Hausa Novels

Kanwar Matata 3

Sponsored Links

🦜 *_K’ANWAR MATATA_*🦜

_Matar Sayyadee_
_Wattpad @Matar_Sayyadee_

☀️ *ZAFAFA WRITER’S ASSOCIATION*☀️

Page 3

Hannu Sarah ta d’aura a kanta tare da fad’in, “Haba Lami wannan wani irin magana kike yi haka? Mai yasa a kullum burin ki, ki zubar min da mutunci a idanun Farouq? So kike kiyi ta danka mu a cikin gidan babu aure?” Sarah ta fad’i tana kuka sosai. Shi kuwa Farouq da idanu kawai yake bin Sarah da mahaifiyarta kamar wawa. Don sam bai son gasgata abunda kunnuwansa suke ji. “Bak’ar munafuka! To sai nayi magana. Wato baki so nima na samu rabo na ko? To wallahi komai dani za ayi shi. Juyo nan ka bani amsar tambayata, shin kai ne uban cikin dake jikinta?” Wani irin b’acin rai ne yake tasowa tun daga can k’asan zuciyar Farouq, bai iya magana ba sai kallon fuskan Sarah yake yi yana son jin wani k’arin bayani ko kuma ta k’aryata zancen da mahaifiyar nata take yi. Amma maimakon haka, Sarah sai girgiza kanta kawai take yi hawaye na zubowa daga idanunta. “Wai ba da kai nake yi bane Umar da kayi min banza kamar wata sa’ar ka!” Lami ta fad’i a zafafe. Gyara tsayuwa Farouq d’in yayi tare da kallon Lami k’asa-k’asa sannan yace, “Ban san maganar da kike yi akai ba! Kwata-kwata ma ban fahimci mai kike cewa ba Mama.” Dak’uwa Lami tayi masa tare da fad’in, “Uwarka nace kaji? Ai nasan ka fahimci wannan ko! To ni menene ma na tsayawa sai naji ko kai ne kayi cikin ko ba kai bane. Bayan na san kai d’in fak’iri ne ba wani abun kirki zan samu daga gare ka ba. Amma sai dai ka sani, daga yau ban k’ara bata ko loma d’aya daga cikin abincin gidana, don sai taci ne abun cikinta zai ci, kuma ni da in ciyar da jinin ka, gwara na ciyar da karuwai goma babu lada.” K’asa-k’asa Farouq yace, “Ai yanzu ma karuwan kike ciyarwa a cikin gidan.” Kallonsa Lami tayi tare da matso da kunnanta tace, “Kace me?” Kau da kai Farouq yayi tare da fad’in, “No babu abunda nace!” Dogon tsaki taja sannan ta juya ta shige cikin gidan har da bugo masu k’ofa. Kicib’is suka ci da Na’ima taci uban kwalliya ta tsuke cikin k’ananan kaya kamar d’iyar arna, “Y’ar albarka har zaki wuce?” Yamutsa fuska tayi tare da fad’in, “Eh! Idan kun ji shuru ku rufe gidan kawai, don ba lallai na dawo gida na kwana ba.” “To Allah ya tsare.” Fad’in Lami har da d’aga mata hannu. Duk abunda Na’ima da Lami suke cewa, tsaf a kunnan Sarah da Farouq. Fitowa Na’ima tayi daga cikin gida tare da gallawa Farouq harara ta saki tsaki tare da tsirtar da yawu. Har tayi gaba, sai kuma ta dawo dai-dai inda Farouq d’in yake a tsaye tare da sauke glasses d’in fuskanta k’asa kad’an sannan tace, “Ina fatan masoyiyar taka ta fad’a maka tana d’auke da ciki har na tsawon sati biyu.” Ta k’arisa maganar tana daga yatsunta biyu a fuskan Farouq d’in. Wani banzan kallo Farouq ya bita dashi mai cike da tsana. Sarah kuwa ji tayi dama tana da layar b’ata ta danna kawai ta ganta a cikin gida saboda tsananin kunya mai had’e da tsoro da take ji. Farouq yana kallo Na’imar ta bud’e gaban motar wani mutum wanda a haife ta haife ta, yaja motar suka bar layin. Juyowa yayi tare da kallon Sarah wacce kanta ke k’asa, ya jima yana kallonta tare da had’iye wani miyau mai d’aci da ya tokare masa mak’oshinsa sannan yayi k’arfin halin fad’in, “Sarah mai nake ji haka daga bakin mahaifiyarki da y’ar uwarki?” Kuka kawai Sarah ta fashe dashi do ita kanta abun jinsa take yi kamar hauka ko rainin hankali ta bud’e baki tace bata san ta yanda aka yi ciki ya shiga jikinta ba. D’agowa tayi ta kallesa tare da fad’in, “Ni wallahi tallahi…..” D’aga mata hannu yayi tare da fad’in, “Na fahimta, basa son alak’ata dake ne shiyasa suke son raba mu da wannan zancen na su. Ni kuma idan har ba canza hali za kiyi ba Sarah, babu mai raba mu idan ba mutuwa ba. Ni dai alfarma d’aya nake rok’o a wajen ki Saratu, dan girman Allah ko sau d’aya kada rayuwar da y’an uwanki suke yi ya burge ki. Idan kika mun haka, ni kuma zan cigaba da tsaya miki duk rintsi, kunnuwata zasu kasance a toshe, haka babu wani suka naki ko kuma laifin y’an uwanki da za ayi amfani dashi wajen nuna min bak’inki har yayi tasiri a waje na.” Kuka Sarah take yi har da shasshek’a, ita kad’ai tasan mai take ji a cikin zuciyarta. “To wai kukan na miye ne haka? Idan har ba b’acin rai na kike son gani ba, ki share wad’annan hawayen naki.” Bayan hannu Sarah ta saka ta share hawayen fuskanta tare da k’irk’iran murmushin babu babu inda ya tsaya sai iya lab’b’anta. “Yauwa ko ke fa! Sannan abu na gaba, ban ji dad’in yanda ba ganki d’azu ba, na d’auka tuntuni mun riga mun gaba magana akan irin shigar da kike yi. Kin san fa da shigar jikin mutum kad’ai akan iya gane wanene shi. Dan girman Allah ki daina saka wannan zaro-zaron gashin idanu nan da wannan k’umbar dake hannunki. Ni wallahi kyama yake bani. Wanda Allah yayi maki ma ya ishe ki Sarah.” Hawaye na zuba a idanunta ta furta, “In sha Allah daga yau ba zan k’ara saka d’aya daga cikin abunda ka lissafo ba.” Ajiyar zuciya Farouq yayi tare da fad’in, “Allah ya miki albarka amaryata ta sati hud’u masu zuwa. Ki shiga gida hadari ne sosai a gari. Sai mun yi waya.” Bata iya cewa komai ba sai murmushin da tayi tare da yi masa bye-bye ta shige cikin gidan. Tana turo k’ofa ta jingina da k’ofar tare da dafe k’irjinta da hannu d’aya sannan ta toshe bakinta da d’ayan hannun tana kuka sosai. Juyawa tayi ta lek’a ta wani d’an rami a jikin k’ofar, ga mamakinta sai ganin Farouq tayi tsaye a wajen amma ba k’ofar gidan yake kallo ba, wani wajen yake kallo daban. Can kuma ya saki ajiyar zuciya tare da tsallake kwatar dake gaban gidan ya wuce. Sai a sannan Sarah ta zame k’asa ta fashe da wani irin kuka mai tafasa zuciya. Ta jima a wajen tana kuka kamun ta mik’e ta nufi cikin gidan. D’akin su ta shiga ta cire hijjab d’in jikinta ta ninke tare da rataye sa a hannun wardrobe sannan ta cire suwaitan jikinta ta mak’ale a abun rataye jaka sannan ta kashe wutar d’akin don babu kowa a ciki, sauran y’an uwanta suna d’akin Lami kamun masu zuwa fita dasu su k’araso. Hawa kan gadon tayi ta kwanta rigingine tana sak’awa da warwarewa akan cikin dake jikinta. Sosai tayi zurfi a tunanin ta yanda aka yi ta samu ciki, sai dai duk iya zurfin tunaninta, bata gano bakin zaren ba, don zata iya dafa Qur’ani tayi rantsuwa bata tab’a sanin wani d’a namiji ba a duk tsayin rayuwarta. Daren ranar bacci b’arawo ne ya kwasheta. Kiran sallar asubahi kuwa, a kunnanta ladani ya kwad’a shi. Saukowa tayi daga kan gadon tare da kunna wutan d’akin haske ya kawo, babu kowa a d’akin, hakan ne ya tabbatar mata da ita kad’ai ta kwana a d’akin. Don da ace y’an uwanta sun dawo daga yawon banzan su jiya, babu abunda zai saka su kyale ta ta kwanta a kan gado ba tare da sun turo ta k’asa ba. Kai tsaye d’akin mahaifinta ta nufa, kamar yanda tayi tsammani hakan ce ta faru. Zaune ta samu mahaifin nata ya fuskanci gabas yana sallah a zaune. Don ciwon k’afar nasa bai barin sa yayi sallah a tsaye. Tun kusan shekaru biyar baya sallah dare ta zame masa tamkar jinin jikinsa. K’arfe uku kamar a kunnansa take bugawa saboda sabo da tashi. Bai kuma komawa bacci sai gari yayi tarwai tukun. Sarah d’aukar roban pentin da yake yin bowali tayi ta fitar dashi tare da zubar dashi a makewayi sannan ta dawo dashi ta ajiye sannan ta fita ta koma bayin ta kamo ruwa sannan ta fito ta d’auro alwala. Kamar zata wuce, sai kuma wani zuciyar ta jata ta nufi d’akin Lami. Tun daga bakin k’ofar take jin wani wawan munshari mara dad’in sauraro kamar an danne rago. Hannu ta d’an d’aura akan k’ofar ta tura, sai taji k’ofar a bud’e. Tura kai tayi ta shiga d’akin tare da lalubar bango ta kunna globe d’in dake d’akin. Lami ta hango tayi wani irin washarere a kan gadon kamar gawa, babu riga a jikinta daga ita sai d’aurin k’irji, shi kansa zanin yayi gefe, mamukanta kuwa d’aya ya kalli arewa, d’aya ya kalli kudu. Gata Ma sha Allah irin jibga-jibgan matan nan ne. Hatta bakinta a bud’e yake. Kau da kai Sarah tayi ta kalli d’ayan gefen da autarsu y’ar shekaru goma sha bakwai da watanni take. Ita ma dai bacci take yi cike da rashin tsari domin bacci ne irin wanda ba’a son musulmi ya rik’a yi wato ruf da ciki. Hannu Sarah ta kai ta d’aka mata duka cinyarta ta baya da yake a kwaye. Da sauri Aina’u ta kai hannu wajen ta Sosa ba tare da ta yanke baccin da take yi ba. Wani dukan Sarah ta kuma kai mata, wannan karan a furgice ta mik’e tana mitsitsitsike idanu tare da sakin wani irin hamma kamar d’iyar arna. Sai da ta ware rass sannan ta k’arewa Sarah kallo wutar balbalin bala’i na taruwa a kwayar idanunta. Don Aina’u irin fitsararrun yaran nan ne wad’anda duk girman mutum ko da kuwa jikinsa kaf furfurace bata raga masa. Y’an unguwanmu sun ce ita ce tayo sak halin Lami, wasu sun ce tafi Lami d’in ma. Tun tana k’ank’anuwarta makirar yarinya ce ta bugawa a jarida. Ga salo kamar wata uwar mata. “Uwar me zan maki cikin daren nan da zaki zo ki katse min bacci na!” Fad’in Aina’u kamar harcenta zai zazzago, don ta kasance irin matan nan masu harshe. Duk yanda tayi magana a hankali, ji za kayi kamar a kwar gida take magana. Da dare da rana basu da bambamci a wajenta. Yanzu haka da tayi magana kasancewar dare mai d’aukar sauti, har sai da mahaifinsu dake d’akinsa ya jiyo sautin muryanta. Hatta Lami mai bacci kamar gawa sai da ta farka a firgice tana sambatu. “Sallah nazo tashin ki kiyi. Don gashi can shirin tada sallar ake yi a masallaci. Ace duk k’arar speaker d’in masallacin can ba zai iya tada ku kuyi sallah ba!” Fad’in Sarah tana mai k’ok’arin juyawa ta bar d’akin duk da kuwa ta san cewa ba sallar za suyi ba. “Dan ubanki baza muyi sallar ba. Idan mun d’aga k’afa zamu shiga aljanna sai ki dawo damu baya saboda ta ubanki ce! Fita ki bar d’akin nan tsohuwar annamimiya!” Fad’in Lami tana mai nuna mata hanyar k’ofa. Komai Sarah bata ce ba, sai ma ficewa da tayi daga d’akin ta koma nata d’akin ta shimfida darduma ta tada salla. Tana nan zaune ko da ta idar da sallar har sai da gari ya waye tass, lokacin k’arfe bakwai sannan ta soma jin bacci a idanunta, amma kuma bata son yin baccin. Burinta ta shirya ta kuma fita domin yawon bin asibitoci ko za tayi dace da asibitin da scanning machine d’insu zai k’aryata cikin da wasu asibitocin da suke cewa tana dashi. Ta yunk’ura zata tashi daga kan sallayar taji muryoyin mata na tashi a tsakar gidan su. Gabanta ne ya buga da k’arfi sai tayi saurin d’aga labule kad’an ta lek’a waje. Da sauri ta saki labulen tana mai dafe k’irjinta da zuciyarta ke barazanar fasowa ta fito saboda arba da tayi da yayyin Farouq mata uku da kuma aunties d’insa guda biyu, gaba d’aya fuskokinsu a turbud’e…………..

_Ko mai zai faru a gaba?🤔_

 

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_

Leave a Reply

Back to top button