Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 68

Sponsored Links

CHAPTER 68

Shiru Ammi tayi badan tasoba ta zubawa ƙanwarta dake kwance saman gado ido duk ta rame ta zube lokaci guda kaman wacce ta kwanta jinyar kwanaki,sauke ajiyar zuciya tayi sai kuma ta kalli Ahmad dayayi zuru da faisal dake gyawa mahaifiyar sa kwanciya tace”yanxu ya’ake ciki?
“Eh Ammi yanzu haka nayi report tun tuni harma an baza jami’an tsaro dukkan nin madakatai tashan mota harma da airport jami’an mu na nan dakuma dukkan nin checkin point faisal ya amsa mata da faɗi haka.

“Allah ya bayyanar da ita yasa asame mata cikin aminci da salama”amin suka amsa”su kuma waƴan da suka ɗauke ta Allah yatoni asirin hegu”hmmm ƙwafa Alh badamasi yayi haryasa kai ze fita sai kuma yatsaya jin Ammi na tambayan Ahmad”kai meyakai ka tafiya da ita wajen shagalin su,bayan kasan uban yariyar nan yayake yanzu a wani hali ma ƴar mutane keciki?”shin tana hannu nagari kokuwa?Ahmad ina jin tsoro gaskiya bazan ɓoye maka ba ina jiyewa ƴar nan tsoron wa annan azzaluman sai kuma ta ɗaga hannun ta sama tana tacewa ya Allah ga baiwarka nan Aisha hannun ɓata gari ya Allah karka bawa duk wanda yakeson ya cutar da ita dama,karka basu daman da zasuyi galaba a kanta.

“Wai ke ma’arufa mekike nufi da Alh sunusi ne?nasan duk wannan abun washi kikewa,shin wani abu yataɓa haɗaki dashine?kinfa saka bawan Allan nan gaba haba haba ko dan suru….ɗaga masa hannu tayi bata bari yaƙare maganan sa ba tace”yanzu me nace Alhaji fisabilillahi kokaji na ambaci sunan wani anan sai kuma ta juya ta kalli Ahmad tace mundin ba’asami ƴar mutane ba wallahi kadeji na rantse maka ko ƴar sarkin makka ce jibi baza’a ɗaura wannan auren ba.

Dasauri Alh badamasi ya juya yana kallon ta baki buɗe shide Ahmad be’iya cewa komai ba saima ƙasa daya sakeyi da kansa dan shi kadai yasan abunda yakeji acikin zuciyar sa.

Basma saida tayi kukanta taƙushi sannan ne salaha da tunɗazu ke bata baki tasamu daman ta kulata tace”yanzu me wancan kucakan take da wanda ni bani dashi,eh salaha kiga yanda mine ya tozartani a bayyanan nasi?ai wannan ma tozarci ne ke kinsan irin yanda nariƙa cika baki a cikin ƙawayen mu amma abunda zemun kenan irin sakayya da ze mun kenan dan yaga inason shi nasan tunda yace bazezo ya halarci partyn mu ko ɗaya ba matsawa danayi akan sai yazo na haɗa da daddyna yama daddynsa magana yazo shisa yamun haka ba komai taƙare magana. tana share guntun ƙwallan idon ta”amma ke yanzu bade kina nufin daga shi har itan sunci bulus ba?kallon salaha tayi tace”ban gane mekikeson kice ba?”ina nufin yanxu tashi zamuyi idan akwai kuɗi a hannun ki muje wajen wani malami da zeyi mana aiki akan sa dama ta ita yarinyar ta yanda koda akwai wani alaqa tsakanin su a raba adasa musu tsanar junan su a zukatan su sannan a dasa soyayyarki a zuciyar sa ta yanda zeji duk duniya ba wanda yakeso da kauna sama dake koda uwar da ta haifesa sai abunda kikace zeyi mata.

Hmm tasauke ajiyar zuciya basma tayi cike da jin daɗi abunda salaha tace saide zuciyata taso rabuwa kashi biyu ɗaya zuciyar tata na hani gareta yayin da ɗayan ke ingizata ga tabi shawaran salahan da nuna mata ta hakane kaɗai zata rama abunda sukai mata wajen maida Aisha ƴar aikin ta shikuma Ahmad sai yanda tayi dashi dan ko wanka idan taƙi sai tace ya ɗauketa yaje yamata tana wannan tinanin kawai ta ssaki murmushi tamiƙe a hankali tayi taku ɗaya biyu tayi wani juyi tace”hmmm waya ganni ina juya mine yanda nakeso,ƴar dariya salaha tayi sannan tayi ƙasa da murya tace idan kinaso yin haka zakiyi kede kawai shirya muje gobe dawuri dan musamu zuwa da wuri saboda nisan waje kinga yanzu dare yayi amma gobe karfe shidan safe zamu fita dan musamu isowa dawuri”amma daddyna fa tafaɗa da alaman tsoro agareta”sai kisan karyar da zaki musu,abu mai sauki ma ce musu zakiyi zamu je raba iv kinga bazasu tuhumeki ba,ajiyar zuciya ta sauke tana cewa”amma gaskiya salaha kin iya law sosai dama ace law kika kiranta,dariyar jin daɗi salaha tayi itako basma toilet ta shiga cike da ƙwarin gwiwa ta wanko fuskarta tafito tazo gaba tangamemen madubi ta dake jera kayan shafe shafe dakuma turaruka masu sanyin kamshi dakuma tsada ta gyara fuskanta sannan tafito zuwa falo wajen ƙawayen ta dasuke zazzaune ana hiran yaushe gamo fitowarta yasasu yin shewa da dariya itama biye musu tayi tsaɓanin ɗazu dasukai mata irin haka tasaka musu kukan haushi yanzu ko samun waje tayi ta zauna a kacigaba da hiran da ita.

Hajia mariyah duk kunya ta lulluɓeta da abunda basma tayi,shuru sukai dukkan su ko wannensu da abunda yake ayyanawa aran sa sai hajia shema ce ta katse shiru da cewa”gaskiya hajia mariyah bazan ɓoye miki ba sam baku bawa yarinyar da tarbiya daya dace da ita ba,wannan shine abunda zatakai gidan mutane irin abunda zataje tayi ma surukan ta kenan,amma kinfi kowa sanin hajia ma’arufa ba macece tsayayya a gidanta dan ko abinci bata yarda da ƴan aiki su dafa mata ba,ita keyin koman ta amma ni banga alamun ko ruwan shayi basma ta iya dafawa ba.

“Taya kuwa zata iya dafawa bayan sun sangarta yarinya bata ganin kan kowa da gashi idan ba haka ba ina basma zata tsaya tana kallon tsaban idon mu tace mufaɗawa uwarta abunda zamu faɗa mata idan yaso ita tafaɗa mata daga baya,hajia balki ce ke wannan magana.

A ƙule hajia mariyah ta miƙe tsaye tace”ya’ishe ku haka me haka ai be kamata kurinƙa faɗin irin haka a gabana ba,ita din yarinyace karama zata denane wataran.

*********

Bayan kwana biyu

Aishace zaune a babban falon gidan dasu Goga da safe jama’an gida gaba ɗaya sun hallara suna karin kumullon safe dan dama wannan yaxame musu ɗabi’a duk safe tare suke karyawa kafin kowa ya kama gaban sa kuma anan duka suke kawo report din abunda suka samo.

Goga dasuke tattaunawa da daddy ishaq yamasa nuni da Aisha da take zaune tayi shiru sai jujjuya kofin shayi datake riƙe dashi da cokali take”Aisha Abbanta yakira sunan ta”na’am Abba ta amsa masa sannan taɗago tana kallon sa”kinason komawa gida ko?

Tsunkuyar da kanta tayi kasa ba tare data amsa ba yacigaba dacewa yanzu mustapha ze mai daki saide karki manta da duk abunda na gayamiki jiya,komai ze tafi yanda muka tsara karki mance da komai yarana zasuna bibiyarki suna tare dake ako ina kuma duk sanda kikaso ganina zaki iya sanar da yarana dake tare daku sukawo ki inda nake koda wasa ko ƴar baba karkice mata kin gannin(khadija kanwar ta yake nufi)”meyasa Abba?batasan sanda bakinta tafurta tambayan ba”sai lokacin hakan yayi tukun na.

Mustapha ne yashiga bayan ya gaida su yasamu wajen zama ya zauna yana haɗawa kansa abincin ɗan dungurin sa goga yayi yana cewa”ummm mustapha acici kode aci towa ba cewar goge yana dariya dan sunan da suke kiransa tun yana karami dan baya wasa da cikinsa wajen cin abinci shiyasa suka saka masa suna aci towu.

Saida yagama cin abinci yacika cikin sa sannan yakoma ya zauna yana fuskantan daddy ishaq yace”oga akwai matsala”wace irin matsala kuma mustapha?suka haɗa baki wajen tambayan sa”eh oga dan hajiya mariƙiyar Aisha bata da lafiya jininta ya hau sosai ta tashi hankalin ta sosai bata da aiki sai kuka da kiran yar amana take,taƙi kwantar da hankalin ta balle asamu jinin nata yasauka.

Sosai Aisha taruɗe jin halin da Anty hajia ke ciki”kinga kwatar da hankalin ki yanzu za maidaki Abban nata yafada amma ina duk yanda yaso Aisha nitsu kasa nitsuwa tayi daga karshe kuka tasaka masa dole yace to shiga kishirya kixo ya kaiki aiko da sauri tamiƙe tanufi ɗaki da take.

Ajiyar zuciya suka sauke duka kana suka maida hankalin su kan mustapha bayan shigar Aisha ɗaki”muna jinka yauwa ajiya da darene aka kawoma Alh badamasi takardan sammaci daga babban kotu,sannan a daren yau ne Alh sunusi dama yan kungiyarsu baki ɗaya suka shirya taron gaggawa”aina zasu gudanar da taron nasu wannan karon?”meyasa kakeson sanin inda zasuyin tafiya zakayi?”gogane yayi tambayan farkon yayinda shima goge ya tambayeshi yaji shin zashine dayake tambayan”eh zani kasan darene sannan akwai wasu abubuwa da bazamu sani ba sai wani cikinmu ya halarci taron nasu mafi akasari sunfi yinsa karfe biyun dare sa’ilinda ƙafa yaɗauke.

“An mustapha ina wannan na’ura dana baka jiya”oga nabawa sani yama ajiye a falo karkashin centar table dake tsakiyar falon”good cewar daddy ishaq”very bad sir kallon goga yayi dan son jin ƙarin bayani”eh saboda centar table ɗin na glass ne kaga dole a gani oga,dan jim sukai duk sai kuma goge ya kira sanin a waya dan yace ya canza ma na’uran waje,bayan sani ya dauki wayan suka gaisa sai goge yace”kana jina sani?”eh ina jinka oga yauwa wannan ɗan abun da mustapha yabaka jiya ka dauka kamai dashi can jikin tv dake falon ka maƙala ta wajen baƙin jikin tv ta yanda baza’a gani ba”angama oga ya amsa sai kuma goge yace bawata matsala ko ta wajen naku”yanzu de babu saide ina ga kaman yau dukkan su a ruɗe suke barin ma Alh bala”ko kaji me yaruɗar dashi”gaskiya bankai gasanin abunda yake faruwan ba amma zan saka ido nagani idan naji zanyi alert dinka”yauwa hakan yayi daga haka suka kashe wayan a tare basa bukatar karin bayani dan wayan a free hand yake sunji komai dasuke tattaunawan daidai nan Aisha tafito dan haka miƙewa mustapha yayi.

Kallon ta Abban nata yayi fuska ƙunshe da murmushi yace”Aisha ki kikula sosai sannan maganan wani natasha da wancan jami’in yayi miki bashi inajiye miki tsoron faɗawa tarkon sunusi dan ba imani ne dashi ba,ze kuma iyayin komai saboda biyan buƙatar sa ta duniya.

Shi faisal bashine babba wajen aikin suba yana da nagaba dashi sannan umurnin su yake jira a kowani lokaci,kinga kuwa bazeyu yace zeyi wani aikin shi kaɗai ba tare da sanin su ba,idan ma yayin akasamu akasi ya turaki kinge can shikuma yasamu kiran gaggawa kinga dole umurnin manyan sa zebi ya tafi kiran da akai masa ke kuma fa?shiru yayi ita ma Aishan batayi magana ba amma ta gamsu da bayanin sa ɗari bisa ɗari,dan haka ya daura da cewa kibar zancen natashan nan kiyi abunda muka saki kawai aikin ki ze farane daga jibi a gidan muna da yaran mu can kama daga maigadi da mai wanki da guga harma da matar da take aikace aikacen cikin gida dukkan su yaranmu kinga ko zasamu matsala abun zexo da sauki”in sha Allah Abba bazama asamu matsalan ba wannan karon sai kayi nasara sai duniya tasan waye Alh sunusi dakuma abunda yake aikatawa Abba na barku lafiya,tace dasu daga haka tanufi kofan fita tana share hawayen da take ta kokarin riƙisu.

Ko a mota batama mustapha magana ba rufe kanta tayi da dan kwalinta tashiga yin kuka saida tayi mai isanta sannan tayi shiru tashare idon a hankali ta maida dubanta kan mistapha dake tuƙin sa hankali kwance tace”kai ni A&B daga haka tayi shiru shima be nemi sanin meyasa tace yakaita can din ba,suna shiga layin sun danyi tafiya kaɗan sai tace tsaya anan yayi parkin motan nesa da wajen saida ta fita tace”zaka iya juyawa saboda akwai cctv camera a can din banason a ganmu tare,daga haka tanufi takawa a hankali tana ɗan share hawayen ta dayaƙi tsayawa harta ƙarasa shiga ciki tun daga bakin get maigadi yadinga kallon ta yana mata sannu tana shiga ciki khalid ne yasoma ganinta aikuwa kaman ƙaramin yaro yakwasa dagudu sai office ɗin ahmad yana haki beko tsaya yin knocking ba kwai sai ganin sa sukai yafaɗa daidai basma dake zaune tafara aiwatar da abunda boka yace tayi dan daga wajen boka suke ko gida bata je ba tabiyo ta nan din,ta buɗe wani ɗan karamin ƙwalba ta daura saman babban table dake cikin office din ta ɓoyeta bayan jakarta zata zuba maganin ciki kenan Aisha ma tafaɗo office ɗin wani irin zabura basma tayi garin miƙewar da zatayi kawai kwalbar ta faɗi ƙasa sai ji kake tatasss……

Leave a Reply

Back to top button