Furar Danko Book 2 Page 53
‘…..!!
5️⃣3️⃣
…….“Banda abinka Sulaiman Garko idan kaji makaho yace ai wasan jifa ai ya taka dutse ne. Toni a wannan gaɓar dutsina na taka bama dutse ɗaya ba. Sorry fa, inata son zuwa na maka jajen abubuwan dake ta faruwa amma nayi busy da yawa. Sai kuma naji yau ma wata yarinya ta ɓaro muku babban aiki, dan kaima banace bakayi ba. Wanda zai iya yima ƙanwarsa uwa ɗaya uba ɗaya fyaɗe ai abune mai sauƙi yayma sauran ƴaƴan jama’a ciki harda wanda ya haifa ma…..”
“Da hannunka kenan a ciki? Dama an tabbatar min da yarinyar ƙawar ƴarka ce ai. Isma’il karka manta ni zaki ne. Nakanyi farauta a duk dajin da yay min na kuma ci kowacce irin dabba na zauna lafiya batare da ko jin ɗar ba tattare da ni….”
“Banda Giwa, dan koda ka kadata namanta bai ciyuwa gareka sai da taron dangi Sulaiman Garko. Tabbas Nadiya ƙawar Mawaddat ce bakayi ƙarya ba, idan kuma kace zaka nuna wani giggiwa a wannan kadamin karan bana ne zai yi maganin zomon bana. Dan ka tabbatar da Mawaddat ce ta haifi Mawaddat, kasan kuwa tunanin zai iya zama duk iri ɗaya, hakama jarumtar. Ballema a yanzu da take a jingine a jikin matashin *_ZAKI_* na haƙiƙa ba arar suna ba irin ka. Gefenta ga *_DAMISA_* ƙi sabo. Sannan ga addu’ata biye gareta a dukkan motsinta. Ai nasha faɗa maka ni da ƴata da zuri’arta gaba ɗaya *_FURAR DANƘO_* muke, *_A SHEKARA ANA DAMU BAMU FARAU-FARAU_*. Idan kai acan ka wuni, ni kwana nayi. Maza ka sake shiri *_MAZAN_* ƙwarai da *_MACE_* mai kamar maza ne tafe bisa kanka ƙaramin biri……”
“Isma’illll!!!!!!”
Alh Sulaiman ya kira sunan Daddy cikin wata irin Mummunar tsawa mai razani. Kafin Daddy ya ce komai ya ɗora da faɗin, “Amma dai kasan zan iya karar da duk jama’ar asalin ƙauyen da ka fito bama kai kawai ba ko??!!!”.
Dariya Daddy ya ƙyalƙyale da shi tare da faɗin, “Ai ga fili ga mai doki nan Sulaiman Garko, zaka iya gwadawa idan har zaka iya, dan wlhy ba jama’ar garin jiƙamshi ba, koda ƙasar jiƙamshi ka taka da manufa saina karya ƙafafunka ta yanda bazasu ƙara ɗaukar gangar jikinka ba har gaban abada. Amma kafin ka tafi jiƙamshin ƙarar dadu ka tabbatar ka fara duba saƙo ga shi nan zai zo a hannun matarka shashasha ƙaramin biri abin wasan yara a tsakkiyar kasuwa”. Ya yanke wayarsa.
Haukacewa ne kawai Alh. Sulaiman baiyi ba da kalaman Daddy masu ƙona zuciya. A wani irin birkice ya ɗaga wayar ya naka a ƙasan tiles. Dai-dai nan amaryarsa ta shigo hannunta ɗauke da leda. A ɗan tsorace da ganin yanayin nashi ta ajiye ledar tana faɗin, “Saƙone aka kawo a baka, yanzu maigadi ya kaw….”
Yanda ya juyi a fusace ya hanata ƙarasawa. Har ya juya shima da nufin baida lokacinta sai kuma ya juyo tare da wani irin fisgar ledar. Zazzageta ya shigayi cikin tsumar jiki. Babu komai a ciki face Flash drive. Cikin rawar jiki data ruhi ya kai zaune daɓar yana mai janyo laptop ɗinsa ya saka flash ɗin jiki. Gaba ɗaya ya manta da kasancewar matarsa a wajen yay playing video ɗin da ke cikin Flash ɗin. Ba komai bane face fuskar mahaifiyar Lulu tana kuka da faɗin wannan shine kundin manyan laifuka na shi a ciki. Tana roƙon ko bayan babu ranta iyayensu su sani shine yayma Sultana fyaɗe….”
Ai bai ma kai ƙarshen video ɗin ba ya buga wata irin kuwwa da hankaɗa Laptop ɗin ƙasa itama ta kifu. Amaryasa data gama jin komai cikin firgita ta buga ihu itama tana neman hanyar fita a guje. Cikin tashin hankali yay tsalle ɗaya ya taɗota ta zube ƙasa. Idanunsa a rufe ya kai mata wata irin wariyar shaƙa. Tuni idanunta suka juye ta fara ƙaƙarin mutuwa.
“Mi kika ji?!! Na ce, “Mikika ji!!? Dan uban uwarki”.
Kanta take jujjuyawa alamar bataji komai ba. Wawan mari ya ɗauke fuskarta da shi ta bayan hannu da sake maƙureta. “Idan ma kinji ko kin gani wlhy wlhy wlhy ki zama kurma. Idan ba haka ba da hannuna zan kashe ki, na gina rami a tsakkiyar falon nan na bizneki. Kuma har abada babu mai sake jin labarinki ko tambayata ina kike. Baƙar mayya mai leƙe-leƙen masifaa!!”. Ya ƙare maganar da yarfar da ita ƙasa. Ya wuce bedroom ɗinsa a birkice. Babu jimawa sai gashi ya fito. Har lokacin tana kwance a wajen yabi takanta ya fice abinsa. Umarni ya bama maigadi akan kada wanda ya fita a gidan. Daga haka ya birka motarsa da kansa yau ya fice a bala’in guje….
*_★UK★_*
Cikin tashin hankali Lulu ke kallon Smart. Dan duk abinda ke faruwa tsakanin Alh. Sulaiman da matarsa akan idonsu ne kasancewar sun saka direct camara a jikin Alh. Sulaiman batare daya taɓa farga ba. Sun yi wannan aikinne kuma a lokacin da ya tafi jiyya bayan jami’an tsaro sun sake sa akan kidnapping ɗin Lulu da yayi. Sun haɗa baki da likitansa aka saka masa camara a gefen kunne ta wajen wuyansa a zuwan wani tabon theatre da akai masa ne a wajen wai na’urar na rike jijiyar kunnensa. Wannan aikin Uncle Yousuf ne, sun zaɓi saka masan ta yanda bazasu gansa ba sai dai suga abinda yake aikatawa saboda yanayi na yau da kullum irin na ɗan adam. Wanka da makamantan hakan. A kuma duk lokacin da zai shiga ɗaki da matansa ko aikata wata Masha’arsa da karuwansa sukan tsaida gani daga wajensu domin kiyaye dokar ALLAH. Ta wannan direct camara suke sanin duk wani motsin Alh. Sukaima batare da shi ya farga da hakan ba dan yana kallon abinda aka saka masan ne a yanda aka faɗa masa cewar tana riƙe jijiyar kunnesa da ta samu matsala.
“Wannan mahaukacin fa zai iya kashe matar nan. Ya kamata muyi wani abu”. Lulu ta faɗa cikin tashin hankali itama ganin yanda Kawun nata ya fita a hayyacinsa. Murmushi kawai Smart yayi yana ɗan lumshe idanu da zamewa ya kwanta. Kamar bazaice komai ba sai kuma zuwa can ya firzar da iska yana bata amsa da, “Babu abinda zai maita, wannan hargagin da kikaga yanayi na rashin mafitane kawai da ruɗanin da yake a ciki. Amma ba itace a gabansa ba yanzu Daddy ne da ke sai kuma mu da yake son sanin su wanene. Ina mai tabbatar miki yanzu haka gidan Daddy zai je”.
Da sauri Lulu ta ce, “What! Gidanmu fa kenan?” sai kuma ta fisgo computer ɗin gabanta ta sake buɗewa batare da jiran amsar Smart ɗin ba. Ilai kuwa sai ga Alh. Sulaiman na kwaɗa gudu a saman titi. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi a anguwarsu, a ma ƙofar gidansu. Sai dai ya gagara ƙarasawa saboda jami’an tsaro da ke zagaye da street ɗin ma gaba ɗaya musamman jikin gate ɗin gidan nasu. Wani irin duka ya kaima steering ɗin kamar zai fasa ihu. A haukace yay reverse ya koma ganin jami’an tsaron sun yo kansa…. Bata ma san lokacin data kwashe da dariyar data saka Smart buɗe idanu yana kallonta ba…
___________________★
Abubuwa tako ina suna cigaba da kwaɓema Alhaji Sulaiman Garko. Domin kuwa da zaman meeting na maganin matsala da yayi musu. Dan kullum a cikin yinsa suke. Kowace hanya sunbi domin ganin sun cutar da Daddy ko zuri’arsa al’amarin ya gagara. Yanda Daddyn ke zagaye da jami’an tsaro lamari ba’a cewa komai. Sun kai hari gidan su Smart shima dai, sai dai anyi rashin sa’ar samun gidan a baje sai masu aikin gini. Iya bincike kuma kowa a anguwar sai yace bai san inda suke ba a yanzun. Fahimtar kamar raina masa wayo sukeyi ya sakashi komawa gida rai a ɓace neman mafita. Kowa bai nema ba a matansa ya nufi sashensa kamar zai tashi sama. Wani irin kallon ɓacin rai yabi falon da shi, ganin yanda ya barsa a harmutsensa haka ya dawo ya tadda abinsa. Abinka da mai zuciya a kusa, tuni ransa ya sake ɓaci. A dai-dai nan Hajiya Turai ke shigowa sashen nasa. Ganin ko’ina a harmutse ga shi yanata faman huci ya sata zuba masa ido. Sai kuma cikin dauriya ta ce, “Alhaji lafiya kuwa kake miya sameka haka?”.
“A’a a cikin turnuƙun yaƙi nake? Ke ban san iskanci fa da rainin wayo”.
“Ikon ALLAH, ALLAH ya baka haƙuri da ga tambaya”.
Bai sake tanka mata ba, itama saita fara ƙoƙarin tattara falon. Taɓa Laptop ɗin sa da tayi ya sashi tunawa da Flash ɗin dake jiki. Cikin tsawa ya ce, “K bani ita nan!”. Bata musa ba ta miƙa masa zuciyarta na sake shiga mamakinsa. A fisge ya amsa. Sai dai me babu Flash ɗin a jiki. “Ina Flash ɗin jiki yake?”.
“Flash kuma? Ni banga wani Flash ba, a gabanka fa na ɗaga ta”. Wani irin kallon zan kashe ki na binne anan ya shiga binta da shi. Hannu ya miƙa mata alamar bani. Sai duk ta sake dabircewa. “Wai Alhaji kana lafiya kuwa. Wlhy ban ɗaukar maka wani Flash ba. A gabanka fa na ɗaga Lap-top ɗin nan ba wani waje naje da ita ba balle kace.”
Babu zato babu tsammani taji saukar mari har biyu. Kafin ta gama dawowa a hayyacinta ya sake miƙa mata hannu da tsananin tsawa yace, “Turai!! Bani”.
“Wlhy tallahi Alhaji ban ɗaukar maka komai ba. Wai yau ka fara zama dani ne? Koka taɓa ajiye abinka ka nema ka rasa da har zaka ɗaga hannu ka maran!”.
“An mareki ko zaki rama ne?”.
“Bazan rama ba, amma zan barka da ALLAH”. Ta faɗa tana ficewa fuuu. Mutumin naku tuni zuciyarsa neman fitowa take ta baki, amaryarsa da ya bari a falon nasa ta kuma ji komai ce tazo masa a rai. A harzuƙe ya nufi sashenta, babu ko sallama ya banka ƙofar ya shiga. Baiko kalli ƙanwarta dake gaishesa a falo ba ya wuce bedroom ɗinta kamar zai tashi sama.
“Wlhy aunty ba ƙazafi bane ba naga komai fa da idona, kuma na faɗa miki ƙanwar nan tasu data rasuce ma fa a video ɗin, ɗayar kuma ƙanwar tasu ce ta ɗauka mahaifiyar yarinyar nan da ake cema Lulu….”
Waɗan nan kalamai da suka nema fasa zuciyar Alh. Sulaiman ne ke fitowa da ga bakin amaryarsa. Abinda kuma yaji na tabbatar masa taga komai da komai kuma ta faɗa ma wadda suke wayar. Ta buɗe baki zata sake magana idonta ya sauka a kansa. Zabura tayi, kafin ya iso gareta ta kwasa da gudu ta shige toilet ta banko ƙofar. Yana dannawa tana dannowa har dai ALLAH ya bata sa’a ta murza key. Wasu manya-manyan ashariya ya fara mulmula mata yana jijjiga ƙofar tamkar zai cireta. Itako duk da a tsorace take faɗi take, “Wlhy ko zaka kasheni bazan bada ba”.
Ashariya ya cigaba da ingiza mata da tabbatar mata wlhy sai ya kasheta…….✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
Zafafa
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*