Cinikin Rai Book 2Hausa Novels

Cinikin Rai Book 2 Page 6

Sponsored Links

Volume:6 Choose Me or Him

Buga table din Shatima yayi yana faɗin. “How dare you, zaka ce na biyaka? An ci kuɗinka Malik anci kuɗinka kuma we shud see waye zai Malik Zeeno!”
Baya Malik yayi da kujeranshi ya ce mishi.
“Ba wani abu kuɗina! Zaka bani sai ka daina min haushe kamar jaki!” “Don’t insult me! Malik kada ka zage ni domin na fika mutunci a idanun duniya!”
“Waye kai?” Malik ya tambaye shi, “Nace waye kai? Kai waye?” Ya kuma tambayar shi a sanyayye. Amma daga yadda fuskarshi take murtuke zai tabbatar maka da cewa ranshi a b’ace yake. “Ni kake tambaya? Ni Khamis Shatima, mutumin da kowa yasan ban ketare iyaka ba? Bana bin mata bana bin maza. Ni ba makashi bane irinka,. Ni ba kazami ba ne me hada halak da haram! Kai wani ne da xaka yi alfahari?” Toothpick Malik ya dauka ya shiga sakace haƙoranshi. “Mtseeeeeew! Na zata wani Mashahuri gawurtaccen namiji ne, ashe kwailata ta fika cikar nasaba. Oya pay my money ka ɗauke ta ku tafi.”

“Kai Malik!” Ya shure ture keken guragu Malik ɗin da zai zauna. Garin rike keke ya fado akan kujeran, “wai meye haka ne?” Zeenobia ta tambaye shi, a hasale. “Me kike tambaya na? Ki rabu da shi kizo muje!” Ya fada yana shure kenan. Sake tare shi tayi tana faɗin. “Wai lafiyarka Boy?” “Lafiya ta lau, wannan kazamin mutumin nake so ya fita a rayuwarki! Macuci azzalumi!”
Shigowar Elbashir ya sami Malik zaune a kasa. “Subhanalillahi! Malik!” “Dauki Baby girl ku bar gidan nan!” “Ka da ka kuskura ka tab’a ta, domin idan na gama da nakasashrn nan zan dawo kanka!”
Janyo keken Zeeno tayi, cikin takaici ta ce mishi. “fadar da kake ba shi zai baka abin da kake bukata ba, don Allah ka kyale ni, ka je na gode!” Fisgota yayi yana faɗin.
“Billahi azim, babu dan iskan da ya isa aurenki.”
“Ka tafi da ita Bashir!” “Malik me kake nufi da Zeenobia? Ke dawo nan! Ko zab’a ko ni ko shi?” Baki daya bata taɓa cin karo da irin wannan masifar ba, hawaye cike a Idanunta ta ce mishi. “Ba da abun da zaka biya min kuɗinshi, da na salwantar. Sannan babu wata hanyar da tafi na zauna a karkashin ikon shi na zabe shi.”

“Keee! Zeenobia kin san waye shi?”
“Bashir ka tafi da ita!” Domin Malik ya fahimci, baki daya kunyanta shi Shatima yake shirin yi, jan hannun Zeenobia yayi tana kallon Malik da yake zaune a kasa yana kallonsu damuwa da tashin hankalin da ya hango a fuskarta ya sashi sake mata murmushin yana gyada kai. Ya kai mishi Mangari, sai dai kuma kafin hannunshi ya isa ga Malik yayi nasarar cika mishi toothpick din a tafin hannunshi, tare da murde hannun sai da ya durkusa, kuwa cikin fushi ya sakar mishi wani irin duka a gadon Baya, sai da ya sume.
Sannan ya ture shi, tare da jan kekenshi shi, ya koma kai ya zauna, cikin izza.

“Bindin Malik don Allah kada wani abu ya faru da shi, ka ga ya ture shi a ƙasa.”
“Malik zai ji da kome!”
“Ba zai iya ba, kana ganin shi ba kafa ba”
“Ranar da kika gudu a asibiti taya kika tafi asibitin? Kin kai Kanki ne?”
Girgiza kai tayi, tana faɗin. “Amma kuma.”
“Trust me, babu abinda zai faru.” Yadda yayi mata maganar sigar lallashi yasa ta gyada kai, yau ta ga lukutar masifa.
“Yanzu zabi yana hannunki, rayuwar al’umma charity House da kuma Maza biyu, idan kika bi ra’ayinki, rayuwar al’umma yana danger. Idan kuma kika zabi al’umma baki da case domin ko tsinke naki Malik ba zai barshi ya samu matsala ba.”

Baki daya ta shiga damuwa, haka suka isa gida wurin karfe uku na yamma, ta wuce cikin gidan, sai murna suke. Kai tsaye ta wuce ɗakinta bata iyawa kowa magana ba, haka suka yi ta binta da idanu.
“Allah ka ga zuciyata, bana son tsoho. Amma baki daya bawan Allah nan ya min bazata.” Ta fada tana jin kamar ta fasa ihu, kuma pride irin nata, ba zai saka tayi kuka ba, sai ta zauna a dakin shiru. Ammy da Abbas suka shigo Dakin, zama suka yi kusa da ita. “Me yasa kika koma haka? Malik ya miki wani abu ba ne?” Hawaye ne ya zubo mata,a hankali ta fashe da kukan da ta rasa waye zata gayawa tarkon da Malik ya d’ana mata.
“M
Ammy na shiga uku!” A rude Ammyn ta d’agota. “Me ya same ki? Malik ya miki wani abu ne?” Kai tayi tana faɗin. “Bai min kome ba.”taki gaya mata domin tasan matukar ta gaya mata gaskiya Ammy zata ce a bada gidan tunda suna da enough money da zasu iya sayan wani dan zama iya su!

“Kawai yace yana sona ne, ni kuma bana sonshi, amma ban san ya zan gaya mishi bana sonshi ba, domin yayi min tsofa!” Murmushi Ammyn tayi tana faɗin. “Ba shi kenan ba, Y’ata tayi goshi amma kin san da haka me yasa kika kwana a gidanshi anya Yar kunamar da na sani ne?” Wacce babu ruwanta da maza? Kada ki kuma kwana gidan wani namiji, duk da ba akan sonki da yake yi kike kuka ba, nasan sai dai akan wani abu na daban, idan har aka ne, tow ki daina kuka, Allah yana sane dake. Sannan idan wani abu ne ko gaya min In sha Allah ba zai gagara ba!” Tausayinsu ya kara cika mata zuciya. “Zimmmmm!” Taji wani irin kara, duba pepar bag din da Elbashir ya bata ta leka, waya ce sabuwa dal, wani kwali pink colour, a hankali ta ja kamshin turaren Shumukh ya daki hancinta.

A hankali ta shiga warware igiyar da aka rufe kwalin ta bude shi d’aga murfin tayi, tare da shaƙar kamshin shumukh, take dakin ta ya game da kamshin, “ikon Allah ji wani turare me shegen kamshi!” Kamar an cillota ta fado dakin. “Kai kutumalesi! Baby wannan kayan haka?” Karamin Alqur’ani ne pieces, izu goma goma. Sai jalbabba da counter. Su kenan kayan a cikin kwalin,domin kuwa kyauta ce ta musamman.

A hankali take kallon kayan, saka hannu tayi a jakan ta ciwo set na kayan kwalliya, sake baki yayi tana me zubawa a gaban Ammy da Hafsy. “Wani egen kika samo mana?” Juyar da kai tai tana faɗin. “Mayor Malik Menk Jordan!”
“Ahirrrrrrrrrrrrr;” ta rangad’a guda, “Don Allah nice me Miki kwalliyar biki!” Tab’e baki tayi, domin da sun san abin da ta faru ba zasu shiga farinciki haka ba, a bangaren hawaye ne yake zuba, ita tayi biyu babu. Babu ba saurayi matashi dan shekaru ashirin da takwas zuwa talatin ta kare a tsoho me furfura..bata san lokacin da ta fashe da kuka ba. Duk suka zuba.mata idanu domin ga abin dariya ga abin tausayi. Haka ya ci kukanta idan ta tuna cewa bayan tsofar baya tafiya akan kafarshi sai taji hankalinta ya kuma tashi, haka tayi ta kuka tana jin kamar wani abu ne yake yawo a ranta, suma gajiya suka yi da rarrashinta suka zuba mata idanu, duk abin da ya saka Zeeno kuka ai kasan ba karamin al’amari ba ne, amma yarinyar nan tayi ta kuka. Zuciyarta da shaidan suna kara ingizata. *Tsoho da furfura, nakasashr mara tafiya. Dan luwaɗi. Zai aure ki domin covering issues dinsa da siyasar shi.*
Yadda take kuka zaka rantse da Allah mutuwa aka mata, amma ina tsabar tashin hankali da damuwa. Kiranta yayi tayi har sai da ta gaji ta dauka. “Me kake so na maka? Ba ka ce zaka aure Ni ba, me kake so kuma?”
“Calm down! Idan kin huce an jima za a zai daukarki zamu fita shan iska!”
“Babu inda zani!” Ta fada tana kwalla.
“Karfe takwas da rabi bana buƙatar African time, ina bawa lokaci muhimmanci!”
“Malik don Allah ka kyale ni!”
“Taya zan kyale ki? Mrs Mayor! Gaya min taya zan kyale ki? Idan ba so kike duniya ta dauka barazana na miki ba!”
“Mene ne banbancin? Barazana na nawa kuma? Al’umma charity House yana karkashinka,sai yadda kayi da shi.”
“Yes na yarda da haka, amma kuma rashin zuwarki zai saka a fara yayyata gulmar da zai fito nan da wasu hours!”
“Malik!”
“8:30pm ina jiranki, rabona da fita yawo na manta so a ci gayu sosai!”
Kasa magana tayi wato Malik ya gama cin uwar rena mata hankali, cikin shashekar kuka ta ce mishi. “Babu inda zani!” Dariya yayi ya ce mata. “Ok Abbas ga Zeenobia!”
“Yan mata!” “Abbas ka tawo ka bar wurinshi.” “A’a gashi ya samu Baban Hibba an ba ni auren hibba!”
“Mua Baby ina jiranki, kada ki sake raina ya b’aci koda yake raina ba zai barci ba, zan zo na gaida Ammynku!”
Zabura tayi tana faɗin. “Malik me yasa kake min haka ne? Me yasa ka shiga rayuwata ka hana ni sakat?”
“Ina da naci a duk abin da na saka kaina. That’s all!”
Kwalla ne ya kara tuttulowa daga idanunta. “Allah yana ganinka, sai ya saka min!” “Daga taimako sai a nime yi min Allah ya isa da tattabatsinin!”
“Kai ka sani!”
“Tabbas ni daya na zan san yar kwailata!”
“Ni ba yar iska bace!” Dariya yayi yana faɗin. “Zan so ganin yadda kike kuka, sai kin fi haka kyau!” Yadda yaƙe zolayarta zaka ɗauka babu kome a ranshi, sai dai kuma haduwa da Zeenobia ya taimaka mishi wurin sauya shi sosai. Domin a da can ma bai da yawan sakewa. Balle yanzu da abubuwa suka canza, sai dai shi mutum ne me wanda ya san sirrin rayuwa da iya amfani da mutum domin cimma manufar shi a sassaukake.

Kashe wayar tayi baki ɗaya.

Shatima bar farka ba, sai wurin karfe biyar na yamma. Dafe kirjinshi yayi da yake shirin fashewa. Ya juya tare da kallon gefenshi Malik ne zaune yana karanta jarida. Ya kara kallon shi sosai tabbas murde shi yayi ya zuba mishi dundu a gadon Baya. Yunkurin tashi yayi kirjinshi ya amsa.
“Tsinanne kashe ni kaso yi? Kuma daga yau xan cire hannun jarina a kamfanoninka”
“Eh tow ina taya ka,murna kasan dai babu na biyu na a saka hannu jari a kasar nan. Karewa Ni nake da kaso mafi girma a kamfanin KJK!” Dafe kirji Shatima yayi tar da tashi zaune kamar zai hantsilo daga gadon. “Idan naso na karya kowa ina da wannan Powerful! Ina da karfin tsiya da zan rushe mutum daga sama, na san kome na kuma san halin kowa. Idan na ce zan mai da ka abokin gabana wallahi mafaka ba zaka samu a kasar nan ba, balle kuma a garin nan babu shegen da ya isa baka mafaka. Ban damu ba don ka cire hannun jarinka sam baka bani tsoro ba, sai dai ka sani Ni Abdul Malik bana cikin mutane masu tsoro da shakkar karyawa.

A duk lokacin da haka yazo min ina daukar shi, matsayin darasin rayuwa. Ka zata ban san shirinka da ka turo min auren Nadrah ba ne? Ni mutum ne da kafin ka iso min da bukatarka na san dalilin haka, da na amince na amshi auren Nadrah da yau an raba kome nawa an kwace ko? Hmmm kayi tunani da 6 dinka mana. Allah ba zai nakasani ya kuma hana ni hikima ba, domin da Abdul Hakim ana saka min da wallahi baka isa ba, Ni Abdul Malik ne shi yasa nake mulkarku ko kuna so ko baku so, ni sarki ne a garin nan. Bakin ciki,hassada, Kyashi, a jikinku yake duk yadda wani yafi ku sai kun adawa ce shi. Sai kun nuna mishi shi ba kowa bane, shi bare ne, bai san kan rayuwa ba. Na gaya maka da sassaukake murya ka nisanci Zainab idan kuma na kuma ganinka .” Lumshe idanunshi yayi ya bude shi tar sannan ya ce mishi. “Zan yake maka azzakarinka idan kana ganin karya ne bismillah ga fili ga me doki.”

Daga haka ya juya kekenshi shi, sai kuma ya ce mishi. ” Baka san me yasa Zainab ta ji haushinka ba? Ture ni da kayi sannan, ka kuma ture keken. Ni kuma naki kula ka, shi jarumi a gaban macen da yake son burgewa lusari ne, yana tadda jarunta shi ne a bayan Idanunta. ” Ya kai yatsar shi kanshi. “Ina lissafi da shekaru na, ni ba matashi bane, amma zan iya hawa skill matashi, ina abu na ne da lissafi da ace ka iya tow ba makawa ka gama da ita, kasan me naga bakinka yana rawa ka kiyaye abin da zai fito.”

Daga haka ya tura kekenshi shi, yana faɗin. “zaka iya amfani da kowacce hanya amma kan Yarinyar da na Zabe a daren da wata yake cikar shi, sai na manta da halaccin da ka min na kararaya kasussuwanka, sannan ta manta da girman abotar mu a tsakanin mu!”
Kafin ya saka kai ya fita, rintsa idanunshi yayi tare xa kiran Faruq, yaronshi ne ko nace drive ɗinshi. Shigowa yayi ya ce mishi. “Gani sir!”
“Ina wayata!” “Gashi nan!” “Murmusawa yayi ya ce mishi.” Ka tabbatar ka kira Zeenobia ka gaya mata, Malik ya min dukar mutuwa, ina kwance ban san inda kaina yake ba!”
“Ok sir!”
“Maza kirata!”
Ai kuwa ya shiga kiranta wayar bata shiga ba, “Yallabai wayar bata shiga ba!”
“Kira min Jalilah!” Kiranta yayi yana shiga ya mika mishi. “Jalilah! Kina ina Malik ya samu wata yarinya zai aura! Ke ya lalata miki rayuwa yaki aurenki, tow ki sani ni n janye auren da zan bashi na Y’ata ki san yadda zaki yi Yarinyar ta bijire mishi.”

Kashe wayar yayi bai bata damar magana ba, ya kira Lalla Salmah..
“Uwar wayo, tow Malik ya samu wata yarinya danya sharab, kuma ya ce ba zai auri yaran mu ba, sai ita yarinyar damar ku ce ni dai na hakura domin akan al’amarin ya dake ni,dakyar nake miki maganar nan!”
“Kana ina yanzu?”
“Ina asibiti ba lafiya an daure min bayana zuwa kirjina;”
“Innalillahi wacce shegiyar ya samu haka?”
“Wata yar jagaliya ce, akan Yarinyar zai iya kashe kowa.”
“Al’amarin yayi ƙamari ne haka?”
“Ya wuce yadda kike tunani! Lalla Salmah, idan na mutu ki rike min Nadrah kin san bata da uwa!” Don makirci ya kama tari, kamar tanshi zai fita, ya kashe wayar baki daya, yasan hankalinsu zai tashi.
Komawa yayi ya kwanta, yana sake wahalallen murmushi. Ko yanzu kasuwa ta watse dan koli ya ci riba, zai ga yadda Malik zai auri Zeenobia. Dariya ce ta kwace mishi, tabbas ya daku a hannun Malik, ya haɗa shi da matan nan, sannan ya koma gefe ya hada shi da Ita kanta uwar gayyar, Zai ga yadda zai escape daga sharrinsa dole Zeenobia ta zabe shi ta bar wani banza can. Sannan kafin nan zai san yadda zayi a sauke Malik a Mayor da karfin tsiya domin….
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/10, 9:17 PM] Yan Mata:

Leave a Reply

Back to top button