Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 34

Sponsored Links

Chapter 34

“Kinyi mamaki ya’akai nasan wannan ko?

Shiru nayi masa wannan kundun yanuna mun yans cigaba da cewa wannan shine amsan ki,rannan da kukazo gidan Anty hajia takira ni da nadawo gida sanda kika tashi tsaye yafiɗo ajikin ki.
Tunda daga kan rubutun bangon littafin danayi a ganin farko na fahinci zan masu sirrika da muka daɗe muna nema bamu sane sa ba.

Dalilin wannan nayi ta bibiyarki kafin kisake dani dakyar nasamu na dauki littafi shafi biyu kawai na karanta a ciki sauran aikin kece zakiyi nikuma huras wace tawa saide aiki yanada hatsari tunkarar mutum kaman Alh sunusi.

Numfashi nasauke sai yanzu nasami daman yin magana nace”shidin ba mutum bane?

Murmushi faisal ya sakarmun yace”mutum ne shi amma ba kaman kowa ba,sabida dalilai da yawa,abu nafarko da nakeso kisani kuma ki zauna kiyi tunani akai shine taya mutum mai imani da sanin yakamata ze saka rayuwar abokin sa aminin sa cikin hadari bayan bashi da kaman sa ya rabashi da ahalin sa na tsawon rayuwa yacutar dashi zekuma kashe rai dan biyar bukatar sa bakomai bane a wajen sa yin haka.

Alhaji sunusi
Duke yake gaban shugansu duk yabi ya haɗa zufa yana cewa”ya shugaba abu lamarin nan wallahi kuɓutar ishaq da matarsa hatsarine gare,nayi kokarin bin bayan ta amma wallahi kaman mummunan kadamine ke bibiyata mota ta hanani tafiya.

Aduba mun ko zasan inda suke”hhhhhhh dariya shugaban ya tuntsure da ita yace”kaga kwantar da hankalin ka ishaq mun gusar masa da hankali baze iya tuna kansa bama balle wani koya ya iya tona maka asiri, sannan ita matar ai tuni tayi hadari ta mutu garin gudun ceto mota tabi ta kanta matso nan kagani.

Matsowa Alh sunusi yayi yayi wani tanƙamemen ƙwarya dake gaban sa mai cike da wani irin ruwa mai yauƙi ne ya bayyana yana leƙawa kowa sai ga wata mata tana falfala gudu taxo daidai bakin gwalta wata mota kuma tazo da karfi tabi ta kanta,ajiyar zuciya yasauke yana cewa duniya sabuwa yanzu bani da wani saura fargaba.

“Nuna masa wata ƙwarya shugaban yayi da hannu ko beyi magana ba yasan me yake nufin da yayi tuɓewa yayi yasa alƙalamin sa cikin wannan ƙwarya wani irin turirine yake fita ta dukka ƙofofin jikin sa dukka wannan abun saboda son duniya yake yinta.

Allah yakare mu da son zuciya koda yaushe kasa mufi karfin zuciyar mu kakaremu da imanin mu ja kyautata karshen mu Allahumma amin.

******
Yau tun safe ta shirya dan ta fita aikin ta kuma a yaudinnan take son fara yin suwa bincike dan gani take sau da yawa ana ha’intar Ahmad ba tare da sanin sa ba.

Shiga ta alfarma tayi da daya daga cikin kayan da malika ta bata light me up tayi tayi rollin kanta da tsiriyar gyale ta fito hannun ta rike da hand bag ɗinta tun kafin ta karasa shigowa falon ƙamshin turen da tafesa yadaki hanci ƴan falon da kallon suka bita dan ba karamin kyau tamusu ba yau”masha Allah malika ta furta tana yaba kyaun da tayi yau,malik kuwa kallo ɗaya tamata ya dauke kai yana taɓe baki da cewa”sai wani zuzutata kuke kalen son yarinya fara raina mutane,dariya hajia ikilima tayi tana cewa”a to mutum koya ƙyasa saide yayi hakuri dan ba bashi diyata zanyi ba.

“Allah ya sauwake wallahi narasa wacce zan so hajia sai wannan kucakar yarinyar,yafada yana nuna Aisha da hannu ku kuke sawa ta raina mutune.

Miƙewa yayi yanufi ƙofa yana kaɗa makullin motarsa”yaya malik dan Allah idan fita zakayi karage mun hanya zazzaƙar muryarta mai dadin sauraro ya daki kunnen sa.

Tsuka yayi”dan Allah yaya malik cewar malika “mutafi amma wallahi idan kin ɓatan lokaci da wannan yauƙi naki tafiya zanyi na barki.

Tunda ya doshi bakin get ɗin ma’aikatan nasu ake ta kallon su dan basaba ganin ta da irin wannan shiga ba,sannan a wani ya kawota da mota kai koda wani namiji daban shisa abun yazame musu kaman sabon abun ita kanta jitake banbarakwai wai namiji da suna larai.

Motar Ahmad ne yadoso tasu tunda ya doshi inda suke tsaye ya kafeta da ido jiyake kaman ya sauka ya hauta da duka dan haushin ganinta tare da wani haka kawai yaji wani mololon abu ta tsaya mashi amaƙoshi.

Shi be zaice yana sonta ba amma duk sanda yabude ido yagata tare da wani ɗan namiji suna hira tasake fuska tana murmushi ko dariya sai yaji wani abu mai kama da kishin ta yataso masa.

Yanzu ma hakance ta faru fashi ganin ta da malik yayi mamaki ba kadan ba ina malik yasanta kode budurwar sace”kai ina ko faisal yaushe yake da budurwa balle malik yaro dashi nawa yake,haka shi kaɗai yayi ta surutansa kaman wani zautacce har ya karaso yayi parkin motarsa daidai khalid daya iso inda suke yana cemata”nagode Allah sister yaude gaki ina kika shigane tsawon mako guda ba sanarwa suhail yana neman kasheni da kira.

Fari tayi da ido tana sake kallon sa tace”yaya khalid ina kwana shima malik yamika masa hannu sukai musabaha sannan ya zagayo suka gaida da Ahmad daya kafesu da ido.

“Ya karatu?
Ahmad din ya tambayi malik”Alhamdulillahi ya amsa masa yana cewa dama wannan kwailar nan take aiki ashe?
“Uhmmm kawai ya iya yacewa batare da yasake kallon inda suke tsaye da khalid dake ta zuba ba.

Shi kaɗai yasan abunda yakeji a zuciyan sa,sallama malik yayi masa yadawo inda khalid ke tsaye yamasa sallama harya kama murfin motar ze bude ya shiga yaji tana cewa”yaya malik injira ka anjima zaka dazo?yanda tayi magana tana wani shagwaɓe fuska sakin murfin motar yayi yayi kanta ai kuwa dagudu ta ranta tayi ciki tana dariya shikuma yakoma yana zan gamu dakene yarinya.

Tana dariya tashiga balcony da ze sadata da ainihin hall ɗin da suke ɗinki batayi aune ba taji an damƙo mata hannu bude baki tayi da nufin kurma ihu kaman yasan abunda zatayi yayi saurin rufe mata baki da ɗaya hannun nasa,gwalo ido tayi waje saboda tsoro dakuma mamakin wanda tagani ɗin.

 

Leave a Reply

Back to top button