 2}    IDAN JINI YANA WASA

   Misali mace tana yin haila duk wata kwana uku, amma wani trace ranar  juma’a daya. bata yi ranar Asabar ba sai tace Lahadi biyu, bata yi ba ranar litininba sai tace talata uku kuma koda tsallaken kwana nawa yake yi. haka zatayi Lissafinta na Kwanakin da taga jini,      

Wani fadin Ance zata kirga da kwana kin da bat yiba.
      Amma a maganar bata karfi kamar ta farko. sannan musali idan mace jini yazo mata rana daya a wata, bata sake ganin jini ba har sai bayan kwana takwas, to wanda yazo bayan kwana takwas din to sabuwar haila ce. to amma a wani fadin ance tayi haila amma bata sake ganin jiniba sai bayan kwana Goma sha biyar,  to shi jinin da yazo bayan kwana Goma sha biyar ya zama sabuwar haila, wato maganar farko tana nufin indai akwai kwana takwas a tsakanin jinin da wani jini na biyu sabuwar haila.
    Amma magana ta biyu tana nufin jinin ya zama bayan daukewar sa  akwai kwana goma sha biyar a tsakakani to na biyun sabuwar hailace, wannan maganar ta biyu tafi karfi.

      {3}  ABUBUWAN DA HAILA TAKE HANAWA
                       SUN KASU KASHI BAKWAI :

1- SALLAH
    mai haila baza tayi sallah ba. domin Annabin Rahama yace”idan mace tana haila baza tayi sallah ba “.                                 (BUKHARI)

2- AZUMI
      Idan mace tana haila baza tayi azumi ba amma zata rama bayan jinin ya dauke  Annabin Rahman” “yana fada in mace tana haila baza tayi azumi ba.
          (BUKHARI).

3- DAWAFI
   Mai haila baza tayi dawafi ba  domin Annabin  Rahama yana cewa” Shi dawafi (kamar) sallah ne sai dai shi anyin magana a cikinsa. (TIRMIZI DARU KHUDNI).
  Sanan Annabi yana cewa ” A’isah kiyi duk abinda Alhaji yake yi amma banda dawafin dakin Allah” wato mai haila zatayi komai na aikin haji in banda dawafi.

4- DAUKAR AL~KUR’ANI MAI GIRMA
   Mai haila baza ta taba ko shafar Al-kur’ani ba cikin mafi yawan maganganun Malamai domin Allah yana cewa” SHI Al-kur’ani mai girmane babu mai shafarsa sai masu  tsarki.
 Annabin Rahama yana cewa “Karka shafi Al-kur’ani sai kana da tsarki Amma babu laifi Abuda ta karanta ko tilawa wato karatu da ka batare da rike Al-kur’ani ba.

5- SHIGA MASALLACI
  Mai haila baza ta shiga masallaciba,saboda Annabin Rahama yana cewa” bazan halartawa mai haila ko janaba shiga masallaci ba.
                                                     (ABU DAUDA)

6- SADUWA
    Mai haila mijinta bazai sadu da ita ba saboda Allah yayi hani a cikin Al-kur’ani ‘ inda yake cewa Manzon Allah ( S. A. W.) ” suma tambayarka abisa masu haila to kace musu shi haila cuta ne ku kaucewa mata in suna haila kar ku kusancesu har sai sun sani tsarki.” kuma har sai sunyi wankama  za’ a kusancesu.
    Sanan Annabin yace”kar a sadu mata har sai sun sami tsarki. amma babu laifi ayi wasa dasu in dai saduwa akayi ba. saboda Annabin Rahama yace” ku aika ta komai da mata. amma banda saduwa.

7- SAKI
    Baza a saki mace ba in tana haila saboda wata rana Abdullahi dan Umar ya saki matar sa tana haila sai Annabi ya bada umarnin adawo da ita in yaga dama bayan ta gama hailar ya saketa ko ya rike matar sa amma malamai sunce koda mutum ya saki matar sa tana haila to sakin ya zartu
wato ta saku.

                                وبالله التوفيق.

daga dalibinku
 musa s zage

15-07-2019

 

Leave a Reply

Back to top button