Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 57

Sponsored Links

CHAPTER 57

NAGODE DA ADDUO’IN KU GARENI MASU KIRANA TA WAYA KAI TSAYE DA MASU TURA SAKON KARTAKWANA DAKUMA MASU YIMUN MGN TA WHTAPP ALHAMDULLAHI NAJI SAUKI ALLAH YABAR KAUNA FATAN ANYI SALLAH LAFIYA

Suna gama wayan ta sauke jiki a sanyaye take sanar dasu abunda ke faruwa da mijin yayar tata kowa dake wajen sai da jikinsa yayi sanyi kuma sun kaɗu dajin wai cid aka jedashi wannan yana nufi da cewa case ɗin ba karami case baneba tunda harda su cid aciki”Anty hajia ko zaki kira yah faisal ki sanar dashi abunda yake faruwa cewar Aisha”nima abunda nake son cewa kenan kika rigani inji malika.

Koda Anty hajiya takira wayan faisal cemata yayi yanzu haka suna cid office shida Ahmad amma bawani feedback tunda aka shiga dashi ciki kuma sunnemi ganawa da manya amma babasu wannan daman ba ajiyar xuciya ta sauke kana tace”karka bar ɗan uwanka shi kaɗai katsaya dashi dan ganinka tare dashi ze bashi kwarin gwiwa,amsa mata yayi da In shaa Allah Anty hajia bazan taɓa barin sa shi kaɗai ba duk yanda ake ciki zan kasance dashi,daga haka yakashe wayan.

Yana ɗan kallon Ahmad dayake waya da commissioner ƴan sanda dayake mutumin daddyn sane amma sai ce masa yayi”Ahmad kayi hakuri sannan kuyi ta addu’a ba abunda zan iya yimaku dan case ɗin na Alhaji babban case ne akwai kuma lauje cikin naɗin daga haka ya kashe wayansa yana mai bawa Ahmad din hakuri.

Shiru Ahmad yayi idanun nan nasa sun kaɗa sunyi jajur jijiyoyin kansa sun tashi rudu rudu saboda ɓacin rai,bakin nan nasa yabushe kai kace yashekara besha ruwa ba,case din Alhaji akwai lauje cikin naɗin shine abunda yake ta maimaitawa waye?
Waye wayake son ganin yaɓatawa mahaifinsa suna tawannan hanyan waya zaɓi ɓatasu a idon duniya ta wannan lalle maishi koma wanene yayi babban kuskure.

Dafashi faisal yayi dan ganin yanda yake kai komo yana maganganu yace”lafiya?
Girgiza masa kai yayi sannan ya labarta masa yanda sukai da commissioner shiru faisal yayi sai can ya dago yana kallon Ahmad yace”kai me kafahinta anan?”babu saide inason fahintane dan wallahi nagano koma wanene yakeson jafa daddyna cikin wannan mawuyacin halin saina kasheshi da hannuna yakare magana a fusace.

Murmushi faisal yayi yadaura da cemasa dadina dakai saurin fushi amma katsaya kayi tunani a tsanake zero sai shegen zuciyar banza data wofi yanzu kai baka tunanin da saka hannun wasu ko wani shin baka zargin wani cikin wannan abun?

Shiru sukai duka kaman masu tunano wani abu sai can Ahmad ya dago yana kallon faisal ɗin yace”gaskiya bana zargin idan ma zan zargi wani to Alh sunusi ne amma fa ko shiɗinma bana tsammanin zai ɓatawa daddyna suna ko dan saboda abotansu.

“Hmmm bro kenan irin su Alh sunusi zasu iyayin komai saboda biyan buƙatar kansu yanzu de abu ɗaya nakeson kaimun dan son samun bakin zaren ni kuma zanyi aiki da ƙwarewata dan ganin mun kama duk wani mai hannu cikin wannan case din amma da sharadi”wace irin sharaɗi fadi koma wacece zanyi dan ganin anyi released daddyna kuma an wankeshi a idon duniya.

Gyaɗa kai faisal yayi cike da gamsuwa yace”yanzu de ɗauki wayanka kakira shi Alh sunusi kace ka amince da auren basma dama tsarinsu na tarewarka gidan sa,kallon baka da hankali ahmad yamasa eh ta nan kaɗai zamu samu kama masu lefin a hannu da shi Alh sunusi shike sarrafa cocaine a company ta Al hakk bincikemun yanuna shike amfani da mazuban capsule dakuma tambarin Al hakk ɗin waje guda suka ware suna wannan aikin a binciken da mukai saide bamu da ƙwakƙwaran hujja dazamu gabatar koda mun kamashi.

Cike da gamsuwa ya gyaɗa kansa cemasa zakayi yanzu ga halin da daddayn ka ke ciki kana neman alfarman a ɗan ɗage auren zuwa lokacin da zaa saki daddynka idan zargina akansa daidaine to dazaran yaji haka zaka ganshi ya dawo nan kuma ze tsaya tsayin daka dan ganin yafito da daddy yau din nan tunda yasan manya sosai.

Alhaji sunusi zaune suke a guest house ɗinsu suna shakatawa gefe guda kuma ga ƴan mata nan birjik suna sha’aninsu wasu na tikar rawa wasu na zazzaune suna zukar shisha wasunsu kuma na ƙwaƙulal junan su gefe kuma samarine matasa manyan Alhazawan nan ke hakewa ba kunya ba tsoron Allah,Allah yakiyashemu wayan Alh sunusi ce tayi ringin yana kaganin mai kiran nasa saida ya kwashe da dariya kaman wani boss yace”yaro man kaza sannan yayi pickin call ɗin yakara a kunnen sa”sallama Ahmad yamasa amsa masa yayi kaman bayason amsawa ya daura da cewa”ya iyayen naka?rintse ido Ahmad jin tambayan da yamasa daurewa yayi yace”suna lafiya yadaura da cewa dama nakira na sanar dakaine ina bukatan a karamun koda sati daya saboda matsala da daddyna nake ciki kafin sannan ƙila musamu ko a warware idan komai ya daidai ta satin sama sai a daura auren idan yaso zuwa weekend idan baƙi sun watse sai natare a gidan naku kaman yanda kabukata”wace matsala Alhajin ke ciki?muna nan ai bazamu bari ya tozarta ba yanzu faɗamun meke faruwa da Alhajin yafaɗa ai abunda yashafi Alhaji yashafeni koba komai shidin abokinane sannan mutumin kirkine shi yanda yake tambayan kai kace kuka zeyi nan Ahmad ya labarta masa abunda ke faruwa da inda suke ba kunya ya kaɗa baki yace dayake rabona da sauraro ko new paper tun shekaran jiya bansan abunda ke faruwa ba amma gamunan yanzu zamuzo kuma in shaa Allah yau Alhaji gida ze kwana ai wannan tozarcine kashe wayan yayi yakai dubansa ga abokan sa yana washe baki yace plan A tayi yanzu zamuje ga plan B get ready to play yanzu wasan yasoma.

Cikin abunda be wuce minti ashirin ba su Alhaji sunusi da muƙarraban sa suka hallara a cid office yana fitowa daga cikin motarsa waya kange a kunnesa sai magana yake a fasace sude su Ahmad sundeji yana cewa”Alhaji badamasin ne baku saniba kode kawai kunason tozarta shine bana bukatar hakurin ku kawai ku hadani da manyan ku yanzu gani nan harabar wajen yana kare fadin haka yakashe wayan yanufi inda ya hango su Ahmad”wanene na kusa da Ahmad din nan ya tambaya?”wannan ai shine faisal din nan jami’in da kadade kana nema Alh shehu ya amsa masa”wace alaqa ke tsakanin sa da Ahmad din?”kila ta abotane yanzun Alh bala ne ya amsa da fadin haka.

Koda suka karasa hannu suka mika musu cike da ladabi da biyayya shikansa Alh sunusi yaji daɗin yanda yaga Ahmad din yabashi girma ko ba komai yasan aikin da akai masa yasoma kamashi dariya yayi aransa yana cewa sai na juyaka kaman waina a tanda kai da uban ka,amma a zahiri yanu alhinin da rashin jin dadin abunda yafaru da Alhajin yakuma ce in shaa Allah yanzun nan zafito dashi waƴan nan yanuna Alh shehu da Alh bala yace manyan membobine a ƙungiyarmu muna cikin meetin ɗin karshen wata kiranka ya iskeni shine muka katse meetin din mukazo nan dan wannan ba abunda zaka zauna kace sai daga baya zaka zo ba dan shi kansa Alhaji ba mutum daya bane idan wani abu yasamu dan kungiyarmu koda matashine tsayuwa yake sai yaga komai ya daidaita sannan hankalin sa ke kwanciya”ai Alhaji ba mutum ɗaya bane wajen nuna tausayin sa ga waƴanda suke tare dakuma taimakonsa ga kungiya cewar Alh bala”wannan haka yake Allah de yakare shi yakuma shiga tsakanin sa damasu son ganin bayan sa cewar Alh shehu Amin su Ahmad suka amsa sauri zungurin sa Alh sunusi yayi yana masa alama da ido mecece na addu’an.

Zuwan su ba jimawa sai ga Alh badamasi da mutanen da suka je gida suka zo dashi sun fito dashi suna ta bada hakuri kan kuskure sukai rai ɓace Ahmad ya kalle su yace”bawani kuskure da kukai saide ku faɗawa shi wanda yasaku cewa da Allah muka dogara kuma da yardan Allah baze taɓayin nasara akanmu ba idan yana da wata bukata to yatun ƙaromu gaba da gaba wannan shi ze nuna shidin namijine bawai sari kanoke ba kuma wallahi ko da wasa wani daga cikin wannan hukuma taku tasake taka ƙofar gidanmu bada wata ƙwaƙƙwaran dalili ba wallahi kotu zata rabamu dashi dan ko yanzu cctv na tanaɗi komai kuma zan ajishi hujja saboda gaba daga haka yayi gaba yabarsu baki sake shikansa Alh sunusi dake rugume da Alh badamasi yana nuna murnan sa amma hankalin sa yanaga maganan da Ahmad din keyi da mutanen wannan yaron wannan yaro anyi hatsabibi yafiɗi haka yafi a kirga a ransa.

*******
“Ammi amshi ruwa kisha ki ƙwantar da hankalin ki in sha Allah yanzun nan zakiga daddy yadawo karɓan ruwan tayi ta kurɓa tana cewa”ɗiyata Aisha ni ba kame Alhaji da akaine damuwata ba damuwata ɓata masa sunanan sa data sana’arsa daya ɗau shekaru yanayi yasha wahala kafin yataka wannan matsayin amma lokacin ƙanƙani wani yazo daga sama yaɓata masa suna kinsan abun da cin rai.

“Hakane ammi amma idan kika fauwalawa Allah komai kika miƙa masa da ƙogon baranki sai kikaga ya amsa miki addu’arki kuma kinsan addu’ar mata ga mijinta addu’ace karɓaɓɓa dakuma iyaye ga yaransu musamma uwa idan kika dage da kaiwa Allah kukanki dakuma yawaita sadaka sai kiga komai yazo da sauki.

“Gaskiyarki ɗiyata kin sake tunatar dani abunda namanta in shaa Allah zandage dakaiwa Allah kukana nakuma gode da Allah daya bani ke matsayin surukuwa fatan zaki zauna da Ahmad kikuma karɓesa matsayin miji dan inaji ajikina zakuyi farin ciki da wannan haɗin namu naga…..rufe fuskarta tayi da tafin hannunta cike da kunya”wai yaya me kuke tattauna da ɗiyarki haka sai faman rurrufe fuska take Anty hajjia ce ke tambaya tana kokarin zama ganin yasa Aisha miƙewa ta zura ɗaki da gudu daidai su faisal dake shigowa falon da sallama miƙewa Ammi tayi ba tare da jin nauyi ko kunyan kowa ba tanufi Alhajin ta tarungume sa ta saki kuka…

Leave a Reply

Back to top button