Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 11

Sponsored Links

Chapter 11

A speed motar tazo kusa da napep ɗinda nake ciki sai kuma ta rage gudun ta jinayi kaman nasaki fitsari saboda tsaban rudewa danayi,sauke glass din motar naga anyi wani mutum yaleƙo da kansa yace”ƴan mata gyara mayafinki ko gyaɗa masa kaina kawai na iyayi kaman wata ƙadangaruwa bayan wucewar motan nasauke wata ƙatuwar ajiyar zuci da godiya ga Allah daya saka ba wannan masharrancin nan ne yabiyo bayana ba.

A gajiye na isa gida sallama ɗauke a bakina na shinga tadda Anna nayi zaune a tsakar gida da alama girki ta gama take shara,rungume nayi cike da farin cikin samunta da nayi cikin ƙoshin lafiya”nayi kewarki Anna nafaɗi ina saka ƴar dariya”nima haka tace dani tana shafa kaina cike da kulawa maza jeki kiyi wanka kizo”da to na amsa ina tambayarta ina su khadija suke?
“Kinga kabiru ne yazo ɗazu yafita dasu yawo,takare maganan tana kwashe sharan da tatara hmm kawai nace dan harga Allah banason fitan da kabiru yake dasu dan de kawai karnai maganane Anna taga kaman kyautatawan da yake manane banaso,niko ba haka bane gareni kawai ina jiyewa wulakancin mutanene tunda kowa kallon rashin uba dakuma dangi yake mana.

Ahmad tunda yabar bakin ma’aikatar nasu yakwanta jikin kugeran motan yayi lamu khalid nata masa magana amma ina bajinsa yake ba,sabida zurfi dayayi a tunanin da yake dakuma jinjina karfin hali irin tawa wai yarinya kaman wannan mai karancin shakaru ta iya ɗaga hannu batare da shayi ko tsoron komai ba tamari saurayi irin wannan ɗan manya wayanda ƴan mata ke mutuwa a kansu mari lalle wannan idan mutum yasake mata fuska dayawa zatayi rashin kunya idan kaganta kamar wata mumina amma da alama shirin kunyace fal cikinta.

Usman a fusace yashiga main falon saboda ɓacin rai dayake ciki bema kula da mummy ɗinsa dasuke zaune da sister dinsa ba,sai dq mummy mariya tace”my son lafiya na ganka haka waya taɓamun kai?
“Mummy wai kamanni wata figigiyar yarinya ta mareni can you imagen?wai ni mummy miƙewa tsaye hajia mariya tayi ta kafeshi da ido cike da ɓacin rai tace”waye ubanta a ƙasar nan dazata ɗaga hannu ta mareka,watsa hannun sa yayi alama shima be sani ba cigaba tayi da cewa ko waye ubanta inaso ka tattaka shegiya inga uban daya tsaya mata duk wanda yama kan kara kai masa na rodi ban yarda koda wasa kabari wani yataka kaba muna muke da ƴaƴan banki a hanu,murmushi yayi yana cewa”that my mom shisa nake kara sonki wallahi,dariya sukai baki ɗaya banda basma dake faman taɓe baki tana daddana waya.
Ita kuma wannan menene matsalarta mummy?
Taɓa baki hajia mariya tayi tace”ai kasan tatsuniyar gizo baya wuce ƙoƙi wai Ahmad take kira a waya kuma yaƙi ɗagawa,girgiza kansa yayi ya tashi daga kugeran da yake zaune yazo ya zauna kusa da ita yariƙo hannun ta yace”haba sister karki bada mata mana ki zauna namiji na ɗaya nawasa da hankalin ki,bashine ze kira kiba ke kikira ma baze ɗaga ba ai wannan ci bayane cike da masifa ta miƙe tace”kaga malam karka wani cikani da surutu iba ruwanka dani ne?dawani zaka tsuma bakinka lamarina banason shisshigi tawani hayayyaƙu masa kaman zata cinyesa ɗanye tawu saman ɗakinta,hajia mariya na kiranta amma ko nuna tajita batayi ba”rabu da ita mummy ƴar wahala irinta yaushe zaka tsaya namiji na garata in banda kauyanci ta rashi wayo irin tata wai wanda zamusu auren haɗi take irin wannan haukan akan sa ni wallahi mummy kima faɗawa daddy wallahi karma yace nima ze hadani da wata ƴar abokonsa dwn wallahi ba yarda zan ba.

Aisha:sai da mukai sallar magriba sannan kabiru ya dawo dasu khadija da sayayya niƙi niƙi sai murna suka mubaraq ya hau cewa”Anty aisha mun hau lilo da doki kai anty harma da mota ƴar dayiya nayi na maijin daɗin ganin su cikin farin ciki nace”lalle kace yau uncle kabiru yasha surutu dariya yayi khadija tace”wallahi kuwa kaman kinsani anty bakin sa yaki rufuwa har muka dawo gida bebar surutu ba,au anty na mance uncle kb yace kisa mesa a waje,kicin kicin nayi da fuska Anna ta kalleni ta girgiza kai tace”yanzu Aisha ko saboda yanda wannan bawan Allah yake hidima da ƴan kanneki yaci ace kin sassauto da zuciyarki ko bakomai ai zuciya nason mai kyautata mata,gaskiya anna ta faɗa dan duk rashi kulashi danake hakan be hanashi kyautatamun ba,da duk wani abu dayasan zanyi farin ciki yana kokarin yimun sai de indan baya gari dan aikin sa a lagos yake.
hijabi na nasaka nafita tsaye nasame shi ya jinjina jikin motarsa yana ƴan danne danne da waya yana hangoni yayi sauri maida wayan aljihun wandon sa fuska sake yake kallo na,ƙasaso inda yake nayi nace”amincin Allah ya tabba gareka,faɗaɗa murmushin fuskan sa yayi yace”amin harda ke gaidashi nayi ya amsa yana cewa lalle yau wace ranace haka?dan ɓata fuska nayi ɗan taɓa hira mukai muna sallama sai ga fadila tana kallona da kabiru tayi kicin kicin da fuska tawuce tashiga cikin gida ba kotsaya ta kalle mu ba,girgiza kansa yayi yace kinga shiga daga ciki dan naga alama wannan ƙawar taki ita ke hana ruwa gudu ɓata fuska nayi zanyi magana yabuɗe kofar mota ya dauko wata leda ƙatuwa mai tambarin wajen sayan kayan yamiƙa mun yace bawa Anna ki isarmun sakon gaisuwata gareta kafin na wuce gobe in sha Allah zanyi kokarin shigowa mugaisa.

“Yah kabir bade har komawa zakayi gobe ba?”kinaso na zauna ne?ya tambayeni yana tsareni da ido cike da jin kunya nace”sai da safe mun gode Allah yakara buɗi”Amin yace yana bude motar yashiga nima nashiga cikin gida.

Fada Anna tayi tamun maiyasa na amshi kayan duka ai wannan hidima tayi yawa,dakyar tayi shiru ɗaki muka shiga da fadila nan muka baje kolin hira tace”kawata albishiriki amsa mata nayi da goro tace”nasami aiki cike da murna na rungumeta nace”masha Allah kice kin kusa zama mai kudi cike da zolaya nayi maganan,ga mamakina sai naga ta washe baki tace dani”wallahi kaman kinsani dan nasami aiki a wata ƙungiya mai zaman kanta kuma da alama akwai romo a wannan tafiya,kungiya na maimaita a zuciyana nace”kungiya kuma ƙawata nide gakiya ina jiye miki abunda zakizo kiyi da kinsani daga baya.

Shiga ƙungiya kinsan ko wace ƙungiya tana da ƙa’idojinta dakuma manufofinta shin macece ƙa’idar ƙungiyar da kika shiga kuma fa idan kinshiga ƙungiya halartar taro wabijinine gareki koda yaushe kuma ko aina za’ayi pls ƙawa nide haka kawai naji sam shiganki ƙungiya be kwantamun araina ba.

Ture hannuna tayi daga riƙon da namata tace”gaskiya kinga Aisha ina da burin yin ƙudi bafa zan zauna cikin talaucin nan da aka haifemu ciki muka girma cikin ta ba,kowa da kika gani yana da burin yaga cangi a rayuwar sa dan haka zancan ina fita a ƙungiya be taso ba kede kawai kibini da addu’a ko bakyason ganina cikin canjin rayuwane,na dauka zakiyi farin ciki idan kinji nasamu canji.

Jiki a sanyaye nace”ba haka bane kawata Allah yasanya alheri,dariya tayi tace”amin daga nan muka shiga hiran duniya nan naji tace wai ashe matar nan bata hakura ba saida tasake zuwa ɗazu wai so take ki soma aikin wanki gobe asabar zata aiko da driver yazo yakaiki can gidan nata,”amma ke waya fada miki dan ni bamuyi haka da ita ba.

“Anna ce take faɗamun yanzu amma dan Allah kawata kar kije,hmmm”haba kemade fadila ai ba abunda ze kaini nida nasami aiki kuma da alama nasamu karɓuwa daga masu wajen mai zai sake kaini wanke ɗan kamfan mace ƴar uwata sabida tsaɓan ƙazanta irin ta ƴaƴan masu kuɗi ko pad idan sunyi amfani haka suke bari jikin pant ɗin saide nina cire”Allah de yabudawa kowa amma talaka naganin tasku a rayuwa dakuma rashin daraja wajen masu kuɗin.
“Barcewa haka fadila muma talakan munada daraja bawai bamu da ita bane sannan muna da baiwa da Allah yayi mana saide wasunmu suke zubar da daraja da Allah yamusu wajen maida masu kuɗi ababen bautarsu madadin suroka a wajen Allah amma sai kiga sunje suna rokon masu kuɗin taya zasu ganmu da daraja wallahi fadila matukar mutum yaroƙa wajen Allah sannan ya jajirce wajen neman nakansa da tsayuwa tuƙuru zesami Allah baze taɓa barin sa ba.

Washe gari yakama asabar tunda mukai sallah asuba na tasa su khadija gaba muna tilawar al-qur’ani mai girma wajajen karfe takwas muka fatiha muka ci ɗumamen tuwo da anna takawo mana bayan mungama muka daura da ruwan bunu muna hira akai sallama gidan namu daga bakin ƙofa kafin wani daga cikin mu yaleƙa yagani sai ga maman salmanu da tafaɗo mana ɗaki tana washe tace”wani mai motane yake sallama da Aisha wai hajiace ta turoshi,fuska na ɓata nace”amma maman salmanu matsayin mu na musulmai ai yaci kimana sallama kafin kifaɗo mana ɗaki haka idan sallamarce take miki wuyan faɗin to kice gafaranku mana,ƴan soshe soshe tafara cike da kunya ruwan bunun anna ta zuba a kofi ta miƙa mata ta amsa tana kurɓa zata zauna nace kinga tunda ke akabawa sakon koma kice bazan jeni ba,daga Anna har maman salmanu zubamun ido sukai suna kallon na yayin da nikuma jikina yayi sanyi dan gani irin kallon da Anna ke jifana dashi nasan nagargadine..

 

 

ALLAH YASA MUDACE
[5/2, 8:34 AM] Xeenat: 💕 *AUREN WUCIN GADI*💕

Leave a Reply

Back to top button