Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 21

Sponsored Links

Chapter 21

Yaso dakatar da Ahmad amma gani yayi koya dakatar dashima kaman aikin banzane shi bayama tsammanin ze saurare shi yakuma fahince sa,dan haka miƙewa yayi ya nufi ɗakin Ammi taddata yayi tayi wankanta tayi shirin kwaciya sai baxa kamshi take kallo ɗaya tamasa ta ɗauke kanta.

Gani yayi bazata kulashi ba inde bashine ya fara yi ba,takowa yayi a hankula tsaɓanin yanda ya faɗo ɗakin zama yayi bakin gado ya riƙo mata hannu cikin ƙasa da murya yace”yi hakuri Ammin yara ɗazun rainane a ɓace yanzu ina ruwan wanka dan sulhu yake nema da ita,banza tayi masa,riƙe kunnensa yayi ya duka da gwiwansa kasa yamarairaice fuska yace pleasa wify yanda yayi kaman karamin yaro yasata sauke ajiyar zuciya tamiƙa hannunta ta kamo nasa tace”shikenan nayi hakuri ammafa badan wai na huce bane kawai zanyine saboda banason yaranmu su fahinci akwai wani abu narashin jituwa tsakanin mu,kuma dan Allah idan ranka yaɓaci kariƙa ƙoƙarin ganin kasarrafa fushinka karka kasake mun irin haka a gaban yara dan su yara iyayensu sune madubinsu banson munayin irin haka suke gani suma su ɗauka.

Aisha dake zaune tana ma nusaiba yankan kayan ankon bikin yayanta,kallon ta nusaiba tayi tace”kefa kinji da dadinki Aisha
“Da akai mefa?
“Ba ruwanki da komai gashi kin mai da hankalinki wajen aikinki gaskiya rayuwarki tana burgeni saboda kin riƙe talaucinki kwata kwata abun duniya be rufe miki ido ba.

Murmushi ɗauke saman fuskata na kalle ta nace”ai kema haka rayuwarki take ba ruwanki da shiga tsabga da bata shafeki ba,ƴar dariya tayi tana girgiza min kai tace”kai Aisha baki da dama kekan,nima dariyar nayi nace”sai hagu ko,dariyar muka sakeyi baki ɗayan mu.

Can ta kalleni tace”Aisha nikan mutuniyarki kinga yanda ta koma kuwa?
“Wace kenan?
Damamaki ta kalleni tace”fadila mana ko kina da wata mutuniyarce bayan ita,ɗan ajiyar zuciya na sauke zuciyata namun zafi dan tunawa da nayi da rashin mutunci da atamun nace”ayyar nusaiba aikinsan yanayin aikin mu daga ni har ita,lokacin da nake gida ita tana wajen aiki ko ita tana gida ni kuma ina wajen aiki balle kuma ita aikin ta da ba weekend.

“Hakane kuma fa Aisha amma kuwa kinga wani irin mahaukacin mota da take hawa kuwa,hmm ina faɗa miki aisha wannan rushesshen tsohon ginin gidan nasu ai yau bakiga yanda aka rushesu ya dawo sabo ba,wallahi aisha kuɗi yayi a rayuwa muma Allah yabamu”mai albarka zakice nace da ita”amin aisha wannan haka hake mai albarka”amma aisha ke bakya zarginta da shiga ko irin ƙungiyarnan ta matsafa?

Ɗagowa nayi ina kallonta sannan na maida hankalina ga abunda nake nace”yaka mata murinƙa kyautata zato ga ƴan uwamu zato haramun ne koda yazama gaskiya,katseni tayi amma Aisha nima katseta nayi ina cewa”kinga nusaiba kinsan yanda muke da fadila nafi kowa sanin abunda zata iya da wanda bazata iya ba,sannan na fiki sannin inda take aiki dakuma irin aikin da sukeyi ba abun mamaki bane idan tace miki tana samun dubu ɗari kullum”to ke aisha ke mai yasa bazata miki hanyan inda take aikin ba,
“Nusauba kenan ai ni ɗinki da kika gani inayi shine burina soyayyata da ɗinki daga jinina yake kuma ina alfahari da kasancewata tellah wata ran kina zaune saide ki ganni ana haskoni a tv ko kiganni a jarida an hasko da hotona wacce tayi fice a duniya ƴar africa talle ta mace dariya tasaka tace Allah yasa nace amin daga nan mukaci gaba da hira amma ƙasan zuciyata ina tunanin maganan nusaiba da tayi na ƙungiya da fadila take.

Fadila ta kalli alh shehu da rinan nun idanunta tace”amma alhajina kana cikin hayyacinka kuwa?
Kasan abunda kake cewa kuwa?
Aisha fa Aisha kace kanaso kasan alaƙata da ita kuma kasan kuma nariga da na sadaukar da jininta wa ƙungiya shin baka….”kinga fadila wannan ba abun ɗaga hankali bane ai tun randa kuka zo ta gaidani naji duk duniya ba wacce nakeso tamun sama da ita,kuma zancen sadaukar da jininta da kike wannan abu mai sauƙine kawai ki shirya fansar da ita da wanda yafi kusanci da ke, zaro idonta tayi waje kaman zasu faɗo kasa tsaban firgita da ruɗani da tashiga dakyar cikin rawan murya ta buɗe baki tace….wallahi ko ƙasa da sama zasu haɗu bazan taɓa bari kasami aisha ba…kuma jinin ta ai nariga da na sadaukar tunda nasaka mata wannan zoben kuma kullum sai nasha kufi ɗaya duk dare kaman yanda shugaba ya bukaceni nayi wani irin zabura yayi ya damƙo wuyarta ya shaƙeta…

 

Leave a Reply

Back to top button