ADABIN BAKA

KA’IDOJIN RUBUTUN HAUSA DA KALMOMIN HAUSA.#002.

Sponsored Links

       KA’IDOJIN RUBUTUN KALMOMI DA 

           YADA KAMATA KA SANI, KAFIN      

                                RUBUTU       

                  CIKIN HARSHEN HAUSA.


                     KASHI NA BIYU

Gabatarwa 

   Daga 

by didigi


Tsangayar da ta himmatu wajen kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al’ummar hausawa.

  by

 msz

ai dai duk da gyare-gyaren da aka yi wa ka’idojin rubutun da kuma kalmomin Hausa, sai ya zamanto tsugune ba ta kare ba, wato ba rabu da Bukar ba, an haifi Habu, inda al’amarin ya koma ana kukan targade sai ga karaya, domin an dada rikita mutane ne, wanda ya sa a rubutu guda sai ka ga ana amfani da tsohuwar ka’ida da kuma sabuwar ka’ida. 


  Haka abubuwa suka yi ta tafiya a kudundune, ba tare da kuma an samu mafita ba, wannan matsalar ta ci gaba da ci wa masana ilmin harshen Hausa tuwo a kwarya. Da tura ta kai bango ne, ganin ruwa yana neman karewa dan kada bai gama wanka ba, ma’ana ganin rubutu cikin harshen Hausa na neman ya ci tura, sai masana ilmin harshe na kasar Jamhuriyar  Nijar suka gayyaci takwarorinsu na Najeriya, inda a nan suka shirya wani gagarumin taro a birnin Yamai, a Cibiyar Harshe da Tarihi ta Sarrafa Adabin Baka a Turance (Centre for Linguistic and Historical Studies by Oral Traditions ), a da su jagorancin Majalisar Hadin Kan Afirka (OAU), wanda yanzu ta

dawo Tarayyar Afrika (AU), an yi taron ne tun daga ranar 7 zuwa 12 ga watan Janairu, a shekarar 1980.


Daga farko sun daidaita kawunansu a Bakake da Wasulla da Auren Wasulla da kuma Tagwan Bakake, kana daga bisani suka daidaita ka’idojin rubuta kalmomi.

            Ga abubuwan da suka zayyana kamar haka:

 

BAKAKE

Bakaken da aka yarda da su, su ne:

 

KANANA: b, b’(mai lankwasa), c, d, d’ (mai lankwasa), f, g, h, j, k, k’(mai lankwasa), l, m, n, r, s, t, w, y, ’y, z 

MANYA:   B, B’ (mai lankwasa), C, D, ‘D (mai lankwasa), F, G, H, J, K, K’ (mai lankwasa), L, M, N, R, S, T, W, Y, ’Y, Z

 

WASULLA

 

KANANA: a, e, i, o, u

MANYA:  A, E, I, O, U

 

AUREN WASULLA

 

KANANA: ai        au         maimakon      ay      aw

MANYA:   AI      AU       maimakon       AY    AW

 

TAGWAN BAKAKE

KANANA:  fy, gw, gy, kw, ky, kw(mai lankwasa), ky (mai lankwasa), sh, ts

MANYA:    FY, GW, GY, KW, KY, KW (mai lankwasa), KY (mai lankwasa), SH, TS.

Anan zamu diga aya sai kashi nagaba sai mu dora inda Aka tsaya.


                      Domin Karin

 Domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu, 


Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.


Leave a Reply

Back to top button