Hausa NovelsInda Rai Hausa Novel

Inda rai 10-11

Sponsored Links

*INDA RAI*….🥰🥰

*By*

*MARYAM ABDULLAHI*

(💔💋Oum Shaheed💔💋)

*MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION*

10 -11

Sudais ya so ya tambayi Daddysu wa ye a jikin pic ɗinnan amma ya kasa, jira kawai ya ke lokacin da likita ta ɗiba musu ya ci ka.

Tun ƙarfe biyar Daddy ya ke damun Sudais akansu ta fi office ɗin su ƙarisa jiran ta a can, da ƙyar da ban baki ya shawo kansa akan su bari har lokacin da ta basu ya ci ka kafun suje, Sudais ya ɗaura da faɗin “Daddy wallahi na ji na tsani wannan likitar sam bata da mutumci, kawai ta sallamemu mubar asibitinnan tun kafin raina ya gama ɓaci a kanta dan na kusa ɗaukar mataki, zan kaita ƙara gun na gaba da’ita.

Shiru Daddy ya yi ya najin ɗan nasa da maganganunsa, amma ya kasa ce masa uffan, ba yi da damuwar da ta wuce su zauna ta faɗa masa a ina Imran ya zama ɗan ƙasar india,? tambayoyi ne fal ke cinsa amma ya barwa ransa har zuwa ƙarfe biyar ɗin kamar yadda ta ce.

Suna zaune kowa da abin da ya ke saƙawa a ransa, lokaci na cika suka miƙe domin zuwa in da ta umarci zaman zai wakana.

Suna zuwa suka same ta da wasu mutane su uku, mace ɗaya sai maza guda biyu, ɗaya daga cikinsu kana ganinsa kasan ɗan uwan Anjali ne, saboda kamar da sukeyi har ta ɓaci, sai ɗayan da ke gefenta, shi kuma zai kai shekuru sittin babu in da ya bar ɗansa Imran, sannan macen mahaifiyar Anjali ce wato Ummy, daga gefe kuma hamshaƙiyar ce wa to Anjali.
Ba ƙaramin shork su Daddy suka shiga ba ganin mai kama da Imran sak, amma saɓanin Daddy Sudais ya fi razana, to wai mai ya ke shirin faruwa ne? ya tambayi kansa, ka zauna a yanzu zakaji komi, ɗaya daga cikin ban garan ziciyarsa ta basa umarni, jiki a mace suka zauna, bayan dogon gaisuwa da jajantawa juna ya mai jiki mai shekaru sittin ɗinnan ya fara magana kamar haka.

Da farko Allah shine abun godiya, muna godiya garesa, “na kasance ƙani a gurin mahaifin Safras, mun rasa shi shekaru huɗu da suka gabata, dalilin wani tarzoma da ta faru a yankin LANHORE, da ke ƙasar FAKISTAN, wanda ƴan siyasa da da munafukan ƙasa suka assasashi, bari na baku labari a taƙaice.

Mun kasance ƴan ƙasar fakistan, muna zaune cikin kwanciyar hankali da jin daɗi, mahaifimmu babban mutunne mu uku ne yaransa dani da ɗan uwana Salman sai ƙaramar kwanwarmu Anisha muna matuƙar son junammu sosai har lokacin aurammu ya yi in da ɗan uwana ya nai mi yar gidan minister, an kai ruwa rana kafun ayi wannan aure bayan shekaru uku da aurensu Allah ya azurtasu da samun yaro, bayan wata uku muka zaɓa masa suna Safwan ( Safras) yaro ya taso cikin so da kulawa ta ko wanne bangare sai dai sam ƙanwar mamarsa ba ta ƙaunarsa, an sha kamata ta na yunƙurin halakar dashi, amma Allah bai bata sa’a ba, a cewarta wata bare daga gefe baza ta zo ta gaje musu gida ba haka dai ɗan uwana ya ta haƙuri har yaro ya girma ya mallaki hankalin kansa, ba yi da abokan shawara wa ƴanda suka wuce iyayensa, kwatsam ɗan uwana ya zo min da wani labari mai rikitarwa, wai ɗamnu Safras ya zama jami’in ROW hankalina ya tashi sosai a lokacin, amma sai na kwantar masa da hankali, kuma na sanar masa mu godewa Allah da yasa muka sani da wuri, sannan mu bisa da adda’ar alheri, bayan na fahimtar da shi girman ƙaddara sai ya ke cemin yana so ya haɗa ɗansa Safras aure da ƴar wajena Anita, nan muka gama duk wata shawara da zamuyi, bayan kwana goma cit na ɗauki Anita mukaje gidan yayana domin mu basu dama su fuskanci juna, amma sai abunda Safras ya shaida mana ya yi matuƙar girgizamu, ba komi ya faɗa mana ba sai cewar ya samu yarinya a birnin delhi kuma ya mata alƙawarin aure, duk yadda mukaso mu fahimtar dashi sam yaƙi fahimtarmu, saboda muna da banbancin addini da kuma al’adu, to abun da Allah ya so babu mai hanasa, sai dai mun samu ƙalubale sosai a kan lamarin, kasancewar ƙanwar mahaifiyarsa ta na son haɗa sa aure da ƴar wajanta, sosai akayi rikici a wannan family kafun komi ya dai daita daga ba ya, suna zaune lafiya har da samun ƙaruwa a tsakani, sun samu yaro namiji muna ce masa, Arshad, kwatsam muka samu sanarwar acikin jami’an Row ɗin da su ke bakin iyaka ankai musu hari, kuma acikin wa ƴan da bom ya tashi da su hadda Sarfas, mun shiga tashin hankali ba kaɗan ba, a sadiyar haka zuciyar ɗan uwana ta buga, mahafiyarsa kuma a halin yanzu ta na kwance ba lafiya, wannan shine taƙaitaccen labarin Safras da ahlinsa.

“To yau kuma ga shi Allah ya dawo mana dashi bayan cire da da mukayi da sake ganin sa, sai dai kuma da alama ya samu matsla a cikin kansa, tunda dagamu har matarsa babu wanda ya gane a ciki.

Galala, Sudais ya yi yana kallon ikon Allah, ya kalli wancan ya kalli wancan, har yanzu ya kasa gane mai suke nufi da ɗan uwansa Imran,? idan akan sa suke magana ta ya zasu ce shekarunsa huɗu da ɓata? sannan yaushe ya yi aure hadda ɗa busu saniba, nooo shine abun da ya fi to daga bakinsa ba tare da ya shirya ba.

Murmushin jin daɗi da kwanciyar hankali Daddy ya yi bayan gama jin wannan labari, hankalinsa ya kwanta jin ba abunda ya yi tunani bane, tunda ai shi ya na tare da ɗansa tun haihuwarsa.

Gyara zama ya yi ya fuskanci mutumin da ya kira kansa da ƙanin mahaicin ɗansa, gudan jininsa, “naji duk magan ganunka bawan Allah, sai dai kasani kunyi kuskure babba, domin dai wannan dake kwance a wannan asibiti ba ɗanku bane, hasalima bai sanku, bai taɓa ganinku ba, wannan ɗan uwansa ne, ya nuna musu Sudais, ya ci gaba, ” su uku Allah ya bani, idan kuna da jaa a magata ku bani zuwa gobe, zan gabatar muku da duk wata shaida da ta ke nuna cewar Imran ɗanane na cikina, wanda muka haifa da matata, bawai ɗan riƙo ba.

“Bawan Allah kar muyi haka da kai, domin Safras jinimmu ne, har gwaji NDA sai da muka masa, duk wata shaida muma muna da ita a hannu, Barrister Sudais da ransa ya gama ɓaci dajin wannan rainin hankali ya miƙe ya kalle su ɗaya bayan ɗaya ya ce mu haɗu a kotu gobe, sai muga waye zaiyi nasara, dan naga kuma kuna buƙatar ganin likitan kwakwalwa, tsawa Daddy ya buga masa jin yana ne man zagin wa ƴan da suka girme masa, duk da shima ransa ya ɓaci sosai amma bazai bari ɗansa ya raina na gaba dashi ba. Kama hannunsa ya yi suka fi ce daga office ɗin ba tare da sun tsaya sauraron maganganun da suke musu ba.

“Wai mai yake faruwane Daddy,? su waye wa ƴannan ɗin? mai suke nufi damu? ni dama tunda naga yadda likitannan ta ke ta kunta nasan akwai abun da ta ke shiryawa, ya zama dole mu ɗau mataki a kanta, zan kaita ga nasama da ita.

Kallonsa kawai Daddy ya ke yi tunda ya fara magana ba ya ko tsayawa, tabbas idan da waccar maganar ce ta fi to fili bai san da wani idonu zasu kalli yaran nasu ba, to amma ya zama dole bayan dai dai tar komi su sanar dasu duk wani abu da ya faru a wancan lokacin.

Maryama ce kwance a ɗakin Sudais ta na kuka mai cin rai, a duk lakacin da ta tuna da Innarta ta ji tashin hankali sai kuma ta tuna ta nada Sudais sai hankalinta ya kwanta, to gashi ma ya na neman juya mata baya, ya zata yi idan har ya kasance mafarkinta na jiya ya tabbata? lalle rayuwarta zata shiga matsala babba, domin a halin yanzu bazata iya rayuwa babu mijinta kuma abun sonta ba, a ɗaya bangaran kuma ga ta kurawar Sahla, gaba ɗaya yanzu ta dawo gidan da zama, babu abun da ta ke yi sai takura mata, ta mai da ita kamar ƴar aikin gidan, bata bari ta huta ko ƙaɗan, Mommy kuma tana ganin komi amma ba ta taɓa tsawatar mata ba, Allah shine gatanta sai kuma Samha, juyi ta yi ta sake rumgume fillow da ta ɗaura kanta akai ta na shaƙar kwamshi turarensa.

A bangaran Mommy jira kawai take Sudais ya dawo ya saki yarinyar can kodan ta samu kan ahlinta da a yanzu wasu daga ciki suka juya mata baya akan laifin da ba nata ba, gara kawai ta yadda ƙallon mangoro ta huta da ƙuda.

“Zagaye falon take taje ta dawo, ta kasa tsayawa waje guda, ya zama dole a wannan karon ta yi nasara, domin ba zata yadda da faɗowa ba a karo na biyu, tashi Sakku ta yi ta ƙarisa wajan da mahaifiyarta take tsaye, sai Anwar dake zaune gaba ɗaya abun duniya ya masa yawa, wai dama Mommansu ƙanwar mahaifin Safras ce? lalle duniya abun tsoro ce, shikan tunda ya gane Safras ɗn uwan sane bazai ƙara yadda a cutar dashi ba ya yi kuskure a baya amma yanzu ya tuba ya bi Allah.

Sakku ta na ƙarisawa ta rumgume mahaifiyarta ta baya ta ce, “gakiya Momma na gaji, idan bazaki iya komi ba kawai ki bar ni na yi aurena, ga masoya ina da su kinsa sai walaƙanta kaina na ke yi akan wani can da bai san dani ba.
Juyowa Momma ta yi ta kama hannun Sakku ta zaunar da’ ita sannan ita ma ta zauna, sosai sukayi magana a kan yadda komi zai ta fi yadda ta ke so, daga bisani kowa ya tashi da sa kalar tunaninsa, Anwar ya yi alƙawarin wargaza wannan shiri na mahaifiyar tasu amma ya bar komi a ransa tukunna har zuwa ya bar asibitin.

Duk wasu shaidu da takaddu Dadda da Sudais sun ta nada shi, jiran lokaci kawai sukeyi, ta ban garansu Anjali ɓa hakanne.
A kuma wannan lokaci Imran ya shirya barin asibitin ko ta halin ƙaƙa, yana wannan tunanin ta buɗe kofa ta shigo, zama ta yi sosai a kusa dashi kamar zata shige jikinsa, miƙa hannu ta yi ta riƙo hannunsa ta na mrza ƴan yatsunsa, a hankali ta kwanta akan girjinsa ta fara magana cikin yaran hindu, “wan har yanzu Meh Buba zaka tunani ni ba, ? ni ce fa matarka abun sonka, sannan ko baza tunani ba ka tuna da ɗanka abun sonka, galala Imran ya yi yama kallon ta baki a sake, lalle wannan ba ƙaramar ƴar dirama ba ce, ya zama dole ya koya mata hankali, janye jiki ya yi daga gareta jin ta na son sanja salo, da sauri ta sake saka hannu ta riƙo sa sosai, da sauri ya waiga ya wanke mata fuska da mari mai rai da lafiya, har sai da ya kisa faɗowa, fararan idonsa da suka jaawur ya zuba mata ya hau mata kashedi, karki “kuskura ki sake gigin taɓani kinji na faɗa miki, wannan shine last da sake hakan ok? sannan ko ki sallemeni ko karki sallemeni a yau kuma a yanzu zan bar wannan asibitin banza saka rai kawai, ya sa kai ya fi ce ya bar ta tsaye a wajan sake da baki ɗauke da matsanacin mamaki.

 

Ba tare da su Daddy sun san mai ya faru ba kawai sai gani sukayi an basu ta kaddar sallama, Sudais ya so su tsaya su kashe wan can kes ɗin amma Daddy ya hana faruwar hakan, a cewarsa kawai subar ƙasar baki ɗaya..

Da gudu Sudais ya ƙarisa ya rumgume ɗan uwansa da mahaifinsa daga nan suka wu ce gida dan zuwa gobe zasu kuma gida NIGERIA

DA YAUSHE AKA YI HAKAN?
MAIYASA AKA BASU SALLAMA BA TARE DA SANIN ANJALI BA?
SHIN IMRAN YABAR INDIA KENAN KO KUMA ZAI DAWO?

WRITING BY OUM SHAHEED

Leave a Reply

Back to top button