Bakar Ayah Hausa NovelHausa Novels

Bakar Ayah 14

Sponsored Links

Page 🖤14🖤

 

A haka suka koma gida cikeda ta’ajjibin abinda aka faɗa musu. Sannan kuma Daneji tacigaba dayi mata wankan maganin da mlm Alwasu yabasu.
Bayan sati daya dayin hakan suka sake komawa,aka yi yankan sadaka da kuma sauƙar karatu,sannan ya kuma basu wani maganin wanda za’ayi mata.
Sai a sannan ne hankalin su mlm Ahmadu ya kwanta,amma ba duk ba,saboda har yanzu idonta babu abinta ya sauya daga shi,saidai sun samu kwanciyar hankali jin cewar ta rabu da aljanun da suke jikinta.
Wasa wasa abu yayi ta tafiyah,har an shafe watanni biyar,tun su Danejo na boye Bombee idan sukaji sallama,har yazamo mutane sun gane abinda yake tattare da ido.
Dama ance idan rana tariga ta fito,tafin hannu bai isa rufeta ba.
Kuskus a cikin jama’a har zance yabaza gari ko ina ya ɗauka ƴar gidan mlm Ahmadu mayya ce,tun Danejo batajin mai yake faruwa har zance ya dawo kunnenta.
Inna laari tana sayar da kayan miyah,wanima da gangan yake tsallake anguwarsu yazo gidan su siyan abu,badon komai ba sai don yaganewa idonsa labarin abinda yakeji a gari.
Itakam inna laari cinikinta nunkuwa yake a kullum,ko kyaushe cikin siyeda siyarwa takeyi,kowa kuma idan ya shigo idonsa yana kan ɗakin Danejo,domin yaga ta inda zaiga Bombee.
Kullum a rana Danejo bata da aiki sai boyeta a cikin daƙi,saidai yanzu abin yayi mata wuyah,dan tafara rarrafe,ga ta da rawar kai bataji ko kaɗan,kota ajiyeta a ɗaki saita fito waje,wani lokacin inta takura bazata fita ba tasaka mata kuka,har abin ya isheta ta daina hanata fita wajen.
Batada ikon rufe bakin mutane ko kuma idanuwansu,amma kuma tana damar rufe nata idon da kuma bakin,shiyasa tasakawa idonta ƙyalle ta rufeshi,kunnenta ma ta tosheshi daga abinda zataji akan ƴar tata.
Inna laari ce take ƙirga karago itada mai talle…..basu fargaba sai ji sukayi yarinyar ta junduma ihu ta fita gudu waje.
Gefe suka kalla inda Bombee ke zaune kayan duk ya baci da rarrafen datayi,ashe mai tallan ta dafa zata tashi,itakuma kallon idonta yasa ta fita dagudu.
Shuru sukayi daga Danejo har inna laari,wannan abin ba barauba kenan a gidannnan.
Babu yanda inna laari batayi da ita tazo ta ɗauki kayan tallanta ba,dole sai ita ce taje zauren takai mata tukunna.
A bakin ƙofar ta haɗu da muruje yashigo cikin gidan,tundaga baƙin ƙofah yake tafi da hannunsa,itama Bombee da take zaune tana kwaikwayonsa,koyaushe tana zaune babu mai ɗaukarta ko yi mata wasa a yara saishi,shiyasa idan taganshi tayi ta ɗaga hannun ya dauketa.
“Ina mai idon kuliyar,kamata kamata gatanan gatanan,zatasha alewa?”
Waka yaketa reramata itakuma tana dagalemasa baki da haƙora biyu a ciki.
Kinkimarta yayi zai fita waje Danejo tayi saurin cewa.
“Muruje ina zakujene haka?”
“Gidanmu zan kaita wajen umma,mu bamuda yarinya a ɗakinmu,nasan inna zata karbeta”
“Ahah muruje ku zauna a nan kuyi a wasan,karka fitada ita kaji”
” toh Innar Bombee amma bari muje zaure toh”
Fita sukayi suka zauna a zauren,inda yahaɗa abubuwan wasa kala kala,shikaɗai yaketa maganarsa ita saidai ta bishi da ido,ko kuma inya haɗa abin wasan ta rugujemasa da ƙiriniyarta,gata da kazar kazar da zafin hannu.
Ɗaukar buta tayi bayan tagama shanyar kayan da Bombee ta bata tashiga banɗaki. Bayan ta fito sai taji babu motsin muruje da Bombee a zaure inda ta barsu.
A jiye butar tayi da sauri ta nufi zauren domin leƙosu,amma babu su babu ɗuriyarsu,gabanta ne yafaɗi rass,a ranta tace shikenan ta faru ta ƙare.
Kama katanga tayi ta leƙa gidanna su.
Yana nishi daƙyar ya ƙarisa zuwa cikin gidannsu yana cewa.
“Kai sule kagani nima nasamo tawa ƴar,daga yanzu inzamuyi wasa bakai kaɗane mai ƴar wasa ba,nima ina da ita”
Yaƙarisa maganar yana kallon sulen ɗan gidan larai,yanayi yana zukuɗa Bombee wacce tayi masa nauyi saboda ƙibarta dumur dumur.
Larai ce ta bankaɗa lalubulen dakinta ta fito,aikuwa carabb idonta ya sauƙa kan na Bombee wanda suke shining suna ɗaukar hasken rana.
“Lahh ilah haillallahu yau mai zangani,yanzu wannan mai idon mayun kaje ka jajibomana cikin gidan,a garin wato cusuwarka irinna uwarka koh,wannnan ɗa zakayi abu da yawa a rayuwarka.
Wato kalan ta lashemu dukka ku babu tsiyarku,…….uhmm wayasani ma abu a duhu ko kuiɗn tsarkakkune,dan dama ance duk inda mayu suke sunajin ƙanshin mutanensu idan suna kusa dasu,babu mamaki biri yayi kamada mutum kake nanewa a gidan wannan mayyar yarinyar. Maza tun kafin raina yabaci kafitamin da wannan annobar a cikin gidannan,kafin ma ta kawo mana baƙar sa’a”
Shatu ce datake ɗaki tana famada tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe taji hayaniyar taƙici kuma taƙi cinyewa.
Ja tayi da ƙyar tafito daga ɗakin dan ganin mai yake faruwa,dan tasan kullum zancen dai ɗayane baya sanja zani.
Larai ce itada muruje,ita ko kunya ma bataji,kullum idan aka jita to ita yarane ,tun yaran suna tsoronta har yazamo yanzu sun maidata tamkar mahaukaciyah.
“Kai muruje mai yafarune ,mai kayi kuma yanzu”
“Inna Bombee fah kawai na ɗakko zamuyi wasa,shine inna larai tace wai na maidata,kuma wasa kawai zamuyi,ba kuka take ba”
“Kaga maza kaita wajen innarta kartayi kuka kaji,kadaina ɗakkota,ka dunga zuwa can ɗin kuna wasanku kaji?”
“Toh inna”
Daga haka ya juya da Bombee tiri tiri zuwa gidanna su.
Duk abinda yafaru akan idon Daneji,wacce take tsayen tana kallon su larai,hawayen dayake kwaranya a idonta ta share tareda sauƙa akan katangar,bayan taga muruje yafita zai dawo da Bombee.
A bakin zauren ta tsayah,yana shigowa tasa hannu ta karbeta,tun kafin tayi magana muruje ya sunkuyar dakai tareda bawa Danejo hakuri.
Tausayinsa ne yakamata,ganin ashe shima koƙari yake yakai wacce zasu dunga wasa a gidannsu,saidai a halin da ƴar tata take ciki bazata iya yin wasan dashi ba yanda yakeso,dan tata ƙaddarar ne warewa daga cikin mutane,saboda halittar da take ɗauke dashi.
Ko a haka ma yaron yana burgeta sosai,yanda koda darana ɗaya bai taba nunawa ƴar tata ƙyama ba,saima burinsa shine yadunga fita da ita wasa,shima a ga tasa ƙanwar,kallonta yake a matsayin kanwarsa wacce bashida itah.
“Babu komai muruje kaji,nasan kanason fita da ita,amma baka ganin yanda take ne,mutane zasu gudu idan suka idonta,dan haka ku dunga wasan iya a zaure kaji,yanzu jeka gidan kar innarka ta nemeka”
Ɗaga kai alamar yaji kafin ya tafi yanayi mata bye bye,itama tana miƙa masa hannu alamar zata koma.

___***____***____***___

Wata ƴar fara yarinya ce bazata wuce shekara biyar ba tashigo gidan tana kuka,babu ɗan kwali a kanta,silifas ɗinta a hannu,jikinta yayi butu butu ta ƙasa.
Kana ganinta kasan tuburbuɗata akayi a cikin ƙasa,kai tsaye inda Danejo take ta nufah tana mitsitstsika ido.
Tsayawa tayi da busar hatsin datake ta kalleta tundaga sama da ƙasa tareda jijjiga kai.
Bata tsayah wani bata lokacinta ba wajen jin mai yake faruwa,domin abin kullum ne kamar faɗar Allah.
Tunda Bombee tayi ƙafa tana fita waje,kullum kwanan duniya saita dawo gidan cikin kuka,wani lokacin an fasa mata vaki,a kwai lokacin dazata dawo ma jikin jini yara sun jefeta da dutsi,kowa yana cewa ga mayyah tazo.
Duk yadda kuma Danejo tayi ta hanata fita abin ya gagara,kullum tana wajen cikin yara,a cizeta a jefeta a tumurmusata,amma hakan bazai hana idan an jima ta koma ba,haka zatayi tayi har sai dare yayi ta kwanta,tun Danejo na tambayar ta mai ya faru harta daina ma tambayarta,dan zancen kullum ɗayane.
Yanzun ma jawo tayi kusada ita,tareda matsar da garin tuwon dayake gabanta tana tankaɗe. Kama gefen zaninta tayi ta kaɗe mata ƙasar jikinta,har sannan idonta yana manne tana kuka.
“Saikiyimin shuru ai,buɗe idon naga miye a ciki”
“Inna inna ƙasa ce a ciki,shule(sule )ne ya zubamin,wai idona ya rife ya daina ganinsa,shannan kuma ya tureni a ƙasha dannan karbi abin washana a wajen rahama”
“To naji kiyi shuru kinji,kullum ina faɗamiki,idan kinga zasu dakeki ki gudo gida kinji,sannan kuma ki ƙyalesu,wanda yadaki wani bai ramaba allah zai saka masa”
Rarrashinta Danejo ta dungayi,daƙyar ta samu tayi shuru ta manta da zancen,jikin dukk tabon dukane da kuma rauni,inda yara sukayi mata,abinka dama da farar fata.
Suna cikin hakanne inna laari tafito daga banɗaki tana tura ciki,haihuwa ko yau ko gobe.
Da farko jinya tafara,wasa wasa abu ya dunga yin gaba,har mlm Ahmadu ya ɗauketa zuwa asibiti,aikuwa gwajin farko aka ce cikine da ita,murna a wajen mlm Ahmadu nan ma kasa misaltuwa tayi.
Tunda aka dawo gida yayi wanan yayi wannan,haka inna laari tacigaba da rainon cikinta,wanda kallo daya zaka mata kasan tanajinsa har a cikin ranta,sannan kuma tayi godiya ga Allah,da itama yayi mata kyautar da bata taba zaton samu ba,bayan tsawon lokaci data ɗauka da cire rai.
Danejo ma a fili takeyi mata murna tareda ƴan uwa da abokan arziƙi,lokacin da labarin ya isa ga mutane ,gidan cika yayi maƙil da mutane,wai ma ba haihuwar ba kenan,inaga idan haihuwa kuma tayi?.
“Bombee mai yafarune naji kukanki daga banɗaki,ko yauɗin ma dai jiya i yau,ke bazaki rama ba kenan,taya zaki kare ƙanwar taki kuma ko ƙaninki uhm?”
“Jan dukasu idan suka tabamiin ƙanwa,bajan barsu ba Inna yaari”
Dan murmushi inna laarin tayi tareda cewa,
“Ko kefah,haka ake son babba da jarumta kinji,ki bar kukan haka,barina kawomiki ƙarago,ko bakya so kai?”
“Inasho”
“Tam barina kawomiki mutumiyar,ladan samomin allura da kikayi,wacce nake nema jiya a ɗaki”
Tsalle Bombee tayi jin za’a bata ƙarago mai suga,ita kuma murmushi tayi sannan ta shige ɗaki.
“Karfah kiyi fada a waje fah,ina kinajina koh,duk wanda yayi miki abu kizo ki faɗamun kinji,karnaji kinyi faɗa”
Danejo ta faɗawa Bombee fuskarta ɗauke da damuwan halin ƴar tata.
“To innah bazanyi ba”

…….to sai muce Allah ya sauƙi inna laari lafiyah………

 

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

 

 

 

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

 

Leave a Reply

Back to top button