Cinikin Rai Book 2Hausa Novels

Cinikin Rai Book 2 Page 20

Sponsored Links

Volume:20
Zama Zeeno tayi, kanta ya daure bata san me zata yi ba. Yadda Hafsy ta ce zata gayawa Ammyn gara tazo. Kiranta tayi tana faɗin. “Don Allah Bestie ki kawo min zan sha, wallahi ba zan kuma ba”
“Shi kenan jibi zan zo kin sansu Ammy suna hanya wata sati?” “A’a bata fada min ba” “Ok xan zo mu gyara musu part dinsu.”
“Kina nufin a nan zasu zauna?” “A’a bai gaya miki baa gama musu gyaransu ba ne?” “Nifa ban san kome ba!” “Ina zaki sani wawuya kin mai da kanki baya, wallahi kika sake Malik ya samo wacce ta fiki hankali da sanin ya kamata kin rasa shi kenan.” “Ji ki da wani shirme!” Ta fada tana dariya, domin kuwa tasan bata son Malik baya ga dalilin da zai saka ta ji haushinsa ba don ya nime wata mace.
Haka suka gama wayar asannan ta kwanta, a nan barci yayi gaba da ita. Can wurin karfe ɗaya. Fitsari ya matseta, ta nufi banɗakinta. Tana fitowa ta ji sautin tv.
Kugi cikinta yayi alamar yunwa, a hankali ta nufi hanyar waje. Maidah da Malik ne a falon, wai suna kallo. Kawai sai ta dauke kai ta wuce kitchen abinta, ta haɗa tea domin shi ne abin da ko mutuwa tayi ya farka zata hada ta sha bata wahala ba. Ta haɗa da cake da ta gani a kitchen din, ta fito falo ta zauna tana me kallon tvn itama. Wani station ne suka saka 365 kuma da alamu ba a jima da farawa ba. Kallon Film din tayi ta tuna sun tab’a ganin shi da Hafsy. Kai hannunta yayi ta dauki remote din, kafin ta kashe received ɗin tare da wani irin haɗe rai ta ce mishi. “Ina ga a matsayinka, na uba wannan Film bai da ce da kai ba, balle a matsayinka na me rikon Yaran wasu.” Sai a lokacin abubuwan da yake mata suka shiga fado mata, wani irin rintsa idanu tayi tare da girgiza kanta da ƙarfi. Bata san lokacin da ta nime kwarewa ba, ta mike zubur mike tare da nufar dakinta. Tana shiga Malik yana biyo ta,
“Me kazo yi?”
“Ina son ki bani labarin Film din can?” “Kai ina ni yunwa nake ji!” “Fa sai kin bani labarin film ko kuma na kunna na gani a dakinki!” “Sai kayi kuma” ganin ba zata bashi hadin kai ba, ya nufeta da sauri. Garin ta gudu, ta kware a karo na biyu da tea din, zama tayi tana tari.
“Sannu!” Ya shiga shafa bayanta yana mata sannu. Ganin haka yasa ta jinjiga kai tana kokarin mikewa, ya kuwa shammaceta ya daurata akan cinyarta. “Ki kulani don Allah!” “Kai jinjiri ne da zan baka nono?” Sama yayi da rigar jikinta. Yana shafa kirjin. Buge hannunshi yayi yana faɗin.”ki bar ni na more sadakina!” “Ni dai bana so!” Hannunshi baki ɗaya ya daura a fuskarta yana faɗin. “Me nayi miki? Ko kina so na gayawa Ammyn ne kina bani wahala?” Ware idanu tayi, tana faɗin. “Idan ka gaya mata, mutuncina zubewa zayi”
Dariya ta bashi ya ce mata” tow gaya min ya zan yi?”
“Hmmm! Ka ga dai ni waɗannan abubuwan ciwo suke min, ranar da kayi min dakyar na saka riga. Haka ma na ranar ban iya daura towel ba a saman shi!” Bakin shi ya kai kunnenta yana faɗin. “Basu saba ba ne, idan suka saba ba zasu miki ciwo ba! Ki bari nayi.” Shiru tayi kafin ta rintsa idanunta.
Duk abin da suke Maidah tana jin kamar ta fasa ihu. Tana tsaye tana jin yadda Malik yake kome, idanunta sun yi jajjur. Komawa dakinta tayi ya kasa zama ta kasa tsaye. Har wurin asuba. Malik da yar kwailarshi kuwa, yau ma ba karamin hadin kai ta bada ba, domin shi kanshi ya sha mamakinta, abin da bai sani ba, jikinta ya fara sabawa da abin da yake mata, yadda dan tab’awa idan yayi take jin haka a ranta, har bata son ya daina tab’a ta. Sai dai a bangarenshi kan babu wani cigaba, abu ya tsaya cak kamar wanda aka haramta mishi kulawa da kome.
Kusan a jikinshi ta kwana, a karon farko a rayuwarta, duk da sauran kwanan da suke ba kamar wannan ba, an samu body contact, wanda ya kara effect ɗinsu ba su sani ba, ga Malik za a iya cewa ya sani amma ga Ita gimbiya sai a hankali.
— Washi gari babu wanda ya fito daga cikinsu, sai karfe daya na rana, domin sake yi suka yi bayan sallah asuba da suka. Ya kuma matseta, haka da wurin karfe sha daya sai da ya kuma hargitsa mata lissafi, sannan ya samu sauki wai shi a tunaninshi.kada shin sauke hakkinta.

Abun karyawa yana ajiye, har an gama na rana basu fito ba,.daki ta koma ta kira Lalla Salmah tana kuka. “Maama yarinyar nan makira ce, da zarar Dadi ya ganta bai da nutsuwa sai ta bar wurin.”
“Listen to me, abinda zaki lura anan Malik yana sonta ne sosai, don haka ki saurari abin da zan gaya miki da kyau!”

“Kina tsammanin haka zai tafi daidai Maama?” “In sha Allah!” Daga haka suka ajiye hiran. Lokacin da Malik da Zeeno suka fito wasai fuskarsu. Haka suka sha hira suna karyawa.
Wunin ranar Malik ya ki fita ko ina, yana zaune a gida, sai dai har ga Allah ya gagara Manta Elbashir, sai yanzu yake jin.babu dadi amma ya share kamar bai wani damu ba.
***
Demark
“Kuma kawu da ka zo nan, ka bar shi cikin makiya adalci ka mishi? Gaskiya kawu baka kyauta ba, nasan yallabai Malik baya Abu sai da hujja. Ka koma yana da dalilinsa!” “Bai da hujja! Yarinyar da yaƙe aure ta sanadin Malik ta manta da kome nata, ta sanadin Malik aka kashe iyayenta, me ya kama yayi? Sai ya dauke kome a kanshi y zauna da ita, amma ya taso ya kwaso Lalla Salmah jikinshi.”
“Duk da haka, ka kyale shi ka bi a hankali akwai dalilinshi nayi haka!”
“Taya zan bi a hankali? Yarinyar tausayi yake ba ni, yasan sarai idan ta fahimci wacece ita ba zata barshi ba yasa yake mata haka, ba zan iya ba.”
“Tow yanzu fushi kayi ko kuma barin Malik kayi?”
“Duk ɗaya nayi, na bar shi da fushin?” Kallon shi Adnan yayi baki sake, sannan ya ce mishi, “Kawu wani lokaci, na kan kasa gane kai da Malik waye me fahimta. Shima nan wani lokaci yayi fushi ya bar maka Keivroto yanzu kai ma ka bar mishi Keivroto. Sai kuyi ta yi tunda ku ba yara ba ne.”
“Kai ni sa’anka ne? Sai na sab’a maka, dismissed” ya nuna mishi hanyar waje. “Ka da ka manta yarinyar da kuka cillata cikin tashin hankali, saboda muradinku Allah ba zai bar ku ba” Yana gama fadar haka yayi gaba abin shi. Tsaki Elbashir yayi yana kanshi kamar zai cire.
***
Keivroto
Suna zaune a falo, Maidah ta rike kanta tana yar zabura kaɗan, “Lafiya kuwa?” Zeenobia ta tambaye ta, dake Malik yana dakin karatu, nazarin wasu ayyuka yake, bai san yadda suke ba. Mikewa tayi zata wuce dakinta, ta yanki jiki ta fadi tare da fasa ihu me mugun ƙarfi, tana faɗin”Wayyo Allah na, zasu nan zasu tafi da ni?” Tana ja da baya,kallon wurin tayi bata ga kowa ba, ta kai hannu zata rikota ai kuwa ta fasa ihun da sai da security guard suka shigo gidan, Malik babu shiri ya fito dakin karatun.
Aka rufa a kanta, ita kan Zeenobia bata tab’a ganin tashin hankali irin na yau ba, don haka tayi ta binsu da idanu. Kafin wani lokaci Maidah ta hargitsa gidan, dole aka wuce da ita dakinta, a can tayi ta faɗa Malik yana mata addu’ar da tazo bakin shi. Yau yake jin kewar Elbashir. Har asuba yarinyar nan ta hana Malik fita, karewa a wurin suka kwana, su uku. Da assussubar fari, Lalla Salmah ta dira a gidan.
Aljanun suna ganinta, suka fara magana. “Wayyo Allah! Gara da kika zo da wuri kafin a kassara mana godiyar mu, Keee fita kafin mu shanye jininki, alugunguma munafuka. Karuwa wacce ta zubda ciki babu iyaka, fita kafin mu tona asirin kika saka a binne kawarki zasu zo ta kawo miki maganin da zaki mallake Malik!” Shiru tayi ta fara gurnani. A hankali Malik ya riko hannun Zeenobia ya fitar da ita zuwa dakinta. Sai da ya shigar da ita sannan ya zuba mata idanu, zma tayi a bakin gado jikinta babu kwari. Sunkuyar da kai tayi, zagin da aka mata yake yawo a kanta. Wani irin d’ago kanta tayi, suka kalli juna idanu cikin idanu, da sauri ta rintsa idanunta, a hankali jini ya fara saukowa daga hancinta. Mikewa tayi yayi ya saurin fisgota ta faɗa, jikinshi wani azzababen rawa jikinta yake, idanunta ya rufe. “Relax! Ina tare da ke, ai ya gaya miki na yarda da ke, me yasa zaki razana? Idan ma duk kinyi haka ai don ni kika yi ko? Ina sonki. Show then you love me! Tell then how you love me! Kada kiyi faɗa a kaina, kaina Please ban yarda da ire -iren wadannan abubuwan ba. Ya Isa haka!”
Tura kanta tayi kirjinshi, tana kuka a hankali, har barci yayi gaba da ita. Kara rungumeta yayi suka koma gadon. Har g Allah a nan ya manta da Salmah da yarta. Basu farka ba, sai karfe goma na safe shima wayar Malik da yake ta kara ne a falon. Tana jikin a nade sai barci take. A hankali ya cire rigar jikinta, ya ɓalle botirin rigarshi yana jin fatarta a cikin nashi. Kara rungumeta yayi. Yana goga mata hancinsa a dokin wuyarta.
Zare jikinshi yayi ya shiga wanka, a dakinta. Sannan ya fito ya nufi dakinshi yayi Sallah sannan ya shirya ya kuma fitowa, a wurin cin abincin ya samu yar karamar wasikar Lalla Salmah.
*Malik ban ji dadin, abin da ya faru ba. Na mai da Maidah gida ta karasa jinyarta*
Ajiye wasikar yayi ya koma, dakin wurin Zeeno ta fito wanka tana saka hijab zata yi Sallah ya ce mata. “Maidah ta tafi!” “Allah ya bata lafiya!” Daga haka ta taddata kabbara. Tayi sallanta. Tana idarwa ta sauya kaya ya fito cin abincin. Suna cikin cikin abincin, sai ga Maidah kamar an korota.
“Dadi! Ban san me ya faru ba kawai na farka na ganni a gidan Maama don Allah ka ce kada ta kuma tafiya da ni.”
“Babu kome.” Ya nuna mata hanyar dakin. Wasa wasa, Maidah ta sako Zeenobia a gaba da iskancin da aljanun karya. Idan ta gama zaginta zata buge da barci. Idan kuma dare ne babu wanda ya isa rintsawa. Rashin barci ua haifawa Malik hawan jini domin ko kebewa yayi Zeeno zata fara ihu da hauka.

Duk Zeeno ta zama abin tausayi,domin idan ta fara haukar ita kanta Zeeno bata isa tayi barci ba, tayi.ta ihun a kira Zeeno. Wannan abin ya dami Malik don haka dole ya kira Sayyada Quddisiya ya gaya mata abin da yake faru. Ba tare da sanin Zeeno ba. Domin ya gayawa Maidah zasu tafi Demark. Amma bai gaya mata har da Zeeno ba. Ta kira Uwar ta gaya mata. Ita kuwa ta haɗawa yarinyar kayan gyaran jiki ta ce. “Na san halinsa ki bashi duk abin da ya bukata!”
“Tow!! Ana gobe zasu tafi ne, Hafsy ta zo. Tunda ta zo ta ga Zeeno zaune tana gyangyadi. “Ke ko mun samu Baby ne? Kin san gobe su Ammy zasu zo?”
Tashi tayi tana murmushi, duk ta lalace ta ce mata. “amma ba iya Saudiya suka tsaya ba?”
“Sun tafi Dubai hada kayan auren Abbas ne, meke damunki?” Gyara zama tayi ta fara bata labari, kallon Zeeno take kamar ta rufe ta da duka. “Amma ban tab’a ganin banza sakarya irinki ba. Kina zaune ana shirin rabaki da mijinki? Wannan sharrin makirci ne fa. Ba Aljanu ne suke damunta?”
Shiru tayi tana kallon Hafsy. “Ba zaki gane ba, sai ya tashi a gabanki.” Kamar jira take Zeeno ta fadi haka ta fara zuduma musu ihu, ke kuwa Hafsy da iskanci ta zafi wayar chaji ta nufi waje, tana kwance a kasa sai burgima take, Allah ya bawa Hafsy sa’a ta shiga zane ta, ai tuni ta qare ta fara ihun niman taimako. Ita kuwa Hafsy cewa take. “Yasarkumu zarkkukka, maza fita kafin na kona ka da ayar Allah!” “Wayyo Allah na, wallahi nice Maidah”
“Kece Anya kuwa?”
” Ba dai Maidah ba, Aljana Julka ce bari na cire ta don ubanta me rantamemen kai!” Sai da ta mata likis, sannan suka kyaleta. Murmushi Zeeno tayi ya ce. “Sayyada Hafsah ga Aljanu dai sun fita ya zamu yi kenan?” “Idan kina da barkono ko garin barkonon dauko a jika mata yayi wanka sauran a nimo abin turaren wuta a mata hayaki muje kafin ta farka a barci!”
Suna fita Maidah ta tattara ta gudu, bata yarda ta tsaya ba, balle yan iskan yara su kasheta.
Lokacin da ta isa gidan, ta samu Shatima da Lalla Salmah. Mikewa Uwar tayi tana tambayarta. “Waye ya miki haka?” “Wadancan Yaran! Wallahi duka suka min” ta fada cikin kuka. “Kin yarda yarinyar she meant to Malik? Duk yadda zaa raba su, ba za a yi nasara ba. Har saka nayi a rufe min shi, kada yayi kome da ita amma kin ga aikin bai yi tasiri ba, don haka dole yau na fatauci Malik har lahira! Su kashe shi su dauko min ita.”
“Ina ganin haka duk ba yi bane, amma dole muyi kashe muraba da dukiyar shi!”
“Duk inda yake a cikin gidan na basu aikin farautar shi, a kashe shi a yanko min kanshi. Khuldu Jahid Khan shima ua bukaci na kashe Malik, shu’iba ma haka har kuɗi suka saka min sun bani kafin alkalami. Ni kuma nace su hada Malik da yarinyar su kashe domin ko sun kawo min ita ba zata yi min amfani ba.”
“Ina Elbashir ya tafi!” “Ya rabu da Malik tuntuni!”
“Kai wannan abin ya min dadi! Zamu iya Daurawa Elbashir ɗin”
“Wannan shi ne shirina!”
Sun jima suna saka yadda zasu kashe Malik, kafin suka ajiye maganar daren yau. Zasu kashe Malik.
***
A bangaren Zeeno kuwa, aikin abincin suka yi da Hafsy. Har yamma , dake zata kwana a gidan ne, Malik ya ce a’a ta je gida. Su Ammyn ma ba yau zasu dawo wata sai wata sati suna can Demark.
Aikuwa Zeeno taji haushi bana wasa ba domin taso su kwana da Hafsy su tashi akan aikinsu.
Wani irin abu take ji, kamar an tsoma ta a cikin ruwan sanyi haka yasa baki daya , bata da kuzarinta. Ga uban faduwar gaba. A can waje kuwa Malik ya sallame kowa yana ce musu cin dare zai yi tafiya don haka su koma gida zai nime su.
Wannan shirin ba iya Shatima yayi ba, shi kanshi yayi shirin akansu, shi yasa ya janyo Lalla Salmah jikinshi………
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata:

 

Leave a Reply

Back to top button