Furar Danko Book 2 Page 60
‘…..!!
6️⃣0️⃣
……..Sai da suka tabbatar ya gama jigata da bullet ɗin da ke jikinsa sannan suka cire masa. Washe gari suka bisa da duka na hauka wanda ya kaisa harda karaya a ƙafa, suma kam yayita babu adadi suna farfaɗo da shi. Duk wanda yaga yanda ake wajiga rayuwar Sulaiman zai tabbatar da al’amarin da biyu ne. Inda ma aka ɓoyesa kawai tashin hankali ne. Dan da ƙyar Daddy da Lulu ta matsawa da son ganin Alh. Sulaiman ɗin sukaje aka barsu suka ganshi, ya samu wannan alfarmar ne kawai saboda taimakon da ya bama jami’an tsaro wajen cafke su Alh. Sulaiman ɗin. Daƙyar Alh. Sulaiman ya iya ɗaga ido ya kalla Daddy da Lulu data juye masa tamkar mahaifiyarta, saboda duka ya taɓa masa ido ɗaya. “Miya kawoka wajena?!”.
Ya faɗa da ƙyar muryarsa na karkarwa. Iska Daddy ya firzar yana mai ƙoƙarin maida hawayen da suka cika masa ido. Dan ganin yanda akaima Sulaiman ɗin raga-raga a kwana biyu kacal ya ɗaga masa hankali. Da ƙyar ya iya danne rawar lips ɗinsa ya furta, “Nazo ne na tabbatar maka wasan ya ƙare Sulaiman. Dama irin wannan ranar nake guje maka a baya amma ka kasa raurarena da fahimtata sam. Ka ɗauki tsawon shekaru kana tsula tsiyarka amma ka duba cikin abinda bai wuce awanni arba’in da shida ba ka koma tamkar bakai ba. Wannan fa kamun mutane ƴan uwanka kenan. Inaga kamun UBANGIJI kuma Sulaiman. Duk wahalar da kasha rani da damuna da sanyi, wahalar yawon ƙasashe domin tara dukiya kawai kallo a inda ka kasance yanzu. Talakan da bai taɓa riƙe dubu hamsin ba ya fika. Babu abinda yafi neman halak komai ƙanƙantarta sauƙi a wannan rayuwar. Koba komai zaka rayu cikin kwanciyar hankali ka kuma mutu cikin mutuntawar UBANGIJI. Mutane su ɗauki gawarka da girmamawa, a taya iyalinka kuka da jajantawa a tausaya musu. Amma ta irin hanyar da kuke bi fa? Zaka kasance cikin ALLAH wadai wa zuri’ar ka da al’ummar gari, kabar iyalinka da hantara wanda ma bai kai ya takasu ba ya taka su. Maimakon addu’a ga mutane sai ALLAH wadarai ke fita a bakunansu. Duk inda mutum ya buɗe a yanar gizo ciki da wajen Nigeria zancenku ne. Miye amfanin ɗaukakar ALLAH ya tsine irin wannan. Kasaka iyayenka a wani hali da iyalanka. Iyayenka mutanen kirki ne Sulaiman musamman mahaifinka, mutumne mai daraja da kima a wajen mutane, a duk inda ka zagaya alkairinsa ke fita daga bakunan mutane. Amma yau gashi kasa al’umma na ambatar sunanka a matsayin jininsa. Albasa batai halin ruwa ba Sulaiman……”
Kuka ya sarƙe Daddy mai cin zuciya. A mamakinsu sai ga Sulaiman na hawaye shima. “Maganganunka dukansu gaskiya ne Isma’il. Tabbas mun kasance masu son zuciya a rayuwarmu. Burin tara dukiya duk da wasunmu mun tashi a gidan dukiyar. Burin zama wasu abu a duniya batare da muna tuna muna mutuwa ba. Da’ace na saurareka tun a wancan lokacin Isma’il da ba’a kai wannan gaɓar ba. Yau gani a matsayin wanda ya rasa komai. Babu iyayen da suka sha wahalar haihuwata da bani tarbiyya da ilimi. Babu matan dana ɓata lokaci wajen neman dukiyar dan na birge su, babu ƴaƴan da nake zumuɗin tarawa domin a kirasu ƴaƴan wane. Babu ƙarfin da nake kai duk wanda ya bijiremin ƙasa. Babu ƙarfin da nake tunanin wataran zan iya sarrafa ƙasar dama wasu ƙasashe a hannuna. Komai ya ƙare Isma’il, komai ya kufce a gaɓar da nake gab da cimma nasara mara amfani. Komai ya tafi kamar bai taɓa zuwa ba…..” kuka ya sarƙe sa.
“Dan ma bakaji irin tsinuwar da uwarka ke maka bane ba! Da nadamar haihuwarka”. Lulu ta faɗa kanta tsaye babu alamar tausayinsa ko ɗigo a ranta. Dan itafa in dai ka kasance kayi fyaɗe to babu abinda zaisa taji tausayinka dan ta ganka a wani hali. Cikin tashin hankali Alh. Sulaiman ya ɗago yana kallonta. Ta wani ƙyaɓe baki da cigaba da faɗin, “Ai yanzu bakaga komai ba ma. Dan an gama wasanne saura yaƙin. Shi kuma yaƙin yanzunne aka fara shaiɗani. Wai kaine kake kuka nadama a cikin kwana biyu kacal. Ƙaryane ma na yarda da hakan makiri. Idan ma tunaninka Daddy na zai taimakeka ka fito ne ka cire hakan a ranka dan ka shiga kenan, kabarinka ma anan zasu gina maka shi su bizneka babu wanka babu sallar gawa. Wannan da kake gani yafi ƙarfinka kamar yanda ya faɗa maka tun farko, bama shi ba, mu dake ƙasa da shi munfi ƙarfinka dan gashi a ƙanƙanin lokaci mun sabauta rayuwarka tamkar ma ba’a taɓa yinka ba balle iyawarka. Nasan dai bazaka manta da wannan fuskarba ai”. Ta faɗa tana juya masa wayarta. Smart ne ya bayyana AA zaune a saman cinyarsa. Fuskarsa ɗauke da murmushi ya ɗaga ma Alh. Sulaiman hannu da faɗin, “Hy ƙwaro”. Sai kuma ya saki ƴar dariya yana ɗage gira sama ganin yanda Alh. Sulaiman ɗin ya saki baki da hanci yana kallonsa. Nunasa ya shigayi wasu irin zafafan hawaye na rige-rigen sakko masa. Lips ɗinsa na rawa sai dai ya gagara cewa komai.
“Kwantar da hankalinka ai basai kace komai ba zan ƙarasa maka. *_Aliyu Mika’il Idris Mawashi_* ne dai naka. Yaron nan daka tura aiki jiƙamshi family. Idan baka manta ba na faɗa maka kada ka ƙulla wasa dani zan iya kaika ƙasa. Amma sai ka gagara ganewa saboda kana kallona yaro ƙarami ɗan talakawa da zaka iya hurewa tamkar silin gashin kanka a lokacin da kaso. Kayi kuskure Sulaiman dan ba’a raina maƙiyi koda na jinjirin sauro ne. Kamar yanda na faɗa maka ni kurari baya razanani hakanne, sai ma ƙaimi da yake ƙaramin. Da’ace baka kalleni a ba komai ba maybe da kaci nasarar tsallakewa da ga tarkona. Sai dai kash girman kanka da ɗaukar kanka sama da kowa yasa kai sake ɗan zaki ya girma yay gawurtar da ya wuce da saninka. Ka sani ni bani da wata matsala da kai dan babu abinda ya taɓa haɗamu kafin saninka. Kawai na ƙarasa aikin family na na biyu ne. Wato aikin surukina da surukata da kuma matata, dan duk wanda ya taɓasu kowaye shi bazan taɓa ƙyalesa ba saboda sunansu AHALINA suma a yanzu. Ni kuma ba’a taɓamin AHALI a zauna lafiya, sai nayi kaca-kaca da rayuwar mutum ta inda bai zata ko tsammani ba. Kamar dai yanda a yanzu muka shafe tarihinka da babinka. Ka sanar musu su cire maka camara ɗin dake gefen kunnenka dan aikina ya ƙare, bana buƙatar cigaba da ganin yanda kake cin ubanka a hannunsu bye bye Solomon”.
Dariya Solomon daya kirashi ya bama Lulu. Ta shiga ƙyalƙyalawa kuwa. Dai-dai nan jami’in ya shigo yake sanar musu lokaci ya cika. Ko’a jikin Lulu ta miƙe tana ɗagama Sulaiman yatsu biyu. Sai kawai ya bita da kallo wasu irin hawaye masu zafi na silalo masa. Dan babu abinda yake gani a tattare da ita sai mahaifiyarta. Gaba ɗaya ta juye ta koma masa Mawaddat ƙanwarsa. Duk da dama tana kama da ita mai tsananin gaske. Jiki a saɓule shima Daddy ya tashi ya fito.
Koda suka tafi a mota kasa cema Lulu komai yay sai da sukaje gida yace ta biyosa falonsa……
Wannan zuwa na Daddy ya tsayama Sulaiman a rai matuƙa. Zuciyarsa bata nema bugawa ba sai da aka cire camara ɗin da Smart yace a gefen kunnensa. Wani irin raɗaɗi yake ji a ransa da mamakin ta ya akai camara a jikinsa bai sani ba, har tsawon wane lokaci yaran nan suka ɗauka suna wasa da hankalinsa batare da ya taɓa farga ba. Sai yanzu ya gane Smart ne *_AMM_* da ya dinga turo masa saƙwanni. Tabbas yaron yayi gaskiya, ya ɗaukesa a bakomai ba, amma gashi ya zame masa komai. Ya kaisa ƙasa a lokacin da bai zato ko tsammani ba, ashe abinda suke zargin wani babban mai faɗa aji ke musu shine ke aikata musu shi. Yaron da basu taɓa kawowa a hasashen su ba. Shi baima taɓa kallonsa a jerin maƙiyan da zasu iya juya rayuwarsa haka ba. Ranar yaci kuka mai suna kuka da har sai da ya rasa hawaye. A rana ta uku aka ɗaukesa da ga Kano gaba ɗaya zuwa Lagos. A rayuwarsa bai taɓa sanin akwai azabar rayuwa irin wannan ba a duniya. Duk da yasan shi mugune, sun kuma kashe mutane da dama a dalilin harkar ƙwayar da sukeyi idan suka bijire musu. Amma wannan ɗin na musamman ne. Duk taurin zuciya da taurin kai irin na Alh. Sulaiman a wannan gaɓar sai gashi yana hawaye, shi kansa yasan anzo dai-dai wajen kuma. A randa aka isa da shi Lagos wahalar da yaci bai ma san ya fara kiran sunan Dada da Baba Garko ba akan suzo su taimakesa ya tuba, har Hajiya Turai da Tajuddeen da sauran ƴaƴansu sai da suka sha kira. Wannan itace nadama mara amfani, domin kuwa bakin uwa shine ke tasiri akansa tare da haƙƙokin mutane dana ƴaƴansu da suka zama sanadin lalatama rayuwa ta hanyoyi da yawa, gashi nan a kwanaki uku kacal rayuwarsa ta sauya a yanda ko maƙiyinsa ya gansa dolene ya tausaya masa, dan a yau ma sai da suka sake masa karaya biyu a hannu ɗaya. Bai san sanda azaba ta sakashi fara lissafo abokan huɗɗarsa ba. Wanda dama tunda aka kamashi hankulansu a tashe suke matuƙa suma, sau faman kai gwauro da mari sukeyi akan al’amarin shiyyasa ma aka ɓoye Alh. Sulaiman ɗin ashe……….✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
Zafafa
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*