Bakar Ayah Book 2Hausa Novels

Bakar Ayah Book 2 Page 57-58

Sponsored Links

Page 🖤 57••58🖤

 

 

 

“Hilyan lokaci yayi dazamu fita daga wannan kogon mu tafi,yakamata ki rarrashi Maryam ki faɗamata”
“Taya kake ganin zata saurara,har yanzu fah taƙi amincewa dacewar haidar ya mutu”
Matsawa kusada bombee sukayi wacce take durƙushe a cikin kogon dutsen,ta runtsa hannunta da ƙasa.
“Anty maryam yakamata mu bar garinnan idan har kinazo mu ɗau fansar dakike muradi”
“Da bancemuku bazan tafiba hilyan,saidai shin bazan samu lokacin da zan lissafawa zuciyata yawan abinda zata rike ba,har zuwa lokacin da damarta zatazo ta ɗaukar fansa.?”
Shuru sukayi a gefe suna jiranta har ta tashi dan kanta ta nufi fita daga wajen.
Tafiya suke tsakar dare cikin dokar daji batareda ɗar ba ko wani tsoron wajen,dan hakan dama yazamemusu jiki aikinsu ne nayi,kasancewar bombee tafisu damar gani idan duhu yayi yasa tayi gaba suna binta a baya.
Kwanan su biyu a jejin suna tafiya,in sun gaji su huta su cigaba,abinci kuwa wanda Allah ya horemusu su saka a cikinsu.
A zaune suke a bakin wutar dasuke haɗa da itatuwa.
Tunda suka bar kogon har yanzu bombee batace komai ba,suma ganin haka yasa basuyi mata magana sosai.
Dan in sukayi ma ba kulasu zatayi ba,a kuda bakin hanya suke,dan suna jiyo wucewar motoci da kuma haskensu.
Wata ƙarace ta doshi cikin kunnensu can lokacin da dare ya fara.
Hilyan ce ta kalli khmees da sauri a razane tace.
“Inaga fah hatsari akayi,kuma babu wasu motoci dasuke wucewa,baka ganin muje mu duba?”
Tashi sukayi zuwa wajen,basu daɗe da tafiya ba bombee tajiyo suna ƙiran sunanta,da baxata jeba saikuma ta tashi ta kaɗe wandonta ta nufi wajennasu.
Motace ta kifah sai jini ne yake zubowa daga cikinta.
Kallon su hilyan tayi wanda suke tsaye sun rasa mai zasuyi,ga kuma kukan jinjiri da suke jiyowa a ciki.
Ƙarisawa wajen motar bombee tayi fasa glass ɗin,hannu tasaka tazaro yaron daga hannun wata mata a cikin motar wacce take kusada window,sai callara ƙara yake saboda matsuwar dayayi da kuma ƙara,duk da kana jin kukan kasan yaron bashida cikykykyiyar lafiya.
“Innalillahi anty maryam da ransa kuwa,ko zamu kaishi cikin gari kai gidan marayu?”
Hannun matar taga yana motsi a hankali tana nuna musu hanyar gaba,wato kada sukoma garin.
Daga nan ta daina motsi.
Miƙawa hilyan yaron tayi tareda yin magana a taƙaice.
“Kisan yadda zakiyi dashi,tunda ku kuka ga haɗarin,ko kuma ki ajiyeshi a wajen ƴan sanda suzo,mukuma mu tafi kafin su taddamu”
Karbar yaron hilyan tayi cikin sanyin rai tareda cewa.
“Amma anty maryam kefah kika Ceto rayuwarsa a cikin motar,sannan idan muka barshi bakya ganin sanyin wajen zayyi masa illah?”
“To me kikeso nayi masa,ki lullubeshi da bargo ki ajiyemusu shi inda zasu ganshi”
Har bombee tafara tafiya tatsaya cak saboda abinda taji hilyan ta faɗa.
“Bakya ganin da hatsari mu barshi anan,wannan ba halin ki bane ba haka kike ba anty maryam”
Tahowa tayi ta ƙarbi yaron a hannun hilyan zata aijiyeshi a gefen motar,sai kuma ta tsayah tana kallon fuskar yaron,wanda yanzu yayi shuru kaman bashiba,duk da har sannan yana ɗan jan zuciya a hankali.
“Hilyan idonsa………”
“Meya faru baya ganine?”
“Irinnawa ne sakk idonsa,blue ne nasama cak nawa,bazan iya ajiyeshi ba zan tafi dashi”
“Meyasa ba…….”
Katseta tayi tareda cewa.
“Saboda inna barshi gidan marayu zasu kaishi,kuma am sure zayyi rayuwa irintawa kenan,wacce ko a madarki banason tunawa,zan tsayamasa naga waye zai masa irin abinda akayi min”
Ƙarisa maganar tayi tana cije baki tareda nannaɗeshi suka bar wajen.
Kallon kalllo khmees sukayi shida hilyan,inda bata da aljanu dama sai suce sun shigeta yanzu,tashi ɗaya saita sanja yanayi.
Komawa cikin jejin da sukayi yaro yace sam bazai zauna ba,dan haka basu da zabi dole suka koma cikin gari a dare.
Musamman yanda suka kulada yankan Dayake ƙaramar cinyarsa jini yana zuba.
Tun kafin su isa bombee taƙira wani abokinta wanda yake aiki a asibiti,tare suka tafi rasha dashi da kuma rahama.
Saidai su sun rigashi dawowa,tunda dama Military doctor ya karanta.
“Hello dr na’im ina kan hanyar dawowa cikin garinnan ta sirri,ganinan nakusa shigowa ka tabbatar ka sameni a bayan gari please”
“What maryam meyasa zaki dawo bayan kinsan haɗarin hakan”
“Uhm wani soul ne yake buƙatar kulawa yanzunnan shiyasa”
Kashe wayar tayi ta cigaba da jijjiga jinjirin wanda yake ta kuka.
Fuskarsu a rufe suna sauƙa a motar har safiya tafara.
Dr na’im suka gani a motarsa,nan da nan ya ɗaukesu zuwa cikin asibitinsa. Ƙaramine amma kuma yana tsari da abubuwan aiki sosai.
Tun a hanya bombee ta shaida masa mai yake faruwa,dan haka gwaji yayiwa jikin yaron domin ganin wanne kalar abincine zai shiga jikinsa.
Safa da marwa take a cikin ɗakin,sudai su hilyan suna zaune suna kallonta,yayinda yake ta ƙoƙarin yiwa yaron gwaji,an jima tace an gama shuru.
Cirewa abinda yake kunnensa yayi tareda fitowa daga cikin labulen inda yaron yake.
“Captain maryam gaskiya yaronnan jikinsa is very weak,duk wata nau’in formular ta madarar jarirai bazata ƙarbi jikinsa ba,sannan bugu da ƙari yayi loosing jini a ciwon daya ji.
Inaga abinda yafi kawai ku kaishi gidan marayu a samu wacce zatayi feeding ɗinsa”
“What na kaishi ina,da kenan amma ba yanzu ba,babu wata mafitar saita kaishi can”
“Akwai mafita amma nasan baxakiyi ba”
“Mecece inajinka”
“A halin da kike ciki bazaki so wata a kusada ke ba,sannan da alama bakyason rabuwa dashi,to mafitar shine saidai ki roƙi abokiyar aikinki kozata amince ta shaya dashi”
“Wai hilyan kake nufi,budurwace fa batayi aure ba,taya zata shayar da jinjiri”
“Wacce bata taba haihuwa ba ma zata iya shayar da yaro,saidai za’abi wasu prosess na injecting wani chemical dazayyi activating ɗin hormones ɗinta na haihuwa da kuma wanda yake kulada sarrafa ruwan mama”
“Ahah naji zayyiyu amma bazanyi wanann son kan ba na lalata mata rayuwa saboda muradina duk da kuwa nasan bazata ƙi amincewa ba.
Karka manta nima macece har yanzu,dan ina maida lamurana kaman maza hakan bai taba halittata da kuma matsayina na mace ba.
Idan har zayyiyu ni zan shayar dashi kayimin aikin akaina,
Amma abin zai ɗauki lokaci kuwa,yaron sai kuka yake?”
“Oh god kina nufin wai zaki shayar dashi,duk da ko aure bakiyi ba”
“Ehh zan shayar dashi,a yanzu shi nake da,zancen aure kam kuma kama barshi”
“Shikenan to zaki saka hannu akan takarda,batun ɗaukar lokaci kuma idan mun yi miki allurar zaki kwanta na wani lokaci,shikuma kafin sannan zamu saka masa ruwa wanda zai zame masa tamkar abinci”
“Okay deal”

Buɗe idonta take a hankali wanda yayi mata nauyi sosai,ƙoƙarin tashi take amma sai taji jikinta yayi mata nauyi,musamman ma ƙirjinsa wanda taji kaman an ɗora musu dutsi.
Tashi tayi ta zauna tareda jingina da jikin gadon,hilyan ce a zaune a gefenta ta taso da sauri kusada ita.
“Wai anty maryam mai ya kaiki wannan gangancin,baki duba da halin da kike ciki ne a yanzu zaki sake sakawa kanki wani,da nasan har haka zaki bi wajen ceton yaronnan da tun farko na ajiyeshi a gefen hanyar”
Taaƙarisa maganar tana share hawaye kaman zata rushe da kuka.
“In kin gama mitar miƙomin ruwa nasha,jinake kaman maƙwogarona zai daskare dan ƙoshirwa. Wai tukunna ma tsawon wanne lokaci nayi a kwance?”
“Awa shida fah da wani abun”
Tayi maganar tana miƙamata ruwan.
Ƙarba tayi takafa shi a bakinta saida tayi masa kaff kafin ta ajiye.
Gumine yake to mata,duk da ac dayake ɗakin.
Suna cikin hakane dr na’im yashigo riƙeda yaron a hannunsa,wanda yayi luff a farin ƙyalle.
Miƙawa bombee shi yayi tareda cewa.
“To bismillah saiki gwada ki gani shin ko ruwan nonon yazo”
Babu wata nadama kuwa bombee tasaka hannu ta karbi yaron a hannunsa,fita yayi shida hilyan aka barta ita kaɗai.
Kallon fuskar yaron takeyi,ƙyakykywane sosai,amma babu komai a fuskartasa sai hanci zuwatt,saboda ƙanƙantarsa,ga ƴar carnula da aka saka masa hannu.
Yaron yayi matuƙar shiga zuciyarta da kuma tausayinsa daya kama ta.
Ɗaga t-shirt ɗin dake jinkinta,tana kallon yanda ƙirjinnata ya sauya a lokaci guda.
Matsawa tayi ga mamakinta kuwa ruwan madara fari tass yafito daga ciki.
A bakin yaron tasaka masa,duk da ba wani sanin takamaimai yanda akeyi tayi sosai ba,amma dai tunda yashiga bakinsa kuma yana nema yana sha shikenan.
Ɗan jingina kanta tayi a jikin gadon tanajin yanda yaron yakejan ruwan zuwa bakinsa,kowacce ja ɗaya idan yayi har cikin ranta take jinta,tamkar ƙara dasa mata kusanci ake da yaron.
Muryar hilyan taji tana yimata magana.
“Uhm dr. Na’im yace wai dole zamu yi koda sati biyune saboda ki gama sanin mai yake faruwa,sannan zaki dunga shan magunguna da kuma allurar na kwana uku kafin ruwan nonon yazam standard”
“Ba matsala,amma kice masa sati guda kawai zanyi anan,kafin sannan kicewa khmees yaciro kuɗi a acct ɗina kusiyo min duk abinda nakeso,sannan kice ya saci hanya da ɗakko min motata a bayan ga barrack inda na ajiyeta”
“Tamm zan faɗamasa,to baki saka masa sunaba ma,yawwa ga nan kayan da aka cire a jikinsa da towel ɗin”
Miƙowa bombee kayan hilyan tayi kafin ta fita faɗawa khmees saƙon.
Bacci yaron yayi a jikin nonon,dan haka ta cireshi tareda kwantar dashi a gefe.
Kayan tafara duddubawa,purse da samu a cikin towel ɗin,da alama ta mahaifiyar yaronne.
Buɗewa tayi da ID card ɗinta a ciki na Nurse da kuma wasu takardu.
Buɗewa tayi taga takardar yarjejeniya ce tsakaninta da wani,harda sign a gefe.
Da alama wani ne yabata yaron akan ta riƙe,kuma ta mince ta karba.
Da alama kenan ba ɗanta bane matar.
Sunan wanda ya bata yaron ta gani.
Abdulmaleek Aliyu Jaan,(biological uncle).
Itakuma nurse ce wacce ta ƙarba ɗin..
Kenan basason ɗan ya rayu a gidanne,abu biyune ya faɗo mata a rai shine.
Ko dai Mugun nufi ne yasakasu nesanta yaron da gidansu,ko kuma saboda kareshi ne daga wani a gidan,koba komai binciken hakan bazai mata wuya ba,tunda tasan JAAN Company,amma kuma issue na gidanne bata sani ba sam.
Kafin lokacin dolelene ta boye identityn yaron kafin tagama gane kan komai.

*** ***

“Daga lokacinne bayan nakoma gembu gabaɗaya bincikena yatafi a familyn Gen abdu manga da kuma na gidannan,dama nariga nasaka a raina cewar idan na ɗau fansar Haidar,to zan bayyana matsayin ƙaramin haidar a wajenku,koda kuwa a bana zaune a gidan.
Saikuma gashi tun kafin hakan yafaru Hajiyah Zeenah ta nemeni da kanta,bawai kuɗinda zata banine yasaka ni amincewa da ƙudurinta ba,saidan ganin yanda damammakina suka zomin a lokaci guda.
Ganin hakanne yasa na faɗawa su hilyan cewar kada koda wasa suyi maganar da wani kan cewar bani na haifi haidar ba,har sai wannan lokacin yaxo”
Wannan ne labarin haɗuwata da Haidar da kuma rainonsa wanda nayishi a cikin gidannan tsawon wata takwas kenan zuwa yanzu.
Sauran kuma dalilin bada shi da Abdulmaleek yayi duk zakuji daga bakinsa,duk da nasan ina kyautata zaton ɗan Hafsa ne,tunda ranar daya bata shi a ranar ne kuma hafsa ta rasu itada ɗan cikinta”
Kowa shuru yai,yayi jugum da labarin da Bombee ta bayar,babu wanda yataba kawo haka a cikinsu,ciki kuwa harda Abdulmaleek ɗin.
Tunda kafin wani yasake magana sukaji iyah sayyada ta rushe da kuka,durƙusawa tayi tareda kamo hannun yaron,wanda shima ya runtuma kukan bai santa ba.
“Yaka nan ɗan arziƙi,dama ashe jinin hafsafuna yayi saura kuma zan ganshi a duniyar,kuma ma wai yana cikin gidannan tsawon lokaci ban sani ba,ohh Allah ni ƴa su,sannu ƴar nan aradu kinyi ƙoƙari,ashe muna tareda tarin maƙiya munan bamu sani ba,hmmm bama ya wannan shegiyar mai ido kaman na ƙwarƙwata,ashe zambo take mana cikin aminci bamu sani ba”
Ɗauke kai Lailah tayi cikin nadama,firgici da kuma razani na labarin data ji a yanzun.
Abdulkareem ne ya kalli ɗan uwannasa wanda ya tsurawa yaron ido ko ƙiftawa bayayi,dama tun kallonsa dashi na farko yaga kaman yagane idon yaron,saidai abinka da maza taya zai tuna,kuma ganin idon bombee shima haka yake waye zayyi tunanin ba ɗan ta bane.
“Bro kaikuma menene dalilin ka nacewar haidar ya mutu bayan ba haka bane”
“Saboda ina son cetar rayuwarsa mana,baka ganin lokacin halin da ake cikine,kowa fah yasan lubnah ce take cutar da matan yah Jabeer,to amma wazai yi magana kowa yayi shuru.
Ganin hakanne dana shiga ɗakin naga gawar Hafsah a kwance,ga kuma jinjirin yana motsi kaɗan kaɗan, tausayinsa da kuma muradin tseratar dashi suka shiga raina.
Itama Sister suwaiba wacce take tsaye a gefena tausayin yaron nagani a idonta sosai.
Hakanne yasa mukayi yarjejeniya da ita akan takarda,kan cewar zata raineshi har zuwa yagirma yayi koyi kare kansa batareda matsala ba kafin ta dawo dashi.
Kafin sannan kuma zamu kai gawar jaririn daya rasu mu ajiye mata mu boye rayuwar ɗan.
Hakan kuwa akayi na fito nace sun rasu dukkansu itada yaron,har doctorn ma a lokacin bashida masaniyar mai ya faru.
Bayan angama zaman makoki an ƙare na nemi number sister suwaiba na rasa,dan dama tacemin zata tafi garinsu adamawa,inyaso saita dawo tace ɗan kanwarta ta dakko a can.
Ganin ban sameta ba yasa na je asibitin,ananne aka shaida min cewar tayi hatsari a hanyarta tafiya,kuma dukka mutanen cikin motar suka rasu babu wanda ya tsira.
Anan na tabbatar shima ya rasu kenan,tunda babu wanda yacemin jinjiri a rayu a motar.
Wannan ne nima abinda nasani gameda lamarin,naso faɗawa Jabeer abinda ya faru,saidai kuma a ganin yanayinsa a lokacin labarin babu abinda zai haifar koda yaji”

Bayan jin labarin Abdulmaleek nan kowa ya tabbatar da cewar haidar ɗan Jabeer ne na jini gaba da baya.
A lokacinne kuma ƴan sanda suka shigo fita da Hajiyah rabi da kuma Lailah da mijinta.
Kowa a falon bayyi magana ba ballantana yaji tausayinsu har aka fice dasu.
Lailah da Hajiyah rabi sai zage zage suke kan cewar bazasu yarda sam,dole su ɗauki mataki,amma wannan duk ihu bayan harine.
Tunda aka fara bada labarin Hajiyah Zeenah take kukan nadama,wanda daman kowa yake faɗamata zaizo watarana,wanda tabawa yardarta take ganin sune masu sonta ashe burinsu ɗaya ne a rayuwa shine ganin bayanta itada a halinta.
Wacce kuma ta tsana take ganin ta a matsayin tantiriya ashe tsawon lokaci ta ɗauka tana taremusu harin abokan gaba batareda saninsu ba.
Wai kuma ƙarshen bayani ma har jinkanta ta riƙe tamkar ɗan cikinta ta shayar dashi ta kulada shi,sannan ta toshe kunnuwanta ta aibatashi da akeyi,duk ta kuwa tasan asalinsa da matsayinsa,badan komai ba saidan Kada ta bayyana koshi a waye a cutar dashi.
Yau itakuwa mai zatace da wannan matar ɗanta,wacce a yanzu kunyar haɗa ido take da itah.

A hankali kowa yake watsewa yabar sashen bombee ɗin,daga ita sausu inna Danejo kawai danginta,wanda rabin zamannasu duk nasiha Malm Ahmadu Yake musu itada su hilyan,haƙiƙa shi kansa yaji tausayin ƴar tasa sosai dayaji abinda tashiga a rayuwa.

Kanta a sunkuye tashiga cikin falon,kana ganinta kasan dama taji labarine daya birkita mata tunani.
Da alhj Aliyu taci karo a falo shida Maleeka..
Ƙarisawa tayi wajen sa ta zauna a gaban kujerar tasa.
“Shin yanzu kin yarda da abinda na dunga faɗamiki a baya,na cewar ki daina fifita watacan bare kina ɗaukar maganarta fiyeda ahalinki,sannan bakomai ne dan bakyaso zaki ce sai ya zamo yanda kike so ba,wani lokacin akwai yiyuwar mutum yayi haƙuri da abinda yagani kokuma yake faruwa,yarinyar nan babu abinda bakice gameda ita ba,kin sheganta ɗanta fiyeda kima ashe yaronnan jikanki ne kuma jininki”
Rushewa tayi ta kuka kaman ranta zai fita,dan dama neman hanya take.
“Wlh nagani,naga ayah fiyeda yanda kowa yake zato,a yanzu banajin zan iya fuskantar ta ma,dan allah ka yafemin mijina”
“Nidama ban taba riƙarki da komai ba,saboda nasan akwai ranar dazata zo ki gane abinda kike kuskurene,yanzu tubanki a waje ɗaya zamu ganshi shine aikinki da kuma yanda zaki zauna da mutane”
“Inshaallah zan gyara daga yanzu”

Yana kwance akan gadon yana kallonta har tagama shafa mai tasaka kayan bacci.
Bakin gadon ta matso ta zauna,daina abinda takeyi tayi tana kallon Jabeer wanda ya kafeta da ido.
“Ina yake?”
Murmushi tayi takaitacce kafin tace.
“Uhm nemansa kake,ai yanzu kam ganinsa zayyi maka wahala,yana wajen iyah wai,maleekah ce tazo ta ɗaukeshi da magriba,wai a can zasu kwana wajenta”
“Amma ai zayyi kuka tunda ɗazu ma kuka yayi data ɗaukeshi”
“Uhm amma bazayyi ba idan da maleekah ne tunda yasanta,sannan ba fitsari yake ba inya kwanta saida safe,ɗazu yatafi har kayi kewarsa?”
“Uhm nayi kewarsa,amma idan ke kika tafi ba kewa zanyi ba,zuwa zanyi na sameki”
A hankali yake maganar kamar mai koyo,kana gani kasan tursasa kansa yake yin maganar da itah.
“Yakamata ka kwanta jikinka yasamu hutu,don yau baka samu baccin rana ba”
Taƙarisa maganar tana jawowa system ɗinta.
Tun kafin ta buɗe yaɗora hannunsa akai,tsayawa tayi da buɗewar tana kallonsa,shima kuma itan yake kallo.
“Naji zanyi bacci amma kema yakamata ki bar wannan aikin ki kwanta ki huta,kada ki damu da taruwarsu,idan nasamu sauƙi dukka zan gama su a lokaci kaɗan”
“Amma……”
“I need to hug you and sleep with together,zan iya samun damar hakan,yafaɗa yana buɗemata hannyensa”
Sauƙe a jiyar zuciya tayi tareda ajiye system ɗin.
Fuskantarsa tayi tashige jinkinsa ,a hakan suka kwanta maƙaleda juna…..

Gud night,muhaɗu a last chapter inshaallah……..

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

Leave a Reply

Back to top button