Bakar Ayah Book 2Hausa Novels

Bakar Ayah Book 2 Page 25-26

Sponsored Links

Page 🖤25••26🖤

 

Saida ya sauƙe wayar daga kunnensa kafin ya kashe komai na motar ya fito waje.
Maida murfin yayi ya rufe tareda nufar sashennasa yana ɗan Jijjiga key ɗin dake hannunsa.
Ɗan sauri yake da alama so yake ya sanja kayansa yabar gidan.
Hannu yasaka ya buɗe ƙofar shiga falon,sai kuma ya tsaya ya kalli wajen tukunna,domin yayi tunanin koba sashennasa bane,saboda ƙamshin ɗaɗɗan turaren daya tunkari hancinsa.
Ƙafarsa yasaka cikin falon,inda sanyin tile ya ratsa tafukan ƙafafunnasa,yayinda hankalin sa kuma da idanuwansa suka bazu cikin falon suna karemasa kallo.
“Anyah kuwa nawa sashen na shigo”
Yafaɗa a ransa.
Komai yayi ƙal ƙal kaman glass,kujerun ma kaman basuba..
Idonsa ne yakai kan kulolin abinci,kaman jiya yauma an ajiyesu a dinning ɗin.
Nufar inda suke zai buɗe yauma yaga menene a ciki..
Da ƙaramar takarda yaci karo a wajen an ninketa.
Buɗewa yayi domin ganin kai ta ƙunsa,rubutune bamai yawa ba
“Ban ajiye Juice akan dinning ba yana cikin fridge.Sannan inkana buƙatar wani abu ka dunga rubutawa kana ajiyemin”
Ajiye takardar yayi ya nufi ɗakinsa domin cire kayan aikinsa,har sannan sauyin dayagani a sashennasa bai bar cikin kansa ba.
Nan ma wani abin mamaki yayi arba dashi,an sanja bedsheet ɗinsa da kuma duvet,kayansa dasuke hanger an ɗebesu,an share an saka room freshner mai ƙamshi.
Jan dogon numfashi yayi tareda sakinsa hade da murmushin dabai san ma yaƙwace masa ba.
Banɗakin yashiga shima a gyare,dama yayi tunanin hakan.
Taƙaitaccen wanka yayi kafin yafito zai saka saffan kaya a jikinsa.
Shima wardrobe ɗin an masa gyara na musamman,wajen kayansa na yadi daban,suit daban,hakama na bacci da kuma na shan iska.
Da sauri yagama shiryawar yafito wajen abincin,dan na jiyama har yanzu ɗanɗanonsa bai barshi ba,ga kuma wani zai sake ɗanɗana.
Bayan yagama buɗe fridge yayi zai ɗauki juice ɗin data faɗa.
Anan kam harazana yayi tareda matsawa baya,wai anya kuwa ba mafarki yake ba?
Abubuwan sunyi wuya a ƙirasu da gaske ne,yanda yaganta batayi kama da matar gidan dazatayi waɗannan abubuwan ba,duk yasan tabbas akwai dalilinta nayin hakan,amma yagagara daina bashi mamaki abin.
Duk girman fridge ɗin an cikashi tamm da sinadaran motsa baki,kaman a super market
Snacks jucicess kala kala,kowanne kala da inda aka shiryasu..
Hannunsa yakai ya ɗauki wani cup da farin abu a ciki,anyi seeling bakin da ledar cup ɗin.
Buɗewa yayi ya zuba abakinsa,daya kafa bai ajiyeba saida ya kusa shanyewa,saboda yanda ƙamshin ayaba da kuma madara ya ziyarce shi ga kuma sanyi.
“Anyah kuwa wannan ba asiri tayimin ba nakejina kaman a wata duniyar daban,abin kaman yawuce ace ƙwaƙwalwa ta ɗauka,irin waɗannan abubuwan ko asiri takemin takeyi babu abinda zai dameni,in mutuwa ce ma tasameka a daɗi ba’a wuyaba.
Ɗakinsa ya sake komawa har sannan kofin yana hannunsa yana kurba,takarda ya ɗauka da biro ya dawo falon.
“Na dawo gida na tarar da abin mamaki wanda na daɗe banga irinsa ba,koda akwai wani dalilinki nayin hakan,amma nidai a zuciyata naji daɗin hakan,in bazaki damuba inason na haɗu dake zamuyi magana”
Yana gama rubutawa ya ajiye a inda ta ajiye nata kana ya fice daga sashen cikeda na nishaɗin tarbar daya gani.
Bai nufi sashen Lubnah ba sai ya shiga motarsa ya bar wajen,dan dama tun safe ta ƙirashi a office cewar bata nan,inda sabo ya saba sai tayi tafiyarta kafin tace masa ta tafi,tun abin yana damunsa har ya daina ma sakashi cikin ransa.

Tun sanda taji wayar da Jabeer yayi a shigowarsa cikin gidan,har sannan bata motsa ba tana zaune,Hilyaan ce tashigo da sauri tareda cewa.
“Anty maryam yadawo ya sake fita fah”
“Eh nasani”
Daga haka batasake cewa komai ba ta nufi sashennasa,shurun data tsinci kanta dayi,da kuma shiga nazari yabata mamaki matuƙa,meyasa to zataji babu daɗi akan hakan.
Ahah ba babu daɗi taji ba,kawai yarinyar ce bata kwanta mata a rai ba sam,dolene tayi ƙwaƙwƙwaran bincike a kanta.
Ga wannan aikin data ƙirƙira nayiwa mutuminnan,badan komai bane saidan tashiga ɗakinsa tasamo bayanai gameda mai yake wakana,amma babu komai daya shafi abinda take so a ɗakin.
Haushine ya ƙulleta ɗazun ganin aikinta ya tashi a banza.
Yanzu batada zabi illah tasake shiga jikinsa sosai,ta hanyarsa ne kawai zata iya yiwa Gen abdu manga burki batareda ta saka mutanen ta a haɗari ba,itama kuma bataje ta aikata ba.
Wajen data ajiye abincin tanufah,kaman yanda tayi tsammani ya ajiye takarda kuwa.
Bayan ta gama karantawa mitstsiketa tayi tana cije baki.
“Ina ruwana dajin daiɗinka,yafimaka dakasan da wata manufa nayi badan kaji daɗiba,wato kaji daɗin abinda nayi a banza ni ban samu abinda nakeso ba koh? Hmm”
Kulolin abincin ta ɗauka tafito,tana murmushi wanda bawanda yasan ma’anarsa sai ita.
Jaleelah ce a zaune akan tabarmar daƙinsu itada Fareeda,suna ta taɗi akan ya aurenta zai kasance,dan yaune mutane zasuzo daga gidan su Jabeer.
“Iyeee nifah ban taba kawowa a rainaba Jaleelah zakiyi aure ba,ballanta kuma nan kusa,shikenan wato zaki tafi ki barni koh?”
Fareeda tafaɗa kaman zatayi kuka.
Kama hannun Fareeda tayi tareda yin guntun murmushi.
“Haba sweetynah inna tafi ai ba munrabu bane,nasan zaki dunga zuwamin koh,alaƙarmu bazata tatsayaba dannayi aure na tafi na barki ba ai”
“Eh naji dai,da alama wannan mutumin yaciri tuta tunda ya saye zuciyarki daga bayyanarsa lokaci guda.
Inna tace tundaga yanzu za’a fara shirye shirye,dan Baba bazaisaka doguwar rana ba sosai”
“Uhm hakana naji an faɗa,nima kaina auren a bazata naji yazomin wai zanyi aure,ko yaya ƙawayenmu zasuji”
“Ahh ya zasuji kuwa,yanda naji mana”

Hira suka cigaba dayi,gabaɗayah mutum bazai gane suna san auren yakasance ko ahah ba.

Tarba mai kyau akayiwa ƴan uwan Jabeer a gidan su Jaleelah,a mutunci da komai aka gama tsaida magana,nan da wata uku masu zuwa Auren Jaleelah da Jabeer,ba’a saka dayawa ba sannan kuma ba’ayita a ƙurraren lokaci ba.
Lokacin da Jabeer yaji wata uku aka saka baiji daɗi ba sosai,don yayi tunanin baifi wata guda ba.
Amma kuma su iyayenta suna buƙatar shirye shirye na aurar da ƴar tasu,sannan koda yace basai sunyi komai ba yasan bazasu yarda ba,shiyasa kawai ya haƙura tareda cewa Allah ya kaimu.

“Hajiya hajiya hajiya…..!!!!!”
Wata mai aikice take runtumawa Hajiya rabi ƙira a zaune,wacce tashigo sashennata da sauri kaman zata kifah.
“Ke Lu’ube mai yasameki haka kaman kinga Aljan”
“Hajiya…..hajiya Jawaheer ce hajiya,ta yanka tsintsiyar hannunta jini yana ta zuba,tana riƙeda wuƙar ta hanamu mu isa inda tak…..”
Tun kafin tagama Hajiya rabi ta mangajeta ta nufi sashen Jawaheer ɗin da gudu,tun kafin ta isa take jiyo jan ajiyar kukan Jawaheer,da alama kuka tayi har ta godewa Allah.
Kaman yanda Lu’ube tafaɗa tana riƙeda wukar a hannunta,jini kuwa yanata zuba a hannun ba tsayawa,abinka da jikin hutu cikeda jinin lafiyayye,yasamu hanya ai ba tsayawa.
Wani jirine yake ɗiban Hajiya rabi saboda zunzurutun tashin hankalin datayi tozali dashi a yanzu.
Cikin rawar jiki take takawa zuwa inda ƴar tata ke tsaye,wanda itama jirin take saboda rashin jini.
“Jawaheer ƴata mai yasa haka,mai yayi zafi,mai kika rasa a duniyar nan ki faɗaminshi dahar kike ƙoƙarin tafiya ki barni akan sa?”
“Jabeer mommy,mommy kinkasa bani Jabeer,mutumin da tunda na buɗi ido na tashi da sonsa,kin kasa bani shi kullum sai kwana kwana kukemin.
Yau kawai saijin labari nayi wai an bashi mata ansaka rana,nikuma ina nan ina dakon soyayyarsa wacce take cin raina kullum.
Tunda bazaku banishi ba gwanda na mutu na huta kawai”
Tana gama faɗin hakan yafaɗi yaraff a ƙasa. Da sauri Hajiya rabi ta kinkimota daga ƙasan tana sharbar kuka kaman ƙaramar yarinya.
Ihu take tana ƙiran driver wanda yashigo ya taimaka mata suka kinkimeta zuwa mota sai asibiti.
Sai bayan Hajiya rabi taga anshiga da ita emargency an tsaida jinin kafin tasamu nutsuwar ƙiran wayar Hajiya zeenah.
Tana ɗagawa tunma kafin tace wani abu tafara zazzaga masifa_
“Kin kyauta Hajiya zeenah,ɗanki zai angwance nan da wata uku,nikuma ƴata zata mutu kafim sannan”
“Innalillahi hajiya rabi mai kike faɗa haka,van fahimceki ba wlh”
Labarin abinda ya faru ta maida mata ta waya,da sauri kuwa tashiryah zata taho asibitin,dan abin babbane sosai.
Hajiya rabi tana nan tana safa da marwa Hajiya zeenah tashigo aaibitin.
Da saurinta kaman an jehota,wajen ta nufah fuskarta itama ɗauke da tashin hankalin
“Yayah jikin yarinyar ta farfaɗo?”
“Ina kuwa ta farfaɗo Hajiya zeenah,har yanzu likitoci basu cemin komai ba,tun sanda nayi miki wayah nake zaune wajennan ban motsaba”
“Ahah aikuwa yakamata ki dan zauna ki samu nutsuwa,inshaaallah kyakykywan labari zamuji,kada ma ki damu kinji.
Ruwa ta dauka a fridge na wajen tabawa Hajiya rabi tasha,sunan zaune babu mai cewe komai wata nurse ta fito.
“Hajiya karki damu ta samu sauƙi sosai,saidai dayake jikinta yayi weak,to tana buƙatar ɗan hutu kafin ta dawo normal”
“Yanzu bacci take kenan babu abinda ya damet”
“Eh babu wata matsala,zaku iya shiga ma,amma kada ku tasheta daga baccin”
A tare suka shiga ɗakin da Jawaheer ke kwance,ita kaɗaice a ɗakin kasancewarta VIP patient.
Kaman yanda nurse ta faɗa bacci take hankali kwance,hakanne kuma yasake kwantar da guntun tashin hankalin ta hajiya rabi ke ciki.
“Da alama ta samu sauƙi,amma menene abinyi na gaba kenan?”
Hajiya rabi tafaɗa tana dafe da hannun Hajiya zeenah.
“Abunyi ɗayane shine mudawo da aurenta zuwa lokaci ɗaya da waccar matsiyaciyar yarinyar kawai,ta hakanne kawai zamu ceceta daga sake cutar da kanta.
Ajiyar zuciya ta sake jin abinda Hajiya zeenah tafaɗa,kuma dama abinda take so taji kenan tun dazu.
“Shikenan hakan yayi kam,yanzu idan tatashi zan sanar da ita,saiki sanarwa Abban shi Jabeer din ya turo kawunnanasa kumadu a saka itama wannan ranar”
“Karki damu da hakan,tamkar ya farune,dama ai babu wanda bai san da zancen ba,kawai a saka ranar dukka lokaci guda,kinga daga nan saimusan yanda zamuyi da ita waccar ɗin”
“To ya zancen waccar yarinyar kuma da kika kawo,bakya duba mai takeyi kina ganin hakan ba matsala”
“Nima nayi tunanin hakan,shiyasa ma na saka iyani tasamo min dattijuwa wacce zata dunga kulamin da shige da ficensu dukka,saboda barinta tayi abinda taga dama batareda sanina ba akwai hatsari sosai.
“Gaskiya kam,yanzu idan ta tashi sai a fara maganar shirye shirye toh”

Daga haka hankalin Hajiya rabi ya kwanta,dandai bazata so ciwon ƴar ta ba,amma jin labarin abinda Jawaheer tayi ga kowa yasa An saka ranar fiyeda yanda take ma tsammani,da alama burinta zai cika na ganin Ikon Jaan family a hannun ƴar ta,zatayi komai kuwa wajen ganin sauran matansa biyu basu haihu ba kafin ƴar ta,dan ita Lubnah bata kawo mata treating kaman Bombee da Jaleelah.

Mutane basu yi tsammani ba sai jin labarin wani baikon sukayi na Jabeer,wato dai nan da wata uku mata biyu zai aura lokaci guda kuma rana ɗaya.
Surutu kuwa babu mai tsayar dashi na wannan labari daya taso.
Ko kaɗan Bombee bataji komai ba dataji labarin,dan dama tayi tunanin hakan daga Jawaheer ko Hajiya rabi,a duk lokacin da labarin baikonsa da Jaleelah ya isa garesu.
“Toh so funny,ashe gidannan zai zama filin nishaɗi kenan?”
Bombee tafaɗa tana ƙaramar dariyah.
“Meyasa kika ce haka anty maryam?”
“Ohh ke baki gani ba,mata uku a waje daya ai zansha kallo,kuma kowaccensu tanaji da nata salon”
“Naji kina zancen mata uku,amma nikuma mata huɗu nake tunanin zasu zauna a nan ɗin koh,beside ai kallo yana ga dramar dazakiyi dasu ,ni wannan zata fi burgeni”
Hilyaan tafaɗa tana kallon wani waje daban,yayin da a wani bangaren kuma tana dariyah ƙasa ƙasa.
“Hmmm karki sakani cikin jerin matansa masu zama suyi kishi dominsa,ni mai tafiyace inna gama abinda zanyi”
“Anya kuwa tafiyar zata yiyu in zuciyar mai tafiyar takafe anan din?”
“Hilyaan!!!”
“Yi haƙuri na daina,barima naje haidar ya tashi,haidar zakasha kallon faɗan mamarka da kishiyoyinta kenan”
Tana daga hanyar corridorn take iyo maganar,wanda yasaka Bombee yin murmushi tana Jijjiga kai.

“Maleekah ina faɗamiki ki bani hanya naje wajen ubanki. Ban cika Sayyada-tateen ba idan har na bari suka kashe min jika,mennene amfanina kenan a gidan.”
“Iyah meyasa kike hakan,tun jiya da daddare nake fama dake,matan fah yana sonsu,kuma shizai zauna dasu,kemai naki a cikin to fisabilillah”
“Mai nawa a ciki,kinci gidanku da mai ruwana a ciki Maleekah.
Mata huɗu russ a tare,ta ina kunkuminsa zai gamsar da mata huɗu yana kuruciyah shiba sadauki ba,duk da kakanku jarabbene zai iya gado amma inashi ina Mata huɗu.
Saboda suna haifeshi saina barsu su tsufarshi da wuri.
Duk wannan ba laifin kowa bane sai zeenatu,munafukar mata,ta maida yaronnan kaman injinnnan mai kamada mutane nacikin Telebijin(robot).
Allazee aiki,inazaka aiki ina ka fito aiki,saisun nakasashi tukunna zasuji daɗi?”
Kanta Maleekah ta kama tana runtse ido,gaba ɗaya kanta ciwo yake na masifar da Sayyada-tateen ta kwana tana balbala mata,ita bata ci zomo ba amma kuma itace da gudu.
“Maleekah yanzu ina magana kikayi kunnen uwar shegu dani koh?”
“Mai zance miki toh Iyah,nayi iya yina,inkinka zakije to kije,amma karki manta idan abba yaji hayaniyah suma yakeyi saboda ciwonsa,kina zuwa kikayi hayaniya zai suma sai an kaishi asibiti”
Zaro ido tayi tareda yin gajeran tunani.
“Asibiti kuma ke ƴar nan,jikinnasa ne ya tashi kaddai”
“Jikinsa bai tashi ba,amma idan kikayi je kikayi hayaniya zai tashi”
“Ahah nikuwa ina zan bar jiki ya tashi ƴar nan,abinda ake neman lafiya tasamu,toh bazajen sashennaku ba,amma ki ƙiramin ita uwar taki,tacan kisaka ayimin kunun tsamiyah ki kawomim.
Ina nan ina jiranki,saura kuma ki maidani goruba ki shanya baki dawo ba”
Taƙarisa maganar tareda zama akan kujerarta tana hamma.
Jijjiga kai Maleekah tayi tana dariya ƙasa ƙasa,dan kuwa kaman tasani bazata dawo ɗin ba,kunun ma aikowa zatayi a kawo mata,bazama ta dawo sashen ba saita manta da zancen auren Jabeer ɗin tukunna.
“Haba fitinnanniyar tsohuwa kai,saida nace abba ya barni na bar kasarnan na tafi karatu yaƙi,babu abinda nake fuskanta a gidannan sai fitinar rigima.
Su ya Abdul sunji daɗinsu basama ƙasar,yah Jabeer ne kaɗai ke shan wahala damu.
Wai meyasa mommah ma take ta auramaka matannan oho,bazata barka ka huta ba.
Barina shiga sashennasa naga mai nene a ciki”
Ƙarisa maganar tayi cikin damuwa tareda yin hanyar dazata kaita sashen Jabeer ɗin.
Tafiyah take tana kalle kalle har ta isa wajen.
Wulgawar mutum tagani tacikin bishiyoyin wajen,saida tasake dubawa taga ashe mata biyune suka nufo hanyar da take,suma da alama sashen zasu shiga.
Tun daga nesa tayi tsammanin dama Matar yayannata ce da mai aikinta,dan su kaɗaine a wajen sai Lubnah,ita kuwa tafi haka girma sosai.
Suna iso wajen Maleekah ta kalli wani wajen,dan bata san mai zatace ba, cikin ƙaramar murya tace.
“Matar yah Jabeer ina kwana”
“Lfy”
Shine abinda Bombee tafaɗa mata a taƙaice kana tayi hanyar shiga ciki.
Binta tayi kallo tace a ranta.
“Daga ganinta kam dama batason mutane”
Hannun taga Hilyaan ta miƙomata tana murmushi,wacce bazata wuce sa’arta ba.
“Barka da Maleekah ykk”
“Uhm barka amma taya kika san sunana?”
“Lahh yaza’ayi ina zaune a gidannan matsayin mai yimata aiki kuma nakasa sanin familyn mijinta”
“Kenan itama tasanmu dukka”
“Babu wanda batasani ba gameda danginku. Karki damu da yanda tayi miki,batada saurin sabo da mutane,amma yanda kika ganta ba haka take ba,tanada kirki sosai antynnaki,kema zaki gane hakan wata rana”
“Uhm nagani kam,kowa yana cewa batada mutunci,amma nikuma sainaji ta burgeni kawai,barina tafi,amma bansan sunanki ba.
Dama lambunsan zai shiga”
“Ni sunana Hilyaan,tunda har kinzo nan kizo mushiga ciki mana ki huta”
“Ahah babu komai”
“Wacce irin ƙanwace bazata shiga gidan yayanta ba,zo muje ciki kada ki damu”
Hannun Maleekah Hilyaan taja suka shiga sashen Bombee.
“Yawwa tunda kingama surutun kinshigo ki ɗauko haidar ya tashi naji kukansa. Ni barina ɗebo kulolin abinci,nasan zuwa yanzu yagama dasu”
Saida tagama maganar ta kulada Maleekah wacce hannunta ke riƙeda na Hilyaan ɗin.
Saurin cire hannunta tayi daga na Hilyaan ta sunkuyar dakai,dan tasan matar yayannata bata tsammaci ganinta a falon ba.
Bata ce komai,duk da tayi mamakin ganin Maleekah ɗin,saima buɗe ƙofar da tayi na sashen Jabeer ɗin tashiga.
“Karki damu ba abinda zatace,zo muje ɗakina”
Binta tayi a baya kaman jela ,saida ta ɗauki haidar a ɗakin Bombee kafin suka nufi nata ɗakin.
Kuka yake lokacin data shiga,amma tana ɗaukarsa yayi shuru yana ƙinkishi.
“Shima idonsa irin na uwarsa”
“Uhm idonsu iri ɗayane”
Daga haka Maleekah bata sake tambaya ba,itama kuma Hilyaan batasake bata ƙarin bayani ba.
Wanka tayi masa a bandaki ta fito,tana shiryashi suna magana haka sama sama da Maleekah,wacce take zaune a bakin gado.
“Naga yau da makaranta ko bakije bane?”
“Uhm banida lecture yau,iyah Madeenah ce takeda,tun ɗazu ta tafi,kefa wacce makaranta kike?”
“Hhhh ni iya diplomer nayi na gama”
“Ayyah kuma kinaso kici gaba?”
“Eh to ina aiki ai bayan nayi karatun,na ajiyene saboda wani dalili”
“Ayyah da alama kinaji da matar yah Jabeer,dan naga tsakaninku kaman ba mai aiki da uwargidanta ba”
“Sai yaya da ƙanwa koh?”
“Ehh mana haka nagani?”
“Kusan hakan muke,dan Allah duk abinda kika gani a sashennan kada ki faɗama kowa mai yake faruwa a wajen,in ban roƙa dayawa ba hadda Hajiya zeenah ma”
“Lahh kada kidamu inshaaallah bazan faɗawa kowa ba,naji daɗin yanda kika sakemin karon farko daga haɗuwa”
“Nima naji daɗin maganarki,let be friend”
“Dama kuwa kaman kinsan banida ita,indai banida lecture zaman gidannan gundurata take,saina rasa mai zanyi,wayama gajiya nake da dannawa. Yanzu nasamu abokiyar hira.
I hope dai bazan takura miki ba koh?”
“Bawani takura,nima nasamu abokiyar hira ai da daɗi sosai”
Bombee ce ta turo ƙofa suna tsaka da hirar .
Suma itan suke kallo.
“Miƙomin ɗana inkin gama shiryashi,duk sanda kuka gama hirar saiku fito ku sameni”

_*SADI-SAKHNA CEH*_

 

____****🖤🖤****_____

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

 

 

Leave a Reply

Back to top button