Cinikin Rai Book 2Hausa Novels

Cinikin Rai Book 2 Page 33

Sponsored Links

33- Yasan Shatima zai ta fatan ya kashe shi, zai yi fatan ya mutu ya huta shi kuma ba zai kashe shi ba, ba zai mishi kome ba, zai bar shi a raye domin fuskar ukubar rayuwa, zai kare rayuwarshi yana gudun da bai da karshe, Lalla Salmah ba zai kuma bin ta kanta, domin bai da lokaci na kulata.
Haka yasa shi zama strong da facing rayuwarshi da Zainaba. Baya wurin a zaune amma baki daya rayuwarshi yana tare da ita, bai san haka yake son lafiyarta ba sai da wannan abin ya faru kara jin lallai yana son ta haifi cikin jikinta lafiya lau. Don haka zai ta jiransu, har zuwa lokacin haihuwar abin cikin.
***
Wasa-wasa barci ya zama shine abinda yafi fa’ida a rayuwar Zeeno kodan cikin jikinta,da ake son rabata da shi few weeks.
Amma ana bukatar kafin ayi aikin ta farka, ta samu walwala yadda za a cire Babyn da koshin lafiya. Haka suke fata domin Zulfah har ta kira dangin Babansu ta gaya musu halin da ake ciki kuma Alhamdulillahi ya gaya mata ana kan shirin tarbansu, haka suna yawan kiranta su ji halin da Zeeno tace ciki. Haka ɓangaren dangin Mamansu na Maiduguri kuwa, ana saka ran za aturo kanwar Mamansu, daga can don har ana sa ran zata taso nan da sati daya ne.
Ba ciki daya suke ba, ƴaƴan mata ne, duk da Jalilah tana kokari. Amma suna bukatar wacce zata zauna da ita. Dake tana barci Malik yana yawan kiransu ya ji halin da take ciki, bayan nan babu wani abun da yake kuma kira yaji, amma ana kashe kudi, domin ko inda suke zaune dai an kashe kwantar da wani mara lafiya, ita ɗaya ce a ward din sannan an zuba jami’an tsaro, kamar ana faɗin shugaban ƙasa.

***
Sai da ya kwashe kwana biyar yana gudu, koda yake yana cikin Keivroto. Duk abin da yake tafiya duk yana sane, amma bai da ikon fita yayi yawo.
Katin bankin shi ma, wani ya bawa ya ciro mishi kudi me shegen yawa, yana huci ya ce. ” A ina kasan zaka samu min mahaya masu kashe mutum domin kudi?” Kallonshi yayi sannan ya ce masa.
“Kayi kokarin barin garin nan, zuwa wani wurin ba zaka rasa ba. Amma nan zai yi wuya ka samu domin suna yiwa Malik biyayya babu me maka wannan aikin!”
“Taya zan tafi bayan ina son ganin bayan Malik? Gaya min ina zan shiga bayan Malik ya mamaye min dukiya ta!”
“Kayi nisan kiwo, yadda babu me gane ka, ai ja da baya ga raggo ba faduwa ba ne, sabon shirin tunkarar makiya ne. Nasan zaka yi nisa kuma zaka dawo domin fansarka!”

D’ago kai yayi yana kallon mutumin kafin ya ce . “Zan tafi kuma zan dawo, amma dawowar ba zai zama me alkhairi ba, zan dawo na kashe kowa domin na rantse sai na saka kowa a cikin halin ni y’asu ” sannan ya kwashi abin da zai iya amfani da shi na kudin, sauran ya barwa mutumin yana tafiya yana surutun zai dawo, sai ya ga bayan Malik da yasa shi rayuwa a titi kamar ƙare, ko ta yarshi baya ji, don ma Malik yasa an sake yarinyar an mai da ita wurin familyns Uwarta, tare da kanwar Mamanta, domin ba yason ya gayawa Yarinyar abun da Ubanta yake aikatawa, ko wanda yayi mutuwar mahaifiyarta, baya ganin baya cikin tsarinshi ya lalata dangantaka tsakaninsu domin cimma manufar shi, shi ba ya tunanin haka, asalima da ya saka aka sake ta, kiranta yayi ya mata fada, da ta nutsu ban da rashin ji da rashin da’a. Yana son kafin wani lokaci ta fitar da miji ya mata aure ya gaji da ganinta, bata iya cewa kome ba, sai ya ƙara mata nasiha sannan ta ce mishi. “Wai da gaske Abbana ya cutar da kai?”
“Wannan tsakaninmu ne, idan har kika shiga tow kin yi shishigi” ya fada cikin rarrashinta. Bayan sun gana wayar ya ajiye, yana nazarin yadda zai bullowa matarshi domin bai san yadda zai yi da ita ba.
***
Lalla Salmah.
Bata taɓa zaton Malik zai iya zakulo abin da take boyewa ba, asalima gani take kamar ita ɗaya ta san sirrinta babu wanda ya isa ya san sirrinta. “Ku kira min Malik.” Ta faɗa da mugun ƙarfi, tana zare idanu domin inda aka kawo ta, bata tsammanin sun san Allah. “Nace ku kira min Malik!” Babu wanda ya kulata, ganin zata tara musu jama’a. Aka office din MD na hukumar kare hakkin dan Adam, “Sir Lalla Salmah ta ce a kira mata Malik” shiru yayi kafin ya ce. “Ok” kiran Elbashir yayi.
“Yallabai Elbashir, Lalla Salmah tana son magana da Malik!”
“Zan zo amma ba zata samu ganin shi ba, ku kyale ta.”
“Tow Yallabai!”
Ya lashe wayar yana kallon mutumin, “Malik ba zai zo ba, amma P.A dinshi zai zo, ka kyaleta abin da ta aikata shi take girba.”
Sai bayan one hour, ya iso office din. Ya sa aka fidda ta, ya zuba mata idanu yana kallon yadda tayi buzu buzu.
“Sati Daya kawai kika yi, kamar wacce ta shekara a daure?”
“Ka saka wancan dan iska ya sake ni!”
“Wa kike magana?” Ya tambaye ta a izgilance. “Wancan coward” murmushi yayi ya ce mata. “Ke kuma me zan kira ki? Monster Mother? Ni ina da ja akan Maidah anya ke kika haifeta? Ni ban san kome ba amma Malik yasan kome, ina saboda Sheikh ya musanta Maidah ba yarshi ba ce, kika rabu da shi kada ya gano yar shi ta asali!” Ba zata maganarshi ya zo mata, kamar ta fashe da kuka. “Kin san inda Shu’iba yake gaya mana!”
Dariya tayi sannan ta ce mishi. “Ba zan faɗa ba, ba zan gaya muku ba.”
“Kyale ta Bashir, an gaya min inda yake, ba sai ta faɗa ba.”
“Malik ka saka a sake ni?”
“Ki gaya min ina iyayen Maidah suke? Waɗanda kika raba su da yarsu?”
“Ban sani ba, ba zan tab’a gaya maka ba. Koda zaka kashe ni kana raya ni ba zan faɗa ba.”
“Ok! Kin ce kina son gani na?” Cikin takaici ta ce . “Ba zan amsa ba, sai kazo ba karenka zaka turo min ba!”. “Ok Bashir dismiss!” “Ok Malik!” Daga haka ya mike ya zuba mata idanu. “Idan ban da zuciyar Muslunci, da zuba miki harbi zan yi har sai kin mutu, amma na kyale ki. Kowani mutun yana farincikin rayuwarshi da aurenshi ni kin min sanadin da narasa wannan farin cikin. Shaidaniyar banza.”
Ya fice daga dakin, cikin d’aga murya ta ce mishi. “Baka tambaye ni yadda aka yi na samu, yarinyar zaka aura ba? Baka tambaye ni yadda aka yi na ja ra’ayinta ba? Shin baka son kasan yadda yar matsiyata ta sayar da yardanta da Amintarta? Idan har ina da hanyar da zan shiga jikin na kusa daku, gaya min ai kashe ku baa abu me wuya bane, saboda kowannenku nasan inda karfinshi yake, sannan bana jin zan iya kyale Malik ya saka idanu, tabbas sai ya amshi hukuncin da ya dace.”
“Ki godewa Allah, Malik ya hana ni aikata kome, da na miki abin da zaki bukaci gara ki bukaci mutuwa da rayuwa!”

Murmushi tayi ta ce mishi. “Ba zan kula dan kwaikwayo ba, zan kula zaki ne idan ya shirya zama dani!” “Baki yi wannan isar ba, baki kai wannan me isar ba, zaki kare rayuwarki a nan babu me cetonki!” Daga haka ya ficce daga cikin office ɗin, tana ganin ya fita ta fasa ihu, tana maganganun banza kamar mahaukaciya.

A hankali ta bude idanu tana kara
, har ta bude baki daya. Zulfah da Ammyn ta gani suna magana kasa-kasa, dafe goshinta tayi, tana faɗin. “Wash Allah na?”
“Zainab kin tashi ne?” Gyada kai tayi, fita Ammyn tayi ta kira nurse, ya duba ta. Sannan ta cire mata karin ruwan.
“Ko zaki cire mata, roban fitsari ne?”
“Ok” daukar hand glove tayi, ta cire mata, atana mata sannu,, ana cire mata ta ce. “Zan yi bayan gida!” “Tow muje!” Ta wuce da ita ban daki, sai da ta gama ta kuma tara mata ruwa tayi wanka, tana faɗin. “jikina ciwo!” “Sannu kinji!” Gyada kai tayi, Ammyn tana kallon yadda kafaffunta suka kumbura, tausayi ta bata baki daya ta fita ta hayacinta. Kamar ba ita ba, suna fitowa sallah ta gabatar sannan ta koma ta kwanta tana hutawa don ta gama gajiya, abincin Zulfah ta zuba mata, ta tashe ta. Tana ci tana mata hira. Har suka gangaro kan hiran iyayensu, kuka Zeeno ta fara tana faɗin. “Na zata idan yana kasuwancin shi da cinikayyar rayuwar mutane, ba zai tab’a saka iyayenmu a cikinsu ba, na tattara rayuwata na danka mishi ashe shi nashi rayuwar, ashe ba haka ba ne shi nashi rayuwar kawai ya kashe ya hana kowa magana.”
“Kin ga yanzu baki da lafiya, ko don abin cikinki, ki hakura ki samu lafiya sai mu san me zamu yi za a turo Aunty Yagana daga Nigeria tazo ta kula dake, amma nace musu subarta akwai Mommy Jalilah, ita zata kula dake, shi yasa basu zo ba, ana miki aikin sai mu tafi can ko!”
“Ba zan jira sai anyi min aiki ba, kawai ku mai dani wurin danginmu”
“Zainab kina da matsala, ki bari a fara ji da lafiyarki sai a san yadda za ayi kinji”
“Wallahi ba zan zauna a garin da Malik yake ba, kawai ki fita ki gaya musu a sallame ni!”
“Zeenobia ki yi hakuri mana, kafin a miki aikin!”
“Wallahi ba zan zauna a garin nan ba, kawai ku mai dani, wurin danginmu.” Yadda ta tire da bala’in rigima yasa suka nimo Malik akan lokaci, tunda ya shigo ta zuba mishi idanu, kafin ta janye nata daga gare shi. “ka sallame ni,”
“Ba zan iya sallamarki ba, ki nemi wata alfarman banda ita.”
“Ka sake ni domin ba zama zan yi da kai ba, rayuwata da abin.cikin jikina yana da muhimmanci a rayuwata da shi, bayan nan ban sanka ba, ban san waye kai ba. Na had’aka da Allah ka kyale mu daga ni har shi ba zamu kara waiwayarka ba don Allah!”
“Don Allah, kada ki min iyaka da abinda nake fadi tashi domin na rayu. Nasan illar kadaici, idan idan kika raba ni da shi zan shiga tasku!”
“Na maka adalci ne, na bukaci ka nisanta kanka da mu, idan kuma kana son a rasa mu gabakidaya zan hakura da nawa rayuwar mu tafi inda zamu huta, shawara ya rage gare ka ”
“Yanzu Zainab hukuncin da zaki yanke min kenan, na rabani da ke?”
“Shi yafi dacewa da zamanmu, a duk lokacin da na tuna kai ka kashe min iyayena. Zan ji kamar na kashe ka, amma idan na fahimci girman rabon da yaƙe tsakaninmu ya wuce na aikata abin da zai saka ni, kuka da abin cikina. Don Allah ka sahale min!”
Takawa yayi ya rungumeta, fashewa tayi da kuka, tana sonshi yanzu tun daga lokacin da Hafsy ta mata gorin taji ta shirya ta bashi kome, sai dai sakamon kashe mata iyaye da ta gani ba zata yafe mishi ba.
“Ba zan yafe maka ba. Ba zan tab’a yafe maka ba, koda zai rage daga ni sai kai a duniya ba zan yafe maka ba, na Barka da Allah na Barka da wanda ya halicce mu, rabuwa da kai ba wai bana sonka bane amma dole nayi nisa da kai, dole na nisance ka, da fatan zaka sahale min”
“Don’t let your heart led you to the mistake, ki fahimce ni na gaya miki gaskiya!”
Wani irin ihu da kuka ta saka tana rike cikinta. “Me kake nufi? Kana nufin zaka min dadin baki ne? Kana nufin zaka rufe gaksiya ce? Wato da kasan kai ka kashe min su, shi ne kazo ka yaudare ni, ka sani aurenka babu dalili? Me ysa ka min haka? Me yasa?” Ta fada tana kuka, a hankali ya ja kujeran gabanta yanzu yana kallonta.
“Kiyi hakuri! Wata rana zaki ji abin da ya faru, promise me, idan kika tafi ba zaki yi kukan bana tare dake, ki min alkawarin ba zaki yi kuka idan wani abu ya faru da ni ba, ki min alkawarin zaki bawa dan mu kulawa har girmanshi! Zainab ina sonki, ina kaunarki. Zan zauna jiranki da jiran kiranki. Kira daya kika min zan zo gare ki! Da kira daya kawai!”
Daga haka ya mike zai fita ta ce mishi.
“Don soyayyarka da Annabin Allah ka sahale min!…..
*Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata:

 

 

Leave a Reply

Back to top button