Hausa NovelsInda Rai Hausa Novel

Inda Rai 1

Sponsored Links

*INDA RAI* 💞

 

*By*

 

*MARYAM ABDULLAHI*

(oum shahee)

 

 

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

 

BOOK 01

 

FREE BOOK

 

09033255221

 

 

GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MAƊAUKAKIN SARKI, DA YA BANI IKON FARA WANNAN LITTAFI, WANDA SHI NE NA FARKO, ALLAH KUMA YABANI IKON RUBUTA, ABUN DA ZAI AMFANI AL-UMMA.

 

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

 

 

 

page 01

 

 

 

 

A yau cikin garin kano, an tashi da tsananin zafin rana, wanda hakan ya tilasta ma wasu daga cikin mutane zama a ƙarƙashin inuwa, dan gujewa tsananin zafin ranar, da wata irin iska mai ƙarfi.

 

Unguwar zangon dakata, wani ƙaramin gida ne, kana iya hango cikin gidan tun daga waje.

 

Gaban gidan ko ƙofar kirki babu, babu walwar fili, a takure yake, ɗaki biyu ne a cikin gidan, ko ina ka duba babu datti, a share yake fes, ɗaya daga cikin ɗakin, wata murya ta ce

 

“Maryam ita rayuwar duniya, ko wani bawa da yanda take zuwa ma sa, matuƙar, mutum ya na shaƙar, iskar duniya, kuma mumini ne, to ya kamata ya fuskanci ƙaddarar rayuwa”.

 

“Ɗago kai Maryama tayi

tana kallon yanda mahaifiyarta ta ke jan numfashi da ƙyar, cikin matsanacin ciwo, wanda yaci ƙarfin ta. Inna Haule ta ci gaba da cewa, “Maryama, ki mini alƙawari, ko bayan raina za ki kula mim da kan ki, kuma duk rintsi kar ki bari, dangin mahaifinki, su ci galaba a kan mugun nufin su”.

 

“Sake jan numfashi Inna Haule tayi cikin a zabar ciwo, zata sa ke magana, “Maryam ta yi saurin saka dogin yatsunta a kan bakin Innarta, ta na mai girgiza ma ta kai, “ki dai na takura kan ki da yawar magana Inna, kina buƙatar hutu a halin yanzu, yau tun safe babu a bunda ki ka sa a bakin ki. “Murmushi ƙarfin hali Inna Haule ta yi, ta lumshe idanun ta, ba ta ce komi ba, ganin hakan ya sa Maryama ta ce, “Inna, bari naje gurin Innar Rabi, na sa mo miki ko gasara ce, yanzu na da ma miki koko, sai ki sha kin ji Innata,?? “buɗe ido Inna Haule tayi, dan ba ƙaramar wahala ta ke sha ba, kawai ta na daure wane, saboda ƙwanciyar hankalin ƴar’ta ta, ɗaga ma ta kai kawai ta yi dan da gasken ta na son ta sa abu a bakin ta ya sauƙa a cikin ta. “Maryama ta ta shi ta fi ta, sa kafar ta cikin tsakar gidan kenan taji muryar mahaifinta, Malam Bukar, “ina za kije? kode ya won ta zubar ɗin zaki,? “Dam zuciyar Maryama ta buga da ƙarfi, har sai da ganin ta ya ɗauke na wani ɗan lokaci,

 

“Cikin ladabi kan ta ƙasa Maryama ta ce, zan je gidan su Rabi ne, “mtswww, Malam Bukar ya ja dogon tsaki, “to saura ki wu ce yawon gan talin da kika saba zuwa, mtswwww, ya sake jan dogon tsakin, ya sa kai ya yi wucewar sa cikin ɗakin da ta fito.”Da ƙyar Maryama ta ke ɗaga ƙafa ta na jin yanda ƙirjin ta ya mata nauyi sosai, dama kuma tun ta shinta yau ɗin ta ke jin hakan.

 

 

“Assalamu alaikum,”

 

“Wa’alaikissam,”cewar Innar Rabi, da ke zaune a ƙasan bishiya ta na aikin sanwar rana, ƙarisa shigowa tsakar gidan Maryama ta yi, cikin san yin tafiyar ta ƙarisa har gaban Innar Rabin, gaisheta ta yi kan ta a ƙasa cikin ladabi da sanyin jikin da yau ta ke jin sa tun ta tashin ta yau ɗin, amsawa Innar Rabin ta yi cikin kulawa, ta ce Maryama ya jikin Innar ta ki? “da sauƙi sosai Inna, dama zuwa na yi idan kin rage sauran gasara ki bani na je na damawa Innata, yau tun safe ba bu abun da ta ci, “subhanallahi, haba Mero, mai ya sa ki ke hakan?bayan ni da kai na na ce kina zuwa karɓa mata kokon tun sanyin safiya,? sake yin ƙasa da kai Maryama ta yi tana wa sa da gefen mayafin fa, tashi Innar Rabin ta yi, ɗaukan kofi ta yi ta ciko mata da shi da kokon, har lokacin ko motsi Maryama ba tayi daga in da ta ke ba, miƙa mata kofin ta yi tace, gashi maza han zar ta ki kai ma ta, sannan ki tabbatar ta sha sosai, nima ina gama aikin nan zan shigo naga jikin nata.

“Hannu biyu Maryama ta sa ta kaiɓi kofin kokon ta ce, mun gode Inna, Allah ya saka miki da mafificin alheri.

 

 

“Cikin sauri ta ke tafiya ta na jin farin cikin samun kokon, yanzu zata kai wa Innarta, ta sha ba sai ta tsaya hura wuta ba.

 

Shigowar ta gidan ya yi dai dai da tsin kewar zuciyarta, ganin har lokacin mahaifin nata ya nan, magana yakeyi shi kaɗai amma ba ta iya jin mai yake cewa, cikin sanyin jiki ta ƙarisa ƙofar ɗakin, sallama ta yi amma ba bu wanda ya amsa ta, daga baffan na ta da baya amsawar dama har Innar ta’ta, jim ta yi kafin ta ɗaga yadin da’aka sa kale a bakin ƙyauran ɗaikin ma tsayin labule mahaifin nata kaɗai ta gani zaune a gaban Innarta ya na ta sanbatu shi kaɗai, jan zanin da ke kusa dashi ya yi ya rufe wa Innarta ta duka jin ta, cikin sauri Maryama ta ce, baffah Inna ba ta son zafi, ka buɗe ma ta ko iya fiskar cema, ko kallon ta Malam Bukar baiyi ba ya sa kai ya fi ta, cikin sauri Maryama ta ƙarisa shiga cikin ɗaikin, kofin hannun ta ta ajjiye ta na cewa, Inna ta shi zakiyi daga baccin nan kisha kokon, gashi nan an samo bama sai na hura wuta ba, shiru ba ta ji Innar ta yi magana ba, hakan ya sa ta ƙarisa kusa da ita ta janye zanin da’aka rufeta dashi, cak ta tsaya da zanin a hannun ta, kanta ta ji ya sara mata da ƙarfi, kafun ƙirjin ta ya amsa, ƙwaƙwalwar ta ta karɓa, duk da ba ta ta ɓa ganin gawa a gaban ta ba to yau tabbas tasan Innar ta tafi, kenan rasuwa tayi?ta tambayi kan ta, innanillahi’wa’inna ilaihirra’ji’un, shine kalmar da samu damar fi towa daga bakin ta, kafun jin ta ya fara ɗaukewa, ganin ta ya fara barin cikin ƙwayar bakin idanun ta, luuuuuu ta ta fi ta faɗa kan gawar Innarta ta.

 

 

MUMBAI ƘASAR INDIA

 

“Tafiya ya keyi kamar mahaukaci sabon kamu, ko’ina yaga ƴan mata sai ya tsaya ya duba ko Allah zai sa ya da ce, amma har yanzu 12:20pm ba bu a lamaun zai ga koda mai kama da mrs dream ɗin sa, ƙarar wayar sa ce ta dawo da shi daga dogon tunanin da ya tafi, ya zama dole zuwa gobe ya bar Mumbai zuwa new delhi, ko Allah zai sa ya gan ta a can, Imran kenan, mashin saurayi mai kimanin shekaru talatin da biyar a duniya, ƙyaƙyƙyawa ajin ƙarshe, farine tas, irin farin a salin shuwa arab, dogo mai cikar zati, ha kyau ga ilimi, uwa uba a sali, gashin kan sa kwance luf kamar ba india asali, sake shigiwar kiran wayar sa, a karo na biyar ya sa shi ɗaga wayar, cikin husky voice ɗinsa mai daɗin sau raro ya yi sallama, “haba Son, ya kamata ace zuwa yanzu ka dawo gida hakanan, cewar momma ɗin sa Hajiya Ashshe, “Imran ya ja dogon numfashi, cikin shagwaɓar da ko a cikin mata sai an yi da gaske a samu ya ce, “oh oh my sweetheart, i’m coming back to nigeria soon in shaa Allah, cikin wahalar magana ya sa ke cewa, “Pakistan sun ta da rikici mommy, “subhanallahi, yanzu kana ina? fatan in ca ka ke akwai tsaro? kana lafiya kuwa?oh god, “Imran ganin yanda hankalin mommyn sa ya tashi ya sa ya buɗe idanu kamar yana ga ban ta cikin ƙasa da murya dan da gaske ya gaji da magana ya ce, “no mommy ina lafiya ba bu abun da ya sameni, ina cikin kulawa sosai,but karki faɗawa kowa, musamman bro da daddy, gudun tashin hankalin su, “numfashi Hajiya Ashshe ta sauƙe ta ce, shikenan tun da kana lafiya, ka kulamin da kan ka kaji,? “karki damu momcy zan kwanta yanzu, bye, kit ya katse kiran, ya furzar da wata isaka mai zafin gaske a bakin sa, kafun yaja ƙafa da ƙyar ya ƙarisa can in da ya yi parcking ɗin motar sa ya yi gidan sa.

 

 

Gudu take yi ya na bin ta, amma ya kasa kamata, ganin zata masa nisa ya sa ya ƙwala ma ta kira amma sam muryar taƙi fito wa, ya na ganin wani abu mai duhun gaske ya sha gaban su, a hankali haske ya ya fara wanzuwa ya na ya ye wannan duhun, can daga nesa ya hango ta, tana nufar in da hasken yake fito wa, wasu santala santalan yara ne masu ƙyan geske ta ke nufa, amma me? su kuma yaran gurin sa suke ta howa da gudu suna kiran sa da abbuuu.

 

A firgice ya farka daga baccin nasa ya jiƙe sharkaf da gumi, dafe kansa yayi ya na addu’a, a fili ya furta ina zan ganki,? tashi ya yi ya nufi wani tamgameman phato, wanda sai kayi masa kallon tsaf, za ka ga zanen da a ka yi, a ƙasan photon, an yi wani rubutu da ruwan gwal kamar haka.

 

“What did your ayes do me

“They made me forget myself”

“let me stay somwhere near you”

“I don’t release who I’m any more”

“My heart truly Say’s”

“That I’m falling

In love with you.

I’ am lossing my heart to you”…

 

Writing by oum shaheed🥰💞💞

Leave a Reply

Back to top button