Hausa NovelsSakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 45

Sponsored Links

;

SAKAYAH

 

45

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

 

 

Assalamu alaikum mutanan arziki masoya kamshi ma abota kamshi Amaren kamshi masu jargon kamshi Yammata wadanda sukasan darajar kamshi ni Aysha Aliyu Garkuwa na kawo muku tallan wasu Amintattun turarukana masu matukar kamshi da Kama jiki

Masu saukin farashi sannan ga biyan bukata

Yarhjya_incense_and_more

Ta shirya tsaf domin ta gwangwajeku da Turaruka na alfarma

Farar khumrah

Bakar khumrah

Turaren Wanka

Oil 6ml 1

Oil 12ml 1

Turaren fesawa 24 hours guda 1

Duka Akan 10k kacal

Sannan kayanta suna tafiyane da guarantee duk wacce tasiya taji babu kamshin nan na alfarma ko kuma basuda lasting to tayi alkawarin mayar muku da kudinku

Wannan garabasar zata kare on 5th September insha Allah

Ku hanzarta ku mallaki naku domin kayan yarhjya babu Danasani a cikinsa saidai kuyi alfahri da siyan kayanta

Account number 1419787445 Amina Umar usman access bank

Kitura evidence of payment to

08092664954

Kuyi saving number TA domin ci gaba da ganin Turaruka Kala Kala

 

 

Yayin da gaba dakin sune bin Khausar kallon, sabida yadda annurinta ya cika fuskarta, tare da haska ɗakin, lokaci daya ta zama tamkar tauraruwar da tafi ko wacce haske acikin duniya.

 

Acan cikin sauran ɗakunan kuwa, tuni su Ummi da kuma su Aunty Hajara, Aunty rukayya, Hajiya Bunayya, sun sha kwalliya cikin shigar Alfarma, had’i da kece raini, sun kuwa yi matukar kyau, domin hatta su Innayi da Hajja Nana ba abarsu a baya ba, musamman Hajja Nana duk tsufanta, bai hanata yin kyau cikin doguwar rigar data sanya ba kasancewarta ƴar duma-duman tsohuwa kai hakama bata shekarun da take da suba, dukansu sunyi kyau sai ɗaukar idanu suke, kowanne daga cikinsu kuwa kaga ni kasan yana cikin farin ciki, musamman Innayi da ayau farincikin dake kan fuskarta ya kasa ɓuya.

 

Hakama ɓanƙaren su Abban Jameel da Lamiɗo da Malam Arɗo Bappa Jimeta da Haiydar harma da Dr Jameel sosai sukayi shiga ta al’farmar.

Su tuni sun iso wurin taron bisa jagorancin Sheykh Jabeer.

 

Hakama su Innayi suma tuni sun sauƙo bisa jagorancin innayi, sun zauna a gefen inda su Abban Jameel suke, don dama an ware musu wurin zamansu na musamman.

 

Aɓangaren Moddibo kuwa tsaye yake acikin cikin ɗakin da ya lura nanne ɗakin Ibraahim,  yayinda yake cikin wata irin Amintacceyar shiga ta al’farmar da kamala.

Dandatstsiyar jalabiya ace a jikinshi Sky blue mai masifar kyau da shaƙi sai ɗauke ido take tamkar madubi, sai kuma wata tattausar Al’kebba fara ƙal mai ratsin Sky blue da golding  kala na zaren da aka yayyarfawa alkebbar wani irin Mashahurin aiki mai cike da tambarin masarautar Mouley ɗin. Sai kuma farin hirami mai gidan dara-dara Sky Blue, wow Masha Allah. Wani irin sheƙi da ƙyalli yakeyi kai kace taurarone sajenshi kuwa sai walwali yakeyi fuskarshi ta fito ras.

Cikin ɗan fesar da numfashi yace.

“Anya zan iya wannan tsaraɓe-tsaraɓen kuwa”.

Yayi mgnar cikin ƙosawa da yadda ake wani shiryashi kamar yaro.

Murmushi Ibraahim yayi, had’i da cewa.

“A’a zaka iya, mana, kayi haƙuri kasan al’adarmu ce anan, duk ranar da za’ayi wani abu na musamman, shirya mutum ake, musamman irinka masu girman daraja.”

Kai Modibbo ya girgiza cikin yanayin k’osawa yace

“Afwan ni a barni haka”.

 

“A’a Yah Aleey dan Allah, kasan nan masarauta ne, kuma kana da matsayi na musamman, kadai bari ashirya kan.”

 

Kokarin magana yake, sai kuma ya fasa saboda Sheykh Jabir daya shigo, cikin shiga ta alfarmar da takasance shigarsa akoda, wanda a wurinshi Modibbo ya gaji don irin wannan shigar,  ganin  Modibbo’n azaune yasa shi, bud’e baki da mamaki yace.

 

“Har yanzu Aleeyu basu gama shiryaka ba, lokaci yana k’urewa, tashi maza a ƙarisa shirya ka da hanzari.”

 

Ya k’are maganar yana me jawo hannunsa, suka nufi gaban dressing mirror wanda yake cike tab da ababen gyaran jiki, komai na wurin tsabtsab yake, komai neat da alama Ibraahim din gwanin tsabta ne.

 

Suna isa wurin ɗaya daga cikin hadiman ya ja mishi kujera, ya zauna, bisa umarnin Sheykh Jabeer way’annan hadiman suka ci gaba da shirya, shirin da ya bayyana cikakken kwarjininsa me burgewa.

“Masha Allah.”

Ibraahim ya fad’a lokacin da kwararrun hadiman nan suka nad’a masa kyakkyawan farin hirami me ratsin adon sky blue akansa, da yayi matuk’ar k’ara bayyana kwarjininsa, still suka gyara mushi zaman tattausan farar, alkyabbar da taji ado, me d’auke ido da jan hankali, wacce tana da faɗi kuma a buɗe take, tabbas zan iya cewa Modibbo bai tab’ayin kyau irin na yau ba, domin shi kansa ya shaida hakan, saboda tsananin kyaun da yayi, Sheykh Jabeer da Kuma Ibraahim murmushi kawai suke idan sun kalleshi.

Kyakkwawan takalmin sarauta light blue aka sanya masa aƙafarsa, wanda shiya ƙara cika adon nasa, domin harda adon bit din gold ajikinsa, ahannunsa kuwa wani tsadadden agogon gold suka d’aura masa, wanda cikinsa ke d’auke da tambarin masarautar tasu ta Mouley.

 

Murmushi Ibraahim ya sakeyi, wanda hakan yasa Modibbon ƙanƙan da idanunsa, cikin sanyi da taushin muryar da taza me masa d’abi’a yace.

 

“Wai Ibrahim duk wanna murmushin na menene?”

 

Murmushi Ibraahim din yayi, yana me gyara masa zaman takalman ƙafarsa yace.

 

“Duk wannan murmushin da shigar taka ta musammance, yau din rana ce ta farinciki Yah Aleey, yau da za’a gabatar dakai awajen dangin mahaifinka, yau kowa zai san da zamanka, ni gani nake kamar masu shiryakan ma basa sauri.”

 

Ya ƙare maganar yana sake kallon tattausar alkyabbar dake jikin Ya Aleey’n nasa, wacce Sheykh Jabeer ke k’ara gyara masa zamanta.

Aransa yake yaba baiwar kyau kwarjini had’i da haiba da Allah Yayiwa Aleey’n.

Abayyane kuwa cewa yayi.

 

“Masha Allah,

 

Sheikh Jabeer kuwa cikin kulawa yace.

“Fatabarakallahu fiy ahasanil khali kiyn.

Allah Ubangiji ya albarkaci rayuwarka, ya kareka daga sharrin mugun mutum da aljan, ya kuma tsareka daga sharrin idanun al’ummar da zasu kalleka, ka shiga da addu’a, Ubangiji na tare dakai akoda yaushe.”

Amin Ya Allah, Jabeer bin Jabeer dake shigowa ya amsa.

Shi kuwa Modibbo Cikin dai ɗaurewar kai da har yanzu ya ke ciki ya gyaɗa mishi kai.

 

Yayinda Ibraahim kuwa, tsananin kyaun da Yah Aleey’n yayi duk ya gigitashi, hakan yasa shi zaro wayarsa kirar iphone 14pro max ya shiga daukarsa hoto, yana me sake yaba kyawun da yayi, koda ya kammala yi musu hoton falo ya fito, nan ya iske Dr. Jameel da kuma Zakareeya suna zaune cikin shiga ta al’farmar da alama suma sun gama shiryawa, ganinsa yasa suka miƙe tsaye, sai kuma suka juyo jin motsin su Modibbo kusan a tare sukace.

“Wow masha Allah, lallai jini baya ɓuya”.

Suka ƙare mgnar suna matsowa kusa da Modibbo.

 

Shi kuwa Ibraahim da sauro ya nufi inda za’a gudanar da taron, yana zuwa cikin babban falon taron masarautar tasu kuwa ya tararda wajen acike maƙil, ƴan uwa duka sun hallara kowa da kowa nasu na nan, iyaye, kakanni dama jikoki harda ƴaƴan jikoki, babban falon ya cika maƙil, yayinda acan gefe kuwa wurin da aka warene waje na musamman na zaman amarya da ango zasu zauna a tsakiya.

 

Sai kuma gefen su Didi dake zaune tare dasu Lalla Hafsa da Lalla Khadija sai sauran matan Abualeey da yaransa.

Ibraahim na shigowa Rahma ta miƙa da sauri tazo nufoshi tana fad’in.

“Yah Ibraahim, har yanzu baku gama ba, duk an fitofa ku ake jira, dangi duk sun zak’u dason ganin Yah Aleey.”

 

“Yanzu zamu shigo, nazo duba yanayin wajen ne.”

Ibraahim ya amsa yana me shakan daddad’an kamshin turaren wutan dake hannunta, wanda hayakinsa ke tashi acikin kasko.

Cikin sassarfa kuma ya juya, domin yiwa Modibbo da kuma Kakansu Sheykh Jabeer jagora.

A falon ya samesu cikin jin daɗin yace.

“Bismillah mufa ake jira”. Ya faɗa tare da tsayawa gaban Modibbo, yayinda Sheykh Jabeer kuwa yake gefen damanshi, Zakariyya kuma da Dr Jameel a gefen hagunshi

Kana suka fito cikin Corridor da zai sadasu da falon.

Dr Jameel a hankali ya ɗan ja baya ya koma cikin falon da suka fito ɗin sabida ganin kiran Babynshi.

Amsa kiran yayi tare da maida ƙofar ya rufe.

 

Su Zakariyya kuwa basuma kula ɗaya komaba.

Sabida Hadiman da suke zagaye dasu.

Tafiya suke a hankali cikin ƙasaita da Kuma nutsuwa, haɗi da tsananin jinin sarautar dake gudana acikin jinin kowannensu, musamman Modibbo, wanda yake jin kansa acikin wani irin yanayi na daban.

Tsantsar girma yake ji, haɗi da zumma da ƙasaitar da bai tab’a jin kwatan kwacinsa ba, haka suka nufo babban falon dake cike da dangi da y’an uwa.

 

Acan side din da Khausar take kuwa, jakadiya ce da kanta tare da Lalla Salma wato mahaifiyar Zakariyya, suka rik’o Khausar din wacce ta zama tamkar wata flower saboda tsabar kyau, kamshi kawai take bazawa me tsuma zuciya.

Lalla Salma da takejin Kaunar Khausar har cikin zuciyarta ne ta ɗan sunkuyo da kanta daidai saitin kunnen Khausar din tace.

 

“Ki yawaita ambaton sunan Allah a bakin ki har muje mu dawo, Ubangiji Allah Ya kareki daga sharrin masu sharri, Allah ya tsareki ya kuma kauda idon mak’iya daga gareki, Allah Yasa ki shiga cikin zuri’ar mu da k’afar dama, alfarmar annabi da al’qur’ani, kiyita adduan Allah ya tsareki da fuskantar k’alubalen da surkuwarki ta fuskanta lokacin da ta shigo ahalinmu, Allah ya miki al’barka ya dauwa mar dake cikin farinciki.”

 

Da “Aameen” ta amsa cikin ranta, yayinda a fili kuwa jinjina kanta kawai tayi, tanajin matar ta kwanta mata arai, saidai tambayar azuciyarta take wai shin menene ke naɗe cikin tarihin Modibbo waye shi, meyasa innayi ta koma dashi can? Me hakan yake nufi haka tai ta jerawa kanta tambayoyi?

Tambayar da bazata samu amsarta ayanzu ba.

Ahaka suka ci gaba da tafiya Jakadiya da kuma Lalla Salma na rike da ita, sai kuma Hadimai dake biye dasu abaya, hadi dasu Asmau Asiya da kuma Dije.

 

Sassanyan busar sarewa me tsananin dadin jine ya cika kuwannuwan way’anda ke zaune a falon, kasancewar isowar su Modibbo, wanda hakan yasa duk idanun mutanen dake wajen ya koma kansu.

“Masha Allah, fatabarakallahu fiy ahasanil kali kiyn.”

Shine abunda ke fitowa daga bakin tarin mutanen dake wajen, saboda yanda Modibbo yayi matukar kyau had’i da k’awatuwa, tsananin kwarjini da haiba sun bayyana akan kyakkywar fuskarsa, da tayi kama dana mahaifinsa sak, sarautar zalla yau ita ta bayyana kanta ajikinsa.

Yayinda wasu daga cikin mutanen wajen kuwa, suke raba idanunsu wajen kallonsa shida Ibraahim, saboda tsananin kamar da sukeyi da juna.

Ayau fuskokin da yawa daga cikin  masarautar ya cika da farincikin da har ya kasa ɓuya.

 

Cikin tsananin jin dadi suke wasu dayawa ke fitowa suna rungumar Modibbo, wanda tsananin kwarjininsa ya haifar musu da soyayyarsa me tsanani.

 

Cikin sauri Innayi ta nufi inda suke tare da fara ware wannan sandar nan da take ajiye dashi da ƴan silalla, ware sandar ta farayi daga cikin furen da aka naɗeta.

Tana isa wurin ta tsaya gaba Modibbo tare da miƙa mishi sandar, shi kuwa Modibbo cikin tsananin mamaki da kaɗuwa ya ware idanunshi a kan fuskarta murya cike da mmki yace.

“Yah Salam wa nake gani a gabana ni Aliyu”.

Murmushi mai cike da farin ciki innayi tare da kamo hannunshi ta danƙa mishi sandar kana tace.

“Innayinka ce a gabanka ba kama bace, nice nan Modibbo nazo maka da tsaraba mafi daraja a gareka tare da rakiyar masoyanka”.

Ta ƙare mgnar tare dayi mishi nuni da inda su Abban Jameel Malam Arɗo Bappa Jimeta Lamiɗo Haiydar, suke zaune.

Cikin sauri ya dawo da ganinsa kan Innayi tare da cewa.

“Yah ilahi Abba harda Lamiɗo da kuma Malam Arɗo”.

Sai kuma ya kalli inda ta nuna mishi tana faɗin.

“Harda Umminka ma ba”.

Wani irin amintaccen numfashi ya fesar lokacin da kwayar idanunsa suka sauƙa kan fuskar Ummi, yalwataccen murmushi ya sakar mata, sai kuma ya kalli Innayi da tuni ta juya ta nufi wurinsu Ummin sai kuma ya kalli Hajia Bunayyah, tabbas ya ganeta a fili yace.

“Toh ita kuma me haɗina da ita?”.

Sai kuma ya maida kallon sa kan Haiydar dake mishi murmushi a hankali yace.

“Harda Haiydar”. Shi kuwa Haiydar cikin jin daɗi ya kalli Lamiɗo tare da cewa.

“Kai Masha Allah Abba kalli yadda Modibbo yayi kyau, kai shigar sarauta akwai kyau”.

Murmushi kawai Lamiɗo yayi dan ya fahimci cewa shima Haiydar jinin sarautar ne ya motso.

 

Shi kuwa Modibbo bisa jagorancin Sheykh Jabeer da kuma Ibraahim Zakariyya da Jabeer bin Jabeer ne yasa yake biye dasu zuciyarsa fal tarin tambayoyi kana da mamakin ganin su Innayi musamman kuma Lamiɗo barma ace ta Bappa Jimeta da baisan shiba.

Ahaka har suka isa wajen da zasu zauna, Sheykh Jabeer na riƙe da hannunsa.

Saidai kasancewar a tasu al’adar ango baya bazai zauna har  harsai amarya ta ƙaraso hakan yasa koda suka iso wajen zaman tsayawa sukayi, yayinda tuni Fadawa suka zagayesu tare da ware tabka-tabkan rigunansu sukayi musu ƙawanya.

Suna tsayuwa kuwa suka soma jiyo, wani daddaɗan busa sarewa, me ɗauke da sassanyan kirarin da akayita da harshen larabci da marabta baƙi.

Wanda hakan yasa gaba ɗaya idanun ya koma saman steps din dasu Khausar ke takowa, domin tuni anfara shelan zuwan amarya.

 

Jin hakane yasa fadawan nan kuma janye rigunansu, tare da zagayawa suka koma bayan kujerar da aka ƙawata dan zaman ango da amarya, yayinda wasu kuma duk suka rusuna ƙasa.

 

Shi kuwa Modibbo kasancewar yana fuskarta ta inda suke tahowanne yasashi saurin ware idanunshi a saman lips enshi yace.

“Asma’u?”. Yayi mgnar da ko Ibraahim dake gab dashi baijiba, cikin son fahimtar me ke faruwa ya kuma kalli Asiya sai kuma ya maida idonsa kan Asma’u dake sakin murmushin, shi kuwa idon shi ya maida ƙasa tare da fara kallo su daga ƙasa.

Ahankali suke taka kan stairs din da yasha red carpet me masifar kyau da ƙawa yayinda kan ko wanne step akwai Hadimai gefe da gefe suna riƙe da kaskon turaren wuta.

Asmau ce ke gefen damanta yayinda Asiya kuwa ke gefen hagunta, sai Dije dake  gefen Asma’u.

Sai kuma wata ƴar matashiyar Haɗina dake bayanta wacce ita ke riƙe da mayafin da aka sanya mata akanta, wanda saboda tsabar tsawonsa har jan ƙasa yake yi.

Sunyi matukar kyau da burgewa, hakan yasa duk aka maida kallo kansu.

Tafiyarta me tsananin jan hankali da ma’ana, haɗi da tsananin ƙawatuwar da shigar nata shiya sanya Modibbo dake tsaye zuba mata ido, duk da cewar baya iya ganin fuskarta, amma tsananin annurin da take fitarwa ya cika masa ido, yayinda takun da takeyi me kama da tafiyar ɗawisu ya tsaya masa arai, domin yanajin tamkar ya taɓa sanin me wannan tafiyar, tabbas ya taɓa ganin irin tafiyar.

 

Jin ana shelar amarya ta iso tare da fara zuba kirari.

Amarya Fatima Zahra mata a gidan Aliyu Youseep  Mouleey.

Da sauri ya rumtse idanunsa da ƙarfi dan so yake ya nazarci kalaman.

 

“Amaryar kuma? Toh amaryar waye? meyasa naji ana kiranta da matarta, wace matarta kuwa? me suke nufi? Yaushe aka aura min ita? Toh ma wacece ita? Shin wai su waɗannan me suke nufi dani? da zasuyi ta juya min rayuwa suna sarrafa min abinda basu nemi izininaba”. waɗannan tambayoyin su suka cika zuciyarsa da ta samu kanta cikin tsananin ruɗani.

Shin me ake nufi dashi ne? me sukeson maidashi? wani irin aurene wanda akayishi babu saninsa? Bare sahalewarsa, toma uban waye yace musu shi ya shiryawa aure a wannan taƙin.

Ya kuma yiwa kansa tambayar yana me tsareta da idanunsa, duk da cewar baya iya ganin fuskarta saboda mayafin da aka sanya mata.

Ji yayi kansa na wani irin juyawa zuciyarsa kuma na bugawa da ƙarfi, so yake ya buɗi bakinsa ya cewa Sheykh Jabeer shifa kada a liƙa mishi wata jarabar amman ina ya gaza sabida ruɗanin da yake ciki.

 

Sun Khausar kuwa ahankali suka ƙaraso cikin parlorn, wasu daga cikin Hadiman dake ta hidima ne suka nunawa Asma’u Asiya da Dija, wajan zaman da aka tanada musamman domin su, haka yasa cikin nitsuwa su Asma’u suka nufi wurin zamansu, yayinda Hadiman kuma duk suka zube a ƙasa.

Yayinda su Lalla Salma  kuwa suka nufo da ita wajen dasu Modibbon ke tsaye.

Da sassarfa Rahama ta taso ta biyo bayansu.

Lalla Salma ce ke rike da Khausar yayinda kowani taku ɗaya da sukeyi na kusanto inda Modibbo yake.

Hakan ke kara duk’unzuma tunanin Modibbo, wanda yakejin abubuwan suna zuwa masa awasu yanayi na daban.

 

Dab dashi Lalla Salma ta kawo Khausar din, tare da sakin hannunta, da sauri Rahma ta ƙaraso hannunta rik’e da wani babban glass bowl wanda cikinsa ke d’auke da kyakkyawan furanni masu fitar da sassanyan k’amshi.

Cikin tsananin farinciki ta soma watsa musu furen, Lalla Salma kuwa matsowa kusa dashi tayi, tare da ɗan ranƙwafowa ahankali tace.

 

“Abisa al’ada Aleey kai zaka buɗe fuskar amaryar taka ka juyata ta fuskanci family inka su ganta da kyau, kayi Bismillah ka bud’e fuskarta, idan ka juyata an ganta sai ka riƙe hannunta ku zauna bisa kujerar nan ka tabbatar kun zauna da bisimilla.”

 

Cikin sauri ya kalleta hadi da kallon Ibraahim dake gefensa na dama, sunkuyar dakai Ibrahim yayi kana cikin yin kasa da murya yace.

“Dan Allah Yah Aleey kayi abunda Lalla Salma tace, kada kayi abunda za muji kunya, kar kayi abunda zaisa mutane su fara tunanin babu abunda ka sani adangane al’adun masarautar da ake tunani za’a damƙa maka ragamarta a hannunka, kayi hakuri dan Allah Yah Aleey!!”

 

Ya k’are maganar cikin magiyan, da yasa Modibbon juyawa ya kalli Didi  da ta tsura masa ido.

Sai kuma ya ɗan juya idonshi ya kalli Innayi wacce itama kallon nasa take, tare dayi masa alama akan yin biyayya.

 

Idanunsa ya dan lumshe tare da shakan numfashin dake kokarin kwace masa sabida tsanantan bugun da zuciyarsa keyi.

Cikin bada umarni Sheykh Jabeer ya ɗan matse hannunsa dake cikin nasa, kana ya ɗan rongofo tare da faɗin.

“Kayi abinda ya dace, umarnin kakarkace macen da tasha wuyan rainonka tsawon shekaru, kana kuma fata ne da burin mahaifiyarka data raini cikinka tsawon wata tara da kwana tara, sannan burin mahaifinka kanan”.

A hankali ya buɗe lumsassun idanunsa lokaci da yaji zuciysrsa na bashi umarni.

“Buɗe kaga wacece?”.  ji yake wani abu na fusgarsa, batare da sani ko shiryawa hakan ba, sai ji yayi hannayensa na motsi, duk da karkarwar da suke.

 

Ganin haka yasa Rahma dake bayan Khausar ɗan turo Khausar din tare da cewa.

“Yes my Aunty jeki kusa da mijinki ya buɗe mana fuskarki mu ganki”.

Sai kuma ta ɗan ƙara ɗan tureta kaɗan da kafaɗarta, wanda haka yasa Khausar da zuciyarsa ke buga lugude tara-tara ta ɗan yi motsi kaɗan da yaɗan ƙara kusancinsu da Modibbo.

 

A hankali ya ɗan ɗago hannunsa, yatsunsa biyu yasa gefe da gefen mayafin nata ya kamo tare da d’an d’ageshi sama, yanajin zuciyarsa nayi masa wani irin duka uku uku.

Yana janye mayafin kuwa kyakkyawar fuskarta na bayyana.

 

Cikin wani irin baƙin al’amari ya zazzaro idanunsa cike da kad’uwa had’i da mamakin ganin fuskar Khausar, wani irin masifeffen kasalane ya rufe mishi jiki da zuciya, a take kuma yaji wani irin abu mai masifar sanyi ya tsoki ƙahon zuciyarsa, kana a take ya kuma jin wani irin abu daya harba daga tsakiyar maɗigan kansa, ya game dukkan sasanjikinsa, har zuwa kan babbar yatsarsa, wani abu me kama da mamaki, hadi da mutuwar jiki ne suka lullubeshi lokaci d’aya.

Bak’on yanayi me kama da zazzafar bege da bai tab’a jiba ya lullube dukkan jikinsa, dake wani irin tsuma.

Hadi da sanya masa wani yanayi na kaucewar tunanin.

Wanda ya sashi bud’e hannayeshi tare da ware  tattausar al’kyabbar dake jikinsa.

Wanda ganin hakan yasa Rahma ɗan ƙara tura Khausar, kasancewar takalmin da ta sanya me tsinine hakan yasa ta tafiya garesa batare da ta shiryawa hakan ba.

 

Shi kuwa Modibbo wani irin mataccen numfashi yaja tare da fesar da sassayan numfashi mai dogon sauti.

Kana ya yayi mata Kekkyawan masauƙi a ƙirjinsa tare bata cikekkiyar kariya

da yalwatacciyar alƙyabarsa ta hanyar bata wani irin kyakkyawan runguma, me ɗauke da ma’anoni masu tarin yawa, da yafi kama da tsananin shauki hadi da zallar kewa da bege.

Rungumeta yayi tsam a cikin jikinshi ya mannata da ƙirjinsa da ƙarfi har yakai ga suna iya jiyo ɗumin jikin junansu wanda kuma tuni yayi mata garkuwa da yalwatacciyar Al’kebbar jikinsa mai cike da ni’imtaccen ƙamshi.

Lib Khausar tayi a jikinshi tare da shaƙan numfashi daya wadatu da ƙamshin turaren jikinsa wasu irin tagwayen numfarfashi take fesarwa tare da lafewa a jikinshi da kyau tamkar mai tsoron kada a janye mata shi haka nan takejin tamkar a barta ta rayu a kunshi a haka har gaban abadan haka yasa ta liƙe lip a jiki nai.

 

Shi kuwa Modibbo a hankali ya lumshe idanunsa tare da laso gefen lip inshi sama,

 

Yanayi ne na musamman a garesu, daya sanya su lumshe jujjuya kwayar idanunsu a tare, musamman ita Khausar da taji ya lulluɓeta da alkyabbarsa.

Wata duniya ce ta daban me shiɗarwa suka lula.

Cikin wani irin aminci da salama Modibbo ya ɗan sunkuyo kanta kaɗan tare da  kawo bakinsa dai-dai saitin kunnenta.

Cikin sarƙafeffiyar muryarsa me kama da raɗa,cikin tsananin sanyi, ta yanda ita kadai zata iya jiyoshi atausashe yace.

 

“I miss you my trouble maker. I really miss you my trouble student.”

 

Wow gaba ɗaya falon ya kacame da tafi da sowa.

Sai kuma sarewar da ta karaɗe falon.

 

Ummi kuwa wani irin amintaccen numfashi ta fesar.

Yayinda Didi kuwa tayin ƙasa da kanta tana sakin murmushin.

Su Lamiɗo da Malam Arɗo kuwa duk ƙasa sukayi da kansu cikin konciyar hankali.

Haiydar kuwa wayarshi ya zaro tare da fara musu video, hakama Rahama.

Yayinda tuni kuma masu ɗaukar hoto suka fara kebta musu.

 

Zakariyya ne ya ɗan zunguri kafaɗar Modibbo da tashi kafaɗar tare da cewa.

“Kai Jinin Mouley a tsakiyar mutanefa kuke, ka ritsa yar mutane kamar zaka maidata cikin ƙirjinka”.

A can sama ya jiyo muryar Zakariyya wanda ya sashi buɗe idanunsa a hankali.

Hango Lalla Khadijah da wasu mata a ƙalla su bakwai ne ya ɗan sashi sassauta rungumar da yayi mata.

Tare da ɗan jan baya kaɗan.

Fuskashi ya ɗan tsuke tare da kara ronƙofo da kanshi a hankali yasa bakinshi dai-dai iunnenta  murya can ƙasa yace.

“Toh yau dai burinki ya cika ai, na ruggume ki, hankalinki ya kwanta tunda kinji ɗumin jikina ko? Kin samu abinda kikeso ko”.

Mui-mui tayi da bakinta

Kara matseta ya ɗanyi tare da cewa.

“Rashin kunya zakiyi minko”.

Baki ta ɗan tura tare da cewa.

“Ni ka sakeni”.

Ɗan haranta yayi tare da cewa.

“Kece ai kike riƙe dani mayya uwar son jiki, tashi min a jiki Mage”.

Da sauri ta ɗan janye jikinta kaɗan.

Dai-dai lokacin kuma Khadijah suka iso.

Kusan a tare suka fara yi musu wani irin….!

 

*Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta abinki cikin Salamah 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER’N 09097853276 in tura miki abinki ki karanta cikin salam ba tare da kin karanta na Allah ya isaba*

 

 

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Reply

Back to top button