Cinikin Rai Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Cinikin Rai Book 1 Page 3

Sponsored Links

BOOK ONE
003
“Mr Amjad!” “ Kiyi abin da na saka ki, babu ruwanki da Malik Menk Jordan, idan da kin ga abin da ya faru, ba zaki fara shiga wannan lamari ba. Kowani mutum yana da iyakarsa don haka ki tsaya iyakarki” kallon shi tayi na wani lokaci, kafin ta ficce daga office ɗin, lallai tana son sanin waye shi? Me ya taka har haka da kowa yake jin shakkarsa haka. Tana fita Mr Amjad ya kalli MD da Salim. “a firgice nake, ina ga zan zauna a kamfani na tsawon kwanaki, domin Malik ya manta da ni, idan ba haka ina fita qur’ani kashe ni zai yi.”

Shiru sukayi kowannen su, da abin da yake yawo a ransa, kafin Salim ya ce masa. “Yallabai me yasa ka razana haka ne? Ni fa bana tunanin Malik ya kai yadda kuke fada, kawai kashe prime minister yayi haka ne domin ya cusa muku tsoro da firgici. Kuma yayi nasarar haka” juyar da kai Mr Amjad yayi yana kallon window waje. Kafin ya mike kana ganin yadda fuskarsa ta nuna zaka fahimci yana cikin damuwa soka hannunsa yayi cikin aljuhun wandon ya ce.
“Tabbas rayuwar tana tafiya da yadda mutane suka tsarawa kansu, amma rayuwar da Malik ya tsarawa kansa, yafi kowacce rayuwa bala’i.” Kallon juna MD da Salim suka yi kafin suka mai da hankali kan Mr Amjad.
Kuma aka rasa waye zai magana, wayar Amjad ne yayi gunji. Kamar ba zai dauka ba, ya dauka.“Amjad Lamid ne?” kamar wanda aka watsa mishi ruwa haka ya amsa da cewa. “Eh ni ne, waye” “Na kira ne, na baka shawara kada ka sake shiga abin da babu ruwanka tsakanin Malik Menk Jordan da Mr Khuldu Jahid Khan”

“Amma waye kai?” Mr Amjad ya tambaye shi, murmushi me sauti na wayan yayi sannan ya ce mishi. “Sani na bai da wani amfani, amma zan baka shawara ka nisanta kanka, daga wannan hatsaniyar Malik ya fi ku hauka, a duk lokacin da ya fahimci kana cikin masu niman shi sabga shi.” ya fada mishi yana kashe wayar.

Wani azzababen tsoro ne ya mamaye zuciyar Mr Amjad, ilahirin jikinsa rawa yake, yadda zaka fahimci, yana cikin tashin hankali. “Sir akwai matsala ne?” Kallon MD yayi da ya tambaye shi, sannan ya ce mishi.

“Na jima ina Kasuwancina, ban tab’a shiga tashin hankali irin na yau ba, amma qaddara sai da ta haɗa ni hanya da Malik Menk Jordan, a da wai-wai nake shi a yau da na gani da idanuna na tabbatar shi din ba kanwar lasa ba ne.”

“Sir wai mene ne matsalar ne?” MD da shima yake razane, domin daga yadda Mr Amjad yake firgice zai tabbatar maka da cewa yana razane. “Ban san kaddaran da ta hada ni da Malik ba? Amma nasan mutuwa ta ce ta kusa bayan haka” kura mishi idanu suka yi. Sannan ya cigaba da cewa. “Idan har kuka ji labarin na mutu don Allah ku saka idanu akan iyalina.”
Su kansu a rude suke, domin kuwa labarin mutuwar Prime minister ya ratsa lungu da saƙo na cikin garin Keivroto city.

^^^^
A lokacin da Zeenobia ta bar S….. Digital art, ta nufi hanyar gida da mutanenta, a nan ne ta fahimci garin ba lafiya domin duk inda suka wuce zanga-zanga ake wanda zai nuna maka, alamar kowa a fusace yake, ko da yake ai ba kowa bane domin wannan rigimar ba don talaka aka yi ba, suna yi ne domin kare muradunsu da aljuhunsu. Duk wanda zaka gani tow ba yana yi don talaka ba ne, yanayi ne domin cikawa aljuhunsa yan canji.

Ajiyar zuciya Zeenobia tayi tana kallon yadda ake fashe-fashe, babban burinta su isa Al’umma charity House, domin kare wannan gidan hakkine da ya rataya akanta, ba iya ita ba, ga duk wanda yake numfashi a cikin gidan. Domin ganin yadda yan zanga-zanga suke barnan dukiyar gwamnati, yasa ta kalli black ta ce mishi.
“Ka taka motar, mu isa akan lokaci domin za a iya saka curfew nan da wani lokaci.”
“An gama Yar kunama!” Ya kuwa karawa mutanen gudu, cikin ikon Allah suka isa gidan cincirindon jama’ar gidan a bakin get din gidan yasa ta sauke ajiyar zuciya. “Yar kunama!” Sauka tayi daga motar tana kallonsu. “lafiya kuka yi cirko-cirko?” ta tambaye su, tana cire glass din idanunta. “ina zamu iya nutsuwa mun ji labarin gari babu lafiya, ke kuma da su Dundurosu kuna waje.” murmushi tayi ta wuce bakin get ta ja kofar tare da rufe kofar gidan bakidaya. “ina son nayi magana da murya daya, kowani lokaci za a iya saka dokar tab’aci, ban lamunci wani ya ketare gidan nan ba, idan na fahimci haka ya faru hmm.” ta fada tana haurawa sama.

“Didih wai da gaske Malik Menk Jordan, shaidani ne?” juyawa tayi ta dauki yarinyar da bata wuce shekara uku ta shiga tafiya da ita. “Sweetheart ban sani ba, Shaidani ne ko mutumin kirki ne, abin da na sani ya kashe Babban mutum me daraja.” ta fada tana shafa kanta.

“Didih Abbana ya ce wai shaidani ne, shine Iya tace kar a bari kiji labarin kome.” juyawa tayi ta kalli Iyar da ta mata yake. “Iyah sun fadi wani abu ko Sweetheart?” Gyada kai tai, sannan ta wuce kofar dakinsu yarinyar ta ajiye ta, sannan ta wuce ɗakinta, kafin ta bude ta samu Hafsy tana dakin. “Alhamdulillahi kin dawo lafiya” kallon juna suka yi, sannan ta wuce ban daki. Sai da sauya kayanta, sannan ta dawo falon dakin. Bude karamin firji tayi ta dauki abin sha, ta zauna tana me kunna TV. “Ni tsorona daya kada wani abu ya same ku, sai gashi kin dawo akan lokaci.” kurban fanta tayi tana kallon tv.
_Izuwa yanzu hukumar sun saka dokar curfew na tsawon awanin kafin a gama binciken mutuwar mai girma Prime minister._ gidan tv suka fada, rage ƙarar tayi tana faɗin. “Ban san wacce duniya muke ba, amma kuma.” saukowa daga gadon Hafsy tayi, ta rike hannunta. “Meke faruwa?” gyara zama tayi sannan ta ce mata. “Aikin da aka ba ni, wai zan na gayyatar mutane su saka hannun jari a kamfanin na zata security service zasu bani.” ta fada tana sauke ajiyar zuciya.

“Tir security service? Allah ya sauqaqe miki. Ai wuce wannan level din, matsayinki ne. Zaki kara zama yar gayu eyee!” ware idanu tayi, tana gyada kai kafin ta ce mata. “Hafsy ina son aikin amma kuma.” sai da ta sauke ajiyar zuciya me nauyi, wanda zai tabbatar maka tana cikin damuwa. Kafin ta cigaba da cewa. “ina son aikin amma kuma, gani nake kamar akwai kasada. Domin ban saba harka da mutane ba, taya zan iya bibiyar mutane don su saka hannun jarinsu. Ala misali wani abu ys faru nice a ciki fa.” rike hannunta hafsy tayi tana faɗin. “ina ji a jikina zaki yi nasara, matuƙar aka samu matsala tow dauke shi a matsayin jarabta, bayan nan kuwa labarin zai sauya.”

Kurawa Hafsy idanu tayi tana, ta kasa kiftawa. Kafin ta ce mata, “ni kuwa gani nake kamar wani abu zai tafi ya dawo. Bana son abin da zai d’aga min hankali!” Dariya Hafsy tayi tana fad’in. “Ni kuwa gani nake ba wani abin da zai faru, domin kuwa khair in sha Allah.” Ajiye tin din fanta din tayi tana cewa. “Allah yasa.” Daga nan suka bude hirarsu.
ΠΠΠ
A cikin Keivroto city kuwa, rikici ake wanda ya haifar da kona-kone, wanda yasa dole jami’an tsaro suka shiga kame mutane, don kuwa barnan tayiwa. Kuma take-taken mutane shi ne nufar manyan masana’antun Menk Jordan manufacturer’s, don haka aka zuba matakan tsaron ko ta kwana. Sannan aka bada umarnin duk wanda ya isa wurin a tashe shi.
——-
Public Officer For Legal Investigation and Criminal Emergencies stations Keivroto city (Police stations) fitowa jami’an yan sandan suke da sauri. “Ya ku jami’an tsaro, ku sani a yau garin Keivroto yana fuskantar tashin hankali da barazanar barkewar rikicin siyasa da kabilanci, sakamakon mutuwar Prime minister, Zubair Fatihu Sayyad! Don haka a cikin sanarwar da muke samu ya tabbatar da cewa manyan kamfanonin Mayor Malik Menk Jordan, yana fuskarta barazana don haka dole zamu kwantar da tarzoman da ake yi, sannan mu tabbatar mun kare takalawa da dukiyar al’umma da gwamnati.”
“Yes Sir” suka fada lokaci guda, kafin su rufe baki sai ga wasu manyan motocin Hilux 4×4 bakake wuluk har guda shida. Hankalinsu ne ya tsaya akan motar. Suna yan sanda ne suka fara fitowa a motar da bayan motar. Kafin suka budewa bakar audin da take tsakiyarsu. A hankali aka sauko kafa, sannan ta fito sanye da bakar madubi. Sara mata aka shiga yi, ta fito rike da sandarta, tana me zare glass din daga idanunta. “Barka da zuwa Asp Zulfa!” Nufar cikin Office din yan sandan tayi tana faɗin. “Ku tattaro min baki daya yan sanda office din nan, da na sauran yankuna baki daya, ina son ganawar gaggawa. ” “Yes Ma” suka fada mata, kafin minti Talatin, bakidaya sun haɗu. “Barkanku jami’an tsaronmu. Duk da a kurarren lokaci na iso, ayi kokarin rubayyan tsaro da kwantar da hankulan al’umma, sannan a tabbatar an saka shinge ga wasu wuraren kafin zuwa gobe, kafin nan a tabbatar an kama duk wani me tadda hankalin al’umma, umarni ne daga sama ba umarni na wa ba ne.” ta fada tana kallon kayan sadarwan. “Akwai dakin tsaro?” “Eh ma!” Gyada kai tayi tana faɗin.
“Ku kai ni dakin na ga yadda kulawar garin take, za a turo jami’an tsaro daga Gista nan da awa ashirin da huɗu, sannan ina
son na je inda gawar Mai girma Prime minister yake!” “Yes ma, gawar Prime minister tana, trust palace hotel. Anan suka gabatar da taron.” dakin tsaron suka kaita, kai tsaye ta umarci a fara aikin binciken wucin gadi.
Daga nan, hotel inda aka yi zaman suka wuce. Cikin gari aka kara baza jami’an tsaro, inda gawar Prime minister suka inda aka saka zaren criminal scenes. A hankali suka tsallaka wurin, leda suka bata a ta saka a cikin takalmin, sannan ta amshi handglove, kafin ta wuce. “Ma baki saka facemask ba!” “Ok officer” a hankali ta shiga zaga motar, tana gefenta wani dan sanda ne, yana rubuce rubuce. Sai da suka gama zaga motar kafin ta bude motar inda prime minister yake zaune. “ina masu binciken gawar me suke samu?”
“Gasu nan” mikawa juna hannu suka yi, sannan ta ce mata. “Khairat Hadi, nice na jagoranci binciken gawar prime minister, sai dai rashin ƙwanciyar hankali yasa ban gama ba, na koma gefe domin kuwa akwai abubuwan da ya faru. Bayan zuwanmu.” gyada kai tayi tana faɗin. “Ok gba damuwa, yanzu sauran binciken dole sai kun wuce da shi office din ku ko?”

“Eh haka nake son na gaya miki!” kallon hotel ɗin take, tana me gyada kai kafin ta ce. “Akwai Cctv a cikin hotel din nan, daga shigowa zuwa nan harabar guda shida ne, don haka a nad’e mun duk wani bayani da aka shigar na wata shida baya, har zuwa yau. Sannan a kai ni dakin da aka yi taron.” “Tow muje ma” haka ta shige har cikin hotel. Ganin yadda ma’aikatan hotel suke cikin damuwa. Murmusawa musu tayi tana faɗin. “kada ku damu, aikin mu zai yi shi ne bisa goyan bayanku. Sannan idan muka gama, zamu tafi.” Inji dan sandan da yake bin bayan. Shiru tayi tana kallon fuskar mutanen wurin. Kafin ta ce musu. “A wani daki aka yi taron?”
Fitowa Manager din hotel din yayi, yana fadin. “Sunana Nuhu Kasim, ni ne manager na hotel din, muje na muku iso cikin dakin taron.” gyada kai tayi, suka shiga cikin hotel ɗin, sannan suka fara zaga cikin dakin taron. “lokacin da aka gama taron baki daya suka fito ko daya bayan daya suka fita?” girgiza kai yayi ya ce mata.
“Mr Elbashir Jamal Arab ta fara fita, tare da yan majalisunsa, sai Prime minister.” kallon shi tayi tana kallon agogon hannunta. “an samu minti nawa a tsakaninsu?” shiru yayi yana kallon sama kafin ya ce mata. “Za a kai minti Talatin zuwa arba’in!” gyada kai tayi tana cewa. “Ok ina son zan duba dakin da Cctv din ku yake.” “Ok Ma” da ya fada, tare da yiwa ɗan sanda da suke tare jagoranci har dakin. Ita kuma ta cigaba da zaga dakin taron tana kallon wurin.

Har yamma suna zaune a wurin, kafin karfe uku garin yayi tsit, a hotel ɗin tayi salla, sannan suka koma office dinsu. Anan ta ga an kama mutane dayawa, wasu yan jagaliya ne, kallonsu tana faɗin. “waɗanan sune aka kama ko?” “Yes ma!” wucewa Office dinta, ta nufa tana me zama a kujerenta. “Ma ya zamu yi da su?”
“A rufe su, kada a ba da belinsu, a tura su ga kotu.” shiru yayi kafin ya ce mata. “ Ma akwai mutanen Xno kuma ba a kama su da laifin tadda zaune tsaye ba, kawai dai sun fito ne zasu kai Yara asibiti aka kama su” “Umarni aka ba ni, idan shima Xno din ya taka doka a karya shi, don haka kayi yadda nace.” shiru yayi sannan ya ce mata. “Mace ba namijin ba ce.” d’ago gajiyayyun idanunta tayi tana faɗin. “ Mace ce kuma yar daba?” ta tambaye shi, gyada mata kai yayi. “Ku tattaro min files na masu laifi bakidaya, don haka babu zancen sake su.”

Shiru yayi yana kallonta, bata san inda take tura kanta ba ne hala. “Hala baki san wace ce ita ba? Gaskiya ba zan iya wannan aikin ba, kawai a sallame mutanen.” sake baki tayi tana kallon shi,.kafin ta ce mishi. “Nawa take biyanka?” murmushi yayi mata sannan ya ce mata. “Ai ko daya bata biyana amma kuma ina gaya miiki gaskiya ne domin su yan jagaliyar nan sun fi mu, yanci don haka ki kyale mata Mutanenta, domin kowani lokaci zata iya zuwa kuma zata dauke su.”
Murmushi tayi sannan ta ce mishi. “Ok ina jiran zuwanta. Ina jiran abin da zata yi.”
——-
Bubuga kofar dakinta ake, domin tun bayan da tayi sallah hafsy ta fita. Ƙwanciyarta tayi abin, bata san wainar da ake toyawa ba, abun da ya faru kuwa tighgas da ake wurgawa ne ya haifarwa Chu-chu numfashinta ya fara sarkewa wanda yasa dole Black da Dundurosu suka fita da ita zuwa asibiti basu gaya mata, bayan sun kai ta asibitin ne, shi ne Black ya ce bari ya zo ya sanar halin da ake ciki, ai kuwa yana barin asibitin yan sanda suka kama shi, duk yadda ya musu bayani amma fir suka ki yarda suka saka shi cikin yan kame. A gidan kuwa kiran Dundurosu suka yi ya gaya musu, ai ya turo Black an kwantar da Chu-chu. Ai ko ba gaya musu ba, an kama Black. Jin bugub ba na kare bane, yasa ta bude kofar “Zeeno an kama Black ” barcin da bai gama wartsakewa bane ya neme shi ta rasa. “Garin yaya?” nan suka gaya mata…….
#Mmmj
#Zeeno
#Beauty
#Beast
#RomanceS
#Tycoon
#WeatherMan
#Rumors
#Jelousy
#Cursed
#Mai_Dambu
*08130269641 for more info*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: *CINIKIN RAI……*
Beauty and the beast♡

Leave a Reply

Back to top button