Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 6

Sponsored Links

Chapter 6

“Aisha lafiya muke irin wannan gudu kaman waƴan da akace munyima sarki sata?”hmm fadila bazaki gane bane?”to ki fahintar dani mana ta yanda zangane kuma wannan da kike gudun sa wayeshi?

“Ɗan Hajia bilkisu ne na amsa mata ina samun gefen wani bishi nakai zaune ina haki,itama zaman tayi tana maida numfashi tasake cewa “wai kan wani dalili kikasa mukayi wannan uban gudun?dariya nayi mata kawai dan son kawar da zargi nace”ke marina ya taɓayi kuma kinsan banason abunda ze taɓamun lafiyata.

Dogon tsaki naji tayi tace”amma de anyi matsoraciya wallahi kikasa mukaci uban gudu haka nadauka ma wani abunne da nasan hakane wallahi dan banci wannan uban gudun ba,takare magana cike da jin haushina nide hakuri kawai narinka bata har nasamu ta hakura.

“Mummy gaskiya kiyi wani abu dan kar narasa guy ɗinnan wallahi inason shi takare maganan tana marairaice fuska murmurshi Hajia mariya tayi tace”kede kibar komai a hannuna ai bakida wani miji sama da Ahmad ko uwar da takawoshi duniya bata isa ta hana wannan auren ba,kede abunda nakeso dake duk wani abunda kikasan ze burgeshi kiyi sannan kiriƙa kai masa ziyara office ɗinsa tanan ne zaki saka ido a kansa inma so kike kikoma da aiki can inda yake kinga sai inma mahaifinki magana kinga hakan ma wata damance ta yanda zaku kasance kullum tare koya kikace?tsalle tayi tadire cike da murna ta rungumi mummyn nata tace”wayyo mummy wallahi wannan shawara tayi dan kinga tanan ne zan samu daman nuna masa soyayyata.

“Dot kasan fa gobene zamu fara ɗaukan sabbin ma’aikata ko?numfasawa yayi dayin ɗan tsaki”ai basai nazo ba kaima zaka iyayi”saifa kazo dan tantance masu ɗinki kasan wancan karon da kabarmun aiki yamun yawa daga baya ansamu matsala dan haka gobe karfe 8:00am yazamana kana office dan wannan karon akwai tsala tsalan ƴan mata ko zamu sami wata mai sa’a tayi mana wuf dakai,yafada cike da zolaya banza Ahmad yayi dashi dan shi yanzu hanyan da zebi ya gujewa aurensa da basma yake nema kwata kwata yarinyar bata daga cikin tsarin matan da yakeso.

“Wash Anna mungaji wallahi”salamu alaikum anna barka da gida.
Wa’alaikum salam fadila sannunki kinji ƴar albarka kwalo fadila tama Aisha”au anna dan banyi sallama shine kika sanya mata albarkar ita ɗaya”eh hakane kinko canka daidai.

Aisha Allah yashiryeki inba lalaci ba nan da gidan hajia bilkisu shine zakice kingaji?kafin Aisha tayi magana fadila ta amshe da Anna ba dole mugaji ba kinga yanda tasa muka dinga gudu kaman marasa gaskiya”kai Aisha kina girma amma kina daɗa maida kanki kaman wata karamar yarinya”gwarade ki faɗa mata Anna dan bakiga gudun famfalakin da makasha ba.

“Ba dole muyi gudu ba kinfi kowa sanin koda can yanda banason taɓamun lafiyar jiki shisa koda yaushe nake kiyaye latti zuwa makaranta,riƙe haɓa Anna tayi tace”oh niƴasu Allah de yashiryeki Aisha ta wannan tsoro naki dan kika bari akasan logonki wallahi haka kawai zaki bewa wasu hanyan tsorataki.

Suna cikin hira Maman Abba tayi salam tashigo amsa mata sukai Aisha da fadila na rige rigen amsan ƴar karamar ƴarta mai suna yusra,dariya maman abba tayi tana samun gefen tabarma ta zauna suna gaisawa da Anna nan suma su Aisha suka gaisheta daga nan maman abba ta kalli Aisha tace”nikan Aisha kwanaki kinfara tafiya shagon hafiz dinki yakuka kare haryanzun kina tafiya ko ya?”tab hmmm maman abba ai sau ɗaya taje dan iska tantiri mai riƙe hakkin mutame katse fadila nayi nace”haba fadila dena irin wannan zagin ai sai kasa mudauki zunubi madadin kawai kibada amsa kai tsaye.

Na ɗan juyo na kalli maman abba nace”wallahi sau daya kawai naje amma bansake zuwa ba,dan jiyama yazo yana bani hakuri akan nakoma shagonsa nace bazan sake zuwa ba,kumama kinga yanzu haka ma daga gidan hajia bilkisu nake wai kawarta hajia mariya taso naje gidanta narikewa mai aikinta aiki har tadawo daga tafi.

“To Aisha wani hanzari ba gudu ba amma kafin kije can ɗin mai zai hana ki gwada zuwa can ma’aikatan su Baban abba kinsan suna da fanni daban daban to gobe suna son ɗaukar sabbin ma’aikata fanni ɗinki ko zaki gwada sa’anki dan wallahi idan kisamu nan kin haye suna bada albashi mai tsoka ta yanda zaki samu daman kula da anna harma da makarantar su khadija koya kika gani?

Kan nayi magana anna tace Allah yazaɓa mana abunda yafi zamowa alheri”amin muka amsa baki ɗaya,nan muka barsu nan tsakar gida muka ƙule ɗaki da fadila muna shiga taciro wata dan ƙareriyar waya tare da kuɗi masu yawa ta nunamun.

Zaro ido nayi nakarɓi wayan ina kallo baki sake kan nace”fadila ina kika samu wannan waya bade sata kika fara ba?dariya tayi tana dafani tace”ko daya kawata wallahi wata babbar harkace shisa nakeso kizo mu jone amma naga ki haryanzu kaman kanki a tukunya yake duba kigani jiya wani Alhaji da muka haɗu dashi yabani harma da kuɗi dubu ashirin yace nasaka kati kinma gansu nan.

Jiki a sanyaye nace”fadila gaskiya bazan ɓoyemiki ba dan bani da ƙawa sama dake tun muna yara haka muka taso duk inda akaga ɗayanmu to ɗaya nakusa amma wannan hanya dakika ɗauka bamai ɓollewa bace ba.

Fadila kalli irin rayuwar da kuke wallahi kinfini gata tunda ke kota halin ƙaƙa mahaifinku zai nemo baze bari ku kwana da yunwa ba”amma mufa?sai anna ta fita zata samo mana aikatau wanki ba wanda bamayi duk de dan murufawa kanmu asiri fadila kar abun duniya da tsanar da kikewa talauci yajefa rayuwa cikin ha ula’i.

“Au Aisha yanzu baƙi ciki zakimun dan kinga naci gaba ashe kima kina daga cikon waƴanda zasu nuna basason ganin cigabana to ai shikenan da naɗauka zakifi kowa farin ciki da cigabana”ayya fadila dan Allah kiyi hakuri wallahi banyi dan inuna baƙin ciki kan cigabanki ba wallahi zanfi kowa farin ciki kawai de gani nake kaman dan nuna adawarki da talauci my fadee ta kauce hanya dan tafaso gari nakare maganan cikin tsigar zolaya dacewa yauwa tashi muyi photo muma kaman sauran mutane kinsan andade da barinmu abaya dole tasaki ranta mukai photona masu yawa amma har kasan raina bana farin ciki da wannan sauyi na fadila lokaci ɗaya dan gani nake kaman bata hanyan mai kyau tasamu ba.

Washe gari
Tun karfe 7:30 nafita daga gida bayan munci ɗumamen tuwo nama anna sallama fatan samun nasara tamun ta miƙamun naira ɗari tace nahau napep karna makara.

Doguwar riga ta shadda light blue nasaka ire iren kayanda hajia ikilima kan bani tuɓensu hijabi ma da takalmina da jakana duka fari nasa banwani wahala samun wajen ba,dayake wajen sanannen wajene mutane da nagani tabbas yasaka zuciyata karaya saboda yawanmu har wata zuciya tana cemun nakoma gida kawai bazan samu ba.

Karfe 8:00 daidai aka bude mana wani ƙaton hall kekunan ɗinki a ciki sukai ɗari biyar ga fankoki ko ta ina kaɗawa suke shiga mukai kowa yasami waje ya zauna nayi mamakin ganin duk yawanmu da nake gani amma wajen ya dauke mu harma kekunan dayawa yarage.

Zamanmu befi miti biyar ba sai gawani ƙamshi mai daɗi daya doke mana hanci tun kafin maishi ya ƙaraso wani haɗaɗɗen matashine yana tafiya irin na zaratan maza sallama yayi mana muka amsa kai ɗaya sannan yafara jawabi kaman haka.

Sunana Ahmad kuma nine mai wannan wajen matsayinku na matasa ƴan uwana inason kawannen ku yamai da hankalin sa da nutsuwar kan abunda zeyi yanzu za raba muku hotunan ɗinki kowannen ku saiya zaɓi kayan da ze dace da ɗikin fatan nasara yamana harzai juya yasake juyowa ya kalleni akai dace nima shinake kallo karaf mukai ido hudu dashi take natuna rashin m danayi masa kwanaki daga taimako mukut na hadiye ƴawu.

Warning yamun da ido take tsoro ya dabai bayeni duk kan ilahirin jikina ba inda baya rawa can yana fita wasu yanmata suka fara bara hoton ɗinkuna da zamuyi kowa ana bashi idan an baka sai a ɗauki sunanka dakuma numbar keken ka miƙomun nawa akai ina kallon ɗinki take wani irin zufa yakaryomu tun daga tsakar kaina harzuwa yatsan kafata hanyan guduwa kawai nake nema dan nasan da gayya aka bani wannan ɗinkin mai shegen wahala.

Masu karatu
Karfa kumanta wannan littafin nakuɗine idan kina kibiya ɗari 300 dan karanta labarin har karshe.

ALLAH YASA MUDACE
[5/2, 8:34 AM] Xeenat: 💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Leave a Reply

Back to top button