Auren Wucin Gadi 79
CHAPTER 79
A hankali cikin dabara ta share siririn hawayen daya zubo saman fuskar ta,jin sunyi shiru sun dena dariya da duke babbakawa dashi ta gefen ido ta kalli inda suka mai da hankulan su tsaye yake yana goye da hannuwan sa saman kirjinsa yana kallon wani wajen idan duk kwabkwafin ka baka iya ga inda ido yake gani ba.
Kallon gefen ido tayi masa tsaye yake kyam ba zaka gane yanayin sa ba miƙewa tayi tana ƙaƙalo murmushi tace”hajia fatan actin ɗin nawa yayi kaman yanda kika bukaci nayi?
Da ƴar dariya mami ta shiga amsa mata da”eh eh yayi sosai kinyi yanda ake bukata ke din nan zaki iya zama babbar jaruma kinga yanda ki kai kaman wata KATRINA KAIF jarumai Kasar India din nan,tana kaiwa karshen maganan fashewa sukai da dariya,amma kana ganin fuskokin su kasan dariyar tasu iya fuska ce da zaka kalli zukatan su tsoro ne fal lullube da su.
“Murmushi ta sakar musu tana dan juyo wa inda yake tsaye tace”sannu Oga ba de harka dawo bane?
Kai ya gyada masa yana laluben hannun ta cikin dabara ta zame hannun ta daga nashi yace”ki daukon mun wasu file dana mance yana nan zaki gan shi saman centar table,kai ta gyaɗa masa tawuce zuwa ciki dan ɗauko masa tana takawa a hankali cikin sanyin nan nata daya zame mata jiki ta nufi ciki dan ɗauko masa da file din.
Binta da ido Mami da Fauza sukai wani irin tukuƙin baƙin ciki yana turnuke musu zukatan su dukkan su biyun a tare.
(Masu karatu kumun afuwa a shafin da ya gabata madadin nace Fauza sai nace Safna)
Mami ce tayi karfin hali ta soma kame kame kunya duk gama lulluɓeta tace”am Ahmad dama dama nace ko zaka tsaya ka ɗanci wani abu tunda ka zo.
“Nap mami in nafita zan samu abuda zanci ba haka taso ji daga gareshi ba,amma ba yanda za tayi dole tayi shiru tunda ance tabarmar kunya da hauka ake naɗe shi,kallon sa take sanda yake maganan ita de zata iya cewa ko a fuska ba zata ce taga wani canji tattare da shi ba,saima gwarjini da kara mata a ido.
Zungurin Fauza mami tayi tana mata alama ta masa magana,daidai ta kanta tayi daga barin kallon Aisha data ɓacewa ganin ta,tana far da ido ta matse murya tace”Yah Ahmad baka ci komai bafa tunda jiya da kaxo,Abinci dana shirya maka da dare ma baka taɓa komai ba.ta kare magana cike da shagwaɓa.
Ba tare daya kalle inda take ɗin ba yace”dama ita na nemawa kuma bata ci ba,jin maganan nasa tayi kaman saukar aradu.
Basma duk ta birkice sanda tasamu labarin barin Ahmad garin kaman tayi hauka.
Gashin kanta daya sha kari an mata ƙiso blue da ja kitson bob marli duk ya barbaje kuka take riris idon ta duk ya kumbura bayan ta gama fashe fashen ta,kallon Mum dinta tayi da itama bata da aiki sai kiran matattu da basu hakuri Ya hajjo tayi tambayar duniya amma taƙi cewa komai,ƙawarta Hajia bilki ma koda tazo taga halin da take ciki bata sake zuwa ba gudun zargi.
Gwaggo Tani ko idan ta zauna sai ta rabka tagumi tayi nishi uhmmm tace”ikon Allah ni Tani ta Malam Tanko tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin inda Mutum baligi mai cikekken hankali yake neman yafiyar gun wanda ya mutu ba.
Kallon ta Alh sunusi da shigowar sa kenan tayi da shima duk abun duniya ya ishe sa komai yana neman dagule masa yace”wai Gwaggo tun yaushe take akwance koma ba ara wanda ze faɗamun a cikin ku,hararar sa tayi saida ta gutsuri ɓarin goro ta tauna sannan tace”kaidin ina kake da zabika a faɗamakan?
Ni narasa wani irin zama kuke ƴan birni da iyalan ku,sam bakwa bawa iyalan ku lokacin ku, lokutan ku duka na neman kuɗine data neman duniya ne .
Yo in banda haka mutum da gidan sa da matar sa da ƴar sa ace besan komai nasu ba,tunda mukaxo ni koda wasa banga kashigo nan ɗin ba,ko irin ƴar shawarar nan a kan wannan biki banji kuna yi da junan ku ba,mu ba haka muke a karka ba idan mutum yayi magana ace be waye ba,idan ko hakan da naga kunayi shine wayewa to Allah tsine…..”haba Gwaggo kiyi shiru haka dan Allah.
Yah hajjo data fahinci Gwaggo ba shiru zatayi ba tayi saurin cewa”yau kwana uku kenan bata da maganan komai sai matattau.
“Amma Hajjo ba inda taje ta kafin faruwan wannan?kuma ba wanda yaxo gunta?
Ɗan shiru tayi tana kallon ƙanwar tata dake kwance saman gado cike da tausayin ta tace”to kasan mu kallon ƴan ƙauye take mana amma de sun fita da wannan ƙawar tata mai yawan zuwan nan wata zaka ganta ƴar duma duma haka gajera baƙa to ina kyau tata zaton ita tasan komai,ni tsoron ma nake idan ba Maƙabarta sukaje ba.
“Maƙabarta kuma Hajjo?
A ɗan ruɗe yayi tambayan jin inda tace sunje ɗin,ta amsa da”eh yanda na fahinta kenan tunda can ɗinne de maƙwancin matattu idan ko ba a can ɗin ba ai nane zata ga wasu Matattu da har zata ruɗe ta zauce lokaci ɗaya,shiru yayi sai kuma yace”ita kuma Basma a wani hali take yanzu?
“To itama yanzu ta barnan bayan ta gama wa uwar kuka,rintse idon sa yayi yana jin zafi halin da suke ciki a ransa bata da maganan komai sai ta Ahmad yatafi ya barta ɗazun nan saida tasaka mukaje har can gidan su yaron amma halin da muka iske Mutanen gidan ya tabbar mana da kaman Gidan ba lafiya.dan mun tadda likita yana duba Mahaifin sa sannan ita Mamar Yaron wata Mata ko ƴar uwar tace tana zaune bata baki akan tayi hakuri ta cigaba da masa addau’a Allah yakare sa aduk inda yake,ni narasa wani irin hau ne wannan.
Kaman waƴan da suke tsaɓawa Allah wannan abun naku gaskiya abun dubawa ne,ganin yaƙi cewa komai sai ta daura da cewa jekaga halin da Basma ke ciki dan ita ma halin da take ciki abun dubawa ne,dan sai sumbatu take idan ma kunsan kuna aikata ba daidai ba kamata ku koma ga Allah tun kafin lokaci ya ƙure maku baki ɗayan ku,da sauri ya ɗago ya kalle ta,jin jina masa kai tayi tace kana mamakin abun da nace ko?to karkayi mamaki bansan komai a kanku ba amma ɗan zamana gidan nan naku naɗan fahinci wani abun dan gane da yanda kike zaune daga kai har iya mariya.
Ba kwa bawa junan ku lokaci ko kaɗan ace Mutum da gidan sa da matar sa da ƴar sa amma ba zaka iya zama ko na minti biyune da su ka fuskance su suma su fuskance ka ba,ko wannen ku tsabgan gaban sa yake.
Be barta ta karasa maganan ba ya wuce yana ficewa daga ɗakin yana cewa”ki kimtsa ta zam turo likita yaxo ya dubata daga haka ya fita daga ɗakin.
Ɗakin Basma yanufa yana tura ƙofan ɗakin yayi saurin rintsa idon sa ganin yanda ta hargitsa ɗakin ita kanta a birkice take kaman mahaukaciya sabon kamu.
Rufe kofan yayi ya nufeta da sauri yana kiran sunan ta,tasowa tayi ta faɗa jikin sa tasa kuka saida tayi mai isanta sannan tayi shiru tana ture shi tana komawa saman gado ta zauna.
“Mai haka baby?
Kinga yanda kika maida kanki kan namiji ɗaya.
Idan shi ya gujeki ai zaki samu wani bawai ii zauna kina irin wannan haukan ba.
Sauri ɗagowa tayi tana kallon sa da jajayen idon ta da suka kumbura saboda kuka tace”mahaukaci ya.
Ka kirani dan ina nanu alhinin rasa masoyi da nayi.
Daddy ka kasani bani abun da nakeso,ka kasa cikamun burina na mallakan Ahmad matsayin miji ka…”ya isa haka baby..ita ma katse shi ta tana cewa barnj nayi magana barni na faɗi abun da yake raina ko zan samu saukin abun da nakeji,baka taɓa sakani ban yima shi ba,koman wuyan sa koda raina bayason abun nan zanyi shi saboda cikan burin ka.
Amma yau ka kasa bani abun da nake so kasa cikin mun burin dadday idan nasara shi kowa ma ze rasa tana kai karshen maganan ta ta fita waje da gudu mara mata baya yayi tare da kiran sunta.
Masu karatu dan Allah kumun afuwa rashin jina kwana biyu wasu uxururruka ne suka tsaidani .
ALLAH YASA MUDACE
- ALLAH YASA MUDACE