Auren Wucin Gadi 14
Chapter 14
Daidai wannan lokacin da duk wani mahaluƙi yana ga makwancin sa harta ga tsuntsaye,sai masu neman duniya dakuma bayin Allah salihai masu ganawa da mahaliccin su sune kawai suke a farke,
Daddy ishaq dake ɗaura alwala saboda yin nafila kaman yanda yasaba,tar tsatsin wuta yagani a sararin samaniya kaman ana kesta wuta tsai yayi yana kallo sai can yaji dajin duka na amsa sunan Aisha da muryoyi ma bambanta wani irin faɗiwa gaban sa yayi duk da bashi da tabbacin Aishar tashince amma jikin sa yabasa akwai abunda ke faruwa,saurin ƙarasa alwalan yayi ya tashi ya fuskanci gabas yafara gero nafila saida yayi raka’a huɗu sannan ya ɗaga hannu sama idonsa na zubda hawaye yace”Ya Allah gawata baiwarka tana bukatar taimakon ka ya Allah kaceci rayuwarta kakuma tsareta daga hannun waƴan nan azzaluman haka yarinka ƙwararo addu’a yana hawaye dakuma roƙon Allah yakawo karshen su Alhaji sunusi da iri irinsa.
Aisha ina baccina mai daɗi kawai sai ganina nayi tsakiyar wasu mutane masu jajayen kaya sun zagayeni ko wannan su hannun sa riƙe da candil dukkan su sun haɗa baki suna karantu wasu surƙullen su da ba gane wa nake ba,
Innalillahi Allahumma ajirni hasbunallahu iri irin wannan addu’oin su suka zomun baki kaman yanda suke karanta surkullen su da karfi haka nima nakara ƙaimi ina ɗaga muryata kaman maƙogorona ze yage nakeyi ga wani irin tsoro daya lulluɓeni wanda ya haddasa mun rintse idona dan banason nabude idona nayi arba da waƴan nan halittun dan nama dauka ko mutuwa nayi mala’iku suka zomun sai kuma natuna ai mala’ikun Allah masu tambaya cikin kabari ba da irin wannan suffa suke zuwarma mutum ba,kaman yanda aka koyar damu a islamiya to ina ne nan menayi musu da suke neman halakani,lahaula wala ƙowata illah billahil alim….wata murya ce tadamun tsawa muryar mara daɗin sauraro yana cewa zaki rufe baki kidena waƴan nan addu’oin da kike ko kuwa?
Ahmad kwance yake saman royal bed dinsa yayi daidai sai bacci yake bakajin komai a dakin sai ƙaran ac dake aiki,da alama yanajin daɗin baccin nasa dawani irin zabura yatashi sakamakon wani mummuna mafarki da yayi jikin sa yajiƙe sharƙab da zufa kaman wanda yayi wanka dafe kansa yayi da hannun sakamakon sarawa da kan keyima sa.
Anna zaune take tana azkar bayan ta sallame nafila kafin tatashi ta sake wani sai ganin Aisha tayi cikin wani irin yanayi da bata ɓace saninta da shi ba,jikin ta sai ƙirma yake gawani irin gumi da ta haɗa har ɗiga yake,amma duk da halin da take ciki bakinta be fasa kiran sunan Allah da addu’a ba,ɗaga kanta Anna tayi ta ɗaura saman cinyarta tashiga kiran Aisha Aisha amma ina Aisha bata masan Anna nayi ba,ruwa Anna ta jayo tana shafa mata a fuska idonta na tsiyayar da ƙwalla kira take ya Allah kaine gagara gasan masu gasa baka ɗaurawa bawayinka abunda bazasu iya ɗauka ka ba,ya wahabu ga ƴata kakare mun ita da kariyar ka ya samadu karka basu ikon cutar da baiwarka ya Muzambil kakarya alkadarin su kamaida musu da sharrinsu garesu,bamu cutar da kowa ba kar kabasu iko akan bayinka ya zul-jalalu wal-ikram kakawo karshe waƴan azzaluma sai kuma ta ɗauki qur’ani tafara karatu tanayi tana kuka ba komai take tunawa ba sai mijinta abun alfarinta ta rasashi asanda yafara irin wannan abunda tagani ga Aisha.
Sake kwanciya Ahmad yayi bayan yasha ruwa yayi addu’a kaman yanda manzon rahma(s-a-w)yakoyar mana ya canja gefen sa saide baccin nasa beyi wani nisa ba yasake yin wannan mafarki wannan karon zaburan da yayi har yafi na farkon tashi yayi zaune saman bed din sa yashiga tariyo abunda ya gani a mafarkin nasa ga dukkan alama Aisha na bukatar taimakon sa.
Wai meyasa yake damuwa da yarinyar ne tun ranan da yasona ganin ta,wacece ma ita tukunna me wannan mafarki yake nufi.
Mafarkin sa na farko Aishan ya gani cikin wani daji mai matukar duhu mai yalwan bishiyu ana janta a ƙasa tana kiran taimako jama’a duk da ba alaman wani mahaluƙi dake rayuwa a wajen,hakan be hanata neman taimako ba,
Jin ihun nata yasa shi zuwa wajen da gudu saide kafin yakaiga karasowa gareta tuni an fizgeta anyi gaba da ita,baya ganin kowa sai ita dake ƙasa tana neman abunda zata riƙe ta tokare amma ba komi wajen sai ganyaye.
a haka har suka kai bakin wani rami yana miƙa hannu ze riƙota yaji an fizgeta da karfi ta rubta ramin mai matukar duhu tana kira ya ahmaaaad.
Sai kuma na yanxu wai yana zabe bakin ramin gwiwa a ƙasa yana kuka sai ga wani mutum cike da kamala ya dafashi yana cewa dashi”kaine wanda ze ceto rayuwar yarinyar nan daga hannun waƴan nan azzaluman amma saika jajirce kuma bazaka sami yin hakan ba,sai idan ta kasance mallakinka wato matar ka ta sunna.
Gefe guda kuma sai ga daddyn sa yana cewa karka yarda dashi son karya yake maka karɓi wannan zoben kasaka,shikuma wancan mutumin cewa yake karkasa wannan zoben ita ma yarinyar sun saka mata irin sa kayi ƙoƙarin ganin karabata da shi,daddyn sa kuma sai karyarta mutumin yake tare da cewa my son kasande bazan maka karya ba dan haka karka yarda da wannan mutumin mugune gardama ta ɓarke tsakanin su daidai nan yata shi,a fili ya furta komade mainene wannan mafarkin nawa yana da alaƙa da wannan yarinyar to ita kuma ɗaya yarinyar dake laɓe bayan bishiya ita din wacece?