Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 52

Sponsored Links

CHAPTER 52

“Waini keda waye? Anty hajia ta tambaya ganin yanda take ta fara’a Anty malika kuwa warce rigan tayi ta warware tana kare masa kallo.
“Hmmm Anty hajia yau ina cikin farin ciki na fusata wani fusataccen mutum daya ɗauka dukiya zata iya saya masa komai saide nanu masa cewa ba komaine zaka iya mallaka saboda kana da dukiya ba.

“Wow wow wow Anty malika keta faɗi sanda ta warware rigar ta ƙare masa kallo nan take taciro wayanta cikin jakanta tashiga duba screenshot da ƙawarta ta tura mata ɗazu datake faɗa mata yana trendin a media yau, cikin zumuɗi takai dubanta ga Aisha tace”kai sis aina kika samu wannan kayan daya kawo wuta a media yau ɗin nan kinga ruwan liking da comment kuwa cikin abunda be wuce awa ɗaya da daurasa ba hmmm kice nice first person da zansa wannan riga ranan dining broz Ahmad nasan za’ayi karya awajen dan harkace ta big big girl tafada tana ƴar dariya.

Warce kayanta tayi daga hannun Anty malika dake ta zuba kaman bishiyar kanya tace”tabb ai kuwa Anty malika saide kiyi hakuri dan bakisan irin gurmin da na haɗa yanzu bane nan tashiga maida masu yanda suka da basma da mahaifinta dakuma gargaɗinta dayayi dakuma kawota gida dayanzu Ahmad din yayi.

Ajiyar zuciya suka sauke dukkan su kusan a tare salati Anty hajia tayi tasanar da ubangiji tana tafa hannu tace”ai Alhaji sunusi inde akan ƴaƴan sane ba zance ba zaiyi haka ba zeyima fin haka dan wallahi watannin baya bakiga wani takadarin ɗansa daya biyo ummu sa’ad ƙanwace ga Ahmad gida wai yana sonta ba,yaya ma’arufa tayi faɗan tayi lallamin amma a banza daga karshe hadashi tayi da Ahmad yamasa jan ido sannan ya ɗauke kafarsa da zuwa gidan daga baya kuma mukaji labarin wai an fiddashi kasar wajeyin karatu niko nace umma ta gaida assha yaro ko anan ma ya lafiyan kura balle kuma anbude masa hannya,haka de Anty hajia yayi ta basu labari karshe ma sai Aishan ce tace”kode zaku fasa fitan mukoma daga ciki muci gaba da hiran mu naga kaman zefi armashi ko?

Yanda takare maganan cikin zolaya yasa Anty malika kaimata dukan wasa tana cewa”oya mutum tashiga ciki tayi zaman yimana gadi kafin muzo aini wallahi nama gode Allah da mutum baze iya fita ko nan da can batare da yanemi izini ba wallahi kunnuwa nama sun futa da jin taƙulla taƙullan nan shima mai jan kunne yaje yanemi daidai shi.

Ɓata fuska Aisha tayi tana kunkunni tayi shigewarta ciki tana cewa cikin ɗaga murya”ai wallahi duk bakin cikin mutum nida suhail mutu karaba takalmin kaza,dan wannan auren na dan uwanki na wucin gadi aini ban ɗauke sa abakin komai ba wallahi”kede kika sanda wannan amma mu namu auren waya faɗa miki na wuncin gadine ai daga nan gidan duniya har gidan aljannan mutum de yadena wani botsare mana dan kardaga baya mutum yaji kunya.

Murguɗa mata baki tayi tana cewa”ana maganan zuman farar tsaka kinzo kina wani…..”yi hakuri Aisha ɗiyata Anty hajiyace ta katseta dafaɗin rabu da wannan Antyn taki danma an musu alfarma idan ba hakaba su harsun isa takara da balarabe shiga ciki kiyi wanka kici abinci kafin mudawo cikin tsigar rarrashi Anty hajiya tayi maganan tana makawa Malika harara.

Zumbura baki Aisha tayi tana cewa”wallahi Anty hajia kimata magana nide,gwalo anty malika tayi tana shiga mota ta barsu dan ita tasan aikin gama ya gama tunda an daura da sannu zaku so junan ku,magana take aciki ranta ita kaɗai.

ALHAJI SUNUSI.

Rayuwarsa ta ɓaci zuciyarsa tayi baƙi wani tukuƙin baƙin ciki kaman ya karsa wai yau shine aka samu wata ƴar mitsiyar yarinya ta tsaya a gabansa take faɗa masa abunda ranta yake so waye ubanta a garin nan shida ko maxa ƴan uwansa jira umurninsa kawai suke cikawa ne nasu cikin gaggawa amma amma sai kuma yayi ƙwafa da jan tsuka mai tsayi yana maida dubansa gefen titi”kaini Al hakk yace da drivern sa,shi kaɗai yasan irin tuƙuƙin bakin cikin da yake ji cikin ransa na gamida da abunda Ahmad ɗin yamasa harma gwara yarinyar dan yasan ƙila ita batasan kowaye shi ba,amma shi kumafa?

Uban sane daidaini bashi karamin mara kunya ba,koda motar tasa da shiga cikin harabar company tunma kafin yafito daga cikin motan nasa Alhaji badamasi ya tunkaro sa yana tabashi hakuri kaman ze zube kasa dakyar da tsuɗin goshi ya hakura da sharadin dole sai yakawo masa Ahmad da yarinyar sun ba shalelen sa hakuri da sauri Alhaji badamasi ya amince da sharadin nasa nan yamasa rakiya yakoma mota tare da alkawarta ma daya koma gida ze tistsa ƙyeyar Ahmad yakaisa har can gidan yabasu hakuri kuma ya mallaka ma shalele rigar da ta bukata ko kuma rankowa ya ɓaci da haka suka rabu.

Hajia mariya koda ta koma gida haka tashiga zarya dan neman mafita,dan kuwa tasan tabbas hajia balki gaskiya tafaɗa mata gwara ta yagi yabonta ashe mata suna can suna juya dala zuwa naira suna hawa jirgi daga wannan ƙasa zuwa wancan da sunan kasuwanci suna murza sitarin mota da sukaga dama amma ita anbarta da yawo da driver abun dubu goma bata iya tama kanta ba sai tayi karamar murya,ashe izzarta da mulkinta duka abanza tunda iya masu masu aikin gidanta take yiwa hamm manya mata suna can inda suke ashe duk wayewa da nake ganin inada ita ashe har yanzu ni baƙauyiya ce ina bara ta saɓuba bindiga a ruwa bara Alhaji yaxo tukunna ta faɗa a fili daidai basma tada fado falon kaman wacce aka jefo tayi cilli da takalmin dake kafarta sannan tayi jifa da jakar hannunta ta faɗa saman kugera tana sakin kuka maikarfi yaune rana ta farko a rayuwarta data taga wani abu takwallafa ranta akai kuma tagaza samun sa kuma har mahaifinta da take tutiya dashi kan komai ze iya sayamata matukar kuɗi ze saya sai gashi tanaji tana gani karon farko a rayuwa kaman wannan alfarin nata bazeyi mata amfani ba.

“Ke wai lafiya kin wani shigowa mutane da kuka kode wanine ya mutu?tambayar da Hajiya mariya take mata kenan ba tare da rarrashi ko lallaɓata kaman yanda tasaba yi mata da ba.

Kawai saita sake fashe mata da sabon kuka tana cewa”yanzu mummy kiganni cikin damuwa amma kigaza rarrashina”iko cewa hajia mariya yanxu ke basma yarinyace da zaki faɗomun falo haka da kuka ni kinsan halin da nake cikine to nima da kike ganina babba yau da zansamu kukan zanyi dan fuce taƙaici……

 

“Ma’arufa ma’arufa Alhaji badamasi ne keta kwallah mata kira kaman wanda ze bar garin,zubur Ammi tamiƙe itako Anty hajia gyara zamanta tayi dan cewa tayi bataga abun tada hankali anan ba tunda tariga tasan kan zance tasan tatsuniyar gizo baya wuci ta ƙoƙi.

Illa kuwa hakane dan ko ida shiga falon beyi ba yashiga faɗin”yanzu saboda yaron nan be daukeni a bakin komai ba nine zanbashi umurni yaƙi karshema dan nayi masa magana ze kira yarinyar nan yamata cin mutunci bakiga yanda ran Alh sunusi yaɓaci dashi bane yau.

Ajiyar zuciya ammi ta sauke tana faɗawa sanan kugera tare da dafa goshinta tashiga kaukawa da numfashinta dan ba karamin firgici ta shiga ba dataji irin kiranda yake mata.

Ina magana kinyi shiru kin mai sheni mahaukaci to wallahi kisani bazan lamunci wannan ba da ran Alh sunusi yaɓaci gwara ran kowama yaɓaci yafaɗa yana huci.

“Iko sai lillahi yanzu shi Alh sunusin ne yace maka Ahmad ya ɓata masa rai a hakan kuma kuke tunanin haɗa zuri’a tsakanin ku wane irin zama za’ayi anan?

Saida yaji muryata ma sannan yasan cewa ashe ba ita kaɗai bace”yauwa ikilima yafaɗa yana nufarta yanzu dan Allah abunda yaron na yayi daidaine?
Kaman zeyi kuka yake tambayarta tare da daura cewa kuma fa shine surukinsa na gobe.

“Hakane amma yah badamasi kamata kanemi shi Ahmad din kaji ta bakin sa dan Ahmad yarone mai biyayya baze so bata maka rai dagangan ba,sannan shi abokin naka meyakaisa shiga tsabgar yara yanzu idan anyi auren ma haka zena zuwar musu gida yana tambayar ƴarsa matsala kai kuma idan ankawo maƙara ƴar siyasar nan ta baka baka iya ba sai ka hau zuciya kayi ta masifa ba tare da ka bincika ba,kowa fa son farantawa nasa yake amma duba kaga yanda kashigo gidan nan a hargitse kaman wanda akace maka Yayah ta zagi iyayenka.

“Ai ikilima hakama zakice yo ba gwara ma’arufan tazagi kaf dangina ta ɓata musu rai data taɓa mutum mai ƙima kaman sunusi kai da kaga yanda yake maganan kasan da iya gaskiyarsa yakeyi dan ba alamun wasa ko sassauci a fuskan sa”ALLAH ya kyauta idan kaga Ahmad ɗin cene mai inason ganin sa tana faɗin haka ta miƙe tanufi hanyan ɗakinta batare da ta ko kalli inda yake tsayen ba.

“Kagani kaɓata ma matarka rai akan wani banz….”kul kika zagesa ikilima dan yanzu sai muhau sama dakene.

 

Leave a Reply

Back to top button