Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 30

Sponsored Links

Chapter 30

Duk yanda Anna taso danne zuciyarta kasawa tayi saboda yanda Aishsn ke wasu irin maganganu kaman mai aljanu,sai kira take innallahi Anna shikenan mama rabi ta mutu anmata kisan gillah Anna kalli nan kigani na shiga uku sun kasheta suna taran jinin cikin wata ƙatuwar ƙwarya lahaula ya ilalil alamina Anna harda fadila cikin wannan aika aikan kalli kukama take saboda munafinci.
Rufemata bakin Anna tayi dan bazata iya sauraron wannan kayan taƙaicin ba cike da tausayin ƴartata tasoma cewa”ya’isa Aisha kiyi shiru ki nutsu bude idonki ki kalleni nan sai kuma tashiga dan marin ƙuncinta a hankali ta yanda bazataji zafin marin ba tanayi tana kiran sunan ta.

Duk yanda Anna taso Aisha tayi shiru batayi ba sai wajejen asubah bacci mai nauyi yayi awun gaba da ita.

Washe gari muka tashi da mummanan labarin mama rabi ta amsa kiran Allah,sakamakon amai da gudawa cikin dare kafin akai ga zuwa asibiti rai yayi halin sa.

Anna tasha kuka sosai da ta tuna da maganganun Aisha na daren juya sai ta ɓarke da kuka karshede sai zazzaɓine mai zafi yarufeta ta lulluɓa da abun rufuwa sai rawan sanyi take kar kar kar.

Kwanan basma uku a asibiti zuwa wannan lokacin jikin ta yayi kyau an kuma tsaida lokacin biki sati biyu zo kaga murna da rawan kai wajen basma yayinda ita ma hajia mariya ta ɗaga dubai ranan da aka sallame su a asibiti da dare domin sayayyan kayan gado da kuma kitchen na gani na faɗa acewar ta bikin ƴar gata za’ayi.

Ammi zaune take tayi jigum saboda tunani neman mafita wa ɗanta damasu baki ɗaya dan ita harga Allah bata yarda da wannan haɗin ba gani take kaman da wani abun a ƙasa.

Kasa hakura tayi saida ta kira ƴar uwarta hajia ikilima ta waya dan su sami zama,
Bayan sunyi waya kaman da minti ashirin sai gata dama a hanyarta da zuwa gidan takira ta.

Bayan gaishe gaishe Ammi ta gabatar mata da ruwa da lemu da ɗan abun motsa baki sannan suka zauna zaman tattaunawa.

Nan ta fayyacewa ƴar uwatata komai”yanzu ikilima ina mafita cikin wannan lamarin nifa gani nake kaman da akwai wata a ƙasa sannan narasa gane kan Alhaji inde magana tashafi Alh sunusi wallahi hankalin sa baki ɗaya bacewa yake bashi da ra’ayin kansa saita wannan bawan Allah wallahi ikilima bana tantama wannan mutumin ze iya kashe rai dan biyan bukatar sa.

Nisawa haj ikilima tayi ta kalli ƴar uwartata tace”yaya ni a tunanina mafita shine munewa Ahmad wata ƴar wacce zata kula dashi ya aura.

“Anƴa kina ganin Ahmad ze yarda da wannan?
Ko wannan da za’ayi yanzu fa saida yarinyar tanemi ta kashe kanta shine fa ya yarda amma tun tuni Alh yana maganan auren yayi biris.

guntun murmushi haj ikilima tayi tace”AUREN WUCIN GADI zamu masa kuma na tabbata kafin wa’adin yacika ze sota ya kaunace ta saboda kyawawan ɗabi’un ta sannan wannan yarinya zata maxa kariya gareshi haka shima ze zame mata kariya.

“Taya ƴar uwa?

Kawo kunnen ki nan tama Ammi wasu maganganu cikin kunneta sai ga Ammi tana sakin murmushi dacewa”inde wannan ce na yarda nabaki wuka na baki nama sai yanda kimayi.

“Wuka da nama kika damƙawa ikilima anƴa baza’ayi abun arziki awajen.

Dukkansu a tare suka juya dan ganin mai maganan alh badamasi ne da yasako kai falon yake tambaya dan jin maganan Ammi.

“Au ashe kana kusa dama maganar lefe naxo muyi dariyar jin daɗi yayi yace”a’a lalle yau anyi abun kirki ashede kin fara hankaltuwa,yakare maganar cike da zolaya.

“Au da me kaɗaukeni?
Fuska a washe ya amsa mata da cewa”ai ke dince maciji sari ka noke.

“Lalle Alh ai kaikan ka kasani idan nayi sarata bana nokewa dan nasan a gaɓanda nakeyi.

“Yanzude barwannan ai ni ina jinjina ƙoƙarin kabiru daya iya hakuri zama dake tsawon wannan shekarun batare da anji kanku ba.

Saida tayi dariya sannan ta amsa masa da”saboda ire irenku masu bacci da ido yasa kuke kashe abun tare bunne tare batare da kunjimu ba kadeji.

Saida suka ɗan taɓa raha sannan ya cake musu maƙudan ƙudi dan hada lefe acewarsa lefen ƴar gata nan yayi musu sallama yafita Ammi tana masa adawo lafiya.

Yana fita sai ga Ahmad ya danno kai falo yana waya magana yake ƙasa ƙasa da harshen turanci be kula da haj ikilima dake zauna sana sake tattaunawa da Ammi ba saida yaxo tsakiyar falo sannan ya lura dasu kashe wayan yayi.

Yanufo su yana huggin dinsu da ɗai ɗai yana sakin fuska gaidasu yayi a tare sannan ya juya kallonsa ga haj ikilima yana cewa”Anty hajja yaushe a gari?

Da kulawa take kallon sa tace”daren jiya Amminka ta hanani sakat dole na hawo jirgi nazo.

Maida kallon sa yayi yana kallon Ammin yana marairaice fuska kaman wani karamin yaro”nide dena bina da irin wannan kallon dan ina kan bakana karkaga na amince da auren ka da wancan ɗin nayine saboda tausayi kuma a matsayina ta uwa.

Sauke numfashi yayi yace”dan Allah anty hajja kice wani abu mana,cike da shagwaɓa yayi maganan yana kwaɓe fuska.

Shafa kansa tayi”tace ai yanzun ma magana da muke kenan,tsayawa zakayi a kan kalaman ka nason matarka ta tare a gidan ka bawai kai kabita gidan su ba.

Matukar tanason ka zata yarda ta biyoka gidan ka,sannan kuma kaman yanda ka yarda ka amince kakuma amshi wannan auren to itama yaya so take kayi mata wannan biyayyar kaman yanda muka sanka da biyayya a baya to yanzu so muke gobe za daura maka aure da wata kuma insha Allah zakayi alfahari da wannan zaɓin.

A zabure ya miƙe wani irin gumine ya jiƙashi sharkaf tuni yanemi ƴawun bakin sa yarasa muƙushin sa yabushe riƙo hannun sa haj ikilima tayi ta zauna dashi kusa da ita sannan ta soma magana cikin taushin murya tace.

“Ahmad kanitsu ka saurare mu da farko de dalilin mu nason yi maka aure ba wai dan mu saka rayuwarka cikin ƙunci bane,munfi kowa son muganka cikin farin ciki da walwala arayuwar auren ka.

“Amma anty hajja kubarni naji da abunda yake damuna mana bawai ku sake dauramun wani ba haba anty hajja na dauka zaki rokarma Ammi ta janye da batun auren nan amma sai naga kaman ke kinma fita son ganina cikin damuwa.

“Ba haka bane Ahmad ta amsa da sanyi murya.

“To yayane anty hajja wallahi ni kaɗai nasan irin ƙunci da nake ciki da maganan wannan aure.

“Yauwa Ahmad tsaya kaji dalilin mu muma nason yimaka wannan auren da farko de kai bakacin abinci ƴan aiki.
Sannan gyara maka makwanci dakuma wanke maka irin ƙananun kayanka irin gajeran wando dade sauran su sai matar ka kula da duk wasu kananun abubuwan cikin gida.
Kasande ɗakin kwananka sirrinka ne kai mai gida be dace ace wata wai ƴar aiki tashiga dan ta gyara ko tashere maka ba sai matar ka.

Amma idan kana ganin matar taka zata iya kula da dukkan waƴan nan abu buwan dana lissafo to shikenan.

Ammi ta amshe tana cewa”ina fa zata iya yarinya da akace ko pant tacire nan take bari sai mai aikine zata dauke mata yo ina kike tsammanin zata yiwa miji saide idan ko shime xe zaje yayi kayansa amma wannan ƴa bana tunanin ko ruwan shayi ta iya dafawa.

“Ai yaya karin wani ta kaicima sai kingani wallahi har pad idan tayi amfani barin sa take cikin pant ɗinta sai mai wankine ze cire ya yar shisa duk mai wanki da suka ɗauka idan yayi sau daya baya sake dawowa dan gudun kayan ƙazanta,tunda suka fara magana shiru yayi yana jin abunda suke tattaunawa akai ɗin xuciyar sa takasa yanke masa abu guda.

Sai maganan haj ikilima ne yadawo nashi inda take cewa”kede yaya bari kawai inaga kawai AUREN WUCIN GADI zamu masa idan yaga kamun ludayin matarsa nan da wata uku saiya sauwake ma yarinya takama gabanta koya kikace?
Hakane amma kinyi tunani mai kyau yaxamu da iyayen yarinya kode zamu faɗa musi manufarmu ne.

“a’a yaya kawai matsayin ƴar aiki zamu daukota sai musami wani malami ya daura auren.

“Anty hajja wannan wanj irin magana kuke dan Allah.

“To kai ina ruwanka ina kai kasan ita din matsayin matarka take yo mai aciki dan ita bata sani ba.

Kawai mu kalla daya muke jira a wajenka wato na amince shikenan sauran komai kabarshi a hannun mu.

Sauke numfashi yayi yana duba agogon dake daure a hannun sa yace”ni zantafi inada abu yin sosai amsarku kuma shine yaɗan kalli ammin sa yanda ta zuba masa ido tana jiran taji wace amsa ze bada gyaɗa kai kawai yayi batare da ya iya furta komai ba saboda yanda yaji bakinsa yamasa dauyi lokaci guda.

Kabbara da Ammin tayi yasashi dan bude idonsa daya lumshe yana zubasu saman fuskarta hango farin ciki dayayi kwance saman fuskarta tana ta sakin murmurshi da sanya masa albarka yasa yaji sassauci cikin zuciyansa koba komai tu da mahaifiyarsa tana farin ciki koda shi ze shiga ƙunci yayarda gwamma yarasa nashi farin cikin ita ta dauwama cikin ta.

Karfe goma daidai aka kai mama rabi gidan ta na gaskiya Allahu akbar duniya kenan budurwar wawa duniya gidan kashe abu,shikenan mama rabi antafi kenan saide muce Allah yajikanta da rahmarsa.

Mutane da yawa sun halarci jana’iza ciki harda irin su Alh shehu Alh sunusi dama wasu manyan da dama mutane dayawa suna mamakin ganin irin manyanda suka halarci jana’izan saide wajen wasu ba abu mamaki bane duba da yanda fadila take bin manyan mutane.

Sanda Aisha ta matso kusa da fadila dayi mata gaisuwa da jajanta mata kan rashin mama rabi da sukai kuka mai tsanani fadila taɓarke dashi wanda tunda akace mama rabi rai yayi halinsa bayi irin sa ba sai yanzu.

Rike hannun Aisha tayi gam ida kadai tasan abunda takeji a ranta dangane da ido hudu da sukai da Aisha dakyar Aisha tamu ta kwace hannunta daga irin riko da tayi mata sukai sallama ita da Anna da tafita jikin Anna duk yayi sanyi haryanzu zazzaɓin be saketa ba,suna fitowa bakin ƙofan gida kaman ance da Anna ɗago kanki kawai sukai ido biyu da Alh sunusi dake kokarin bude mota cak ya tsaya daga bude motar”Na…na..nafi yakare maganan da in ina Anna kuwa nan take taji zazzaɓin yasake wani karfine yazo mata ta fizgi hannu Aisha suka ranta ana kare….

Leave a Reply

Back to top button