Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 13

Sponsored Links

Chapter 13

Tabbas maganar tata ta dakeni idan nace banji zafin sa ba to nayi karya,nasake faɗaɗa murmushi a fuskata nace”ayyah Hajia shi daraja dakike gani Allah shike ba wanda yaso bawai dan yafi sonsa bane ba,ya daraja shi kan wasu bayinsa ya gani shin ze gode masa abisa ni’ima da yayi masa ko kuwa ze daukarwa kansa girman kai dakuma jiji dakai dan kawai Allah ya bashi daraja.

“To matsassako mai bakin magana kewai wace iriyar yarinyace komai mutum ya faɗa kin tanadar da amsarta dan Allah ni wuce ki bani waje bancika son yawan magana ba amma sai da kikayi yanda nayi harkin samun ciwon kai,ruwa ta dauka ta kurɓa da daura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana mai maida kanta ga kallon tv dake kunne tun ɗazu tashar mbc 2 suka hasko wani american film xmen.
Ni made tsuke bakina nayi basma dake kishingiɗe sai aikomun da harara take niko da mun haɗa ido da ita sai nasakar mata murmushi haushi kaman yakarta shiko sokon yayan nata tsaye yayi ya rungumi hannuwan sa a ƙirginsa sai kallona yake dawasu ƙananun idanun sa,har tsayuwan yafara gundurana saboda idanu da suka zubamun su biyu kaman masu son gano wani nakasa a halitta.

Dakyar laure ke jan dustbin ɗin kayan zuwa nayi na taimaka mata muka kama muka fito dashi waje can baya wajen famfo mukai sai da muka ajiye taje ta daukomun robobi sai da natara ruwan wankin sannan nazube kayan duka a ƙasa sai ganin laure nayi ta zaro ido cike da tsoro yana cemun”ƴar nan kika zubur da kayan a kasa? kallon mamaki nake binta dashi murmushin nan de nasakar mata nace”Inna laure idan ban zubar a ƙasan ba ya za’ayi nagane waƴan da zan wanke da omo da wanda zanyi da sabulu kinga da wannan tsoron naki dama zuwa kikayi kika anso sabulun da omon zefi,ajiyar zuciya ta sauke tace”kede ina jiye miki fushin hajia a kanki hmmm na sauke ajiyar zuciya nace”aini da fushin tayi wallahi zamma fi jin daɗi daga nan ban ƙara tanƙa waba ita ma bata sake yimun magana ba dan gani take kaman ƙuruciya ke damuna bansan ciwon kaina ba.
Sai da naware komai pant da bra duka na maida mata da abunta cikin dustbin ɗin dan na alkawartawa kaina bazan sake wanke pant ɗin mace ƴar uwata ba,wanki nake tuƙuru sai sha biyu da rabi na rana nagama wanki na ƙwashe wanda suka bushe na linke nakai ciki a falo na tatta da hajia cikin kwalliya kaman mai shirin zuwa anguwa saman kugera nasamu na zube kayan akai nace”hajia barka da hutawa a wulakance take bina da kallo sai can tace”wai da mekike takane da bazaki iya rusunawa kimun magana ba?kin wani tsayamun ƙerere a ka kina sakarmun da wannan murmushin naki na rainin hankali,ganin murmushin nan nawa yana ƙular dasu yasani sake faɗaɗawa nace”kinsan abunka ga wanda be sabayin hakan ba hajjaju saide fa hakuri mtssss taja tsuka mai tsayi tace jeki kitchen kice laure ta baki abinci kici kinsan muna da karamci duk wanda yashigo gidan nan bazamu barshi yatafi beci komai ba.
Ƴar dariya nayi nace”da girman kugeranki hajjaju saide fa aƙushe nake da zaki bani hakkina natafi da yafi mun wannan tayin abincin naki a guna kinsan ciki kuma ba lalle cimarku ta zamo ɗaya da tamu ta talakawa ba karna zarme naci dayawa cikina ya ruɗe.

A harzuke ta miƙe tsaya dan jin abunda nace saurin riƙe kunnuwana nayi nace afuwan hajjaju ban fadi haka dan naɓata miki rai ba,kawai de nafaɗi iya gaskiyana ne amma idan hakan ya taɓaki yi hakuri,dan Allah yanason bayinsa masu hakuri,komawa tayi ta zauna ta ɗaura kafarta saman canter table tace zauna ki matsemun ƙafata inaji ya ɗanmun tsami.
Kaman na kai mata mangara haka nakeji dan haka cike da jin haushin ta na zauna ina jamata kafar a hankali har wani lullumshe ido takeyi saboda yanda take jin daɗin sa,ina cikin ja mata kafar basma ta fito cikin kwalliya ta kalleni ta watsar tace”mummy zanje shoppin zaram na miƙe tsaye nace”yauwa sai ki saukeni bakin hanya yamutse fuska tashiga yi kaman taga kashi niko ko akwalata ta bankamun harara tace”wai nice zan ɗaukeki a motata tayi maganan tana nuna kanta”eh na bata amsa a taƙaice kana nadubi hajia mariya dake kaɗa ƙafa nace to hajjaju zan tafi sai abani hakkina dan musamu nasawa a bakin salati kinsan abunka ga talaka sai yafita zai sami abunda ze saka abaka.
Yanda nayi maganan ina karkace kai sai kadauka da gaske nake yinta har zuciya niko iya baka ne”ki tafi zan aika miki tace ba tare da ta kallin inda nake ba”haram hajia da kinsan bazaki biyani hakkina ba ai tuntuni da kin faɗamun da mutum yayi magana sai ace talaka wace daraja gareshi amma ansan yanda za’a tauye masa hakkin….kafin na karasa magana a fusace basma ta cillomun 2k tsugunawa nayi na ɗauka banko kalli inda hajia ke zaune ba balle ita dake ta huci kamar wata macijiya na nufi kofan fita na tsinkayo muryar hajiya na cewa”tsiyar talaka kenan murmushi ɗauke a fuskata na juyo nace”yauwa Anty basma na manta ban faɗa miki ba na barmiki raguwar ruwa da omo a can baya ko zaki wanke kunzugunki naga duk sunyi tsotsa shisa nabar miki dan bazan iya kayan ƙazantar nan ba,ƙila ke zaki iya tunda nakine,mutum yakoyi ɓuye sirrin sa kafin yaga rashin darajan wasu wace darajane ga maccen da bata iya ɓuye sirrin ta ba,koda yake…..bara de nayi shiru kawai nasa kai nafita a falon inajin hajiya nace wa wallahi sai naje gaban wannan tsomararriyar uwar taki sannan na cicci ubanki oho de nide nafita laure da taleƙo zata tambayi hajiya abunda zata dafa a ɗari takoma ciki tana mai zaro idonta waje da rufe bakinta da tafin hannunta tare da jinjina rashin tsoran wannan yarinyar da take kasada da rayuwarta dan tasan wace hajia wajen rashi imani.

 

2:am

Alhaji sunusi yamiƙe tsaye ya kalli dandazon mutane da suka halarci wannan taro na ƙungiya sabbi da tshoffi yace”ina mai farin cikin halartanku wannan taro namu na ƙungiya ba tare da ɓata lokaci ba munason ganin duk wani sabon member namu anan,miƙewa sukayi suka zagaye wani ƙaton ƙwarya dake saman wani rami shi baya sama kuma be zauna a kan ramin ba yanade tsaka tsakiya ya umurci ko wanne cikin su da cewa ya yanke hannun sa ya diga jinin sa cikin wannan kwaryar,bamusu sukai bayan sun gama sai suje gaban wani katon mutum dake zaune cikin jajayen kaya sumasa sujjada(wa iyazu billah Allah yakiya shemu da son zuciya)shi kuma sai ya daura wani abu mai kamada gashin ɗawisu a kansu yayi wasu surutai.
Bayan sun gama sannan Alhaji sunusi yace barkan ku da shiga kungiyar asoka muna da sharuɗan mu kafin kazama ɗaya daga cikin mu harsai ka cika wannan sharaɗin kun shirya”eh suka amsa masa bai ɗaya da farko dole halartan kowani taro namu koda baka garin dole kazo dan ka halarta,sannan ko wanne cikin ku wajibine ya sadaukar mana da jinin mutumin da yafi soyuwa aransa,kafin yasamu cikin burin sa,mutukar mutum ya cika sharuɗamu shida talauci saide yagani anayi.
Fadila tunda taji sai ta sadaukar da jini take jikinta ya dauki ɓari karkarkarkar miƙawa kowa wani kogo akai duka amsa sukai amma banta ita data lula duniyar tunani da zullumi”kee taji wani kakkausan murya daya sata firgita saboda amsawa da dajin gaba ɗaya yayi karɓi kisha aka faɗa cike da bata umurni kin shigo cikinmu bake ba fita tunda kintsani talauci muddin kika kawo mana wasa cikin lamarin mu jinin iyayenki ya halasta garemu……wani irin faɗiwa gaban ta yayi madadin ta ambaci sunan Allah kawai sai jin bakinta tayi ya ambaci sunan Aisha saboda tunawa datayi da maganan su rannan”AISHA AISHA AISHA taji wajen yaɗauka take tazube wajen sumammiya.

Leave a Reply

Back to top button