Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 15

Sponsored Links

Chapter 15

Kinran sallan da akasoma shi yadawo da hankalin Aisha ta sauke nannausan numfashi tana gyara kwanciyarta,sai a sannan Anna dake zaune itams hankalinta ya ɗan kwanta tabari idan anyi sallan asuba taza tambayi Aisha taji.
Ahmad shima anashi ɓagaren hakane kiran sallane yata dashi daga zaunen dayake yanufi bayi ya dauro alwala raka’atul fajir yayi kafin ya tashi yafita zuwa masallaci bakin get sukaci karo da daddyn sa zai shiga gidan da motar sa,tambayan kansa yayi daga ina daddy yazo a wannan lokacin,nufar motan yayi saide Alh badamasi be bashi wannan daman ba dan be tsaya ba yaja motarsa zuwa cikin gida ganin haka yasa Ahmad saurin fita waje dan jin antada iƙama.
Sai wajajen karfe shidan safe Anna ta tadani nayi sallah ko azkar banyi ba nasake ɓegirewa daga wajen na kwanta karfe goma natashi saida nayi wanka Anna tabani raguwar kunun koko da ƙosai da suka ragemun nasha nasake kwanciya ina cewa”Anna wallahi jikina duk ciwo yake mu.
Shafa kaina tayi da hannu tace”jiya wani irin mafarki kikayi daya kin firgitani sosai wallahi na tsorata sosai da yanayinki na daren jiya,mamaki ɗauke saman fuskata na dubi anna nace”ni kuma”eh tace dani ɗan jim nayi sai kuma namiƙe zaune kaman mai tunani saide nakasa tunano kamai.

Hajia mariya zaune suke da kawayenta biyu da suka kawo mata ziyara ɗaya mai suna karime tace”gaskiya mariya kinyi sake dayawa taya zakice har yau kunkasa shawo kan Ahmad yace yanason basma sai itace ke hauka akansa amma kallo bata ishesa ba gaskiya sai ki tashi tsaye waye Ahmad yo ko uban sa badamasi idan kinason a karkato da hankalinsa kan ƴarki abune mai sauki amma kin tsaya wai wani ahmad yana juya miki ƴa kaman waina a tanda,hmm ta sauke ajiyar zuciya tace”wallahi ƙawata Ahmad yawuce duk inda kikayi zato dan shu’umin kansane shima,
Sai kuma hajia balki ta amshe yo kema ai saiki nuna kin fishi shu’umanci tun tuni na faɗa miki kishirya muje wajen bokan nan dake amma kinƙi dan kina ganin kaman kin samu duniya”yo wace duniya tasamu karime ta amshe dacewa ai namiji tamkar Zuma yake saida wuta,ai kullum sai kina service dan inganta aikin ki akansa bawai kitsaya tsakaka baki bude kina ganin kin riga kingama dashi kawai baki ankare ba saide kijiki a salansa wata tayi miki wuf da miji.

“Kayya karime bar faɗin haka wannan sai kisa jinina hawa wallahi,dariya suka fashe dashi harda su shewa nan suka saka jibi zasuje wajen boka na gangare kafin su shirya zuwa ogomosho can garin yarbawa.
Basma fitan da tayi a gida saida ta biya ta ɗauki ƙawayenta fa’iza da surayya tukunna suka wuce wajen shoppin saida sukai shoppin tamusu sayayya kafin su wuce shan ice cream,zazzaune suke bayan ankawo musu order da sukai suna cikin sha fa’iza ta kai dubanta ga basma da ta shagala kallon wasu miji da mata cike da sha’awa take kallon su ta shagala sosai da kallon nasu saida surayya ta tafa hannun ta da karfi sannan tadawo da kallon ta kansu”sun burgeki ko?
“Wallahi kuwa har imagin nake wai ni da Ahmad ne dakuma ɗanmu,ko sai yaushe zan sami kulawa da nake bukata daga Ahmad?
Ta kare maganan ta cike da rauni dafata fa’iza tayi tace kawo kunneki ta raɗa mata wani abu danima kaina banji mai tace ba,sai gani nayi basma ta ɗan gwalo ido waje tana kallon fa’iza tace”kina ganin wannan shawaran zeyi”ware mata fici ficin idonta tayi da cewa”mai ze hanashi yuwa.

Aisha zaune muke da yamma ina taya Anna tsintar shinkafa muna taɓa hira saide duk yawancin hirar tamu ya ta’allaƙane kan wajen aikin da nasa nan na gyara zama nace”wallahi Anna kingade kwanan nan nafara aiki a wajen amma gaskiya ana ha’intan mai wajen.
Kallona Anna tayi tace”taya keda bawani jimawa kikayi sosai a wajen ba.
Hmmm”Anna kenan sai kace baki sannin ba,wajen lura da abu dakuma riƙeshi cikin ƙwakwalwata hmmm da ace yau zanga wannan abokin Abban mu mai yawan zuwa garinmu wallahi zan iya ganeshi dan na haddace hoton fuskansa a kaina wallahi mutumin mugune Anna.
Bansan nayi wannan magana ba saida Anna tace”kintaɓa ganin yana wani muguntanne Aisha?
Wayyo Allah kaga matsalan tsuɓutar baki kenan nafaɗa araina amma a fili sai nace”Anna kece kawai baki sani ba amma duk zuwanda yake akwai abunda yakeson Abbanmu ya bashi shi kuma Abba yaƙi bashi wannan abun shine rannan cikin fushi naji yana cewa Abba zaka gani tunda nabika da lallami kaƙi.
Sauke ajiyar zuciya Anna tayi zatayi magana kenan saiga sallamar fadila cike da murnan ganin juna muka rungumi juna har ƙasa ta zauna tana gaida Anna amsa mata Anna tayi da sakin fuska da tambayarta yasu mamarta nan tace kowa lafiya,ledar hannunta mai ɗauke da kayan marmari ta miƙawa Anna tace happy hourn nasu khadija da mubaraq ne godiya Anna tamata sannan muka ranƙaya ɗaki da ita.

Kallona tayi cike da rauni tace”ƙawata nafa samu wannan aiki harma nafara zuwa jiya”wow na tayaki murna kice kin kusa zama hamshaƙiya tawan nafaɗa cike da zolaya dariya tayi tace”kwarai kuwa kaman kuwa kinsani tace dani tana miƙomun wani zobe mai shegen kyau da ɗaukar ido kallon zoben nake azahiri amma abaɗini tunanin nake kaman nataɓa ganin wannan zoben,take jinane ya ɗauki rawa tunawa da nayi da mafarkin da nayi jiya.

 

Leave a Reply

Back to top button