Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 39

Sponsored Links

 

 

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/19, 9:04 AM] +234 701 497 9567: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

3️⃣9️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

  Kusan sau uku ana
zuwa nemana a gidan ban fita ba bansan ya akayi wani cikin samarin ya samu
layin wayata ba ya dameni da kira karshe kashe wayan nayi gaba daya.

   Gwaggo Ai ce ke
fadin wai baki son muyi siriki a kano ne kome ya hanaki fita indai don mune ki
tashi ki fita abinki tunda mu ba jikaki zamuyi musha ba a gida.

    Sai gwaggo shafa
kece mata indai mamace ai kyayi kya gaji ki bari don ba fita zatayi ba nina
taba ganin yarinya irin haka da bata kula kowa a gida.

    Sai matar baffan
mu guda naji tace a,a wallahi wace indai mamace tana da mabidin ta hala kin
manta fadan da akayi dakin hjy ne da uwarta da hjy maimuna.

    Ai maganan har
gaban su Alh yakai kuma an kira saurayin Allah yace baiji dadin yadda officer
yayi mashi ba don yace yaci zarafin yaron sosai a ranan kuma nasan an zugashine
tunda ba halinshina ba hakan ?

   Ke yaushe ankayi
haka bamu da labari gwaggo shafa ta fada cikin mamaki matar baffa din tace ai
gata nan ku tambayeta ku jiya ai tasan komai da ankayi.

   Gwaggo shafa din ta
dago tana fadin wai haka ankayi maamah murmushi kawai na sake a fuskana ta
gyara zama tana fadin wallahi sam ban san anyi wagga maganan ba.

  Keko ina zaki sani
maganan suta ta maza ai sunkayi tsakanin komu mujiya ran Alh gidan mune da ya
baci shina har munka sani yake hwada muna.

   Shi yaron dan
wanena a cikin gusau gwaggo shafa ta tambaya to ai shina yakawo maganan mamanta
fada taci gaba da fadin .

    Wai ance yaron
baida usuli, ke ke ke kibar wanga zance don Allah ?

    Gwaggo shafa ta
fada da sauri tace badai fadin mutane na ba yan hana ruwa gudu .

   Sai gwaggo shafan
ta juyo inda nake tana fadin keko maamah ashe yaya yafi gaskiya a,a kika jawo
muna mara asali mu hada iri dashiya.

   Ke wah hwada maki
walle da ubane hwa hwadin mutanena kawai in baka da komai yanzu duk wani sherin
duniya daukowa akai a dagwara makashiya.

    Ance dai tun yana
goye a baya ubanai yai tahiyatai kasan su yabarshi bai dawo garai ba ,har yau
shina fa matsalan yaron dai da mutane ka hwadi .

   Amma walle da
ubanai ba shege bane ke dan gidan malam ladan na kwanan maigemu labil labil
mana ai kesan yarshi Rukkaiya dai da aka hwadin boko tta aura dauri ya gudu ya
barta da goyon da nai ?

    To shina hwa aka
magana nai yanzu ko ance shi office ya hwa sosai don wadda Alh ka hwadi ko
saurarenai bayi ba a ranan ya kira yaron ya hwada mai ko sabulun wanka maamah
bai mai jari.

  Jin hakan yasa na
dago kai da sauri na kalli mataAbbane ah nawa dake bayani wani iri naji har
cikin raina don kalamin bai mun dadi ba quit oright nasan cewa Ahmed dai dan
tallakawane.

   Amma kuma baisan
mahaifin shi ba ake nufi ko me gashi muyi waya dashi last yace min yana hanya
zai tafi wajen mahaifin shi.

   Ko dai mama ta zuga
Abbane don kawai ta bakanta min rai idan ko hakane har sheri tayiwa Ahmed din
bazan taba rabuwa dashi ba a rayuwana kuwa sai naji gwaggo shafa na fadin.

    To in Allah yayi
mijintana da ya hwadi mai wanga magana haka a a zaiyi da kunyane gaba baka sone
da yarka ka sallameshi kawai yayi tahiyane amma ka hwada ma mutum irin wagga
magana haka babu dadin ji.

   Tsam na mike na bar
wurin don ba zan iya ci gaba da sauraren su ba a lokacin dakin mahaifiyar mommy
da muke kwana na nufa babu kowa a dakin don haka na samu wuri na kwanta abina
ina tunanen mafita a garemu.

    Gashi duk kwanakin
nan idan na kira Ahmed din wayan shi baya shiga har hakan ya fara bani tsoro a
raina don bansan halinda ake ciki ba dashi.

    Sai can zuwa dare
maryam ta shigo dakin ta sameni kwance take fadin au ashe kina nan nayi zaton
kina can gun yan uwanki ai yasa na zauna dakin su mommy muna hira.

  Kafin in bata amsa
mommy ta fado dakin tana fadin Zahra ashe baki fita wurin yaron nan ba kika
shanya shi haka a waje sanyi na dukan shi.

    Yaron nan fa dan
gidan manyan mutane ne bai fito gidan banza ba wallahi da nasan tun dazun baki
fita wajen shiba da nazo na fita dake da kaina yarinya arziki na kiranki kin
tsaya tsiya kada kiwa kanki tsiya wallahi kowa nason yazo wurinta kaf taron nan
amma ya ganki yace ke yake so.

    Mommy nifa ko gida
bana kula samari kin sani barshi kawai ya wuce eh bakya kula wasu dai kinfi son
irin samarin ki da kike tarawa yan karya masu tsamin hammata.

  Wani kallo na dago
nayi mata na mamakine kona tsana ban sandai zan iya mata irin kallon ba tana
ganin haka ta juya ta fita daga dakin.

   Hayene suka biyo
fuskana lokaci guda ban kara magana ba na koma na kwanta sai maryamce ke fadin
aina fada maki wallahi mommy karima bata da dadi ko kadan.

  Taso tayi amfani
dakene ta samu kudi don ita kudi baya isanta yadda kike da kyau din nan yasa ta
daukoki tazo taci kasuwanta a nan dake .

  Haka takeyi dasu
small mum tana amsan kudin samari a wurinsu tana ganin kamar ba a gane me
sukeyi ba dasu.

   Har tayi ta kare
zancenta ban taka mata ba sai gyara kwanciyana dana ina danasani yafi dubu a
zuciyana na biyota da nayi har taso ta gurbata min rayuwa naki shine ta aza min
sherin kazafi kuma.

    Bin ko ina na
gidan yakeyi da kallo yana mamakin ikon Allah yadda aka narka kudi akai aiki
haka aka zuba a kasa kuma wai maishi bai faye zama a cikin gidan ba akace.

    Bai kai ga kare
mamakin shi ba yaji masu tsaron kofan na mashi sannu da zuwa suna kallon junan
su tare da fadin ka shiga daga ciki yallabai sannu da zuwa.

    Suna wani bashi
girma suna kus kus a tsakanin su amsawa yayi ya kama hanya  kamar zai shiga dan bayaro ya dan jawoshi
yana fadin kai baka da hankaline malam kasan inda zaka shiga kuwa ?

   Nan fa ba gidan
wasan yara bane idan kana karban dan abinda zai bayarne kaje mubi layin can har
layi yazo garemu mu karba mu wuce zaifi muna sauki kada ka jawo a lankada muna
dukan tsiya a wurin nan yanzu.

    Zan karba ko dan
naga Alh da idona amma ba don nayi amfani da kudin shi ba ya fada can baya
kadan ya tsaya duk wanda ya ganshi a layin sai ya danja baya ya bashi wuri.

    Har wa yanda ke
kula da layin suka farga da hakan suna duban shi sai da suka kadu kallon tsab
sukai mashi suka koma gefe suna magana kafin dayan yazo ya nuna shi yana fadin
zo ka shiga cikin tsarguwa da ganin shi.

    Ya dan gyara rigan
shi da kyau ya kutsa kai cikin falon da ake shiga din wani sanyi ya daki
fuskanshi ga kamshi dake shiga mai hanci wani farin mutum ya gani a zaune wanda
baiyi tsammanin haka zai ganshi ba.

   Yana zaune saman
kujera ta alfarma ya baza babban riga a jikinshi tana maiko sai kamshi ke tashi
ga tulin kudi yan dubu dubu dari biyar biyar da dari bibiyu ko wani layin su
daban .

    Yana waya a
lokacin Ahmed din ya tsuguna a gaban shi har saida ya kare wayan ya juyo yana
fadin ehe saiwa kuma ?

   Sukai arba da juna
ya kalleshi tsab kamar yadda shima shi yake kallo kamar zaiyi magana sai kuma
yayi shiru ya mika hannu wurin yan dari biyar biyar ya dauko dubu ukku ya miko
mashi.

   Ya mika mashi kai
ya girgiza mashi yace bashi nazo karba ba nazone na gaida ka in fadama cewa yan
zamfara daka bari suna gaida kai sun gode.

    Yana fadin hakan
ya mike ya fita sai kallon mamaki ya barshi dashi zaune wanda suke tare yace ka
sanshine Alh ?

    Kira min shi kawai ya iya fada ya mike da
sauri suka fito saidai babu Ahmed din babu labarin shi don yana fita ya ja dan
bayaro suka haye mashin zuwa unguwarsu.

   Tambayan duniyan
nan dan bayaro yayi mai sai cewa yayi a karshe yace kudin sun kare inyi hakkuri
yace kai amma dai bamu da rabo wallahi.

   Ai yau da muma mun
dangwali arziki munci zakkanshi don ban taba yin dace da yazo ba yana rabon
kudi sai yau amma zan kama zagaye in gani ko zan dace watarana nima in samu.

    Suna zuwa dan
bayaro yashiga mashi godiya shima gode mai yayi ya shige gida kai tsaye ya samu
inna shattu tana sharan tsakar gidan su ya gaida ita yana kokarin karban
tsintsiyan a hannunta.

  Tace ya barshi shi
namiji ina shi ina shara kuma ta kara da fadin hankalin mallam ya tashi yanzu
ya fita ya dubaka yaga kun dafe baku dawo ba.

   Ga abinci can a
rufe ka zauna kaci yace zanci inna amma saina gama shara zan zauna inci dole ta
sake mai tsintsiyar ya karba ya fara sharan gidan .

  A haka malam musa ya
dawo ya sameshi da mamaki ya karaso yana salati yace jam jam jam shattu bakona
kika bawa shara yana da namiji dashi.

  Haram gashi nan sai
Ahmed din yace nina karba a hannunta baba bata so hakan ba itama au ce nake dai
ita ta nemi ka taimaketa ai kasan halinsu na mata.

   Tas ya share gidan
saida sukai mamakin hakan ya gama kuma ya koma ya gyaro bandaki kafin su farga
ya fara cika randar ruwan su na gidan.

   Saijin karan zuba
ruwa sukaji don duk kwanakin shike tashi da safe ya cika masu ko ina nagida da
ruwa malam musa yayi fadan hakan amma ya roko malam musa din da ya barshi ya
diba don Allah.

   Bai samu kanshi ba
sai bayan sallah isha,i daya dawo lokacin ya zauna ya dan tsankwari abinci
kadan don bai iya cin komai a lokacin saboda yadda yake jin zuciyarshi na mashi
zafi. 

  Dan aikin dole yayi
ranan da gaiya don ji yake zuciyar shi na shirin buga mashi zazzabi ne mai kada
mutum ya buga mai nan take ya fara rawan sanyi sai amai kuma ya biyo baya.

   Hankalin mutanen
gidan ya tashi sosai da ganin hakan malam musa ka  fada yakewa Shattu cewa aikin da yayi ne yaja
mashi hakan.

   Da kyat ya bude
baki yace ai da zazzabin ya kwana zuwa safene yaji saukin shi shine yanzu kuma
ya tashi mai fita maigidan yayi ya dan jima sai gashi ya dawo da ledan magani a
hannun shi.

    Ya dan sha ya samu
ya kwanta sai barci mai nauyi ya daukeshi bai kara falkawa ba ganin haka suka
fice suka barshi ya samu barcin lokacin.

   Nan hankalin kowa
dake wurin ya tashi ganin yadda hankalin maigidan nasu ya tashi lokaci daya
haka gashi duk wanda aka tambaya ina yaga yaron nan yabi sai yace dashi ai bai
ganshi ba.

  Sai wani mutum
dayane yace yaga sun bi nan da sauri sun tafi amma bai kula da hanyar da suka
bi gaskiya.

   Kudin da baici gaba
da rabo ba ke nan ya juya ya shiga gida a rikice ba tare da yayiwa kowa bayanin
abinda ya faru ba.

  Dakin shi ya shige
yasa key bai sake fitowa ba donko matanshi basu ganshi ba a ranan sai washe
gari yadda yaga dare haka yaga da safiya don ya kasa barci yana son tuno
abubuwa da dama a rayuwan shi game da yaron nan amma ya kasa hakan.

    Daga cikin makarraban shine aka samu wanda
ya tseguntawa matanshi abinda ya faru hankalin ta farkon ne ya tashi sosai don
tunawa da abinda bokatan ya fada mata cewa.

   Kada ta yarda suyi
ido biyu da yaron don duk ranan dayayi arba da wanan yaron asirin kwalban daya
bata din zai kare .

  Ba komai bane kuma
sai adana duk wani tunanen shi kan yaron daya fada yana dashi a can inda ya
fara zama din daya bata.

   Sai gashi yau duk
da ba a tabbatar ba an fada mata wani mai kama dashi yazo gidan har yaga Alh din
inda hankalinta ya dan kwanta mai bata labarin ya fada mata cewa ai sam basu da
kama ko ina da yaron na jini.

    Hakan yasa ta
kwantar da hankalinta tayi barcin ta harda nasari washe gari kuma tana tashi ta
shige zuwa yola wurin buki dama shi suka shigo yi.

    Don haka bata
dauki wanan da cewa komai bane ta dauka gajiyane ya kama mijin nasu sai bayan
tafiyantane balli ya tashi don Alh ya tubure kan cewa lalai danshine ya gani a
jiya yazo gidan  nan.

  Abu tun matarshi ta
biyu tana daukan hakan wasa har yakai ta bugawa yan uwanshi waya tana sheda
mashi suzo babu lafiya fa don bata gane kan mijin nasu ba yau.

    Bayan sunzo ne sai
gashi ya fito falon suka gaisa nan suke tambayan shi meke farune wai ya dan
murmusa yana gyara zama tare da fadin.

   Yaya sale nayi
sakaci da yawa sosai don tun dawowana garin nan na fada maku nayi aure a can
har matar ta haihu dani mun haifi da daya.

   Amma kuma sai wanan
zancen ya fita min rai ga baki daya don ban taba zancen yaron nan ba daga baya
ma sai na manta dashi sam ga baki daya a zuciyana.

  To jiya yaron nan ya
biyoni suna jin hakan suka fara kallon junan su kamar suna zargin ya tabune don
dama zargin da sukan masa ke nan wani lokaci tunda ya taba barin gida da girman
shi.

   Yace kwarai don
yanzun haka zancen nan da nake maku yaron nan yana cikin garin nan tare damu
sai dai bansam a ina yake da zama ba.

    Don jiya yazo nan
wurin amsan taimako tabbas akwai kama sosai dani dashi dayasa na danji faduwan
gaba lokacin dana kalleshi .

   Amma kuma abinda ya
fada min kafin ya fita shine ya tabbatar min da cewa shi din ne dai ya biyoni
garin nan don cewa yayi.

   Sai kuma yai shiru
ya dukar da kanshi kasa kamar yana tunane ko takaicin abinda zai fada jin
shirun yayi yawa daya daga cikin su yace muna jin ka .

   Dago kai yayi da
niyar magana amma kuma hawayen da suka zobo mashine suka hanashi magana suma
jikin sune ya mutu don ganin halin da dan uwan nasu ya shiga ciki a lokacin sun
san ba karamin zance bane wanan.

Leave a Reply

Back to top button