Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 29

Sponsored Links

Chapter 29

Zumbur ya mike kaman wanda aka tsikara da allura yanufi cikin ɗakin dayake jiyo ihun hajia mariya da gudu ita kuma tana shirin fitowa dan neman masu taimako,saura ƙiris yafaɗi da abunda idon sa suka gane masa basma yagani ƙwance idanunta duka a kakkafe bakinta na fitar da wani irin kumfa.
Batare daya tsaya ɓata lokacin sa wajen tambayan dalilin ba kai tsaye yanufi bakin gadon ya kinkimota yayi waje da ita dagudu hajia mariya na mara masa baya bayan mota yasaka ta hajiya mariya ma tashiga shima yazaga yashiga mazaunin driver yajasu a guje yafita daga gidan wani asibitin kuɗi yatafi yana shiga harabar asibitin ko parkin beyi daidai ba yafito daga motar yabude kofar baya ya kinkimota dagudu yayi ciki yana kiran”dr dr dr ganin yanda yake a ruɗe yasa kowa hanya yake bashi kafin wasu nurse biyu suka fito ɗauke da gadon ɗaukar marasa lafiya emergency room aka shiga da ita,kafin dr uku suka rufa masu baya tare da kullo ƙafan.
Tsakanin Ahmad da hajiya mariya an rasa wanda zeba dan uwansa hakuri itakan hajiya mariya sai kuka take riris shiko ahmad sai safa da marwa yake aranshi kowa Allah Allah kar ƴar mutane tamutu ta sanadin sa,awa uku curr suka ɗauka a wannan yanayin kafin aka buɗe ƙofar wani dr yafito da sauri suka tunkarosa da tambayan ya’ake ciki?

“Kusameni a office yace dasu cike da fargaba suka rufa masa baya saida yasamu waje yazauna sannan yamusu nuni da wajen zama,zama sukai jiki ba kwari gyara zaman glass ɗin sa yayi sannan ya kallesu yace”kune kune kuka kawo wannan yarinyar”eh eh suka hada baki wajen amsa masa dan sun kagu yafaɗa musu halin da take ciki.
Numfashi ya sauke yana mai kafe ahmad da ido yace”mijin tane kai ko?
“A’a ya amsa a gajarce”mamarta ce ni hajiya mariya ta amsa da wuri”ok amma me kukai mata dazafi haka wanda har take ƙokarin illata kanta?
Wai maiyasa sam wani lokaci iyaye bakuda kula akan lamuran yaranku wajen maida hankali akan me sukeso dakuma wanda basa so,kuma gode Allah ya takaita kunyi saurin kawota akan lokaci badan haka ba da yanzu saide tashin zance ƴan rubuce rubuce yayi a farin paper ya ɗago yada kallon sa garesu yana cigaba dace musu su kula da ita sannan a kiyaye duk wani abu daze jefa rayuwarta cikin hatsari idan ma saboda saurayi tayi hakan to a gaggauta mallaka mata da abin da takeso dan gujewa faruwan irin haka nan gaba.

Aisha
A ɗari na shiga cikin gida tun kafin na karasa ciki nake iya jiyo yanda anna ke wani irin tari ba kakkautawa maman salmanu sai jera mata sunnu take,sauri karasowa wajen nata nayi na rungumeta jikina ina kuka da tambayan maman salmanu”meya sameta?
Me fadila tamata da tafita yanzu naruɗe har nasara meke mun daɗi sai sumbatu nake ina wallahi idan wani abu yasami anna wallahi bazan yafema fadila ba.
Sai kuka nake can da kyar muka su tarin ya lafa tayi matukar jiƙata sai numfashi take saukewa akai akai sake maimaita tambayar tawa nayi me fadila tazo yi gidan mu bayan mamarta ta shata mana layi,da mamaki naga suna kallona khadija ce ta iya bade bakinta dakyar tace”anty aisha ai ba wanda yashigo ina kuka haɗu da anty fadilan dakike ta ambatar sunan ta tun ɗazu?
Sakato nayi ina kallon ta to inba ita nagani ba wa nagani yanzu har mukai magana kode nafara samun matsalan ƙwakwalwa ne tun ina mafarkin dare karde ace zaucewa nayi nafara ƴan gane gane.
Dafe kaina nayi da hannu biyu dake wani irin saramun nama rasa wani irin tunani zanyi nide nasan tabbas naga fadila kuma harma munyi magana da ita baki da baki ya salam na furta da karfi.
Dafani maman salmanu tayi tace”gaskiya khadija tafaɗi ba wanda yazo gidan nan tun bayan tafiyanki aiki jikin mamar taku ya matsa ko makaranta yaran nan basu samu zuba,nayi tunanin yi miki aike kidawo gida saboda jikin nata amma ta hana kiranki,yanzun nan tafara tari muna zaune tare.
Tunda maman salmanu tafara yimun wannan bayani jinta kawai nake amma bawai da ina fahintarta ba ganin kaman bana cikin nutsuwa yasa tayi shiru ta barni na kafe Anna da ido kaman me son gano wani abu ajikin ta,amma duk ƙwaƙwafina ba abunda idona suka gane mun tattare da ita,ba wai dan nayarda da abunda suke cewa ba nadeyi shiru ne kawai.

Hajiya maryama ta kalli ahmad bayan sun fito daga office ɗin likita fashewa masa tayi da sabon kuka cikin kukanta take cewa”na haɗaka da Allah ahmad ki taimake mu badan halin mu ba kaceto rayuwar basma,yanzu haka ceto rayuwarta ya ta’allakane a wuyanka saurin ɗagota yayi ganin tana neman durkusa masa kafin yayi magana wayansa tayi ƙara cirota yayi daga aljuhun sa yana karawa a kunnen sa,a ɗaya ɓangaren akasoma magana kaman haka”iba kashigane tuntuni muna kiran wayanka baka ɗagawa?
Numfashi yafesar mai zafi bakin sa ɗan waigowa yayi ya kalli hajia mariya da sannan matsan ƙwalla take cikin sanyi murya yashiga faɗawa Ammin nasa abunda ya tsaida shi’cike da jimami tace yanzu wani hali take ciki ita basman?
“Alhamdulillah ya amsa mata dashi sannan yafaɗa mata sunan asibitin da suke tace gata nan yanzun nan yana kashe wayan ya koma wajen hajiya mariya yace”hajia kiyi hakuri kibar zubda hawayen nan haka komai zezo da sauki kuma in sha Allah inde nine na amince zan aureta saboda ceto rayuwar ta kaman yanda kika bukata.
Cike da jin daɗi tawashe bakin ta sai sanya masa albarka take phamacy yanufa dan sayo musu magunguna da likitan ya rubuto masu yana barin wajen takira Alh sunusi ta sanar dashi abun da yake faruwa,aruɗe yanufo asibitin kan kace me asibitin yacika da ƴan uwa da abokan arziki zuwa dubiya kowa kaga fuskansa da damuwa bama kaman alh sunusi dan rufe idonsa yayi yama Ahmad faɗa harcewa yake wani irin zuciyace gareka da batada tausayi sai kace zuciyar kafiran farko yajuya yakalli hajia ma’arufa yace yanzu fisabillahi saboda ba ƴarki bace baki damu kota mutu ko tayi rai ba,kingade halin da ƴar nan tashiga kuma duk a saboda son da takema ɗanki matsayin ki na uwa ki kaddara idan ƴarki ce take a wannan hali wani mataki zaki ɗauka?
Ya zakiji abun a ranki?
Dan Allah kisawa ranki salama matsayinki na uwa kima ɗanki magana dan sai yafi jin naki magananki dana mahaifin sa.

Jiki a sanyaye Ammi ta kalle sa tace”bakomai wallahi Allah yabata lafiya yakuma sanya albarka a abun dama can ni ba hanawa nayi kawai de yanda kukayin ne bemun ba ina lefin tunda dukkan ku kuna da ƴan uwa kamata yayi aje neman aurenta itama kaman yanda addini dakuma al’adarmu ta tanada.

Washe baki alh sunusi yayi yashiga da bata baki dan hararo nasaran cikin lamuransa,daga haka sukai masu sallama suka koma gida tare da fatan samun sauki har mota hajia mariya ta raka Ammi nata ta zuba mata godiya.

“Aisha koda dare yayi kasa rintsawa nayi saboda abubuwa da sukaima kaina yawa,tabbas nafaga fadila ido da ido amma kowa cewa yake beganta ba a gidan,dan waigowa nayi na dubi sashin da Anna ke kwance”bakiyi bacci bane Aisha?
Natsinkayo muryarta”eh nace a sanyaye na daura da cewa Anna aikema bakiyi baccin ba,hmmm ta sauke ajiyar zuciya tana kai gyara kwanciyarta tace”Aisha ɗazu hajia ikilima tazomun da wani batu kuma kinsan yanda muke da ita ba abunda zata nema aguna matukar bamufi karfin abun ba zamuyi mata shi alal hakika zancen da nake dake yanzu an daura aurenki da ɗan yarta ɗazu kuma nasan bazaki zuban kasa a ido ba zaki….bata iyata karasa maganan nataba dan ganin Aisha bata cikin hayyacin ta idanun ta akafe sai wasu irin sammatu take”innalillahi na shiga uku ni nafi wai make shirin faruwa da rayuwar ɗiyar nan ne daidai ta karoso ta rungumi Aisha zuwa jikin tana sakin wani irin kuka mai cikin rai.

Leave a Reply

Back to top button