GUZIRIN MAI HAILA

GUZIRIN MAI HAILA KASHI NA HUDU

Sponsored Links

                         بسم الله الرحمن الرحيم   

   (4)ABINDA MAI HAILA ZATA KULA DASHI

 Dolene in mace tana haila in zata kwanta barci ta duba ta gani ta sami tsarki haka ma in ta tashi sai ta duba yadda zata duba shine. sai ta sami farin yanki ko auduga ko Toli Fefa ( Toilet paper. ) ta saka a cukin farjinta, in taga ALAMAR jini a jikinsa to bata sami tsarki ba, in taga alamar jini A jikinsa to bata sami tsarki ba kenan domin mata zamanin Annabi (S A W) sukan aikowa da Nana A’isha da tsumma da alamar jini a jiki sai tace musu basu sami tsarki ba harsai sun sa a farjinsu sun ga babu komai sannan suka sami tsarki.

    (5)    ALAMAR DAUKEWAR JININ AL’ADA

  Alamar daukewar sa dai hanyce biyu ce :

 1- In mace tasa farin yanki ko auduga ko Toli Fefa (Toilet paper) cikin farjinta ta duba amma bai canja kalaba to tasami tsarki kenan.

2-  shine ganin (kassa) abin da ake nufi da kassa shine wani ruwa mai fita daga farji bayan gama jini mai kamar ruwan siminti ko ruwan kobewa, in mace ta ganshi to ta sami tsarki kenan.
   Amma shi wannan ruwan (ga wace ta saba ne).

1    guzirin-mai-haila-kashi-na-biyu.

 
 2    guzirin-mai-haila-kashi-na-uku.

3      falarlar-rakaatiyil-fajar.

 4  ilimin-hadisi-saukake-kashi-na-biyu.

    (6) LOKUTAN DA SALLAH TAKE WAJABA GA MAI HAILA TA RAMA.

A – Misali idan mace ta sami tsarki kafin rana ta fadi misalin  a iya raka’a biyar kafin rana ta fadi ko ace saura minti biyar rana ta fadi ita kuma ta sami tsarki tayi wanka kuma ya rage minti biyar ko a iya raka’a biyar to zata rama  sallar azahar da la’asar.

B- Hakanan idan jini ya dauke kafin alfijir ya keto bayan tayi wanka ya zama za ‘a iya sallah raka’ a hudu misalin saura minti hudu alfijir ya keto to zata  yi sallar magariba da isha’i.

   c- kuma jini ya dauke bayan tayi wanka ya zama za ‘a iya sallah raka’ a uku ko muce bayan tayi wanka saura minti uku alfijr ya keto to zata rama  isha ce kawai banda magariba.

      Daga dalibinku
musa s zage

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button