TUNATARWA

YADDA AKE KOYA WA YARA TSARKI,ALWALA,SALLAH

Sponsored Links
   

     
  YADDA AKE KOYA WA YARA         TSARKI,ALWALA,SALLAH 


                                                                         NA                                             
   

                  AISHATU MUNNUBIYYA Hassan
                                   (MRS , munnir )

 Hakkin Mallaka (m) Aishatul Mannubiyya

                     L.S.N 978-978086923

       AN FARA BUGAWA A: 2005 An sake bugawa da tsara sababbun hotuna a 2017.

               Tsarawa da bugawa a na’ura mai kwakwalwa.

           A.M Mai rubutu Books, No. 1743 Gwammaja  Housing Estate, Kano State Nig.

   Manarul Huda Islamiyya Publishing Department Fagge.

     Muhar Ventures Gwammaja kwanar gidan
                        Malam Aminu Kano.

                     ADIRESHIN MARUBUCIYA:

    Aishatu Mannubiyya Hassan (Mrs Munir)
          P.O. Box 11753 Kano State, Nigeria.
                      GSM: 08039268521
                          E-mail Address:
                  aishatul40@yahoo.com. 

      MALAMAN DA SUKA DUBA LITTAFIN SUN HADA :-

1 . Ma’aikatar bada ilimin baida daya ta jahar kano (SUBEB)
2 .Baffa amin (ministry of education kano )
3 M. Suwaidi hassan madabo
4 M. Umar sani fagge
5 M. Bashir Muhammad kyari
6 M. Fatima Muhammad kyari.

                   ABUBUWAN DAKE CIKI

                  FASALI NA FARKO  (TSARKI)

 1. Tsarki
 2. Ruwa mai Tsarki
 3. Tsarkin Kari
 4. Tsarkin Dauda
 5. Ladubban Tsarki
 6. Yadda ake yin Tsarki
 7. Wankan da ya wajaba ka sani
 8. Tambayoyi .

                      FASALI NA BIYU (ALWALA) 

 9. Alwala
10. Farillan Alwala
11. Sunnonin ALwala
12. Mustahabban Alwala
13. Masu Warware ta
14. Yadda ake yin Alwala
15. Tambayoyi.

                 FASALI NA UKU (TAIMAMA)

 16. Taimama
17. Farillan Taimama
18. Sunnonin Taimama
19. Mustahabban Taimama
20. Abubuwan da ba a yin Taimama da su
21. Tambayoyi.

                FASALI NA HUDU (SALLAH)

 22. Sallah
 23. Sharuddan Sallah
 24. Sunnonin Sallah
 25. Mustahabban Sallah 
 26. Masu Warwareta
 27. Yadda ake yin Sallah
 28. Kabli
 29. Ba’adi
 31. Tambayoyi

                       FASALI NA DAYA TSARKI

    Tsarki shi ne kawar da najasar da ta fito dan kofofi guda biyu. Kofar da ake yin ba (Fitsari) da kofar da ake yin gayadi da rihi. 

RABE RABEN TSARKI

Tsarki ya kasu kashi biyu:-
 1. Tsarkin Kari 2. Tsarkin Dauda
 
  Dukkannin su basa ingantuwa sai da ruwa mai tsarki mai tsarkake wa.

                 RUWA MAI TSARKI 
  Shi ne wanda launinsa bai sauya ba, ko dandanonsa ko kamshinsa. Kamar ruwan sama, ko ruwan rijiya, ko na korama, ko in ya cika sharuddan da aka ambata.

   Ruwan da yake zama mara tsarki shi wanda ya jirkita da jini, ko zabibi, ko ďanya mai, ko soyayye, ko romo, ko dauda, ko sabulu, famfo, ko kazanta da makamantansu.

                          TSARKIN KARI

  Shi ne tsarkin da ake yi saboda faruwar abubuwa guda biyar-
 1. Fitar fitsari
2. Yin gyadi
3. Fitar Maziyyi
4. Fitar Maniyyi
5. Fitar Wadiyyi

                                 FADAKARWA:-
 
    A cikin karrai da aka lissafo a sama akwai wadan da faruwarsu yeke wajabta wanka, wadannan sune

1. Fitar maniyyi ta hanyar jin dadi, yana wajabta wankan janaba.

2. Fitar jini na haila, yana wajabta yin wanka na haila yayin da jini ya dauke.

3. Fitar jini na haihuwa, yana wajabta yin wanka na biki yayin daya dauke.

                        TSARKIN DAUDA

 Shi ne tsarkakewa daga najasa ta daudar jiki ko tufafin da ake sanye da shi, kamar najasar da ta shafi fitsari ko gayadi ko jini da makamantansu.
  Ko najasar da take jikin mutum kamar jinin haila, ko biki Ko tsarkake najasar da ta shafi wajen da za yi ibada, kamar najasar fitsari, ko gayadi da makamantansu.

                     YADDA AKE YIN TSARKI

 Tsarki guda biyu ne, yadda mace take yin tsarki da yadda namiji yake yin tsraki.

                          TSARKIN NAMIJI

  Bayan ya gama yin fitsari, sai ya bari ya dige sannan ya yi wani abu da ake kira (Saltu) da ( Nataru).


  Saltu: Shi ne sanya “yan yatsu guda biyu na hannun hagu, babban dan yatsa da mabiyinsa, ana kiran wadannan yatsu Sabbaba da Ibhama, ana sanya wadannan yatsu guda biyu daga saman azzakari (kaciya) karshe zuwa farkon kan kaciya, yana mai tatso fitsarin da ya yi saura a cikin al’aurarsa, wannan tatsewa ita ake kira Saltu. 


  Yayin da yatsun suka zo kan kaciya sai ya karkade fitsarin da ya tatso, wannan karkadewar shi ake kira Nataru. Wannan shi ne cikakken tsarki na namiji, kuma wannan tsarki shi ake kira tsarkin (Istinja’) wato tsarkin ruwa, bayan wannan tsarkin, namiji yana iya yin tsarki da hoge, yayin da ya kasance babu ruwa a kusa, kuma ya matsu da yin fishari sai ya dauki tsarkakakken dutse, ma’ana wanda ha shi da wata katsanta ko ‘yan Kananan duwatsu, sai a goge kan kaciya da su.

     Bayan an gama tsarki an tatse, wannan tsarki shi ake kira Istijimari, sai dai malamai sun yi bayani kan cewa ana iya hada tsarkin biyu na ruwa dana hoge a lokaci guda, saboda samuwar Hadisin da aka saukar wa mutanan Kuba.

  Manzo Sallallahu alaihi wasallam ya çe “da mutanen Kuba yana mai tambayar su. “Hakika Allah ya yi yabo a gareku, ko da me kuka samu wannan falala?”
   Sai suka amsa, suna cewa, “Idan mun yi tsarkin ruwa muna karawa dana hoge”
         

   Bukkari da Muslim suko rowaitu.

                               FADAKARWA:

 Idan a lokaci guda ka yi fitsari da gayadi, ana so ka fara tsarkake wajen fitsari kafin ka tsarkake wajen gayadin, saboda samun ingantacciyar lafiya.

  Haka kuma ka sani bayan ka yi gayadi ana so ka yi dan kankanin nishi bada karfi ba, domin idan akwai saura sai ya fito, sannan ka yi tsarki sosai kana mai tabbatarwa babu wani alamu na santsi a tattare-tattaren fatar jikin “Dubura” wajen fitar kashi, saboda tsarkinka ya inganta Haka kuma wajen tatse azzakari, ana so k tatse a hankali ba da Karfi ba.

                         TSARKIN MACE

  Yayin da kika gama fitsari ana so ki bari ya dige tas, sai ki yi dan nishi kadan ba da karfi ba domin idan akwai saura a mararki sai ya zube, sannan ki rika kwaro ruwa da hannunki na dama kina yin tsarki da hannun hagu, har sai kin ji wajen ya fita tas, babu wani santsi ko kazanta.

 A nan a naso ki kiyaye, wani lokaci ko da kin yi haka akan samu fitsari ya make a mara, don haka ake so bayan kin gama fitsari da tsarki sai ki mike ki sake tsugunnawa ko ki yi dan tattaki a cikin bandakin wato ki yi ‘yar tafiya gaba sannan ki dawo ki sake tsugunnawa ki yi dan nishi fitsarin ya dige, sannan ki yi tsarki ki mike.

FADAKARWA: Ana so mace ta kiyaye a wajen yin tsarki, kada ta bari yatsanta ya nitse a kofar gabanta yayin gabatar da tsarki.

MALAMI/ MAI KOYARWA: Yana da kyau a fahimtar da mai koyo yadda zai tai nisishin wajen fitar da sauran fistarin da ke mara,yadda za tayi nishin a hankali ba da karfi ba dan kauce wa dukkan hadarin da zai iya shafar lafiyyarta .

                      LADUBBAN TSARKI

 A cikin ladubban tsarki sun hada da:-

1. Ka kasance ka shiga bandaki da farawa da sanya Kafar hagu tare da yin addu’a, ana cewa:- ” Bissimillah Allahumma inni a’uzubika minal khubusi wal khaba’isi.”
           ” بسم الله لهم إني أعوذ بك من الخيث والخبانث”
2. Ya yin da za ka fito ana so ka fara da sako kafarka ta dama tare da yin addu’a, kana cewa: 

  “Gufranak  Alhadulillazi  azhaba  anil  aza wa’afani”
       غفرانك، الحمدالله الذى اذهب عني ألاذى و عافانى

 3. Ba ya halatta ga wanda zai shiga bandaki ya shiga da abin da yake dauke da sunan Ubangiji Mai girma, kamar zobe ko sarka da makamantansu. 


4. Ka kasance ka suturce al’aurarka har dai ka kusanta da kasa.

5. Ba ya halatta ga wanda zai yi tsuguno (yin fitsari ko gyadi) ya fuskanci alkibla ko ya juya mata baya in ya kasance a fili zai yi tsugunon.

 6. Ba ya halatta ga wanda ya shiga bandaki ya rinka magana, har sai da muhimmin dalili kamar halakar rai ko dukiya ko kiran iyaye.

7. Ki kasance kin zuba ruwa a kafafuwanki bayan gama fitsari da tsarki, domin kawar da najasar da ta fallatsu a kafarki, domin tsira daga azabar Allah, kuma domin ibadarki ta inganta.

                                ΤΑΜΒAΥΟΥI

Menene bambancin tsarkin namiji da na mace?
2. Rubuta rabe-raben tsarki.
3. Rubuta uku daga cikin ladubban tsarki.
4. Rubuta abubuwa uku da suke bata ruwan alwala. 
5. Me ake nufi da Istinja’i da Istijimari?

  ANAN NE MUKA KAWO KARSHEN KASHI NA DAYA NA 
         WANNAN LITTAFIN SAI MU HADU A KASHI NA  BIYU .

          DAGA DALIBIN KU
MUSA S ZAGE  KANO MUNICIPAl

Leave a Reply

Back to top button